Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 45
Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 45: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 45. Mahmudu ya girgiza kai ya ce "A'a ranka ya daɗe. Rashin gane kowansa ba…
3,370 words
Mahmudu ya girgiza kai ya ce "A'a ranka ya daɗe. Rashin gane kowansa ba shi da nasaba da zuwansa Nigeria"
"Saboda me?"
"A can ɗin ma ba gane kowan yake yi ba"
Abduou ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Zoben Azurfarsa fa guda ɗaya da baya hannunsa, ina fatan ka san inda wannan yake?"
A zabure Mahmudu ya kalli Abdou matawalle, jin abin da ya faɗa.
"Ka daina zaro mini ido, kwanaki biyu kawai ka ke da su, ka faɗi inda zoben yake, ko kuma ka rasa rayuwar ka baki ɗaya, zaɓi ya rage naka"
Abdou ya miƙe, ya ja rawaninsa ya rufe fuskarsa ya fice daga ɗakin.
Cikin matsanancin tashin hankali, ya bi bayan matawalle da kallo. A Nigeria babu wanda ya san ma'anar zobunan da suke hannun Imam. Kuma ya yi iya ƙoƙarinsa gurin ba shi dukkanin kariya, balle ya ce wani ya san muhimmancin su ne ya karɓa. Matuƙa ya ji yana son ya ga Imam, ya gana da shi, sai dai ya san ko mai zai yi babu mai ba shi wannan damar. Ga shi ya ji Abdou ya ce tun da aka dawo da shi, bai farfaɗo ba balle ya yi magana. Gefe guda kuma yana jin tsoron kar a koma a Nigeria a bibiyi Nana, saboda za ta shiga matsala ba kaɗan ba. Koma a wani hali take ciki yanzu? Ya tambayi kansa yana jin wata irin damuwa ta mamaye zuciyarsa, tare da ɗora wa kansa laifi amincewa da auren Imam da Nana, ya kuma ɓoye mata komai a kan Imam ɗin. Ya dafe kansa da yake jin tamkar zai tarwatse dan damuwa.
Nana ta nutsu da zaman gidan Nene, duk Nenen akwai faɗa kamar yadda Hajara da mijinta suka din ga faɗa, amma sam hakan bai damu Nana ba, dan ba ta yi mata abin da za ta yi faɗan. Nana ta fuskanci Nene sana'ar Abinci take yi, wasu lokutan tun safe idan ta fita sai daf da magariba take dawowa. Ta kan dawo tar e da yaran da suke yi mata aiki, su fara rage aikin Abincin sayarwar da za a yi washegari. Nana tana jin yadda Nene take yi musu bala'i bisa kuskure kaɗan. Nene ta din ga gwada Nana, da ajiye kuɗi ko ina ta ga dama, ko ma ta fita ta bar ɗakunanta a buɗe, amma ko allura ba ta taɓa rasawa ba. Kullum sai ta ba wa Nana Abinci, na safe kan su fita na sayarwa ta ba ta na rana, idan sun dawo ta ba ta na dare, har da ma tsaraba ta masu ciki. Ma'aikatan Nene sun ɗauka ma, Nana 'yar uwatta ce. Idan sun dawo Nana kan fito ta ce za ta taya su aiki, Nene ta yi ta faɗa ta ce ba za ta yi ba. Sai dai hakan ba ya hana Nana kama musu wasu ayyukan. Nana ta shafe kusan wata guda a gidan Nene, ta ga kullum sai Nene ta ba ta Abincin nan sau uku, ba ta taɓa nuna mata ta gaji da ciyar da ita da take yi ba, wasu lokutan har tambayarta take yi, ko tana son cin wani abin ne daban. Da daddare ta kira Nana, Nana ta fito ta zauna a kusa da ita. Ta buɗe takarda fal kifi ta ce "Nana ga kifi ko za ki iya ci, idan ƙarnin ba zai dame ki ba".
Nana ta dube ta ta ce "Nene, dama ina son mu yi magana ne"
Nene ta ce "To ina jin ki"
"Na ga kullum sai kin bani Abinci sau uku a rana, na ce ko za ki ba ni wani aikin na din ga yi miki, a maimakon Abincin da ki ke ba ni, ko gurin sayar da Abincin sai na din ga bin ki, ko wanke-wanke na din ga yi miki" Ta dubi Nana, sannan ta numfasa ta ce "Ni kuwa duk rashin imanina, da wannan tsohon cikin sai na saka ki aiki, dan dai abin da za ki ci sau uku ba zai gagara ba. Ban san takamaiman abin da ya kawo ki ƙasar nan ba, ban san kuma lokacin komawar ki ba, amma ba na tunanin abin da za mu ci ni da ke zai gagare ni. Ba zan ɓoye miki da fari ban so zamana da ke a gidan nan ba, saboda ba na son matsi da takura ko kaɗan, da su Auwwalu sun matsa ne, dan kora da hali na so yi miki. Amma yanayin ki ya nuna mini ki na ɗauke da damuwa mai nauyi a zuciyarki. Ba ƙaramin dalili ne zai sanya yarinyar mace, mai ƙanan shekaru kamar ki, ta baro gida ta taho uwa Duniya ba ga juna biyu. Kuma ki na yawan zama ki yi shiru, fuskar ki ɗauke da damuwa. Na kuma jarraba ki ta ɓangarori da dama, ban ga alamar rashin nutsuwa a tare da ke ba, shi yasa na ji zan iya zama da ke. Amma Nana tsakaninki da Allah wannan juna biyun na ki, na halal ne? Kuma da sanin iyayenki ki ka taho nan?" Tambayar Nene ta yi wa Nana mugun zafi a ƙirjinta, amma sam ba ta ji haushinta ba, dan kowaye dole ya yi irin wannan tambayar. Sai da ta ji hawaye ya cika mata ido, da tuna ire-iren waɗannan tambayoyin dole ta ci gaba da amsa su, a cikinta da abin da za ta haifa, muddin ba gano inda Sayyid yake ta yi ba. Ta haɗiye wani irin yawu mai zafi ta ce "Nene cikina na halal ne, ni matar aure ce, ban kuma gaya wa iyayena zan taho nan ba, sai da na riga na yo nisa da gida"
"To saboda me, kuma ina mijinki?"
Kawai Nana ta fashe da kuka, ta ce "Shi na fito nema, mijina da danginsa" Nene ta ce "Shikenan, ya isa haka ki kwantar da hankalinki, mu bar maganar ma yi wani lokacin. Amma sai dai ki yi haƙuri, dan dole sai mun ƙarasa wannan maganar Nana, saboda ni uwa ce, dole na mu'amalance ki na yi miki nuni da abin dai-dai da akasin haka. Ban ga alamar ki na magana da wani a can gida ba, ko ta tarhon hannunki ce ba. Mahaifiyarki tana raye?" Nana ta jinjina kai tana share hawayenta. Nene ta ce "Shikenan, share hawayenki mu ci kifin"
Ta girgiza kai ta ce "Ƙarnin hawa kaina yake yi na ƙoshi" daga haka Nana ta tashi, ta koma ɗakinta. Sai dai ta din ga kuka, saboda ita kanta ba ta san ta ina al'amuran za su warware ta cimma abin da ta fito nema ba.
Shukura ta rasa gane kanta da kanta, saboda rashin lafiya da take ta fama, ga Sagir ya rage ba ta kulawa, duk da yana ta ɓoye-ɓoye amma tuni ta daɗe da gano shi, sai dai ta maze ita ma ba ta nuna masa ba. Hajiya Amina ce ta je gidan, Shukura ta ji daɗin zuwanta sosai da sosai, a nan Hajiyar take gaya mata batun Nana.
Cikin damuwa Shukura ta ce "Wallahi Mami, tun da aka yi auren nan, nake jin tausayinta, gaba ɗaya ban ga riba a abin da babanta ya yi mata ba. Babu bincike babu komai a ce an aura mata mutum, wasu lokutan na kan rasa ina tunanin mutanenmu yake tafiya"
"Ke dai a yi sha'ani kawai, amma na jinjina batun ni kaina"
"Shikenan an saka rayuwarta a gagari, ga ƙarancin shekaru" suka ci gaba da jajanta lamarin. Hajiya ta fuskanci yanayin Shukura kamar ba ta da cikakkiyar lafiya, ta kira Doctor Sharif ya zo ya duba ta. Shukura ba ta so ba sam, dan ko ƙaunar ganin Sharif ɗin ba ta yi, amma tuna ta yi wa Hajiya Alƙawarin komai ya wuce, ta yi tawakalli ta dangana ya sanya ta haƙura. Ya zo har gida ya yi mata gwaje-gwaje, ya kuma tabattar mata da tana da juna biyu. Hajiya Amina ta din ga murna, a duk lokacin da aka ce ga wata mace da ciki, sai ta yi ta murna, ta ji dama ita ce. Shukura ba ta wani yi murna ba, saboda ita gaba ɗaya haihuwar ma ta fita daga kanta. Da yamma Hajiya Amina ta koma gida, saboda tsabar zumuɗi, tana zuwa ta tarar da Alhaji Zailani a gida, ta hau ba shi labarin Shukura wani cikin ne da ita. Wata irin mummunar faɗuwar gaba ce ta ziyarce shi, yana tsoron a wannan karon ma, kar a nemi ya bayar da wani abu da ya danganci iyalinsa.
Hajiya Amina ta din ga jin wani irin bacci, tana idar da sallar isha'i, ta ɓungire a gurin ta hau bacci.
Ita da Nana ta gani a falo, a zaune suna hira, kamar yadda suka taɓa yi kwanaki lokacin Nanan, na zuwa gidan rainon Haidar. Ta ce "Hajiya, kin kuwa ci gaba da bibiyar Likitoci a kan matsalar rashin haihuwar ki?" Hajiya Amina ta ce "Nana ai ni na haƙura ma na bar wa Allah, yanzu shekaruna sun wuce na haihuwa"
Nana ta ce "A gurinki ba, a gurin Allah yana bayar da falalarsa a inda ya so, da kuma lokacin da ya so ne. Ki daina biye wa wannan mijin naki, ya din ga sarrafa rayuwar ki yadda yake so. Ki nemi mafita a kan matsalolinki. Kuma Shukura ta dage da Addu'a, kar wannan ɗan ma ya sake raba ta da shi"
Maganar Alhaji Zailani ce ta tashi Hajiya Amina daga mafarkin da take yi, tana kallonsa kawai ta ji gabanta ya faɗi"
"Lafiya ki ke kwance a ƙasa haka ki ke bacci?"
Ta ce "Bacci ne ya ɗan ɗauke ni ban sani ba"
Ya ce "To ki tashi ki koma gado mana, kar wuyanki ya yi ciwo" Ta yinƙura ta tashi ta canza kaya ta hau gado ta kwanta, sai dai ta din ga jin mafarkin da ta yi da Nana a jikinta, tamkar a zahiri ya faru.
Fadila ce zaune a kusa da Alhaji Fatuhu, gefenta kuma jaririnta ya yi wayo, yana ta bacci. Ta miƙa masa lemon da ta haɗa masa a kofi, ta zuba masa ido, yana sha a hankali. A ranta take faɗin "Ubangiji Allah ka bawa wannan bawa naka lafiya, albarkacin ayoyin Alkur'ani' Ta kalle shi tsaf, ya yi rama ta ban mamaki, dan ma yanzu ya ɗan ciko, ba kamar da ba" ya shanye ya miƙa mata kofin, ta karɓa ta ajiye a gefe. Ta matsa kusa da shi tana ɗan ƙara gyara masa filulluka. Ya ce "Na gode sosai, Allah ya yi miki albarka, ya raya miki Muhsin"
Ta ce "Amin Daddy"
"Da lafiyata ƙalau, da mun yi sauri, nan da wata wata taran, ki kuma haifo mana wani" Murmushi ta yi ta ce "Allah ya baka lafiya ya tashi kafaɗunka" ya amsa da Amin yana riƙe hannunta cikin nasa da ya yamuste kamar na tsoho. Hajiya Suwaiba ta ce ta shigo ɗakin, Fadila ta ɗan zabura ta ja da baya. Hajiyar ta ja tsaki ta ce "A hakan ma da kake wani abin ka ke ƙoƙarin yi, ai sai ku rufe ƙofa kar yara su faɗo, a lalata mini tarbiyyar yara" Fadila ta ce "Haba Hajiya, abu na ba shi ya riƙe hannuna, and laifi ne dan ya riƙe hannuna wani abin ki ka ga na yi?"
"Kar ki yi mini rashin kunya dai? Idan ma yin ku ke, ku ƙarata ku da Allah" Ran Fadila ya yi mummunan ɓaci, ta yinƙura da niyyar, ta ɗauki ɗan ta ta bar ɗakin, amma ya riƙe hannunta, ya hana ta tafiya. Hajiya Suwaiba ta gama bala'inta ta tafi ta bar su. Idan ya ce Suwaiba ba ta ƙoƙari a kan rashin lafiyarsa ya yi ƙarya, tana iyakar ƙoƙarinta amma wasu lokutan tana da saurin ƙosawa gashi haryanzu azababben kishi na ɗawainiya da ita.
Gidan Maijidda kuwa, Iliyasu bai taɓa tsammanin, Maijidda na da taurin kai haka ba. Gaba ɗaya ta tarkata shi ta yi watsi da shi. Iyakarta da shi, ta girka Abinci ta ba shi, idan buƙatarsa ta tashi, ya yi kiɗansa ya yi rawarsa. Gaba ɗaya ta sanya damuwa a ranta, ta rame sosai da sosai, dan ko Abincin kirki ba ta iya ci, kusan kullum cikin kuka take, ko ta zauna ta yi shiru. Ga shi ya lura 'yan uwanta sun fara gajiya da sinturin kai ƙararta da yake yi, ba yau ba gobe.
"Anya ka na ganin haka rayuwar Imam za ta ci gaba, duk lokacin da ya farka sai ihu da fizge-fizge, sai dai a yi ta yi masa allurar da zai yi bacci? Idan aka bar shi a haka rayuwarsa fa ta nakasa kenan har abada"
Sultan ya ce "Abdou, ni kaina ala'amarin nan yana damuna, na rasa yadda zan yi. A ɓangaren ƙwaƙwalwar ma, babu wani gamsashshen bayanin abin da ya faru da shi. Ta ɓangarenka ma babu wani nagartaccen bayani daga bakin shi yaron, balle mu ji ko wani abin ɗin aka yi masa".
"Sultan, ka ƙi bayar da dama a sanya 'yan doka, su maguza yaron nan, ya faɗi gaskiya ko ya ƙi Allah"
Sultan ya girgiza kai ya ce "A'a, duk ranar da Imam ya samu lafiya, muddin ya ji labarin an cuzguna masa, zai yi fushi, kuma zai ji babu daɗi kai ka san irin alaƙar da take a tsakaninsu."
"Amma yanzu ai yanzu a kan gaɓar bincike a ke Sultan. Amma tun da haka ka ce Shikenan, za a ci gaba da bin komai sannu a hankali"
Sultan ya amsa da "Yauwwa"
BAYAN WATA ƊAYA Sabo turken wawa, rashin ganin Ƙaisar da Nana ta daina yi, ya sanya ta din ga tunanin ko wani abin ne ya faru da shi. Sai dai yau kwatsam cikin barcinta, ta ganta a cikin Librarynsa. Sai dai ta gurin ƙwalam babu litatafai babu kayan rubutunsa sai mudubin da yake nuna mata abubuwa a cikinsa. Ta waiwaya ta lelleƙa, amma babu Ƙaisar babu alamunsa. Wani littafi guda ɗaya tal, ta hango a kan teburin rubutun Ƙaisar, ta ƙarasa ta nufi teburin ta ɗauki littafin.
Bangon littafin na fatar wata dabba ne. Dan har da gashi-gashi a jiki. Yanayin bangon littafin ya sanya ta yi tunanin, ko mene ne a rubuce a littafin ba yanzu ya faru ba, ya kwana biyu da faruwa. Littafin ba wanda ta karanta tarihin su Lanti ne a ciki ba, wani ne daban. Hoton wata alƙarya ce, da ke tsakanin duwatsu, da aka rarake aka samar da katafariyar daula. Ta buɗe littafin shafin farko, ta fara karantawa.
"Tushiya..." Shi ne abin da ke rubuce a shafin farko na littafin.
"Ka sani,har abada da ɗan Gari a kan ci gari. Kuma ba a cimma buri da tausayi ko jin ƙai. Wannan mataki na farko kawai ka cimma, na sharar fagen cimma nasararka. Ka na buƙatar sanya wa mutane tsoronka, da shakkarka domin cimma burinka, kuma hakan ba zai taɓa yiwuwa ba sai ka zubar da jini, duk wanda ya biyo ta hanyarka ka datse rayuwarsa, kar ka damu da adadin rayukan da za a rasa, ka zubar da jini ba ƙaƙƙautawa har sai mutane sun fara jin fitsari a duk lokacin da aka ambaci sunanka. Ka kame mutanen gefen alƙaryar nan, ka mayar da su bayi, matansu ka mayar da su naka, mazansu su zama bayinka, ka yi amfani da ƙarfinsu da fikirarsu ka gina alƙaryar da babu wani mahaluki da zai iya ɗaga maka yatsa, kar ka gushe kana aikata hakan, har sai buƙata ta biya. Zaka kasance cikin sanyawar albarkar Aljanu, za su baka dukkanin goyon bayan da ka ke buƙata kar ka saurarwa kowa"
Cikin damuwa mutumin ya kalli mai maganar ya ce "Ka sanya ni na kashe mahaifina da hannuna, yanzu ga wani abin ka sake zuwar mini da shi, kar ka manta ina da 'yan uwa maza, ba za su zuba mini ido, duk na yi wannan ba, na ɗauki abin da ba nawa ba, alhalin su na gaba da ni ba" Ji ta yi mudubin gurin yana wata irin ƙara tamkar zai tsage, a take ta ajiye littafin ta nufi mudubin tana kallonsa. Wata irin wuta ta gani tana ci a cikin mudubin. Wutar mai matuƙar ban tsoro saboda yadda take ci. Wani mashi ta gani a soke a jikin wani ƙwarangwal, ɗaya gefen mashin an yi rubutu a jikin wani abu mai kama da takarda. Ta ƙara matsawa domin karanta mene ne a jikin takardar amma ta ga mudubin yana hayaƙi yana baƙi yana washewa. A kusa da wutar ta ga wani abu mai kama da mutum, a lulluɓe da wani mayafi yana zuba wani abu a cikin wutar wanda yake ƙara sanya wutar ƙara balbala. Imam... ta iya gani a rubuce a jikin abin, mai kama da takarda, a gaban Imam ɗin akwai wani sunan, sai dai ba ta iya karanta sunan ba. A jikin wutar ta ga taswirar fuskar Sayyid yana jijjiga jikinsa na ƙonewa yana kururuwa yana kiran sunanta. Wata irin zabura ta yi ta kuma tunkarar mudubin gadan-gadan, mudubin ya yi wata irin tsawa ta ja da baya ta faɗi ƙasa. A gigice Nana ta farka, ta haɗa uban gumi ta yi sharkaf, ga wata irin ƙullewa da cikinta ya yi haɗi da mararta. Ta yinƙura da ƙyar ta tashi ta tafi banɗaki, a zatonta fitsari take ji, ko kuma bayan gida, amma ta ji ba bayan gida take ji ba, ta fitsarin amma still mararta kamar an saka wani abu an ɗaure mata. Ta yi alawala ta koma ɗakinta. A zaune take salla saboda yanayin girma da nauyin da cikin ya yi. Ta kasa tuna abin da ta gani, sai iya wutar nan da wannan tsawar da mudubin ya yi su kawai take iya tunawa. "Allahumma ajirni mina narr" Ta maimaita da tuno yadda ta ga wutar nan. Ta ji sam mafarkin nan bai yi mata daɗi ba, ko mene ne babu Alkhairi a tattare da shi sam. Sai da gari ya waye, sannan ta samu afuwa daga wannan ɗaurewar da mararta ta yi da bayanta. Jikinta babu daɗi, haka nan take lallaɓawa ta daure kar Nene ta fuskanci wani abu. Nana ta dama kunu da kanta, ta tashi tana tafe da kyar, Nene ta ce "Nana wai cikin nan naki wata nawa ne?"
Ta ɗan yi shiru ta ce "Ina ga bakwai ne" "Anya kuwa Nana, kalli yadda ya cure guri ɗaya ya cure guri ɗaya ya yi ƙasa sosai a ce cikin nan na watanni bakwai ne kawai? Amma ban sani ba ko biyu ne. Yakamata ma mu je Asibiti a duba ki, ni wallahi na ma manta shaf ana zuwa awo. Ko danmu lokacinmu ba awon ake yi ba oho" Nana dai ta yi murmushi kawai tana jin yadda ɗan yake ta motsi yana danno ta.
Da ba rufe cikakken sati, mijin Hajara bai zo gidan ba, dama yana fargabar kar Nana ta kasa zama da Nene, saboda faɗanta, kuma cikin ikon Allah ya ga lafiya kalau suke zaune. Dan haka ya rage zuwa sosai. Tun da Nana ta je gidan, Neme ba ta barin ta ta fita, saboda ta ce mata tana da aure, kuma tana yawan gaya mata, ba a son mace mai ciki ta din ga yawo jama'a su na kallonta, saboda baki da ido. Ma'aikatan Nene duk sun saba da Nana, duk a tunaninsu 'yar uwatta ce, sai dai sukan tambayi Nana, ya aka yi hausarta ba irin tasu ba. Wasu lokutan sai Nene ta cewa Nana ta zauna a ɗaki kar ta fito, dan haka babu inda Nana ta sani a garin. Nana ta kwana huɗu, tana fama da wannan ciwon a tsaitsaye. Sai dai na yau ya fi na kullum, dan sam ba ta yi bacci ba, kuma ba ta gaya wa Nene ba. Da safe kan Nene ta fito, Nana ta yi shara ta wanke banɗaki, ta ɗora abin karin kumallo. Ta kuwa sha faɗa a gurin Nenen, sai dai ita ko a jikinta. Sun gama karyawa, Nene ta shiga ɗaki, ta ji Nana na kiran sunanta, cikin mawuyacin hali. Nene ta fito da sauri ta ce "Nana lafiya?"
"Nene yoyon fitsari nake yi, ba na iya riƙe fitsari" gaban Nene ya faɗi ta ce "Kamar yaya?"
"Ji na yi kawai fitsari yana bin ƙafata, kin ga" ta yi maganar tana ɗaga wa Nene doguwar rigarta, ruwa na ta bin ƙafafuwanta".
"Nana wannan ai kamar naƙuda ki ke yi, anya ba ruwan mahaufa ba ne?"