Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 50
Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 50: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 50. Kamar yadda ta saba ji haka ma wannan karon, ta ji muryarsa, da gudu ta…
3,360 words
Kamar yadda ta saba ji haka ma wannan karon, ta ji muryarsa, da gudu ta ajiye abin da take yi, ta nufi taga ta leƙa sai ta hango giftwarsa da doguwar riga baƙa a jikinsa. Da gudu ta fita daga gurin, ta nufe shi tana ƙwala masa kira, amma ya ɓace mata. Cike da takaici ta yi juyi, tare da jan guntun tsaki, kawai ta ji hancinta ya fara shinshino mata, ƙamshin wannan ɗakin na cikin dutse, da take ganinsi tare da Sayyid. Ta buɗe idonta a hankali, ta ji ana shafar cikinta a hankali, tare da yi mata numfashi a wuyanta. "Sayyid" ta furta a ɗan tsorace. "Asmyna, ina kewarki da yawa, gangar jikina na ta kewarki. Idan ina jin zafi babu mai bani sanyin da ki ke bani, babu wanda yake iya fahimtar kurman baƙin rayuwata, ki ƙaraso gare ni Please" ya yi maganar yana shafa wuyanta, tare da yin maganar ƙasa-ƙasa. Ta saka hannu ta shafa gashinsa ta ce "Ina ta gaya wa Allah Sayyid, ya san lokacin da ya dace ya haɗa mu, amma jikina yana ba ni, ina daf da kai in sha Allah" "Ki ƙaraso da wuri Asmyna, ina cikin matsananciyar buƙatarki" "Ina ta ƙoƙari Sayyid, kuma ina gaya wa Allah, na san zai haɗa mu a nan kusa, kuma ina roƙonsa ya kare mini kai a duk inda ka ke, na san kuma yana ji ya kuma amsa in sha Allah" "Nana, wai ba kya salla ne, gari ya fara haske fa" ta ji muryar Nene. Ta tashi tana mustustuke idonta, hancinta na ci gaba da jiyo mata sauran ƙamshin turaren nan. Da ta yi salla ta idar, ta je ta samu Nene a ɗakinta, suka gaisa.
Ta ce "Nene na amince"
"Da me?"
"Zan tafi gurin yin girkin nan"
Nene ta ce "Ina fatan ba wani ne ya matsa miki ba? Ko kuma kunyata ki ka ji ba ki ka ce za ki je?"
Nana ta girgiza kai ta ce "A'a, wa ma na sani na saba da shi, da zai ziga ni na ɗauka? Babu wanda ya ziga ni"
Nene ta ce "To shikenan, zan kira ta a waya na ji, idan ba a samu wata ba, sai ki je. Sai mu je gurin jami'an tsaro mu yi yarjejeniya mu yi rubutu, mu je a yi a gaban su Auwwalu ma da Hajara"
Nana ta girgiza kai ta ce "A'a Nene, na yarda da ke, abin duk bai kai haka ba ai"
Nene ta ce "A'a, haka kurum wani irin ki ka yarda da ni, ɗan mutum fa zan riƙe miki, a'a, mu je mu yi a rubuce, yadda jami'an tsaro ma za su din ga sanya ido, kar wani abu ya faru ma. Sai dai abin da Allah ya aiko na ƙaddara wannan ba yadda muka iya, kuma na san za ki yi mini uzuri a wannan. Amma idan aka yi haka kema sai kin fi sakewa, hankalinki ya kwanta.
Nana ta jinjina kai ta ce "Ni dai, bakin da zan yi miki godiya ba ni da shi, amma ina fatan Allah ya yi miki tukuici da abu mafi dacewa da abin da ki ka yi mini na alkhairi, a duniya da kuma Lahira"
"Amin Nana, ai ɗa na kowa ne, Allah ya tabattar mana da alkhairinsa, ya kuma bayyana miki mijinki da ahalinsa cikin aminci".
"Amin uwata ta kaina" ta yi maganar tana murmushi.
Sai dai tun da Nana ta amince za ta bar wa Nene Muhsin, ta fara jin kewar ɗan nata, ta din ga jin kamar ta ce ta fasa. Saboda kallonsa kawai na sanya mata matsanancin farinciki da nishaɗi, idan ta tuna mallakinta ne shi ɗin. Tana jin ko ba ta ga Sayyid ba tana da ƙaramin Sayyid, duk da tana fatan ta gan shi ɗin, ko ba komai al'umma sa kalli ɗan nata da kima da daraja.
Ko da Nene ta kira matar, Matar ta tabbatar wa Nene, akwai sauran space ɗin da Nana, za ta yi musu aiki, sai dai a saka ranar da za su tafi ta kai ta.
Haka nan fargabar Nana ta ƙaru, ta rasa murna take ko tsoro, duk da abu mafi rinjaye kewar ɗan jaririn ɗanta ne, da yanzu take ƙara shaƙuwa da shi,ƙaunarsa take ƙara shiga ranta. Tana jin tamkar ta fasa tafiyar nan, amma ƙasan zuciyarta tana jin tafiyar ta ta alkhairi ne.
*
Ɓangaren Abba kuwa, sai da aka yi wa Jamila ƙarin ruwa, typhoid ne ya yi mata mummunan kamu. Sai kuma damuwa da take ciki, jininta ya ɗan hau. Abba ya biya duk bills ɗin, ya janyo kujerar ɗakin, ya zauna a gaban gadonta, ruwan da aka saka yana shiga jikinta.
"Ko a kira Mama a waya a sanar mata ne?" Ya yi maganar cikin kulawa.
Ta ce "A'a, na gaya mata Asibiti zan je, ana gamawa sai ka mayar da ni gida"
Ya ce "To shikenan, mai zan sayo miki ki samu ki ci?"
"Ba na son cin komai, kawai kar ka matsa daga kusa da ni, ka zauna a nan" ta yi maganar tana riƙe hannunsa a cikin nata. Ji ya yi zuciyarsa ta narke, da matsanancin tausayin kan su, ya ce "Ina tare da ke matata, har abada in sha Allah" ta yi murmushi tana ƙara riƙe hannunsa. A hankali kuma ta saki hannun nasa, da tuna rashin dacewar hakan, sai dai wani irin abu mai wuyar fassara take ji, game da Abban. Yana kallon kiran Hajiya Sa'a, amma ya ƙi ɗagawa, kawai ya din ga jin zafinta. Har azahar sannan ruwan da ake saka mata ya ƙare, ya ɗauke ta a motarsa, ya yi mata sayayya sannan ya mayar da ita gida.
Sai da ya tabattar ta shiga gida, sannan ya kira Mummy.
"Sai yanzu ka ga damar ɗaga wayar tawa?"
"A'a caji take yi ne, ki yi haƙuri?"
"Kana ina ne?"
Ya ce "Na ɗan je wani uzuri ne, na zo ne?"
"A'a shikenan" ta ƙyale shi, bayan tuna shawarar da Safiyya ta bata, wato maman Khairat.
*
Kamar yadda Nene ta buƙata, sai da suka je gurin jami'an tsaro, suka yi yarjejeniya, aka rubuta da yaren hausa, French da kuma turanci, duk suka sanya hannu, a gaban su Auwwalu da jami'an tsaro.
Daga nan suka dawo gNene ta ba wa Nana wata 'yar madaidaiciyar Jaka, da za ta haɗa kayanta da za ta buƙata a ciki. Ta kalli Nana ta ce "Nana dan Allah ki kula da kan ki, duk da na san ke kamammiyar yarinya ce, ba mutuniyar banza ba, amma tunatar da mumini abu ne mai kyau, ki riƙe mutuncinki, ki kiyaye hakkin aurenki. Idan ki ka ga wani abu na ba dai-dai ba, ko wanda ya saɓawa addininki, a haƙura da sabgar nan. Kuma cikin hikima za ki din ga bincikawar,ba sai kowa ya fuskanci ainihin abin da ya nai ki gurin bax
Nana ta jinjina kai ta ce "In sha Allah Nene zan kula da kaina, ba zan ba ki kunya ba, ki taya ni da addu'a, Ubangiji Allah ya sanya zuwana ya zame mana alkhairi baki ɗaya"
"In sha Allah, addu'a ina nan zan ci gaba da yi miki ita da yardar Allah."
Nana ta haɗa kayanta, amma ji take kamar ta fasa tafiyar, amma ta ƙarfafi zuciyarta, ta hana hakan yin tasiri a ranta. Ranar Asabar, da safe matar ta zo domin tafiya tare da Nana.
Nene ta ce mata "Dan Allah gata nan amana, Hansatu, kar ki kai ta idan za a cutar da ita, kin ga yaro ne da ita ƙarami, dan Allah idan akwai matsala a gurin nan, gara ki saka a sallamo ta ta dawo gida."
Hansatu ta ce "Haba Nene, ya ki ke haka kamar ba ki yarda da ni ba ne?"
"A'a ba rashin yarda ba ne ba, 'yar amana ce shi yasa nake jadda da miki, ga kuma ƙaramin yaro da take da shi"
"Ba ki da matsala fa, ki kwantar da hankalinki"
Nana ta kalli Muhsin, da yake jikin Nene, yana wasansa, idanun Nana fal hawaye ta ce "My little Sayyid, zo ka yi sallama da Umminka" ya taso daga jikin Nene ya nufo Nana.
Hatta dogayen gaɓoɓin jikinsa, irin na Sayyid ne sak.
Ta rungume shi a jikinta, hawaye na zuba daga idanunta "Allah ka kula mini da ɗa na, Allah kar ka saka wani abin cutarwa ya same shi, Ubangiji Allah ka sanya na je na dawo na tarar da shi lafiya" ta furta a hankali ƙasa-ƙasa.
Ta ɗago ta kalle shi ta ga yana yi mata murmushi, ta sumbaci goshinsa, ta miƙe ta ɗauki jakar kayan nata, Nene ta rako su har bakin ƙofa, suka hau abin hawan da Hansatu ta zo da shi, suka tafi.
08081012143 Nana ta din ga waige, tana hango su Nene tare da Muhsin, har suka ɓacewa ganinta gaba ɗaya.
Hansatu su na tafe su na ta hira da direban motar, aka biya gidanta, aka ɗauki wasu matasan matan sannan suka ɗauki hanyar tafiya.
Tana jin yadda suke ta hirarrakinsu a cikin motar, amma ta kasa tofa komai, da ta rufe ido, ɗan jaririnta take hangowa, gefe guda kuma zuciyarta cike da fatan Allah ya sa tafiyar nan, ta yi mata rana.
A ƙalla sun yi tafiyar awanni biyu da rabi a mota, sannan suka isa wani gida. Hansatu ta yi musu bayanin, a nan za su sauka su huta, washegari ta kai kowacce inda ta ɗaukko ta za ta kai ta. Nana ta din ga addu'a da fatan Allah ya sanya ba mugun hannu ta faɗo ba, duk da kafin ta taho Nene ta bata layi ta saka a wayarta, ta ce mata duk abin da ta ga ba ta yarda da shi ba, ta kira ta ta sanar mata. A duk lokacin da Nana ta ɗaga wayar ta kalla, sai ta tuna Hajiya Amina, Haidar da kuma sauran jama'arta na Nigeria.
A gidan nan suka yi salla, aka ba su abinci suka ci, sai dai Nana ta yi mamaki ganin mata da yawa a gidan. Duk da ƙabilu ne daban-daban matan, akwai Zabarmawa, akwai Bugaje, da hausawa da sauran ƙabilun ma da ba ta sani ba a Nijar. Wai gidan kamar kamfani ne, wannan matan aiki ake nema musu, duk ciki Nana ce kawai 'Nigeria a cikinsu. Gaba ɗaya ta takure kanta ta kasa jikinta da su. Gaba ɗaya daren ranar, Nana ta kasa bacci, ta din ga tunanin Muhsin, da tunanin ko zai yi kukan rashin ganinta. Washegari Hansatu ta ce wa Nana ta shirya, ta ɗauki kayanta su tafi. Haka kuwa aka yi ta sake ɗaukarta su ka fita.
Nana ta sha mamaki, ganin haɗuwar da gurin cin abincin ya yi, kuma babban abin da ya ƙara bata mamaki, gurin cin abincin tamkar hotel. Suka shiga cikin gurin, Hansatu ta kai Nana wani katafaren ofishi, da yak3 gurin mai kula da ɗaukar ma'aikatan, da yake namiji ne. Rawaninsa ne ya tabattar mata da buzu ne, ganinsa kawai sai Nana ta ji wani irin sanyi, tamkar ta ga Sayyid.
Nana ta gaishe shi, ya amsa sama-sama yana ɗan basarwa. Hansatu ta ce masa "Wannan ita ce ma'aikaciyar, na kawo ta a yi mata gwajin, a gani idan za ku ɗauke ta" Ya ɗaga kai ya sake kallon Nana ya ce "Sannu ko"
Nana cikin girmamawa ta ce "Yauwwa sannu da aiki"
Ya miƙo mata ƙunshin wasu takardu ya ce "Ga wannan duba, ki ga yadda tsarin aikin namu yake, ki gani idan sun yi miki, kafin mu je inda za a yi miki gwajin, idan kin ci sai ki sanya hannu a takardun, ki fara aiki da mu" Nana ta saka hannu ta karɓi takardun, amma ta ga rubutun French, ta kalli Hansatu, ta kalle shi ta ce "Ai ban iya fransanci ba"
Ya kalli Nana ya ce "Ba ki yi makaranta ba?"
Ta ce "Na yi, amma ni ban iya French ba, turanci na iya sai Hausa"
Hansatu ta ce "A yi haƙuri Yallaɓai, 'yar Nigeria ce, daga Nigeria take"
Sai kuma ya kalli Nana ya faɗaɗa murmushinsa ya ce "Daga Nigeria ki ke? Ki ka baro babbar ƙasa kamar Nigeria ki ka zo jamhuriyar Nijar ki yi aiki da mu?" Nana ta ɗan risunar da kai tana murmushin dole, ganin yana murmushi shi ma.
Ya ce "Ahh to ai 'yan Nigeria ƙawayenmu ne, ba ma ƙawaye ba 'yan uwanmu ne. Dan haka zan ba ki aiki amma da sharaɗin za ki koya mini turanci, idan kin yarda na baki aiki" Nana ta yi murmushi, saboda yanayin yadda ya yi maganar cikin zolaya. Ya yi 'yar dariya ya ce "Ai duk wanda ya zo Nijar, mussaman daga Nigeria baƙonmu ne, akwai buƙatar mu karrama shi sosai da sosai, ko dan ƙara zumuncinmu da mutanen Nigeria. Dan haka babu wani abu, wannan wani ci gaba ne ma zan iya cewa gurin Abincinmu ya samu, kin ga girke-girken da ba a yi a nan, na can ƙasar kya din ga yi mana. Mu na da gurin kwana na ma'aikatanmu, awa ashirin da huɗu muke yi mu na aiki. Kamar yadda ki ka gani babban gurin cin abinci ne da manyan mutane ke zuwa cin abinci. Masu sayar da abinci daban, masu girki daban, ke za ki kasance a ɓangaren masu girki ne. Mu je mu zagaya ku ga gurin sosai da sosai. Ya jagoranci su Nana, ya nuna musu gurin, tsarin ya yi wa Nana sosai, duk da abin da ba ta ji daɗi ba, maganar zuwa hutun sati ɗaya ne kacal, duk ƙarshen wata. Su Hansatu za a din ga tura wa albashinta, su cire nasu kason su bawa Nana sauran. Ita Nana duk hakan bai dame ta ba, babban fatanta buƙatarta ta biya kawai.
Suka kammala duk cike-ciken da za su yi, aka sallami Hansatu, Nana kuma aka kaita gurin kwanan ma'aikata. Ɗakin da aka kai Nana, su uku ne a ciki, da banɗaki a ciki. Ta ajiye jakar kayanta, Hansatu ta kalle ta ta ce "To Nana, kamar dai yadda ya gaya miki, mu kamfani ne, kuma a ƙarƙashinmu ki ka zo nan, dan haka gurinmu albashinki zai din ga tafiya, mu zamu din ga sallamar ki" Nana hakan ko a jikinta, dan ita ko ba za su ba ta komai ba, indai akwai gurin kwana da abinci, kuma kwalliya za ta biya kuɗin sabulu, hakan ba damuwarta ba ne ba.
A fili ta ce "Babu damuwa, hakan ma na gode sosai da sosai, Allah ya saka da mafificin Alkhairi".
"Amin, a hakan ma gaskiya kina da sa'a sosai da sosai, sai da muka kawo musu mata uku, da ƙyar suka ɗauki ɗaya, wai duk ba su yi musu ba, wasu kuma sai an zo yi musu gwaji sai su faɗi. Amma ke ya ce ba zai yi miki ma gwaji ba, kawai an ɗauke ki aikin. Abin da zan gaya miki kawai shi ne ki kula, ki kula da kanki sosai da sosai, banda ƙazanta banda son jiki. Sannan kar ki ga kin tsallake wannan matakin, ya ɗauke ki aiki a haka cikin sauƙi, ki zata miƙe ƙafa za ki yi, mace ce mai gurin nan, kuskure kaɗan za ki ta ci mutuncinki ta kore ki. Su kan su ma'aikatan kwantar da kai suke yi, su na yi mata biyayya, duk wata tijara da bala'inta kawai ki toshe kunnenki ki yi haƙuri." Nana ta yi shiru, sai da Hansatu ta gama gaba ɗaya sannan ta numfasa ta ce "To Ubangiji Allah ya iya mana"
Hansatu ta amsa da "Yauwwa Amin"
Hakanan Nana ta ji a jikinta, ba za ta ɗauki wulaƙanci da cin zarafi ba, duk da kuwa abin da take son cimma. Ko Nene da ake kambama faɗanta da masifarta, ba ta cin mutunci, kuma duk abin da za ta yi faɗa a kai, to a kan gaskiya ne. Amm yanayin yadda Hansatu take yi mata bayanin mai gurin nan, a kaikaice dai ba ta san darajar mutane ba.
Ɗakin da Nana take, ita da wasu Zabarmawa ne guda biyu. Ta yi alwala ta yi sallar Azahar. Ta daɗe a kan abin salla, tana gaya wa Allah, cikin magiya a kan ya sanya ta samu abin da ta fito nema, ya kuma raba ta da duk wani sharri da abin ƙi. Bayan ta idar, ɗaya daga cikin 'yan ɗakin, ta ce mata ta zo su je ta zagaya da ita. Can ɓangaren da ake girke-girken ta kai Nana, suka zagaya daga nan ta kaita cikin gurin da ake sayar da abincin. Nana ta yi mamakin girman gurin, da yadda gurin Abincin yake da tarin kwastomomi. Sai dai da gani ka san na manya ne, dan duk waɗanda suke zuwa gurin cin abinci akwai alamun abin hannu a tattare da su.
*
Ɓangaren su Shukura cikin jikinta ya tsufa sosai, sai dai a wannan karon ta dage fafur ta ƙi yin awo a Asibitin su Doctor Sharif. Gefe Sagir ya jewa mahaifiyarsa, da maganar son dawo da Yusra, amma ta ce ba ta lamunta ba, ba ta buƙatar ya sake rayuwa da Yusra, gara yaje ya auro wata can daban, amma ba Yusra ba. Gaba ɗaya ya shiga damuwa, saboda mugun sabo da shaƙuwar da ya kuma yi da Yusra. Ita ma Hajiya Halima tun da ta samu labarin, Sagir ne tsohon mijin Yusra yake zuwa gurinta, ta din ga bala'i ta ce ko shi ne autan maza, Yusra ba za ta koma hannunsa ba, balle a sake ci mata mutunci a sako ta. Ga shi daga shi har ita su na son junansu. Dan haka ya yanke shawarar tafiya gurin ƙanin mahaifinsa ya yi masa magana. Shi kuma ya kira Hajiya Halima ya din ga yi mata faɗan dan me za ta hana shi mayar da matarsa alhalin sulhu alkhairi ne, wancan karon da auren ya mutu ma, gutsuri tsomarsu ce ta kashe Auren. Mussaman ta kira Sagir gida, ds ya je ya same ta, ta dirarar masa da bala'i. "Wato ƙarata ka je ka kai wa ƙanin ubanka saboda mace ko Sagir?"
Ya girgiza kai ya ce "A'a Hajiya ba ƙararki na kai ba" "Rufen baki ko na make ka, ba ƙarata ka kai ba ya kira ni yana faɗa? Tun da abin da ka zaɓa kenan, ka je ka yi duk abin da ka ga dama" Kalaman na Hajiya, tamkar ɗsure shi ne da jijiyoyin jikinsa, gaba ɗaya ya rasa abin da yake yi masa daɗi ba ya son ya yi abin da daga baya zai zo yana dana sani, saboda rashin amincewar Hajiyarsa.
Daren yau sam Nana ba ta samu isasshen bacci ba, da yake sai washegari aka ce za ta fara aikin, ba ta yi aikin komai ba ranar. Raba dare ta yi tana nafilfili addu'oi, saboda a jikinta tana jin wani abu game da gurin, wanda ta kasa tantance ko mene ne. Washegari da safe, suka shirya ita da 'yan ɗakinsu, suka tafi gurin aikin Abincin. Kayan girki ne ga su nan a zube, kamar abin banza, yanayin yadda aka jibge kayan a gurin, Nana ta sha jinin jikinta, ta san aiki ne tuƙuru za a yi shi gurin. Aka ba su jadawalin abinccicikan da za a girka a ranar, Nana ta san wasu, wasu kuma ba ta san su ba. Su na nan tsaye shugabar ɓangaren na ƙara yi wa Nana bayani, da gurɓatacciyar hausarta, sai ga mutumin jiya shigo. Gaba ɗaya suka wani ruɗe, masu gyara tsayuwa na yi, masu kama aiki suna yi, Nana dai ta ƙame a gurin da take. Ba yabo ba fallasa ya din ga amsa gaisuwar da ake yi masa, sai da ya zo kan Nana ya saki murmushi ya ce "Baƙuwarmu, ya ki ka ga gurin namu, ba dai wata matsala ko?" Nana ta girgiza kai ta ce "Babu matsala"
Ya ce "Yauwwa, ki saki jiki ki yi aikinki da mu, kamar kina Nigeria, duk abin da ba ki gane ba, ga shugabar sashin nan, idan kuma ba haka ba ni ki zo ki same ni ki yi mini magana" Ta jinjina kai ta ce "To in sha Allah, na gode sosai da sosai"
Ya kalli matar ya ce "Dan Allah kar a ce za a sakar mata aiki lokaci ɗaya, a koya mata abin da ta sani ba a hankali, kafin a sakar mata aiki"