Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 6
Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 6: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 6. Ta nufi banɗaki, tana jin Yaya Atine tana kiran ta, amma ta yi mata banza,…
3,345 words
Ta nufi banɗaki, tana jin Yaya Atine tana kiran ta, amma ta yi mata banza, ta shiga ta yi alwala ta koma ɗaki ta tayar da sallar azahar. Tana zaune a bigiren da ta yi salla, ta kasa addu'a ko lazumin ta kasa, haka zalika ta kasa kukan ma, ta rasa me ma za ta ce. Kawai ta haɗa kanta da gwiwarta ta yi shiru. Har yanzu ji take tamkar kawai barazana ake yi mata, amma ba da gaske ne wai an yi mata aure ba. Ga yunwa tana ji, ga jikinta a mace babu ƙwari, ga damuwa gaba ɗaya ji take kamar ma ba ita ba ce ba.
Can ɓangaren Hajiya Amina kasa zaune ta yi ta kasa tsaye, ta din ga mita tana faɗa, har da cewa sai ta kai Baban Nana Human rights.
Shukura ta ce "Mummy ki na da ɗorawa kai, mutumin ya yi wa 'yar sa aure, kuma ki ce za ki kai shi human rights?" Ayshacool "To Shukura na rasa abun da zan yi zuciyata ta yi mini sanyi ne, gaba ɗaya tausayin yarinyar nake ji. Ba na tunanin an tsaya an ji ta bakin ta. Ke ba kya gurin lokacin da aka kira ni, aka ce an ganta a ɗakin masu gadi. Gaba ɗaya ba ta hayyacinta, ba ki ga a yadda aka fito da ita ba. Kuma shi ma a buzayen wannan wanda ba ya maganar ne fa, har aka yi ta balahirar nan aka gama bai yi magana ba. Ke wait kamar fa yarinyar nan ita ma tana da mental issues"
Shukura ta ce "Au ke sai yanzu ki ka gane? Ni na daɗe da fuskantar hakan, shi yasa wasu lokutan ba na sakewa da ita, ko na ganta da Haidar"
Cike da damuwa ta sake cewa kuma babanta ya san mutumin da ya aura matan, yana da mental issues?"
"Mummy ina zan sani ina nan?"
"Oh my God" Mummy ta faɗa tana zama.
Ta ci gaba da cewa "Wannan mutanen da ba sa iya zama guri ɗaya, yanzu suna nan anjima su na can, yanzu haka za su yi ta yawo da ita, ko kuma can ƙasar ta su zai kaita oho. Dan Allah Shukura, ki ɗan haɗo ɗan abin da ya sauwwaƙa mu haɗa a kai mata, ko ma mene ne ya same ta, duk a dalilin mu ne"
Shukura ta ce "A'a ba a dalilinmu ba ne, ki daina ɗora mana laifi Mummy, zan haɗa abin da ya samu, ni yadda za mu yi da Haidar kawai nake ji wallahi, dan yadda yake ƙaunar ta ba ya ƙaunata haka. Inda Allah zai taimake ni babansa cikin satin nan zai dawo, da ban san yadda zan yi ba"
Mummy ta yi murmushi ta ce "Ina jin sa fa tun safe yake bin Jummai, yana ce mata ina Anty. Tana tsokanarsa tana cewa antynta ce ba ta sa ba, har da kukansa ya zo yana gaya mini, in cewa Jummai Anty Nanansa ce ba ta ta ba"
"Ai sun shaƙu sosai ne, zan ga abin da zan yi a kai". Shukura ta yi maganar tana ɗaukar remote.
**** Cikin ƙanƙanin lokaci labarin aure Nana, ya karaɗe dangi da unguwa baki ɗaya, Mama na ta nanata ai cikin dare aka ɗaura auren a gidan mai unguwa, jin hakan ya sanya sai mutane su tambayi ba'asin dalilin yin hakan, saboda ba abu ne da aka saba da shi ba, mussaman auren budurwa, a ce an ɗaura shi cikin dare kamar yaƙi.
Sai Mama ta ce "Hmm ku dai a yi sha'ani, labarin ne babu daɗin ji"
Yaya Atine ce ta bi Nana da kwanon abinci har ɗaki ta tsaya a kanta ta ce "Ki tashi ki saka wani abu a cikin ki, kina ta kwanciya kin wuni ba ki ci komai ba" Nana ta yi mata banza ko ƙwaƙwƙwaran motsi ba ta yi ba.
A hasale Yaya Atine ta ce "Shikkenan kin yi wa kanki" Nasiru kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye, idan ya fita ya zagaya sai ya dawo ya leƙa Nana, har aka yi sallar magariba salla ce kawai take fito da Nana, babu wanda ta tankawa a gidan.
Saura ƙiris Alhaji Zailani ya furzo abincin da yake ci, bayan da Hajiya Amina ta kammala yi masa bayanin abin da ya faru. Ji ya yi tamkar ta zuba masa wuta a zuciyarsa. Wannan shi ake cewa ga ƙoshi ga kwanan yunwa. A zuciyarsa ya ce amma wannan an yi la'anannen tsoho, mu gama yarjejeniyar zai ba ni aurenta burina na daf da cika, kawai sai ya aurawa wani, saboda hauka. A fili kuwa cikin ƙwarewa da iya duniyanci, ya nuna halin ko in kula ya ce Allah ya kyauta. Bayan ya kammala cin abinci ya cewa Hajiya Amina ta zauna a sashenta kawai, zai ɗan fita.
"Amma na ga yaushe ka dawo, da har zaka sake fita koma mene ne ka bari sai da safe mana?"
"Yaushe ki ka fara kafa mini dokoki a gidana?" Yayi maganar yana tsare ga ido, babu shiri ta ce "Allah ya baka haƙuri"
Kamar zai haukace, haka ya ɗauki mota ya fita, yana tafe yana ta ɗure-ɗuren ashariya a cikin mota, yana zage-zage. Gidan malam Gambo ya nufa, gurin sha ɗaya na dare, haka ya kira shi a waya ya fito.
"Alhajin Allah, lafiya kuwa ka zo a daren nan, ba yau ka dawo daga tafiya ba?"
Cikin damuwa ya ce "Babu lafiya, dan kuwa an yanka ta tashi"
"Too ikon Allah, me ya faru?"
"Yarinyar nan, da za a ɗaura mana aure, babanta ya yarda zai bani aurenta, ina murna muradina zai cika, kawai yau na dawo na tarar wai ya aurawa ɗaya daga masu gadin gidana, saboda an ganta a ɗakinsu, wai ko yana zarginta ne oho masa, ni ko inda yake ban je ba, dan Allah meye abin yi? Ni fa ina iya saka a kashe ko ma uban wa aka aura mata, muddin muradina zai cika"
Ayshacool "Idan ma kin kashe kanki, ƙaddara ta riga fata, dole ki tashi ki ƙwarara jikinki, ki ci abinci ki ware. Ko dai mu yi gaba da gaba da ƙalubalen da yake tunkaro mu, ko kuma ki amince na ɗauke ki baki ɗaya, idan ba haka ba ba zan iya cewa ga abin da zai faru ba"
Nana ta ɗaga ido ta kalli inda yake zaune, ta yi masa shiru ba ta ce masa komai ba.
Ya miƙe tsam ya rufe littafin, ya miƙa hannunsa can saman wani guri, ya ɗaukko wata kwalba, ya zo gabanta ya zauna, ya ƙura mata ido, take ta ji tamkar an zare mata kuzarinta.
Ya watsa mata wani koren abu a fuska, babu shiri Nana ta yinƙura ta tashi zaune tana tari.
Ummi ta gani a ɗakin da take a asibiti.
"Zan sha ruwa" Nana furta a wahale. Aka kawo mata ruwa, ta sha sosai sannan ta koma ta kwanta. Sai da Nana ta kwana a asibiti sannan aka sallame ta, wata irin azababbiyar yunwa da ta sako ta gaba, haka ta din ga cin abinci.
Sun koma gida babu daɗewa sai ga Hajiya Amina, tare da Haidar. Yana ganin Nana ya je ya maƙalƙale mata yana murna. Ita kanta Nana ta yi murnar ganin Hajiya Amina da Haidar.
"Nana, duk da ni ba na zargin ki, kuma ba zan takura miki da tambayar jin abin da ya faru ba, amma ki yi haƙuri da abin da ya faru, amma idan ba kya son auren nan ki yi mini magana, a shigar da ƙara a hukumance a raba auren, kalli duk yadda ki ka rame"
Jiki a sanyaye Nana ta ce "Na gode sosai da sosai Hajiya, Allah ya saka da alkhairi ina fatan Allah ya sanya haka shi ne mafi alkhairi, ni ba auren ne damuwata ba, zargin da ake yi mini.. ta kasa ci gaba saboda yadda kuka ya ƙwace mata.
Ta dafa bayan Nana ta din ga rarrashinta. Kaya ta kawowa Nana, har da bedsheets sabo da tsofaffi amma masu kyau, ga 'yan kayan kitchen da ta kawo mata, da Shukura ta bayar a kawo mata. Ta yi ta godiya, ta tashi za ta tafi, Nana ta ce za ta raka ta, ta ce "A'a ai ke yanzu matar aure ce, ki yi zaman ki Allah ya sanya alkhairi" ta ƙarasa maganar tana danƙawa Nana kuɗi a hannu.
Maƙwabta na ta zuwa Allah ya sanya alkhairi, da biyu domin su ga halin da Nana take ciki, har da 'yan islamiyyar su, da tun da ta bar makarantar babu wanda ya bibiye ta, balle a ji dalilin daina zuwan ta.
Baba sai kaiwa yake yi, yana komowa yana nanatawa Nana ta haɗa kayanta cif, ta fara shiri. Yanayin yadda take ganin duniya ta juya mata baya, ta ji ina ma ba a haife ta ba, kuma duk wannan abin babu wanda ya kira mahaifiyarta ya gaya mata halin da ake ciki. To me ye ma amfanin gaya mata, tun da ba wani abin za ta amfana miki ba, kuma kin san ba zuwa za ta yi ba. Wata zuciyar ta tunatar da ita.
Da daddare gari ya yi tsit, Nana tana ta juyayi da tunanin wa ma aka aura mata a cikin buzayen, tun da su na da yawa. Babu tsammanni bacci ya yi awon gaba da ita, sai dai ta din ga jin ta tamkar a zahiri ba mafarki ba. Da wata irin murya mara daɗin ji, cikin maɗaukakin sauti mai matuƙar razani da kiɗima zuciya ake yi mata magana.
"Ko kin san wa ki ka aura? Mutumin da shi kansa bai tantance waye shi ba, bai san mene ne jinsa ba, mutum ne shi ko aljan. Rayuwa da shi na iya sadar da ke da ajalin ki. Lokaci ya yi da za ki biya abin da kakannin ki suka aikata, da kuma abin da ya faru a silar ki ke ce tabbas ke za ki biya wannan bashin. Ki tsira da ranki ki bar gida, ki yi nesa da gida, ko kuma ki fuskanci rayuwa mafi muni da hatsari" A gigice Nana ta tashi, ta fita tsakar gida da gudu tana haki, jan burki ta yi duk da zuciyarta na raya mata ta zare sakata ta ruga da gudu. Wani irin zafi take ji da matsanancin tashin hankali, ji take kawai ta buɗe ƙofa ta fita shi ne za ta samu nutsuwa.
Juyawa ta yi da nufin ta fice ta bar gidan, amma ta ji kamar ta na ƙwaƙƙwaran motsi, zuciyarta za ta yi bindiga saboda bugun da take yi.
"Ki na ƙara ɗaga ƙafarki, zuciyar ki za ta tsaya da aiki. Sai da na gaya miki, babu irin kashedin da ban yi miki ba, ki ka yi kunnen uwar shegu da ni, wallahi da kin sake kin buɗe ƙofa kin fita, haukacewa za ki yi. Yanzu dabara ta rage ga mai shiga rijiya" A wannan karon ta gane muryar ƙaisar ce, amma ta farkon ba ta san muryar waye ba. Ayshacool Zumbur ta tashi zaune, tana kallon ɗakinsu, a iya saninta dare ne ta kwanta tana bacci, amma yanzu ta ga azahar ce.
Yaya Atine ta shigo ɗakin tana faɗin "Kin gama shure-shuren da ihun, kin ga dama kin tashi kenan? Wallahi tun wuri ki ajiye wannan haukan aljanun naki, ki kama kanki, ba kowa ne zai zauna kina masa wannan shirmen banzar ba, idan kin ga dama ki tashi ki wuce ki yi wanka ki zo ki ci abinci" Nana ba ta motsa ba, tana tunanin ko ta yi sallar asuba?.
Ummi ta shigo ɗakin da jaka fuskarta ɗauke da mamaki ta ce "Nana" Nana ta ɗaga kai ta kalle ta.
"Kin ga yanzu daga fita ta, na haɗu da wasu buzaye, wai 'yan uwan mijin ki ne, suka ba ni wannan kayan wai a ba ki, sun ce , a ce ki yi haƙuri abin ya zo babu shiri, kuma ba su da isassun kuɗi. Kin ga dubu hamsin, wai a baki ki yi wani abin ga kuma kaya"
Yaya Atine ta waro ido ta ce "Buzayen?"
"Wallahi kuwa"
"Kirawo Rabi maza a yi a gabanta" aka kirawo Mama, aka buɗe zip ɗin jakar.
Danƙareriyar shadda bazin ce a farko, fara ƙal an yi mata aiki irin na buzaye, har da awarwaraye da ɗan kunne, da sarƙa. Kaya dai Atamfa set biyar, sai takalma guda biyu da turare har da na wuta.
Ummi ta ce "To ke Nana ki na ta wani buntsire-buntsire da alama wannan za su kula da ke. Kalli a yadda aka yi auren fa, amma har suka yi miki wannan kayan haka." Ita kanta Mama abin ya ba ta mamaki ya tsaye mata a rai ta za ta Nana za ta tozarta fiye da haka.
Ummi ta ce sai An yi wa Nana gyaran jiki an yi mata lalle da gyaran gashi, tun da har sun ƙoƙarta sun kawo wannan kayan. Da aka gaya wa Baba nuna wa ya yi ko a jikinsa, duk da cikin ransa ya ji daɗin kayan da suka kawo mata, damuwarsa kar ma a fara yi masa zancen kayan ɗaki. Dan sadakin ma naira dubu hamsin ya ware zai ba ta.
**** A tsanake yake ƙare masa kallo, tun daga kansa, har zuwa kan yatsunsa da suke ɗauke da manyan zobunan azurfa. Duk da fuskarsa a rufe take, sai idanunsa kawai ake iya gani, yatsun hannunsa su ka fallasa asirin kalar farar fatarsa.
"Ko za ka sauke rawanin naka mu yi magana?" A hankali ya juya ƙwayar idonsa, yana kallonsa amma bai yi magana ba.
"Magana nake, ka sauke rawanin fuskarka mu yi magana" still bai sauke ba, kuma bai yi magana ba, sai ma yinƙurawa da ya yi, ya juya zai fita" cikin azama ya tashi ya sha gabansa ya ce "Ya mu na magana za ka tashi ka tafi?"
"Me yasa ka kira ni?" Ya yi maganar yana tsare shi da ido.
"Buƙata ce"
"Ta me?"
"Ina so ka gaya mini ko nawa ka ke buƙata, ka saki yarinyar nan Nana da babanta ya aura maka"
Ya gyara tsayuwarsa sosai yana kallon cikin idanun Alhaji Zailani, ya ce "Je devrais divorcer?" Alhaji Zailani ya yi ƙuri da ido yana kallonsa, dan bai gane me ya ce ba.
Ya taka a hankali ya je gaban Alhaji Zailani ya tsaya, sannan ya ce "Me yasa ka ke so na sake ta?"
"Saboda na fi ka buƙatar ta"
Ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Ka ce ka fi ni buƙatar ta?" Kafin Alhaji Zailani ya ba shi amsa, kawai ya gansu a tsakiyar dokar daji.
Ya saka hannu, ya sauke rawanin fuskarsa, kyakyawar fuskarsa ta bayyana ya ce "Ka ce ka fini buƙtarta? Har ka manta da abin da na yi maka a wancan lokacin?, shi ne ka sake biyo ni da wannan maganar?"
Ya saka hannunsa a wuyan Alhaji Zailani, wasu irin dogwayen farata suka tsiro a yatsunsa, a hankali kamaninsa suka gushe, fuskar wani tsoho tukuf ta bayyana.
Ya ƙara tsananta shaƙe Alhaji Zailani ya ce "Ni na fika buƙatar ta, fansa ta zan ɗauka a kanta. Mallakina ce, fansa zan ɗauka, dan haka na fika buƙatar ta!!
Jin numfashin sa ya yi, ya dawo iya ƙirjinsa, jini ya fara zubowa daga gurin da ya huda shi da faratansa.
Ayshercool 08081012143 Ayshacool **** Gidan su Nana kuwa, ranar ta kasance ranar da za a kaita, sai dai babu wanda ya san ina za a kai ta, kuma ko katifa Baba bai saya ba. Da Ummi ta yi masa magana sai cewa ya yi ba shi da kuɗi, ita ta yi mata. Abin ya ɓata mata rai, babu wanda ya san wani irin guri za a kaita, idan babu labule da katifa a ƙasa za ta zauna? Ga kuɗin sadakin Nanan har dubu ɗari biyu a hannunsa.
Nana kuwa kawai dai ga ta nan ne, hankalinta ya kasu kashi-kashi, tana tunanin maganganun da ta ji da wannan muryar, ga kuma abin da ƙaisar ya gaya mata. Duk da wani ɓangaren na zuciyarta na gargaɗinta da yadda da maganganun Aljanu, wataƙila kawai wasa suke yi mata da hankali. Tana jiyo Mama tana ɓaɓɓaka dariya tana cewa yanzu idan buzayen su ka ƙi zuwa, su nuna in da za a kai Nana, ko kuma suka gudu shikenan Nana ta zama bazawara. Maganar ta sosawa Nana rai nesa ba kusa ba, wato duk bayan abubuwan da ta yi mata a baya, har ma tunani take yi, ta yi zawarci. A take Nana ta yi wa kanta alwashin ko bangon duniya wanda aka aura mata, zai ɗauke ta ya kai ta, za ta bi shi ko da kuwa zai din ga azabtar da ita ne, ta gwammace hakan da ta sake dawowa gidan nan da sunan zawarci tun da dai ibada take yi. Abubuwan da suke damunta kuwa, ta fauwwalawa Allah, ta dake ta je ta yi wanka. Ta yi kwalliya da wannan shaddar, da kayan da aka kawo mata. Kasancewar Nana tana da fata mai kyau, 'yan kayan da Ummi ta haɗo ta yi mata gyaran jiki na kwana biyu, ta yi kyau fatar ta ƙara haske. Ga zanen lalle an yi mata. Gashin kanta ma ya yi kyau, komai kyau ne da shi idan ya sha gyara.
Sai da Mama ta yi saroro, da Nana ta fito cikin kayan nan, tamkar matar wani hamshaƙin mai kuɗi. Duk da ta rame sosai, amma kayan sun zauna a jikinta, tamkar tela ya gwada ta. Fuskarta babu yabo babu fallasa ta fito tana gaisawa da 'yan uwa da abokan arziki.
Nan gida ya ɗauki guɗa, aka din ga yi mata fatan alkhairi. Duk da ga a yadda auren ya zo mata, kuma har a lokacin ba ta tantance waye ma mijin nata ba. Amma ganin mutanen da suke ta shiga su na fita, ana cin abinci, a dalilinta. Kawai ta durƙusa ta yi sujudu shukur, ko ba komai wannan wata rana ce da kowace mace da ta san ciwon kanta, take fatan gani a rayuwarta.
"Allah ga Nana, Allah ga baiwar ka. Ina godiya da tarin ni'imomin ka a gare ta" ta ɗago fuskarta duk hawaye. Suwaiba ta ce "Ji wata gulma, har da sujjada kamar auren gaske, wai a dole sai an raina wa mutane hankali. Mu dai a hanzarta a yi a bar mana ɗaki"
Nana ta kalle ta ta ce "Suby kenan, ai duk ci gaba ci gaba ne, ba ɗaki ba gidan zan bar muku baki ɗaya ku sake, ina fatan aniyar kowa ta bi shi"
Suwaiba ta ce "Aniyar kowa ta bi shi kamar yaya, me ki ke nufi?"
Ta girgiza kai ta ce "A'a ba zan biye miki ba, ni yau ina cikin farin ciki ne a gare ni, ba zan biye miki ki lalata mini ita ba" Suwaiba ta ci gaba da faɗar maganganu. Nana kuma ta fice ta bar mata ɗakin. A hakan an sassamu wanda suka bayar da gudummawa sosai da sosai, domin kowa yana yabon Nana da halaye na gari, dan duk 'ya'yan malam Isa babu mai haƙurinta da biyayya, duk da wasu lokutan ita ma tana da faɗa, amma akwai ladabi. Ummi ta kasa ta tsare tana karɓar kaya da kuɗin gudunmawar da kanta, Ta kuma din ga ƙoƙarin, duk wani yinƙurin kawo hargitsi da Mama take ƙoƙarin yi a gurin taron ta hana. Nana ta samu kayan kitchen, da kuɗaɗe daga hannun jama'a da dangi.
Da yamma sai ga Yusuf da mota, tare da Sule, Hajiya Amina ta ce a ɗauki Nana a ciki.
Yaya Atine ta ce a fara zuwa su ga gurin, su san abin da za su saya, amma Yusuf ya ce babu buƙatar hakan, amarya za su ɗauka.
Gaba ɗaya jikin Nana a sanyaye yake, su Yaya Atine suka saka ta sake wanka, Ummi ta bata wata lafaya da ta saya mata, ta saka ta feshe ta da turare.
Ana ta rangaɗa guɗa, aka kai Nana gurin Mama wai ta yi mata nasiha.
Mama ta ce "A'a ni me zan ce, ai ta san komai ba abin da ba ta sani ba, a sauka lafiya"
Nana a ranta ta ce "Ko ba ki faɗa ba lafiya zan sauka, kuma sai Allah ya kunya ta ki".