Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 40
Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 40: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 40. "Ba wani zafi. Waccan ranar ma wayo ka yi mini, wai na baka sanyin jikina"
3,342 words
"Ba wani zafi. Waccan ranar ma wayo ka yi mini, wai na baka sanyin jikina"
Dariya yake son yi sosai, amma sai ya yi kaɗan ya cije, ya ce "Ai ni Ƙaisar wasu lokutan taimakona yake yi"
A sanyaye ta ce "Shi me yasa ba ka kishi da shi?"
"In ji wa? Kawai abu ɗaya ne da babu yadda muka iya. Alaƙarsu ta ɗa da mahaifi tana tasiri a rayuwarmu ni da ke" Cikin mamaki Nana ta ce "Ta yaya? Kuma ya aka yi ka san Ƙaisar ɗan Giyaz ne?" "Yadda ki ke ganin Ƙaisar ku yi magana, haka nake ganin Giyaz, kuma na fuskanci waye shi a tattare da ni. Yanzu ki je ki dawo" "Kai amma na yi mamaki fa, kuma ba ka taɓa gaya mini ba. Bari na je na dawo, ina da tarin tambayoyin da zan yi maka"
"Tom sai kin dawo"
Ta saka hijjabinta, har za ta fita ya kirawo ta. Ya ce "Ba ki yi mini ba"
Ta yi masa kiss a goshinsa, da bakinsa. Ayshacool "Allah ya yi miki albarka. Ki kula mini da kanki, kar wani ya kula mini ke, ki kular mini da babyna ki tafi a hankali ki je ki dawo"
Ta kalli cikin ta ce "To Shugaba, in sha Allah" "To a dawo lafiya, I love you"
Cikin murmushi ta ce "Inyee ɗan gayu, ka yi furansanci, ka yi turanci, ka yi hausa ga kuma yarenku. Zan koyo yaren da baka iya ba, na din ga tashin kanka da kalaman soyayya"
Ya ce "Je ki dawo ki yi mini waƙa"
"Sai dai na je na dawo, na yi maka tsifa, na yi maka sabon kitso" ya tsuke fuska yana hararata. Ta fita tana waigensa tana murmushi.
Tana fita ya jingina da jikin bango, yana dafe saitin zuciyarsa, yana haki sama-sama. Ya fito tsakar gida da kyar, ya zauna yana sake danne saitin zuciyarsa da yake jin wani irin abu kamar shocking daga zuciyarsa yana zagayawa bayansa har cikin kansa. Tsayuwar motoci ya ji a waje, sai dai hankalinsa ba ya kan hakan. Ya ji an daki ƙofar gidan da ƙarfi. Ya ɗaga kai ya ga wasu murɗaɗɗun ƙarti sun shigo cikin baƙaƙen kaya.
Duk da mawuyacin halin da yake ciki, haka ya yinƙura ya tashi da ƙyar, ganin an shigo da Habu hannunsa da sarƙa.
Ya din ga bin mutanen da kallo, Habu cikin matsananciyar damuwa ya zube a kan gwiwoyinsa ya ce "Ka yi mini Afuwa Imam, ba laifina ba ne ka yi haƙuri, na gaza baka kariyar da ta dace" Sayyid ya din ga bin sa da kallo, da alama ma ba ya gane me Habu yake nufi. Ƙartin nan biyu daga cikin su, suka yo kansa, suka riƙe shi.
A rikice ya ce "A'a, ku rabu da ni. Me na yi muku?"
Ƙoƙari suke su tasa shi su tafi da shi cikin salama, amma ya turje. Suka juya yare zuwa faransanci, su na rarrashin sa, ya wuce su tafi.
"Ba zan je ko ina ba? Ina zan tafi na bar matata" Habu ya din ga girgiza masa kai da alamar ya daina faɗar maganar da yake yi.
"Ku rabu da ni, ina zaku kai ni na tafi na bar Nana" maganar da yake yi cikin ɗaga murya, ga ƙoƙarin turjewa da yake yi, ya sanya zuciyarsa yin rauni, ya yi baya zai faɗi. Suka tare shi suka saɓa shi suka yi waje da shi. Aka saka Habu a cikin wata motar daban, Sayyid kuma aka saka shi a cikin wata baƙar Highlander mai tint glass, aka rufe suka tafi da shi.
Nana tana tsaye ta bayar da kuɗi, za a bata kankana, dan daga ita har Sayyid, kawai ta ji gabanta ya yi wata irin mummunar faɗuwa. Ta yi shiru, ta jiki gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi. Kawai ta juya ta tafi. Mai kayan yana ta yi mata magana, amma ba ta tsaya ba, ta nufi gida har da ɗan gudu saboda azabar sauri. Tana zuwa ƙofar gidan ta ga ƙofar gidan a ɓalle, da hanzari ta shiga gidan, tana kiran sunan Sayyid. Amma wayam ba ya nan, ta shiga ɗaki baya nan. Ta duba banɗaki nan ma ba ta gan shi ba.
Ta fita waje da sauri, tana kalle-kalle, ta tafi hanyar inda bishiyar kukar nan take, tana tunanin ko jikinsa ne ya motsa, ya tafi can, sai dai can ma baya nan. Ta sake komawa gidan cikin tashin hankali, da wani yaro da yake zuwar mata aike ta haɗu a ƙofar gidanta ta ce "Ashiru, ko ka ga Sayyid ya fito daga gidan nan? Wannan mutumin na gidana farin nan?"
"Wasu mutane ne suka shiga gidan suka tafi da shi, a mota suka zo"
Sak Nana ta tsaya, tana ƙure Ashiru da ido, tamkar ma ba ta gane yaren da yaron yake yi.
Ayshercool 08081012143 Ayshacool Cikin rawar murya Nana ta ce "Wace irin mota kuma Ashiru? Ka tabattar kuma Sayyid ne?"
"Wallahi na tabattar, ina nan ina wasa suka zo, a motoci wannan farin na gidanki suka ɗaukko." Tamkar mahaukaciya ta bi sahun motar, ita ce har titi ko za ta ga motar da Ashiru ya ce, amma babu wata alama na za ta ga motar da aka daukar mata Sayyid aka saka a ciki. Gaba ɗaya ta kasa kuka, sai tsuma da jikinta yake yi tamkar mazari. Tuni rana ta faɗi, an fara kiran sallar magariba, ba ta san tafiyar da ta yi da nisa ba, sai da ta tashi dawowa. Gidan Uwani ta nufa, ta tarar da ita ta yi alwala, za ta yi sallar magariba. Uwani ta ce "Ke Nana, uban me ya fito da ke da magaribar nan, ga juna biyu kina da shi, duk da na san ba ki da ɗan aike amma koma mene ne, ai kya bari a idar da salla ko?" Nana ba ta yi magana ba, ta nemi guri ta zauna a ƙasa. "Ke lafiya kuwa?" Uwani ta yi maganar tana tattara hankalinta a kan Nana. Amma Nana ta kasa magana, sai murza zoben hannunta da take yi, tana ajiyar zuciya. "Ke ki yi mini magana, kar ki tayar mini da hankali mana". "Sayyid ne ya ɓata"
"Kamar yaya sai ka ce wani zakara?"
"Da gaske nake"
"To ai ban gane ya ɓatan ba ne? Mutumin da yake jinyar ne ya iya tashi ya fita har ya ɓata?"
"Ai kwana biyu jikin da ɗan sauƙi, dan har ya ce mu zo nu gaishe ki" Ta yi maganar ba tare da tana iya tantance me ma take faɗa ba.
"A'a Nana, wataƙila dai wani wajen ya je zai dawo. Tashi ki yi sallar magariba, zuwa anjima a raka ki gidan ko ya dawo"
Nana jin Uwani kawai take yi, ta tashi ta yi sallar magariba, aka yi isha'i. Uwani ta saka Nana a gaba zuwa gidanta, sai dai kamar yadda Nana ta bar gidan wayam babu Sayyid babu dalilinsa. Nana dai ba ta gaya wa Uwani abin da Ashiru ya gaya mata ba, na ya ga an zo da mota an tafi da shi ba. Sai wajen goma na dare, hankalin Uwani ya tashi. Ta sanar da samarin gidan halin da ake ciki. Nan suka bazama a cikin Buda yawon neman Sayyid, duk da galibi ma ba su san shi ba, kwatancensa Uwani ta yi musu, suka tafi yawon neman sa, har gurin jami'an tsaro aka kai rahoto. Sai dai har bayan sha biyun dare, babu wanda ya ji ko ɗuriyarsa. Uwani ta saka aka rufe gidan, ta ce Nana ta zauna a nan, ko zuwa dare zai dawo.
Nana a ranta ta ce "Wane dare kuma bayan wannan"
Daren ya zame wa Nana dare mafi tsawo a rayuwarta. Damuwa da tunani ya cika mata zuciya. Ba ta tunanin Sayyid zai iya tafiya ya bar ta. Idan kuma da gaske zuwa aka yi aka tafi da shi, to suwaye su ka tafi da shi? Ina suka kai shi, me ya yi musu? Ko dai wani laifin suke aikatawa ba ta sani ba? Amma shi da yake kwance babu lafiya, kullum tana tare da shi a gida, yaushe har yake aikata wani rashin gaskiya da ba ta sani ba. A haka har aka yi assalatu, a kan kunnenta.
****
Dare malafar rana, kowa ya bika ya shirya maka.
Danƙareriyar mota ce, ƙirar highlander baƙa, take ta kwarara gudu a saman kwalta, tamkar hanyar domin direban kawai aka yi ta. Gefe da gefen hanyat baki ɗaya babu komai, banda yashin sahara, sai busassun bishiyu jefi jefi. Kasancewar dare ne, wata ya kai kwana goma sha huɗu, ya haska ko ina, ga taurari sun yi wa sararin samaniyar ado. Titin ta tsakiyar sahara ya ratsa, wadda yashin saharar ya bayar da sassanyan yanayi.
Kallon sa ya yi, daga bisani ya ce "Kilomètre nawa ce ta rage mana ne?"
Direban ya waiwayo ya kalli mai maganar wandaa fuskarsa a rufe take cikin rawani ya ce "Bai fi 95 kilomètre ba"
"Dans quelques minutes ?? (Nan da wani lokaci?)".
"Bai fi awa ɗaya ya rage mana ba"
"Dole fa mu ƙarasa dai-dai lokacin da aka umarce mu, ni ina tsoron ma kar ya farka. Ka ƙara sauri"
Ya yi maganar yana haska fuskar Sayyid, da yake kwance a jikinsa ya haɗa gumi, cikin wani yanayi kamar bacci kamar suma, sai dai yadda yake gumi ya nuna a wahale yake baccin, babu in da yake motsi a jikinsa, sai ƙirjinsa da yake ɗagawa yana sauka lokaci zuwa lokaci, numfashinsa yana fita da ƙyar.
Ya kai hannunsa, ya ɗora a kan ƙirjin Sayyid, idan zuciyar sa ta buga sau ɗaya, sai ta jima kafin ta sake bugawa. Sai dai duk bugawar da za ta yi, da ƙarfi take bugawa tamkar za ta tsaga ƙirjinsa ta fito dummm!. Ayshacool Cikin damuwa ya ce "Lowalli, sai ka ƙara gudu fa, kar ya mace mana, bugun zuciyarsa raguwa fa yake yi. Kuma ka san idan ya mace mana mun shiga uku mun lalace"
Lauwalli ya jinjina kai yana ƙara gudun motar. Ya ce "In sha Allah a raye za mu kai shi, ba za a samu matsala ba. Dan dai ka ƙi yarda ne, da na ce mu tsaya a Asibiti".
"Kai dalla ka daina maganar tsayawa a wani Asibitin nan. Ka yi ka hanzarta mu cika umarnin nan, mukaɗai ake dako"
"To shikenan, mun kusa in sha Allah" ya yi maganar yana ƙara gudun motar.
**** Antin Yusra ce ta kalle ta, ta ce "Yusra duk wannan kwalliyar fa? Ta karɓar baƙon ce?"
"Eh mana Mami, yana hanya ma ai" ta yi maganar tana tafiya ɗakinta, ta fesa turare. Wayarta ce ta fara ringing, ta ɗaga wayar tana murmushi ya ce "Gani a layin"
"Duba lambar gidan, za su buɗe maka"
Ya ce "Ok"
Bayan mintuna goma sha biyar, ta fito ta ce "Mummy na tafi"
"To a gaida baƙon, ya tabattar mana da alkhairi"
Kawai ta fice tana murmushi. Tana zuwa ta gan shi a tsaye a cikin falon, yana kallon ƙaton frame na hoton mai gidan, da yake retired soja. Ganin abin take tamkar a mafarki, wai Sagir ɗin ta ne a gabanta. Jin ƙamshin turarenta ne ya sanya ya waiwaya. Da gudu ta ƙarasa inda yake ta faɗa jikinsa. Babu tunanin komai, Sagir ya ƙanƙame ta a jikinsa, bar siririn mayafin da ta yafa a kanta, yana zamewa gyararren gashin kanta, da yake ta ƙamshin mayuka ya bayyana. Ya din ga shafa bayanta yana murmushi, kawai ya ji tana sheshsheƙar kuka. A ɗan rikice ya ce "Lafiya, kuka kuma Yusra?" Ya zauna tare da ita a jikinsa, ya ce "Ina ta murna zan zo na gan ki, amma in zo ki din ga kuka, ko ba kya son ganina ne?" Ta girgiza masa kai alamar a'a. "To mene ne" "Ka daina so na, tun da ka sake ni ba ka ƙara nema na ba" Ya ɗago fuskarta su na kallon juna yace "Da na daina son ki, ba zan zo nan ba Yusra, kin san yadda rabuwarmu ta kasance, ban daina sonki ba, ban kuma daina tunanin ki ba"
"Almost three years, ba ka sake nema na ba"
Sagir ya marairaice murya ya ce "To yanzu ba gani na zo har nan saboda ke ba? Haba wifey" ta zumɓura baki cikin ɗabi'arta ta shagwaɓa. Duk da ya zuciyarsa na tunatar da shi, tare da gargaɗin sa a kan Yusra ba muharramarsa ba ce, amma ya kasa yaƙar kansa, ya ƙyale ta a jikinsa yana jin yadda ya yi kewarta.
"Talk mana, na zo kuma kin haɗe rai?" Tashi ta yi daga jikinsa, ta zauna a kusa da shi ta ce "Ya hanya?"
"Alhamdillah, ki na lafiya ya jikin naki?"
"Da sauƙi"
"Kin warware?"
Ta girgiza kai ta ce "Bayan ƙin yadda ku ka yi da gaske ba ni da lafiya. Sai ga shi na haɗu da wata Nana, ita ma tana irin ciwon da nake ji, ai ita ta san ba ƙarya nake yi ba."
Ya ce "To yanzu dai duk ba wannan ba, i miss you Yusra, irin sosai da sosai ɗin nan fa"
"Bayan ka yi aurenka, ba wani missing ɗina da ka yi" ta yi maganar tana tsiyaya masa lemo a cup ta miƙa masa. Ya karɓa ya kai bakinsa yana tsare ta da ido. Ta kalli screen ɗin wayarsa da ya kawo haske, hoton Haidar ya bayyana a kan screen ɗin. Ta ɗauki wayar tana kallon yaron ta ce "Waye wannan?"
"Ɗanki ne Haidar, recently ma ta kuma haihuwa ɗan ya rasu" ta yi masa wani kallo, da bai tantance na mene ne ba ta ce "Da tuni nima wataƙila na haihu"
Ya yi murmushi ya yi shiru, yana cin abincin da ta zuba masa. Cikin hikima ya karkatar da zancen suka ci gaba da hira. Wayarsa ce ta fara ringing, ta ajiye masa ganin hoton heart a kan sunan. Ya ɗaga wayar tare da yin sallama "Hello love"
"Ka sauka lafiya?"
"Alhamdillah am good dear"
Shukura ta ce "To sai ka dawo, Allah ya tsare mana kai, take care"
Ya yi murmushi ya ce "In sha Allah dear" wani abu ne ya tokare wa Yusra a ƙirji, ta zuba masa ido.
Ya ajiye wayar, bai kalle ta ba ya ce "Yusy, kin san na yi missing ɗin girkinki over?"
Jin ta yi shiru ya sanya ya ɗaga kai ya kalle ta, ya ga tana hararsa. Ya yi murmushi ya ɗebo Abincin ya kai bakinta. Ta murguɗa masa baki ta tsuke fuska.
"Smile, haba sweetheart" ta buɗe bakin ya saka mata Abincin. Haka ya ribace ta, suka ci gaba da hira.
A nan ya yi sallar la'asar, sannan ta fito raka shi. A jikin motarsa suka tsaya, tana yi masa wani irin kallo mai ƙayatarwa. Ayshacool "Tom sai yaushe zan dawo?"
"An jima kaɗan"
Ya yi murmushi ya sake kallon ta ya ce "Yusra"
Ta ce "Na'am"
"Yaushe za ki dawo gidana, ji nake kamar na ɗauke ki, na tafi da ke Kano, ina kewar ki sosai da sosai. Yaushe za ki dawo gidana?"
Ta girgiza masa kai ta ce "Ba zan dawo ba"
Cikin mamaki ya ce "Saboda me?"
"Ka auri wata, kuma Hajiyarka ba za ta bari na dawo ba, su Mami ma ba za su bar ni ba, kuma ma haryanzu ban gama warkewa ba"
"Haryanzu ki na so na?" Ta kalle shi ta sunkuyar da kanta ƙasa.
"Idan ba kya so na, me yasa ki ka nemi lambata, ki ka kira ni? Kuma har ki ka ba ni dama na zo?" Ta sunkuyar da kanta ta ci gaba da murza yatsun hannunta. "Yusra Sagir ɗin ki ne fa, ɗago ido kalle ni" Kawai ya ga hawaye na bin fuskarta.
"Sagir ɗina, da ya rabu da ni, saboda ba ni da lafiya ba" Ta yi maganar tana sheshsheƙa. Ganin babu kowa a gurin da suke, ya sanya ya janyo ta jikinsa, ya ɗago kanta yana kallon idonta ya ce "Yusra, ki na so na haryanzu?" Ta yi shiru hawaye na ci gaba da bin idanunta. "Ki na so na har yanzu, shi yasa ki ka neme ni. Dan haka batun ina da aure, Hajiyata ba za ta bari ba, 'yan uwana ba sa son ki, haryanzu ba ki da lafiya, duk ba ta taso ba. Za ki dawo gidana a karo na biyu in sha Allah. Haryanzu ina son ki Yusra"
"Amma...
"Babu amma tsakaninmu, believe me zan dawo da ke gidana in sha Allah" Jikinta ya yi sanyi. Ya cika ta a hankali, ya shiga motarsa. Ta tsaya ƙyam tana kallonsa, shi kansa da kyar ya tafi, tamkar ya ɗauki Yusra ya tafi da ita.
Har ya kama hanyar Kano, zuciyarsa cike da tunanin ta ina zai fara. Dan shi har ga Allah yana son matarsa, ba a son ransa ya rabu da Yusra ba. Yanzu kuma da ya ganta, gaba ɗaya ya ƙara rikicewa ba abin da yake sai tuno soyayyar da suka yi, daga saurayi da budurwa zuwa auren su.
Ko da ya je gida, Shukura ta karɓe shi tana yi masa sannu da zuwa. Amsa mata ya yi yana kallon ta, kafin ya ƙaraso ta kira shi ya fi sau biyu, yana zuwa hatta ruwan da zai yi wanka ta tanadar masa. Ya cire kayansa ya shiga wanka, kamar ta san ba zai iya salla ba, sai ya tsarkake jikinsa, saboda rungumar da ya yi wa Yusra. Tana cikin tattare kayansa, hancinta ya ji ƙamshin turaren da ba na sa ba a jikin kayansa. Turarensa ɗaya ne da ta san shi da shi. Jikinta ne ya yi sanyi, domin ta daɗe da karantar alamomin rashin gaskiya a tattare da shi. Wani abu ne ya soki zuciyarta amma ta yi ta maza ta haɗiye tare da ajiye kayan.
****
Aka shiga kwana na biyar, ba tare da jin ko ɗuriyar Sayyid ba. Nana duk ta fita hayyacinta, ba ta iya cin abinci, ba ta bacci. Ga Uwani tun tana rarrashinta, ta koma yi mata faɗa tana ganin ta ƙi tawakalli ta ci gaba da addu'a. Ga shi ta hana ta komawa gidan nasu, a nan gurinta take zaune tare da ita.
Yanzun ma Uwanin ce ta miƙo mata kofi da fura a ciki ta ce "Ungo ki samu ki sha furara nan Nana, ko ɗan cikinki ya samu wani abu shi ma. Rayuwa ba za ta yiwu a haka ba kina zaune babu Abinci, ga juna biyu ba. Idan wani gurin mutumin nan ya tafi, idan da rabo zai dawo ai" Nana ta karɓi kofin, tana ajiyar zuciya. "Maza ki shanye, kan na fito daga banɗaki" Nana ta jinjina kai tana kallon kofin. Uwani na shiga banɗaki, Nana ta ɗauki mukullin da aka kulle gidansu, ta tafi. Gani take kamar tana shiga za ta tarar da shi a inda ta bar shi. Ƙofar dama a lanjare take aka rufe ta. Ta shiga ɗakinsu, amma ta tarar wayam babu kowa a ciki. Ta kalli kan katifar su, ta ga abin hiraminsa na rawani a kai. Ta durƙusa a kan gwiwoyinta, ta damƙi hiramin nan, da yake ta ƙamshin turaren sa. Tamkar ta damƙi Sayyid ɗin. Cikin kuka ta ce "Haba Sayyid, daga cewa na je na dawo, sai ka tafi ka bar ni? Haba Sayyid yau kwananka biyar ba ka tare da ni. Da mutuwa ka yi na san wannan hukuncin Allah ne, dole na tawakalli, amma me yasa zaka tafi ban san halin da ka ke ciki ba. Haba Sayyid Haba Sayyid Nana ce fa" ta din ga soki burutsu tamkar zararriya. Wani irin kuka take yi mai haɗe da gunji da ƙunar zuciya. Ba ta san lokacin da Uwani ta shigo ba, tare da abokiyar zamanta Sabuwa ba, sai ji ta yi ta taɓa ta ta ce "Nana shi ne sai da ki ka fito ki ka zo ko? Ba na ce kar ki fito ba?" Ayshacool "Uwani. Sayyid ya tafi ya bar ni, na zata mafarki nake yi, me yasa zai tafi ya bar ni?"
"Ke ki ji mini 'ya da rashin ta ido, yo ina zan san dalilin da ya sanya ya tafin ni? Ke ba za ki iya dakewa ki kama kanki ba, idan guduwa ya yi fa?"