Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 42
Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 42: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 42. "Eh, gaskiya za a yi masa wannan allurar ne kamar yadda na yi maka…
3,368 words
"Eh, gaskiya za a yi masa wannan allurar ne kamar yadda na yi maka bayani, idan kuma ba haka ba, gaskiya sai dai a saka masa na'ura a zuciyarsa wadda za ta din ga taimakawa bugun zuciyarsa"
Na kusa da Dattijon mai sanye da shuɗiyar shadda, da babbar riga, kansa ya yi naɗi da baƙin rawani ya ce "Ka gani ko Sultan, Allah kaɗai ya san abin da suka yi masa a Nigeria. Dole yaron nan ya ɗanɗana kuɗarsa a ci gaba da tsare shi, har sai ya yi bayanin abin da ya yi masa a Nigeria, da aka neme shi aka rasa tsawon wannan lokacin. Su kan su sauran da aka kama su tare, dole a killace su a guri ɗaya, haryanzu ban bari an sake su ba, saboda idan maganar nan ta fasu akwai matsala" Sultan ya numfasa cikin damuwa ya ce "Ni wannan bai dame ni ba, na bar ragamar komai a hannunka, ni lafiyar sa ce a gabana yanzu. Likita ku yi duk abin da ya dace kawai. Lafiyarsa ce damuwata a halin yanzu"
Likitan ya ce "In sha Allah" Dattijon ya saka hannunsa a cikin na mara lafiyan,yana kallonsa cikin matsananciyar damuwa. Kamar mafarki ya ga yana motsawa a hankali, sai ya ƙara tattara hankalinsa a kansa yana kiran sunansa. Wata irin miƙa ya yi, yana ƙoƙarin buɗe idanunsa, amma ya ji tamkar an cika masa idanun nasa da barkono. "Imam.. Hannunsa ya ɗora a ka yayi wata irin kururuwa, jin yadda naman jikinsa yake yi masa wata irin azaba, tamkar ana cizgar naman jikin nasa. Ga wani irin zafi da raɗaɗi da yake ji kamar yana cikin wuta.
"Zafi! Wayyo wuta Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wuta zafi jikina"
Kansa suka yi gaba ɗaya cikin tashin hankali, su na ƙoƙarin rirriƙe shi, amma ya watsar da su ya diro daga kan gadon, yana girgiza kansa da yake yi masa wata irin azaba tamkar zai tarwatse. Tunaninsa ne ya hargitse gaba ɗaya, ƙwaƙwalwarsa na ta kokawar ƙwato wani abu daga cikin memories ɗin sa, amma abu ya kacame, gaba ɗaya tunaninsa ya hargitse, ya kasa tantance komai. Fizge-fizge ya din ga yi yana kururuwa jikinsa na rawa. Dattijon nan cikin jarumta da ƙarfin hali, ya bi shi da sauri ya damƙe shi iya ƙarfinsa. Kokawa suka din ga yi, a rikice likita da ɗaya mutumin suka yo kansu, likitan ya haɗa wata allura ya yi masa. Jikinsa ya saki a hankali bacci ya ɗauke shi. Kan gadon suka mayar da shi suka kwantar. Ɗaya mutumin ya kalli likitan ya ce "Ka na ji na?" Likitan ya jinjina kai cikin nutsuwa. "Ka san dai waye wannan, kuma ka san matsayinsa da girmansa ko?" Ya yi maganar yana nuna masa mara lafiyan.
Ya jinjina kai ya ce "Na sani"
"To muddin mu ka ji maganar abin nan da ya yi, ya fita waje, to ba wani ba ne ba kai ne, dole ka yi shiru da bakinka, kare sirrinsa wajibi ne a kan duk wani wanda yake yankin nan, idan kuma aka samu akasi ka furta wani abu, da rayuwarka za ka biya"
Likitan yana tsuma ya ce "In sha Allah ba zan faɗa ba"
Da safe mijin Maijidda ya shura takalmansa ya fice, bayan sun gama jayayya da ita, tana ta roƙonsa tana yi masa magiya. Gaba ɗaya Nana ta ji dana sanin zuwa Bauchi da ta yi. Babban abin da ya bata mamaki, ƙatuwar kaza Maman ta saka aka yanka, ta gyare ta tsaf, ta yi wa Nana farfesunta, aka sayo mata ƙaton buredi ta haɗa mata shayi.
"Mama daga zuwana na ɗora miki ɗawainiya, ba ma na iya cin Abincin ni"
"Ɗawainiyar ƙaniyarki, da can na yi miki ne Nana? Dan Allah ki daure ki mayar da hankali ki ci ki ƙoshi, idan kuma ki na son cin wani abin, ki gaya mini sai na dafa miki"
"A'a ba na son cin komai, amma ki zo mu ci tare da su Walida"
Maijidda ta ce "A'a, babu wanda zai ci, da rana ma ci Abincin tare, wannan dai na ki ne" Haka ta takura Nana, ta karya.
Nana ta fito da nufin, ta kama musu ayyukan gida, amma Mama ta hana, ta dafa mata ruwa ta yi wanka. Ta fito ta tarar Mama tana wanke kayan da ta cire.
"Haba Mama dan Allah ki bari na wanke da kaina, ya za ki din ga yi mini wanki?"
"Tafi ɗaki ki je ki zauna ki huta, ga lemon fata can da rake, ki ɗan sha saboda ɗanɗanon bakinki. Akwai riɗi ma mai gishiri da mai suga, idan da wanda ki ke so" kawai Nana ta tsaya tana kallon ta, tana murmushi.
Maijidda ta ce "Ya dai?"
Ta girgiza kai ta ce "Ba komai Mama, na gode sosai"
Nana ta shirya ta canza kaya, Khadija da take 'yar autar Mama, Nana ta kama ta tana tsefe mata kai. Ta ɗauki wayar Nana tana kallon hotuna. Sai ta buɗe wani video da Nana ta yi wa Sayyid, ta yi masa kitso sai hararta yake yi tana cewa "Ka ga yadda ka yi kyau 'yan matana, yi murmushi mana" ya ɗago kansa ya hargitse idanunsa. Nana tana dariya. Sai da tsigar jikin Nana ta tashi, gani take kamar ta shiga cikin wayar ta ga Sayyid ɗin ta.
"Anty Waye wannan?"
"Mijina ne" ta ba ta amsa tana murmushi.
"Ya na gan shi da kitso, kuma fari?"
Nana ta yi dariya ta ce "Ni kuma baƙa ko?"
"Eh, kuma ba kyau maza su yi kitso fa"
"Wai in ji wa? Ba ki ga gashin nasa ne da yawa ba?"
Khadijah ta ce "Eh, to yana ina yanzu?"
"Ya je unguwa, zai dawo ya ɗauke ni mu tafi"
"To ki nuna mini shi idan ya zo" Nana ta ce "To in sha Allah"
Mama ta ce "Ke Khadijah, tashi ki bar ta ta huta, Nana kwanta ki huta, ki rabu da surutun yarinyar nan"
Khadijah ta tashi tana zumɓura baki, Nana ta ɗan kashingiɗa kawai wani abu mai kama da bacci ya yi awon gaba da ita, kasa tantance ma me take yi ta yi, bacci ne ko kuma ido biyu.
"Ma Vie" ta ji muryarsa a kunnenta. A razane ta waiwaya cikin damuwa. A tsakiyar sahara ta hange shi ta ce "Sayyid" Ganinsa ta yi a tsaye a kanta, kayan jikinsa duk a yayyage, ya yi baƙi kamar ya ƙone, gashin kansa a hargitse jikinsa sai fitar da hayaƙi yake, ya ce "Ma Vie sun mayar da ni inda za su kashe ni, dan Allah ki zo kar su kashe miki ni." Yayi maganar yana hawaye.
Ta tashi cikin tashin hankali ta ce "Suwaye? Kuma a ina suke?"
"Dan Allah ki zo, ni ban san su ba, amma na san mutuwa zan yi, dan Allah Husnah ki zo gurina, za su kashe ni. Idan kuma sun kashe ni, ki kular mini da ɗa na"
"Sayyid, dan Allah kar ka tafi ka bar ni, dan Allah Sayyid ka dawo? Ka gaya mini kana ina, sai na zo na same ka na tafi da kai" Guguwar Sahara ce, ta taso ta turnuƙe gurin. Nana ta din ga tari, muryar Mama ta ji a kanta tana faɗin "Tari ki ke haka Nana?" Kawai ta ga Nana ta tashi, ta yi waje. Ta riƙe ta ta ce "Ina za ki ke?"
Idanunta a rufe, fuskarta a murtuke ta ce "Ba ki ji Sayyid ne yake kirana ba?"
"Waye hakan?"
"Mijina mana" ta faɗa a fusace.
"A'a babu wanda ya kira ki fa"
Nana ta fara ƙoƙarin fizge hannunta ta ce "Yanzun nan fa ya fita daga ɗakin nan" "Nana babu kowa fa a gurin nan, daga mu sai ke"
"Ni ki cika ni, na ji Muryar mijina gurinsa zan je yana kirana"
Tsawa ta daka wa Nana ta ce "Ina magana ki na ɗaga mini murya? Wuce ki zauna babu wani wanda yake kiran ki" Nana ta buɗe idanunta, ta kalli Mamanta, sai dai ba ta yi magana ba, kawai ta ga Nana ta yi baya za ta faɗi. Ta riƙe ta ta kwantar da ita. Jikin Nana ya hau karkarwa, idanunta na fitar da hawaye. Cikin matsananciyar damuwa take kallon Nana, tana tunanin dama har zuwa yanzu, tana fama da larurar nan?.
Ta rungume Nana a jikinta, ta kama goshinta, ta fara karanta mata Suratul Jinn, tana tofa mata a fuskarta. A hankali jikin Nana ya saki ta fara bacci. Ta yi shiru tana kallon fuskar Nana, tana tuna lokacin da take rungume da ita tana jaririya, cike da so da ƙauna. Tare da tuno irin soyayya da rawar ƙafar da Isa ya din ga yi lokacin da aka haifi Nana, ba ta taɓa tunanin zai yi wannan riƙon sakainar kashin da rayuwar Nana ba.
Adda Saude ce ta yi sallama, Mama ta amsa mata.
Ta ɗan yi turus ta ce "Ya dai Nanan ba ta da lafiya ne, na ganta a kwance a jikinki haka?"
"Wallahi kuwa, shigo daga ciki" ta zauna ta ajiye kayan da ta zo da su. Ta ce "Tun jiya na so zuwa, tun da muka yi waya da ita da ta ce mini tana garin nan, babansu ne baya nan bai dawo da wuri ba ga yara gidan babu kowa. Ikon Allah ciki ne ma da ita haka?"
"Ga shi nan dai, har ya yi girma ma"
"Ikon Allah, na yi mamaki da na ji zuwa ta yi babu sanarwa, tare da mijin suka zo?"
Maijidda ta numfasa ta ce "A'a, matsala ma aka samu, ba a san inda mijin nata yake ba"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, garin yaya ina ya tafi?"
"Wallahi ban sani ba, na dai ce ta zauna a nan, kafin nu ga abin da Allah zai yi. Ashe rashin lafiya ya sha, yarinyar nan ba ta taɓa gaya mini ba. Ga babanta bai karɓe ta ba, ƙarshe ma sai Buda ta koma ta yi jinyarsa, kuma dai ma ya tafi ba a san inda yake ba"
Cikin jimami Saude ta ce "Kai subhanallah, abin nan bai yi daɗi ba, yanzu meya same ta haka?"
"Iska ne ya buge ta, na ba ta abinci ta karya, ta fara bacci kawai ta tashi wai mijin ne yake kiranta. Ashe haryanzu tana fama da wannan matsalar. Wallahi Adda na yi dana sanin biye wa Iliyasu na watsar da yaran nan." Ta yi maganar hawaye na cika mata ido.
"Ki yi haƙuri, amma yanzu ya ku ka yi da shi?"
"Hmm mu na nan muna ta bugawa, wai sai ta bar gidan nan, ni kuma Nana ba za ta bar gidan nan ba, sai dai mu tafi tare"
A ɗan tsorace Adda ta ce "A'a Maijidda, idan da matsala, a kaita gidan Fati tun da tana da yalwar guri, ko gurin Yakumbo,kar ku samu matsala"
Ta girgiza kai ta ce "Ni na ke son kula da Nana da kaina. A cikin su ban san wanda zai ji ƙan wani ba, dukkaninsu su na buƙatata".
Nana ta farka tana ɗan yin miƙa, ta cewa Maijidda fitsari za ta yi, ta raka Nana banɗaki ta je ta yi fitsari, ta saka ta ta yi alwala ta koma ta kwanta.
Har zuwa yamma Adda na gidan, sai daf da magariba ta tafi, Nana kuma ta wartsake sai ciwon jiki da mararta da ke ɗan murɗawa. "Nana, ranar Litinin in sha Allah za mu je Asibiti, a fara yi miki awo, kuma zan duba gurin masu magungunan islamic ɗin nan, mu je a duba ki" Nana dai ta yi shiru ba ta ce komai ba.
Da sallar Isha'i, Baban su Walida ya dawo, tun da ya hangi Nana a ɗaki, ya turnuƙe fuska ya kalli Mai Jidda ya ce "Me na ce miki a game da yarinyar nan?"
"Baban Walida, ba a yi wa ɗa mugunta, dan Allah ka yi haƙuri ka bar Nana a gidan nan, ka ga 'yan uwanta ma duk ba su santa ba, ba su saba ba. Kuma ba a san me gobe za ta haifar ba. Wataƙila ita ce mai tallafar rayuwar ƙannen nata nan gaba."
"Ni ba nusari ne kamar ubanta ba, ni zan tallafi rayuwar 'ya'yana. Ba na buƙatar ko sisinta a kan yarana. Ta koma gidan mijinta ko gidan ubanta, idan ba haka ba sai dai ki zaɓa, ko ta bar mini gida, ko kuma auren ki."
Kafin ya rufe bakinsa ta tari numfashinsa ta ce "Na zaɓi 'ya ta, zan tafi tare da Nana, ko a daji ne na rayu da ita na kula da ita. Tun da ba dan wahala da bautarka da ta 'ya'yanka kawai Allah ya yi ni ba. Ba ka da kara Iliyasu. Nan har 'ya na riƙe maka na aurar da ita ban yi mata mugunta ba. Har 'ya'yan 'yan uwanka ka kawo mini na riƙe, ban taɓa muzguna musu ba, na riƙe maka, nawa 'ya'yan ne na banza kenan? Ƙiri-ƙiri ɗan da na durƙusa na haifa ya tsane ni, saboda yana ganin na kawo su Duniya amma ban damu da su ba. Su 'ya'yan da na riƙe maka haifar su na yi? Ko kuma dolena ne su, ni 'yar guda ɗaya ka gaza yi mini kara a kanta? To ka sani duka yau duka gobe shi ke sanya baƙin ba'auzine yin tawaye. Zan zube maka yaranka na ɗauki 'ya ta na tafi da ita, na kula da ita. Ka kwaɗa gidan ka cinye da kai da 'ya'yan naka"
Cikin matsanancin mamaki ya ce "Maijidda, ni ki ke gaya wa wannan maganganun?" Cikin ƙunar rai ta ce "Na faɗa ɗin, shekara nawa na rayu da baƙin cikin rashin ganin 'ya'yana, kullum na motsa zargina ka ke da tsohon mijina. Ƙaddarar haihuwar yaran nan biyu ta sanya ban aure ka da fari ba na fara auren sa, amma a kan dalilinku marasa tushe balle makama kun azabtar da ni da nesan ta ni da yarana. Wallahi wannan karon na zaɓi 'ya ta"
Kamar zubar wuta, haka Nana take jiyo cece kucen su. Dana sanin zuwa gidan ya cika mata zuciya. Tabbas ba za ta so mahaifiyarta ta kashe aurenta, da wannan gayyar 'ya'yan saboda ita kaɗai ba, idan ta bari hakan ya faru ba ta yi musu adalci ba baki ɗaya. Zurfin tunanin da ta tafi, bai bari ta gama jin yadda rigimar ta su ta kaya ba. A cikin daren bayan gari ya yi tsit, ta tashi ta haɗa kan kayanta cif. Ta laluba jakunkunan yaran na makarantar boko, ta samu biro da takarda ta yi rubutu, ta ninke ta ajiye a kan katifar ta. Da Asuba, Mama ta zo ta tashe ta, ta yi alawala ta yi sallar Asuba. Ganin yaran na ɗaya ɗakin su na salla, Mama ma tana bedroom ɗinta, tana salla, ya sanya ta lallaɓa ta ɗauki jakarta ta fice daga gidan. Ta din ga zumbuɗa sauri, tamkar za ta tashi sama, ga faggon kaya. Tafiyar ƙafa ta ci sosai da sosai, har sai da gari ya yi haske, masu abin hawa suka fara fitowa, ta tari wani ta ce ya kai ta tasha. Yana kai ta tasha, ta yi sa'a an yi lodi saura gurin mutum biyu, tare da wata mata suka shiga tasha suka nufi babbar tashar Bauchi. Daga babbar tashar Bauchi, ta hau wata motar, duk da zuciyarta na raya mata kamar matakin da ta ɗauka ya yi tsauri, wata zuciyar kuma na raya mata shi ne mataki mafi cancanta da za ta ɗauka, mussaman idan ta tuna yanayin yadda ta yi mafarkin Sayyid. Wayarta ta ciro, ta shiga lambar Ummi, ta rubuta mata saƙo, sai da ta tabattar ya tafi, sannan ta kashe wayar, ta cire layinta daga cikin wayar.
Gari ya ɗan fara haske, Baban su Walida ya fice, a matuƙar zuciye, ya yanke shawarar tafiya ya kai ƙarar ta, tun da dama ya san ya saba samun goyon baya, ba ga taɓa kai ƙararsa ba, amma shi ya kai ta ta, ya fi sau shurin masaƙi. Su Khadija har sun fara ƙiriniya a tsakar gida, a zuciye kasancewar da takaicin ubansu ta kwana ta daka musu tsawa, ta ce su koma ɗaki, kar su tashi Nana. A zaton ta Nana tana cikin ɗaki tana bacci.
Jamila ce zaune a gidan Ummi, tana jajanta abubuwan da suka faru da Nana, ba tare da ta san ma hakan ya faru ba. "Wallahi Ummi da an sanar da ni zancen matar nan, da suka ce Nana mayya ce, wallahi da sai na saka an rufe ta, sai na ja shari'a da su har gaban Alƙali, sun san girman sharrin maita kuwa?"
"Hmm ke dai a yi sha'ani, ga shi Nana ta bar gidan, amma an ce Haryanzu tana kwance babu lafiya matar, ni na fi tunanin ko Aljanun Nanan ne suka yi mata wani abin, tun da ta ce Nana take gani. Jamila wayar Nana fa ba ta shiga, ni kaina sai na shafe sati biyu ban yi magana da ita ba, saboda garin babu network. Haka nan za mu tafi kawai."
Ummi ta shirya, da Jamila Abba ta so ya kai su, sai ta yi wani tunani ta fasa, dan ba ta san a yanayin da za su je su tarar da su Nana ba. Sai dai Ummi ta sha mamaki da suka isa garin, suka tarar da gidan Nana a garƙame. "Ikon Allah, ita kuwa Nana ina tafi haka? Ko sun je Asibiti ne?"
Jamila ta ce "Asibiti yau Asabar?"
"To maybe emergency suka je, kin san matsalar Zuciya yake fama. Mu ƙarasa gidan Uwani".
Suka zagaya gurin Uwani, ta yi murna sosai da sosai da ganinsu, sai dai ta hau Jamila da faɗan ba sa zuwa sai yanzu, da yake Nana ce a garin. Ummi ta yi ta bata haƙuri, ta ce sun zo duba Nana ne, sun tarar da gidan a rufe.
"Ohh abin tsiya, ba ma kwa bibiyar halin da take ciki, to Nana tun shekranjiya ta bar Buda, mijinta aka nema aka rasa ko sama ko ƙasa sama da sati biyu, ta ce mini gurin Babarta za ta tafi a Bauchi, babu yadda ban yi da ita mu yi zamanmu da ita a nan, amma fafur ta ce in ƙyale ta, tafiya za ta yi".
Jamila ta ce "Danƙari"
Ummi kuwa "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" kawai take maimaitawa.
"Amma me yasa Nana ba ta dawo gida ba, sai ta tafi Bauchi, bayan ta san halin Baba"
"Baban wofi, uban me zai tsinana mata, ko ta je gurin nasa"
Suka gama jimamin da za su yi, suka tashi suka tafi.
Jamila ta ce "Anya Ummi mu gaya wa Baba kuwa?"
Ummi ta ce "Tun da shi ya haife mu, ba dole a gaya masa ba. Wallahi duk cikinmu babu wanda ya sha azabar ds Nana take sha a rayuwarta, da kin ga yadda take shan wahala da mutumin nan, sai kin tausaya mata, gaskiya idan guduwa ya yi ya bar ta, bai yi wa kansa adalci ba."
Suka ci gaba da jajanta lamarin.
Da suka shigo gari, Jamila ta tafi gida, Ummi ma ta tafi nata gidan.
Mama na ganin Jamila ta dawo, ta fara yi mata tambayoyi, amma Jamila ta yi burus, ba ta gaya wa Mama komai ba.
Tare da Kawun Mai jidda Iliyasu ya dawo, yana ta faman bambamin ta lalace, abin da ta ga dama shi take aikatawa. Sai kuma Adda Saude da suka taho tare, dama sai da ta yi tunanin a samu matsala saboda zuwan Nana.
Suka tarar da Maijidda idanunta jawur, fuskarta babu annuri. Suka zazzauna a falonta, kawunta ya dube ta ya ce "Mai Jidda ban san ki da rashin ji ba, me yake faruwa ne?"
Jiki a sanyaye ta miƙa masa takardar da Nana ta bari a kan shimfiɗarta.
"Wannan ɗin na mene ne?"
"Ku duba" ta yi maganar hawaye na zubo wa daga idonta.
Adda Saude ta karɓa, ta buɗe takardar "Assalamu alaikum, na san lokacin da za ki ga takardata, na riga na yi nisa. Mama ina mai baki haƙuri da matakin da na ɗauka ban sanar da ke ba. Ba zan so a dadlilina nikaɗai ki bar ƙannena ba, dan Allah Mama ki yi haƙuri ki zauna da su. Na tafi neman mijina, a bawa baban su Walida haƙuri, amma kwana biyun nan da muka yi tare, ya fi kowane kwanaki yi mini daɗi a rayuwata na gode sosai Nana Asma'u"