Kenza eBookz

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 51

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 51

Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 51: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 51. Matar ta risuna ta ce "In sha Allah, amma za a yi mata gwajin ne ita ma?"

3,359 words

Matar ta risuna ta ce "In sha Allah, amma za a yi mata gwajin ne ita ma?"

"Kin ji na ambaci hakan ne, a maganata?"

Ta girgiza kai ta ce "Tuba nake"

Ya ce "'Yar Nigeria, a yi aiki lafiya"

"Na gode sosai" Nana ta yi maganar cikin girmamawa. Ya wuce ya fita. Bayan ya fita suka juya yare, suka ɗan yi maganganu, sai dai duk da Nana ba ta jin yaren nasu, ta san gulmarta suke yi. Suna aiki amma gaba ɗaya hankalin Nana ba a kan aikin yake ba, yana kan halin da Sabir yake ciki. Tana ta tunani yaya yake? Yana rigima ko kuwa bai damu ba ya kwantar hankalinsa, haka ta yi ta wasi-wasi a zuciyarta.

* Hajiya Amina ce ta yi shirin tafiya Umara, ta tsaya a Egypt za ta kwana biyu, ta tsaya a ɗan binciki lafiyarta. Sai dai ta din ga ji a ranta, yakamata a ƙara bincika mata matsalarta ta rashin haihuwa, mussaman da take tuna maganganun Nana. Sai dai gefe guda tana tuna yadda Alhaji Zailani yake gargaɗinta a kan shi ya fauwwala wa Allah, bai damu lallai sai ta haihu ba, tun da an nemi magani ba a dace ba. Sai dai a wannan karon, ta sake jin tana son jarraba da bibiyar lafiyarta, da ganin likita, ko za a dace, tun da ba ta daina al'ada ba ma. Da harshen turanci suka tattauna da Likitan, ta yi masa bayani, ya rubuta mata gwaje-gwaje ya ce ta je ta yi, ciki har da hoto. Kasancewar komai na su ba kamar na ƙasarmu ba, cikin ƙanƙanin lokaci aka yi duk gwaje-gwajen, aka tura wa Likitan sakamakon. Bayan ta koma gurin Likitan ya duba na'ura mai ƙwaƙwalwarsa, ya kalli Hajiya Halima ya ce mata "Sakamakon hoton da aka yi mata, ya nuna babu mahaifa a jikinta gaba ɗaya" wata irin ƙara cikinta yayi, zuciyarta ta buga a jejjere da ƙarfin gaske, sai ta hau kame-kame tana tunanin, ko kunnuwanta ba su ji daidai ba? Ko kuma turancin nata ne ya ƙwace.

Cikin rawar murya ta ce "Ka tabattar da abin da ka gaya mini, ko kuma nice ban fahimta ba?"

Ya ce "Na tabattar, shi ne sakamakon gwajin da aka turo mini, amma idan ba ki yadda da sakamakon ba, kina iya zuwa wani Asibitin a sake duba ki!.

Yammm ta ji kanta yana yi, ta daina gane komai, hankalinta ya rarrabu kashi-kashi, tana son yi wa likitan tarin tambayoyi amma kanta ya kulle. Shin da gaske ana iya samun mace babu mahaifa, ko kuma wani abin ne daban? Ya aka yi duk tsawon lokacin da ta ɗauka tana bulayin neman haihuwa ba a taɓa gaya mata ba ta da mahaifa ba sai yanzu?. Gaba ɗaya Hajiya Amina, ta rasa kalmomin da za ta tattaro ta sake furta wani abu. Jikinta rawa kawai yake yi, wani irin gumi yana tsatstsafowa ta kowace kafa ta gashin jikinta. Likitan ya ci gaba da yi mata bayani, amma ta kasa fahimta. Ba ta san ma da ya aka yi ta bar Asibitin ba, ta koma masaukinta saboda tsabar ɗimuwa. Ta kuma rasa wa za ta kira ta sanarwa wannan maganar. Gaba ɗaya kanta ya juye, dan ba ta ma iya tuna yadda su ka ƙarƙare da Likitan ba. Tana so ta zubar da hawaye, ta ji sanyi a ranta, amma abu ya gagara idanunta suka bushe zuciyarta ta yi nauyi. Babbar tambayarta ita ce, dama ana iya samun macen da ba ta da mahaifa? Ko kuwa ta ta ce ta yi ɓatan dabo?. Tambayar da ta rasa wa za ta yi wa, balle a ba ta amsa.

*

Nana kuwa gurin nan aiki ake yi tamkar babu gobe, duk da ba ta da son jiki, amma aikin yana da yawa ga babu isasshen hutu, sai aikin ɗorawa da saukewa. Ga shi ta kasa sakin jiki da ma'aikatan gurin, saboda yadda suke tsangwamarta, da nuna mata ƙabilanci, saboda ita ba 'yar ƙasar su ba ce ba. Sam ba sa gaban Nana, duk da tana ɗan saka ido ta ga, ko akwai wata mai hankali da za ta ji ta yarda da ita, a kaikaice ta ɗan fara ƙwanƙwasa cigiyar Sayyid. Sai dai gaba ɗaya ba su yi mata ba ma'aikatan gurin, gaba ɗaya ba ta ji ta aminta da ko mutum ɗaya daga cikin su ba. Kullum da safe Al hussain, mutumin da ya ɗauke ta aiki, sai ya zagaya su ya ga yadda suke gudanar da aikin safe da yamma. Da ya zo ma'aikatan suke nutsuwa, kowa ce ta kame kanta, marasa kamun kai kuma su fara ɗan karairaya. Shi kuma ya tsuke fuska yana basarwa. Sai dai da ya ga Nana sai ya saki fuska, ko ba ta kula shi ba, shi sai ya yi mata magana.

"'yar Nigeria ya alƙawarinmu ne?"

Nana ta ɗan saki fuska ta ce "Wanne?"

"Au har kin manta?"

Ta yi murmushi ta ce "Duk lokacin da ka shirya, sai mu fara"

Ya ce "Kin san akwai wani abokina, sonake kafin na haɗu da shi, ko gaisuwa na iya da turanci, saboda ya iya turanci ni ban iya ba, ya juya yare ya yi ta magana ba na gane me yake cewa, to kin ga yakamata na ba shi mamaki nima"

Nana ta ce "Gaskiya ne, shi ma Buzu ne kamar ka?"

Al Hussain ya ce "Ya aka yi ki ka san ni Buzu ne?"

"Ga rawani nan ka na yi" ya yi dariya ya ce "Kash, to shikenan tun da kin gane, shi ma buzu ne, mun kwana biyu ma bamu haɗu ba, ban je Agadez ba"

"Duk Buzaye a Agadez ku ke?"

Ya girgiza kai ya ce "A'a, sai dai mun fi yawa a can, ko kina son zuwa ne? Mu na da wani gurin Abincin ma a can, babban wannan sai a mayar da ke can" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a tamabaya dai kawai na yi"

Ya jinjina kan ya ce "To yaya aikin?"

"Alhamdillah"

"To ma sha Allah, Allah ya taimaka"

Tun da suka fara hirar nan, Nana ta lura da irin kallon da ake yi mata, saboda ya tsaya sun yi hira. Sai dai ita ba kallon ne ya dame ta ba, a jikinta take jin sam ba ta kyauta ba, tsayawa da ta yi tana magana da Al Hussain har take yi masa murmushi ba, saboda ta san da Sayyid yana gurin, ko da makamancin wasa ba za ta taɓa aikata hakan ba, saboda yadda yake tsananin kishinta. A hankali ta ce "Ka yi haƙuri Sayyid, babu yadda na iya ne, duk a ƙoƙarina na son zuwa gare ka ne, ka yi mini afuwa" ta furta a hankali kamar mai raɗa.

"Nana wai a ina ki ka san Al Hussain ne?"

Nana ta ɗaga kai ta kalli Shugabar gurin nasu, da take yi mata tamabaya cike da tuhuma. Kamar Nana ba za ta yi magana ba, sai kuma ta ce "Waye hakan?"

Matar ta ce "Kamar yaya?"

Nana ta ce "Wanda ki ke tambayata"

Gaba ɗaya suka kalli Nana, jin yadda take bawa Adama, shugabar ɗakin girki. Ita kuwa Nana ko a jikinta da irin amsar da ta bawa Adaman.

Cike da takaici Adama ta ce"Mutumin da ya fita yanzu"

Nana ta ce "Au sunansa kenan dama? A nan Nijar na san shi, meyafaru?" Ta yi maganar tana tsare Adama da ido, tana jiran abin da za ta sake cewa. Sai dai ta yi shiru ba ta kuma magana ba, su kuma suka hau mamakin irin amsar da Nana ta bata, kuma ba ta iya ce mata komai ba. Gaba ɗaya Nana hankalinta ya koma kan sauran kwanaki nawa ta koma gida, duk da kullum sai ta yi waya da Nene. Amma ta ga kamar kwanakin ba sa matsawa sam. Hajiya Amina revers ta yi, ta dawo gida Nigeria, saboda kiɗima da tashin hankali da take ciki, ta rasa wanda za ta fara tunkara da maganar. Ta so samun mijin Alhaji Zailani a waya, ta fara yi masa bayani, amma ba ta same shi a waya ba. Ta koma gida a kiɗime, amma ta tarar da saƙon ya yi balaguro zuwa Abuja.

Jikinta na rawa ta kira Doctor Sharif, ya ɗaga yana faɗin "Hajjaju barka da yamma"

"Sharif abu zan tambaye ka dan Allah"

Gabansa ya faɗi, saboda yadda ya ji muryarta cike da tsoro da kuma damuwa.

"Hajiya lafiya dai?"

"Lafiya ƙalau, tambaya zan yi maka dan Allah"

"To Allah ya sa na sani"

"Dan Allah Sharif ana iya samun matar da ba ta da mahaifa dama?"

Ya yi shiru sanann ya ce "Me yasa ki ka tamabaya?"

"Ka bani amsa kawai"

Nutsuwa ya yi ya tattara hankalinsa, kar ya ba ta amsar da zai fallasa wani ɓoyayyen abin da bai kamata ba. Duk da bai san dalilin da ya sanya ta yi tambayar ba.

"Eh ana samu Hajiya, sosai ana samu wani abu ne ya faru?"

"A'a shikenan na gode sosai" ta kashe wayar, sai a lokacin hawaye ya fara gangaro mata, da ta ƙara tabattar da har abada ba za ta samu haihuwa ba. "Amina butulci za ki yi wa Ubangiji? Sauran ni'imomin da ya yi miki fa?" Wata zuciyar ta tunatar da ita. Sai dai kasancewarta biladama mai ɗauke da zuciya irin ta ɗan adam, sai ta kasa jurewa ta bi nasihar da zuciyarta take yi mata, ta fashe da matsanancin kuka mai taɓa zuciya. Duk da ta daɗe tana yin sa a ɓoye, amma ba ta yanke tsammani ba ta ci gaba da addu'a, amma a wannan karon da ta san ba ta da rabo baki ɗaya, sai ta sare.

* Shirye-shiryen bikin Abba yayi nisa, dan bai fi saura sati biyu bikin ba, ta ƙara saka masa ido da shi da Jamila. Jamila sam ba ta nuna mata cewar ta san abin da take yi ba, ta rabu da ita. Ya kasance taronsu na ƙungiya lokaci yayi, dan haka suka shirya tafiya a wannan karon har da maman Khairat. Da suka je masaukinsu ma a garin Abuja, Jamila ba ta shiga sabgarsu ba, harkokinta kawai take yi.

Maman Khairat ta ce "Wai Jamsy ya ne? Duk kin zama so silenta, babu wannan rawar kan" Jamila ta ɗan taɓe baki kawai. Hajiya Sa'a ta ce "Jamila haushina take ji, ban san me na yi mata ba"

Jamila ta ce "Mummy kenan"

"A'a ba wani Mummy kenan, magana za ki yi"

"To Mummy, ki na ta daughter daughter, amma ƙarara ki ka nuna ba kya ƙaunata, daga ganina tare da Abba, ki ka haɗe rai ki ka yi kicin-kicin, ki ka tashi nema masa aure. Abin ya bani mamaki"

Hajiya Sa'a suka haɗa idi da maman Khairat, ta ce "Haba daughter, ya za a yi na ƙi ki da Abba, ke me ma za ki yi da aure? Na daɗe ina gaya miki za ki iya rayuwa ki da kuɗinki, ba tare da kin yi aure ba. Za ki huta ki yi duk abin da ki ke so."

"Amma Abba ma ai yana da kuɗi, shi me yasa ba ki ce ya yi rayuwa da kuɗi kawai ba, ki ke shirin yi masa aure? Duk wata ƙasaita, kuɗi da wadatar mace, inuwar aure ginshiƙi ce kuma sutura ce ga 'ya mace. Amma na san saboda ni rayuwata ta gama lalacewa, ke kuma kina son ɗan ki ya yi kyakykywar rayuwa, ki ka yi ƙoƙarin raba ni da shi. Sai dai tun ran gini tun ran zane. Ban ji haushinki ba ko kaɗan Mummy, abin da ki ka yi shi kowacce uwa za ta yi. Ina yi mana fatan dacewa da ƙarshe mai kyau" Tana gama maganar ta yinƙura ta tashi, ta bar ɗakin.

Safiyya ta ce "Kin ga Hajiya, ki bi yarinyar nan a hankali, alamu sun nuna hankali ya fara shigarta, ta san ciwon kanta, kuma abin da aka yi mata duk da ta samu kuɗi ya yi mata ciwo. Kar ki bi ta da ƙarfin tsiya ta yi tawaye"

Hajiya Sa'a ta numfasa ta ce "Na ga alama, amma ba zan taɓa rainon ɗan kwiykwiyo, ya girma ya fara yi mini haushi ba. Ina son samun jinin 'yar uwatta na riga Zailani samu ko ta halin ƙaƙa, daga nan zan yi maganinta"

Safiyya ta jinjina kai.

Doctor Sharif ya din ga kiran Alhaji Zailani, ya sanar da shi kiran da Hajiya Amina ta yi masa, amma ya kasa samunsa a waya, saboda su shinga taron manyan ƙungiya da suke yi, wanda sai sun kwana uku suke fitowa, sannan ayi babban taro na kowa da kowa da ke cikin ƙungiya.

Ganin kiran Hajiya Amina ya bawa Shukura mamaki, dan idan tana Saudiyya sai dai su yi video call. Ta ɗaga ta ce "Mami, yaya ba ki samu tafiyar ba ne?" "Shukura za ki iya zuwa gida, ban takura miki ba"

Cikin tashin hankalShukura ta ce "Lafiya kuwa, ya na ji muryarki a haka?"

"Dan Allah idan da hali ki zo gida"

"Shikenan, gani nan zan kira baban Haidar na gaya masa, gani nan Allah ya sa lafiya"

Hankali a tashe, ga tsohon ciki haka ta ɗauki mota ta tafi gida. Tana matuƙar jin Hajiya Amina a zuciyarta, saboda bayan rasuwar mahaifiyarsu, tun su na ƙanana babu yadda ba ta so cuzguna mata ba, amma Hajiya Amina babu ruwanta. Ba ta damu da abin da mutane za su ce ba, ta riƙe ta da halin ta, sai da ta ƙara wayo sannan ta gane ba ta da wata uwa da ta wuce ta. Shi yasa take matuƙar jin damuwarta a ranta tamkar uwar da ta haife ta. A bedroom ta tarar da ita, idanunta jawur sun kumbura. Cikin tashin hankali ta ƙarasa ta zauna ta ce "Lafiya kuwa? Ko ba ki da lafiya ne?"

Ta girgiza kai ta ce "Yi haƙuri Shukura, na taso ki ga tsohon ciki, na rasa da wanda zan yi zancen nan na ji daɗi a raina."

Cikin damuwa ta ce "To meyafaru?"

"Shukura wai ba ni da mahaifa"

Shukura ta yi saroro, ta ce "Kamar yaya?"

Ta share hawayenta ta gaya mata duk abin da ya faru. A ƙarshe ta ce "Na kira Doctor Sharif ya ce mini eh ana iya samun mata da basu da mahaifa, amma na yi mamakin yadda duk yawon Asibiti da na yi a nan, ba a taɓa gaya mini ba"

Shukura ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Anya kuwa? Kin san fa kin daɗe da daina zuwa Asibiti a kan matsalar nan, Daddy ba ya so. Sannan ku ne ku ke yarda da maganar Sharif ɗin nan, ki rabu da shi mu je wani Asibitin daban, a sake duba ki a tabattar da abin da yake faruwa. Duk da ba na tunanin za a samu matsala a abin da can Egypt ɗin suka gaya miki."

Ta girgiza kai ta ce "A'a Shukura, babu inda zan sake zuwa, na yi maganar ne da ke dama na samu sanyi a raina, na kira babanki ba ta shiga"

Shukura ta yi shiru, kawai dai ta ji ita abin kamar akwai lauje cikin naɗi.

*

Nana ta shafe sati na biyu, tana aiki a wannan gidan Abinci. Sai dai ita kanta tana mamakin irin yadda Al Hussain yake kyautata mata. Hakan ya sanya gaba ɗaya suka ƙara saka mata ido suka tsangwame ta, mussaman Adama da 'yar ta Raliya, da alamu suka nuna Al Hussain take so. Idan aiki ya ɗan yi sauƙi, Nana kan fita ta shiga cikin gurin cin abincin, ta zagaya ko za ta ga ko mai da Sayyid ne, amma ba ta ga kowa ba. Sai dai gabanta ya kan faɗi a duk lokacin da ta ga masu rawani sun zo gurin cin abinci, sai ta ga kamar za ta gan shi a cikin su. Ta gama zagayenta, ta koma cikin gurin girkin, Adama ta kalle ta ta tsuke fuska ta ce "Daga ina ki ke, ana tsaka da aiki?"

"Na ɗan je wani uzuri ne"

"Na me, kuma a ina?"

Nana ta ce "Uzuri dai na ɗan Adam, na yau da gobe, ai rayuwa na buƙatar sirri ko?"

"Ni fa na fuskanci take-takenki na rashin kunya baki da kunya ko kaɗan, saboda kin ga Al Hussain yana tsaya miki, wallahi idan ba ki yi wasa ba sai na kawo ƙarshen aikinki a nan, sai na saka an kore ki daga gurin nan" Kallonta kawai Nana ta yi ta kawar da kai, ta ci gaba da abin da take yi. Har ta gama bala'inta, 'yan korenta suka taya ta, Nana ba ta tanka mata ba.

Washegari da sassafe, Nana ta baro ɗakinsu, ta tafi kitchen ta fara aikinta, duk da wasu lokutan suna yi mata mugunta, su din ga sakar mata aiki.

"Ina sauran ma'aikatan gurin nan?" Ta ji wata murya ta daki kunnenta, da ba ta san mai ita ba. Ta ɗaga kai ta kalli matashiyar matar, doguwa fara jawur, mai kama da Al Hussain. Kawai ta mayar da kanta ta ci gaba da aikin gabanta.

"Ke ba kya ji ina magana ne?"

Nana ta ɗago kai ta ce "Su na zuwa"

Nana na rufe bakinta, sai ga Adama ta shigo, ita da sauran ma'aikatan.

Wata irin rikicewa suka yi, suka hau tsuma su na gaida matar.

"Wace ce wannan? Da ba ta da mutunci ba ta da ɗa'a, nake magana tana bani amsa a wulaƙance" ta yi maganar tana nuna Nana. Nana a ranta ta hau mamakin wane wulaƙancin ta yi mata, ita da ta zo guri babu sallama babu gabatar da kai, koma wace ce ba zai wuce ita ce mai gurin da ake faɗa ba. Nana a ranta ta ce "Koma wace ce ke, Allah ya fi ki" sai dai ba ta sake ɗaga kai ta kalle su ba, ta ci gaba da yankan kabejin hannunta.

Ayshercool 08081012143. Adama ta risunar da kai ta ce "Ki yi haƙuri ranki ya daɗe, mu ma haka muke ta fama da ita mu ma, amma ki yi haƙuri baƙuwa ce"

"Baƙuwa kuma ba ta iya magana ba, baƙuwa daga ina?"

Raliya ta ce "'yar Nigeria ce"

" 'yar Nigeria, waye ya saka Al-Husssain ɗaukar wata 'yar Nigeria, dama haka 'yan Nigerian ku ke, ba ku da mutunci ba ku san me ku ke yi ba?" Maganganun matar sun soki zuciyar Nana, tamkar ta mayar mata da martani ta ce "Ku a Nijar ba ku san muhimmancin sallama, da girmama na ƙasa da kai ba" Sai dai ta yi shiru ta ci gaba da aikin gabanta. Haka ya ƙara tunzura matar ta fita fuuuu tana bala'i tana sai Nana ta bar aiki a gurin.

Matar na barin gurin Raliya ta kalli Nana ta ce "Allah ya ƙara, idan kina cin ƙasa ai ki kiyayi ta shuri, yau kin taɓo abin da ya fi ƙarfinki, kin yi a bakin aikinki"

Babban abin da ya ɗaure musu kai, bai wuce yadda Nana ta ƙara yin burus, ta ci gaba da aikin gabanta.

Adama ta ce "Anya yarinyar nan ba mahaukaciya ba ce kuwa?"

Ɗayar ta ce "Ko ta mayar da mu mahaukata ba. Amma idan haukan take ji, ai Hasna babarta ce"

Wata matashiyar mata ce ta shigo, sanye da uniform a jikinta. Ta yi sallama suka amsa. Ta ce "Ina Nana?"

Nana ta ce "Ga ni"

"Ki zo ana neman ki a ofishin Al Hussain"

Ta ce "To gani nan" ta yi maganar tana ajiye wuƙar hannunta, ta wanke hannunta ta bi bayan matar.

Sai dai har matar ta yi gaba ta bar Nana, da ƙyar Nana take iya ɗaga ƙafafuwanta, saboda matsanancin nauyin da ta ji sun yi mata, ga sanyi da ya fara ratsa ta ta ko ina.

"Ya hayyu ya ƙayyum. Allah ka taimake ni, Ƙaisar kar ka yi mini haka mana" Ta furta a hankali zuciyarta na bugawa. Ta saka hannu ta tura ƙofar ofishin. A tsaye ta tarar da matar ɗazu, tana zazzaga masifa, Al Hussain yana zaune yana kallon ta. Sai dai Nana ta yi turus, ganin Ƙaisar a zaune a jikin na'urar sanyaya guri, da ke cikin ɗakin.

"Nana ƙaraso mana" muryarsa ta dawo da Nana hayyacinta. A hankali ta ƙarasa ya ce ta zauna a kan kujera.

"Al Hussain ka na da lafiya kuwa? Yarinyar ta yi mini rashin mutunci, ka ce ta zauna a kan kujera?"

Readers Also Read