Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 52
Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 52: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 52. Ya ce "A'a Hasna, na fa san halinki, kuma a aikin da Nana ta yi da mu na…
3,345 words
Ya ce "A'a Hasna, na fa san halinki, kuma a aikin da Nana ta yi da mu na ɗan lokaci, ba ta da matsala sam. Nana meyafaru ne?"
Nana ta buɗe baki za ta yi magana, Hasna ta tari numfashinta ta ci gaba da masifa. Al-Husssain ya daki tebur ya kalli Hasna, hakan ya sanya ta yin shiru tana harar Nana. Nana ta ce "Ban san wace ce ba ne, ta yi haƙuri"
Hasna ta daki tebur ta ce "Ka gani ko, garin kwashe-kwashe ka kwaso mara mutunci, to wallahi sai ta bar gurin nan, tun da ba na ubanta ba ne"
Al-Husssain ya ce "Tsakani da Allah, Nana mutuniyar kirki ce mai girmama mutane, ba na tunanin za ta yi miki wani abu na rashin mutunci. Nana ki je ki ci gaba da aikinki" Ta jinjina masa ta kalli Hasna ta ce "Ki yi haƙuri, ban san wace ce ke ba, ba ki gaya mini ba, na zata a cikin abokan aikina ne kaw...
"Ke, na yi miki kama da wadda za ta zama abokiyar aikinki?. Za ta ci gaba da magana Nana ta tsare ta da ido, sai ta rikice gaba ɗaya ta rasa abin da za ta ce.
Al-Husssain ya ce "Maza jeki ki ci gaba da aikinki"
Nana ta miƙe tsaye, kawai ta ji jiri ya ɗebe ta, ta yi saurin riƙe kujerar. Al Hussain ya miƙe da sauri ya ce "Ba ki da lafiya ne?" A sanyaye ta ce "A'a jiri nake ji ne"
"Idan ba za ki iya aikin ba, ki je ki kwanta ki samu hutu"
Nana ta ce "A'a zan iya ma, in sha Allah"
Ta lallaɓa ta fita daga ofishin, sai dai tana jiyo Al Hussain yana ce mata, ki yi a hankali kin san mu na da baƙi, idan kuma ki ka ci gaba da hayayaga mutuncinki ne zai zube, wannan halin naki babu abin da zai janyo miki sai raini.
Gaba Nana ta yi, tana bin bango, sai dai sosai ta ji Duniyar na juya mata. Ta lallaɓa ta koma ɗakinsu da ƙyar, sai dai a ɗakin ta din ga jin wani irin sauti mara daɗi, ga sanyi tana ji amma numfashinta tamkar zai ɗauke. Ta buɗe tagogin ɗakin, kasancewar saman bene ne, ta hango wasu irin manyan motoci a harabar gurin. Naɗin kan mutanen ya sanya ta tabattar da Buzaye ne, sai dai suna sanye cikin kaya na alfarma. Nana ta zuba musu ido, tana son ganin fuskar ɗaya daga cikin mutanen da aka buɗewa wata danƙareriyar mota. Wanda haka kurum ta din ga jin kamar akwai wani abu mai matuƙar muhimmanci da yakamata ta sani game da mutumin, da ba ta san ko wane ne ba, duk da yanayin ƙirar jikinsa ba irin na Sayyid ba ne. Wata irin ƙara ta din ga ji cika mata kunne. Ta dafe kunnenta, ta durƙusa hawaye na bin fuskarta. Yanayin gaba ɗaya mara daɗi ne, rashin daɗin da ba za ta iya misaltawa ba sam. Dariyar Giyaz ta din ga ji sama-sama, a hankali dariyar ta cika ilahirin ɗakin. "Hasbunallahu wa ni'imal wakil, wa hifzan min kulli shaiɗanin marid" shi ne abin da ta furta a hankali.
"Asmy" ta ji muryarsa cikin karkarwa, yayin da ƙarar iskar sahara take kaɗawa.
A galabaice ta ce "Sayyid"
"Ma vie"
Ta sake cewa "Na'am Sayyid, na fara sarewa, ina jin kamar ba zan yi nasara ba, ba zan ganka ba, na fara karaya." Ta yi maganar tana kuka.
"A'a kar ki karaya, kar ki yi mini haka, ina buƙatar ki dan Allah"
A hankali take sauke numfashi, idanunta a lumshe ƙirjinta ya yi nauyi kamar numfasihinta zai ɗauke.
*
Daren da Jamila ba za ta taɓa mantawa da shi ba, ya sake maimaita kansa. Daren da ta zama ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar asiri, daren da aka lalata rayuwarta a matsayin maraba da shiga ƙungiyar.
Kamar yadda yake ɗabi'ar ƙungiyar, suna sanye da jajayen kaya. Sai dai a wannan karon Jamila ta gusa daga matakin farko na shiga ƙungiyar. Babban abin da ya bawa Jamila mamaki, bai wuce yadda aka fesa wani abu a gurin, sai ganinsu ta yi a dokar daji ba. Wani irin daji mai ban tsoro, mai ɗauke da manyan dogwayen bishiyu, ga shi baƙiƙirin ɗauke da duhu. A wani fili suke a gaban wani dutse, babu tsammanni ta ga wuta takama a tsakiya tana ci bal-bal. Daga bisani dajin ya din ga amsa kuwwa da wata irin ƙara mara daɗin ji. Aka din ga karanto abubuwan da Jamila ba ta iya fahimta. Aka jefowa kowa ƙyalle da abin da zai sadaukar na shekara, kafin zagayowar wani taron. Jamila ta kalli ƙyallen da yake gabanta, jawur da shi. Hannunta na rawa ta ɗauka ta fara ƙoƙarin warwarewa. Da hasken da wutar ta bayar Jamila ta karanta abin da yake rubuce a jiki, da aka rubuta da jini. Ta din ga kallon ƙyallen tare da rubutun. Ta duƙunƙune ƙyallen ta jefa a wuta, kamar yadda kowa ya yi. Sai dai jikinta a sanyaye, gabanta kuma ya tsananta faɗuwa. A wannan karon har da wasu irin dogayen mutane, da ta kasa gane mutanen ne ko kuwa wani jinsin ne, saboda yadda suka shallake kowa tsawo a gurin kuma suna sanye da baƙaƙen kaya har kansu a rufe yake. A wannan karon abubuwan da Jamila ta gani sai da ta tsorata, ashe wancan karon babu abin da ta gani. Ƙungiyar mataki-mataki ce. Su matakin su Alhaji Zailani ma, kowannensu yana da aljanin da kusan bauta masa yake yi. Sun ba wa aljanun jini babu adadi, na makusantansu, da wanda ma ba makusnatansu ba. Aljanun na iya shiga kowane irin hatsari, dan ganin buƙatar irin su ta biya komai wahalarta. Haka suma su Alhaji Zailani, duk abin da Aljanun suka buƙata suna yi musu, domin ɗorewar biyan buƙatunsu. Alhaji Zailani ya kan karɓi saƙonnin nasa Aljanin ta hannun Malam Gambo, wanda su ne manyan malaman da suke gudanar da sihiri a cikin ƙungiyar bayan ɓangaren neman Duniya da samun kuɗi da suke yi. Su kan kira aljanu daban-daban da sanya su aikace-aikace na sihiri. Aljanin Alhaji Zailani ya buƙaci aiki da jinin Nana, da kuma mu'amala da mai irin tauraronta dan biyan buƙatun Alhaji Zailani, sai dai abu ya gagara kamar yadda dariya ta gagari kare. Hakan ya sanya a wannan karon ma ya sake buƙatar jinin Alhaji Zailani, wanda idan ba Shukura ko Yusuf ba, sai dai abin da Shukura za ta haifa. Ɓangaren Hajiya Sa'a ma hakan ne, bayan sanin fa'idar jinin irin na masu tauraron Nana, da yadda bayan haɗuwarta da Nana karon farko, Aljanin ya yi mata bayanin irin tagomashin da za ta samu, idan ya sha jinin Nana, da kuma bautar da zai yi mata idan ya sha jinin ko kuma ta kawo Nana ƙungiya, ta hanyar na ta bokan na cikin ƙungiyar, kuma bokan ya kwaɗai mata damarmakin da za ta iya samu idan ta mallaki Aljanin kan Nana kamar yadda aka gaya wa Alhaji Zailani ma. Ita ma a wannan karon, an sake buƙatar jinin makusancinta, wanda ko dai Abba, ko Alhaji Fatuhu ko kuma dai ɗansa Muhsin, su ne shaƙiƙanta.
Jamila a firgice ta farka, a tunaninta ko duk mafarki ne, ta farka da wani irin matsanancin zazzaɓi da ciwon kai, ƙoƙon kanta tamkar zai tarwatse saboda azabar ciwo. Maman Khairat ta taso tana yi mata sannu. Ta ce "Wai ke Jamila wace irin raguwa ce ne haka? Ai yakamata a ce zuwa yanzu kin riga kin saba fa"
Hajiya Sa'a ta ce "Dole za ta razana dama, yanzu ta shiga mataki na biyu sai a hankali"
Jamila ta ɗan yi shiru tana so ta fuskanci ko a wannan karon ma an yi lalata da ita, amma ba ta ji hakan ba. Sai kanta da yake ta wata irin azaba, ga jikinta tamkar ana ƙona ta saboda zafin zazzaɓi.
*
Shukura ta je awo, likitan da yake duba ta doctor Sabo, ya na ta ƙara kwantar mata da hankali, saboda a wannan karon ma akwai hawan jini a tattare da ita. Har za ta tashi ta tafi ta ce "Doctor dan Allah wata tambaya ce da ni"
Ya ce "To Allah ya sanya na sani"
"Wai dan Allah ana iya samun mace wadda ba ta da mahaifa?"
Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Eh ana samu, amma a mafi ƙanƙantar lokuta sosai, saboda a cikin mata dubu biyar da ƙyar ake samun mace guda ɗaya da irin wannan case ɗin"
Ta jinjina kai cike da gamsuwa ta ce "To Doctor kai ka taɓa haɗuwa da irin waɗanda ba su da mahaifar?"
Ya girgiza kai ya ce "A'a. Amma me yasa ki ke tambaya?"
"Mamana ce ba ta taɓa haihuwa ba, da tana zuwa ganin Likita amma ta daina, sai last week ta je Egypt, aka duba ta ska ce ba ta da mahaifa" Ya waro ido ya ce "Ba ta da mahaifa, kuma ta taɓa haihuwa?"
"A'a ba ta taɓa haihuwa ba, step mum ɗina ce"
Ya ce "Ikon Allah, kuma ba a taɓa yi mata aiki ba ko makamancin haka?"
Ta yi shiru ta girgiza kai ta ce "Bana tunanin haka, amma bari na kira maka ita"
Shukura ta kira lambar Hajiya Amina ta ɗaga.
Suka gaisa ta ce "Mami, ina Asibiti ne na yi wa likitan da nake awo a hannunsa magana, ya ce na haɗa ku"
"Shukura, ba na ce a bar maganar nan ba kawai?"
"A'a ki yi haƙuri, na riga na yi magana da shi ai" ta ba wa Doctor Sabo waya. Suka gaisa ya ce "Hajiya garin yaya aka ce ba ki da mahaifa ne?"
"Wallahi nima ban sani ba, abin da dai suka ce mini kenan"
"A Nigeria an taɓa duba ki a baya an gaya miki hakan?"
Ta ce "A'a"
"An taɓa yi miki tiyata?"
"A'a Likita ba a taɓa yi mini ba"
Doctor Sabo ya ce "Ikon Allah, kuma yaushe rabon ki da Al'ada?"
Ta ce "Ai dama ba regular nake yi ba, wasu lokutan sai na yi wata shida ma ban yi ba, idan ya zo kuma ba ya fin kwana biyu wataran ma wuni ɗaya ne shikenan"
"To dama tun kina budurwa haka ki ke yi?"
"A'a gaskiya, da lafiya ƙalau nake al'ada daga baya ne ya koma haka".
"Bayan ya koma hakan kin taɓa zuwa an ƙara bincikawa, kuma a baya ba a taɓa gaya miki mene ne ya hana ki haihuwa ba?"
Ta girgiza kai kamar yana ganinta ta ce "Ko a baya komai lafiya ƙalau ake ce mini, daga baya kuma da ya koma haka, mijina ya ce na haƙura da yawon Asibitin nan, dan haka ban sake zuwa a kan issue ɗin haihuwa ba. Amma ina fuskantar matsalolin gynea sai dai akwai likita da nake gaya wa ya rubuta mini magani kawai".
Doctor Sabo ya ce "Idan babu damuwa, akwai buƙatar ki zo Asibiti mu ƙara bincikawa sosai da sosai, wannan serious issue ne"
"Doctor na gode sosai da sosai, amma ba na tunanin zan iya zuwa, na haƙura dama buri ne irin na ɗan Adam amma shekaruna sun ja, na bar wa Allah ikonsa."
"A'a kar ki ce haka baiwar Allah, akwai Abubuwan da farwuarsu daga Allah ne mun sani, wasu kuma akwai sababi. Wataƙila akwai wani abu na musamman a tattare da ke da ya dace a bankaɗo. Ina doubting a ce Egypt su bayar da result ɗin da ba shi ba ne ba. Amma dai za mu ƙara bincikawa." Hajiya Amina ta amsa masa da to, ta yi masa godiya amma sam ba ta ji za ta iya zuwa a wani bibiya ba, kamar tana tsoron wani abu.
Doctor Sabo ya ce lallai Shukura ta lallaɓo ta, su zo Asibiti yakamata a yi ƙwƙƙwaran bincike a kan lamarin.
Alhaji Zailani yana kashingiɗe ya kira Doctor Sharif. Bayan sun gaisa ya ce "Ina cikin uzuri ne kwana biyun nan, shi yasa ban ɗaga wayarka ba, ya ake ciki?" "Dama zan gaya maka ne, Hajiya ce ta kira ni tana tambayata wai ko ana iya samun mace wadda ba ta da mahaifa, to ban san dai mene ne ba, amma na ce maya eh." Wata irin zabura Alhaji Zailani ya yi ya ce "Daga nan me ta ce maka?"
"Ba ta ce mini komai ba ta kashe wayar"
"Shikenan na gode" ya kashe wayar ya dafe goshinsa, "Amina kin fiye taurin kai, dama kaza garin tone-tonenta take tono wuƙar yanka kanta!"
Sannu a hankali Nana take bin doguwar barandar, tana hangen masu shigowa da masu fita daga cikin gurin cin abincin. Tun safe motoci suke shiga su na fita. Sai dai ta jima a tsaye a gurin, ba ta ga wani abu da za ta iya riƙa, ko wani wanda za ta tunkara ta yi wa magana ba. Duk manyan mutane ne na alfarma ba ta tunanin akwai wanda ma zai tsaya saurarta, su kuma ma'aikatan gurin da take sanya ran za ta iya tambaya wani abu, ba zaman lafiya suke yi ba.
Jiki a sanyaye ta juya, ta kama hanyar komawa gurin girke-girken, Al Hassan yana hango ta, ta ofishin sa. A kan hanyarta ta komawa, suka yi kiciɓis da Hasna. Nana ta ɗan raɓe gefe ta ce mata "Ina kwana"
"Lafiya" ta amsa har za ta wuce Nana, sai ta dawo da baya ta ƙara kallon ta ta ce "Au ashe ke ce fitsararriyar nan ko?"
Nana ta girgiza kai ta ce "A'a rashin fahimta ne, yanzu da na san wacece ce ke ai ga shi na gaishe ki" Ta so ta yi wani abu da za ta yarfa Nana da za ta saka ta ji zafi a ranta, amma sai ta kasa. Gaba ɗaya ma sai ta ga Nanan kalar abin tausayi a yau, kamar ba ta da kuzari ko kaɗan fuskarta ɗauke da damuwa. "Amm ki kawo mini shayi ofishina, shayin girfa, kar kuma a cika sugar ba na son sugar da yawa"
"To ina ne ofishin"
"Ki tambaya" ta amsawa Nana tana yin gaba abin ta.
Nana ta koma gurin girkin, ta fara ƙoƙarin dafa shayin girfa, saboda babu shi, Adama ta saka ta wani aikin. Wasu lokutan har rasa yadda za ta yi take yi, sai dai ta kan jure dan kar ta gaza ta sare, dan jikinta yana bata zamanta a gurin nan ka iya sanyawa ta yi nasara. Sai dai abinka da ɗan Adam, wasu lokutan ta kan bujire. Ta kammala ta tambayi ofishin Hasna, aka nuna mata ta kai mata shayin har can. Tana tare da Al Hussain ta tarar da ita, da wasu manyan mutane guda uku a office ɗin. Cikin girmamawa Nana ta gaishe su, cikin gurɓatacciyar hausa suka amsawa Nana. Hasna ta sake mayar da Nana, wai ta kawowa baƙinsu shayi. Haka Nana ta koma, ta sake kai musu wani shayin, duk da hakan ba aikinta ba ne ba.
Ta fito daga ofishin, Al Hussain ya biyo ta yana kiran sunanta. Ta tsaya ta waiwayo ta jira ya ƙaraso.
"Nana ko haryanzu jikin ne ba ki warke ba?"
Cikin ƙarfin hali ta girgiza kai ta ce "A'a jiki na warke"
"A'a idan ba ki warke ba, na saka a kai ki Asibiti, sai a baki hutu"
Ta girgiza kai cike da ƙwarin gwiwa ta ce "A'a na ji sauƙi fa, zan ci gaba da aiki in sha Allah, na gode sosai da sosai" Ta juya ta ci gaba da tafiya. Shi dai haka kurum Nana tana ba shi tausayi, sai dai babu wata dama da ta bari, da za a iya zama da ita a ji matsalar ta, ko za a iya taimaka mata. Ya lura ko a cikin ma'aikatan ba ta da sukuni, ba ta sakin jiki da su. Kuma yanayin ta ƙarara yake bayyanar da damuwa duk da tana da ƙoƙarin dakiya.
*
Alhaji Zailani ya din ga kiran lambar Hajiya Amina. Gaba ɗaya ya rikice hankalinsa ya yi mummunan tashi, ya rasa abin da yake yi masa daɗi, yana tsoron kar ta aikata wani abin da zai kawo matsala. Ga jirginsa sai washegari zai koma Kano, ga shi yana da manyan uzururrukan da yake son yi a Abuja, da ba zai iya tsallakewa ya bar su ba.
Shukura ta je har gida, ta sake samun Hajiya Amina ta lallaɓa ta a kan ta amince su je gurin Doctor Sabo, amma ta ce babu inda za ta je. Da ƙyar ta amince ta ce ba za ta je a ranar ba sai washegari.
Shukura ta ɗan numfasa ta ce "Mami ba na son yi miki maganar nan ki na cikin damuwa, sai dai nima ba a son raina ba, na rasa abin da yake yi mini daɗi"
Cikin damuwa Hajiya Amina ta ce "Dan Allah ki kwantar da hankalinki, kar wannan cikin ma ya sake samun matsala mene ne?"
Ta numfasa ta ce "Sagir ne fa yake ta ƙoƙarin dawo da tsohuwar matarsa" Hajiya Amina ta ce "To shi ne ki ka damu haka? Dan Allah ki rabu da shi ya ƙarata, ki lallaɓa ki haihu lafiya kalau, kin ga ga hawan jini ki na fama fa"
"Wallahi Mami zuba masa idon na yi, takaicina bai gaya mini ba, su na ta ƙwarbai da Hajiya, ta ce ba zai dawo da ita, a bakin ƙannensa nake ji".
"To babu ruwanki, su sha'anin dangin mijin nan ba a zaƙalƙale musu, idan ta dawo ɗin ma wataƙila su tattara su haɗe kai, babu ruwan ki ki kula da kan ki, ki sauka lafiya"
Shukura ta jinjina kai ta ce "In sha Allah, sannan dan Allah Mami ke ma ki kwantar da hankalinki, nutsuwarki ita ce ta wa, dan Allah Mami ki kwantar da hankalinki kema"
"Wallahi Shukura ƙarfin addu'a ya sanya mini nutsuwa da tawakalli, yadda ku ke yi mini biyayya da ke da Yusuf ko ni na haife ku, Alhamdillah na san iya abin da za ku yi mini kenan. Kuma na san ko yau na bar Duniya za ku tuna da ni ku yi mini addu'a"
Idon Shukura fal hawaye ta ce "Mami ke uwa ce abar alfahari, har Duniya ta naɗe ke uwa ce a gare mu, kuma muna alfahari da samun ki" Suka rungume juna da ita da Shukura, Hajiya Amina ta ci gaba da gode wa Allah, tana jin da natan ta haifa wataƙila ma ba lallai su yi mata biyayya haka ba.
Sai bayan tafiyar Shukura, sannan ta shiga ɗaki, ta tarar da kiran wayar Alhaji Zailani rututu.
Yana ganin kiranta ya ɗaga, bai tsaya amsa gaisuwar ta ba, ya hau tambayarta abin da ya hana ta tafiya.
Ta ce "Matsala aka samu, kuma na yi ta kiran ka a waya, ba ka ɗaga wa"
"Matsalar me?"
"Ba komai, idan ka dawo ma yi magana"
Ya ce "Yanzu nake son ki gaya mini koma mene ne, meye dalilinki na kiran Sharif kina tambayarsa ana haifar mace babu mahaifa?"
Ta ce "Amma laifin me na yi haka? Na tsaya a Egypt su duba lafiyata ne, tun ina can nake neman ka, ban same ka ba, sakamakon gwajinsu ne ya tabattar da ba na ɗauke da mahaifa"
"To uban waye ya ce ki je? Ba sai da na ce miki ki bar batun yawon neman haihuwar nan ba, da yake ban isa na saka miki doka ki bi ba, kin raina ni bani da mutunci a idonki?" Duk bayanin da ta so ta yi masa, yaƙi saurararta, ya din ga zazzaga mata bala'i. Ranta ya ɓaci, ta ga Sharif bai kyauta mata ba, ya za a yi daga tambayarsa abu ya ɗau waya ya kira shi ya gaya masa, ai gara ta gaya masa da kanta, duk da ba wani abin ta ce masa ba, tambaya ce kawai ta yi masa.
*
Ɓamgaren Alhaji Fatuhu, Hajiya Suwaiba kamar ta yi bindiga, ganin ya amince ana yi masa maganin gargajiya, a ganinta dan Fadila ta saka baki ne, ta lallaɓa shi yake yi. Yanzun ma Fadila tana ta ƙoƙarin kunna garwashin da za ta yi masa turare, gefe ta kunna mp sautin ayoyin ruƙiyya su na tashi a hankali.
Ya kalli Fadila ya ce "Baby, ina fatan dai magungunan nan, babu wani abu na kauce hanya a cikin su?"