Kenza eBookz

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 47

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 47

Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 47: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 47. * Kwanci tashi asarar mai rai, Nana ta kwana arba'in cif da haihuwa. Sai…

3,232 words

* Kwanci tashi asarar mai rai, Nana ta kwana arba'in cif da haihuwa. Sai da Nene ta kwana goma sha biyar, ba ta fita gurin sana'arta, saboda jegon Nana sai dai yaranta su je, sai bayan kwana sati biyun sannan ta fara fita, shi ma da wuri take dawowa. Ranar da Nana ta kwana arba'in, ta saka Nana ta shirya suka je gidan su Hajara. Sun yi murna sosai da sosai da ganin Nana, duk da ta rame, amma yanayin ta akwai nutsuwa a tattare da ita. Auwwalu ya ɗauki Muhsin ya ce "Ohh Allah ka bamu mu ma ɗan kyakykywan jariri, ka ga ɗa kamar na larabawa" Hajara ta amsa da "Amin dai"

Nene ta ce "Ka ga fitsararru, babu ko kunyar idona?"

Auwwalu ya ce "To ai addu'a muka yi. Ban da rashin kara ma, a ƙa'ida fa ɗan nan, sunana na ya kamata a saka masa"

Nene ta ce "Saboda kai ɗin waye?"

Nana ta yi murmushi ta ce "Yaya Auwwal, ai sunanka ne da shi, laƙanin ne kawai ba ɗaya ba"

Ya yi murmushi ya ce "Kuma fa haka ne" sosai suka karrama su Nana. Da suka tashi tafiya ma, sai da suka kuma bawa Jaririn kyautar kuɗi da kaya, a so samu Nana ba ta so suka karɓa ba, amma Nene ta amshe. Da suka dawo kuma ta zagaya da Nana gidajen maƙwabta, suka gaggaisa. Tun da suka doshi wani gida, Nana ta din ga jin gabanta na faɗuwa, kamar ta cewa Nene ba za ta shiga ba, amma ta kasa. Ta din ga addu'a tare da fatan Allah ya rufa mata asiri ya sanya ba wani abin ne zai faru da ita ba, ko Ƙaisar ne zai dawo ya hana ta sukuni a ƙasar da ba ta da kowa ba. Ko da su ka shiga cikin gidan, sai Nana ta fara jin sanyi, yana ratsa ta a hankali. Aka shimfiɗa su tabarma, da ƙyar Nana suka gaisa da mutanen gidan, ta nemi guri ta zauna. Sai ta daina gane abin da Nene suke faɗa ma. Ta din ga jiyo muryar su Nene can nesa da ita, hakan ya tabattar mata da gidan akwai wani abu. Wani irin sauti ta din ga ji, a cikin kunnunwanta, kamar gurnani kamar nishi. Ta daina ganin su Nene gaba ɗaya, sai wata mata da ta fito ta tunkaro ta. Ga matar babba da ita amma jikinta ɗauke da zaren mahaifa daga cibiyarta dogon zaren har kan wani baƙin ƙwarangwal da yake bin ta, hannun ƙwarangwal ɗin kuma mahaifa ce yake lasa da jini da komai a jiki. Jikin Nana ya hau tsuma, ta din ga kallon matar da ƙwarangwal ɗin, tana son yin addu'a ta kasa. "Nana" ta ji muryar Nene ta kira sunanta. Sai ta buɗe ido ta kalli Nene. "Tashi mu tafi yamma ta yi" Nana ba ta motsa ba, ta ga matar da ta gani yanzu tare da ƙwarangwal ta nufo ta. Matar gidan ta ce "Kar ki kuskura ki taɓa ta, yi haƙuri dan Allah ba ta da cikakkiyar lafiya ne" ta yi maganar tana kallon Nana. Sai dai matar ba ta tsaya ba, ta yi kan Nana gadan-gadan. Wani irin azababben ƙarf ya zo wa da Nana, ta ji zuciyarta na tafasa jira take matar kawai ta ƙaraso gare ta, ta illata ta. Amma Nene ta danƙi hannun Nana, ta hana matar ƙarasawa gurin Nana ta ce "Ke Ashura, meye haka ne? Ba ki ga baƙuwa ba ce?" Matar cikin wata irin harɗaɗiyar magana da zubar da yawu ta ce "Magana zan yi mata, ta saka wannan ƙwarangwal ɗin ya daina bina" gaba ɗaya suka kalli Nana. Ɗaya matar ta ce "Wani ƙwarangwal ɗin, rabonta da magana ma fa ta fi sati biyu"

Kawai matar ta saka kuka, lallai sai ta je gurin Nana, ta cewa ƙwarangwal ya daina bin ta. Nene ta ja hannun Nana suka yi waje. Sai dai ta ji jikin Nana tamkar gawa saboda sanyin da ya yi. Su na zuwa gidan Nana ta nemi guri ta zauna, ba ta cewa Nene uffan ba. Can bayan magariba, sai ga matar da su ka je gidanta ta zo, Nene ta ce "Gaji lafiya kuwa?"

"Dan Allah Nene ki taimaka mini, ko 'yar nan taki za ta zo mu je gurin Ashura, sai ihu take tana burgima tun da ku ka tafi"

"Ta zo ta yi mata me?"

Gaji ta ce "A'a ban sani ba ko akwai wani taimako... "Taimakon me?" Nene ta katse ta.

"Kin san dai Ashura ba hankali ne da ita ba, wataƙila almatsutsan haukanta ne kawai ya tashi take wannan abubuwan, ki tafi babu inda Nana za ta zo" Gaji ta fita jiki a sanyaye, dan idan ta matsa sai Nene ta balbale ta da masifa. Nene ta ajiyewa Nana nonon raƙumi, da abincin dare, amma ta ƙi ci saboda sanyin da take ji. Nana ta haɗa kanta gwiwa, tana jin yadda jikinta yake tsuma ta ce "Sayyid sanyi nake ji"

"Ke Nana" Nana ta ɗago ido ta kalli Nene. "Ba za ki ci abincin ba ne?"

"Na ƙoshi, amma dan Allah Nene mara lafiyar can ta can gidan, ta faɗi wani abu a kaina ne?"

Nene ta ce "Za ki ba ta magani ne?" Sai Nana ta yi turus tana kallon Nene, gabanta yana tsananta faɗuwa. "Ba ta ce komai a kan ki ba, amma idan kin amince za ki yi magana da aljanin nata, ko ki bata magani kamar yadda ake so ki yi, sai mu je" Gaban Nana ya faɗi, ta bi Nene da kallo cike da mamakin, yaya aka yi Nene ta san wannan maganar, alhalin ko da wasa ba ta taɓa gaya mata ba.

"Nana mamaki ki ke yi? Ai ba a banza na yarda na karɓe ki muke zaune a cikin gidan nan ba da ni da ke. Tun zuwanku na ga abubuwan da na gani a tattare da ke. Na ga inuwar rauhanin aljani a tattare da ke, kuma da alama ko dai kin gamu da baƙin aljani a hanya, ko kuma kin yi rayuwa da shi, saboda akwai warinsa a tattare da ke, saboda yana ta'amalli da jini, har ma warin nasa yana ƙoƙarin danne, ƙamshin rauhanin da yake tattare da ke. Sannan akwai alamu na alaƙa mai ƙarfi a tsakanin wannan rauhani da Aljanin da yake tattare da ke. Jiri ne ya fara ɗibar Nana, cikin wani yanayi mai kama da fitar hayyaci ta ce "Nene, wace ce ke? Ya aka yi ki ka san abin da ban gaya miki ba? Ki gaya mini ke wace ce?" Nana, masu iya magana suka ce mugu shi ya san makwantar mugu. Ni na yi harkar bori da bayar da magani, ni baƙin aljani ma na gada daga gurin mahaifina. Ya azabtar da ni ya hana ni aure, na ƙi bayar da magani ya shanye mini ƙafafuwa, na daina al'ada na fara hauka tuburan. Sai da na bayar da magani, bayan wasu shekaru, na gaji na ce zan ajiye, saboda kullum cikin larura nake, ga shi ya sanya na saka a yi ta zubar masa da jini. Ya sake burkita ni, ya hana ni aure, na koma ciwon hauka yau na kuturce gobe na daina gani, anjima na kasa tafiya. Ya buɗe mini ido nake ganinsu muraran a siffofi na ban tsoro, nake jin maganganun su a cikin kunnuwana. Ya ɗauke ni ya kai ni can wata uwa duniya ya yasar da ni, na yi ta gararamba sannan ya gaji ya dawo da ni. Ko ya saka na yi ta zubar da jini babu ƙaƙƙautawa. Duk inda muka je neman magani, sai a ce sai dai na haƙura na ci gaba da bayar da magani. Da ƙyar wani mai magani ya raba ni da shi, ta hanyar yin amfani da wani aljanin. Ya kafa sharuɗɗa sai da aka yi masa yanka, da sauran abubuwa dai na sharuɗɗa sannan Allah ya raba ni da shi. Bayan mun rabun ma, da ƙyar na samu na yi aure, shi ma dai kusan kullum cikin rigima da miji, na zo babu haihuwa, sai rigima sai dai ya dage ya ƙi rabuwa da ni. Sai daga baya Allah ya bani haihuwar ɗa namiji, daga nan ban sake haihuwa ba. Yarona yana can ƙasarku Nigeria. Mijina kuma Allah ya yi masa rasuwa, ni kuma na ci gaba da sabgogina ban sake wani auren ba, duk da wasu lokutan haryanzu abubuwan na taɓa ni." Nana tana Libraryn Ƙaisar, daga can nesa take jiyo maganar Nene. Kai tsaye gurin mudubin nan ta nufa, cike da fatan ta sake ganin ko fuskar Sayyid ne, amma ta tarar da mudubin wayam, sai ma baƙi ƙirin da ya yi. Ta daɗe a tsaye ta zura wa mudubin idanun amma babu alamar wani abu zai bayyana a mudubin ta gani. Ta hango littafin da ta fara karantawa a yashe a ƙasa, inda ta yasar da shi, hakan ya tabattar mata da Ƙaisar ba ya cikin ɗakin karatun nasa na wani lokaci. Ta sanya hannu ta ɗauki littafin, ta nutsu ta ci gaba da karantawa. "Idan ka bari tsoro ya ɗarsu a cikin zuciyarka, to tabbas ba za ka iya cimma abin da ka ke hari ba. Tun da kawar da mahaifinka bai yi maka wahala ba, wannan ma ba zai gagare ka ba, ka kashe su ɗaya bayan ɗaya, ka yi mulki cike da izza ka tara sojoji da runduna da za ta razana duniya". Ire-iren waɗannan kalamai na ziga da kambamawa, ya sanya matashin saurayin jin kansa na daɗa kumbura, tare da ji a ransa zai aikata komai domin cimma burinsa. Ana tsaka da jimamin mutuwar shugaba a garin, ya ci gaba da tattara sojojin sa na ƙarƙashin ƙasa, da shirya hanyoyin da zai bi gurin kawar da dukkanin wanda ka iya kawo masa tangarɗa. Ganin babu abin da ake yi a farkon littafin, ban da tsagwaron zalunci, zubar da jini da rashin tausayi ko imani, tsananin ƙiyayya da kisan kai a tsakanin 'yan uwa, duk don kowa yana kwaɗayin ɗarewa gadon mulki. Ga bautarwa ta fitar hankali ga na ƙasa ba tare da afuwa ko sassauci ba, sai Nana ta ji gaba ɗaya littafin ya ishe ta, ba ya yi mata daɗin karantawa, har ma gara na tarihin Buda a kan wannan.

A hankali ta buɗe idonta, da ya yi mata nauyi, ta ga gari ya yi haske, ta shafa gefenta ta ji babu Muhsin, kawai ta yi zaton ko Nene ce ta goya shi, dan idan Nene na nan, tsakaninta da Muhsin shayarwa ne kawai, ita take yi masa komai kamar ita ta haife shi. Tana ɗaga kai ta ga wannan mahaukaciyar, riƙe da Muhsin a hannunta, gefenta ga wannan ƙwarangwal ɗin baƙi ƙirin da shi kamar an gasa shi da wuta. Ihu Nana ta saka a cike da matuƙar razana, ba wai dan ta ga ƙwarangwal ɗin ba, sai ganin ɗan ta a hannun mahaukaciya ga aljani a bayanta yana ta lasar jinin jikin mahaifar da ke ɗauke da zaren cibi.

Ayshercool 08081012143 Nece ce ta fito hankali a tashe, ta shiga ɗakin da Nana take ciki, ta tarar da Ashura a tsaye rungume da jaririn Nana. A matuƙar fusace ta ƙarasa ta karɓe Muhsin, ta ajiye shi a kan katifa, ta ce "Uban me ya shigo da ke ki ka ɗauke shi?"

Cikin tsoro ta girgiza kai ta ce "Babu komai"

"Uban me ki ka yi masa?"

"Wallahi ban yi masa komai ba"

Nene ta shaƙe ta, ta ce "Ki gaya mini me ki ka yi masa?"

Cikin kuka ta ce "Wallahi ba abin da na yi masa"

"To me yasa ki ka shigo?"

"Wallahi son shi kawai nake yi"

"Ɗan ki ne da za ki ce son shi ki ke yi, wani abin za ki yi masa kenan" cikin kuka ta ce "A'a Nene"

Nene ta ce "Wallahi na sake ganinki a gidan nan, sai na yi miki shegen duka, babu ke babu jaririn nan"

Nana ta saka hannu ta ture Nene, ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri ki daina dukanta, ai ta ce babu abin da ta yi masa"

Nene ta ce "Ba dan kin farka ba fa? idan ta yi masa wani abin, ni ina banɗaki ke ki na bacci fa?"

Nana ta ce "In sha Allah babu abin da za ta yi masa. Zo mu je na raka ki gida"

Nene ta ce "Nana ki rabu da ita ta tafi gidan"

Nana ta ce "Nene zan raka ta, ni duk inda na ga mai irin larurar nan, tausayi yake bani"

Nene ta ce "Can ta matse muku ke da ita, ku je can ku ƙarata, ni dai na sake ganinta a gidan nan, ta taɓa yaron nan, sai na yi mata shegen duka da itace" Nana ta kama hannun Ashura da ke ta rarraba ido, suka fita daga gidan.

* Hajiya Sa'a ta tattara hankalinta a kan Abba da yake zaune a gabanta a bedroom ɗin ta.

"Magana nake yi maka, ka ɗago ka kalle ni, mene ne a tsakaninka da yarinyar nan Jamila?"

Ya ce "Ba komai"

"To ka buɗe kunnenka da kyau ka saurare ni, na sanya katanga a tsakaninka da ita, babu kai babu ita, kar ka kuskura na ji wata magana a tsakaninka da ita, kuma matar aure na samo maka ita, zan baka lambarta ka kira ta ku gaisa. Ka je ku gana, kuma nan kurkusa za a yi komai a gama. Ka fita daga harkar Jamila, ka fita daga harkar ta na gaya maka na kuma nanata maka, idan ba haka ba daga kai har ita ba za ku ji daɗin abin da zai biyo baya"

Ya jinjina kai jiki a sanyaye ya ce "To in sha Allah zan kiyaye"

"Tashi ka bani guri" ya yinƙura ya tashi jiki a sanyaye, ya fice daga ɗakin, zuciyarsa na wani irin zafi. Bai taɓa zaton za ta nuna adawarta da maganar haka ba, ganin yadda take da Jamila.

Ko da ya tafi ɗakinsa, kiran Jamila ya shigo wayarsa, jiki a sanyaye ya ɗaga wayar ya ce "Hello Jamila"

"Jamila kuma, yau ba ƙanwartaka?"

"Afuwan a yi mini afuwa"

Cikin damuwa Jamila ta ce "Yaya lafiya kuwa?"

"Lafiya ƙalau, ina fatan kin je gida lafiya, ba ki bari na dawo na mayar da ke ba"

"Ina sauri ne, kuma ba na son wahalar da kai gaba ɗaya. Ko dai Mummy ta yi maka magana a kan ka daina kula ni ne?"

Da sauri ya ce "A'a ai kin san ba za ta hana ba ko kaɗan"

Jamila ta ce "To shikenan, amma dan Allah in anjima ka zo na ganka"

Ya yi murmushi ya ce "Ni ki ke son gani?"

"Eh mana, ko na haƙura?"

"Ina ni na isa, ina yin sallar isha'i za ki ganni a bar ƙaunar Abba"

"To abin ƙaunar ƙanwarsa, sai ka zo" ya sauke wayar yana murmushi, sai dai yana sauke wayar ya ɗan yi shiru cikin damuwa, bayan tuna abin da Mummyn ta gaya masa na kashedi.

Muhsin ɗin Nana tamkar ana hura shi, saboda girma ya cika ya yi fam. Ga shi fafur Nana ta ƙi bari a yi masa aski, ta cewa Nene babansa ma ba ya aski, dan haka a bar masa sumarsa.

Nene ta fara jinginar da shi, a tsakanin fululluka tana koya masa zama.

Nene ta ce "Nana bari na hanzarta na fita, ki kula da yaron nan dan Allah, ban da shiririta, ko ki ƙyale shi yana kuka ki yi masa banza"

Nana ta ce "To Nene ki goya abinki ki tafi da shi mana, tun da kullum ba na yi muku abin arziki"

"Kya dai ji da shi, ni dai na gaya miki, kuma wallahi mahaukaciyar can ta shigo, ki ka ɗauki yaron nan ki ka bata, sai na ɓata muku rai daga ke har ita"

Nana ta ce "Ni dai ba wannan ba, Nene so nake na fara bin ki gurin sana'ar nan, zaman gidan nan yana damuna, ba akin fari babu na baƙi" Nene ta ce "Nima na yi wannan tunanin Nana, amma bai kamata a ce kina matar aure mu din ga fita bakin titi babu iznin mijinki ba, kin san halin maza wasu ba kirki ne da su ba, mussaman ke ga ƙuruciya ma. Sam ba mutuncinki ba ne ba, dama jira nake yi Muhsin ya ƙara ƙwari, na nema miki ko gurin ɗinki ne ko makamancin haka, ki din ga zuwa sannan mu ga ta ina za mu fara laluben mijinki, amma tun da Muhsin ya yi ƙwari, mu fara lalubawa zaman haka ba zai yiwu ba, motsi ya fi laɓewa ai"

Ta jinjina kai ta ce "To shikenan Nene, duk yadda ki ce Shikenan, na gode sosai da sosai Ubangiji Allah ya saka miki da mafificin alkhairi"

Nene ta ce "Amin yarinyar kirki"

Fitar Nene babu jimawa sosai, sai ga Ashura ta faɗo gidan. Nana ta ba ta ce mata ta shigo ɗakin, amma ta ƙi.

Nana ta tashi ta fita ta shimfiɗa mata tabarma, sannan ta ɗaukko Muhsin, ta zo ta zauna ta ba wa Ashura shi. Ta karɓe shi tana buɗe baki cikin murna, ta kalli Nana ta ce "Ina son yaron nan"

Nana ta ce "Da gaske?"

Ta jinjina wa Nana kai, ya jima a hannun Ashura, sannan ta ba wa Nana shi, Nana ta mayar da shi ɗaki ta kwantar. Sai dai tana dawowa ta tarar da Ashura a tsaye tana kuka, gefenta ga ƙwarangwal ɗin nan. Nana ta ce "Me ka ke buƙata ne?"

"Ki na ganina kenan?"

"Eh ina ganin ka, sannan wannan mahaifar da ka ke lasa mene ne ma'anar hakan? Tun da ƙazanta ce"

Ya ce "Lokacin da aka haife ta ne, da za su dawo daga Asibiti, aka manta mahaifar, shi kuma mai motar ya yar a bola, ni kuma na tsinta na biyo ta."

Cikin damuwa Nana ta ce "Amma baka kyauta ba, tun da babu wanda ya yi maka wani laifi ka ke yi mata abin da ka ke yi mata".

Ya ce "Ai mu ba sai an yi mana abu ba, idan mu na son mutum. Kin ga ke ma da ki ke addu'a wasu lokutan, ba dan tasirin Addu'a da ki ke yi, da kuma tsoron uban duƙusa da ake yi ba, da bataliyar da za su shiga jikinki da yawa. Saboda da guda ɗaya ya yi hanya, wasu ma suke samun kafar shiga jikin mutum. Kuma Allah ya taimake ki, Sarkin baka ya rage tasirin uban duƙusa a tare da ke, da duk inda muke sai kin din ga ganinmu, kuma muraran za ki din ga ganin cututtuka da sihiri a zahiri, sai kin kusa haukacewa idan ba ki bayar da magani ba. Kawai dai shi yana lallaɓa ki ne"

Nana ta ce "Yaya aka yi ka san Ƙaisar, kuma ka san Sarkin baka?"

Ya ce "Jaddul Jinn babu wanda bai san shi a nahiyar nan ba, dan haka sanin jikansa uban duƙusa ba abin mamaki ba ne. Sarkin baka kuma shi ne ya mayar da ni ƙwarangwal, mun taɓa artabu da shi da na shiga jikin sata mesa, ya ƙona ni. Kuma na ga kin haɗa jini da shi, ba yadda na iya da ke ne kawai, da sai na ɗauki fansar abin da aka yi mini a kan ki" Nana ta yi shiru jikinta ya yi sanyi, su na gama maganar Ashura ta juya ta fita ya bi ta a baya. Nana ta din ga jinjina azabar naci da riƙo irin na halittun nan.

BAYAN WANI LOKACI.

Readers Also Read