Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 22
Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 22: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 22. Ta yi murmushi ta ce "Zan ajiye maka duk abin da ka ke buƙata, dan Allah…
3,363 words
Ta yi murmushi ta ce "Zan ajiye maka duk abin da ka ke buƙata, dan Allah ka bari na je Please. Ba dan kar na zaunar da kai ba, sai mu tafi tare ma, to ka ga bai kamata na bari ka na jira na ba"
"A dawo lafiya" ta zabura ta ce "Ka yadda na je?" Ya jinjina kai. "Allah ya saka mini kai a aljanna na gode sosai Shugabana"
Ya yi murmushi ya ce "Sayyid yanzu kuma Shugaba"
"To ai duk abu ɗaya ne" kyakyawar sumbata ya samu a bakinsa, daga matarsa saboda tsananin farin ciki da ta shiga.
Da safe ta ya ƙoƙarin gama girki da wuri, ta ɗora masa na rana, ta dafa ruwan zafi ta zuba masa a flask da duk abin da take sanya ran zai nema.
Ta yi wanka ta fara shiri, su ka yi waya da Hajiya Amina, take gaya mata kwana huɗu kenan, an yi wa Shukura aiki yaron ya rasu. Nana ta ji ta damu sosai da sosai, ta yi mata jaje ta ce za ta je ta duba ta.
Ko da ta ajiye wayar, ta kalle shi ta ce "Sayyid, ka ji Shukura ta haihu yaron ya mutu, dan Allah zan biya na duba ta, sai na tafi gidan Ummi."
"A'a"
Ta marairaice ta ce "Dan Allah, kar su ga kamar wulaƙanci ne, an gaya mini abu ban je ba"
Ya kalle ta ransa a haɗe, ya ce "Kar ki je gidan nan" ta tsuke bakinta, kar ta je gidan Ummin ma, ya hana ta zuwa.
Har bakin hanya ya raka ta, sannan ya koma.
Ta yi tunani ta ga yadda ya tsuke fuskar nan, babu lallai ya bari ta je, kuma Hajiya Amina ba ta cancanci haka daga gare ta ba. Duk da ba shiri suke yi da Shukura ba a baya, amma tana matuƙar tausayinta. Kawai ta yanke shawarar ta je a gurguje, ta duba ta ta wuce gidan Ummi.
Habu ne ya buɗe mata gate, yana ganin ta, ya yi murmushi suka gaisa ya ce "Ina mutumin?"
Ta ce "Yana gida, bai san zan zo ba, wata unguwar na tambaye shi, dan Allah kar ka gaya masa na zo"
"A'a kar ki damu, ba zan gaya masa ba, ina fatan duk ku na lafiya?"
Nana ta ce "Lafiya ƙalau, ba ka zuwar mana kwana biyu"
"Ai na ga babu wata matsala ne, ku na lafiya shi yasa"
"Ko kuma shi ne ya hana ka zuwa, Sayyid kishinsa ya yi yawa"
Ya yi murmushi ya ce "Sayyid kuma?"
Nana ta jinjina kai ta ce "To na rasa da sunan da zan kira shi, amma dan Allah da wani sunan aka ɗaura mana aure da shi ne?"
"Kamar dai yadda na gaya miki ban san komai a kansa ba, kawai cewa na yi a saka Muhammad, amma ban san sunansa ba nima"
Ta jinjina kai ta ce "To da gaske kai ne ka ke ba shi kuɗin da yake kashe mana? Na ga kuɗin aikin gadin ba wani yawa ne da su ba"
Ya ɗan yi dariya ya ce "Ai ainihi ba gadi ne sana'ata ba. Ina safarar dabino ne, da mazarƙwaila da cukui da sassan raƙumi, daga Nijar zuwa Nigeria na rarrabawa 'yan kasuwa. A garin haka ma na tsince shi. Na fara gadi ne saboda na samu na zauna guri ɗaya, a nema masa magani, amma haryanzu ba a dace ba, masu maganin sai su ce abin ya fi karfinsu"
"Amma Malam Habu, me aka ce muku yana damunsa?" Horn ɗin mota su ka ji, ya ce "Bari na buɗe ƙofa"
Ta ce "Shikenan, nima bari na hanzarta"
Ta shiga cikin gidan, Jummai ta din ga murna da ta ga Nana, ta yi mata jagora har ɗakin Hajiya Amina, inda Shukura take jinya.
Sosai Nana ta jajantawa Shukura, tare da ba ta haƙuri, da ƙarfafa mata gwiwa a kan girma da muhimmancin tawakalli ga Musulmi.
Hajiya Amina har so take Nana ta zo, ko tana cikin damuwa, ire-iren wa'azinta, a kan tawakalli da dogaro ga Allah na ƙara mata ƙwarin gwiwa.
Nana ta tambayi ina Haidar, aka ce mata yana gidan kakarsa. Ayshacool Muryar Alhaji Zailani ta ji ya shigo ɗakin, yana kiran sunan Hajiya Amina. Gabanta ya faɗi, ƙwaƙwalwarta ta shiga fafutukar tuno mata, da abin da ta gani a mafarki amma ta kasa, duk da zuciyarta na raya mata mummunan abu ne, kuma kamar a zahiri ya faru. Saboda kaucewa zargi, Nana ta yi ta maza ta gaishe shi.
Shi kansa ya yi mamakin ganin Nana, ya daidaita nutsuwar sa, ya amsa mata ya ce "Ashe amarya ce ya mai gidan?"
"Yana nan lafiya ƙalau. Hajiya bari na tafi ina sauri ne, sai na sake dawowa."
Cikin sauri ta ɗauki jakarta ta yi waje, Shukura na ta yi mata godiya.
Ba ta tarar da Habu ba, kawai ta buɗe gate ɗin ta fice. Ganin da ta yi wa Alhaji Zailani, ta din ga jin tamkar ta aikata wani mummunan saɓo ne.
Tana ta sauri, unguwar shiru babu kowa, ta ga an sha gabanta da mota. Ta ja ta tsaya ƙirjinta na dukan uku-uku.
Duk wannan saurin, na ki tsere mini ne? Idan na so kamo mini ke zan saka a yi, na yi duk abin da nake so, kuma babu wanda ya isa ya ce dan me, ko ya tuhume ni. Biyo ki na yi na ƙara tabattar miki da ina nan a kan baka ta, wallahi ba zan rabu da ke ba, sai buƙata ta ta biya."
Cikin dakiya ta ce "Allah ko? A baya ban taɓu ba, sai a yanzu ka ke tunanin zan taɓu? To kar ka fasa, ka ci gaba da bibiyata da mugun nufinka, kar ka fasa" ta zagaye motar ƙasan zuciyarta tana tsananta addu'a ta bar gurin.
Gidan Ummi ta tafi, Ummi ta yi farin cikin ganinta sosai da sosai, su na hira ana gyara Nana. Nana ta bata wasu daga cikin kayan da su Adda Saude suka kawo mata. Aka wanke mata kai, aka yarfa mata kitso ƙanana, ta yi mata dilka ta zana mata lalle ja da baki, ta turara ta da turarukan wuta.
Nana ta ce "Inyee ko ranar aurena ban samu wannan gatan ba"
"Ai biya za ki yi, ki je gida ki ce ya biya kuɗin gyaran da na yi miki"
"Ba zamu biya ba ɗin" ta yi maganar tana dariya.
Ummi ta bata labarin yadda Saleh, duk ya shiga damuwa da tashin hankali, saboda auren da ta yi, ya tattara ya koma Lagos ma. Daga haka kuma suka koma tattaunawa a kan matsalolin gidan su, yadda Baba ya bar ragamar gida a hannun Mama, gantalin da Jamila take yi, har ta bata labarin dukan da Gaddafi ya yi mata, ga Imarana babu ma wanda yake cigiyarsa. Suka ci gaba da jajanta matsalolin na su, da a yanzu ba su san ma hanyar saita wannan gida na su ba. Gefe ɗan gidan Yaya Atine ya ce yana son Suwaiba, Mama ta ce ba za ta bawa Faƙiri 'yar ta ba. Sun daɗe su na hira, Nana ta bawa Ummi kayanta da take so a ɗiɗɗinka mata. Ummi ta duddubo mata wasu kayan kwalliya, da sauran 'yan kayan buƙatu ta rako ta titi, ta samu abin hawa ta tafi gida.
Ana ta kiraye-kirayen sallar magariba Nana ta isa gida, sai dai ba ta tarar da shi ba. Ta yi salla, kasancewar ta zo da abinci daga gidan Ummi, ya sanya ba ta ɗora girki ba, ta dai kunna gas ta ɗora masa shayi.
Har aka yi sallar isha'i shiru bai shigo ba, sai kuma abin ya fara damunta. Ga shi shi ba waya ba, wayarta ma tana hannunsa, ba waya ta fita.
Tana nan tana kallon hanya, ta ji yana rufe gate. Ajiyar zuciya ta yi, ta jira ya shigo ɗakin.
"Sayyid, duk na damu na ji ka shiru, ina ka tafi ne?"
Ko kallon gurin da take bai yi ba, ya wuce ta ya shiga banɗaki. Sororo ta tsaya tana mamaki.
Ta koma gefe ta jira, ya fito. Ya sake nufar wardrobe. Ta bi bayansa ta na magana. "Sayyid wai meyafaru ne? Ina ta magana ka yi mini shiru"
Ya duba jallabiyar da zai saka ya kwanta. "Sayyid ka yi magana mana"
Ya ajiye jallabiyar, ya kalli Nana a tsanake ya ce "Me yasa na ce kar ki yi abu ki ka yi?"
Gabanta ya faɗi, ce rauni ta ce "Me na yi?"
"Tambayata ki ke yi? Ban ce kar ki je gidan mutumin nan ba? Ban gaya miki ba?" Ya yi maganar cikin ɗaga murya.
Cikin sauri ta girgiza kai ta ce "A'a ban...
"Kar ki yi mini ƙarya kin je, me yasa ki ka je?"
Ta girgiza kai tana tsuma, saboda yadda ya burkice mata.
Ya Kano hannunta ɗaya ya ɗora a ƙirjinta, ya kama ɗaya ya sanya a ƙirjinsa, ta ji yadda zukatansu ke bugawa a tare.
"Haryanzu ki na tunanin ƙarya nake yi, da nace miki akwai ruhina a jikinki?"
Ya saki hannayenta, ya kuma tsare ta da ido, ya ce "Me yasa ki ka je bayan na ce kar ki je?"
Nana ta yi shiru ta ƙi magana. Ayshacool "Magana nake yi miki" ya ƙara maganar yana ɗaga mata murya.
Ta ɗaga kai ta kalle shi, ta ga gaba ɗaya ya canza, fuskar sa kamar bai taɓa dariya ba, jikinsa yana tsuma.
Tsorata ta yi, ta ƙara ja da baya, kawai ta ji ya riƙe wuyanta.
Ayshercool 08081012143 Ayshacool Idanun Nana suka yo waje, ta ji numfashinta ya yi sama, ta saka hannu ta rirriƙe nasa tana kakari.
Da ƙyar ta kalli fuskarsa, gaba ɗaya ta canza naman fuskarsa sai rawa yake yi. Tsohon nan ta ga ya bayyana a gefensa, riƙe da sandarsa yana kallon ta yana dariya.
Jikinta ne ya saki a hankali, ta sauke hannunta. Ya yi jifa da ita kan katifa ya yi baya, yana jin tamkar ana jan kansa.
Tana durƙushe tana wani irin tari, haɗi da kakari, tana ta yinƙurin amai, amma babu abin da yake fita daga bakinta sai wani irin yawu mai yauƙi. Ta ja jikinta da ƙyar ta jingina, ta lumshe idanunta ta buɗe a hankali. Ta ga Ƙaisar ya zura mata ido.
Ya gyara zamansa ya ce "Yanzu da ki ka fara ɗanɗana kuɗarki, wataƙila za ki yarda da abin da nake gaya miki. Laifi na biyu kenan da ya aikata mini, zan kuma taɓa shi a inda ba ya zato".
A wahale Nana ta ce "A'a Ƙaisar, koma dai mene ne, ni ya yi wa dan Allah ka rabu da shi, wannan tsohon na gani a tare da shi, kuma idan ka ce za ka yi masa wani abu, kai ma wannan tsohon wahalar da kai yake yi."
"Ba ke za ki gaya mini abin da zan yi, ki rufe mini baki. Kuma kuskure mafi girma da ki ka aikata, bayan ƙin amincewa da buƙata ta, shi ne ɗaukar cikin da ki ka yi, ba zan taɓa lamunta a samu zuriya ta tsatsonki ba, na ci gaba da ƙuntata rayuwata ina wahalar banza a kan mutane marasa alaƙawri kamar ku ba"
Nana ta kalli cikinta ta kalle shi ta ce "Ciki kuma?"
"Ƙwarai, ga ɗan tayi nan a cikin ki, tun a ranar farko da ku ka kasance tare. Kin ɗauki abin da ke kan ki ba ki da tabbacin wane jinsi ne"
"Mutum ne, Sayyid bil'adama ne, da aljani ne ba zai iya tarayya da ni a zahiri ba, sai dai a cikin bacci, ko ta hanyar amfani da gangar jikin ɗan Adam "
"Ko?"
"Eh" ta ba shi amsa.
"Yaro yaro ne. Kin tabattar bil adama ne, daga ina? Daga wace nahiyar? Wane shiri ki ke da shi, a kan sanin waye shi da inda ya fito? Har ki ka sakankance ki ka amince da ɗaukar ciki?"
Ƙoƙarin juyawa Nana ta yi a kan katifar, amma ta ji jikinta a ɗaɗɗaure kamar an yi mata duka. Ga wani irin azabar sanyi da yake ratsata ko ta ina, tamkar an ajiye ta a cikin ƙanƙara. A cikin kunnuwanta kuma take jin yadda zuciyarta ke bugawa da ƙarfi da kuma sauri. Ga wani irin nauyi da kanta ya yi mata tamkar an ɗora mata. Ga azababben ciwo da yake yi mata, tamkar zai rabe.
Ta juya da ƙyar tana numfarfashi, tana son lalubar abin da za ta rufa, wani irin huci ne ya daki fatarta, ta buɗe idanunta da ƙyar, ta kalli gefenta.
Yana kwance jiginsa na ta jijjiga, yana numfarfashi.
Ta din ga jan jikinta a hankali, ta matsa ta hau kan ƙirjinsa ta kwanta, ba tare da fargabar zai sake yinƙurin cutar da ita ba.
A hankali ta ji zafin jikinsa, ya fara ratsa ta, ta fara rage jin sanyin da take ji, wani wahalallen baccin ya sake yin awon gaba da ita.
"Asmy" ta ji ya kira ta da wani sunan kuma. Ta buɗe idonta da ƙyar ta kalle shi.
Garau da shi kamar babu abin da ya faru.
"Salla" ya faɗa a taƙaice, jikinsa duk danshin ruwan alwala, ya fice ya tafi masallaci.
Da ƙyar ta tashi, tana daddaga bango, ta shiga ta yi alwala, ta dawo ta yi salla a zaune, ta kwanta.
Ganin ba ta tashi da wuri ba, ya sanya shi fara rage aikace-aikacen ɗakin, amma ya ga babu alamar za ta tashi balle ta ɗora girki. Ya matsa kusa da ita ya tashe ta. Ta tashi zaune da ƙyar, kanta kamar ana buga mata guduma.
Ya ƙura mata ido ya ga duk ta canza, sai dai ta yi masa kyau a ido sosai, ƙanan kitson kanta, sun dace ba ƙin gashinta, ga hannunta lalle ja da baƙi ya yi mata kyau sosai da sosai.
Ta saukko daga kan katifar, ta ɗauki wata roba, ta ɗaukko lemon tsami ta yanka, ta fara matsawa a bakinta. A hankali tashin zuciyar da take ji, ya fara raguwa. Shi dai ya zuba mata ido.
Ta gama ta sake ƙoƙarin kwanciya.
"Ki ci abinci, ga ƙosai" ya yi maganar yana nuna mata ledar da ke kusa da gas.
Ta girgiza masa kai ta nemi guri ta kwanta.
"Kin yi mini laifi ki na fushi da ni kuma? Na ce kar ki yi abu kin yi, kuma kina fushi?" Ayshacool Ta kalle shi idonta fal hawaye ta ce "Kuma shi ne sai ka shaƙe ni? Har na yi maka laifin da za ka yi yinƙurin kashe ni, dama ba so na ka ke yi ba" A rikice ya zaro ido ya kalle ta ya ce "Ni? A'a ban shaƙe ki ba. Me yasa zan shaƙe ki kuma? Raina ya ɓaci ne, zuciyata ta kama da wuta, sosai da sosai amma ban shaƙe ki ba. Kamar bacci ma na yi daga lokacin"
Idonta fal hawaye ta ce "Bayan ga shaidar faratanka a wuyana"
Kamar ya yi kuka ya ce "A'a, kin manta kin yanke mini farce, amma ban taɓa ki ba ma, kalli hannuna" ya yi maganar yana nuna mata yatsun sa.
Ya miƙa hannunsa wuyanta, dan ya duba shaidar faratan da ta ce, amma ya ji jikinta zafi rauuu.
Sake rikicewa ya yi ya ce "Ma vie. (Rayuwata) tu as de la fièvre ? (Zazzaɓi ki ke yi?" Ya yi maganar a rikice.
Ba ta kula shi ba ta kwanta, tana jin yadda jikinta yake ɗaukar zafi, cikin ta yake yamutsawa.
Wayarta ya ɗauka ya danna, ya kara a kunnensa. Da French ya yi magana, ya ajiye wayar a kan mudubi, ya dawo inda take ya ce "Tashi ki saka kaya, na kira Habu"
"Sayyid da ba ka kira shi ba, zan warke fa"
"A'a jikin ki ya yi zafi sosai"
Ya nemi guri ya zauna a musa da ita, yana ci gaba da kallonta cikin damuwa.
* Sannu a hankali yake jujjuya wayar hannunsa, yana sake karanta saƙon da ya shigo wayarsa. An shirya tsige shi, daga shugabancin 'yan kasuwa, bisa zargin sa da yin sama da faɗi da wasu kuɗaɗe, na ƙananan 'yan kasuwa.
Tabbas akwai kuɗaɗen wasu a hannunsa, har da wanda kuɗinsu bai kai ba, da zai yi wa ciko ya ba su bashin kaya. Kuma ya tattara kuɗin ya yi order kayan, sai dai sun ƙara wata guda a kan lokacin da yakamata su zo, shima yana ta bibiya ne. Amma ya yi wuri a ce an ɗauki wannan matakin, duk da ba yau ya saba yi wa ƙananan 'yan kasuwan irin wannan tallafin ba, har ma da manyan, amma ba a duba hakan ba.
Fadila ce ta nufo shi, hannuna da ɗan ƙaramin tray, ɗauke da fruit, ta nemi guri ta zauna.
Ta ce "Daddy, ga fav ɗin ka, banana, ga kuma smoothie na yi maka, na ga kamar a gajiye ka ke"
Ya yi murmushin yaƙe ya karɓa ya ce "Na gode sosai da babyna"
Jiki a sanyaye ta ce "Daddy" ya kalle ta ya ce "Na'am"
"Me yake faruwa ne?"
Ya ce "A ina?"
"Damuwa ce a fuskarka, dan Allah gaya mini, meyafaru?"
Ya yi murmushi ya ce "Tsabar gajiya ce kawai, kin san yanayin harkokin namu, babu hutu"
Fadila ta riƙo hannunsa ta ce "Na san wataƙila har da damuwar kayan nan, da suma suka yi delay, amma dan Allah ka yi haƙuri ka daina damuwa, yadda wancan suka kuɓuta, wannan ma da yardar Allah za su tsira. Kar ka damar mini kanka dan Allah"
Maganganun nata sun ɗan ba shi ƙwarin gwiwa, shi bai damu da batun tsige shi daga shugabancin ba, shi haƙƙoƙin mutane da suke kansa, su ne suka dame shi. Yana jin daɗin tattauna matsalolin sa da Fadila. Duk da ba ta kai uwargidan sa shekaru ba, amma yau shekara bakwai da auren Fadila, ta tattara duk ta tsane shi, tana ganin ya ci amanarta, sun yi wahala tare ya ƙaro aure. Duk da duk wani abu na jin daɗi na hakkinta yana sauke mata. Ko ya gaya mata damuwarsa, sai dai ta taɓe baki kawai ta ce Allah ya kyauta, ko ma ta ce masa alhakinta ne. Fadila kuwa ko sun samu saɓani, da ya shiga damuwa, take ruɗewa har sai ya samu mafita, sai dai a wannan karon, ba zai iya gaya mata ba, saboda ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba ita ma.
****
"Husnah" ta buɗe idonta ta kalle shi, lokacin agogon ɗakin ya nuna ƙarfe sha ɗaya da rabi na safe.
"Tashi ki saka kaya, ga Habu can ya zo, za mu je a duba ki"
"Na ce ka daina gaya musu, mu daina saka su ɗawainiya"
"Tashi ki daina yi mini jayayya" ya yi maganar, yana tsuke fuska.
Ta tashi da ƙyar, ya taimaka mata ta saka kaya, ta saka hijjabi, a harabar gidan suka tarar da Habu. Ya yi mata sannu suka fice.
Tun da ya kira Habu ya sanar masa, dama da adaidaita sahu ya zo. Wani ƙaramin asibiti suka je. Buzu yana tare da Nana, Habu ya yi ta shiga yana fita.
Ya sayo kati aka duba ta, aka ba ta gwaje-gwaje. Sun ɗan jima a gurin ɗaukar jinin, ta gaji da zaman, ta zame tana ƙoƙarin kwanciya a gurin, amma ya riƙo ta tsam a jikinsa. Ayshacool Suka koma gaban likita da sakamakon, ya duba ya kalli Nana ya ce "Yaushe rabon ki da Al'ada?"
Tamkar ya sokawa Sayyid mashi, ji ya yi ina ruwansa da zai yi mata wannan tambayar? Amma ya dake bai yi magana ba.
Nana ta gaya masa, ya ce "Ok, to akwai ciki ne, sai kuma malaria++ bai kamata a ce, ga juna biyu ba kuma ga malaria ki na fama ba. A kula sosai. Zan rubuta ruwa da allurai a saka miki, za ki ɗan ji ƙwarin jikin ki in sha Allah"
Ya yi rubuce-rubuce ya basu, Sayyid ya karɓa suka fito.
Ya miƙa wa Habu katin, aka nuna musu inda za su kai Nana.
Habu ya kalle shi ya yi masa magana da yaren su, ya cewa Habu "Tsaya" ya saka hannu a aljihunsa ya ɗaukko kuɗi ya ba wa Habu"
Habu ya kalli kuɗin ya kalle shi, ya ce "Da can kuɗin yi wa Nana amfani da su.
Wani ma'aikaci ne, ya shigo ward ɗin zai sanyawa Nana cannular. Nana ta miƙa masa hannun, ya kai hannu zai kama ya saka mata Buzu ya riƙe hannun Nana.