Kenza eBookz

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 24

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 24

Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 24: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 24. Ta daɗe a haka kan ta ji kamar daga sama muryar Sayyid.

3,364 words

Ta daɗe a haka kan ta ji kamar daga sama muryar Sayyid.

"Rayuwata bacci kuma daf da magariba a ƙasa? Ga abincinki ya fara ƙonewa" Nana ta ɗaga kai ta kalle shi suka haɗa ido, amma ba ta ji komai ba. Ta tashi da ƙyar ta ji mararta ta ƙulle, ga hannunta da ta bugu. Amma ta daure ta kashe gas din, ta shiga yin alwala.

Abubuwa da dama su ka zo zuciyarta, tabbas wannan sabon ƙalubale ne a gare ta. Muddin zai cigaba da fita daga hayyacinsa yana yi mata haka, to tana tsoron wataran ya yi mata illa.

Haka kurum yake jin sa cikin farin ciki, sai dai lokaci ɗaya ya lura ita ba ta cikin walwala.

Su na cin abinci, ya ɗan shafa cinyarta. Ta farga ta kalle shi.

Ya ce "Ba kya cin abinci mene ne?"

Ta yi murmushi ta ce "Lafiya ƙalau, Abincin ne ba na so"

Cikin damuwa ya ce "Na sayo miki buredi za ki ci? Ko ƙos"

"A'a zan ci wannan ɗin" da ƙyar ta tilasta kanta, ta ci.

Yanayin yadda yake ta bin ta da ido, ya sanya ta san akwai abin da yake so, sai dai a ɗan tsorace take. Haka ta ci gaba da addu'oi da neman ɗaukin Ubangiji.

Duk da haryanzu tana jin nauyin sa, amma ta shirya cikin kayan baccinta na gwanjo, da Ummi ta ba ta ta shafa turare. Sai dai zuciyarta gaba ɗaya a tsinke take.

Kwanciyarta babu jimawa, ya zo ya kwanta shi ma.

"Rayuwata duk kin rage walwala"

Ta ɗan ja numfashi ta ce "'yan kwanakin nan, baki ya buɗe, Ubangiji Allah ya ɗorar da lafiya"

"Amin ma vie. Ina jin daɗin haka sosai"

"Saura kuma, Ubangiji Allah ya sanya ka tuna waye kai. Hankalina zai fi kwanciya"

Ya ɗan yi shiru ya ce "Ina wannan ƙoƙarin, ji nake kamar abin ya fi ƙarfina. Amma ko da nan gaba, idan ban tuna waye ni ba, ki nuna wa ɗa na su Habu a matsayin dangina, tun da ku kaɗai na sani" Ya yi maganar muryarsa na rawa.

"Shikenan mu bar wannan maganar." Ya yi shiru bai kuma magana ba.

"Sayyid fushi ka yi ne?"

"A'a ban yi fushi ba"

Ta din ga shafa kansa zuwa bayansa, sai dai daga ƙoƙarin rarrashin sa, ya fara ƙoƙarin zarcewa.

A hankali ta fara jin wannan ƙamshin turaren, yana ratsa kafofin hancinta.

"Sayyid ba ka jin wani ƙamshin turare?"

"Ina ji a jikinki"

"A'a ji nake kamar ba a ɗakinmu muke ba"

Ya yi dariya, ya cika ta ya ce "Ba sai kin yi mini wayo ba, na ƙyale ki" Ya ɗan ja jikisa ya koma gefe, yana ajiyar zuciya. Ta ɗora hannunta a kan nasa ta ce "Ba wayo zan yi maka ba, ai ka san ba na gudun ka."

"Kar ki damu, ki yi bacci" ya ɗora kanta a ƙirjinsa yana shafa bayanta.

*

Shukura ji take yi, tamkar za ta haukace, sai kokawa take da sashe daban-daban na ƙwaƙwalwarta, domin samawa kanta nutsuwa. Gari ya tsit amma ita sai kaiwa take yi tana komowa a cikin ɗaki, tamkar mai jiran saƙon wani abun.

Ta zauna ta haɗa kai da gwiwa ta yi tagumi. Ta sake tashi tsaye, ta tafi bakin taga ta tsaya tana kallon waje. Ta ƙudurce a ranta, sai ta tuntuɓi doctor Sharif ta ji mene ne ya kashe mata ɗa? Haryanzu ta kasa samun nutsuwa da kwanciyar hankali.

Alhaji Fatuhu kuwa, ƙarfin hali kawai yake yi, ji yake tamkar an daddane rayuwarsa da jikinaa gaba ɗaya. Babu abin da yake yi masa daɗi, ya daina jin daɗin komai, tamkar ya fasa ihu ko zai ji sanyi a ransa. Ƙarfin hali ya yi gurin sanya Fadila farin ciki, har ya samu ta yi bacci, tun da ta yi bacci ya raba ta da jikinsa a hankali, ya tashi zaune ya rafka tagumi ya din ga jin tamkar ana buga masa abu mai nauyi a kansa.

Ya shiga banɗaki ya yi wanka, ya yi alwala ya zo ya tayar da salla, amma tunani da wasi-wasi ya mamaye shi, ya kasa nutsuwa a cikin salla. Ya din rafkanuwa. Ya din ga sallamewa yana sake tayarwa har ya gaji ya nemi guri ya zauna. Ayshacool Tunanin yadda kayansa za su iso, a sallami mutane ya ƙara mamaye kansa, ya rasa bakin zaren matsalar baki ɗaya, haka ya zauna har aka yi kiran sallar asuba.

**** Tari ne ya sarƙe Nana, ta tashi ta ji kamar wadda ta ƙware tana numfashi sama-sama. Ta shafa ta ji Sayyid ba ya gurin, ta ji an kama hannunta an bata kofi, ta karɓa ta shanye ruwan, ta ajiye kofin saboda yadda wani irin nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita.

Ƙaisar ta gani a tsaye yana kallonta, jikinsa duk a ƙone, bai yi mata magana ba, ya danƙi wuyanta ya zuba mata wani abu mai kama da hayaƙi a cikin bakinta.

A take ta ji cikinta ya hautsuna, mararta ta ƙulle, ta kalle shi a razane ta ce "Ƙaisar me ka yi mini?".

"Cikin jikinki ba shi da amfani, dole ya bar jikin ki"

"Saboda me, ina ruwanka da cikina?"

"Saboda ba zan ƙarar da rayuwata a matsayin bawa ga zuriyar ku ba, ki na wahalar da ni."

Kafin ta yi magana, ta ji tamkar ana fizgar naman cikin mararta, ta yinƙura ta tashi a gigice.

"Subhnallah, Sayyid, Sayyid" ta kira sunansa a wahale.

Daga banɗaki ya fito a tsorace, ya nufo ta. Ta miƙa masa hannu, ya riƙe ta.

"Kai ni banɗaki" ta faɗa tana rintse idanunta.

Ya kamata ta miƙe, jini ya fara biyo ƙafafuwanta, ya kai ta banɗaki. Su na shiga ta durƙusa a kan gwiwoyinta, ta saka hannu ɗaya ta rirriƙe ƙafarsa tana girgiza kanta cikin matsanancin ciwo. Da ta ja numfashi da ƙarfi, sai ta ji jinin yana zuba da yawa. Ya rasa yadda zai yi, ga baki ya rufe ya kasa magana.

Can ta yi wani irin nishi, ta ƙara rirriƙe ƙafarsa da ƙarfi, sai ga gudan jini ya faɗo. A hankali ta din ga samun releif, ta jinginar da kanta a jikin ƙafarsa ta kasa motsi. Jin yadda ƙarnin jinin ya ishe ta, ya sanya ta motsa a hankali, ta yinƙura ya kama ta, ta tashi tsaye.

"Ka canza kaya ka yi sallar, bari na wanke jikina"

Ya motsa baki, amma magana ta gagara, ya dage yana ƙoƙarin yi, amma gumi ya fara tsatstsafo masa.

"Ya lafa mini, ka yi salla kar ka makara, zan wanke jikina" da ƙyar ya fita, ta rufe banɗakin ta wanke jikinta, duk da tana jin sauran ciwon kaɗan kaɗan.

Ta fito yana salla, ta ɗaura zani, kan ya idar ta goge gurin da ta ɓata, ya idar ya ƙaraso gefen katifar da ta zauna, idanunta har sun faɗa saboda wahala.

Ya zauna ya saka ta a gaba, ga magana amma abu ya gagara, ta kwanta a kan cinyarta, ga ciwon buguwar jiya, ga rashin lafiya da ba ta gama warkewa ba, ga kuma wannan matsalar da ta tashi da ita.

A hankali yake shafa jikinta, yana ɗan matsa mata, ta ji daɗin hakan sosai da sosai. Wajen ƙarfe bakwai, ta kira Ummi, Ummi ta ɗaga ta ce "Lafiya, kira da sassafe?"

"Kira ni kuɗina ba su da yawa"

Ummi ta kira ta, ta ce "Lafiya na ji muryarki a haka?"

"Ba na jin daɗi ne Ummi, dan Allah tambayar ki zan yi, idan mutum yana da ciki yana period ne?"

"Wane irin period kuma? Dama ciki ne da ke? Haba ni fa in ce ranar da ki ka zo na ga alama wallahi. Meyafaru?"

"An ce akwai, kuma yau na tashi da ciwon mara ina zubar da jini"

"Kai, subhnallah bari na sallami yara, gani nan zuwa gidan naki"

Duk da jikinta babu ƙwari, ta tashi ta saka kaya, ta kunna turaren wuta, Saboda a hancinta ba ta daina jin ƙarnin jinin nan ba.

Wajen tara da rabi sai ga Ummi.

Ummi ta gaishe shi, ya ɗaga mata hannu tare risunar da kansa, ranar farko da Ummi ta gan shi babu rawani, ya sha kitso a kansa jelar ta sauka a kafaɗarsa.

Ta ƙarasa inda Nana take cikin kulawa ta ce "Sannu Nana ya jikin?"

"Alhamdilillah"

"Gaskiya ki zo mu je a yi scanic, mu tafi Asibiti"

Nana ta girgiza kai ta ce 'A'a ba sai mun je ba, ni ba na son mu je, a yi ta huda ni"

"To Nana lafiyarki ba ta fi komai ba, tashi mu je"

Nana ta kalle shi, yadda ya tsare su da ido, ta ce "Sayyid za ta raka ni Asibiti, ka zauna kar su zo yau ma a neme ka, baka nan ya zama abin magana."

Ta kalli fuskarsa ta ce "Na gane, ba sai ka yi magana ba"

Ya tashi ya buɗe wardrobe ɗin sa, ya ɗaukko kuɗi, ya miƙa wa Nana.

"Ka bari da kuɗi a gurina, wanda Imrana ya bani"

Tsuke fuska ya yi, dole ta saka hannu ta karɓa, ya ɗauki mayafin yin rawaninsa ya yafa a kansa, ya biyo su har bakin gate, yana kallon Nana. Ayshacool Ta ɗaga masa hannu tare da yin murmushi, shi ma ya ɗaga mata.

Su na fita Ummi ta dasa mita, ta ce "Jaraba, wannan kallon da yake yi miki, sai da na ji kamar na bar masa ke na yi tafiyata, Nana sai ka ce auren Soyayya bawan Allah duk a rikice yake. Kuma dan Allah yana magana, anya na taɓa jin maganarsa kuwa?"

Nana ta yi murmushi ta ce "Yana yi mana"

"To ai ban taɓa ji ya yi ba. Kai tubarkallah Nana Allah ya baki kyakyawan miji, sai ki yi ta kaffa-kaffa saboda 'yan mata. Kodayake yadda yake yi ɗin nan ma wace za ta ce tana so?."

Nana ta yi murmushi.

Ummi ta sake cewa "Na ji daɗin ganin yadda ya nuna damuwarsa a kan ki, Ubangiji Allah ya sanya ya ɗore. Nana idan hankalin mace a kwance yake a gidan mijinta, komai mai sauƙi ne"

Da haka suka ƙarasa Asibiti, su na zuwa aka tura su scanic, da suka yi suka koma, aka tabattar da cikin ya fita. Aka ba wa Nana magunguna suka dawo gida.

Yana ganin dawowar su, ya tashi. Nana ta yi masa murmushi suka wuce ɗaki.

Nana ta cewa Ummi"Kar ki gaya masa, zan gaya masa da kaina"

Ummi ta ce "To shikenan" ta wanke wa Nana kayan da ta ɓata, ta ƙara gyara mata ɗakin, ta yi mata girki. Duk yana waje ya kasa shigowa. Sai da Ummi ta gama ta yi wa Nana sallama, ta fito za ta tafi, sannan ya taso.

Da ƙyar ya iya cewa "Na gode" shi ma sai da ya ji tamkar numfashinsa zai ɗauke.

Ummi ta ce "Ba komai Allah ya ƙara lafiya".

Ya shiga ɗakin da sauri, ya tarar da Nana a zaune a gefen katifa, ya zauna a kusa da ita, ya kamo hannunta, tare da tsare ta da ido. Yana jiran ta yi magana.

Ta numfasa ta ce "Sayyid, ɓari na yi"

Yanayin fuskarsa ya sanya ta fahimci bai gane me take nufi ba.

"Cikin babu, ya fita, jinin da na zubar cikin ne ya zube"

Ji ta yi tamkar hannunsa da ya riƙe ta da shi, ya yi mata shocking, saboda wani irin zirr da ta ji.

A take fuskarsa ta yi jawur, ya ji tafukan hannayensa sun ɗauki zafi, jijiyoyin kansa sun mimmiƙe. Ya ci gaba da motsa bakinsa zai yi magana, amma ya kasa.

"Sayyid lafiya kuwa? Ko wani laifin na yi maka?"

Ya din ga murza tafukan hannayenta da ɗan ƙarfi, yana sauke numfashi.

"Sayyid mene ne?"

Bai yi magana ba, jin ya kasa maganar ya sanya, ya saki hannunta, ya nemi guri ya kwanta yana haki sama-sama.

Abun duk sai ya ɗaure wa Nana kai, to mene ne ma'anar hakan? Me ya sanya shi canzawa haka lokaci guda? Ta waiwaya ta kalle shi, ta ga ya lumshe idanunsa. Ta ɗan matsa kusa da shi, ta taɓa jikinsa ya ji ya fara ɗaukar wannan zafin. Kafin ta yi wani yinƙuri tuni ya fara wannan jijjigar, jikinsa yana kakkafewa. Kawai ta zuba wa sarautar Allah ido, tare da rashin sanin cikakken abin yi.

Ayshercool 08081012143 Ayshacool Ganin abun ba na ƙare ba ne, ya sanya Nana yinƙurawa da ƙyar, jikinta babu ƙwari, ga sanyi tana ji.

Ta ɗauki hularta, ta zubo ruwa a kwano, ta zo ta ajiye a gefensa, ta zauna da niyyar karanta abin da ya sauwwaƙa a Alƙur'ani, ta busa a ruwan ta shafa masa. Amma ta ji komai ya ɗauke daga kanta, ta kaɗa ta raya amma ta kasa tuna komai.

Ta janyo wayarta, ta fara laluben folder karatun Alkur'ani, amma wayar ta fara haske tana ɗaukewa tamkar ta ci screen, abin fa ba taɓa yi ba sai yau.

Ta ajiye wayar jikinta yana rawa, ta rasa abin yi, ga shi yana kwance sai tsuma yake yi. Tashi ta yi ta nufi wardrobe, ta buɗe watso kayanta ƙasa. Jakar gurin sarkin baka, ce ta faɗo daga cikin kayan. Nana ta durƙusa ta ɗauka, ta nufi gurin da yake kwance. Ta ɗora masa a ƙirjinsa. Kamar ta ɗora masa wuta, haka ya zabura, ya juya a hankali ya gyara kwanciyar sa, ya daina wannan tsumar ya hau bacci.

Ta saka hannu ta ɗauki jakar, tana ƙare mata kallo. Sam ba ta ga wani abu na musamman a tattare da jakar ba. Ta ajiye ta, ta kwanta a gefe tana jin yadda jikinta yake yi mata ciwo.

Bayan wani ɗan lokaci ya yi juyi a hankali, ya kalli agogon ɗakin, ya kalle ta ya yinƙura ya tashi, ya yi alawala ya yi sallar la'asar. Ya zauna a kan sallayar ya yi shiru, fuskarsa na bayyanar da damuwa.

Nana ta tashi daga gurin da take. Ta ja ta zauna sosai ta gyara zamanta. Ta ce "Sayyid na kasa fahimtar abin da yake faruwa, ban sani ba ko na yi wani abun da na ɓata maka rai ba."

Ya sunkuyar da kai ya yi shiru, na wani ɗan lokaci, ba tare da ta yi tsammani ba ya yi magana.

"Duk na yi ƙoƙarin ɓoye matsanancin farin cikin da na shiga, da na ji za ki haihu. Na kasa ɓoye damuwar da na shiga, da na ji na rasa abin da yake cikinki Ban san dalili ba kawai na ji ina matsanancin son, abin da ban taɓa gani ba, kuma yanzu na rasa shi, ba tare da na yi tsammanin hakan ba".

Jiki a sanyaye Nana ta ce "Sayyid idan kai ka ce haka, ni na ce me?"

Ya ɗan girgiza kai ya ce "Ba za ki gane ba" ya tashi ya naɗa rawaninsa, ya fice daga ɗakin.

Nana duk ta gaji da kwanciyar, ta yinƙura ta fara mayar da kayan wardrobe ɗin da ta watso. Ta ɗaga labulen window, dan iska ta ƙara wadatar ɗakin, kawai ta hango Siyama ta fito, sanye da doguwar riga da ɗan ƙaramin mayafi, ƙonuwar hannunta, ko gama warkewa ba ta yi ba. Sai dai Nana ta ga Sayyid take tunkara.

Ganin tana tunkaro shi, ya sanya ya sunkuyar da kansa, daga kallon gurin da take tahowa. Sai dai tana ƙarasowa inda yake ta tsaya tare da yin murmushi ta ce "Sannu da ƙoƙari" ya jinjina mata kai, ba tare da ya kalli inda take ba.

"Amm dan Allah magana nake son mu yi"

Ya ɗaga kai ya kalle ta cikin mamaki. Ta ɗan sunkuyar da kanta ta yi murmushi, ta ce "Dan Allah a abubuwan da suka ɗan faru, na rashin kyautawa da na yi maka, nake son ka yafe mini na san na yi kuskure, ka yi haƙuri"

Ya ɗaga idanunsa ya kalle ta, ya mayar da kansa ya sunkuyar.

"Ka yi magana mana" ta yi maganar cikin iyayi.

Jinjina kai ya yi, yana ƙara kawar da kansa gefe.

Ta sake cewa "To ai ba zan gane ba, idan ka haƙura, ka yi magana"

"Ya wuce"

Ta saki murmushi ta ce "Na gode sosai" ta juya ta koma cikin gida tana murmushi. Tabbas Buzun nan, irin mutanen da idan ka ɗora kana relationship da su, za a ga ka haye, ya haɗu ta kowane ɓangare. Ta yi maganar a zuciyarta. Nana rasa abin yi ta yi gaba ɗaya, ta ji ƙirjinta tamkar ta haɗiyi kibiya, wani abu ya tsaya a tsakanin maƙogwaronta da ƙirjinta.

Ta zauna ta yi shiru, kawai ta ji sallamar Siyama. Nana ta ɗaga kai ta kalle ta, sai dai ta kasa magana.

Siyama ta zauna a kusa da ita ta ce "Ƙawata kwana biyu ba ki zo ba"

Nana ta kalle ta ta ce "Kina lafiya?"

"Ashe kuma ba ki da lafiya? Ya jikin naki?"

Nana ta kalli Yusra ta ce "Ya aka yi ki ka san ba ni da lafiya? Waye ya gaya miki?"

"Sai an gaya mini, ina ganin komai ai. Ko kin manta gidanmu ne nima? Allah ya baku wani."

Nana ta ce "Ina cikin damuwa, dan Allah kar ki dame ni"

Yusra ta yi murmushi ta ce "Na sani, amma kin san faɗa ya kaure a tsakanin Ƙaisar da dattijo? Kuma duk a kan ki?"

Nana ta ce "Waye dattijo?" Ayshacool "Wanda ya ke kawo muku ziyara, da ke da mijinki, idan ba ki yi wasa ba, abu mara daɗi zai iya faruwa. Kodayake kar na yi shishshigi, gurin shiga hurumin da ba nawa ba. Amma abubuwa na daf da rikicewa. Me ma ya faru kafin ki yi ɓarin cikin jikinki?"

Nana ta ɗan yi shiru tana son ta yi tunani, amma ba ta iya tuna komai ba, tana ɗagowa ta nemi Yusra ta rasa.

Damuwa da rashin sanin abin yi, ga takaicin abin da ta gani ya haɗu ya sanya, ta tashi ta sake watso kayan wardrobe tana gyarawa.

A cikin kayansa, ta ci karo da wata 'yar ƙaramar jakar fata, mai kama da laya, sai dai ta fi laya girma, da ya kan saka a wuyansa wasu lokutan.

Ta yi shiru tana kallon jakar, ta yi ƙoƙarin ta ga ta ina za ta buɗe ta, ta ga mene ne a ciki, amma ta kasa. Ta ajiye ta, ta ci gaba da gyaran kayan, ta sake ɗaga wata riga, sai ga kuɗi turmus a ciki, na Nigeria da na Nijar.

Har ta kai hannu za ta ɗauka, ta waiwaya ta gan shi a tsaye yana kallonta.

Ta kalli kuɗin ta kalle shi.

"Wannan kuɗin fa?"

"Nawa ne?"

Ta kalle shi ta ce "A ina ka samu?"

Wani irin kallo ya yi mata, jin tambayar da ta yi masa.

"Me ki ka ce?"

Ba ta ji ko ɗar ba, ta sake maimaitawa.

"A ina ka samu?

"A ina ma samu? A gurin Habu. Ai ya gaya miki sana'ar da yake yi ko?"

"Dama shi ya gaya maka, na je gidan kenan?"

Ya girgiza kai yana mayar da kayansa ya ce "A'a"

Da ta tuno yadda ta ga ya kalli Siyama, wani narkakken baƙin ciki yake tokare mata zuciya, kamar ta kwaɗe shi ko ta samu ta huce.

*

Alhaji Zailani ne, tare da Alhaji Fatuhu, zaune a kan fararen kujeru a wata farfajiya.

Fuskar Alhaji Fatuhu, cike da ƙwarin gwiwa yake duban Alhaji Zailani ya ce "Zailani, babu komai dan Allah ka karɓi shugabancin nan, na san za ka iya. Da a bawa wani da ba a san yanayin amanarsa ba, ba gara a baka ba?"

Fuskarsa ɗauke da damuwa ya ce "Haba Alhaji Fatuhu, yaya za a yi kana abokina, aminina a yi maka wannan cin kashin, kuma ka ce na karbi shugabancin nan na yi yaya da shi?"

"Wallahi za ka iya. Na fi jin tausayin ƙanan 'yan kasuwa, idan aka bawa wanda bai dace ba shugabanci, za a karya masu ƙaramin jari"

"Ƙananan 'yan kasuwar, da su suka yi wannan bita da ƙullin, da rubuta takardar lallai a sauke ka daga kan shugabancin nan, su ka ke tausayawa?"

Alhaji Fatuhu ya yi murmushi ya ce "Nima da ƙaramin ɗan kasuwa ne, kafin Allah ya kai ni matsayin da nake a yanzu. Kuma na san ba dukkannin su ne, su ka yi mini haka ba. Ni dai fatana dan Allah ka karɓi tayin riƙon ƙwaryar shugabancin nan da aka yi maka" Alhaji Fatuhu ya ɓata lokaci sosai da sosai, kafin ya shawo kan Alhaji Zailani ya amince zai karɓa.

*

Readers Also Read