Kenza eBookz

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 44

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 44

Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 44: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 44. A tsakar gida suka tarar da matar, ta cake ɗauri tana ta lissafin kuɗi.…

3,360 words

A tsakar gida suka tarar da matar, ta cake ɗauri tana ta lissafin kuɗi. Ta amsa musu sallamar tana yi musu maraba. Suka shiga ɗaya daga cikin ɗakunanta. Ta kawo musu ruwa da lemo ta ajiye. Cikin girmamawa Nana ta gaida matar.

Ta kalli mijin Hajara ta ce "Wannan ce yarinyar?"

Ya ce "Eh Nene"

"To a haka dai ta yi zubin nutsuwa, dan dai ka matsa ne, amma ni ba na son yayime-yayime na je na ɗaukko wadda za ta hana ni sukuni, shi yasa duk girman gidan nake zamana nikaɗai abina. Sannan zan fara zama da ita na wata ɗaya, idan ba ta da matsala mu ci gaba da zama, idan akwai matsala na mayar mata da kuɗinta ta tashi ta bani guri. Kuma wallahi dan ma dai kai ne, da ba zan yadda ba".

Nana cikin girmamawa ta ce "In sha Allah ba za ki same ni da matsala ba, in Allah ya yarda".

Nene ta ce "To Allah ya sa, bari na buɗe ɗaya daga cikin ɗakunan ta zaɓa"

Mijin Hajara ya ce "Ɗakunan a rufe, ai na san sun sha ƙura yanzu, ki yi haƙuri tun da akwai gyararru ki kwashe kayanki daga ɗaya ki ba ta. Kin ga ɗakin da ba komai, sai an nemi labule, da sauran abubuwa". Haka ya takure Nene, ta bawa ɗaki ɗaya, mai ɗauke da labulaye da carfet. Nana ta din ga godiya, ta ce "Saura kuɗin hayar, nawa ne zan biya?"

"Ai na biya ta, ba wani abu in sha Allah, ki zauna kawai"

Nana ta ce "Ai da kuɗi a gurina"

Hajara ta ce "Kar ki damu, ba wani abu ya biya, idan akwai wata matsala ko ba za ki iya zama ba, ki ce Nene ta kira mu a waya, in sha Allah babu wani abu"

Nana sai da ta yi hawayen murna, ta raka su har waje sannan ta dawo. Ta tarar da Nene ta fito da wake fal za ta tsince. Nana ta lallaɓa ta zauna a kan tabarmar ta ce "Kawo na tsince miki"

Nene ta ce "A'a ke da ki ke baƙuwa, yi zaman ki ki huta, kan Auwwalu ya dawo ya ce ina azabtar da ke, tun da ya ce ni masifaffiya ce". Ita Nana har ta gama zaman gidan ma, ba ta san sunansa ba. Ta yi murmushi ta ce "A'a ba komai, dan Allah ki bani na taya ki, ai na ga waken da yawa, kuma daga zaune zan taya ki" Ta dawo da robar waken tsakiyar su, ta kalli Nana ta ce "Nana ko?"

Nana ta jinjina kai ta ce "Eh"

"Ciki ne da ke haka ne?" Nana ta sunkuyar da kai tana tsince wake.

"Ke kuwa me ya yi miki zafi, ki ka baro ƙasar ku da wannan tsohon ciki ki ka taho inda ba ki da kowa? Amma fa ki yi haƙuri da tambayoyina, kin san yanzu duniya babu gaskiya sosai"

Nana ta ce "Haka ne. Mijina ɗan ƙasar nan ne, nice 'yar Nigeria. Na zo neman danginsa ne a nan"

"Allah sarki, to a ina dangin nasa suke? Kuma shi yana ina" Nana ba ta son yayata halin da take ciki, ta fi son sai ta nutsu, ta ga kamun ludayin mutanen ƙasar tukuna, kafin ta saki jiki, amma ga Nene ta saka ta a gaba da tambayoyi. Kafin ta ba ta amsa, Allah ya taimake ta, aka kira Nene a waya, hakan ya sanya ba su ci gaba da zancen ba.

Cikin tsananin tausayawa, yake bin matashin da kallo, saboda yadda duk ya fita daga hayyacinsa. Cikin damuwa ya kira sunansa a hankali ya ce "Mahmudu" ya ɗago idanunsa a galabaice, ya kalli wanda ya kira sunan nasa. "Ka yi musu bayanin duk abin da ya faru, ka faɗa musu iya gaskiyarka, ko Allah ya sanya su rabu da kai, wannan wahalar da ka ke yi ta isa haka?" Murya a cunkushe ya ce "Me zan gaya musu? Me zan ce da ka ke tunanin idan na faɗa za su yarda da ni?"

"Iya abin da ka sani ɗin zaka faɗa"

"A tunaninka tsawon wannan lokacin, ba iya abin da na sani ɗin ba nake gaya musu? Sai dai akwai abin da ko za a kashe ni, ba zan furta ba" "A'a Mahmudu, idan har za ka ci gaba da shiru da ɓoye wasu abubuwan, ba fa za a ƙyale ka ba, za su ci gaba da azabtar da kai ne kawai a banza. Ni dai zan faɗi abin da na sani"

Mahmudu ya ce "Ka kwana da sanin, ka na furta wani abu, to tabbas kai ma za ka tsinci kanka, a halin da nake ciki yanzu. Ka yi shiru mu bar komai a yadda yake. Rufe sirrin Imam wajibi ne, akwai abin da idan na furta, zai iya janyo asarar rayuka ba ɗaya ba ba biyu ba, in dai wahala ce na san ɗayan biyu ne, ko na mutu ko ta wuce. Abu ɗaya nake so da kai, shi ne; dan Allah Ashiru, ka binciko a wani hali yake ciki? Tun da muka baro Nigeria, ba a haɗa mu a mota ɗaya ba ma, ban san ina aka yi da shi ba" Ashiru ya ce "Kai wannan fa babban aiki ne, tun ɓatansa fa, ba a bari labarin ma ya fita ba, balle a sanya ran jin halin da ake ciki yanzu, amma dai zai ɗan ƙyanƙyasa a ɓoye, na ga ko za a samu wani bayani. Sannan ina ƙara neman afuwarka a kan abin da ya faru"

"Babu komai kar ka damu, an saki sauran ko? Su Sulei"

"Eh an sake su, ai tun da suka fuskanci, ba su ma san a kan me ake binciken ba, an sake su amma fa an killace su"

"Shikenan tashi ka je, kar a fahimci wani abu" Haka Ashiru ya tashi ya tafi yana waiwayen sa.

*

Sannu a hankali take tafiya, yana zaune a cikin mota yana hangen ta, ta tsallako titi, ta nufo motarsa tana murmushi. Ta buɗe motar ta shiga ta ce "Yaya Abba me ka ke jira a titin ne haka?"

Ya lumshe idanunsa, jin yadda ƙamshin turaren jikinta, ya gauraye motar baki ɗaya. Ya ce "Wa zan jira ban da ƙanwata, kwana biyu ban gan ki ba, da gida zan bi ki ma, to sai na ji tsoron kar na je ko ki na da baƙo, ban sanar da ke zan zo ba. Kawai na tsaya a nan na ce bari na jira fitowar ki"

Ta yi murmushi ta ce "Ko akwai baƙo, ba dolena na sallame shi na saurari yayana ba, kuma wani baƙi zan yi da safe haka?. To me ma zan samu ne?" Ta yi maganar tana laluba motar.

Ya yi dariya ya ce "Laluba ki ɗauki duk abin da ki ke so" ta yi dariya ta ce "Dan ka san ba ka ajiye komai ba ko? Mu je kar Mummy ta yi ta jira na"

Ya ce "Ok" ya fara tuƙa motar a hankali. Yana tuƙi yana satar kallon Jamila, wani irin kyau take ƙarawa a idanunsa kullum. Kullum ƙara shiga ransa take yi, ga shi ya kasa fitowa ya sanar mata da ainihin abin da yake cikin zuciyarsa. Duk wasu alamu da zai nuna mata sonta yake yi, ya yi amma ya kasa gaya mata baki da baki. Su na daf da shiga layin gidan ya tsaya ya ce "Ƙanwata"

"Na'am Yaya Abba"

"Ina son za mu yi wata magana da ke, amma maybe sai na dawo tukuna"

Ta yi murmushi tare da gyara zaman mayafinta, ta ce "To shikenan babu laifi, a dawo lafiya"

"Allah ya sa, ki kula mini da kan ki Please, zan kira ki idan na je kasuwa"

Ta ce "To, ka sayo mini aya mai sukari a kasuwa"

Yayi dariya ya ce "Aya kawai?"

"Eh ita kawai"

"To an gama ranki ya daɗe" ta fita daga motar tana ɗaga masa hannu"

Da ta shiga cikin gida,ba ta tarar da Hajiya Sa'a a falo na, dan haka ta bi ta bedroom. Ta tarar tana wanka, ta nemi guri ta zauna tana danna wayarta. Can Hajiya Sa'a ta fito daga ita sai towel. Jamila ta kalle ta ta kawar da kai.

"Jamila har na fitar da ran za ki zo ai"

"Ba na jin daɗi ne, shi yasa da kamar ma ba zan zo ba fa"

"Eyya sannu, bari na shirya ki raka ni mu je na duba Fatuhu"

Jamila ta ce "Tom" Hajiya Sa'a ta zauna a kusa da Jamila, ta ɗan riƙo hannunta ta ce "Daughter wai ke haryanzu ba za ki waye ki faso gari ba? Ina ta saita ki a hanya kin ƙi yarda ki shiga layi"

Jamila ta ɗan ɓata fuska tana zame hannunta ta ce "Gaskiya ni Mummy ba na so, ni me zan tsinta a jikin mace 'yar uwata, ni abin ma bai yi mini tsari ba sam wallahi"

Ta yi murmushi ta sake matsawa kusa da Jamila ta ce "Ai da gwaji jirgin sama ma ya tashi Jamila, da za ni jarraba da kin gane abin da nake nufi. Shi ne za ki yi babu ruwanki da damuwa da aure, ko tashin hankalin yin planing saboda ɗaukar ciki. Kuma...

"Ni dai gaskiya Mummy ba na so, ni ban ga abin da mace 'yar uwata, ni abin ma bai yi mini tsari ba sam wallahi" Ta yi murmushi ta sake matsawa kusa da Jamila ta ce "Ai da gwaji jirgin sama ma ya tashi Jamila, da za ni jarraba da kin gane abin da nake nufi. Shi ne za ki yi babu ruwanki da damuwa da aure, ko tashin hankalin yin planing saboda ɗaukar ciki. Kuma...

"Ni dai gaskiya Mummy ba na so, ni ban ga abin da mace za ta tsinana mini ba, ni bai ma yi mini tsari ba gaba ɗaya gaskiya. Ba gara na bi maza ba"

Hajiya Sa'a ta kwashe da dariya, ta ce "Yaro man kaza, ai shikenan Daughter, bari na shirya mu fita". A gaban Jamila ta gama shirinta, ba tare da jin nauyin abin da ta tunkari Jamilan da shi ba, ta gama suka fita.

Umman Fadila ce take kallonta a tsanake, bayan ta gama yi mata komai za ta tafi. "Fadila"

"Na'am Umma"

"Na san yanzu da da ba ɗaya ba ne ba, amma ko yaya ɗan abin da ki ke da shi idan ya samu, ko abinci ko kuɗi, ki din ga bayar da sadaka, da nufin Ubangiji Allah ya kawo muku ɗauki,ya sassauta muku wannan yanayin da ku ka tsinci kan ku a ciki" Fadila ta jinjina kai ta ce "In sha Allah" "Tun kwanank da kawunki, ya zo ya duba mijinki, ya kira ni yake mitar, kun tare ku na maganin Asibiti, kun ƙi mayar da hankali ku yi na gargajiya. Na ce masa mijin naki ne ɗan aƙida, kuma ke na haifa ba shi ba, balle na yi masa dole. Amma nima hankalina ya fara karkata ga a yi na hausan, mijinki mutumin kirki ne, ba zan manta halaccinsa a gare mu ba, dan haka na bayar da kuɗi a yi saukar Alqur'ani, da fatan Ubangiji Allah ya yaye masa koma mene ne, tun da shi Alqur'ani waraka ne. Ki yawaita karanta masa, ko ki kunna ya saurara, ko ki din ga busa wa a abincinsa ko abin shan sa. Ba mu san a inda za a dace ba, wannan abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, na Asibitin ba wani haske da ake gani, idan hagu ta ƙi ai sai a koma dama ko?"

Fadila ta ce "Haka ne Umma, in sha Allah, zan yi duk abin da ki ka ce, kuma addu'a mu na yin ta sosai, ina yi masa. Sai dai kin san lamarin Ubangiji ba a yi masa dole, duk addu'arka sai lokacin yankewar abu ya yi tukuna". Umma ta ce "Haka ne, amma hakan ba ya nufin a sare, a ce an haƙura gaba ɗaya ba za a yi ba" Sosai Fadila take jin daɗin rarrashi da nasihar da Umma take yi mata a duk lokacin da ta zo gidan. Ko da su Hajiya Sa'a suka je gidan Alhaji Fatuhu, Alhaji Zailani yana gidan. Yana sashen Alhaji Fatuhu tare.

Alhaji Zailani ya din ga kallon Jamila, yana ganin kamar ya santa, amma ya manta a inda ya san fuskarta. Suka gaisa Hajiya Sa'a ta kalli Fatuhu ta ce "Yaya ya jikin naka?"

Ya jinjina kai ya ce "Alhamdillah"

"Ka na samun sauƙi, ko dai haryanzu babu afuwa?"

Ya yi murmushi ya ce "Da sauƙi" Daga haka suka koma hira da ita da Alhaji Zailani, tamkar ba dubiya su ka zo ba, bar sai da abin ya ba wa Jamila mamaki. Sun jima sannan su ka shiga suka gaisa da matansa suka tafi.

Su na tafe a hanya Jamila ta ce "Mummy, mara lafiyar nan shi ne wanda ɗan sa ya mutu kwanaki ko? Yaran da Nana take koyarwa a makaranta"

"Eh shi ne"

"Allah sarki, to shi wannan Alhaji Zailanin, ko shi ne a can quaters ɗin bayan makarantar nan na ƙofar famfo?"

Hajiya Sa'a ta kalle ta ta ce "Ya aka yi ki ka san shi?"

"A'a na tambaya ne dai kawai, kenan shi ma Nana ta yi aiki a gidansa, yana da 'ya Shukura ko?" Hajiya Sa'a ta jinjina kai tana kallon Jamila.

"To ai da Nanan gidanmu zai aura, ba a yi ba, aka yi aurenta da wannan Buzun, lokaci ɗaya kawai ya fito ya ce wai zai aure ta"

Shiru Hajiya Sa'a ta yi tana kallon Jamila, ta san abu ne mawuyaci a ce haka kurum Alhaji Zailani ya ce zai auri yarinyar da ta fito daga gida kamar na su Nana, da ƙyar idan ba ya san sirrin da ke tattare da Nanan ba. A take gabanta ya faɗi, dan kuwa ko me za a yi ba za ta taɓa barin Alhaji Zailani ya riga ta amfani da jinin Nana ba"

Jamila ta ce "Mummy ya na ji kin yi shiru ne?"

Ta girgiza kai ta ce "Babu komai Jamila, dole mu nemo Nana ne duk inda ta shiga"

Jamila ta ce "Saboda me?"

"Saboda ƙungiya, za ta iya neman ki kawo jinin mafi kusanci da ke, a kowane lokaci!

Ayshercool 08081012143 Jamila a ranta ta ce "Ni kuwa zan ga abin da ya ture wa Buzu naɗi, zan ga abin da zai faru idan na bijirewa buƙatar ƙungiyar" Jamila ta numfasa ta ce "Mummy, dan Allah tambayar ki zan yi"

"Ina jin ki"

"Wai dan Allah, ya aka yi ki ka shiga ƙungiyar nan?"

Hajiya Sa'a ta kalli Jamila, sannan ta mayar da hankalinta kan tuƙin da take yi tana murmushi. Ta ce "Dogon labari ne Jamila, amma me yasa ki ka tambaye ni?"

"Ina son na ji tarihin gwagwarmayar ki ne, ko nima zan daure na yi koyi da jarumtar ki, haryanzu wasu lokutan zuciyata tana rawa ne a kan lamarin"

"Ai na ga alama kam. Jamila na sha gaya miki, muddin ki na son cimma abin da ki ke buri a rayuwa, babu ruwanki da kowa kan ki kawai za ki din ga dubawa. Na tashi a gidanmu bamu da komai, babata da babar Fatuhu, su ne ƙanana a matan gidan, kamar dai yanayin rayuwar gidanku, a haife ka, ba a damu da ɗawainiyarka ba. Manyan yayyenmu babu ruwansu da mu, saboda iyayen su mata sun cusa musu aƙidar ƙin iyayenmu. Babanmu ya mutu shi ma saboda bai bar komai ba, babu wanda ya damu da mu. Yayyenmu iyayensu kadai suke taimako da ƙannen su, mu kuma namu iyayen ke ta fafutuka da wahala. Fatuhu ya yi ta faɗi tashi da rayuwarsa, da ta mahaifiyarsa, sai dai yana tunawa da ni. Zailani tsohon saurayina ne, da rashin abin yi ya hana mu yin aure da shi. Ya shiga makaranta, bisa tallafin karatu, a can ya samo mana wannan ƙungiyar. Shi kuma lokacin Fatuhu ya fara zuwa kasuwa, ni kuma na riga na yi aure. Zailani ya gaza jan Fatuhu ƙungiya, saboda mutum ne mai tsantseni da ra'ayin riƙau. Ni kuma har a lokacin mijin da nake aure, ba shi da komai ba na samun irin rayuwar da nake so. Sannu a hankali na ci gaba da hulɗa da Zailani ya kai ni ƙungiya, ya zamana ba na rasa kuɗin kashewa dai. Fatuhu kuma ya ja Zailani kasuwa, suke kasuwanci tare, sai dai duk da tasirn ƙungiya, Zailani ya kasa tara abin da Fatuhu yake da shi. Kin san waye mutum na farko da na fara bayarwa?" Jamila ta girgiza kai alamar a'a. "Babban yayanmu, da iyayensu su ka mayar da mu saniyar ware a gida" Jamila ta jinjina kai a ɗan tsorace ta ce "Sai kuma ki ka ba da wa?" Hajiya Sa'a ta yi murmushi ta ce "Zan ƙarasa miki nan gaba kaɗan, yanzu bari mu ƙarasa gida, akwai abin da nake son yi" Jamila ta jinjina kai tana satar kallon Hajiya Sa'a.

Hajiya Sa'a ta ajiye Jamila, sannan ta ja motar ta tafi. Tana tafe ta kira layin Alhaji Zailani.

Sai da ta kusa katsewa, sannan ya ɗaga tare da yin sallama.

Ta ce "Ai na zata ba ka ɗaga ba ne"

Ya ce "A'a ina tuƙi ne? Lafiya?"

"Ƙalau, tambayarka abu zan yi"

Ya ce "Ok, ina jin ki"

"Ashe kwanaki da aure zaka yi?"

Ya ce "Yaushe?"

"Kwanakin baya mana, za ka auri wata yarinya Nana"

Kamar tana gabansa ya tsuke fuska ya ce "Waye ya gaya miki"

"A'a ba sai ka ji wanda ya gaya mini ba, zancen Duniya ba ya ɓuya ai, sai dai ka sani na san da abin da ka ke nema, ni ma shi nake farauta" "Sa'a ban fahimci abin da ki ke nufi ba fa, ki yi mini bayani gwari-gwari "

"Za ka fahimta ne, ka je ka nutsu ka yi nazari" ta kashe wayar ta ajiye ta ci gaba da tuƙinta.

*

Yana zaune a takure a gurin, ya yi shiru tamkar mai jiran tsammannin wani abun, aka buɗe ƙofar ɗakin da yake . Wasu tiƙa-tiƙan murɗaɗɗun maza suka shigo. Ba su yi wata-wata ba, suka yi sama da shi, suka fito da shi daga gurin da yake zaune.

Wani ɗakin aka sake kai shi, sai dai yana shiga ya yi turus, ganin mutumin da yake zaune a cikin ɗakin. Ƙartin suka juya suka fice, suka bar shi daga shi sai mutum biyu a ɗakin.

"Bismillah ka zauna mana" cike da tsoro ya ƙarasa ya zauna yana rarraba ido, ya sunkuyar da kansa.

"Mahmudu, ɗagowa za ka yi ka kalle ni ai" Ya ɗaga kai ya saci kallon mutumin, ya mayar da kansa ya sunkuyar.

"Na san wannan zaman takurar ya ishe ka zuwa yanzu, kasancewarka mutum da ya saba da 'yanci a baya. Ina son ka buɗe kunne ka saurare ni da kyau, tambayoyi nake son na yi maka, muddin ka gaya mini gaskiya ka bani amsa, zaka iya samun sassauci, ko ma na yi umarnin a sake ka, ka yi tafiyarka gaba ɗaya"

Ya jinjina kai ba tare da ya ɗago ba. Mutumin ya sauke rawnain fuskarsa ya ce "Na san an yi maka wannan tambayoyin an kum a baya, yanzu ma zan sake jaddada maka su, me yasa ka sace Imam ka kai shi Nigeria, da ka kai shi kuma me ka yi masa?"

Kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya girgiza kai ya ce "Ban sace shi ba, kuma ban yi masa komai na cutarwa a Nigeria ba"

"To me yasa ka tafi da shi Nigeria ba ka sanar da kowa ba?"

Mahmudu ya ce "Wannan wani sirri ne da ba zan iya tona shi ba, ko da za ku salwantar da rayuwata, wani abu wanda daga ni sai shi Imam"

Abduou ya jinjina kai ya ce "Da amincewar sa ku ka tafi Nigeria kenan?"

"A'a hasalima bai san komai ba, ba wani da zaɓi ne da ya rage, sai abin da na aikata ɗin"

"Mahmudu, na fuskanci zama da maɗaukin kanwa ya sanya maka farin kai. Rayuwa da Imam ya sanya ka koyi baƙin taurin kai irin nasa. Amma ka snai, kama da wane ba ta wane, kuma ina fatan ka san da tun da aka ɗaukko shi daga Nigeria har yau ba ya hayyacinsa, bai yi magana da kowa ba?"

Readers Also Read