Kenza eBookz

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 23

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 23

Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 23: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 23. Ma'aikacin ya ce "Allurai zan yi mata, zan saka mata cannula ne" ya yi…

3,375 words

Ma'aikacin ya ce "Allurai zan yi mata, zan saka mata cannula ne" ya yi shiru ya ƙi magana. Nana ta kalli yadda launin idonsa ya canza. A ranta ta ce "Allah ya yaye maka wannan azabar kishin Sayyid"

Habu ya yi gyaran murya, ya "Ka yi haƙuri, a saka mata, ka ga tana shan wahala sosai. Ya yi mursisi, ya murtuke fuska, ya riƙe hannunta gam, ya ƙi saki. Sai da Habu ya zauna ya din ga yi masa bayani da yarensu, cikin tattausar murya. Ƙarshe ma'aikacin gefe ya koma, ya zubawa sarautar Allah ido. Tamkar gunki ya yi gum, ya ƙi motsi kuma ya ƙi magana.

"Ni idan ba zai yarda a saka mini ba, dan Allah ku mayar da ni gida, na je na kwanta na gaji" ta yi maganar a raunane, cikin yanayin rashin lafiya.

Da ƙyar ya saki hannun Nana, sai dai ya kawar da kansa gefe, saboda yadda zuciyarsa ke tafasa da ganin ya kama hannun Nana ya saka mata ruwa.

Har huɗu su na Asibiti, sai dai ta ji dadin jikinta, zazzaɓin ya sauka.

Aka gama saka mata ruwan, sannan suka tafi gida. Ba ya jin nauyi ko kunyar Habu, haka yake rungume da Nana yana shafa ta, kamar zai lashe ta ya mayar da ita cikin sa.

Suka koma gida, Nana ta samu ruwa ta yi wanka, ta saka kankanar da ya saya mata a gaba, ta din ga sha, saboda itakaɗai ce ta ji ta yi mata daɗi.

Suna harabar gidan, Habu yana yi masa magana, sai ga babar su Yusra ta ƙaraso.

"Kai mai gadi, ina ka tafi baka yi wa kowa bayani ba? Zamu kai Siyama wankin ƙonuwar da ta yi, amma ka yi tafiyarka yawon ka?"

Habu ya ce "Ki yi haƙuri Hajiya, mai ɗakin nasa ce babu lafiya, ba a nuste yake ba, hankali tashe mu ka tafi Asibiti ki yi haƙuri dan Allah"

"Ni ma tawa 'yar babu lafiya ai, ba sai ya yi bayani ba. Tun da idan zai je wani guri yana rubutawa Jamil ba, sai Jamil ne ya buɗe mana muka tafi, ƙonuwar na ta jini"

Habu ya sake cewa "Ki yi haƙuri dai dan Allah"

Ko ɗaga kai bai yi ya kalle ta ba, balle ya kula ta, ko ta saka ran zai ba ta haƙuri, ya bar ta ita da Habu.

"Sannu"

Ta jinjina kai ta ce "Sayyid da ka sani ka ba ta haƙuri, ba na son wannan faɗan da ake yi maka"

"Ya jikin? Kin daina jin zazzaɓin?"

"Amma ka san mun yi laifi, bai kamata mu tafi ba su sani ba"

"Da suka buɗe ƙofar sun mutu ne?"

Nana ta sauke numfashi ta ce "Aishikenan, idan ka janyo aka kore mu, ka nemo mana inda za mu zauna ai" ya yi shiru, bai kuma cewa komai ba.

Daga bisani ya ce "Me za ki ci?"

"Ba komai, ba na son komai, kankanar nan ta ishe ni".

A hankali ya kai hannunsa, ya shafa gashin ta, ya saki murmushi ya ce "Kitson nan ya yi kyau sosai, ya dawo da hannunsa kan hannunta, ya jujjuya hannun, ya kai bakinsa ya sumbata ya ce "Kin yi mini kyau"

Ta kalle shi galala ta ce "A hakan da na fita hayyacina. Tun jiya na so ka kalla ka yaba ba, ka share ni ka yi ta yi mink faɗa"

"Idan na ce kar a yi, to a bari ne kawai, ba na so. Me yasa zan ce kar ki je guri ki je?"

Jiki a sanyaye ta ce "Na san na yi laifi, ka yi haƙuri. Za su ga kamar wulaƙanci ne, sun gaya mini abu na tashin hankali, amma na kasa yi musu jaje. Sayyid ban ji ka ce komai ba, a kan abin da aka ce"

"Wanne?"

"Da likitan ya ce... Sai kuma ta yi shiru.

"Ya ce me?"

"Ina da juna biyu, tsoro nake ji" ta yi maganar tsoron na bayyana ƙarara a kan fuskarta.

"Tsoron me?" Ayshacool Abin da ta so furtawa daban, amma ta kauce faɗar hakan, kar ta tayar masa da hankali ta ce "Ban ga ka yi murna da hakan ba"

Ya gyara zamansa ya dubi Nana a tsanake ya ce "Wata irin wutar zafin, ganin wani ya taɓa ki ne, take ci mini zuciya. Amma wallahi ina cikin murna zamu ƙara yawa, nima Ahalina zai cika, ki haifi namiji mai kama da ni. Ko kuma mace mai kama da ke"

Murmushin dole Nana ta yi, ba dan ya kai zuciyarta ba ta ci gaba da tauna kankanar bakinta a hankali.

*

Yanayin yadda aka banko ƙofar gidan, sai da Baba ya tsorata kamar ya zura da gudu. Ya dai tsaya ya ce "Kai wani mara hankalin ne ya ke yi mana wannan banzan bugun haka?"

Bai yi magana ba, sai ganinsa Baba ya a tsakiyar gida, tamkar ya faɗo daga sama.

"Uban me ya kawo ka gidana?"

"Gidan Ubana ne" ya faɗa yana ɗan rarraba ido yana kallon gidan.

"To uban me ya dawo da kai? Nan ka saka 'yan sanda suka din ga yi mini sintiri a gida, ka kai Gaddafi ƙara, kuma ka gudu, da yake kai duk inda ka tsuguna babu alkhairi tsiya ce take biyo baya. Ka bar mini gida kafin 'yan sanda su zo neman ka"

"Ni fa ban kashe kowa ba wanda suka yi abin ma an kama su, kawai ka wani din ga kora ta, idan na gama abin da nake yi da kaina zan bar maka gidan ai. Ka yi ta wani gidanka kamar wani gidan arziki"

Baba ya ce "Tun da ba na arziki ba ne ba, zo ka fice"

Imarana ya ce "Wallahi ba zan tafi ba. Ina Nana? Ke Nana"

Nasiru ne ya yi sallama a gidan, hannunsa riƙe da ledar kayan miya, yana ganin Imarana ya tafi da gudu ya rungume shi.

Imarana ya ce "Nasiru, na ga kana nema ka kamo ni a tsawo. Wai ina Nana ne?" Baba yana ƙiftawa Nasiru ido, amma tuni ya kwatsa wa Nasiru bayani.

"Ai an yi mata aure"

Turus Imrana ya yi ya ce "Kamar yaya? Uban waye ya yi mata auren ban sani ba?"

"Ni ne nan ubanta, idan kuma kai ka haife ta da sai an sanar da kai sai na ji"

"Kut.. aure fa, wa ka aura mata, ina fatan ba wannan ajawon bane Salisu yake ko wa?"

"Ba Saleh ba ne, wani Buzu ne mai gadi" Nasiru ya sake ba wa Imrana amsa.

Kai tsaye ya ƙundumo ashariya ya ce "Wane irin Buzu kuma? Kai ina ne gidan da aka kai ta?"

Baba ya ce "Wallahi ka taka ka je gidanta ban yafe maka ba. Kar ka kuskura ka je ka yi mata hauka ka kashe mata aure"

"Wallahi sai na je, dama kula ka ke da ni, shi ne za ka yi mini Allah ya isa ta kama ni, amma tun da ni nake kula da kaina ba za ta kama ni ba. Kai Nasiru wuce mu je ka raka ni"

Baba ya ce "Nasiru idan ka raka shi, sai na yi maka dukan tsiya"

"Kai mu je zan baka dubu biyu"

Nasiru ya waiga yana kallon Baba, ga batun kuɗi ya ji, ya maze ya bi Imarana suka fice, Baba na ƙwala masa kira amma ya fifita dubu biyu a kan kiran Baba.

Su na tafe a hanya, Nasiru yana ba wa Imarana labarin, abin da ya faru da yadda aka yi auren Nana. Ba ƙaramin fusata Imarana ya yi ba.

Mussaman da ya gaya masa, gadi Buzu yake yi.

"Uban me mai gadin zai tsinana mata, Allah na tuba mu dai ba mu yi dacen uba ba wallahi mu dai kawai ya kawo mu Duniya yana neman maraba da mu."

Sayyid na zaune yana shan shayi, a harabar gidan ya ji an taɓa gate. Ya rufe fuskar sa da sauri, ya tashi ya je ya buɗe, ya tsaya yana kallon Imran, saboda tsananin kamnninsa da Nana.

Babu jiran komai, Imrana ya ƙarasa hankaɗa ƙofar ya shiga, Nasiru ya bi bayansa.

Nasiru ya ce "Ga mijin Nanan nan" ya yi maganar yana nu na masa Buzu.

Imran ya ƙare masa kallo, ya ce "Ikon Allah, kai ka auri Nana? Tana ina?" Sayyid ya yi shiru yana kallon Imrana.

"Malam magana nake yi, ko kurma ne? Ina take?"

Nasiru ya ce "Kamar fa ba ya magana, amma Nanan tana cikin ɗakin nan"

"Dan Allah ji wulaƙanci, ɗakin mai gadi, ba ta samun arzikin a ajiye ta a gida ba ma, sai ɗakin daga shi waje, koma mene ne ya zo ya afka mata"

Nana tun tana banɗaki take jiwo, kamar muryar Imran, amma ta kawar da tunanin, a ganinta mai zai kawo shi yanzu.

Ta fito daga banɗakin ya shigo, Nana ta zabura ta ce "Imrana" sai kuma ta tsaya da tuna halin Buzu a kan kishin tsiya. Ayshacool "Ke ashe ba ki da hankali? Ki ka zauna aka aura miki mutum kawai ki ka biyo shi yawon gadi? Gidan babanki ba mamora gidan miji ma haka? To wallahi sai kin bar gidan nan, sako hijjabinki mu tafi"

"Imarana mu tafi mu je ina?"

"Ko ma ina ne. Amma wallahi ba za ki zauna a gurin nan ba. Haka zamu zauna babu ci gaba?"

"To ka zauna mana, ka sha ruwa ka ci abinci, sai mu yi magana. Mama ma ta yi mini aike su Adda Saude sun zo...

"Dalla rufe mini baki, ina ruwana da wata? Addar wofi da can ba su zo ba sai yanzu. Ki ɗaukko hijjabinki mu tafi daga nan har human rights, na san biyayya kawai ki ka yi wa Baba ki ka auri mutumin nan, tun da dama ke ba sanin ciwon kanki ki ka yi ba"

Nana ta yi shiru, tana kallon in da Sayyid yake tsaye, ya tsare ta da ido. Tsoro take ji kar Sayyid ya yi wani abun da zai tunzura Imran, dan ta san ko zai kashe shi ba zai yi shiru ba.

"Imran na gode da ziyara, da kuma soyayyar da ka ke nuna mini. Amma ka yi haƙuri ina son aurena"

Wani irin takaici ya kama Imran ya ce "Nana me za ki zauna ki yi a shago, ɗakin nan meye marabarsa da shago? Na san zaman gidanm ne ba kya so, ba can za ki koma ba. Harkoki sun fara buɗe mini, karatu zan mayar da ke, kyakyawar rayuwa nake so na ga kin yi"

Ta sake kallon Buzu, da ya zubo mata idanunsa, Imran ya waiwaya ya ga abin da take kallo.

Sayyid ya shigo cikin takunsa na kamala da nutsuwa.

Ya sauke takunkumin fuskar sa, ya sakar wa Imrana murmushi, ya ce "Kun yi kama sosai, da alama ku na da alaƙa sosai" ya yi maganar yana miƙa wa Imran hannu su gaisa.

"Ba zan gaisa da kai ba, ƙanwata za ka sakar mini, Nasiru ya gaya mini duk wani abin da ya sani. Ni ban ji na gamsu da wannan auren ba ko kaɗan. Ya za a yi sama ta ka a aura miki mutumin da ba ƙabilarmu ba, babu wani dogon bincike. Ni jikina yana bani wani abu, ni ban yarda da auren nan ba gaskiya."

"Nima na fuskanci akwai sharuɗɗan da ban cika ba, aka yi wannan auren. Amma ko me za a yi mini, ba zan iya rabuwa da ita ba, tana ɗauke da ruhina a jikinta. Idan ka raba ni da ita, ni ya zan yi? Zan kula da ita, ka daina raina inda Allah ya ƙaddara zamana da ita, ba ka san gobe ba"

Imrana ji yake kamar ya mangare Buzun nan ya huta, haka kurum ya ji bai yi masa ba. Kuma ya san wannan kyawun ne ya ruɗi Nana, har take cewa ita ba za ta rabu da shi ba.

Ya sake kallon Nana ya ce "Kin zaɓi zama ko Nana?"

Idonta fal hawaye ta ce "Ka yi haƙuri Imran, Allah ne ya haɗa ƙaddarorinmu, ba komai zan iya yi maka bayani ba, amma ina son aurena. Sayyid na buƙata ta a rayuwarsa".

Imran ya haɗiye wata irin ƙwallar takaici. Ya zura hannu a jakarsa, ya ƙirgo kuɗi, ya tako gaban Nana, ya kamo hannunta ya saka mata ya ce "Ga wannan babu yawa, cikin abin da nake tarawa ne, domin na dawo gida na inganta rayuwar ki. Dama Saboda ke na dawo, daga nan ko gida ba zan kma ba, zan tafi inda na fito. Kai kuma tun da ta zaɓi zama da kai, idan ka ci amana na bar ka da mai hudowar rana da faɗuwar ta"

Ras Sayyid ya ji gabansa ya faɗi, ya ji maganar Imran ta yi masa nauyi da yawa.

Ya kalli Nasiru ya ce "Mu tafi"

Nana da tuni hawaye ya wanke mata fuska ta ce "Imrana ba zaɓarsa na yi a kan ka ba....

"Shhh ba sai kin yi mini bayani ba ai, tun da ki na farin ciki da auren ki Alhamdilillah" ya juya zai fita ta sake cewa "Ka bani lambar wayar ka, da zan din ga kiran ka a waya" bai waiwayo ba ya girgiza kai, ya ce "Babu buƙata"

Daga bayansa, yanayin yadda ya kai hannu fuskarsa, Ya sanya Nana gane Imran kuka yake yi. Sakin kuɗin hannunta ta yi a ƙasa ta durƙushe a gurin ta fashe da kuka mai tsuma zuciya ita ma.

Ayshercool 08081012143 Ayshacool "Jiki Alhamdilillah " ta yi maganar tana mayar da hankalinta, kan Hajiya Amina.

"Mummy, wai dan Allah lokacin da aka yi mini tiyata, da a ka fito da ni, an baki babyn a hannunki kin gani"

Hajiya Amina ta ce "Sau nawa zan yi miki bayani Shukura, ke kaɗai aka fito da ke, ba a bani jaririn ba. Doctor Sharif ya ce na ɗan jira, jaririn ne ake fama, ko ba bu wadatacciyar iska ko me, oho maganganun su na likitoci. Na dawo ɗaki gurin ki, ya shigo ya ce mini, an kai babyn Nursery, da safe na je na gan shi"

Alhaji Zailani ya yi gyaran murya ya ce "Shukura, duk wani abu da za ki yi, abin da ya faru ya faru, ba za ki yi jayayya da ikon Allah ba. Kamata ya yi ki gode wa Allah, da ya baki lafiya. In dai da rai da lafiya, Allah zai baki wani mai amfani. Yanzu lafiyar ki muke buƙata, wannan damuwar ba ta dace da ke ba. Kin rasa babynki, nima ba zan so rasa tawa babyn ba, Please ki yi tawakalli na san kin sha wahala a kan cikin nan, amma ki yi haƙuri"

Shiru Shukura ta yi, zuciyar ta fal wasi-wasi. Ta ƙara ƙaimi gurin yaƙar mummunan tunanin da yake ta yi mata yawo a zuciya, ta hanyar kawar da batun mafarki da ta san ba gaskiya ba ne ba. Duk mahaifiyarsu ta rasu, amma ba su tashi da zafin maraici ba, Alhaji Zailani ya yi aiki tuƙuru a kan rayuwar su, Hajiya Amina ma kuma ba ta taɓa yi musu mugunta ba, ta riƙe su da gaske tamkar 'ya'yanta. Saboda haka take ganin tamkar zuciyarta ba ta yi mata adalci ba. Amma fafur take jin ƙiyayyar mahaifin nata a cikin zuciyarta, ta kuma kasa yarda da cewa ɗan ta mutuwa ya yi ta haƙiƙa, ba wani abin ne ya faru ba.

****

Kwana biyu Nana ta samu sauƙin jikinta, jikinta ya ɗan yi ƙwari babu zazzaɓin. Sai dai abinci ne ba ya ciwuwa ta daɗin rai.

Ta saka Sayyida a gaba, a kan lallai sai ta yi wa gashinsa kitso, ta gaji da ganin kan a haka. Yana kwance a kan cinyarta, ta saka kibiya tana tsaga gashin nasa. Ta ce "Sayyid kishi nake da gashin nan naka, gaskiya aske shi zan yi, ya za ayi ina matarka a ce ka fi ni gashi?"

Ya yi dariya ya ci gaba da kallon da yake yi da wayarta. Ta yi guda biyu ta ce "To gyara, a yi na can ɓangaren"

Ya girgiza kai ya ce "Ki ƙyale ni"

Ta ce "A'a sai an ƙarasa"

Fafur ya ƙi gyarawa, ya ce shi fa kitson da zafi.

"Dan Allah ka yi haƙuri mu ƙarasa, haba Shugaba ba ka ga yadda kitson nan ya yi kyau ba. Yauwwa nawan" ya ɗago kansa ya harare ta. Ta sakar masa murmushi tana lumshe masa ido. Ya gyara kwanciyar, ta ci gaba da kitsa gashin nasa, mai matuƙar santsi da laushi.

Babu tsammanni aka bankaɗo labulen ɗakin, sai da Nana ta razana, a hankali ya ɗaga kai ya kalli ƙofar.

Siyama suka gani a tsaye, Kunya ta kama Nana,yanayin da ta tarar da su. Shi kansa dogon wando kawai a jikinsa, ya ɗora kansa a kan cinyar Nana, tana yi masa kitso.

"Amm dama Mami ce ta ce na zo na duba, ko Yusra ta zo ba mu ganta ba da ma. Amma shikenan" Ta saki labulen a hankali ta ja da baya, saboda yadda jikinta ya yi sanyi.

Kamar babu abin da ya faru, ya ci gaba da kallon wayarsa.

" Ya jikinki ya yi sanyi? Me ya faru?"

"Ba komai" ta furta a hankali.

Ya juyo sosai ya kalle ta, sai kuma ya fasa maganar da ya yi niyya, ya sake gyara kwanciyar sa.

Dannewa kawai Nana ta yi, amma sai da ta ji tamkar ta ɗura wa Siyama ashar, saboda kawai su na masu gadi, ya ba ta damar ta shigo musu ɗaki, ba bu izini. Danne fushin ta ta yi, saboda kar ta saka shi a damuwa, amma tana ji a ranta wataran sai ta zagi Siyama.

Da yamma, Nana ta yi kwalliya cikin doguwar rigar material mai taushi, da hula. Ta fesa turare sannan ta ɗora girkin dare, sannan ta kunna turaren wuta a ɗakin. Neman guri ya yi ya zauna a ɗakin ya ƙi fita, sai aikin kallonta kawai da yake yi.

"Shugaba, ba zaka fita shan shayin ba ne?"

Ya yi dariya ya ce "Kin yi kyau sosai da sosai, ba zan fita ba"

Ta sake cewa "Ka ga yadda ka yi kyau da kitson nan kuwa? Zo ka ga"

Ya yinƙura ya taso, ya zo ya tsaya a gaban ta, ta nuna masa mudubi ta ce "Kalli yadda ka yi kyau fa"

Ya shafa kansa ya ce "Na zama kamar mace"

Ta yi dariya ta ce "Ka yi mini kyau sosai a haka, dama nikaɗai ya dace na ga ka yi kyau".

Ya sunkuyo ya yi mata kiss a goshinta. Ayshacool Cikin dariya ta ce "Ni idan ka na yi mini wannan abun, kunya ka ke bani"

Ya ce "Wanne?"

"Ko wanne" ya ƙara tsare ta da ido, da sai da ya sanya ta sunkuyar da kanta saboda kunya.

"To matsa na wuce"

"A'a kirana fa ki ka yi"

Ya yi maganar yana haɗa bakinsa da nata.

Bayan ya cika ta, ta sunkuyar da kanta tana jin kunya. Ji ta yi jikinta ya fara sanyi, ƙirjinta yana bugawa, ta kalle shi ta ga fara'ar fuskarsa ta kau, ya haɗe rai. A tsorace ta ɗan ja jikinta, tana tunanin me ta yi masa. Tana kallon mudubin ta ga duhu ya gauraye ɗakin sai iya wannan tsohon ta iya gani a cikin mudubin a tsaye, sai dai a wannan karon ci yake yi da wuta. Tattara nutsuwarta ta yi, ta fara Addu'a a cikin zuciyarta, ta waiwayo ta kalle shi.

Ta ga fuskar sa ɗauke da murmushi.

Ya miƙo hannunsa zai taɓa ta, ta riƙe hannunsa, ta yi yinƙurin kallon idonsa amma ta kasa, ta ji tamkar zuciyarta za ta buɗe.

"Waye kai?"

Ya amsa da "Mijinki mana"

Ta yi murmushi ta ce "Ba Sayyid ba ne? Ai na riga na ganka. Me yasa ka zaɓi muzgunawa rayuwata ne? Da ina zargin ko Ƙaisar ne, amma na fara fahimtar kai daban shi daban. Mece ce manufarka a kaina? Me ka ke buƙata?"

AYSHERCOOL 08081012143 Ayshacool Wata irin dariya ya saki, ya ce "Har kin yi ƙwarin da ki ka daina razana da ganina kenan. Haka nake so fansa zan ɗauka, yanzu ne lokacin da ya dace na ɗauki fansata"

"Wani laifi na aikata maka da ka ke iƙrarin ɗaukar fansa a kaina"

Ba tare da tsammani ba, ya shaƙe ta, ya ɗaga ta ya yi jifa da ita, ta bugu da jikin wardrobe ta faɗi.

Ɗakin ya gauraye da matsanancin duhu, ta riƙe wuyanta tana numfarfashi cikin yanayi mai kama da ɗimuwa da kuma suma.

Readers Also Read