Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 5
Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 5: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 5. *MAGANIN RAGE TUMBI KODA YAKAI GIRMAN CIKIN YAN BIYU INSHA ALLAH KI GWADA…
3,349 words
*MAGANIN RAGE TUMBI KODA YAKAI GIRMAN CIKIN YAN BIYU INSHA ALLAH KI GWADA MAGANIN AUNTY ZEE DA YARDAR ALLAH ZAKI GODE* *Maganin Rage Tumbi 7k*
*MAGANIN BASUR KODA YAKAI GA YIN TSIRO INSHA ALLAH AGWADA ZA ADACE* *Maganin Basur 5k*
*MAGANIN CIWON SUGAR CIKIN IKON ALLAH MUNBADA ANRABU DASHI* *Maganin ciwon Sugar 10k*
*08162859027* *09070027627*
*Location*KATSINA STATE*
*ACCOUNT NUMBER*
*8162859027* *ZAINAB SHU AIBU* *OPAY*
*OR* *3968303018* *FCMB* *ZAINAB SHU AIBU*
*DAN ALLAH IN KINSAN BAKI SHIRYA BA KARKI YI MAGANA DAN ALLAH KIBARI KI SHIRYA AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA TAKUCE SAI KUNZO*
Page 25
Ko da Baba ya fita Gaddafi ya nemo, a gurin masu shayi.
Gaddafi ya ce "lafiya kuwa?"
"Ofishin 'yan bijilanti zaka raka ni"
"Amma a daren nan? Me ya faru?"
"Mu je za ka gani"
Gaddafi ya bi Baba zuwa gurin 'yan bijilanti.
Baba ya shigar da ƙorafi, a kan zargin yin lalata da yarinyar sa.
Gaddafi ya ce "Baba, babu tabbacin abin da ka ke faɗa fa?"
"Babu tabbaci, aka same ta a ɗaki tare da shi sama da awanni?"
Gaddafi ya ce "Amma ai ka san ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba"
"Ka rufe mini baki Gaddafi" Gaddafi ya yi shiru, 'yan bijilanti suka bayar da mutum biyu, tare da Gaddafi aka tafi taho da Buzu.
Hankalin Habu ya yi mummunan tashi, ganin wai an zo a tafi da ɗan uwansu gurin hukuma. Cikin damuwa ya ce "Wallahi ina da tabbacin babu abin da ya yi mata, ba shi da cikakkiyar lafiya ƙwaƙwalwa ne, amma ba wani abin ya yi mata ba, ai mutane sun ga a yadda muka tarar da su"
Jami'in bijilanti ya ce "To ka ɗaukko takardar shaidar ba shi da hankalin, ka haɗo da ita mu tafi, ko ce maka aka yi mahaukaci ba zai iya wani abun ba" sauran buzayen ma duk hankalinsu a tashe.
Haka aka tasa Buzu da Habu, da wasu daga cikin buzayen, suka tafi ofishin 'yan bijilanti.
Shugaban gurin ya ce "Waye daga cikin su, aka tarar da su a ɗakin? Ina kuma ita yarinyar?"
Baba ya ce "Tana gida a sume"
"A sume kuma? Shekararta nawa?"
"Shekara ashirin da ɗaya"
"Ikon Allah, to waye a cikin su?" Gaddafi ya nuna Buzu.
"Kai malam ya aka yi aka tarar da kai daga kai ita a ɗaki, tsawon awanni, sauke rawanin nan na fuskarka ina magana kana kallona"
Habu ya ce "Yallaɓai ba shi da cikakkiyar lafiya fa, wallahi taɓin hankali ne da shi, ina da tabbacin babu abin da ya haɗa shi da yarinyar nan"
Sule ya ce "Ba ma sa shiri da ita, wallahi rashin fahimta aka samu, na ga kwanon abinci a ɗakin, ina kyautata zaton ma abinci ta kai mana, akwai dai abin da ya faru tabbas"
"Ba da ku nake magana ba, ka buɗe baki ka yi mana bayani, ko kurma ne?" Shugaban bijilanti ya yi maganar yana kallon Buzu. Amma bai ko motsa ba, balle ya yi magana.
Ya sake tsuke fuska ya ce "Sauke rawanin nan kafin na saka a sauke maka shi yanzun nan, ka ƙunshe fuska kamar ɗan taliban" ƙura masa ido ya yi bai yi magana ba.
Habu ya ce "Ka cire rawanin dan Allah, ka yi maganar abin da ya faru"
Sule ne ya kai hannu zai sauke masa rawanin, amma ya riƙe masa hannu.
"Dattijo, alamu sun nuna fa mutumin nan da gaske mahaukaci ne"
Baba ya ce "Wallahi ko dawanau ce a kansa sai an bi mini hakkina, dama 'yan kwanakin nan shi ne yake hure mata kunne, sai ta kai bayan magariba a waje ba ta dawo ba. Ta ƙi aure fafur kowa ya zo ba ta so" Ayshacool "To kai Baba ya ka ke so a yi? Kana gani ya ƙi magana, ita yarinyar ba ku zo da ita ba, ni wannan case a bari gobe in Allah ya kaimu ku tafi gurin 'yan sanda".
Baba ya ce "Duk fa wata shaida da ake nema, ta tabatta tun da abin da suke yi kenan, sai ya aure ta ya je su ƙarata" gaba ɗaya suka kalli Baba. Cikin tashin hankali Habu ya ce "Dan Allah dattijo ka yi haƙuri, wallahi ba su saba yin komai ba, wannan karon ma rashin fahimta ne, Nana mutuniyar kirki ce, shi kuma ba shi da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa, dan Allah ka yi haƙuri"
"Wallahi ba zan haƙura ba, daga nan har kotun ƙoli mu je, a karɓa mini hakkina na ci mini mutunci ta hanyar yin lalata da 'ya ta, ana daf da ɗaura mata aure" Gaddafi dai ya yi shiru yana kallon ikon Allah, bai ta taɓa tunanin Baba zai ɗauki irin wannan matakin ba.
"Dan Allah ka yi haƙuri, ka ga nan ba ƙasarmu ba ce ba, idan aka kai mu gaban shari'a wahalar da mu za a yi, dan Allah ka yi haƙuri" Sule ya yi maganar cikin magiya. Baba ya fututtuke ya din ga bala'i, buzayen nan su na ba shi haƙuri.
"Payer la dot" ya furta cikin harshen faransanci yana kallon Habu. Habu ya waro ido, shi ma ya juye harshe, suka koma magana da french.
Jiki a sanyaye Habu ya kalli Baba ya ce "Nawa ne sadakin?"
Gaddafi ya ce "Baba wai da gaske aura masan ita za ka yi?"
"Eh mana, tun da haka ta zaɓa. Ai wallahi ba za ta zubar mini mutunci a idon duniya ba, dan na san tun da Rabi ta san maganar nan babu wanda ba zai ji a ciki da wajen unguwar nan ba, har a dangi sai ta yi ta yamaɗiɗi, tun da haka ta zaɓa ta samu"
Baba ya mayar da idonsa kan Habu ya ce "Ko ma nawa ne, ku bayar da sadaki da safe ya zo ya ɗauke ta".
Habu ya sake kallon Buzu, cike da damuwa ko zai canza magana, amma ya ga babu alamar hakan.
Hatta 'yan bijilantin, sai da su ka ba shi haƙuri, da rarrashi amma fafur Baba ya ƙi yarda kamar wanda ake ƙara zugawa.
Habu ya ce kuɗin hannunsa ba su da yawa, bari ya kira waya a kawo kuɗi.
Shugaban bijilanti ya ce ba za ɗaura auren nan a ofishin bijilanti ba, sai dai a tafi gidan mai unguwa, a yi a gaban jagororin unguwa.
Haka kuwa a ka yi, abin da Baba bai sani ba, da kansa ya ƙara tagayyara Nana, da yayata maganar.
Naira dubu ɗari biyu Habu ya bayar, a matsayin sadakin auren Nana Asma'u ƙarfe sha biyu saura na dare.
Gaddafi dai Baba ya ƙure masa mamaki, duk da ya san har da ziga a cikin lamarin na Baba.
Sai dai kuma Gaddafi ya yi mamakin yadda buzaye, masu gadi suka iya biyan har Naira dubu ɗari biyu a take matsayin sadaki. Nawa ake ba su kuɗin gadin da har su ka ci suka tayar da kan biyan wannan kuɗin haka?.
Can gida kuwa Nasiru ne yake ta tattaɓa Nana cikin tsoro, saboda sanyin da jikinta ya yi, kamar gawa. Sai can wajen ƙarfe goma na dare ta farka. Ta saka Nasiru ya kawo mata ruwa ƙofar ɗaki. Da rarrafe ta fito bakin ƙofar ta yi alwala. Ko yinƙurawa ba ta iya yi balle ta tashi, saboda wani irin jiri da take yi. Da jikin kaya ta jingina daga zaune ta yi salla. Ta idar ta sake kwanciya.
Nasiru ya ce "Nana ba za ki ci abinci ba? Ga awara na sayo miki mai zafi" amma ya ji shiru. Ya duba sai ya ga ta koma yadda take da farko, hannunta zuwa ƙafafuwan ta duk sun ƙandare sun lanƙwashe.
Sha biyu da rabi Baba suka nufo gida, Gaddafi ya ce "Amma Baba ba a yi ganganci ba kuwa? Kawai ka aura mata mutunen da baka san ma wani iri ba ne ba, dubu ɗari biyu fa suka bayar na sadaki ba ka tunanin ma ko wasu marasa gaskiyar ne?"
"Gaddafi wannan abin da na yi shi ne kawai maganin abin da yarinyar nan take aikatawa. Sau nawa ana yinƙurin aurenta tana ƙi? Mutumin nan da ya fito fa cewa ta yi za ta gudu, ko kuma ta kashe kanta a kan auren, amma ta san ta je ɗaki gurin namiji. Wannan ne kawai hanyar da zan bi na aurar da ita. Muddin za a din ga saka lokaci ba za ta taɓa bari a yi ba".
Gaddafi ya numfasa ya ce "Haka ne, amma ba na tunanin za ta bi maza ko makamancin haka."
"Ba a shaidar ɗan yau Gaddafi. Allah ya zaunar da ita lafiya"
Gaddafi yana son sake yin magana, amma ya fasa ya yi shiru. Ayshacool Mama tamkar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, haka ta ji bayan da Baba ya yi mata bayanin abin da ya faru. "Wallahi ka yi dabara baban Jamila, wallahi da haka za ta ci gaba da zubar mana da mutunci a idon duniya, kuma auren ba za ta yi shi ba, duk wanda ya zo haka za ta ci gaba da korarsa. Kuma shi kansa Alhajin idan ya ji abin da ya faru ba zai yarda ya aure ta ba, ba ma ita kaɗai ba, duk wanda ya ji maganar nan ba zai yadda ya aure ta ba, amma tun da aka yi haka ka ga an yi maganin kowa ma. Kuma asiri ya rufu, tun da ta yi iƙrarin kashe kanta, ko guduwa muddin aka yi mata wannan auren".
"Ai yanzu sai ta yi duk abin da ta ga dama, na yi wa tufkar hanci. Har Gaddafi yana wani cewa ba za ta aikata ba, ba zata aika ta ba uban me ya kaita ɗakin masu gadi? Ƙila ma Allah ne ya tashi tona mata asiri hakan ta faru"
Mama ta ce "To Allah dai ya kyauta"
Jamila kuwa jikinta ya yi sanyi sosai, sam ba ta taɓa tunanin Baba zai ɗauki wannan matakin ba. A yanayin yadda suka tarar da Nana, bai yi kama da wadda ta aikata wani rashin gaskiya ba.
****
Cikin matsanancin ɓacin rai sule yake magana, "Habu yanzu da ka yarda aka yi wannan auren ya zamu yi da su gaba ɗaya?"
Habu ya ce "Amma ai ka na ji, da kansa ya ce a biya sadakin ko?"
"A'a ni ya za ayi na sani, tun da ba iya faransanci na yi ba, kuma da ya ce ka biya masa sadakin sai ka biye masa? Mutumin da ba hankali ne da shi ba, kai yanzu idan aka saka maka takobi a wuya, za ka iya nuna danginsa ko ahalinsa ne? Daga taimako sai jajubo mana wahala? Aure ai ɗawainiya ne, shekarata nawa a Nigeria iyalina su na can sahara, ban kawo su nan ba, yanzu ya ka ke so mu yi?"
Habu ya kwantar da murya ya ce "Dan Allah Souley ka yi haƙuri, duk ba abin ɗaga hankali ba ne ba, idan aka samo wani gidan gadin, sai ya fara aikin gafin kafin a san abin yi"
Tamkar ya gaurawa Habu mari ya ce "A haka zai yi gadin? Mutumin da sai ya yi sati bai ce uffan ba, aikin gadi fa ba buɗewa da rufe ƙofa ba ne kawai"
"Ai ba hauka yake tuburan ba, kuma ko a nan ai mu na tafiya mu bar shi, kuma ya yi gadin, dan Allah ka yi haƙuri ka daina ɗaga muryar nan, zamu san abin yi da yardar Allah"
"Ni wallahi har mamaki ka ke bani Habou, daga tsintar mutum sai wahala ka ke da shi, kamar wani tsohonka, na ga yadda za ayi ai da wannan badaƙalar"
Habu ya dafa kafaɗar Sule ya yi murmushi ya ce "Babu abin da zai faru sai alkhairi in sha Allah, kuma Allah ya na gani taimako muka yi, ba zamu wulaƙanta ba". Da ƙyar Habu ya samu ya shawo kan Sule.
*
Nana ba ta sake tashi ba, sai washegari ƙarfe bakwai na safe, shi ma Nasiru ne ya tashe ta, kamar jiya a bakin ƙofar ɗakin su ta yi alwala, ta yi sallar asuba a zaune. Yana zaune ta idar, tana idarwa ya ce "Nana kar ki kwanta, ga kokona ki sha ki daina wannan baccin, jikin ki fa sanyi yake yi"
Ta girgiza kai ta ce "Na ƙoshi Nasiru, jikina babu ƙwari nima ji nake kamar mutuwa zan yi"
Da sauri ya ce "Ba mutuwa za ki yi ba, yunwa ki ke ji, ki sha kaɗan" ganin yadda ya damu sosai da sosai, ya sanya ta karɓa ta sha kaɗan, ta ajiye ta fara ƙoƙarin kwanciya.
Suwaiba ce ta shigo ɗakin, tare da rangaɗa guɗa ta ce "Amaryar tsakar dare, mai doki ya koma kuturi, ba a auri mai gida ba an auri mai gadi, to Allah ya sanya alkhairi".
Nana ta ɗaga jajayen idanunta ta kalli Suwaiba, ta mayar da idonta kan Nasiru ta ce "Nasiru mafarki ne wai?"
Ya girgiza kai ya ce "A'a a zahiri ne"
"To me Suwaiba take cewa ne?"
Cike da ƙuruciya ya ce "Wai jiya da daddare aka yi auren ki"
"Aurena kuma? Kamar yaya?"
Ya ce "Wallahi nima ban sani ba" Suwaiba ta cigaba da dariya, tana ɗaukar jakar kayan kwalliyar ta.
Baba ne ya shigo ɗakin, ya tarar da Nana a zaune, ga Nasiru a gabanta da kofin koko.
"Yauwwa kin tashi kenan? To ki buɗe kunnen ki da kyau, ki saurare ni"
Ta zubawa Baba manyan idanunta, da suka yi kama da na Japanese sai dai nata manya ne. Ayshacool **** "Jamila" Nana ta furta da ƙyar, saboda yadda take jin tamkar an ɗora mata wani ƙaton dutse a kanta.
"Na'am"
"Da gaske Baba yake yi, an ɗaura mini aure, ko kuwa mafarki ne?"
Jamila ta ɗan taɓe baki ta ce "Da gaske ne mana, zai yi miki ƙarya ne?"
Ta sake cewa "Kuma da buzayen nan?"
"Eh fa"
"Waye a cikin su?"
Jamila da ta fara ƙosawa da tambayoyin Nana ta ce "Ni fa ban sani ba, tun da ba taɓa zuwa na yi ba balle na san su. Ke ma Nana me ya yi miki zafi, da za ki je ɗakin masu gadi me ki ke yi a ciki? Dama ana iƙrarin kin ƙi yin aure, yanzu ga abin da ki ka ja wa kanki nan"
Sanin ko ta yi bayani ba fita za ta yi ba, ya sanya ta jan bakinta ta tsuke. Ta ci gaba da sauke numfashi da ƙyar. Tiryan-tiryan ta shiga tuno abin da ya faru, sai dai tunaninta ya tsaya cak a daidai lokacin da ta ga wannan mutumin a cikin ɗakin, har ta razana ta ƙwala ihu.
Cike da dana sani take raya, da lokacin da ta firgitan nan addu'a ta yi, da wata ƙila hakan ba ta faru ba.
Ta ɗaga kai a hankali, ta ƙurawa ƙofar da Jamila ta fita ido. Wani irin huci haɗi da nishi ta din ga ji, ba tare da ta san daga ina yake fitowa ba. Wata irin narkekiyar macijiaya ce, ta fito daga cikin roofing ɗin ɗakin, tana tsartuwa ta yo kan Nana. Tamkar an ɗaure ta, ta kasa motsi, kuma ta kasa magana kawai ta zubawa sarautar Allah ido.
Ta ci gaba da nufo ta tana tsartuwa, sai kuma Nana ta ga macijiyar ta ƙame a guri guda, tana ta wutsul-wutsul tana fasa kai, tana neman hanyar guduwa.
Wani dogon hannu ta ga an zuro ta taga, an danƙi kan macijiyar, an janye ta, sai da aka janye ta, sannan Nana ta razana ta iya tashi zaune tana maimaita "Innalillahi wa innalillahi raji'un"
Tagar ɗakin ta kalla, ta ga ƙaisar a tsaye, ya tattare macijiyar, ya zura ta a cikin wata 'yar mitsitsiyar kwalba. Har yanzu hannunsa ɗaya da rauni.
Ya dubi Nana ya ce "Wannan ma 'yar aike ce, aka kuma aikota jininki ake so ko ta halin ƙaƙa, kuma 'yar uwakki aka bawa abin da ta zo ta ajiye a ɗakin nan, da zai bayar da damar samo jinin naki. Sai dai waccan jakar ce ta hana macijiyar ƙarasowa inda ki ke" ya ƙarasa maganar yana nuna wa Nana, jakar da sarkin baka ya bata.
"Duk ba wannan ce ma ta saka na zo da kaina gurin ki, rana tsaka ba. Ina mai tabattar miki da wannan auren da mahaifin ki ya yi miki, ya jefa rayuwar ki a cikin sabon babin ƙaddara da ƙalubalen rayuwa, ba kuma ke kaɗai ya jefa ba har da ni. Sai dai na yi alwashin ba zamu wahala muka ɗai ba, sai na yi masa mafi munin azabtarwa a kansa da kuma iyalansa, duk wani farinciki da yake tunanin samu a duniyar nan, sai ya yi hannun riga da shi, ke kuma ki shirya tsaf dan wanda aka aura miki ko dai ya yi ajalina ko na yi ajalinsa!
Ayshercool 08081012143
Ayshacool *AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA 08162859027*
*INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK WANI DATTIN MARA SANYI MAI HANA HAIHUWA SA WARIN GABA RASHIN NI IMA JIN ZAFI YAYIN MU AMALAR AURATAYYA FITAR FARIN RUWA MAI WARI KAIKAYIN GABA TUSAR GABA KURAJEN GABA TUSAR GABA BUDEWAR GABA CIWON JIKI RASHIN GAMSUWA* *Maganin sanyi 5k*
*Maganin sanyi* *5k*
*Maganin ciwon Qoda 10k*
*Maganin HepatitisB ASHA NA TSAWON WATA DAYA MUNBADA ANWARKE DA YARDAR ALLAH 40k*
*MAGANIN MATA KALOLI DABAN DABAN INGANTATTU MASU LAFIYA DA KARA KUZARI AKWAI NA MATA AKWAI NA MAZA UWARGIDA DA AMARE KU GARZAYO WURIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA*
*INGANTACCEN MAGANIN GYARAN NONO MAI TADA KOMADAR NONO DA DUK WATA TAMOWA TA NONO ZAI CIKO DA TUWON NONO YA TADA KOMATSEWARSU BANCE ZASU TASHI BA ZADAI SU CIKO SUYI KYAU* *Maganin gyaran Nono 8k*
*MAGANIN RAGE TUMBI KODA YAKAI GIRMAN CIKIN YAN BIYU INSHA ALLAH KI GWADA MAGANIN AUNTY ZEE DA YARDAR ALLAH ZAKI GODE* *Maganin Rage Tumbi 7k*
*MAGANIN BASUR KODA YAKAI GA YIN TSIRO INSHA ALLAH AGWADA ZA ADACE* *Maganin Basur 5k*
*MAGANIN CIWON SUGAR CIKIN IKON ALLAH MUNBADA ANRABU DASHI* *Maganin ciwon Sugar 10k*
*08162859027* *09070027627*
*Location*KATSINA STATE*
*ACCOUNT NUMBER*
*8162859027* *ZAINAB SHU AIBU* *OPAY*
*OR* *3968303018* *FCMB* *ZAINAB SHU AIBU*
*DAN ALLAH IN KINSAN BAKI SHIRYA BA KARKI YI MAGANA DAN ALLAH KIBARI KI SHIRYA AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA TAKUCE SAI KUNZO*
Page 26
Jin abin Nana ta din ga yi tamkar tunani, kuma tamkar mafarki, domin da ta tashi zaune, ba ta ga ƙaisar ɗin ba, kuma ba ta ga macijiyar ba.
Muryar Yaya Atine ta jiyo a tsakar gida tana faɗin "Wanda ya ƙi ji ai ba ya ƙi gani ba, sam ban ga laifin Isa ba abin da ya yi, wannan hukuncin shi ne ya dace da ita, babu irin rarrashi da ban bakin da ba a yi wa yarinyar nan, amma kowa ya zo sai ta yi burus fafur ta ƙi yarda da maganar aure, hankalinta ba ya kwanciya sai maganar ta lalace, idan wani abin da aljan wani abin tsagwaron iskanci ne kawai, dan a iya adadin yawon nema mata magani da aka yi, ai ya ci a ce ta warke"
Mama kuwa tamkar ta taka rawa dan murna, duk yadda take ƙoƙarin ɓoyewa, sai da farincikin ta ya kasa ɓuya.
Ta yi caraf da maganar Yaya Atine ta ce "To ai yanzu an yi mai ɗungurugum, haihuwa da hanji, ko in ce mai doki ya koma kuturi, tun da babban mutum ne mai rufin asiri ya fito yana sonta, amma fafur ta ƙi, har tana iƙirarin za ta gudu, ko ta kashe kanta, ashe ita gurin wasu take zuwa lalacewa" saurin katse maganar ta yi, bayan da suka yi ido huɗu da Nana a tsaye a ƙofar ɗakin su.
"Rabi, duk abin da za ki ce na yi, ba zai dame ni ba, dan na riga na saba da duk wani ƙazafi da cin mutunci da ki ke yi mini, har ƙazafin maita kin yi mini duk abi dame ni ba, kuskure ma fi girma da za ki yi shi ne, yi mini ƙazafin zina, babu wanda ya kama ni ra'ayil aini, ina yi kar ki ƙara danganta ni da zina"
Jamila ta zaburo ta ce "Nana, Maman ki ke gaya wa haka? Ki ke kiran sunanta gatsal haka?"
"Ba ita kaɗai ba, kafataninku nake yi wa kashedi, kar wanda ya sake gangancin danganta ni da zina, amma idan kun ƙi ji ba za ku ƙi gani ba"