Kenza eBookz

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 39

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 39

Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 39: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 39. "Rufe mini baki Ƙaisar" Ƙaisar ya kalli mahaifinsa jin ya kira shi da…

3,362 words

"Rufe mini baki Ƙaisar" Ƙaisar ya kalli mahaifinsa jin ya kira shi da sunansa na yanka, saɓanin sunan da yake masa kara da shi, na uban duƙusa wanda da shi ake kiransa saboda kara ga mahaifinsa. Dan duk cikin bataliyar 'ya'yan da ya haifa, ya fi ƙaunar sa. Ya ɗora da cewa "Kar ka manta abin da suka yi wa Mahaifina Jaddul Jinn wanda yake kaka ga duk wani Aljani da yake nahiyar nan, da yadda ake girmama shi, sai mene ne dan a azabtar da su. Dan mene zaka hau kan bil'adama a matsayin bawa, duk da kasancewar ka ƙasaitaccen matashin aljani da ake ji da shi a jinsinmu" ya yi maganar cikin ɗaga murya, muryarsa na amsa kuwwa a ilahirin dajin.

"Zaman lafiya da kwanciyar hankali, mu rayu mu da su babu cuta babu cutarwa. Lalata musu amfanin gona, sanya musu rashin lafiya da makamantansu duk ba zai sanya ku huce ba, tun da waɗanda suka yi laifin na sun mutu basa nan"

"Uban duƙusa yanzu ka fifita bil'adama a kan ni mahaifinka?"

"Ko ɗaya, sai dai ka san muna mutunta yarjejeniya. Mun yi yarjejeniya da abokina, zan ci gaba da bawa zuriyarsa kariya, zan kula 'yar sa zan din ga kawo mata magunguna tana bayarwa. Kuma ya yarje mini ci gaba da yi wa zuriyarsa hidima, da bayar da magani ta hanyar waɗanda aka haifa da tauraron 'yar sa Lanti"

"Ƙarya ka ke yi Ƙaisar. Ɗana ba zai zama bawa ga gajiyayyun halittu kamar bil'adama ba, ka sani yadda suke yi mana kallon halittu maƙaryata, haka su ma ba su da cika alƙawari. Ka tuna kai makaranci ne, manazarci kuma marubuci. Ka karanta litattafai da ni kaina ban san adadinsu ba. A ɗakin karatun ka akwai litattafan da aka rubuta dubbanin shekaru kafin zuwanka Duniya. Ka yi yawace-yawace a Duniya domin neman abubuwan rubutawa, kuma ina da tabbacin ka karanta tarin kashedin da magabantanmu suka yi mana a kan bil'adama. Dan haka ba zan bari iliminka da soyayyar da nake yi maka, su ƙare a kan yi wa biladama hidima ba, ba ma su su yi maka ba. Sai dai ka zaɓa, zama da mu ko kuma hidima ga bil'adama!"

Ayshercool 08081012143 Ayshacool Sai da ta shekara biyar, tana aikin jakar nan, tare da jiƙata da magunguna daban-daban. Ban da zanen hatimai kala-kala da yake cikin jakar. Ta haɗa kai da ɗan uwan Sarkin Aska, baya nan ya je ya ajiye masa jakar a ƙasan abin kwanciyar sa. Kuma ƙaisar ya ɓatar da sahun sa, ta yadda babu wanda ya gane a cikin aljanun da suke yi masa hidima. Tun da ya kwana a kan jakar, Aljanun da suke yi masa aiki, suka watse suka bar shi, ya kamu da matsananciyar rashin lafiya da sai da ta yi ajalinsa. Yana mutuwa kuma aljanun suka fantsama kan 'ya'yansa da jikokinsa, sai dai aka rasa wanda zai gaje shi gurin ci gaba da aikin zaluntar al'ummar da yake yi. Sosai mutanen gari suka yi murna da mutuwar sa. Babban ɗan sa da suke bokancin tare ma, cewa ya yi ba zai iya ba. Ƙin samun wanda zai gaje shi, ya sanya aljanun fara sanya wa iyalansa cututtuka. Wasu kuturta wasu suka makance, har da waɗanda suka haukace. Aka din ga ɗauki ba daɗi da Lanti, a kan sai ta warkar da su. Ƙaisar ya gargaɗe ta a kan babu ruwanta ta rabu da su. Lanti ta shafe shekaru Ashirin da bakwai, tana aiki tare da Ƙaisar tana harkokinta na bori da bayar da magani, haka zalika ita ma ta yi wa mutane da dama girka, masu sha'awar harkar bori. Akwai bikin 'yan bori da ake gudanarwa da nuna bajinta duk shekara, wanda a nan ake yi wa masu so girka, ake bikin bajekolin abubuwan ban mamaki, na gidaje daban-daban. Maharba su yi na su, wanzamai, 'yan bori da dai sauran su. Domin bayan mutuwar Sarkin Aska an ɗan samu zaman lafiya, tun da dama shi yake assasa duk wata fitina da rashin zaman lafiya. Sai dai aljanu ba su fasa cutar da su da razana su ba, duk da Lanti tana iya kokarinta. Sai dai ita ma bayan wannan shekarun ta koma ga Allah. Sai dai kan ta mutu, a cikin jikokinta an samu guda ɗaya da take da irin tauraronta. Dan haka bayan mutuwar Lanti, aka ci gaba da ba ta kashi tsakanin mutanen garin, da Aljanun da sarkin Aska ya yi aiki da su, har ma da waɗanda ba 'yan asalin garin ba ne. Sai dai babu yadda Ƙaisar zai yi, a lokacin jikar Lanti ba ta kai lokacin da za ta iya bayar da magani ba. Kuma har a lokacin ba a fasa yi masa magiyar ya rabu da bil'adama ba. Gaba ɗaya ya nesan ta kansa da Ahalinsu.

Bayan jikar Lanti ta fara tasawa, Ƙaisar ya fara bijiro mata, domin yin gadon kakarta, sai ta kasa ɗauka sai ma taɓin hankali da ta samu, duk da ta ɗan taɓa bayar da maganin amma ba sosai ba. A hakan ita ma ta yi aure ta hayayyafa. A cikin 'ya'yanta aka samu wadda ta gaje ta, duk da ba irin tauraronta ɗaya da Lanti ba. A lokacin Musulunci ya shigo cikin mutane, duk da bai yi ƙarfi a garin Buda ba. Asma'u ta bayar da magani ita ma, ta yi aiki tare da Ƙaisar, sai dai ba ta da ƙarfin zuciya da juriya irin ta Lanti. Gaba ɗaya ita ma ba wani daɗin aiki ya ji da ita ba. Ko yaya ya buɗe mata ido ta ga abu, sai ta kwanta ta hau jinya. Daga baya ma ta watsar ta tattara komatsan borin ta ajiya, ta ce ta tuba ta daina. Ganin ba a samun masu irin tauraron Lanti, ya sanya Ƙaisar fara sarewa, da haƙura da batun bayar da magani ta hanyar bil'adama. Sai dai yana iya yin sa gurin bawa zuriyar su Lanti kariya, daga cutarwar zuriyarsu. Duk abin da yake faruwa, Giyaz yana ankare da Ƙaisar, kuma yana murnar yadda ɗan sa ba zai ci gaba da zama bawa ga bil'adama ba.

Aka din ga samun ci gaba a garin Buda, wasu suka din ga barin garin su na tafiya fatauci, wasu kuma tashin hankalin Aljanun da ya addabi garin ne ya sanya suka bar garin, ciki har da wasu daga cikin zuriyar Lanti. A can Bauchi aka haifi Maijidda, har ta girma, an saka mata rana saura watanni uku aurenta, su ka zo Buda, a nan suka haɗu da Isa, ya ƙallafa rai a kanta. Yayar kakarta ta ce sai an warware wancan baikon da aka yi da na can garin Bauchi, an yi da Isa, saboda ƙara danƙon zumunci, kuma hakan zai sanya su din ga kawo musu ziyara a kai a kai, da ƙara samun zaman lafiya a tsakanin zuriyar maharba da ta wanzamai. Ayshacool Aka mayar wa da wancan na Bauchi kuɗinsa, ita kuma ta auri Isa. Gidansa na Kano, inda yake harkokin kasuwancinsa, nan ya tafi da ita. Ya ajiye ta a gidansa da suke tare da matarsa babar Gaddafi. Ya ɗora wa Maijidda son duniya, kamar a kanta ya taɓa aure. Ba uwargidansa ba, hatta 'yan uwansa sai da suka fara jin haushin Maijidda saboda ba ya ɓoye son da yake yi mata, ga ta yarinya ƙarama amma su na ganin kamar ta mallake shi, dan shekarunta goma sha shida a lokacin. Kasancewar daga zuriyar Sarkin Aska Maijidda take, ta auri ɗan zuriyar Sarkin Baka, sai Aljanun da suka yi wa sarkin Aska hidima, suka shiga cikin lamarin auren, su ka fara haddasa musu matsala. Haka kurum sai ta ji ta tsani Isa, ba ta ƙaunar ganinsa ga yawan rashin lafiya. Kishiya da facaloli suka sako ta a gaba, ga jarabar dangin miji. Ana haka ya samu matsala da uwargidansa, da ta haifa masa Gaddafi da Ummi, ya sake ta. Nan ma aka ce Maijidda ce sila. Ya auri Rabi, suka zama ita da Maijidda. Yayarsa Atine ta ƙara haɗe kai da Rabi, su na cizguna mata. Maijidda ke riƙon su Gaddafi, tana iya kokarinta amma kullum cewa ake yi tana azabtar da su. Kasancewar Gaddafi ya fi Ummi wayo, ya tsani Maijidda cewa yake saboda ita aka saki babar su, kamar yadda Yaya Atine take faɗa. Ita kuma Ummi tana matuƙar ƙaunar Maijidda. Nan ma Rabi ta saka Maijidda a gaba, da kishi da ƙage kala-kala. Bayan haihuwar Imran sai da ya shekara uku da rabi, ta haifi Nana. A lokacin Isa ji yake kamar ba a taɓa yi masa haihuwa ba sai a kan Nana. Ya saka mata suna Asma'u, sunan kakarsa da ta riƙe shi take bala'in son sa. Hatta hakika biyu ya yi wa Nana, Ummi ma da ya saka mata sunan mahaifiyarsa bai yi mata abin da yake yi wa Nana ba. Isa kofur ne na 'yan sanda, abokan aikinsa suka yi masa ƙage, aka kore shi daga aiki har da prison. Ya koma harkar fawa, ya fara samun rufin asiri, harka ta buɗe masa yana samun rufin asiri sosai , sai dai kasancewar sa mutum ne da ba shi da sirri, duk samun sa sai ya bayar da labari, abokansa suka jefe shi sana'ar ta fita daga ransa ya daina zuwa ko ina, sai zaman gida. Tun da Allah ya sanya aka haifi Nana Ƙaisar ya ganta ya rikice, tamkar Lanti ta yi kaki ta ajiye saboda kamanin su. Ga irin tauraronta ɗaya da Lanti. Gaba ɗaya Ƙaisar ya tattara hankalinsa a kan Nana Asma'u yana ganin, ya samu uwar gijiya a zuriyar Lanti. Giyaz na fuskantar abin da ke shirin faruwa, ya fara ƙoƙarin raba Ƙaisar da Nana. Dan kullum yana tattare da ita. Wasu lokutan ya zungure ta tayi ta kuka. Manyan bokaye da ƙungiyon Asiri na zawarcin son yin aiki da Ƙaisar, saboda tarin baiwa da kuma ilimi da binciken ƙwaƙwaf da yake yi. Wanda za su aiki da shi ne, ya din ga taimaka musu, su kuma su din ga yi masa hidima, amma fafur ya ƙi. Saboda ba ya son duk wata alaƙa da jini. Ƙaisar ya yi tafiya zuwa wata ƙasa, ganawa da wani tsohon Aljani, a kan wani rubutu da yake yi, ya dawo ya tarar an saki Babar Nana, ita kuma Nana ta daina magana, ta daina tafiya ga Baba ya ƙwace ta, ya hana Maijidda ita. Ya fuskanci aikin mahaifinsa ne Giyaz. Ya je ya same shi yake tambayar sa me yasa ya yi wa Nana haka. Giyaz ya ce "Ka sani ba zan taɓa sake yadda, ka zama bawan bil'adama ba, da ka sake zama bawan bil'adama gara na kashe ta ko na kashe ka, kowa ma ya huta." Ƙaisar ya san Giyaz ba ya magana biyu, idan ya faɗi magana sai ya aikata. Dan haka Ƙaisar ya fara ƙoƙarin kare Nana, ya yi amfani da jakar da ya saka Lanti ta haɗa, ta yi amfani da ita gurin kashe Sarkin Aska. Ya ƙara yi mata aiki, da saiwoyi da wasu hatimai, ya yi wa Giyaz tarko da ita. Cikin matsananciyar sa'a, Giyaz ya faɗa tarkon Ƙaisar, saboda ya san muddin ya bar Giyaz, zai iya nakasta Nana nakasa ta har abada, ko ma ya kashe ta, kamar yadda ya furta. Ya ɗauki Giyaz, ya kai shi can nesa ya sadaukarwa wani boka shi, bisa musayar da za su yi, zai ba shi wani abu mai muhimmanci. Wanda ya yi hakan domin nesan ta shi da Nana da zuriyar Lanti. Ayshacool Duk da abin da ya yi ya dawo ya dame shi, yana matuƙar ƙaunar mahaifinsa, duk da saɓanin da suka samu, amma babu yadda iya, hakan ne kawai zai sanya ya nisanta shi da Nana. Sauran 'yan uwan Ƙaisar da tuntuni suke jin haushinsa, suka yo caaa a kan Ƙaisar, har suka nemi hallaka shi, saboda abin da ya yi wa mahaifinsu, amma sun san ko sun hallaka shi, idan Giyaz ya kuɓuta suma sai ya kashe su. Ɗan uwan Giyaz Duna, ya yi ta ƙoƙari gurin ganin ya kuɓutar da Giyaz, amma abu ya gagara. Nan suka din ga kai wa Nana hari, da yinƙurin hallaka ta. Maijidda kuwa bayan mutuwar aurenta, tana gama idda, Iliyasu tsohon saurayinta ya sake dawowa ya aure ta. Ko da Baban Nana ya samu labari, sai ya ce tana sane, ta ƙi zama da shi, saboda ta koma ta auri Iliyasu, dama son zama da shi take yi ba. Nana ta ga garari tun da ƙuruciya, babu cikakkiyar kulawa, kuma tun ba ta fi shekara uku ba take ganin Ƙaisar, da ma sauran 'yan uwansa da suke ta kokarin azabtar da ita. Maijidda ta so karɓar ko Nana ce, saboda rashin cikakkiyar lafiya, amma Isa ya hana fafur, ita ma can mijinta ko yaya ta motsa tana son ganin 'ya'yanta, sai ya hau bala'i wai za ta gurin tsohon mijinta. Tun Nana na ƙarama, take nuna alamun rashin lafiya, amma babu wanda ya kula. Ta kan wuni tana bacci tun safe, har dare babu wanda zai damu. Wasu lokutan ta daina magana ma ko tafiya gaba ɗaya. Idan kuma ta warware ta din ga fitinar da ta fi ƙarfin shekarunta nesa ba kusa ba. Ta kan ga Ƙaisar a zahiri, ko kuma a cikin bacci. Babu wanda ya damu da ta ci Abinci ko ba ta ci ba, mussaman da Baba ya daina sana'ar komai, sai dai Imran ya nema ya bata. Idan ta fita Ƙaisar ya kan zo a suffar mutum, ya ba ta abinci. Allah ya sanya masa matsananciyar ƙaunarta. Ya fara bayyana a jikinta ne, tun wani duka da Mama ta yi mata, bayan faɗa ya haɗa ta da Jamila. Sai da ta kwana biyu a sanƙame, tun daga nan suka gane halin da take ciki. Da ranta ya ɓaci sai hankalinta ya gushe. Ƙaisar ya sha ɗauke Nana, a neme ta a rasa kwana ɗaya ko biyu ya je ya ajiye ta gurin sa. Baba ya yi ƙoƙarin nema wa Nana magani, amma abu ya gagara. Labari ya iske Maijidda halin da Nana ne ciki, bayan da su Adda Saude suka zo ganin su Nana. Rabi ta haɗa tuggu a gurin Baba, ya ce kar su sake zuwar masa gida, kuma ba zai bayar da Nana ba. Wahala ta saka Imrana fara sace-sace saboda su ci Abinci, Rabi ta saka Baba ya kore shi daga gidan. Haka Nana ta tashi a cikin wahala, ga wanda bil'adama suke yi mata, ga wadda Ƙaisar yake yi mata da sunan kulawa.

Ji ta yi tamkar an sanya hannu an shaƙe ta, a dole ta saki littafin ta ja da baya tana tari.

Ta ɗaga kai ta kalli Ƙaisar, bai ce mata komai ba, ya ɗauki littafinsa ya juya ya tafi. Yana barin gurin Haula ta zagayo ta dafa Nana. Ta ɗaga kai ta kalle ta ta ce "Ƙawata, kwana biyu. Hadiminki ya ƙi saurarata balle na sanya ran zai karɓi buƙata ta, ki yi wani abu a kai dan Allah"

Nana ta ce "Haula, gaba ɗaya jinsinku ba abin yadda ba ne, ki rabu da ni da wannan maganar ta ku"

"Shikenan, na rabu da ke, amma kin yi ganganci abin da ki ka yi wa dattijo, Allah kaɗai ya san me zai yi miki idan ya gama jinya. Kuma har Ƙaisar ki ka janyowa shi ma ba zai bar shi ba"

"Duk hukuncin da ya yi wa Ƙaisar yayi daidai, ɗa na gari ba zai taɓa yi wa babansa abin da ya yi wa nasa mahaifin ba"

Haula ta ce "Kash! Nana kar ki zama butulu mana. Sai dai ina fatan kin fuskanci jakar gurin Sarkin baka da ya baki, wace jakar ce"

Nana ba ta ba wa Haula amsa ba, Sayyid ya tashe ta.

"Ma vie" yayi maganar yana matsawa jikinta sosai. Jiki a sanyaye ta amsa masa. Ya ce "Lafiya dai?"

"Mmm"

"Ko Ƙaisar ɗin ne?"

"A'a"

"To me yasa ki ka tsorata? Mene ne ya baki tsoro?"

"Bakomai"

"es-tu sûr? (Kin tabatta?)"

Ta ce "Eh. Haryanzu hannunka lafiya ƙalau ko?"

"Eh, amma akwai abin da ya tsorata ki, gaya mini mene ne?"

Ji ta yi tamkar ta gaya masa, dan a wannan karon ba ta manta abin da Giyaz ya gaya mata ba, a kan idan ya warke zai sake waiwayar su.

"Ma viee"

"Sayyid" ta amsa a hankali.

Ya yi maganar yana taɓa wuyanta "Sanyi ki ke ji Rayuwata"

"Eh, amma ba sosai ba" Ayshacool "In baki ɗumi ne?" Yayi maganar muryarsa ƙasa-ƙasa

Dariya ta yi ta ce "A'a na yafe, ƙona ni za ka yi"

Shi ma dariyar ya yi ya ce "To ni ki bani sanyin ina so" Ya yi maganar da sigar shawaɓa.

"Wai kai ba ka jin bacci ne? Kawai ka farka cikin dare?"

"Soyayya ce ta tashe ni" Sai da jikin Nana ya ɗan yi sanyi, ta ce "Soyayya kuma Sayyid?"

"Eh, je t'aime ma femme"

"To ai ban san me ka ce ba"

Ya yi kissing ɗin goshinta ya ce "Ina sonki matata" wani abu ne ya tsirgawa Nana, tun daga tsakiyar kanta, har tafin ƙafarta. Shafa hannunsa ta yi, kamar mai tantamar abin da ya ce, ta ce "Sayyid"

"A'a, kar ki yi tantama, ko ki yi kokwanto, shi yasa na baki sunan Rayuwata. Ko a wannan Duniyar, ko ma a wace Duniyar, kawai ina son matata, saboda ita ɗin Rayuwata ce. Babu abin da zai canza hakan."

"Sayyid ina tsoron idan ka tuna waye kai, ka ji ba ka so na, zan cutu da yawa, zamana da kai na shaƙu da kai sosai zuciyata ba za ta iya ɗauka ba" Ta yi maganar cikin rauni da tsoro.

Ya ɗaga kan Nana, ya sanya hannunsa a wuyanta, ta lumshe idanunta hawaye na bin gefen fuskarta.

"Ƙa'idar ba za ta canza ba har abada, babu ruhin da zai samu nutsuwa a gangar jikin ɗayanmu muddin ba ma tare, ki saka haka a ranki. Sayyid yana son Rayuwarsa. Ko babu raina fatalwata za ta ci gaba da sonki" Nana ta yi ajiyar zuciya tare da dariya, ta shafa gashin kansa.

"Allah ya sa haka. Ina son mijina sosai nima" murmushi ya yi yana kissing ɗin ta.

Har garin Allah ya waye, maganganun Sayyid ne ke kai komo a cikin ƙwaƙwalwa, zuciya da kuma gangar jikin Nana. Wani irin shauƙi da farinciki ne yake kama ta, da tuna kalamansa.

"Amarya" ya yi maganar yana kallon ƙwayar idonta.

"Amarya da wannan ɗin?" Ta yi maganar tana nuna cikinta da ya fito sosai.

Yayi murmushi yana shafa cikin ya ce "Duk da haka amarya ce ai, ko kin manta?" Ya yi maganar yana kashe mata ido. Ta yi murmushi tana ci gaba da ninkin kayan da ta wanke.

"Sayyid, bari na je kasuwa na nemo kayan magungunan ka, na dafa maka, ka ci gaba da sha, kuɗin hannuna sun ɗan taru, zuwa ranar Monday in Allah ya kaimu, duk yadda za a yi, mu tafi Kano Asibiti. Na ji haryanzu zuciyarka ba ta bugawa sosai, na san ƙarfin hali kawai ka ke yi"

"Gaskiya kin fiye saka ido, ya aka yi ki ka gane hakan, mai magani?"

Ta jinjina kai ta ce "Au haka ma za ka ce ko? Hmm ai shikenan, za ka ga mai magani, yau sai na wanke ka da magani na kulle ka a ɗaki"

"Eh saboda cin zali ba, kuma ke ki gudu, alhalin kamata ya yi ki yi mana tare"

Ganin yadda yake rungumota ta ce "Sayyid na gama shiryawa, fita fa zan yi"

Ya ce "Na sani"

"Ka sani kuma ka ke son na ɓata lokaci? Dan Allah Sayyid jiya throughout the night mu na tare, yanzu kuma...

"Shhhh... Ba ki ji jikina ya fara zafi ba"

"Wallahi lafiyarka ƙalau, normal babu zafi a jikinka, wai wannan surutun duk daga ina?"

Haka ya hana Nana fita, har bayan Azahar, kawai ta zuba wa Sarautar Allah ido. Kuma a fuskar sa take ganin tsantsar ƙarfin hali, amma ba shi da lafiya. Sai bayan la'asar ta marairaice ta ce "Dan Allah ka bar ni na je na haɗo kayan nan Sayyid, ko haryanzu ba ka gama jin Sanyin ba?" Ya ɗaga mata gira. "To ga mafici, yi ta fifita, har na dawo" Dariya ya yi yana ɗan jan hancinsa. Ya kamo hannunta ya ɗora a wuyansa ya ce "Kin ji da zafi ko?"

Readers Also Read