Kenza eBookz

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 49

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 49

Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 49: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 49. "Kamar yadda ki ke faɗa motsi ya fi laɓewa, na ce ko dai za a jarraba ki…

3,171 words

"Kamar yadda ki ke faɗa motsi ya fi laɓewa, na ce ko dai za a jarraba ki je gurin aikin nan, na harkar dafe-dafen ko Allah zai sanya a dace. Duk da ba na jin a jikina, masu kuɗi a cikin buzaye masu katafaren gurin abinci, za su iya tafiya aikin gadi, amma bamu san ina rana za ta faɗi ba"

Nana ta ɗan yi jimm sannan ta ce "Ban san ya zan yi ba ne, tun da kin ga ga Muhsin. Ko za su din ga bari na je na dawo kullum?".

Nene ta ce "Ki na ji fa ta ce sai ki yi wata ba ki zo gida ba, kuma akwai tazara a tsakaninmu sosai, kuma ba zai yiwu ki tafi da Muhsin ba, ba za su yarda ba. Amma ga shawara idan kin ga kin yarda da ni, ki bar mini Muhsin a nan, ki je ko ai

kin na wata uku ki yi, ko Allah zai sanya a dace, sai ki ci gaba da cigiyarsa a gurin."

Ayshercool

08081012143 Nana ta yi turus, tana kallon Nene.

Nene ta ce "Ba zan yi miki dole ba, dan kuwa wannan magana ce da kowacce uwa sai ta jinjina girmanta da nauyinta. Sai dai ni ba zan takura miki ba kuma ban ce sai kin yadda da ni ba, ko mene ne za mu yi shi ne a gaban hukuma, mu je mu yi yarjejeniya mu saka hannu sannan ki tafi. Ban san dalilin da Allah ya sanya ya haɗa ni da ke ba, duk rashin son mutane na, ki ka shiga raina ba nake tausayinki ke da yaronki. Har ga Allah ina fatan ki haɗu da mijinki ko danginsa, ki samu ki koma gida ki nutsu ki kula da yaronki. Kamar yadda na gaya miki ne, ba zan yi miki dole ba, ki je ki yi shawara idan kin amince shikenan, idan ba ki amince ba babu wani abu, ni dai fatana Ubangiji Allah ya bayyana abin da ki ka fito nema". Nana ta yi shiru, ƙwaƙwalwarta gaba ɗaya ta ɗauki caji da tunani daban-daban.

Jamila kuwa tun da ta je gida, Mama take tambayarta ko lafiya ta ganta wani iri, amma ta ce mata babu komai. Ta shiga ɗaki ta nemi guri ta kwanta, sallolinta kawai ta yi na magariba da isha'i ta sake kwanciya. Gaba ɗaya abin Duniya ya gama damunta, dana sani da takaici duk ya cunkushe mata zuciya. Wayarta ce ta fara ringing, ta duba ta ga baƙuwar lamba ce, jikinta ya ba ta Abba ne, ta ɗaga kiran ta saka a kunnenta. Muryarsa ƙasa-ƙasa ya kira sunanta ya ce "Ya jikin naki?"

"Da sauƙi" ta amsa a hankali hawaye na ci gaba da gangarowa kan kumatunta.

"Dan Allah Jamila ina ƙara ba ki haƙuri, kuma ki dubi girman Allah ki rufa mini Asiri, ke ma kin san hakan ba halina ba ne ba. Wallahi na rasa inda zan sanya zuciyata na rasa abin da yake yi mini daɗi. Yanzu haka zazzaɓi ne a jikina. Dan Allah ki yafe mini Jamila, na san koma mene ne duk laifina ne. Amma in sha Allah kamar yadda na yi miki alƙawari zan aure ki Jamila, wallahi ina son ki, duk abin nan laifin Mummy ne amma ki yi haƙuri ki yafe mini" Jamila ta ci gaba da kuka, ta kasa ce masa komai, ya ƙara ruɗewa ya ce "Dan Allah ki yi mini magana, dan Allah ki yafe mini idan ba ki yafe mini ba na san har na koma ga Allah, ba zan samu nutsuwa ba" Ya yi maganar yana kuka mai cike da nadama tamkar ƙaramin yaro. Duk yadda Jamila ta so jin haushinsa sai ta kasa, tabbas ita shaida ce wannan ba halin Abba ba ne, dan da halinsa ne da ba zai din ga wannan kukan ba, zai ga ya ci bulus ne kawai.

"Yaya Abba na yafe maka, mu haɗu mu nemi yafiyar Allah, sannan ka daina kukan nan dan Allah, ka sha magani ka kwanta. Kuma Asiri idan na tona kaina na tonawa ba kai ba, Ubangiji Allah ya yafe mana"

Ya tashi zaune a kan gadonsa, cikin damuwa ya ce "Da gaske kin yafe mini Jamila?"

"Eh Yaya Abba, sai da safe, kaina yana ciwo sosai"

"To na zo na kai ki Asibiti ne?"

Jamila ta ce "A'a, na sha magani ina jin bacci ma, sai da safe" ta katse kiran tana ƙara duƙunƙunewa a cikin bargo.

Wata irin ajiyar zuciya ya din ga yi, ya nemi guri shi ma ya kwanta, zuciyarsa fal tunani daban-daban.

*

Nana hankalinta ya rabu kashi-kashi, a jikinta ba ta jin Nene za ta cutar da ita, duba da yadda take ɗawainiya da ita da ɗanta, tamkar ita ta haife ta. Sai dai ta yaya za ta iya ta tafi ta bar ɗan ta, da matar da babu dangin iya babu na Baba a tsakanin su. Sai dai tabbas akwai buƙatar ta gusa, ta yi wani yinƙuri, domin ci gaba da ƙoƙarin haɗuwa da mijin nata, amma ba ta ji ta gamsu da wannan shawarar ba. Sai dai tun da suka yi maganar nan, da ta kwanta take mafarki ga ta a gurin girke-girken, tana cikin gurin girkin, ta waje sai ga din ga jiyo muryar Sayyid yana magana. Idan ta fita sai ta neme shi ta rasa, sai dai ta ci gaba da jin muryar ta sa, nesa da ita kaɗan, sai dai ba ta san daga wane ɓangaren muryar tasa take ba. Sai ta yi irin wannan mafarkin sai ta farka. Ta rasa abin da yake yi mata daɗi, kawai sai ta ci gaba da addu'a a kan lamarin, ta juya ta ci gaba da bacci, sai dai babu tsammani sai ga ta a ɗakin karatun Ƙaisar, an yi mata gyara sosai, an ƙara yawan litattafan da suke ciki. Ya saka mudubinsa a gaba, yana ta zuba masa wani ruwa yana wanke shi. Bai ce wa Nana komai ba, har ta gaji da tsayuwa, ta ɗan yi gyaran murya. Ya ɗaga kai ya kalle ta. Ta ce "Sannu da aiki" "Yauwwa" ya amsa yana tashi tsaye.

Ta ce "Kwana biyu ina ka shiga ne?" Ya ɗaga kai ya kalle ta ya mayar ya sunkuyar yana ɗaukar wani littafi.

"Amm dama ina ta son na ganka, na tambaye ka, sannan na roƙe ka alfarma. Dan da kai da Giyaz da duk wani mai son ɗaukar fansa a kan zuriyarmu, ya ɗauka a kaina, dan Allah ku ƙyale mini yarona. Na ga rannan ka ba shi wani abu da ban san ko mene ne ba, dan Allah kar ku yi masa komai" Bai ko motsa ba, balle ta sanya ran zai yi mata magana.

"Ƙaisar ka yi magana ma dan Allah" "Na ce miki ne? Ko har kin manta abin da ki ka faɗa a kaina, saboda abin da na yi wa mahaifina a kan na kare ki?"

Sai kuma Nana ta yi shiru, ta sha jinin jikinta.

Ya wurgo mata littafin nan da ta fara karantawa, ya ce "Ga wannan ki ci gaba da karantawa, wataƙila zai yi miki amfani a gaba" Ta kalli littafin ta kalle shi, ta ce "Me yasa ka amince na karanta wannan littafin, wancan kuma ka hana ni karantawa? Ni ba zan iya ci gaba da karantawa ba, babu komai a ciki sai tashin hankali da zubar da jini na tsagwaron rashin tausayi da adalci, ni bai burge ni ba, ba zan karanta ba"

"Ko? Amma idan an yi magana sai ki nuna kamar babu wata halitta da ta kai ɗan Adam tsarki da tsoron Allah. Allah ya karrama ɗan Adam a kan dukkanin halittunsa. Amma ba duk ɗan Adam ne mai tsarkin zuciya ba. Wannan zubar da jinin da kashe-kashen da yake rubuce a cikin littafin nan, da gaske an yi su, domin cimma buƙatar Duniya, kuma haryanzu ana kan yi ma. Abu ne da ya faru wani ƙarni a baya, kuma abin yake ta bibiyar zuriyar har wannan zamanin. Na ce ki karanta kin ƙi, kin ce ba kya so shikenan ba zan yi miki dole ba, amma bari ki ga wani abu. Ya ɗauki littafin ya buɗe cikin wani feji, ɓangare ɗaya na bangon littafin zane ne, ɓangare ɗaya kuma bayanin yadda taswirar zanen take ne. Ya haska littafin a jikin mudubin. A nan take hoton ya bayyana a jikin mudubin, wannan ɗakin da take ganinta a ciki ita da Sayyid shi ne ya bayyana a jikin mudubin, ba iya haka ba har ƙamshin da gurin yake yi ta fara ji a hancinta. A rikice ta ce "Nan gurin? Dama ina son sanin ina ne, yaya aka yi muke zuwa gurin nan ni da Sayyid, kuma idan abu ya faru a gurin kamar gaske." Ƙaisar ya rufe littafin ya ce "Ai kuma kin yi wa kan ki, ba zan bayar ba. Ya jefa littafin sama ya ɓace ɓat ita kuma ta tashi daga baccin.

Kwana biyu Jamila ba ta je gidan Hajiya Sa'a ba, saboda jikinta da ya matsa, idan Abba ya kira wayarta a kashe, ga shi ba ta zuwa gidansu, shi ba abin ya tambayi Mummy ba. Yana kwance a ɗakinsa, ya tura mata saƙo. "Hankalina a tashe yake ƙanwata, dan Allah ki yi mini ko flashing ne, hankalina na matuƙar tashe dan Allah ki ɗaga wayata" Ya tura mata saƙon, tare da ajiye wayar. Hajjya Sa'a ce ta shiga ɗakin nasa, ta iske shi a kan kujera. Yana ganinta ya tashi zaune. Daga tsaye ta ce "Abba ba zaka fita bane? Baka fito ka karya ba, kuma baka fita kasuwa ba meyafaru ne?"

Ya girgiza mata kai ya ce "Babu komai fa"

"A'a akwai wani abu, na kasa gane kan ka 'yan kwanakin nan, hatta shirin bikinka nikaɗai nake abina, me yake damunka? Duk saboda Jamila ne?"

Ya girgiza kai ya ce "Ba kin ce ba kya son alaƙarmu ba, ni kawai ba ni da lafiya ne" ta yi shiru tana nazartarsa, kawai ta yi ƙwafa ta fice daga ɗakin. Ya koma ya jingina, ya lumshe idanunsa, sai kiran Jamila. Ya ɗauka ya katse kiran ya kira ta cikin azarɓaɓi ya ce "Ƙanwata lafiya kuwa? Ba kya ɗaga wayata ko haryanzu kina fushin ne?"

Cikin numfarfashi ta ce "A'a Yaya Abba, ba ni da lafiya ne haryanzu"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ya aka yi ba ki gaya mini ba? Kina gida ne?"

"Eh" ta amsa muryarta ƙasa-ƙasa.

"To shirya gani nan, bari na zo mu je Asibiti"

"To Yaya Abba, na gode" ta ajiye wayar da ƙyar. Hankalinsa ya yi mummunan tashi, a zatonsa aika-aikar da ya yi ce, ta sanya mata rashin lafiya har haka. Da sauri ya zura kaya, ya ɗauki mukullin motarsa ya yi waje ya tafi gidansu Jamila. Yanayin yadda Jamila ta fito, tamkar ya je ya ɗaukko ta, fuskarta duk ta kumbura, da alama tana jin jiki sosai da sosai. Ya buɗe mata gaban motar ta shiga. Cikin tausayawa ya ce "Sannu ƙanwata, haka jikin naki ya yi ba ki gaya mini ba?" "Ba na son tayar maka da hankali ne, kai ma ba ka da lafiya, amma Mama fa ta kai ni Asibiti" Gabansa ya faɗi ya ce "Allah ya sa ba ta gane komai ba"

Ta girgiza kai ta ce "Babu abin da ta gane, zazzaɓi ne fa kawai"

A tsorace ya ce "Jamila ko ciki ne?"

Ta kalle shi, sai da ta ji kamar ta yi dariya, duk da halin da take ciki. "Tun kan hakan ta faru ai nake rashin lafiya, ba wannan ba ne ba, ba wani ciki".

Ya sake cewa "Amma duk da haka kamar ya assasa miki ciwon, amma bari mu je Asibitin" haka ya ja motarsa su ka bar layin.

Safiyya ce ta tarar da Hajiya Sa'a ta cika ta yi fam, tana zaune a falonta. Da kyar Hajiya Sa'a ta iya amsa mata sallamarta. Ta zauna a kusa da Hajiya Sa'a ta ce "Mummynmu maganin kukanmu, lafiya kuwa na ga ranki a ɓace?"

"Ba dole ki ganni a haka ba? Da gaske fa Abba son Jamila yake yi, nema yake ya bujire mini, kin ga yadda duk ya damu saboda na raba su. Ga bikinsa na ƙaratowa da Yasmin.

Maman Khairat ta tuntsure da dariya ta ce "To meye a ciki, idan tana son sa ki bar su mana"

Hajiya Sa'a ta kalle ta ta ce "Amma ba ki da hankali, yarinyar da shugaban ƙungiya suka kwanta da ita, sai Abba ya auri ragowa? Ba ma wannan ba, kar ki manta idan ƙungiya ta buƙaci ta bayar da jininsa fa, shikenan ta bayar da jinin tilon ɗan nawa?"

Maman Khairat ta ce "Na fahimce ki Mummy, da wasa nake yi miki, amma maganar gaskiya yanzu haka kan na taho ma, na ga motar Abba a unguwarmu, kuma na san ba ku da kowa a unguwar, dan haka gurin Jamila ya je"

Cikin matsanancin ɓacin rai ta ce "Gurin Jamila kuma? Yarinyar nan ta zame mini masifa da bala'i ko? Maganinta zan yi, wallahi sai ta rabu da Abba, ko ita ta haifar mini shi"

Maman Khairat ta ce "Ki yi dai a hankali, kin san halin yaran zamanin nan" Hajiya Sa'a ta ci gaba da huci, tamkar macijiya saboda takaici.

Maman Khairat ta ce "Ina dai ƙara gaya miki, ki bi komai a sannu, kin san halin yaran zamanin nan, sai su baki mamaki. Shi kansa Abban duk yadda yake yi miki biyayya, idan ba ki yi wasa ba, a wannan karon tsaf zai bujire miki".

"Ai ga alamu nan ina gani, amma ni zan sanya wa Abba doka, na hana shi abu, amma ya zagaye ya je ya aikata? Shikenan, na san matakin da zan ɗauka. Da ni suke zancen.

Alhaji Fatuhu ne zaune a harabar gidan sa, a kan kujera, ya kan ɗan iya dogara sanda ya tashi tsaye yanzu. Idan aka taimaka masa har harabar gidan yake iya fitowa, duk da idan jikin ya tashi kuma, sai ba ya iya hakan ko kaɗan. Yana zaune a harabar gidan, yana kallon ƙaramin ɗan sa na gurin Fadila, yana ta wasa da Ball, yana jin yadda ƙaunar ɗan ke ratsa masa zuciya. Gefe guda yana tausayin yaron nasa, dan bai taɓa iya saya masa abin naira biyar ba da kuɗinsa. Hatta abincin da suke ci, 'yan uwa da abokan arziki ne suke kawo musu, ga shi wanda ya sai gidansa ya ba du aronsa suke zaune a ciki, ya fara ƙishin-ƙishin ɗin yana buƙatar gidan.

Fadila ce ta ƙaraso tana murmushi ta ce "Daddy kallon Ball ka ke yi?"

Ya yi murmushi ya ce "Eh mana, yana ta in tashi mu yi tare, ina ma zan iya da ko sau ɗaya mun yi tare, no na saka shi farinciki"

Ta zauna a ɗaya daga cikin fararen kujerun, ta ce "A hakan ma, ka na sanya shi farin ciki ai"

"Fadila"

Ta tattara masa nutsuwarta ta ce "Na'am Daddy"

"Kin san wani abu?"

Ta ce "A'a sai ka faɗa"

"Ina yarinyar nan Nana?"

"Wace Nanan?"

Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Malamar Muhsin, da yake faɗa"

Ta ce "Ohh Allah sarki, na tuna ta"

"Mafarkinta nake yi"

Ta ɗan yi saroro ta ce "Mafarki kuma?"

"Eh Fadila, har aikawa na yi gidansu, a yi mini alfarmar a faɗa mini inda gidanta yake, wani abu nake gani da ya fara damuna"

Ta danne kishinta ta ce "To ka yi mini bayani mana"

"Kin dai san ni ba ma'abocin, biye-biye ba ne ba, da yarda da harkokin shirme da zai sanya na ji wani zai iya cutar da ni ba, amma a jere sau kusan biyar ina mafarki da ita". Cikin ƙosawa ta ce "Daddy ka yi mini bayani, ka na ta kwana-kwana da ni"

"Ganinta nake yi a mafarki, tana ce mini an yi mini sihiri, karo kusan biyar fa"

Fadila ta yi ajiyar zuciya ta ce "Kuma ka yarda?"

"Ba ma son na yarda na gazgata hakan, amma na ji kamar na fara amincewa, saboda yadda nake ganinta abin ya yi yawa, ya wuce a ce shirmen mafarki ne kawai."

Fadila ta numfasa ta ce "Ai ni tuntuni na zargi hakan, amma sanin halinka na rashin son irin wannan abubuwan, ya sanya ba na yi maka maganar. Ko wannan sauƙin da ka ke samu, na san tasirin addu'a ne. Dan kuwa Umma kuɗi take bayarwa ana sauke karatun Alqur'ani."

Cikin mamaki ya ce "Amma ke kina ganin, akwai wanda zai damu da ni, har ya iya yi mini sihiri? Ina azkar ɗina da addu'oina, gani nake sun wadace ni, babu wanda zai damu da ni ya yi mini wani sihiri."

Ta gyara zamanta sosai ta ce "A duk Duniya waye ya koyar da mu azkar ɗin? Na san za ka ce manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, amma an yi wa fiyayyen halitta sihiri, kuma ya kama shi. Daddy ka yi haƙuri da abin da zan faɗa maka. Kana ibadarka ta farilla daidai gwargwado, amma ba ka damu da nafilfili ba, da tsananta addu'a. Kana ganin Allah ya baka duk abin da ka ke buƙata, ba ka fiye tsananta addu'a da neman kariyar Allah ba. Sannan azkar da ka ke yi, kuma a yi shiri ya kama ka, ba ya nufin Allah baya kare ka, amma wataƙila jarrabawa ce daga gare shi, kamar yadda ya ce zai jarrabe mu, ba a fasa jarraba mai imani, kuma jarrabawa alama ce ta soyayyar Ubangiji. Allah ya jarrabe ka da cuta, ka nemi magani shi ma a cikin jarrabawa ne, amma Daddy ka naɗe ka dage, kai sai na Asibiti kawai, bayan akwai magungunan musulunci da suke na halal babu kauce hanya, idan an jarraba ba a san inda za a dace ba, amma ka ƙi ka ce kai sai na bature, na baturen kuma ba a gano komai ba, kame-kame kawai ake yi."

Ya yi shiru yana nazarin kalaman Fadila, ya numfasa ya ce "To yanzu mene ne abin yi? Kin ga yanzu bani da kuɗi, kuma irin wannan abubuwan sai da kuɗi".

"Kar ka damu, zan yi wa Kawu magana, shi ma ranar da ya zo duba ka, ai ya ce a yi na islamic, Alhaji Zailani ya ce ba za a yi ba. Da haka za tuntuɓe shi, in sha Allah ba zai gagara ba"

Alhaji Fatuhu ya ce "Allah ya sa, dama duk ina tsoron, kar a aikata abin da zai kauce wa hanya ne, amma na amince yanzu a yi ɗin"

Ta yi murmushi ta ce "To shikenan, yaya ita yarinyar an gano ta ɗin?" Ya girgiza kai ya ce "Ina fa, an ce wai ba ma ta ƙasar nan, amma ina ta mamakin dalilin da ya sanya nake mafarinta, kuma idan na farka sai na ji kamar a zahiri, shi ya sanya ma na fara yarda"

Fadila ta ce "To Allah ya sanya a dace" ya amsa da "Amin"

*

Ɓangaren Nana kuwa, gaba ɗaya kanta ya kulle a kan lamarin nan, kawai sai ta dasa addu'a, a kan idan da alkhairi a tafiyarta, Ubangiji Allah ya sanya mata son tafiyar, ya tsare mata Muhsin, idan kuma babu, Allah ya cire mata abin daga zuciyarta.

Readers Also Read