Kenza eBookz

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 48

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 48

Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 48: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 48. Girman ɗan mutum babu wuya, in ji masu iya magana, Muhsin ya cika watanni…

3,338 words

Girman ɗan mutum babu wuya, in ji masu iya magana, Muhsin ya cika watanni bakwai, Nana na zaune tare da Nene. Nene ta kai ta gurin koyon girke-girke, yanzu kuma tana zuwa koyon ɗinki. Nana har mamakin yadda Nene take yi mata take. Sai dai ta fara karaya da yanke tsammannin haɗuwa da Sayyid. Nene ce ta shigo gidan, bayanta goye da Muhsin, yana ta mamular cukui. Nene ta sauke shi ta zaunar da shi ta ce "Wannan ɗan naki, idan bai nuna mini halinsa ba, ai ba za a ce ɗan buzaye ne ba, mun taho hanya ya ga raƙuma, wai sai dai mu tsaya ya kalli raƙumi, sai zillo yake a bayana yana ihu, sai da na tsaya na ɓata lokaci yana kallon raƙuma yana miƙa musu hannu. Ya cire hular kansa ya yar, kowa ya ga kansa da wannan kitson sai an tambayi mace ce ko namiji. Ke ma da taurin kan tsiya, kin ƙi bari a yi masa aski, kuma kina yi masa kitso kamar wani mace."

Nana ta yi murmushi ta ce "Ni babu ruwana, ba shiga faɗanku zan yi ba, balle na ji kunya ku gwale ni"

Shi kuwa cukun hannunsa kawai yake mamulawa a bakinsa, Nene ta juya za ta fita tsakar gida ya rarrafa ya bi ta yana kukan ta ɗauke shi.

Nana ta sake yin murmushi ta ce "Na haifa wa Nene ɗa" Tana jiyo rigimarsa da Nene, ya hana ta aiki, idan ta hana shi wannan ya koma wancan. Nana ta din ga dariya daga ɗaki, aka jima kuma Nene ta zuba masa shayi sai kuma ya nutsu, guri ɗaya, yana sha yana wasa da gashinsa. Ashura tana son zuwa gidan Nene gurin Nana, amma tana tsoron Nene, ga Muhsin da ya ganta yake sanya ihu, tsoronta yake ji.

Ɓangare guda kuma, zuciyar Nana na saƙa mata ya kamata ta gusa ta bar gidan Nene, saboda ta ja lokaci a gidan. Amma tana tuna tijarar Nene, da rashin sanin ina za ta dosa. Ba ta san wani irin mutum ne Sayyid ba, mutumin da za a yi alfahari da haɗa nasaba da shi ne ko akasin haka, duk da tana kyautata masa zato. Shi yasa take ɓoye wasu abubuwan, dan kare mutuncin sa da rashin sanin a yaya za ta haɗu da shi.

Washegari da safe Nana ta tashi, ta jiyo hirar Muhsin a tsakar gida. Ta tashi ta fita kar ya yi wata ɓarnar, sai ta gan shi a lungun kitchen ɗin Nene, ya juyo bayansa, kamar dai wani abun ya samu yana wasa da shi. "Kai babyn Sayyid, me ka yi a gurin nan, taho ka sha" bai waiwayo ba ya ci gaba da abin da yake yi. Nana ta nufe inda yake. Wata irin narkekiyar mesa ta gani a cikin lungun, shi kuma yana ta duƙunƙuna kanta da hannu bibbiyu yana hira. Ji ta yi tamkar an ɗaure ta tamau, ta kasa gaba ta kasa baya, kuma ta kasa magana. Mesar ta miƙe sai ga Ƙaisar ya bayyana a gurin. Muhsin ya ɗaga kai yana dariya yana kallon Ƙaisar. Ƙaisar ya ciro wani abu a kwalba, ya buɗe bakin Muhsin ya zuba masa, Nana ta rikice amma ta kasa motsa kowace gaɓa ta jikinta. Muhsin ya kama rigar Ƙaisar yana wasa da ita, yana yi yana kallon Ƙaisar ɗin. Ƙaisar ya saka hannu ya shafa kitson kan sa, ya miƙe tsaye ya ɓace. Sai da ya ɓace Nana ta iya motsawa, amma duk da haka ta kasa zuwa inda Muhsin yake, sai shi ne ya rarrafo ya nufo inda take. Ta saka hannu da ƙyar tana dudduba jikinsa, ko wani abin ya yi masa amma jikinsa lafiya ƙalau. Ta shiga fargaba da tsoron me ya ba shi ya sha?. Ta ja jikinta ta koma jikin bango, ta fara shayar da shi, tana roƙon Ubangiji Allah ya kare mata yaronta daga sharrin su Ƙaisar da kowane irin nau'i na shaiɗani.

Nene na fitowa, ya cika Nana ya tafi gurinta, sai da ya gama wasansa, ya sake komawa gurin Nana. Tana shayar da shi, tana ganin fuskar Sayyid a tattare da shi, dan hatta idan ya ɓata rai, tamkar mahaifinsa. Sai dai tunani da tsoron abin da ka iya samun sa, ya gaza barin zuciyarta, tun daga ganin da ta yi wa Ƙaisar da shi. Ta so gaya wa Nene, amma ta ja bakinta ta yi shiru ba ta gaya mata ba. Sai dai tun gabatowar magariba, take jin sanyi. Ta shige ɗakin ta ƙudundune, ta bar su Nene. Tana tsaye a sahara, sai dai a wannan karon babu ƙurar Saharar, ta hangi Sayyid a zaune yana shan shayi, shikaɗai. Ta taka sannu a hankali ta ƙarasa inda yake, ya ɗago ya kalle ta yana murmushi. Ta zauna a kusa da shi, ta ce "Ka warke ne?"

"Da sauƙi, na yi nesa da inda nake jin ciwon, kuma na yi nisa da gurin waɗanda za su kashe ni"

Cikin damuwa ta ce "Ni fa?"

Ya ajiye kofin hannunsa, ya rungumota jikinsa yana kallon fuskarta, idanunsa cike da hawaye ya ce "Yadda ruhinki da gangar jikinki, suka gaza samun nutsuwa, tun bayan rabuwarmu haka nima nawa suka gaza samun nutsuwa. Ina kewarku gangar jikina ta kasa samun nutsuwa, ina buƙatar ki a kusa da ni" Ita Nana gaza riƙe nata hawayen ta yi, tuni ta ba su dama suke zuba.

Ya girgiza mata kai tare da cewa "Kar ki manta, muddin kina raye kuma ina raye a doron duniya, gangar jikinmu ba za ta samu nutsuwa ba, sai mun haɗu. Ina kewar ki ma vie." Ya yi maganar yana ƙanƙame ta a jikinsa. Ta buɗe idonta tana ji yadda hawaye ya jiƙa mata fuska. Ta tashi zaune da ƙyar, ta yi shiru ta tafi tunani. "Nana ba a bori da sanyin jiki, ci gaba da zaman ki a gidan nan, tamkar ki na matsawa dattijuwar nan ne da take ɗawainiya da ke, kuma ba za ki taɓa haɗuwa da Sayyid ki na zaune guri ɗaya ba, yakamata ki motsa".

Ta tashi ta yi alwala, ta yi sallar magariba da isha'i, ta idar ta shiga ɗakin Nene ta ɗaukko Muhsin, ta dawo da shi ɗakinta saboda ko zai farka cikin dare. Nana ji ta yi tamkar ta fice daga gidan a cikin daren nan, amma ta kasa saboda ba ta san ina za ta nufa ba, a wannan uban daren.

Ta haƙura da niyyar da Asubar fari, ta tashi ta fice, amma bacci mai nauyin gaske ya yi awon gaba da ita, sai da aka kusa idar da salla, Nene ta tashe ta yi sallar Asuba.

Tana idar da sallar kuma, Muhsin ya tashi ya saka rigima, Nene ta ɗauke shi suka tafi ɗakinta.

Tun da wuri yaran Nene suka zo, suka ɗauki kayan Abinci, amma Nene ta ƙi fita ranar ta wuni a gida, yaranta ne suka je suka sayar da Abincin.

Abu kamar wasa a jere kwanaki huɗu Nana tana yinƙurin guduwa, amma Nene ta kasa ta tsare tamkar ta san abin da Nana take shiryawa.

* Jamila ta nuna wa Hajiya Sa'a tamkar ba ta san ita ta taka wa ɗan ta Abba burki a kanta ba, Hajiya Sa'a sai shirin bikin Abba take yi, yayin da gefe guda kuma Jamila ta yi blocking ɗin sa, ta daina ɗaga wayarsa gaba ɗaya.

Dama idan Hajiya Sa'a na nan, ba ya iya yi mata magana, da zarar ta fita kuma sai Jamila ta kulle ƙofar sashen. Ya rasa abin da yake yi masa daɗi, har layi ya canza ya kira Jamila, amma tana ɗagawa ta ji muryarsa ta kashe.

Ga shi tun da Hajiya Sa'a ta fuskanci abin da yake tsakanin su, ta daina yawan fita ta bar Jamila a gidan, idan ma fita za ta yi sai dai su fita tare. Sai dai yau Jamila ba ta jin daɗi, dan haka Hajiya Sa'a ta fita ita kaɗai, saboda ta sakankance Abba yana can kasuwa.

Awa guda da tafiyarta, Jamila na kan doguwar kujera tana bacci, ta ji tsayuwar mutum a kan ta. Ta buɗe idonta a hankali ta ga Abba a tsugune a gabanta yana kallonta.

Tashi ta yi zaune tana tsuke fuska tare da gyara zaman rigarta za ta tashi.

Cikin zafin nama da tsoron rashin sabo, ya riƙe hannunta ya ce "Dan Allah Jamila ki tsaya ki saurare ni" ya yi maganar cikin marairaicewa kamar zai yi kuka.

"In saurare ka ka ce mini me Yaya Abba? Dan Allah ka rabu da ni." Ta yi maganar itama idanunta fal hawaye, saboda ba ta taɓa sanin ta kamu da matsananciyar soyayyar Abba ba, sai yanzu da Hajiya Sa'a take ƙoƙarin farraƙa su.

"Jamila dan Allah ki fahimce ni, kin san a son raina ba zan auri wata ke ga ki na bar ki ba, wallahi Jamila ina son ki, ban taɓa son wata 'ya ba sai ke"

Ta kalle shi hawaye na zuba daga idonta ta ce "Ko ma mene ne, ai yanzu aure za ka yi, ka rabu da ni dan Allah"

Girgiza kai ya yi cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali, ganin yadda take zubar da hawaye, zai yi magana ta fizge hannunta ta shiga ɗaya falon, bai yi ƙasa a gwiwa ba, ya sake bin ta yana ƙoƙarin rarrashinta.

Sai dai kash, garin ya rarrashi Jamila, sai shaiɗan ya buga musu ganga su ka taka rawa, duk da Jamila ta fuskanci cin zarafi da keta haddi a ƙungiyarsu ta asiri, a wannan karon ma tsoro da rashin sabo suka yi tasiri a a gare ta, duk da a nasa ɓangaren ma haka ne.

Daga shi har ita suka saka kuka mai cike da nadama da dana sanin abin da suka aikata.

Maganganun Nana suka din ga dawo mata daki-daki, na nasihar da ta din ga yi mata a baya. Duk da babu wanda ya san halin da Nana ne ciki, a tsawon wannan lokacin kusan shekara guda, amma gara Nana da ita, Ko ba komai Nana aure ta yi, ita kuwa fa da fari bokaye da aljanu sun kwanta da ita, a wannan karon kuma ruɗin soyayya da sharrin shaiɗan.

"Jamila, dan Allah ki yi haƙuri, ki kuma rufa mini asiri, ke ma kin sa hakan ba halina ba ne ba, amma duk yadda zan yi, zan aure ki, ni na fara aikata ɓarnar nan, kuma zan gyara ta in sha Allah"

Jamila ta kalle shi ta kawar da kai, tana jinjina lallai Abba bai san komai ba, tun da bai iya gane ba budurwa ba ce ba, duk da bayan abin da Hajiya Sa'a ta kai ta aka yi mata, bazama ta yi neman magungunan gyara.

Ya lallaɓata ta gyara jikinta, ta nemi guri ta kwanta, ya rasa abin da yake yi masa daɗi. Ya koma part ɗin sa ya rufe ƙofa, kawai ya fashe da kuka. Bai taɓa tunanin aikata zina a rayuwarsa ba, ba ta taɓa burge shi ba, bai kuma taɓa kawo ta a ransa ba. Sai dai yau ya wayi gari da aikata ta dumu-dumu. Sai dai wani abin mamaki duk da abin da ya faru a tsakanin su, bai daina jin matsananciyar ƙaunar Jamila ba. Ya rasa dalilin da ya sanya Mummy ba ta son alaƙar su, duk da irin kusancin da yake tsakaninta da Jamilar.

A kwance Hajiya Sa'a ta dawo ta tarar da Jamila. Ta ce "Daughter haryanzu jikin ne? Ko Asibiti za mu je ne?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a Mummy na sha magani ai"

"Yakamata ki warke, mun kusa zuwa taron ƙungiya fa na shekara, lokaci ya kusa"

Kawai Jamila ta gyaɗa kai.

"Ga shi kuma haryanzu babu wani labari da ki ka samo, a kan 'yar uwakki, dan haka sai ki shirya sadaukar da jini"

Jamila dai ta yi shiru, tana jin kamar ta kashe tsinnaniyar matar ta huta.

*

Nana na zaune tana shayar da Muhsin, Nene tana gefe tana lissafa kuɗin da aka kawo mata daga gurin sayar da Abincinta.

Nana ta numfasa ta ce "Nene wai me yasa kwana biyu ba kya fita gurin Abinci ne?"

Nene ta kalle ta ta ce "Na fita ki samu damar guduwa ko?"

Nana ta yi turus tana kallon Nene.

Nene ta yi murmushi ta ce "Yarinyar nan ki na wasa da ni, tuni na gane duk wani take-taken ki ai, jira nake yi na ga iya gudun ruwanki. Ke yanzu idan ki ka fita gidan uban wa za ki je? Ki na da tabbacin za ki iya sake haɗuwa da mutanen da za su kula da ke ne? Ko an gaya miki kowa ne zai iya yin taimako?

Kin tattara kayanki gaba ɗaya, kina ɗauke ɗanki daga ɗakina, jira ki ke yi ki samu dama ki gudu, to ki tafi duk inda za ki tafi, amma ba za ki tafi da jaririn nan kina gararanba a gari ba, tun da duk ƙoƙarin da nake yi a kan ki ba kya gani. Kina zaune a nan na saka ana ta yi mini cigiyar masu gadi da suke zuwa Nigeria, ko akwai wanda ya san mai suna Habu ko Sayyid ki ka ce sunansa ko wa? Anma ba kya gani, to ki fita ki tafi duk inda ki ka ga dama, tun da ba ki da kan gado, kuma ba ki san darajar igiyoyi ukun da ke kan ki ba"

Nana ta sha jinin jikinta, da faɗan da Nene take yi mata. Ta ce "Dan Allah Nene ki yi haƙuri, na ga na ɗora miki ɗawainiya ne ga shi haryanzu ina zaune babu wani labari a kan sa".

"Ni na ce kin ɗaura mini ɗawainiya ne uwar iya? Ki yi duk abin da ki ka ga dama"

Nana ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri ba zan sake ba" Nene ta yi mata shiru, daidai lokacin kuma Muhsin ya gantsarawa Nana cizo, da 'yan haƙoran da suka fara leƙowa.

A fusace ta dake shi a kan pampers ɗin jikinsa, ta cire shi daga jikin Nonon, ta zaunar da shi tana ƙara tsuke fuska tare da hararsa.

Sexy eyes ɗin sa irin na mahaifinsa ya zuba mata, yana kallonta ko ƙiftawa ba ya yi, gaba ɗaya ya rikiɗe fuskarsa ta koma ta Sayyid sak, farar fatarsa ta yi jawur.

Nene ta ce "Yaka yaron kirki, ka ƙyale ta da halin ta, shi ne za ki huce a kansa, ai ni na yi miki ba shi ba"

Ya rarrafa ya koma jikin Nene ya kwanta yana ci gaba da kallon Nana. Sai kuma jikinta ya yi sanyi ta ji zuciyarta ta yi mata nauyi da abin da ta aikata, ba tare da duba ƙanƙantar ɗan yaron nata ba.

Ta shige ɗakinta ta mayar da kayanta da ta haɗe guri ɗaya inda suke. Wayarta ta ɗaukko da babu layi a cikinta, ta duba jakarta ta ɗaukko memorynta ta mayar kan wayar, ta fara duba hotunan Sayyid da ke ciki. Har da hotunan Haidar ɗan gurin Shukura a cikin wayar, da hotunanta na aure da aka yi mata da wayar.

Gaba ɗaya ta ji tana kewar ƙasa Nigeria, amma hakan bai sanya ta ji za ta iya komawa a yanzu ba.

Tunaninta ya katse bayan da ta ji muryar wata ƙawar Nene a tsakar gida, wadda ita ta yi hanyar kai Nana gurin koyon girke-girke. Amma Nana ta ƙi fitowa.

Hira suke yi da Nene, take ba ta labarin ma'aikata ake nema, wanda suka iya girki sosai a wani restaurant, na wata Hajiya a can cikin birnin Maraɗi.

Nene ta ce "Ba na yi wa Nana irin wannan harkar ne, saboda mutanen banza, ba dan haka ba ai da na ce ta je, tun da ta iya girki sosai" Matar ta ce "To ai a ɓangaren girki kawai za ta zauna, su na buƙatar kuku amma mai tsafta wadda ta iya girki, kuma tana biya sosai kin san buzayen nan kamar ba su san ciwon kuɗi ba, buzuwa ce mai gurin" Nene ta ce "Ai kin ga tana da yaro, shayarwa take yi, ai da na ce a kaita, amma idan za su ɗauke ta da yaron shikenan".

"Anya kuwa, gaskiya ba na tunanin haka, ba ma za su yadda ba. Idan ta tafi a ƙalla za ta iya yin wata, ba ta zo gida ba, za a ba ta komai a can. bari na tashi na tafi dama tsayawa na yi mu gaisa sai anjima"

Suka yi sallama matar ta tafi.

Nana ta fito da sauri ta ce "Nene, ina son zuwa gurin abincin buzayen nan"

Nene ta ce "Kin yarda mijin naki buzu ne kenan? Daga an ce gurin buzuwa kin rikice za ki je, bayan da kin ce mini ba ki san ƙabilarsa ba, Allah dai ya shirye ki."

Nana ta yi shiru, tana mamakin yadda aka yi Nene take iya gano ta idan ta yi mata ƙarya.

Nana tun dukan da ta yi wa Muhsin, juyin duniya har la'asar bai ƙara waiwayarta da sunan ta shayar da shi ba.

Sai da ta ji sun cika, sun fara damunta, sannan ta ɗauke shi ta ba shi, amma fafur ya ƙi karɓa, ta kaɗa ta raya ya ƙi sha.

Nene tana kallon su, ta ƙi magana, ta dama masa kunu ta haɗa da nono ta zaunar da shi ta ba shi ya sha, ya ci gaba da wasan sa.

Nana ta ga sun mayar da ita saniyar ware ma. Har garin Allah ya waye, bai saurari Nana ba.

Ta sake ɗaukarsa, saboda yadda nonon ya cika, yake yi mata ciwo, amma fafur yaron nan ya ƙi sha.

"Dan Allah yaron kirki ka yi haƙuri ka sha, ba zan sake dukan ka ba, dan Allah ka sha ba ka isa yaye ba" Nana ta yi maganar cikin damuwa.

Nene ta kwashe da dariya, ta ce "Kin ga ki ƙyale yaron nan, ina ga fa ya yi zuciya ya yaye kansa, sai dai yi haƙuri"

Kamar Nana za ta yi kuka ta ce "Nene wata takwas sai ya yaye kansa? Ya yi wuri ai"

"To ba ke ki ka janyo koma mene ne ba?, tun da kin ce da babansa yake kama komai da komai, wataƙila har halayensa ya ɗaukko, kuma wataƙila wannan abin da ya yi akwai abin da yake nunawa bamu gane ba. Tun da yana shan kununsa, yana rarrafensa, ki rabu da shi kawai. A haɗa sabaya da sauran saiwoyi, ki yi ta sha saboda kar su lalace".

Kamar Nana za ta yi kuka ta ce "Nene wata takwas fa"

"To ai ga ki nan ga shi. Sai ki ba shi ya sha ai"

Da Nana ta ɗauke shi da nufin, ta shayar da shi, sai ya hau zunduma ihu,yana turjewa sai dai ta ƙyale shi.

Nana ta din ga jinjina yadda aka yi, ɗan wata takwas ya san ya yi zuciya da abu.

Sai da aka kwana huɗu, Nana ta ga da gaske ya yaye kansa, iyaka ya zo jikinta ya yi wasan sa ya tafi.

Nene ta ce "Nana ki daina damuwa fa, girmansa tubarkallah da ƙiriniyarsa kamar ta ɗan shekara guda ce, ki rabu da shi kawai, daga yanzu idan za ki yi magana ki din ga yi masa da girmamawa, ki daina yi masa tsawa, manya ba sa son wargi. Kuma ki din ga duba darajar sunan da ki ka sanya masa" ta yi maganar tana yi wa Muhsin rawa.

"To Nene sai na bari ya lalace ba zan ce masa bari ba?"

"A'a ban ce kar ki ce masa bari ba, amma a wannan yanayin shi sarki ne, abin da yake so haka za ki yi haƙuri ki yi masa. Da kin tsaya a zare masa ido kawai da haɗe rai, amma saboda na yi miki faɗa, ki ka haɗa masa da duka, kuma ki ka ƙwace ki ka dungurar da shi, dole ya bar miki abin ki ai".

Nana kalle shi yana ta wasa da kofi, yana bugawa a ƙasa, shi ma ya ɗago ya kalle ta. Sayyid ta tuna lokacin da ya ritsa ta yana yi mata kashedin a kan daina yi masa tsawa ko ɗaga masa murya.

Wani guntun murmushi ya suɓuce mata.

Nene ta ce "Ni kuwa Nana ga shawara"

Ta ce "To Nene"

Readers Also Read