Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 41
Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 41: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 41. Sabuwa ta ce "A'a Yaya, su fa yaran birni su na nunawa junansu kulawa, ya…
3,371 words
Sabuwa ta ce "A'a Yaya, su fa yaran birni su na nunawa junansu kulawa, ya za a yi mutum mara lafiya a neme shi a rasa, ki ce hankalinta ba zai tashi ba? Kina kallon yadda take tiri-tiri da shi take nula da abin ta ke kin san ba ƙaramin so take yi masa ba, ai da tausayi"
Uwani ta ce "Kuma haka ne, amma tun da shi ya tafi nima jikata nake yi wa kar wani abu ya same ta, ga ciki. Ke Nana kuma ba garinsu ya tafi ba bai gaya miki ba? Ba kin ce ɗan Nijar ba ne?"
"Ba shi da lafiya fa, ba zai iya wannan tafiyar ba"
"A'a kar ki ce haka, idan ki ka bibiya ma, can ɗin ya tafi, amma yanzu ki yi haƙuri ki tashi mu tafi gida"
"Uwani, dan Allah ki yi mini alfarma ki bar ni na kwana a nan"
"To ya za ki kwana a gida ke kaɗai haka ake yi?"
"Ni dai dan Allah ki bar ni a nan, wallahi da safe zan dawo na yi miki alƙawari"
"A'a sai dai na turo yarinya ɗaya ta tayaki kwana" Nana ta amince da hakan, aka turo mata yarinya. Tuni yarinyar ta yi bacci, Nana kuma kwana ta yi aikin kuka. Lokaci Lokaci, sai ta yi tasbihi tare da ajiyar zuciya. Washegari da sassafe Uwani ta zo ta kawo mata abin karyawa. Yadda idanun Nana suka kumbura, ya sanya ta fahimci Nana ba ta yi bacci ba.
"Wai ni Nana, babu wani wanda za ki kira, ki tambaye shi ko yaje? Ko kuma wani guri da za ki je a duba?" Jiki a sanyaye Nana ta girgiza mata kai. "To shikenan sha kunun nan da ƙosai, kar su huce" Nana ta karɓi kunun tana kurɓa a hankali, ji take tamkar tana shan magani, saboda wani irin ɗaci da take ji kunun yake yi mata a bakinta. Amma saboda ba ta son faɗan Uwani, haka ta din ga shan kunun nan da ƙyar. Ta ɗan saci kallon Uwani ta ce "Uwani, ina ga gobe in Allah ya kaimu zan shirya na koma Kano"
"Gurin wa?" Uwani ta jefe ta ta tambayar. Nana ta ɗan yi shiru, Uwani ta ce "Gurin wannan masoron Ubannaki da bai san ciwon kansa ba balle ya san naki? Ya kasa tallafa miki da larura ta samu mijinki, yanzu ne idan kin koma zai tsinana miki wani abu? Ga cikin fari ke ba sanin kan abubuwa ki ka yi ba, ga wannan shu'umar matar tasa, da ƙafa duk dama ba tsayawa za ta yi ta kula da ke ba?. Ban ƙi ba ki kira shi, ki sanar masa abin da yake faruwa a matsayin sa na ubanki ba, amma ba dai ki koma wannan gidan ba. Ki yi zaman ki a nan ki haihu, ki yi biƙinki idan mijin naki bai dawo ba, a san abin yi" Tabbas Uwani tana da gaskiya, idan ta koma gidansu rayuwarta ta sake komawa baya, ta san babu wani abin kirki ko kulawa da za ta samu a gidan, wataƙila ma a kore ta. Ummi kuma ta yi mata ɗawainiya da yawa, tana jin nauyin ta sake koma mata da matsala. Kuma ba ta ji a ranta za ta iya sake ko nufar hanyar gidan Alhaji Zailani ba, saboda yin hakan tamkar cin amanar Sayyid ne, kuma ita ba dolensu ba ce, da za ta je ta ɗora musu ɗawaniya. Dan haka Uwani na da gaskiya. Amma zamanta a nan ɗin ma, shi ma dai ɗawainiyar ce. Ta sake ɗago kai ta ce "To ina son na je Bauchi gurin Mamana"
"Kai Nana ki na da gardama, gurin nawa ne dai ba za ki zauna ba, kin ƙallafa rai tun da mijinki ya bar garin nan kema sai kin bar shi?"
"Ba haka ba ne Uwani, ina da dalili dan Allah ki bani damar hakan"
"Shikenan Nana, ba zan matsa miki ba, Ubangiji Allah ya tabattar da alkhairi, amma ki bari kamar nan da sati ɗaya, ki ɗan ƙara samun nutsuwa. Nima na lalubi na mota na baki"
"Ai ina da kuɗin mota"
"Nima na san ki na da kuɗin motar, na ce zan baki ai" Nana ta ja bakinta ta tsuke.
**** Jamila ta yi shirin fita, tana tsaye tana latsa wayarta ta ce "Baba har ya fita ne?"
Mama ta ce "Tun da uwar kashinsa ta cika ya fita. Da dai bai ci ba da yanzu yana nan yana bin bango yana zabga hamma yana faɗa da ƙadangaru da bokitai"
Jamila ta basar ta ce "Sonake ya bani cikakken kwatancen Buda, zan saka a kai ni, na je na ga Nana"
"Wai ba za ki bar maganar Nanan na ba ko Jamila?"
"Mama meye laifi idan na je na gan ta ne wai?" Ayshacool Nasiru ya ce "Laaa rannan kuwa wannan ɗan uwan mijin nata, da suka zo a ka kaita gidanta ranar biki, suka zo shi da wasu mutane, suka ce mini wai yanzu Nana a ina suke. Na dawo daga makarantar allo, na ce musu tana Buda can garin su Baba, shi ne ya ce na gaida Baba"
Mama ta ce "Ikon Allah, amma yarinyar nan ta ce 'yan uwansa an neme su an rasa. Kai Nana muguwar makira ce ta ƙarshe"
Jamila ta ce "Amm na tafi sai na dawo"
"To Allah ya tsare, a gaida Hajiyar"
" Za ta ji" ta amsa a taƙaice ta fita.
Nana ta zauna ta haɗa kayan da za ta buƙata a cikin jaka guda ɗaya. Tattara sauran guri ɗaya, ta ɗauki jakar gurin Sarkin Baka, da kuɗin Nijar ɗin da suke ciki. Ta tattara sauran kuɗin da suke ɗakinta, tana tunanin ta tafi ko da Uwani ba ta sani ba. Ta tattara kayan kitchen ɗin ta, ta ce wa Uwani sayarwa za ta yi.
"Me yasa za ki sayar da kayan ki Nana?"
"Kawai kuɗin nake buƙata ne"
"Gaskiya ba za ki sayar da kayan nan ba, ki bari ranar kasuwa, zan kai Tinkiyata kasuwa, na baki kuɗin amma ba za a sayar da kayan ba" Gaba ɗaya Nana ta ji ta damu yadda ta ɗorawa Uwani ɗawainiya. "Uwani kar ki sayar da Tinkiyarki dan Allah, gara a sayar... "Za ki rufe mini wannan dogon bakin naki, ko sai na kwaɗe ki? Ke ki ka sani na sayar? Ke dai akwai gardama" Babu yadda Nana ta iya, haka ta haƙura sai ranar kasuwa, aka sayar da Tinkiyar. Uwani ta ɗauki dubu talatin a kuɗin ta bawa Nana ta ce "Ban san iya adadin kuɗin da ki ke buƙata ba, amma ga wannan kya jalauta. Dan Allah ki kula da kan ki Nana, duk inda ki ka je idan kin ga akwai matsala, ki dawo mini nan ni zan riƙe ki na kula da ke" Nana ta din ga juya kuɗin, ta kalli Uwani idonta fal hawaye ta ce "Na gode sosai da sosai, Allah ya saka miki da mafificin Alkhairi na gode"
"Babu komai, Ubangiji Allah ya sauke ki lafiya, ya bayyana mijinki cikin aminci. Nan ma za mu ci gaba da jiran jami'an tsaro ko za a samu wani labari daga gurinsu. Allah ya bayyana shi"
Nana ta amsa da Amin. Jin washegari Nana za ta bar garin, ya sanya 'yan uwa, suka din ga kawo mata abin alheri cikin mutunci da karramawa, tare da yi mata fatan alkhairi.
Washegari da sassafe, Nana ta yi sallama da su Uwani, aka ɗauke ta a babur aka kai ta tashar ƙauyen. Aka kaita Garko, daga nan ta hau motar Kano. A Kano ta hau motar da za ta sada ta da garin Bauchi. Tsawon awanni huɗu da aka shafe, ana tafiya a motar, babu abin da Nana take yi, banda tunani ta saƙa wannan ta kwance wancan. Tunaninta a wani hali yake ciki, ya jikinsa? Su waye suka ɗauke shi? Mene ne makomarta idan bai dawo ba. Lokaci-lokaci ta kan shiga hijjabinta ta yi kuka, ta share hawayenta.
Da ta sauka a tasha ƙarfe sha biyu na rana, ta samu abin hawa, har sunan unguwar da Mamanta take ta sani, sai dai ba ta san takamai ina ne gidan ba. Shi ma daga tashar zuwa garin da maman nata take, sai da aka yi tafiyar awa ɗaya da rabi. Ƙafafun Nana duk sun kumbura, da ƙyar take jan su. Ta ɗaukko wayarta ta kira lambar Anty Fati, ta ji ba ta shiga. Ta kira ta Adda Saude ba ta ɗaga ba. Ta nemi guri ta zauna, ta ci gaba da kiran wayar Adda Saude da ita kaɗai take shiga. Sai dai still ba a ɗaga wayar, ga shi ba ta san daga garin, ina ce unguwar da za ta nufa ba. Ta samu guri ta yi alwala, ta ciro sallaya a kayanta, ta shimfiɗa ta yi sallar azahar. Bayan Azahar sosai, Adda Saude ta kira wayar Nana. Nana ta ɗaga tare da yin sallama. Ta amsa mata ta ce "Nana yi haƙuri, caji na kai wayar ne aka kunna mini, ya ki ke ya gida?"
"Lafiya kalau Adda, kin ganni na zo Bauchi ne na sauka, sai dai ban san sunan unguwar da Mama take ba"
"Ke haba dai, da gaske ki na Bauchi Nana?"
"Eh Adda, na sauka ma tun ɗazu"
"Subhanallah, ai ba ki gaya mini za ki zo ba, da tuni an shirya karɓar ki, ban sani ba an bar ki ki na jira, dan Allah ki yi haƙuri yanzu ki na daidai ina, na zo na tafi da ke?"
Nana ta ce "Kar ki wahalar da kan ki dan Allah, ina garin ma, sunan Unguwar za ki gaya mini" Sai da Adda Saude ta ɗan ji dumm, amma ta maze ta cewa Nana ta samu abin hawa, ta haɗa ta da mai abin hawan ta yi mata kwatance. Ayshacool Nana ta ce "To" ta samu abin hawa, ta haɗa su ta kwatanta masa, sannan ta hau. Nana ba ta isa gidan da Mamanta take ba, sai ana kiraye-kirayen sallar la'asar. Mama na tsakar gida tana ta fama da yara, kawai ta ji sallamar Nana. Ta ɗago da hanzari, sai dai ta kasa amsa sallamar ta nufi Nana da sauri suka rungume juna su na kuka.
Ta ɗago Nana ta ce "Nana ba ki yi fushi da ni ba?"
Nana ta girgiza kai ta ce "Ban yi ba"
Ta ja hannun Nana zuwa ɗaki, ta saka yaran su shigo mata da ƙatuwar jakarta.
"Sannu da zuwa, tare ku ke da mai gidan naki ne?" Nana ta sunkuyar da kai jikinta a sanyaye ta girgiza kai alamar a'a.
"To yana ina shi?" Nana ta yi shiru.
Cikin tashin hankali Mama ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Nana ba dai auren naki ne ya mutu ba?" Nan ma ta girgiza kai hawaye na bin fuskarta.
"Shikenan, yanzu nutsu. Bari na ɗora miki ruwa ki yi wanka, sai ki yi salla" Nana tana iya ganin tsantsar farinciki a kwance a fuskar mahaifiyarta. Ƙannenta suka kewaye ta, Nana ta din ga kallon su cike da so da ƙauna. Har gara Walida ta ɗan santa sauran kuwa duk ba su san Nana ba. Ruwa mai ɗumi ta haɗa wa Nana, ta yi wanka, ta yi sallar la'asar. Ta zubo wa Nana lafiyayyen Abinci, duk da yadda ranta ya biya a kan Abincin, amma ta kasa sakin jiki ta ci. Mama ta din ga kaiwa tana komowa, tana ta ɗawainiya da Nana tamkar ta goya ta, sai ta ji ina ma tuntuni ta samu irin wannan kulawar ta uwa.
"Nana ina Imrana kuwa, ya daina zuwa gaba ɗaya"
Nana ta ce "Lagos yake tafiya neman kuɗi"
Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ai shikenan, ya aka yi ina mijin naki ne? Me ya faru?"
"Nemansa na yi na rasa"
Cikin rashin fahimta ta ce "Kamar yaya?"
Nana tana kuka ta yi mata bayani. Cikin mamaki ta ce "To ina 'yan uwansa? A ina yake a Nijar ɗin?" Sai a lokacin ta fayyace wa Maman komai, game da auren zuwa ɓatan sa.
"Nana, me yasa baki neme ni kin gaya mini ba? Yanzu duk wannan abin yake faruwa amma idan muka yi waya sai ki ce mini komai lafiya ƙalau? Ni kaina nan kina raina, ina ta fafutuka na ga yadda zan yi na zo na gan ki. Ba ki kyauta ba Nana, komai lalacewata, ni mahaifiyarki ce, yakamata a ce kin sanar da ni. Yanzu dai ki zauna a nan, mu ga abin da Allah zai yi, kafin ki haihu mu gani ko Allah zai sanya a ga mijin naki. Amma na yi mamaki matuƙa da mahaifinki ya aura miki wanda bai san usulinsa ba? Yanzu ƙiyayyar da yake yi minin har ta kai haka? Ko yana jin haushina amma ai ke 'yar sa ce, bai cancanci ya yi miki haka ba, amma babu komai. Nana abin da nake so da ke, daga yanzu duk abin da ya faru Nana, ko ba zan yi miki komai ba, ki sanar da ni, ki bani dama na taka rawa ta ta uwa a rayuwar ki ko yaya ne" Ta yi maganar tana riƙe hannun Nana.
Sallamarsa ce ta tilastawa Nana haɗiye abin da take shirin furtawa, cike da tsoro. Ba ita ba hatta Maijidda, sai da zuciyarta ta buga da ƙarfi cike da tsoro.
AYSHERCOOL 08081012143 Ayshacool Nana ta ce "To" ta samu abin hawa, ta haɗa su ta kwatanta masa, sannan ta hau. Nana ba ta isa gidan da Mamanta take ba, sai ana kiraye-kirayen sallar la'asar. Mama na tsakar gida tana ta fama da yara, kawai ta ji sallamar Nana. Ta ɗago da hanzari, sai dai ta kasa amsa sallamar ta nufi Nana da sauri suka rungume juna su na kuka.
Ta ɗago Nana ta ce "Nana ba ki yi fushi da ni ba?"
Nana ta girgiza kai ta ce "Ban yi ba"
Ta ja hannun Nana zuwa ɗaki, ta saka yaran su shigo mata da ƙatuwar jakarta.
"Sannu da zuwa, tare ku ke da mai gidan naki ne?" Nana ta sunkuyar da kai jikinta a sanyaye ta girgiza kai alamar a'a.
"To yana ina shi?" Nana ta yi shiru.
Cikin tashin hankali Mama ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Nana ba dai auren naki ne ya mutu ba?" Nan ma ta girgiza kai hawaye na bin fuskarta.
"Shikenan, yanzu nutsu. Bari na ɗora miki ruwa ki yi wanka, sai ki yi salla" Nana tana iya ganin tsantsar farinciki a kwance a fuskar mahaifiyarta. Ƙannenta suka kewaye ta, Nana ta din ga kallon su cike da so da ƙauna. Har gara Walida ta ɗan santa sauran kuwa duk ba su san Nana ba. Ruwa mai ɗumi ta haɗa wa Nana, ta yi wanka, ta yi sallar la'asar. Ta zubo wa Nana lafiyayyen Abinci, duk da yadda ranta ya biya a kan Abincin, amma ta kasa sakin jiki ta ci. Mama ta din ga kaiwa tana komowa, tana ta ɗawainiya da Nana tamkar ta goya ta, sai ta ji ina ma tuntuni ta samu irin wannan kulawar ta uwa.
"Nana ina Imrana kuwa, ya daina zuwa gaba ɗaya"
Nana ta ce "Lagos yake tafiya neman kuɗi"
Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ai shikenan, ya aka yi ina mijin naki ne? Me ya faru?"
"Nemansa na yi na rasa"
Cikin rashin fahimta ta ce "Kamar yaya?"
Nana tana kuka ta yi mata bayani. Cikin mamaki ta ce "To ina 'yan uwansa? A ina yake a Nijar ɗin?" Sai a lokacin ta fayyace wa Maman komai, game da auren zuwa ɓatan sa.
"Nana, me yasa baki neme ni kin gaya mini ba? Yanzu duk wannan abin yake faruwa amma idan muka yi waya sai ki ce mini komai lafiya ƙalau? Ni kaina nan kina raina, ina ta fafutuka na ga yadda zan yi na zo na gan ki. Ba ki kyauta ba Nana, komai lalacewata, ni mahaifiyarki ce, yakamata a ce kin sanar da ni. Yanzu dai ki zauna a nan, mu ga abin da Allah zai yi, kafin ki haihu mu gani ko Allah zai sanya a ga mijin naki. Amma na yi mamaki matuƙa da mahaifinki ya aura miki wanda bai san usulinsa ba? Yanzu ƙiyayyar da yake yi minin har ta kai haka? Ko yana jin haushina amma ai ke 'yar sa ce, bai cancanci ya yi miki haka ba, amma babu komai. Nana abin da nake so da ke, daga yanzu duk abin da ya faru Nana, ko ba zan yi miki komai ba, ki sanar da ni, ki bani dama na taka rawa ta ta uwa a rayuwar ki ko yaya ne" Ta yi maganar tana riƙe hannun Nana.
Sallamarsa ce ta tilastawa Nana haɗiye abin da take shirin furtawa, cike da tsoro. Ba ita ba hatta Maijidda, sai da zuciyarta ta buga da ƙarfi cike da tsoro.
AYSHERCOOL 08081012143 Har zai gifta, zai shiga ɗaki ya hango Nana, cikin rawar baki, Nana ta gaishe shi, ya amsa mata sama-sama ya wuce, dan kallo ɗaya ya yi mata, ya gane ta.
Jiki a sanyaye Maijidda ta tashi ta bi shi ɗaki, tana ɗan sinne kai, tana jiran ta ji me zai ce, amma bai ce komai ba. Ta kawo masa Abinci, tana jiran ta ji me zai ce, ga hankalinta a kan Nana, tana so ta je ta yi hira da 'yar ta, su yi hira ta ji ɗuminta, amma ta haƙura. Nana ma na ta gaban ne yake faɗuwa, tana tsoron abin da zai ce, saboda ba ta manta karan battarsu. Haka dai a ɗarare suke hira da yaran gidan. Maijidda na ta son yi masa magana, amma ta kasa. Ya gama cin abincin ya fita, ba tare da ya ce komai ba. Yana fita ta koma gurin Nana, suka ci gaba da hira, Nana ta kwanta a kan cinyar Mamanta, tana jin wani irin farinciki yana ratsa ta.
"Kin fara zuwa awo ne Nana?"
Wata irin kunya ta kama Nana, ta ɗan sinne kai ta girgiza mata kai. "Gaskiya yakamata, wata nawa ne cikin? Mu je a yi awo a duba, mu ga abin da zamu fara ajiyewa. Mu jira mu ga ikon Allah, idan an ga mijin naki shikenan, idan ba a gan shi ba kuma, ma san abin yi" Nana dai ta yi shiru, sai kuma ta ce "Mama ki yi mini addu'a, ki ce Allah ya bayyana shi cikin aminci"
Mama ta yi dariya, ta ce "Lallai kam, to shikenan, Ubangiji Allah ya bayyana mini sirikina cikin aminci"
Nana ta yi murmushi, dan kunya ce ta kama ta daga baya, da tuna katoɓarar da ta yi.
Da daddare Mai Jidda ta yi wa Nana shimfiɗa, ta saka nata net. Sannan ta tafi nata ɗakin gurin mijinta, har za su kwanta, Mai Jidda ta dubi Iliyasu, jiki a sanyaye cikin ladabi ta ce "Baban Walida, na ga ka dawo ka ga Nana a gidan nan, ba ka ce komai ba"
Ya dube ta ya ce "To me ki ke so na ce?"
"Ahh dama kar ka ce ban gaya maka ba ne, dama ta ɗan zo ta zauna da ni ne, duba da yadda...
"Kin ga dakata, na ɗaga miki ƙafa ne na yi shiru, na ga gudun ruwanki, kar ta wuce mini gobe a gida, ta wuce ta koma inda ta fito"
"Dan Allah ka yi haƙuri Baban Walida, Nana ta samu matsala a aurenta ne, dan Allah ka yi haƙuri ba za ta daɗe ba, amma dan Allah kar ka ce ta tafi yanzu. Ni ko ruwan gidanka ka ce ba za ta sha ba, na amince dan Allah"
"Ke Maijidda, bari ki ji na gaya miki, wallahi sai yarinyar nan ta bar gidan nan" Ya nemi guri ya yi kwanciyar sa, takaici ya ishi Maijidda. Nana kuwa tana jiyo hayaniyar su sama-sama, abin ya tsaye mata ta kasa bacci sam. Sai juye-juye, ga mararta ta ƙulle duk jikinta ma ciwo yake yi mata.
Kwance yake a kan gadon Asibiti, jikinsa babu riga, sai dogon wando an rufe iya ƙafafuwansa da koren yadi. Ƙirjinsa kuma an manna masa abin ECG. Sai gashin sa a rufe da hular Asibiti. Na'urorin gefen gadonsa sai sauti suke fitarwa. Dattijo ne a tsaye a kansa, dogo fari tas, ya ɗaura hirami a iya kansa, ga gemunsa dogo duk farin gashin furfura a jiki. Ya kalli mutumin da yake tsaye ya ce "médecin (Likita) yanzu mene ne abin yi?"