Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 31
Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 31: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 31. "A'a ai ni da mijina ne"
3,310 words
"A'a ai ni da mijina ne"
"Ku wuce ba wani abu ai" Nana ta yi shiru tana jinjina tumasanci da rashin sanin ciwon kai, na mutanen gidan. Babu yadda ta iya, haka ta kammo hannun Sayyid, ya fito ta rufe ɗakin. Ya ja mayafin ya rufe fuskarsa da rawanin, saboda yanzu ba ya iya naɗa shi, saboda numfashinsa. Tun da ya fito Barira take kallon sa, ta na son ganin ainihin fuskarsa, amma ya sunkuyar da kai, kuma ya rufe fuskar sa suka fice.
Su na tafe Yana hutawa, saboda haki, a hankali har suka isa masallacin. Ta ce "Za ka jira ni na je gidan Ummin na dawo?"
"Zan koma gida da kaina"
"Har ka gane hanya?"
Ya ce "Eh ki gaishe ta"
Nana ta ce "Ai ba daɗewa zan yi ba ma"
Ya shiga Masallaci Nana kuma ta tafi gidan Ummi.
Su Nana na fita, Barira ta buga banɗakin tsakar gida ta ce "Ke Sajida kashin danƙo ki ke yi ne? Ki na manne a banɗaki yau mijin 'yar rainin hankalin nan dai ya fito. Ashe dole ta ɓoye shi, fari ne tas wannan gashin da na gani, da gaske nasa ne."
Sajida ta fito da buta a hannunta ta ce "Kai haba, ban gama ba ne shi yasa ban fito ba, zogala na ci da ƙuli ya ruɗa mini ciki"
"Aikuwa kin rasa, ba ki gan shi ba. Sai na ga kamar mata na rako, da na tuna Gali, ga baƙi ga ƙeya"
Sajida ta ce "Ba gara Gali ba da nawa mijin? Ke Gali na da tsawo, ni nawa ga gajarta ga muni"
"Gaskiya Sajida mijinki akwai muni kam, dogon baki kamar dangin burrai"
Sajida ta tsuke fuska ta ce "Ba na son iskanci kuma. Gara shi dai a kan Galin, da ki ka ce ba ya iya tsinana miki komai a shimfiɗa. Kalarsa kalar... Kafin ta ƙarasa Barira ta ƙunduma mata Ashariya, take faɗa ya kaure, suka ci wa junan su mutunci tsaf, suka tona wa kan su Asiri. Suka gaji dan kan su, suka haƙura.
**** Nana ta bawa Ummi labarin barkono da za a kawo mata. Ta ce "Amma Ummi sai dai a kawo miki nan, can ɗakinmu babu gurin da zan ajiye a can"
"Bakomai a kawo, kuma nan da nan za ki ga an saye shi ba, ai unguwar nan fuskar jama'a ce, idan ka kasa kaya za ka samu alkhairi"
Su na tsaka da hira, babu zato babu tsammani sai ga Saleh ya afko cikin gidan. Wata irin mummunar faɗuwar gaba ta ziyarci Nana, bayan da ta gan shi babu tsammani. Duk ya ƙara lalacewa.
Turus ya yi yana kallon Nana, cikin mamaki ya ce "Nana, dama kina nan?"
"Eh" ta amsa a taƙaice.
"Nana da yanzu nine mijinki, amma ki ka guje ni"
Ummi ta haɗe rai ta ce "Saleh Nana fa matar aure ce, dan haka babu ruwan ka da ita dan Allah"
Saleh ya ce "Dan matar aure ce, kuma shikenan ba za mu yi zumunci ba? Nana kina lafiya? Na ji an ce wani baroroji aka aura miki ko?"
Nana ta haɗe rai ta tashi ta ce "Ummi zan tafi, zuba mini Abincin idan kin gama"
Ummi ta ce "Bari na wanke babban flask, kuma idan Islam ta zo ki ba ta kwano na, dan ba zan bar miki ba" Ayshacool Nana ta ce "Gaskiya sai kin bar mini, ki zo ɗakina, ki ɗauki duk abin da ya yi miki. Kuma a ƙaramin kwano za ki zuba mini. Sayyid na yi masa girki, ni zan ci wannan"
Ummi ta ce "Hajiya Nana, an sake haɗiyar wake kenan, to Allah ya inganta"
"Dawa na haɗiya ba wake ba"
Tsulum Saleh ya sake cewa "A nan unguwar gidanki yake kenan? Na ji Ummi ta ce Islam na zuwa gidan naki. Da aka ce mijin naki gadi yake yi"
A ƙufule Ummi ta ce "Dan zatin Allah Saleh ka fita, ba da kai muke magana ba, babu ruwan ka da mu. Wai har ka manta har ubanmu ka saka a rufe saboda kuɗinka, dan rashin kunya kuma, ka zo zaka addabe mu?"
Sum-sum Saleh ya fice daga gidan. Ummi ta zubawa Nana tuwon shinkafa da miyar yauƙi, har da man shanu, Nana sai haɗiye yawu take yi cikin farin ciki, kamar ta durƙusa ta ci a gurin. Ummi ta shiga ɗaki, ta ɗaukko wa Nana dambun kifi ta ce "Ungo, jiya na yi shi aka kai mini shago, na ɗebar miki"
Nana ta karɓa tana murmushi ganin sa fal a roba, ta ce "Allah ya yi miki abin da ki ke yi mini na alkhairi na gode sosai" suka yi sallama Nana ta fita.
Tana cikin bin wani lungu, ta ji Muryar Saleh na kiran ta. Ta ƙara saurin da take yi, amma ya cimma ta. "Nana dan Allah ki saurare ni".
Rikicewa ta yi, gani take a kowane lokaci za ta iya ganin Sayyid, ba ta san da wani yaren za ta yi masa bayani ba ya fahimta.
"Nana ki tsaya ki ji mana"
"Wallahi zan yi maka ihun kwarto, wace irin jaraba ce wannan ina ruwan ka da ni ne?" Ganin tana ɗaga murya, kuma Akuyarsa ta yi kuka a unguwar, ya sanya sum-sum ya koma da baya.
Tana zumbuɗa sauri, ta je gida, ta san yana can yana jiran ta. Kawai ta ci karo da shi a wani lungu, yana zaune a kan wata sokawe, ya jingina da jikin bango, shikaɗai ƙwal a layin. Sai da ta razana, ta waiwaya bayan ta, cike da tsoron ko Saleh ya biyo ta.
"Sayyid me ka ke yi a nan kuma, ba ka shiga shiga gida ba?"
"Ba zan iya shiga nikaɗai ba" Ta miƙa masa hannu ta ce "Taso mu tafi" ya miƙa mata hannunsa. Sai dai tun da ya saka hannunsa a nata, sai da ya kalli fuskar ta.
Da suka je gidan, danƙam da mata, ana ta hayaniya. Ya rufe fuskarsa Nana ta yi sallama. Gaba ɗaya suka yi tsit, suka zubo wa su Nana ido, musamman ganin hannunta riƙe da na Sayyid.
Kawai ta ja hannunsa, suka nufi ɗakin su.
"Nana kun dawo" Sajida ta yi maganar, tana kokowa da zaninta tana fitowa daga ɗakinta, saboda kar su wuce ba ta gan su ba.
"Eh sannun ku" daga haka ya tura ƙofar ya fara shigewa. Suna shiga ɗakin matan suka saka shewa, ɗaya ta ce "In dai Namiji ne, yarinya za ta gama wannan iyayin ne"
Nana su na shiga ɗaki Sayyid ya tsare ta da ido ya ce "Nana ba ki da gaskiya"
Gabanta ya faɗi cikin tsoro ta ce "Me na yi?"
"Gumi ki ke yi a iya goshin ki, da karan hancin ki. Kuma tafin hannunki ya ya sanyi, zuciyar ki na bugawa da ƙarfi kuma da sauri. Kin yi wani abu da ki ke ɓoye mini ko?" Haɗe rai ta yi ta fara ƙoƙarin ƙwace hannunta daga nasa.
Sai kuma ya sassauta muryarsa ya ce "Ki daina fushi, ba zan iya barin, duk wani abu na ƙi ya tunkaro rayuwata da ke ba, ki daina fushi"
"To sai ka din ga zargina da rashin gaskiya" ta faɗa a hasale.
Ya girgiza kai ya ce "Ba zargin ki nake yi ba. Na tabattar da wani abu ya faru ne, da ba za ki so na sani ba, idan na sani zamu samu saɓani. Kin manta mu ba kamar sauran mutane ba ne. Kuma ina iya jin abin da yake ranki, kin manta ne?" Ya yi maganar yana murmushi da shafo fuskarta. Dole ta saki murmushi.
Nana dai ta din ga yi wa Allah godiya, da ba ganta da Saleh ba.
Nana tana yi wa Allah godiya, ganin yadda jikinsa ya yi kyau. Duk da yana haki bai daina ba, amma yanzu yana cin abinci. Sayyid na matuƙar son zuwa masallaci salla, amma dole yake haƙura. Saboda da gayya matan gidan suke wata shigar, duk da ba tsayawa kallon su yake yi ba. Ga shi ba ya son kallo, amma yana fitowa sai su yi shiru su zura masa ido. Ita kanta Nana lamarin gidan ya ishe ta, ba ta ƙaunar zaman gidan nan ko kaɗan. Maman Nana ta aiko mata da barkonon nan, har da awon kayan Abinci, tamkar ta san a halin da take ciki. Ummi da kanta, ta je ta ɗauki barkonon, domin kuwa Nana daina zuwa gidan Ummi ta gaba ɗaya saboda Saleh. Ayshacool Abu kamar wasa har zuwa wannan lokacin, Sayyid ya kasa gane kansa, abin ya fara damunsa sosai da sosai. Ga shi ya kasa cewa Nana komai a kan hakan. Ita ma kuma ba ta ce masa ba, sabgoginta kawai take yi.
Tun Yamma Nana, ke ƙoƙarin shirya duk abin da za su buƙata, saboda washegari za su tafi Asibiti, kuma sammako take so su yi, saboda su ga likita da wuri. Sai dai duk dauriya kawai take yi, wani irin zazzafan zazzaɓi ne a jikinta, ta kasa cin abinci. Babu abin da take son ci, sama ds kazar da Habu ya kawo farkon auren su. Ga shi ba ta son yin duk wani abu da zai ɗaga wa Sayyid Hankali. Ta fuskanci ko saɓani suka samu, ƙaramar magana sai ta sanya ya fara haki, ya fara nema ya faɗi. Tana ƙofar ɗakinta, tana soya miya, su Barira su na hira, tana yi wa wata maƙwabciyar su kitso. Suke zancen wata mata a bayan layin, wai sai mijinta ya neme ta ya rasa, sai a yi kwanaki ba a ganta ba, sai bayan wani lokaci a tsinto ta a wani gurin, ko a ganta a ɗaki. Barira ta kada baki ta ce "Amma ta mayar da mijin nan tasono, ƙarya take yi gantalinta kawai take tafiya. Meye matan auren ba sa yi yanzu?"
Sajida ta ce "A'a Barira, ki daina cewa ƙarya ne"
"Ke wallahi, ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba, a gidan uban wa Aljani zai ɗauke mutum ya kai shi wani gurin? Ke ni fa da ake cewa ana ganin aljanu, ko su tsorata mutum ban taɓa yadda ba, iskanci ne kawai da ƙaryar banza ce, ba wani aljan duk 'yan iska ne kawai.
Nana ta ji wani abu mai zafi ya soki zuciyarta, duk da ba da ita suke ba, kawai ta ƙura wa Barira ido, ko ƙiftawa ba ta yi. Tun Barira ba ta ankara ba, har ta lura, take ta ji tamkar an kwarara mata ruwan sanyi a jikinta, sai kuma ta ɗan tsorata ta ce "Nana lafiya kuwa?"
Ayshercool 08081012143 Ayshacool Tun da Jamila ta koma gida, jikinta a sanyaye yake, gani take yi, duk wanda ya ganta ya san abin da ya faru da ita. Mama kuwa baki ya ƙi rufuwa, saboda Jamila ta zo da abin Duniya. Kuma kamar yadda ta gaya mata, sarin kaya ta raka Hajiya, babu wani bincike ta yarda da hakan ta amince.
Ta zo ba ta iya bacci sam, da ta kwanta bacc6, sai ta ga tamkar za ta buɗe ido, ta sake ganinta, a wannan gurin da suka je da Hajiya Sa'a.
"Jamila" Suwaiba ta kira sunanta, ta waiwaya ta kalle ta. "Wai ya na ga ki na abu kamar mara gaskiya ne?"
Gaban Jamila ya faɗi ta ce "Me na yi na rashin gaskiyar, me ki ka gani?"
"To ai gani na yi kin kasa sukuni, ki na ta wani mutsu-mutsu gaki nan dai"
"Dan Allah Suwaiba ki ji da abin da yake damun ki, ni babu abin da ya same ni, lafiya ƙalau nake "
Suwaiba ta ce "To ai shikenan"
****
Nana duk sammakon da suka yi, su ne na goma sha ɗaya, a gurin ganin likita.
Wajen sha ɗaya na safe aka zo kan su, Nana suka shiga, sai dai wannan karon wani likitan daban suka samu. Suka gaisa Nana ta yi wa likitan bayanin komai. Tare da ba shi takardun gwaje-gwajen da aka yi masa, da kuma katin da aka rubuta masa magunguna.
Ya karɓa ya duba a tsanake, ya duba Bp ɗin Sayyid, ya duba ƙirjinsa da stethoscope.
Nana ta ce "Doctor yaya jikin nasa? Me ka gani?"
Bai kalli Nana ba ya ce "Me yasa ba ku dawo follow up ba"
Ta ce "Ai ba a bamu lokacin dawowa ba. Dama ni ce naga yakamata mu dawo ɗin. mu na ta ƙoƙarin kuɗin allurar su haɗu ne, ko ba su haɗu ba, zamu yi ƙoƙari ko a anan Asibitin gwamnatin ne, sai mu yi booking a fara yi masa"
Likitan ya ce "Ki na ji na 'ya ta?"
Ta ce "Eh"
"Ai mijinki ne ko?"
Sayyid ya jinjina kai. "To a duniya babu wani abu da Allah ba zai iya ba, babu shi. Batun allura ki bar wannan a hannun Allah. Kuma dan babu kuɗin allaura ba za a daina ganinsa ba. Zamu ci gaba da gwada shi, mu na ba shi magungunan da suka dace. Idan Allah ya yassare kwa zo a yi daga baya. Kuma jikinsa Alhamdillah da sauƙi sosai da sosai. Jinin dai haryanzu bai sauka yadda ake so ba. Amma zai sauka da yardar Allah. Kawai ki din ga kiyaye damuwarsa da ɓacin ransa. Idan kuma akwai wani abu da yake damunsa, ki zauna da shi ku tattauna ki ga ta ina za ku shawo kan matsalar?. Amma babu wani abu in sha Allah" Duk da ba lafiya likitan ya ba su ba, amma kalamansa akwai dattaku da ƙwarewa a kan aiki a cikin sa. Dan haka sosai Nana ta samu relief.
Ya rubuta musu lambarsa ya ce "Duk lokacin da za ku zo, ku kira ni, na baku ranar da nake aiki, ya zo ya din ga ganina." Nana ta din ga yi masa godiya da addu'a shi da iyayensa.
Sayyid ya ja wata takarda, ya yi rubutu ya miƙa wa likitan. Likitan ya karɓa ya duba. Ya yi murmushi ya ce "Madam, ashe kema babu lafiya ya ce na duba masa ke"
Nana ta yi murmushi ta ce "Rashin lafiyata, ai ba komai ba ce a kan tasa, ni na fi damuwa da shi ɗin dai"
"A'a tun da ya nemi alfarma, ai dole a yi masa"
Ya duba Nana, ya yi wa Sayyid bayanin laulayi ne kawai yake damunta, ya rubuta mata abin da zai rubuta mata na magani. Ya kuma ba ta gwaje-gwaje. Sayyid ya ƙi tafiya, sai da suka yi gwaje-gwajen. Suka koma, ya tabattar musu da babu wata matsala, satin cikinta uku da kwanaki, ya rubuta mata magungunan da za ta yi amfani da su.
Suna tafe a adaidaita sahu, Sayyid ya kasa riƙe murmushinsa, ya kai bakin sa kunnen Nana ya ce "Saura kwana nawa ki haihu?" Ta kwashe da dariya, ta ce "Ina na sani, ko cika wata ɗaya bai yi ba ma, mu dai ci gaba da addu'a Allah ya bar mana, ya bamu ɗa na gari"
Ya amsa da "Amin."
A bakin titi, Nana ta yi sayayyar salak, saboda shi take sha'awar ci. Suka shiga layin gidan na su. Su na zuwa gidan, Nana da sauri ta shiga banɗaki, saboda fitsarin da ya cika mata mara. Sayyid tsayawa ya yi, yai shiru yana ƙare wa ɗakin kallo.
Nana ta fito bai ce mata komai ba, ta ɗauki cylinder gas, ta ce "Sayyid gas ya kusa ƙarewa, idan zaka iya fita in anjima sai mu je titi tare mu ɗuro"
Ya ce "To"
"Bari na sake ɗumama miyar"
Ta fito tsakar gidan kenan, Sajida ta ce "Nana, Allah ya taimake ki, da tuni da ke za a tafi bayar da shaida"
Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Shaidar me?" Ayshacool "Jiya hirar da ku ka yi, har ki ke yi wa Barira faɗa, a kan matar nan. Daga jiyan nan zuwa yau magana har ta kai kunnen matar. Ta din ga kuka mijin ya ce ba zai yarda ba da 'yan uwanta. Da yyayyenta ne za su zo su zane Barira. Mijin matar ya hana aka kai ta police station. Tun bayan fitar ku tana can, duk sai da muka je bayar da shaida. Wataƙila dai kafin magariba a sako ta, ta dawo gida."
Nana ta numfasa ta ce "Gara da Allah ya sa ba na nan, dan babu inda zan je, shi yasa a rayuwa yake da muhimmanci mutum ya iya bakinsa. Wannan tara matan da ku ke yi, ku na surutai marasa amfani duk ba hanya ce mai ɓullewa ba"
Sajida ta ce "Wallahi haka ne, shi yasa ki ke burge mu ma"
"Allah ya kyauta"
Har Nana ta yi haɗin salak ɗin ta, ta fara ci, ya lura ba ta fahimci abin da yake faruwa ba, shi ma kuma bai gaya mata ba, ya ci abincin. Ta gama ci ta kalle shi ta ce "Sayyid, ka yi mini addu'a, Allah ya sanya kar na yi aman salad ɗin nan, na rufe sauran anjima zan sake ci"
"Kin cika yaji, sai kin yi ciwon ciki ko?"
Ta ɗan waro ido ta ce "Dama ka gani?"
"Eh ina kallon ki"
Ta ɗan yi murmushi ta ce "Idan babu yajin, ba zai yi daɗi sosai ba. Amma yanzu ya ka ke ji a jikin ka?"
"Ba sauƙi" "Subhanallah, ba sauƙi kuma?"
Ya ce "Eh, kin je ki na hira da likita a gabana"
"Amma ko ba komai, ya kwantar mini da hankali, bai ce mini zaka mutu ba, kalamansa sun bani ƙwarin gwiwar da yakamata na samu" ta yi maganar ƙwalla na cika mata idanu.
Ya girgiza mata kai ya ce "Kar ki bari su zubo".
"To ba kai ne ba, komai na yi sai ka ji haushi na?"
Murmushin sa mai matuƙar ƙayatarwa ya yi, ya ce "Ba haushinki nake ji ba, tsaro nake ba ki, saboda tawa ce nikaɗai. sourire (smile) ki yi murmushi mana" ta noƙe kafaɗarta tana tura baki,ta juya masa baya. Ya matsa bayan nata, ya sumbaci saman bayan ta, ya zagayo da hannunsa ta cikinta, ya kwantar da kansa a kan kafaɗarta. Gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi. Damuwa ce ya ziyarce zuciyarsa, jin yadda Nana ta saki jiki sosai da rungumar da ya yi mata, ko ba a gaya masa ba ya san abin da yake ranta, tuna cewar babu abin da zai iya tsinana mata, ya sanya a hankali ya raba jikinsa da nata, wani irin tausayinta na ratsa ilahirin jikinsa.
Ta maze cikin yaƙe ta ce "Sayyid, ya na ji ka yi shiru ne?"
Ya girgiza kai ya ce "Babu komai"
"A'a akwai wani abu. Dama likita ya ce mu zauna na tambaye ka, ko akwai wani abu da yake damun ka, haryanzu fa jininka bai sauka ba Sayyid"
Ya ɗan sake yin guntun murmushi ya ce "Damuwa ai akwai ta, ba na son ɗaga miki hankali ne kawai. Haryanzu ina tunanin inda su Habu suka tafi, suka bar ki da ɗawainiya, Kodayake ko suna nan ma, kula da ni ba dolen su ba ne. Sai wahala ki ke sha, wallahi idan ina tuna hakan, sai na ji tamkar numfashina zai ɗauke a cikin damuwa nake sosai da sosai. Ba na son saka ki a damuwa ne kawai".
Nana ta tattara hankalinta ta matsa kusa da shi, ta riƙo hannunsa, ta kalli idanunsa da suka yi jawur. "Idan su Habu ba hakkinsu ba ne kula da ki. Ni yanzu ya zama haƙƙina, na san ba a banza Allah ya haɗa mu ba. Mu ci gaba da addu'a Allah ya kawo mana komai da sauƙi. Amma ina fatan dan Allah ka daina damuwa, idan ciwon nan ya matsanta maka a jikina nake ji, ka daina ba na so" ta ƙarasa maganar cikin shagwaɓa.
Kafaɗarta ya ciza cikin wasa, yana rungume ta. Tamkar ba a cikin damuwa suke ba, suka ci gaba da raha, duk da yadda hayaniyar mata ta cika gidan, tamkar a na taro, saboda dawowar Barira, an cika gidan ana mayar da yadda aka yi. Ana fara kiran sallar magariba, ta kai masa ruwan ɗumi banɗaki ya yi alwala. "Za ka je masallaci ne?"
"A'a a nan zan yi"