Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 30
Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 30: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 30. Kuka take yi iya ƙarfinta, tana sheshsheƙa, ya rungume ta gam a jikinsa,…
3,373 words
Kuka take yi iya ƙarfinta, tana sheshsheƙa, ya rungume ta gam a jikinsa, shi kansa ya ji zafi da raɗaɗin satar da aka yi musu. Ba iya kuɗi ba, har da wasu daga kayan amfaninsu na ɗakin an ɗauka, ya san kuma hakan sabon ƙalubale ne, saboda ba su da wata hanyar samun kuɗi a yanzu. Ji ya yi jikin Nana ya saki, kuma jikin yana ɗaukar sanyi. Karkarwa ta fara yi, tamkar ana jona mata shocking. Cikin matsananciyar damuwa, ya zauna da ita a jikinsa, ya ɗauki wayarta da ta saki a gurin, yana haska fuskarta. Ya ga hawaye na fita ta gefen idonta. Hannayenta da ƙafafuwanta su na lanƙwashewa, goshinta kuma yana tsatstsafo da gumi. Jin ta ta yi, jingine da wani abu da ba ta san ko mene ne ba. Ta shafa abin ta ji ƙurzunu-ƙuruzunu, tamkar dutse. Gurin baƙi ƙirin duhu ya gauraye gurin, ko tafin hannunta ba ta iya gani. A hankali haske ya fara shigowa gurin, har gurin ya yi haske ba ki ɗaya. Ta ɗaga kanta ta ga ba ta iya gano ƙarshen ɗakin. Jin tari ta yi a bayan ta, ta waiwaya da sauri, ta ga Ƙaisar a zaune lulluɓe da wani abu mai haske sosai.
"Ƙaisar. Ba ka da lafiya?" Ta yi maganar tana nufar inda yake.
Ya yi shiru bai yi magana ba. Ta sake cewa "Dama kuma ku na rashin lafiya, kamar ka canza gaba ɗaya" ya yi murmushi ya ce "Mu na rashin lafiya mana, guba na ci" Ta waro ido ta ce "Guba kuma? Me yasa?"
"Tsohon nan na jikin mijinki, ya bani."
"Kuma ka sha? Wai meye alaƙar ka da shi? Kuma dan Allah me yasa yake bibiyar mijina?"
"Ba wannan ba, me yasa ki ka kira ni?" Cikin mamaki ta kalle shi ta ce "Kamar yaya? Ni ban kira ka ba ai"
"Fushi da ɓacin rai, duk wanda ki ka yi tamkar kin kira ni ne. Kuma ni yanzu ba ni da wani tasiri sosai, saboda jinya nake yi. Babu wanda ya san ina nan. Giyaz ya saka ni a gaba, ya mamaye Library ɗi na, yanzu rashin ganina zai sanya ya ci gaba da cutar da ku. Ba zan iya wani abu ba sosai yanzu, sai dai zan iya tasiri a kan bil'adama. Duk ba wannan ba, duba can." Ta ɗaga kai ta kalli inda ya nuna mata, Library ɗin Ƙaisar ta gani. Ta ga gangar jikin Sayyid a kwance. Tsohon nan ya ɗaɗɗaure shi da wata irin igiyar ƙarfe. Ƙasan gadon da yake kai kuma, wata irin wuta ce take ci a ƙasa. Nana ta zabura a rikice, ta ce "Wannan ai Sayyid ne" "Ƙwarai shi ne, ba wani ba. Kuma Giyaz shi ya sanya masa matsalar da ku ke ciki na auratayya. Sai dai abu ɗaya zan iya gaya miki. Matsalar zuciya da hawan jini da yake fama, wannan ciwo ne yake damun sa. Amma Giyaz na assasa wani abin. Kuma... Amma dai shikenan"
Nana ta buɗe baki za ta yi magana, ya ce "Kar ki tambaye ni komai, kin san sharaɗin. Kalli" ya yi maganar yana sake nuna mata gurin.
Alhaji Fatuhu ta gani, ta yi ƙuri da ido ta ce "Kamar na san wannan"
"Ba kama ba ce ba kin san shi, ciwo ne da zafin sihirin da aka yi masa ya mayar da shi haka. Sai kuma albishir da nake yi miki, da ƙanwar ki ta zama cikakkiyar 'yar ƙungiyar asiri. Ɗayar kuma wannan bararojin da ta taɓa baki magani, ta aura mata ɗanta, wanda yake baƙin aljani ne. Kuma ta tarkato kan iyalanta duk su na jikinta. Kuma kowanne akwai abin da yake mora a jikinta. Ke in taƙaice miki ma, a kowane lokaci za ta iya rasa hankalinta ko ma rayuwarta gaba ɗaya. Ayshacool Shikenan bissalam"
"Ƙaisar" sai kuma ta yi ido huɗu da Sayyid.
"Kin tashi?" Ta yinƙura ta tashi zaune, tana kallon ɗakin.
Sayyid ya ce "Ƙaisar ɗin ba shi da lafiya ne?" Ya yi maganar yana tsare ta ido.
"Wane Ƙaisar ɗin?"
"Tambayata ki ke yi?" Shiru ta yi, ita ba ta iya tuna koma ma a cikin abin da ya faru ba. Idonta ne ya sauka a kan kayan da suke gaban wardrobe a ƙasa, sai kuma abin da ya faru ya faɗo mata. Afujajan ta tashi ta sake nufar wardrobe ɗin, tana zazzage kayan tana kuka.
"Kuɗin nan fa babu su, an kwashe ki daina wannan dube-duben" ya zauna ta yi shiru ta sanya kayan a gaba tana kallo.
Ya yi mata shiru ya ƙi kula ta, ya kwanta a kan katifa, yadda take a hasalen nan, idan ya matsa faɗa za su yi. Cikin ƙanƙanin lokaci nannauyan bacci ya yi awon gaba da shi.
Barira na kwance a ɗakinta, ta yi ɗaiɗai tana bacci, ta ji kamar ana karta mata farce a ƙafafuwanta. Har ta maze ta ci gaba da bacci, amma ta ji an cigaba. A fusace ta ce "Gali meye haka, za ka din ga karta mini faratanka, ina cikin bacci ne?" Shiru bai amsa ba. Ta laluba ta ji yo ƙeyarsa a can ƙarshen gado, yana bacci. Ta koma ta kwanta, amma ta ji an cigaba, ta tashi zaune tana zabga ashariya. Ta kunna fitila, ta ga babu kowa. Ta yi tsaki ta sauka daga kan gadon, ta fito tsakar gida domin ta yi fitsari. Bayan ta fito daga banɗakin, kanta ko ɗan kwali babu, kawai ta yi karo da Nana a tsakiyar tsakar gidan tana yi mata wani irin mugun kallo.
Ta haska Nana ta ce "Nana lafiya kuwa?"
Sai dai Nana ba ta yi magana ba, ta sake haska ta, za ta yi magana. Ta ga ta rikiɗe ta zama wata irin ƙatuwar mage, baƙa ƙirin, girman ta ya yi na tunkiya ƙosashiya da ita, ta yo kanta tana buɗe haƙora. Da gudu Barira ta shiga ɗakinta, tana ihu tana kiran sunan Gali.
"Ke mahaukaciya, mene ne haka za ki din ga ihu kina kiran sunana a tsohon daren nan?"
Ba ta ce masa uffan ba, ta duƙunƙune, tana mayar da numfashi. Ta tsorata sosai da sosai, da ƙyar ta samu ta yi bacci. Sai dai a cikin baccin ma, mafarkin magen nan kawai ta din ga yi tana bin ta, tana karta mata farata tana cizon ta.
Sayyid kuwa yana jiyo kururuwar Barira, hakan bai dame shi ba, sai ganin Nana da ya yi a zaune, ta haɗa kai da gwiwa. Ya yinƙura ya tashi zaune, bai ce mata komai ba, ya kwantar da ita a kan katifar, ya rufe su da bargo ya rungume ta yana shafa bayanta. Yana jin ta tana kuka, har ta yi ta gaji bacci ya ɗauke ta. Dauriya kawai yake yi, amma ji yake tamkar ya taya ta kukan.
Washegari, Barira ta tashi da matsanancin zazzaɓi da ciwon kai, ta din ga yi wa mijin kuka, tana cewa ya mayar da ita gidansu, mayu sun kama ta a nan gidan, ba za ta yadda a kashe ta a banza ba. Babu yadda ya iya ya tattara ta ya kai ta gidansu.
Kwanki biyu da sace kuɗin nan, Nana ta rasa abin da yake yi mata daɗi. Dubu talatin ce ta ragu a hannunta, shi ma cikin irin kuɗin da ta zuba a jakarta ne suka fita da su. Kuɗin Nijar ɗin kuma ba ta san ma ina za ta a canza su ba. Bayan haka tayi tunanin idan Habu ya dawo fa, me za ta ce masa? Ta din ga tunanin yadda za ta yi da dubu talatin ɗin nan, ba tare da ta rushe gaba ɗaya ba. Ga shi magungunan da yake sha kawai, na wata ɗaya dubu goma sha biyu take sayen su. Sai dai kamar yadda yake nanata mata, ta yi haƙuri, ya sanya ta fauwwala wa Allah lamarin.
Kwana biyar da kwashe kuɗin nan, Sayyid ya hana Nana gaya wa kowa. Sai dai cikin dare ba ta iya bacci, saboda lissafi da tunani. Ta kira Ummi ta tambaye ta batun barkono, ta ce ana ta saya, ta sayar da ya kai rabin buhun. Kayan Abinci da Mama ta haɗo mata da su, take ta cancana musu. Da daddare ba ta iya bacci, saboda damuwa da tunani, sai dai abin yana damun sa fiye da yadda yake damun ta. Su ka wayi gari, ya tashi jikinsa babu daɗi, yana ta numfarfashi.
Abin Duniya ya ƙara damunta, ya kuma ƙi cin komai. Muryar Barira ta jiyo a tsakar gida, da ta dawo, tana maganganu tana ba wa su Sajida labari.
"Mayu sun kama ni a gidan nan, kuma da ƙarfina na dawo, wallahi sai sun ci uban su, kurwata ta fi ƙarfin mutum".
Sajida ta ce "Ban gane mayu ba, suwaye mayun kuma?"
Barira ta ce "Oho, ki zuba ido ki gani, Allah zai tona musu asiri" Ayshacool Ya gama ci, ta dafa ruwa ta kama hannunsa zuwa banɗaki, tamkar jaririn goye ta yi masa wanka. Shi kansa a lokacin ya din ga jin wata lafiyayyiyar iska na shigar sa. Ta saka ya yi alwala, ya fito ya zauna ya fara jero sallolin da ake bin sa. Ta ce "Sayyid kar ka ce sai yi a yanzu duka, sallolin da yawa.ka bari ka din ga ramawa a hankali. Ya jinjina mata kawai kawai, tun yana yi a tsaye ya kasa tsaiwar ya koma yi a zaune. Ta yi shiru tana kallonsa, ta wasu guraren suna da kamanceceniyar halayya ita da shi. Duk yanayin da yake ciki, muddin ba hankalinsa ne ya gushe gaba ɗaya ba, ba ya wasa da salla ko kaɗan. Hakan ya sanya take jin ko a ainihin rayuwarsa haka ya siffantu da kiyaye salla a kan lokaci. Har ƙarfe uku da rabi, dan kansa ya ce "Ba zan iya ƙarasawa ba, numfashina"
Ta ce "To ko za ka yi a kwance?"
Ya girgiza kai ya ce "Na fi so na yi a zaune, ko a tsaye"
Ta ɗage masa labule, ganin yadda yake ta gumi. Ta shimfiɗa masa sallaya a bakin ƙofa, ta jera masa fululluka, ya kwanta.ta zauna a gefen sa tana yi masa fifita. Ta ɗora hannunta a goshinsa tana karanta masa abin da Allah ya sa ta tuna a zuciyarta.
Hannunsa ta ji yana saka wa a rigar ta, duk da idonsa a lumshe yake. Murmushi ta yi ta ci gaba da abin da take yi. Jin yana yi mata cakulkuli, ya sanya ta kwanta a jikinsa tana dariya. Shi ma dariyar ya yi. Ya ce "Ki kwanta a kusa da ni" ya yi maganar yana nuna mata kusa da shi. Kafin ta yi magana ta ga an dalle su da fitila. Cikin hanzari ya juya kansa, ya ɓoye fuskarsa a cinyar Nana, gashin sa ya kwanta a kan filon. Nana ta saka hannu ta kare fuskarta. Muryar Barira ta ji ta ce "Yi haƙuri dan Allah, jin motsi ya yi wa na fara jin tsoro, shi ne na fito na duba, ku yi haƙuri. Ta kashe fitilar ta koma ɗaki. "Sayyid ka yi haƙuri, na san ba ka ji daɗi ba, ka yi haƙuri"
Ya yi mata shiru, kuma bai ɗago daga kan cinyarta ba. Ta shafa gashin ta ce "Shugabana, ka yi magana mana, ko na ji daɗi, kwana huɗu ka na bacci, ba ka yi mini magana dan Allah kar laifin wani ya shafe ni" Sai kuma ya juyo a hankali, ta ce "Yauwwa Rayuwata"
"Kin daina aman?" Ta ji ya tambaye ta babu tsammani.
"Eh na daina"
"Allah ya sa ki haihu wannan karon "
"Amin, kuma Allah ya baka lafiya na haɗa jariraina biyu, babba da ƙarami"
Ya yi murmushi ya ce "In sha Allah, kafin ki haihu, idan na ji sauƙi zan nemi aiki, na kula da ku da kaina"
"To Allah ya amince. Amma Sayyid ina kuɗin nan da na gani rannan, a cikin wardrobe ɗin ka? Da na haɗa mana kaya ban gan su ba. Da sai mu ɗauka a yi maka magani, kuma mu canza gida"
"Ai Habu ya karɓa, ranar da ya zo na ƙarshe, ya karɓi kuɗin Nigeria da yawa, ya bar mini wasu, ya ce na Nijar ne. Kuma da kin duba kayan nawa sosai, su na ciki"
"A'a ni ba na caje maka kaya, idan Allah ya kaimu gobe, sai a lissafa mu gani idan za su isa."
Ya ce "To. Kwanta ki yi bacci" ya yi maganar ya ƙara matsa mata. Ta kwanta tana murmushi.
"Sayyid, idan har ba a ga su Habu ba, ina ga da ni da kai zamu je Nijar, mu nemi danginka da kanmu"
Ya yi shiru bai yi magana ba, ta ɗan taɓa shi ta ji har ya yi bacci.
* Jamila a dole ta saki ranta, jikinta ta ɗan samu ƙwari, ya daina yi mata wannan mugun ciwon da yake yi mata. Raɗaɗin ma duk babu. Sai dai tana jin ƙasan zuciyarta kamar za ta yi bindiga, saboda damuwa da tashin hankali. Sosai abin da ya faru ya tsaye mata, ta shiga banɗaki ta sha kuka. Wai ita Aljani ya kwanta da ita, ta gaba da baya aka ci zarafin ta ta wannan mummunar hanyar.
Tana kwance a cikin bargo, Hajiya Sa'a ta fita shashashancinta. Wayarta ta fara ringing. Ta janyo ta ɗaga. Muryar Abba ta ji ya ce "Ƙanwata, wunin yau ban jiki ba, lafiya kuwa?" Wani irin abu mai zafi ya taso mata, ya haddasa mata karaya. Muryarta na rawa ta ce "Yaya Abba ba ni da lafiya"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Me ya same ki?"
Rasa abin da za ta ce masa ta yi, kawai ta saka kuka. Aikuwa ya rikice ya din ga rarrashin ta.
Da ƙyar ya lallaɓa ta ta ce masa cikinta ne yake ciwo.
"To ina Mummyn take? Ba ta kai ki Asibiti ba?" Ayshacool "Ta kai ni, an ba ni magunguna ma, dan Allah kar ka yi mata zancen, ta yi mini iya ƙoƙarin ta,kar ka yi mata zancen dan Allah"
"No ai ba zan yi mata ba, ba ta san ma ina da lambar ki, mu na magana ba. Ki kwanta ki samu hutu kin ji Ƙanwatax
"To shikenan na gode sosai" suka yi sallama ta ajiye wayar, ta kwanta hawaye na ci gaba da bin idanunta.
*
Yana zaune a cikin mota, yana ƙoƙarin kunnawa, wayarsa ta fara vibrating. Ya kalli screen ɗin wayar, ya ga baƙuwar lamba. Ya ɗauki wayar ya ɗaga ya saka a kunnensa. "Hello" muryarta ta doki dodon kunnensa. Ɗan waro ido ya yi, ya gyara zaman sa ya ce "Wa ke magana?"
A raunane ta ce "Beb abin har ya kai ka manta muryata ma? Shikenan na gode" ta kashe wayar.
Da sauri ya bi kiran wayar, amma ta ƙi shiga, ya yi ya yi, amma ta ƙi shiga, sai haƙura ya yi ya ja motar.
Shukura mamakin abin da ya zaunar da shi a cikin mota take yi, bai tafi ba har yanzu, sai dai tana ɗaga labule, ta hango ya ja motar ya tafi.
Video call ɗin Hajiya Amina, Shukura ta gani, ta ɗaga cikin fara'a tana faɗin "Hajiya Mummy, ya ibada?"
"Ibada Alhamdillah, Shukura dan Allah me yasa ba kya ji ne? Ina zaman zamana, ina ibada kin jawo mini ɓacin rai da damuwa"
Cikin rashin fahimta, ta ce "Ni ɗin kuma? Me na yi?"
"Baban ki ya kira ni, bai taho ba tukuna yana Abuja. Yana yi mini faɗan wai ke ba ki san ƙaddara ba ne? Doctor Sharif ya kira shi cikin damuwa, yana gaya masa a gaban mutane ki na cewa yana kashe mutane, haka ake yi a kan ki a ka fara rasa ɗa? Me yasa ba za ki girma ba ne Shukura"
"Mummy ki na ji na, network ɗin ki mai ƙarfi ne ko?"
Ta ce "Eh, ina jin ki, kuma ina kallon ki"
"Ina son idan kin je gaban ka'aba, ki yi mini addu'a, muddin a kan gaskiya ta nake, Ubangiji Allah ya shiga lamarina ya ƙarfafa mini gwiwa. Idan kuma ba a kan daidai nake ba, Ubangiji Allah ya kawar da kaina daga kai. Ya bani juriya da dangana na daina jin abin da nake ji a zuciyata. Sai dai kin dawo amma akwai matsala ne fa."
"Shukura matsala wace iri ce, za ta sanya musulmi kasa yin tawakkalli?"
"Ki bari dai ki dawo ɗin"
"To shikenan, amma gaskiya mahaifinki ya yi fushi bai ji daɗin abin da ki ka yi ba sam"
Shukura ta lallaɓa ta, ta ajiye wayar.
*
Nana tana jan ruwa a rijiya, tana zubawa a cikin bokitanta, za ta kai banɗaki. Barira ta ce "Nana ki yi haƙuri dan Allah, jiya na haska ku, ba a son raina ba ne, kuskure ne" Nana ta ce "Babu komai"
Sajida ta ce "Uban me ki ka haska ki ka gani?"
Barira ta kwashe da dariya ta ce "Ni babu abin da na gani, duk da bai kyautu ba abin da na gani ɗin. Amma Nana mijinki balarabe ne ko bature?" Nana ta ɗaga ta kalle ta. "Tun da ku ka zo dama bamu taɓa ganinsa ba, gashi na gani kamar na mace dogo sosai"
Nana ta maze ba ta kula ta ba, ta kwashi kayan ruwanta, ta nufi ɗakin su.
Sajida ta tuntsure da dariya ta ce "Maganinki da shegen shishshigi, ga shi ta gwale ki"
"Shegiya ba, ta fiye jin kan ta,kamar 'yar uban wani, kuma da 'yar uban wanin ce, da ba su kama hayar ɗaki ɗaya ba" Duk abin da suke faɗa a kunnen Nana, amma ta yi kamar ba ta ji ba.
Bayan ta gama wanke banɗaki ta fito, ta zo gabansa ta zauna. Ya ɗaukko sauran kuɗin nan, ya ajiye a gaban ta.
Ta kalle shi ta ce "A ina ka ɓoye ne, ban gan su ba?"
Ya yi murmushi ya ce "Su na cikin kayana fa, ba ki duba bane ba. A cikin leda suke. Kuma da sun fi haka yawa, Habu ne ya karɓa".
Nana ta duba kuɗin, sai tarin kuɗin nijar, na Nigeria ba su dubu ɗari da goma ba.
Ta ce "Sayyid, idan ka ɗan ƙara hutawa, ko zuwa gobe in Allah ya kaimu ne, za mu koma Asibiti a sake duba ka. Da za su kai da na haɗa da sauran na guri na, a fara yi maka allurar nan ko guda ɗaya ce"
"A'a, kin manta yanzu mu zamu din ga sayen Abinci. Idan su ka ƙare ba mu da hanyar samun kuɗi. Kuma da akwai isassun kuɗi, gara mu bar gidan nan, da a yi mini magani"
"Ni kaina Sayyid ba na son gidan nan. Mama za ta aiko mini buhun barkono, idan aka kawo, na ga ana ciniki, sai mu ci gaba da sayarwa".
Ya jinjina kai ya ce "To, in anjima ki raka ni masallaci" Ta kalle shi ta ce "Da gaske masallaci za ka je?" Ayshacool "Eh, ina son zuwa masallaci. Idan ki ka raka ni, sai ki dawo"
Ta yi murmushi ta ce "To shikenan, Alhamdillah sauƙi yana samuwa. In sha Allah zan kai ka. Bari na ajiye kuɗin nan, idan na raka ka ma, dan Allah zan je gidan Ummi" ya jinjina kai. Har za ta tashi ya riƙo ta, ya cire hijjabin da yake jikinta.
Ƙonuwar da take wuyanta ya gani, ya ƙura wa gurin ido sosai sannna ya ce "Mene ne wannan?"
Ta ɗan basar ta ce "Ba komai fa, ɗan ƙonewa ne kawai na yi"
"Ba ɗa ba ne ba, me ya kai ruwan zafi wuyan ki? Waye ya zuba miki?"
"Ba wanda ya zuba mini, sha nake yi ya zube" kawai ya rabu da ita, ba dan ya gamsu da amsar da ta ba shi ba.
Ta tattare kuɗin nan, na Nijar ta zuba su a cikin jakar gidan Sarkin Baka. Na Nigeria kuma ta haɗe su, ta saka a cikin kayan ta. Ana kiran salla, ya yi alwala, Nana ta ba shi mayafin rawaninsa, ya yafa a kan sa. Nana ce ta fito tsakar gida. Barira ta gani, tana girki sanye da wata 'yar riga, milik ce amma ta yi baƙi saboda dauɗa, ko brezia babu a jikinta. Ga gashin hammata ya fito zaro-zaro idan ta ɗaga hannunta. Zanin jikinta ma baƙi ƙirin, tamkar an yi matsar man ƙuli da shi, sai annakiya take yi.
Nana ta ce "Barira, dan Allah ko za ki gyara, zamu wuce"
Barira ta ce "Bismillah ki wuce mana"