Kenza eBookz

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 32

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 32

Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 32: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 32. "To yi sallar. Nima sai na yi muje mu ɗuro gas, ko rabi ne sai kuma na…

3,334 words

"To yi sallar. Nima sai na yi muje mu ɗuro gas, ko rabi ne sai kuma na sayo gawayi, Ummi ta bani kurfoti, na din ga haɗawa da shi" Ya jinjina mata kai ya tayar da salla. Yana kallon ta ta idar, ta buɗe jakarta ta ɗebo sauran kuɗin da suka dawo da su, ta nufi wardrobe ta haɗa su da waɗancan kuɗin. Kawai ta ga kayan wardrobe ɗin a hargitse. Mamaki ya kama ta, ta san Sayyid ba ya taɓa mata wardrobe, kuma ita ba a haka ta bar wardrobe ɗin ba. Ayshacool Ta janyo jakar gidan Sarkin baka, ta duba ta ga kuɗin nijar a ciki. Ta laluba ta ɗauki ledar, da kuɗin Nigeria ke ciki ta rasa. Ta watso kayan wardrobe ɗin gaba ɗaya, tana ƙara haskawa da fitilar wayarta. Yana tsaye yana kallon ta. Muryarta na rawa ta ce "Sayyid"

Ya kalle ta. "Kuɗinmu, kuɗin da ka bani na saka a cikin wardrobe na...naa..ajiye a nan ban gani ba, ko ka ɗauka?"

Ya yi shiru yana kallon ta, a zuciye ta nufi hanyar fita daga ɗakin, ya riƙe ta. Jikinta yana tsuma take ƙoƙarin fizgewa amma ya riƙe ta yana girgiza kai ya ce "Kar ki yi magana, ki yi shiru ko waye mu bar wa Allah. Tun da na shigo, na ga alamar an buɗe ɗakin. Kuma laifinmu ne, da ba mu saka mukulli ba, muka rufe ɗakin kawai."

"Sayyid ba a yi mana adalci ba. Kuɗin Abincinmu da maganinka, sun kwashe gaba ɗaya wace irin masifa ce wannan? Daga wannan sai wannan ya ake so na yi ne?" Ya riƙe ta gam yana shafa bayan ta, a hankali ya ce "Ki yi haƙuri, ki daina ɗaga murya, akwai Allah"

Kuka take yi iya ƙarfinta, tana sheshsheƙa, ya rungume ta gam a jikinsa, shi kansa ya ji zafi da raɗaɗin satar da aka yi musu. Ba iya kuɗi ba, har da wasu daga kayan amfaninsu na ɗakin an ɗauka, ya san kuma hakan sabon ƙalubale ne, saboda ba su da wata hanyar samun kuɗi a yanzu. Ji ya yi jikin Nana ya saki, kuma jikin yana ɗaukar sanyi. Karkarwa ta fara yi, tamkar ana jona mata shocking. Cikin matsananciyar damuwa, ya zauna da ita a jikinsa, ya ɗauki wayarta da ta saki a gurin, yana haska fuskarta. Ya ga hawaye na fita ta gefen idonta. Hannayenta da ƙafafuwanta su na lanƙwashewa, goshinta kuma yana tsatstsafo da gumi. Jin ta ta yi, jingine da wani abu da ba ta san ko mene ne ba. Ta shafa abin ta ji ƙurzunu-ƙuruzunu, tamkar dutse. Gurin baƙi ƙirin duhu ya gauraye gurin, ko tafin hannunta ba ta iya gani. A hankali haske ya fara shigowa gurin, har gurin ya yi haske ba ki ɗaya. Ta ɗaga kanta ta ga ba ta iya gano ƙarshen ɗakin. Jin tari ta yi a bayan ta, ta waiwaya da sauri, ta ga Ƙaisar a zaune lulluɓe da wani abu mai haske sosai.

"Ƙaisar. Ba ka da lafiya?" Ta yi maganar tana nufar inda yake.

Ya yi shiru bai yi magana ba. Ta sake cewa "Dama kuma ku na rashin lafiya, kamar ka canza gaba ɗaya" ya yi murmushi ya ce "Mu na rashin lafiya mana, guba na ci" Ta waro ido ta ce "Guba kuma? Me yasa?"

"Tsohon nan na jikin mijinki, ya bani."

"Kuma ka sha? Wai meye alaƙar ka da shi? Kuma dan Allah me yasa yake bibiyar mijina?"

"Ba wannan ba, me yasa ki ka kira ni?" Cikin mamaki ta kalle shi ta ce "Kamar yaya? Ni ban kira ka ba ai"

"Fushi da ɓacin rai, duk wanda ki ka yi tamkar kin kira ni ne. Kuma ni yanzu ba ni da wani tasiri sosai, saboda jinya nake yi. Babu wanda ya san ina nan. Giyaz ya saka ni a gaba, ya mamaye Library ɗi na, yanzu rashin ganina zai sanya ya ci gaba da cutar da ku. Ba zan iya wani abu ba sosai yanzu, sai dai zan iya tasiri a kan bil'adama. Duk ba wannan ba, duba can." Ta ɗaga kai ta kalli inda ya nuna mata, Library ɗin Ƙaisar ta gani. Ta ga gangar jikin Sayyid a kwance. Tsohon nan ya ɗaɗɗaure shi da wata irin igiyar ƙarfe. Ƙasan gadon da yake kai kuma, wata irin wuta ce take ci a ƙasa. Nana ta zabura a rikice, ta ce "Wannan ai Sayyid ne" "Ƙwarai shi ne, ba wani ba. Kuma Giyaz shi ya sanya masa matsalar da ku ke ciki na auratayya. Sai dai abu ɗaya zan iya gaya miki. Matsalar zuciya da hawan jini da yake fama, wannan ciwo ne yake damun sa. Amma Giyaz na assasa wani abin. Kuma... Amma dai shikenan"

Nana ta buɗe baki za ta yi magana, ya ce "Kar ki tambaye ni komai, kin san sharaɗin. Kalli" ya yi maganar yana sake nuna mata gurin.

Alhaji Fatuhu ta gani, ta yi ƙuri da ido ta ce "Kamar na san wannan"

"Ba kama ba ce ba kin san shi, ciwo ne da zafin sihirin da aka yi masa ya mayar da shi haka. Sai kuma albishir da nake yi miki, da ƙanwar ki ta zama cikakkiyar 'yar ƙungiyar asiri. Ɗayar kuma wannan bararojin da ta taɓa baki magani, ta aura mata ɗanta, wanda yake baƙin aljani ne. Kuma ta tarkato kan iyalanta duk su na jikinta. Kuma kowanne akwai abin da yake mora a jikinta. Ke in taƙaice miki ma, a kowane lokaci za ta iya rasa hankalinta ko ma rayuwarta gaba ɗaya. Ayshacool Shikenan bissalam"

"Ƙaisar" sai kuma ta yi ido huɗu da Sayyid.

"Kin tashi?" Ta yinƙura ta tashi zaune, tana kallon ɗakin.

Sayyid ya ce "Ƙaisar ɗin ba shi da lafiya ne?" Ya yi maganar yana tsare ta ido.

"Wane Ƙaisar ɗin?"

"Tambayata ki ke yi?" Shiru ta yi, ita ba ta iya tuna koma ma a cikin abin da ya faru ba. Idonta ne ya sauka a kan kayan da suke gaban wardrobe a ƙasa, sai kuma abin da ya faru ya faɗo mata. Afujajan ta tashi ta sake nufar wardrobe ɗin, tana zazzage kayan tana kuka.

"Kuɗin nan fa babu su, an kwashe ki daina wannan dube-duben" ya zauna ta yi shiru ta sanya kayan a gaba tana kallo.

Ya yi mata shiru ya ƙi kula ta, ya kwanta a kan katifa, yadda take a hasalen nan, idan ya matsa faɗa za su yi. Cikin ƙanƙanin lokaci nannauyan bacci ya yi awon gaba da shi.

Barira na kwance a ɗakinta, ta yi ɗaiɗai tana bacci, ta ji kamar ana karta mata farce a ƙafafuwanta. Har ta maze ta ci gaba da bacci, amma ta ji an cigaba. A fusace ta ce "Gali meye haka, za ka din ga karta mini faratanka, ina cikin bacci ne?" Shiru bai amsa ba. Ta laluba ta ji yo ƙeyarsa a can ƙarshen gado, yana bacci. Ta koma ta kwanta, amma ta ji an cigaba, ta tashi zaune tana zabga ashariya. Ta kunna fitila, ta ga babu kowa. Ta yi tsaki ta sauka daga kan gadon, ta fito tsakar gida domin ta yi fitsari. Bayan ta fito daga banɗakin, kanta ko ɗan kwali babu, kawai ta yi karo da Nana a tsakiyar tsakar gidan tana yi mata wani irin mugun kallo.

Ta haska Nana ta ce "Nana lafiya kuwa?"

Sai dai Nana ba ta yi magana ba, ta sake haska ta, za ta yi magana. Ta ga ta rikiɗe ta zama wata irin ƙatuwar mage, baƙa ƙirin, girman ta ya yi na tunkiya ƙosashiya da ita, ta yo kanta tana buɗe haƙora. Da gudu Barira ta shiga ɗakinta, tana ihu tana kiran sunan Gali.

"Ke mahaukaciya, mene ne haka za ki din ga ihu kina kiran sunana a tsohon daren nan?"

Ba ta ce masa uffan ba, ta duƙunƙune, tana mayar da numfashi. Ta tsorata sosai da sosai, da ƙyar ta samu ta yi bacci. Sai dai a cikin baccin ma, mafarkin magen nan kawai ta din ga yi tana bin ta, tana karta mata farata tana cizon ta.

Sayyid kuwa yana jiyo kururuwar Barira, hakan bai dame shi ba, sai ganin Nana da ya yi a zaune, ta haɗa kai da gwiwa. Ya yinƙura ya tashi zaune, bai ce mata komai ba, ya kwantar da ita a kan katifar, ya rufe su da bargo ya rungume ta yana shafa bayanta. Yana jin ta tana kuka, har ta yi ta gaji bacci ya ɗauke ta. Dauriya kawai yake yi, amma ji yake tamkar ya taya ta kukan.

Washegari, Barira ta tashi da matsanancin zazzaɓi da ciwon kai, ta din ga yi wa mijin kuka, tana cewa ya mayar da ita gidansu, mayu sun kama ta a nan gidan, ba za ta yadda a kashe ta a banza ba. Babu yadda ya iya ya tattara ta ya kai ta gidansu.

Kwanki biyu da sace kuɗin nan, Nana ta rasa abin da yake yi mata daɗi. Dubu talatin ce ta ragu a hannunta, shi ma cikin irin kuɗin da ta zuba a jakarta ne suka fita da su. Kuɗin Nijar ɗin kuma ba ta san ma ina za ta a canza su ba. Bayan haka tayi tunanin idan Habu ya dawo fa, me za ta ce masa? Ta din ga tunanin yadda za ta yi da dubu talatin ɗin nan, ba tare da ta rushe gaba ɗaya ba. Ga shi magungunan da yake sha kawai, na wata ɗaya dubu goma sha biyu take sayen su. Sai dai kamar yadda yake nanata mata, ta yi haƙuri, ya sanya ta fauwwala wa Allah lamarin.

Kwana biyar da kwashe kuɗin nan, Sayyid ya hana Nana gaya wa kowa. Sai dai cikin dare ba ta iya bacci, saboda lissafi da tunani. Ta kira Ummi ta tambaye ta batun barkono, ta ce ana ta saya, ta sayar da ya kai rabin buhun. Kayan Abinci da Mama ta haɗo mata da su, take ta cancana musu. Da daddare ba ta iya bacci, saboda damuwa da tunani, sai dai abin yana damun sa fiye da yadda yake damun ta. Su ka wayi gari, ya tashi jikinsa babu daɗi, yana ta numfarfashi.

Abin Duniya ya ƙara damunta, ya kuma ƙi cin komai. Muryar Barira ta jiyo a tsakar gida, da ta dawo, tana maganganu tana ba wa su Sajida labari.

"Mayu sun kama ni a gidan nan, kuma da ƙarfina na dawo, wallahi sai sun ci uban su, kurwata ta fi ƙarfin mutum".

Sajida ta ce "Ban gane mayu ba, suwaye mayun kuma?"

Barira ta ce "Oho, ki zuba ido ki gani, Allah zai tona musu asiri" Ayshacool "Ni fa ba na son kurman baƙi, a masu shigowa ne mayun, ko kuma zaunannun gidan"

"Na ce ki zuba ido ki ga ikon Allah"

Bai fi mintuna biyar ba, wani irin hayaƙi, mai azabar yaji, ya turnuƙe gidan. Nana da take lafiya ƙalau ma, ta fara tari. Shi m tarin yake yi, numfashinsa kamar zai ɗauke, ta ɗaukko mafici ta din ga yi masa fifita. Ta gaji ta tashi, da nufin ta je ta ga me ake ƙonawa yake wannan uban hayaƙin haka. Amma ya riƙe hannunta ya hana ta. Haka suka wuni a galabaice. Sajida ma sai bala'i take yi, tana cewa Barira za ta kashe ta da hayaƙi.

"Wai Sajida ko ke ce mayyar nan ne?"

"Ke kama bakin ki, wallahi ki ka ce mini mayya, sai mun yi shari'a da ke"

Barira ta ce "Sai ki saurara mini, tun da dai ba ke ba ce" Haka suka wuni, Barira tana gana musu azaba, da wannan azababben abin da take zubawa a cikin murhu. Washegari ma, azabar hayaƙin nan ce ta tashi su Nana, numfashin Sayyid tamkar zai ɗauke saboda azaba. Nana dai ta ci gaba da daurewa, amma yamma na yi, Barira ta sake cika kurfoti da gawayi, ta tayar da wuta ta afka hayaƙin nan.

A fusace Nana ta fita, ta tarar da ita tana ta girgiza kurfotin, tana zuba wani abu a ciki.

Nana ta ce "Barira, dan zatin Allah ki daina zuba wannan abin. Ina da mara lafiya a ɗaki. Yana da matsalar numfashi, jiya kwana muka yi babu bacci. Kuma da sassafe kin banka wani, kuma yanzu ma ga shi kina sake kunnawa"

Ta kalli Nana ta ce "Ai duk wanda ya hana uwar shi bacci, wallahi shi ma ba zai yi ba"

Nana ta ce "Kamar yaya kenan?"

"Kamar yadda ki ka ji"

"Ni dai koma mene ne, ki yi haƙuri idan ba ki yadda ba, zo mu je ɗakin ki ga halin da yake ciki"

"Babu ruwana da halin da yake ciki, kurwata ce ta fi ƙarfin duk wani maye wallahi"

Nana ta ce "Barira mu ne mayun da ki ke faɗa dama? To Barira ko za mu ci mutum ma ci taki, jiki duk dauɗa?"

"Ko ma duk uban mene ne, tun da aka kama ni aka lasa, an ji zaƙin kurwa ta, wallahi sai mutum ya ci ubansa, miyagun banza kawai"

"Mu ne mayun Barira?"

"Eh ku ne, ko na ce ke"

Nana ta ƙarasa daf da Barira ta damƙi tsintsiyar hannun Barira ta ce "Ki ka ce ni mayya ce?" Barira ta yinƙura za ta fizge hannunta, ta yi bala'i. Kawai ta ji jikinta ya yi wani irin nauyi, kuma jikin ya yi mata wani irin sanyi, ta kasa motsa komai. Kawai ta silale ta faɗi ƙasa.

Ayshercool 08081012143 Ayshacool "Gidan Nana kuma? Ina ne gidan Nanan, kuma matsalar mene?"

"Baba mutanen unguwa sun taru, za su dake ta, kar su kashe ta ni ban ya zan yi ba"

A sukwane Baba ya miƙe ya ce "Ƙarya ne. Nanan za su kashe mini, ai zan yarda kowa zai iya ɗaukko magana a cikin ku, amma ban da Nana. A can gidan gadin nata ne za su dake ta?"

"Baba wane gidan gadi kuma, ai sun bar gidan tana nan kusa da ni, ka manta ne? Ka cewa Nasiru ya rako ka ya san gidan"

"Gani nan zuwa" ya kashe wayar ya yi waje da sauri.

Ummi ta tsaya a bakin ƙofar, tana ta ba su haƙuri. Amma sai nema suke yi su ture ta, su shiga ɗakin.

"To ban da wulaƙanci ma, ta shige ɗaki taƙi fitowa, da yake ba ta da gaskiya. Maimakon mijinta ya fito ya bayar da haƙuri, shi ma ya yi zamansa saboda rashin tsoron Allah, da rashin gaskiya"

Ummi ta ce "Mijinta ba shi da cikakkiyar lafiya, ita ma aljanu sun buge ta, dan Allah ku yi haƙuri" Sai dai abin ya fi ƙarfin Ummi, ƙoƙarin hankaɗe ta kawai suke yi, su cimma Nana. Ana haka sai ga maƙwabcin su Nana, tare da jami'an tsaro. A dole mutanen suka saurara. 'yan sanda suka ce, a tafi da Barira Asibiti, abin da likitoci suka ce, da shi za a yi amfani.

Ana haka Baba ya ƙaraso, cikin tashin hankali.

Ummi na ganin sa ta yi ajiyar zuciya. Ummi ta ce "Baba ka zo?"

"Eh, ina Nanan take, kuma uban me ta yi za a dake ta da?"

"Ai gama 'yan sanda sun zo, saɓani suka samu da wanda suke zaune gida ɗaya, shi ne suka ce mayya ce"

Baba ya ce "Maita kuma? In ji uban wa?"

Mijin Barira ya ce "Ga shaida Baba, kalli matata a baje a kwance"

"Kuma sai ka ce 'yata mayya ce? To wallahi ƙarya ne, kaf danginmu babu mayu, ku dai nemo wani abun, ba maita ba wallahi" 'Yan sanda suka shiga maganar, aka tafi da Barira Asibiti.

Sai da aka bar 'yan sanda biyu, gudun abin da ka iya faruwa, saboda matan da abun ya faru a gaban su, su na ta ƙara balbalawa wutar fetur. Tare da mayar da abin da aka yi da wanda ma ba a yi ba. Gaba ɗaya zancen ya zagaya unguwa. Har sha ɗayan dare case bai ƙare ba, Nana ta farfaɗo ta ga Ummi a ɗakin su, ga duhun dare ya fara yi.

"Ummi lafiya kuwa?"

"Ina fa lafiya Nana, meya haɗa ki da mutanen gidan nan, ga shi ana cewa ke mayya ce".

"Mayya kuma?"

"Eh mana, yanzu case na hannun 'yan sanda, Baba yana can tare da su, ana jiran likitoci su faɗi sakamakon binciken su."

Nana ta gaya wa Ummi iya abun da ta iya tunawa. Sai dai ta sha mamaki, ta ji wai Baba ya zo kan matsalar ta. Ta kalli Sayyid da yake kwance lamo, abin Duniya duk ya dame shi. Sajida ta haɗa kayanta, ta gudu ta ce ba za ta iya kwana da Nana a gidan ba.

Sai zuwa da safe, Likitoci suka tabattar da anemic shock ne ta samu, bayan binciken ƙwaƙwaf da suka yi, suka gano ta yi ɓari sati biyu baya, ta kuma zubar da jini sosai ba ta je Asibiti ba. Ta zo ta yi zazzafan zazzaɓi na typhoid amma suka alaƙanta hakan da mayu, nan ma ba a je Asibiti ba. Hakan ne ya haddasa faɗuwar ta. Bayan fito da sakamakon, mijinta da 'yan uwanta suka ce ba su yarda ba, sakamakon ƙarya ne kawai aka gaya musu. Ga Barira ta farfaɗo, tun a cikin daren ma, har ta ci Abinci, amma suka ci gaba da surutu a kan Nana mayya ce.

Ummi tare da su Nana ta kwana, saboda tsananin tsoro. Dan da gidanta akwai guri can za su tafi ma. Sai dai tashin hankalin abin da ya faru, ya sanya jikin Sayyid rikicewa gaba ɗaya, ya zamana kamar ma ba ya gane wanda yake kansa.

Hankalin Nana ya yi mummunan tashi, ga shi babu isasshen kuɗin tafiya Asibiti. Ta kuma san tashin hankali, da damuwar abin da ya faru ne, ya sanya jikin nasa ƙara rikicewa.

Nana ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ga matan gidan kowacce ta koma gidansu, sun ƙi dawowa gidan wai tsoro suke ji. Ummi ce ta yi sallama, Nana ta amsa ta yi mata izini ta shiga ɗakin. Hannunta riƙe kular Abinci. Ta kalli inda Sayyid ke bacci a wahale, numfashinsa na fita sama-sama. Cikin damuwa Ummi ta ce "Yanzu Nana haka jikin nasa ya koma?"

"Wallahi Ummi, gaba ɗaya hankalina a tashe yake"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ana wata ga wata"

Cikin damuwa da rashin fahimta ta ce "Me ya faru?" Ayshacool Cike da karaya, da matsanancin tausayin ƙanwarta ta ce "Mai gidan nan ne, ya je ya same ni, ya bani dubu goma sha biyu, wai ga sauran kuɗin ku nan, ku tashi. Ba ya son tashin hankali, kuma ga sauran 'yan hayar sun ce ko ku tashi, ko ya mayar musu da kuɗinsu su tashi. Nayi-Nayi ya ƙara wani abu, tun da ko wata ba ku yi ba, amma ya ƙi wai wannan ɗin ma da ƙyar ya samo su ya kawo."

Nana ta jingina da jikin bango tana maimaita "Innalillahi wa Innalillahi raji'un"

"Nana mene ne abin yi yanzu?"

Nana ta girgiza kai, jiki a sanyaye ta ce "Ban sani ba Ummi"

"To ko wani gidan za a nemo? Sai na koma na neme shi, na roƙi alfarmarsa?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a Ummi, an riga an yi mini mummunan tambari a unguwar nan, abu ne mai wahala ma mu sake samun wani gidan a unguwar nan"

"Bari na kira Baba na ji me zai ce"

Nana ta ce "A'a Ummi, kin san halin Baba, kar ranki ya ɓaci"

"To Nana ya zamu yi, dole a kira shi mu ji me zai ce" Ummi ta kira lambar Baba, yana ɗaga wayar muryarsa a sama ya ce "Ya kuma aka yi, ba an kashe case ɗin a gurin 'yan sanda ba?"

Ummi sai da ranta ya sosu, amma ta maze ta ce "Baba ba wannan ba ne. An kori su Nana daga gidan da suke ne, mai gidan da suke ya ce sai sun tashi"

"To sai kuma aka yi yaya? Ni zan nemo musu wani gidan? Ko kuma mijinta ne yakamata ya nemo musu wani?"

"Baba ka fa zo gidan nan, ka ga halin da mijin nata yake ciki na rashin lafiya, saboda haka aka kore shi daga gurin aikin gadi. Dan Allah Baba ka yi wani abu a kan yarinyar nan. Nana yarinya ce ƙarama pressure ta yi mata yawa."

Readers Also Read