Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 46
Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 46: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 46. Duk da ƙoƙarin da ta yi, za ta yi magana, sai ta kasa saboda wani irin…
3,335 words
Duk da ƙoƙarin da ta yi, za ta yi magana, sai ta kasa saboda wani irin gigitaccen ciwo da ta ji.
Har Nene ta fita suka samo abin hawa, Nana na cikin halin ciwo, ba ta iya gane komai. Nene ta ɗaukko wa Nana wasu kayan, su ka fita suka tafi Asibiti. A Asibitin ma, da aka tambayi Nana, cewa ta yi cikinta wata bakwai ne, sai dai da aka yi hoton cikin, ya nuna satin cikinta arba'in da biyu. Likitan ya yi mata tambayoyi, yaushe ta yi al'ada na ƙarshe, ta ce ita ba za ta iya ganewa ba, saboda ɓari kawai take yi a jere. Ya tabattar mata a cikin ɓarin da ta din ga yi, tun da ba Asibiti take zuwa a duba ba, akwai wanda bai fita ba ya ci gaba da girma, dan haka naƙuda take yi.
Gaba ɗaya Nene ta rikice, kamar 'yar ta ce za ta haihu, sai a lokacin ta fita, ta sayo kayan jariri da ba ta san ma na wani jinsi ba ne, da ɗan abin da za a buƙata. Ma'aikata na tsaye a kan Nana, su na ƙoƙari, duk ta galabaita ma ta kasa nishin can ta ce "Ya hayyu ya ƙayyum" ta yi yinƙuri sai ga kan ɗan ya fito. Ita dai ba ta san yadda aka ƙarasa ba, ta ji kukan jariri ya cika ɗakin.
Likita ta ɗago mata jaririn ta ce "Kalli me ki ka haifa?"
Nana haushi ya kama ta, ta gama shan wannan uwar wahalar ga ɗan a hannunta, kuma a din ga tambayarta me ta haifa. Ta kalli yaron namiji ne, ta ga wani irin shirgegen ɗa, kamar ɗan wata biyu, sai ta hau mamakin yanzu wannan ɗan duk girmansa a jikinta ya rayu, kuma ta ɗan wannan gurin ya fito? Wata irin zabura ta yi ganin fuskar yaron, ta miƙa hannunta gaba ɗaya tana ƙoƙarin karɓe yaron daga hannun Likitar a kiɗime.
Yana kan gadonsa na marasa lafiya a kwance, su ka ga ya yi wata jijjiga sai da gadon ya girgiza kamar an jona masa wani abu, kawai suka ga ya buɗe idonsa. A rikice suka kewaye shi, su na kiran sunansa, sai dai babu wanda ya amsawa sai bin su da yake da ido, kamar ya ga baƙin halittu. Sultan ya riƙo hannunsa ya ce "Imam ka gane mu kuwa?" Ya yi shiru yana bin Sultan da kallo. Abduou ya ce "Ikon Allah, ka ga wannan karon bai tashi da ihun ba, sannu Imam" Kawai ya yi shiru kamar saƙago, sai ƙwayar idonsa da yake juyawa.
Ayshercool 08081012143 Nana kuwa da sauri wata ma'aikaciya ta mayar da ita ta kwantar, ta ce "Kar ki tashi, ai miƙo miki shi za a yi" Abin da ya razanata kuwa, bai wuce yadda ta ga fuskar Sayyid sak, a jikin ƙaton jaririn nata ba, ga sumar kansa a cike har goshinsa. Ga shi jariri amma hatta girar sa da gashi, haka jikinsa ma akwai gashi sosai. Aka ɗora mata shi a ƙirjinta, ta yi wata nannauyar ajiyar zuciya, tare da furta Alhamdillah.
Ta sanya hannayenta, ta zagaye shi, ta ɗora hannunta a kansa ta din ga karanto masa addu'oi. Ta din ga hasko irin murnar da Sayyid zai yi, da ya na nan aka haifi jaririn nan. Hawaye ya din ga gagangarowa ta gefen idonta. Tana jin Likitan tana tsokanarta da har da kukan daɗi, ba za ta bayar da jaririn ba sai an ba ta tukuici mai tsoka. Nana dai ta lumshe idanunta tana murmushi. Aka ɗauke jaririn aka gyara ta, aka yi mata ɗinki, sannan aka kai ta ɗakin hutu. Bakin Nene ya ƙi rufuwa, ta din ga kallon jaririn. Ta kira wayar su Hajara, ta gaya musu baƙuwar su Nana ta haihu. Nana ta din ga kallon Nene, da mamakin yadda take ta murnar haihuwar nan, tamkar ita ta haihu. Sai dai da Nana ta kalli fuskar jaririn sai jikinta ya yi sanyi, ta rasa abin da yake yi mata daɗi, tana tsoron idan ba ta haɗu da Sayyid ko 'yan uwansa ba, yaya za ta yi mene ne makomar yaron kenan? Ga fargaba da tsoron kar su Ƙaisar su yi masa wani abu, kar shi ma ya yi mummunan gado kamar yadda ta yi. Haka dai ta ɗan saki fuska babu yabo ba fallasa. Bayan awanni shida aka sallame ta daga Asibitin suka koma gida. Aka bata magungunan da suka dace ta yi amfani da su, duk Nene ta biya komai. Nene ta shiga hidima da Nana sosai, ruwan wankanta da na jariri. Ga lafiyayyen Abinci, Hajara kanta idan za ta zo, sai ta yi girki. Kowa ya ɗauki jaririn Nana, sai ya burge shi. Ita kanta Nana tasirin Addu'a ne ya sanya Allah ya kawo mata wannan ɗaukin da gaggawa, mutanen da ta haɗu da su suke sonta.
Kwana na biyar da haihuwarta, ta ɗebo kuɗi a cikin jakar gurin Sarkin baka, ta samu Nene ta ce "Nene kuɗin nan za su isa a sai wa yaron nan abin yanka?"
Nene ta ce "Kar ki damu, mun yi magana da Auwwalu za a samo abin yanka in sha Allah"
Nana ta ce "A'a Nene, ko ke ki ka haife ni, wahalar da za ku yi mini kenan, kuɗinki na sana'a ne. Ina son a saya masa kaya, a saya masa abin yanka, ko ba za su isa ba, a karɓa a ƙara irin kuɗin mahaifinsa ne, dan Allah kar ki ce a'a" Da ƙyar Nene ta karɓa. Dan kuɗin da yawa, aka sayo ƙaton rago, Nene har da ɗawainiyar yin girki, ta gayyaci maƙwabtanta suna. Muhammad Muhsin, shi ne sunan da Nana ta sanya wa jaririn, Muhsin saboda sunan ɗan gidan Alhaji Fatuhu da har abada ba za ta manta da mutuwarsa ba.
Maƙwabtan Nene da ma'aikatanta sun yi wa Nene kara, sosai suka tara mata abin alheri na kuɗi, da kayan sakawa kasancewar Nene duk masifarta akwai kyauta, shi yasa take shiri da mutane.
Da daddare Nene ta yi wa Muhsin wanka, Nana ma ta yi ta ba ta jaririn ta shayar da shi. Ta fita tsakar gida ta ƙarasa aikace-aikacenta. Kukan jaririn ta din ga ji, Nene ta ce "Nana ya ne, ki kula da shi mana" Amma Nana ba ta amsa ba, sai kukan jaririn da ta ci gaba da ji. Ta koma ɗakin ta ɗaga labule, kawai ta tarar da Nana, ta saka jaririn a gaba tana ta uban kuka. Hankali tashe ta shiga ɗakin cikin damuwa ta ce "Ke lafiya, kukan me ki ke yi?" Nana ta kasa magana, ta ci gaba da kuka, ga jaririn a kan cinyarta amma ta kasa riƙe shi. Nene ta ƙarasa ta ɗauke jaririn ta ce "Ba za ki illata ɗan mutane ba, maza yi ta kukan, idan kin gama kya kula da shi" Nene ta goye shi a bayan ta, ta ci gaba da sabgoginta ta ƙyale Nana. Ba ta sake kula Nana ba, sai da ta yi kuka mai isarta ta gaji. Nene ta gyara shimfiɗarta, ta kwantar da Muhsin da ya yi bacci. Ta koma gurin Nana, ta zauna. "Nana" ta kira sunanta. Nana ta ɗaga kai ta kalle ta. "Ki gaya mini tsakaninki da Allah, yaron nan ta hanyar aure ki ka haife shi ko kuwa? Na san tambayar nan tana baƙanta miki rai, amma haƙuri za ki yi da ni"
Nana ta share hawayenta ta ce "Nene ni ba ƙarya na yi miki ba, ina da aure wallahi ɗan sunna ne" "To Alhamdillah, dama jira nake Allah ya sauke ki lafiya, idan ta kama da kaina sai na je Nigeria, na mayar da ke gaban iyayenki Nana, wannan zaman naki kina yarinyar mace, ba kamace ki ba"
"A'a ba zan koma ba Nene"
"To saboda me?"
Hawaye na ambaliya a fuskar Nana ta ce "Sai na haɗu da Babansa, ko danginsa. Ai sun san na taho neman sa"
Nene ta ce "To a wane garin baban nasa yake?" Ta girgiza kai ta ce "Nima ban sani ba"
"Kamar yaya? Meye sunansa da garin da yake ko hotonsa, sai a taya ki cigiyarsa" Nana ta sake girgiza kanta ta ce "Ban sani ba"
"Wacce daga cikin tambayar ce ba ki sani ba?"
"Nene ban san garin su ba, ban san sunansa ba, kuma ba ni da hotonsa"
Nene ta ce "Ke kar ki raina mini wayo mana, na kwaɗe ki, ta yaya za ki auri mutum ba ki san sunansa ba, ba ki san sunan garinsu ba kawai ki ka kamo hanya ki ka taho? Me ki ke ɓoye mini ne?"
Nana ta ɗan yi shiru ta numfasa ta ce "Ƙaddara ce ta haɗa ni da shi muka yi aure, ban san sunansa na gaskiya ba, ni ba shi sunan Sayyid. Ba shi da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa kuma." Nan Nana ta warware mata komai da ya danganci aurenta da shi, duk da ba komai ta gaya mata ba. Nene ta yi shiru sannan ta jinjina kai ta ce "Ikon Allah, dama shi ne Sayyid ɗin da ki ke ambata idan kina bacci? Amma Nana iyayenki sun yi ganganci. Ke yanzu ko hotonsa ba ki da shi. Kawai Nana ta ɗaga mata kai alamar eh. "To ai Nana zama guri ɗaya a haka, ba zai sanya a gano shi ba, dole sai an taɓuka wani abin, wane ƙabilar ne ko shi ma ba ki sani ba?" Nana ta yi shiru ta rasa ma me za ta cewa Nene.
Nene ta ce "To shikenan, amma ba kya ganin yakamata gidanku su san kin haihu?"
"Nene babu buƙata goben jaririn nan nake hange"
"Haka ne, to Ubangiji Allah ya kyauta, amma wannan lamarin naki akwai sarƙaƙiya Nana. Amma ba komai Allah ya taƙaita"
Nana ta amsa da Amin.
Baba yana tsakar gida yana shan kunu, sai ga Suwaiba ta fito, gaba ɗaya ta zama wata iri kamar shiri-shiri. Ta kalli Baba ta cake a ƙofar ɗaki ta ce "Nana fa ta haihu" ba shiri ya ajiye ludayin kunun ya kalli Suwaiba ya ce "In ji wa? Waye ya gaya miki?"
"Nanan ce ta gaya mini"
"Ke a ina ki ka ganta?"
"Ina bacci a ɗaki, na ganta da jaririn, ta ce mini haihuwa ta yi"
Wani uban tsaki Baba ya ja, saboda jin shiritar da Suwaiban take faɗa. Dan da fari ya zata ma da gaske take yi.
Alhaji Zailani ne tare da Malam Gambo, su na zaune fuskarsa ɗauke da damuwa. Malam Gambo ya ce "Wai duk me yasa ka damu ne har haka? Ka na tsoron ƙungiya ta sake cewa ka kawo jininka ne?" Alhaji Zailani ya numfsa ya ce "Abu na farko burukana biyu, ɗaya ya cika na durƙusar da Fatuhu. Amma samun yarinyar nan ya zame mini bala'i, ƙarewa ma da yake azzaluma ce mai baƙin hali, wai ta tafi Nijar. Ban kuma san ta yadda zan yi na same ta ba. Babu yadda ban yi na samu yarinyar nan ba, amma duk lokacin da na yi wani yinƙuri a kanta, sai hankalina ya gushe. Yanzu babban tashin hankalina wannan jarababbiyar Sa'a, ashe ita ma ƙoƙari take yi, ta mallaki jinin yarinyar nan. Ga shi na rasa dalilin da ya sanya Shukura take ta zargin likitan da yake yi mini aiki, da kisan jaririnta."
Malam Gambo ya numfasa ya ce "Ka tattara nutsuwarka guri guda, nasara na buƙatar kasada a kowane lokaci. Ita waccan yarinyar ka jingine batunta a yanzu tukuna, tun a wancan lokacin ai na gaya maka tana ɗauke da wani shu'umin aljani ne mai taurin kai a kanta ba zai taɓa barin burinka ya cika ta daɗin rai a kanta ba. Ba kai kaɗai ba koma waye kuwa. Sannan ƙungiya idan ta sake buƙatar jini, sai ka bayar da na ɗaya daga 'ya'yanka ko namijin, ko kuma ita yarinyar taka a bar jaririn nata ba shikenan ba. Kawai ya zuba wa Malam Gambo ido, idanunsa suka yi jawur sai dai bai ce komai ba ya tashi ya fita.
Ɓangaren Sagir kuwa, sosai yake sintiri tsakanin Kano da Abuja, saboda Yusra, saboda soyayyar da suke yi ma a yanzu, ba su yi ta a lokacin da suke saurayi da budurwa ba. Wata irin muguwar shaƙuwa suka yi, da shaiɗan ke barazanar shiga cikin lamarin nasu, ga shi ya rasa ta inda zai tunkari Hajiyarsa da batun, domin ba son Yusra suke yi ba. Shukura tuni ta daɗe da gano inda ya dosa, amma ta zuba masa ido ta ga ina ne ƙarshen alewar zai kasance.
Kwanci tashi asarar mai rai, Nana ta yi wata guda da haihuwa, Nene ta tattara ta daina fita gurin sana'arta. Sai aikin kula da Nana, ga shi kullum da sassafe kan ta ci komai, ake kawo nonon raƙumi fresh Nana ta sha, sannan ta ci Abinci. Nana tana kwance tana bacci da azahar, saboda yadda Muhsin ba ya barin su bacci da daddare, saboda ba ya ɗaga wa Nana ƙafa da tsotso, ga kuka sai dai Nene ta taya ta riƙonsa. Yana gabanta yana bacci, ita ma ya ɗauke ta, ta ɗaga kai ta ga ya shigo ta ƙofar ɗakin. Tana kwance ba ta motsa ba ta ga ya ƙaraso ya zuba musu ido, daga ita har Muhsin, ya sanya hannunsa ya shafa gashin jaririn, ya durƙusa ya sumbaci gishin yaron. Sannan ya kalli Nana idanunsa cike da hawaye. "Sayyid, yaushe za ka zo ka ganmu? Mu na buƙatar ka a kusa da mu, dan Allah kar ka tafi ka bar mu" Ya kama hannayenta ya riƙe a cikin nasa, sai dai bai yi magana ba. Sai da aka jima sosai yana murza yatsun ta a hankali sannan ya ce "Ma vie" "Na'am" "Gangar jikina ta kasa samun nutsuwa, rayukanmu su na kewar juna, ki kula mini da rayuwata da ke jikin ki, da jikin ɗa na, ina ƙaunarku Nana" Riƙe Sayyid ta yi, tana kuka tana "Dan Allah Sayyid kar ka tafi ka bar mu, mu na buƙatar ka a rayuwarmu, dan Allah Sayyid, dan Allah" Nene ta yi shiru tana kallon yadda Nana ta riƙe ta tana kuka. Da yake sheshsheƙar Nanan ta jiyo, ta taho ɗakin tana zuwa ta tarar da Nana tana nema ta danne jaririn. Bayan ta ɗauke shi ne, Nana ta riƙe mata riga. Nene ta zuba wa Sarautar Allah ido, Nana ta buɗe idanunta a hankali ta ga yadda ta riƙe Nene gam. A hankali ta cika ta tana sunkuyar da kai. Sai dai ta ɗaga kanta tana kallon ɗakin, tana jin ƙamshin turaren Sayyid a hancinta. Nene ba ta ce mata komai ba, ta goya Muhsin ta fice da shi daga ɗakin. Nana ta lallaɓa, ta tafi gurin da kayanta suke, ta bubbuɗe jakar kayan shafe-shafensa, da take ta adanawa tana kallon su tana jin daɗi. Sai dai a wannan karon hawaye take yi, tare da jin zuciyarta tamkar za ta buga. Ta zazzage kayan ta din ga bin su da kallo, ta ɗago Azurfarsa da ya ba ta, ta ce ya yi mata yawa, ya ce ta ɗaure da zare ta yi sarƙa da shi. A hankali ta furta "Da mutuwa ka yi na san Allah ne ya karɓe ka babu yadda na iya, da aurenmu ne ya ƙare shi ma na san wannan ƙaddara ce, ba a kaina a ka fara ba. Amma ban san a wani hali ma ka ke ba, duk a inda ka ke ina fatan Ubangiji Allah ya sanya ka na cikin aminci da kwanciyar hankali Sayyid.
Yana zaune a kujerar da ke cikin ɗakin, da abu a cikin kofin yana sha a hankali. Murmushi ya gaza barin fuskar Sultan, ya zauna a kusa da shi yana murmushi ya ce "Alhamdillah, sauƙi yana samuwa Imam, ya jikin naka?" Ya kalli Sultan ya mayar da hankali ya ci gaba da shan shayin da ke cikin kofin hannunsa ba tare da ya furta komai ba. Cikin damuwa Sultan ya ce "Har yanzu ba ka gane ni ba Imam?" Har yanzun dai bai yi magana ba, bai kuma fasa shan shayinsa ba. Sultan ya riƙo hannunsa guda ɗaya cikin nasa, ya ce "Imam ka kalli Abbanka mana, ka yi magana ko hankalina zai kwanta" Ya waiwaya ya kalli dattijon. Cikin murna Sultan ya ce "Ka na jin abin da nake faɗa?" Ya yi shiru yana ci gaba da kallonsa, bai yi magana ba. "Ka yi mini magana ka ce wani abu mana" A hankali ya zame hannunsa daga na dattijon, ya tashi daga kan kujerar ya koma gadonsa na marasa lafiya ya kwanta. Sultan ya yi shiru yana kallonsa, sai dai ya rasa abin da yake yi masa daɗi. Kar a ce ƙwaƙwalwar ɗan sa ta taɓu. A yadda alaƙarsa da ɗan sa take, ba ƙaramin abu ne zai sanya ya yi masa haka ba. Kwanciyarsa ke da wuya, ya fara jijjiga, a rikice Sultan ya nufe shi. Sai dai ya fara kururuwa yana faɗin "Wuta zafi" Matawalle ne ya shigo ɗakin da sauri, suka rufu a kansa, Sultan ya din ga tofa masa Addu'a. Har ya daina jijjigar. Abdou ya kalli Sultan ya ce "Abubuwa fa kamar ƙara rikicewa suke yi, mene ne abin yi yanzu. Ina tsoron a bi diddigi a gano halin da yake ciki fa"
"A fita da shi waje kawai, wataƙila a dace a can, ni na kasa gane kan abubuwan da ake yi masa a nan"
"A wannan yanayin, da ihun da yake yi"
"Abduou" Sultan ya kira sunansa cikin ɗaga murya.
Abduou ya risunar da kai ya ce "Za a shirya duk abin da yakamata, za a yi abin da ka ce".
Jamila ce take ta juyi a kan katifarta, tana jiran reply ɗin Abba, saboda chatting suke yi. Sai dai shiru bai yi reply ba har ta gaji ta yi bacci. Da safe sai gurin sha ɗaya ta tashi daga bacci, da yake tana fashin salla. Ta duba wayar, ta tarar da tarin messages ɗin sa da kiran waya, ta share ta je ta yi wanka ta shirya. Daga tsakar gida ta ce "Mama ni na wuce"
"Ba za ki tsaya ki karya kumallo ba?"
"Zan ci a can, sai na dawo"
Suwaiba na tsakar gida, tana goge kaushi, ta ce "Jamila"
"Yes" Jamila ta amsa.
"Nana fa na gaishe ki, ba ki ga jaririnta ba"
Jamila ta ce "Ai dama ke da Nanan, kan ku ba ƙalau ba, shi yasa ke kaɗai take kawowa ziyara a mafarki." Sai kuma ta ɗan yi shiru cikin damuwa ta ce "Allah sarki Nana, ko ta na wani halin yanzu oho" ta ɗan ja numfashi ta sauke ta fita, tana ci gaba da tunanin Nana.
A falon Hajiya Sa'a ta tarar da Abba yana zaune yana Video game. Tana shigowa ya yi murmushi ya tashi zaune ya ce "Sannu da zuwa" Ta murguɗa masa baki ta nufi bedroom ɗin Hajiya Sa'a. "To ai ba ta nan" ya yi maganar yana miƙewa ya bi bayanta. "Me na yi miki ne ki ke hararata? Na tura miki saƙo duk ba reply" Ta kalle shi ta ce "Ba jiya na yi ta jiranka da daddare ba, ka ƙi kula ni"
"Eyya, bacci ne ya kwashe ni, ki yi haƙuri"
"Ba wani nan, da budurwarka ka ke chatting ka share ni" Ya waro ido ya ce "Wallahi ba ni da wata budurwa bayan ke, kema kin san ba na iya kula 'yan mata kema da ƙyar ai na gaya miki ina son ki" sai kuma ta tuntsure da dariya ya taya ta shi ma. Za ta yi magana kawai Hajiya Sa'a ta shigo falon, ta gan su a zaune a kan dining suna hira har da dariya, alhalin a gabanta basar da juna suke yi.
Ɗan saroro Hajiya Sa'a ta yi tana kallon su, Jamila cike da bariki ta ce "Mummy sannu da zuwa" "Yauwwa" ta amsa a taƙaice. Abba ma kam kasa magana ya yi gaba ɗaya.
Ya yi wa Jamila sallama ya fita, sai dai Hajiya Sa'a ta yi kicin-kicin ta ƙi sakar wa Jamila fuska gaba ɗaya.
Jamila kuwa ta din ga ƙissimawa a ranta, muddin abin da take zargi ya zama gaskiya game da Hajiya Sa'a za ta ba ta mamaki ba kaɗan ba.