Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 53
Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 53: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 53. Ta girgiza kai ta ce "Haba Daddy, kai ma ka san ba zan yi duk wani abu da…
391 words
Ta girgiza kai ta ce "Haba Daddy, kai ma ka san ba zan yi duk wani abu da zai taɓa imaninmu ba in sha Allah, Kawu ne duk ya bayar da su, kuma ka san shi ma masanin Addini ne sosai. Babu wani na shirka a ciki."
Ya ce "To ki yi haƙuri, kawai da na tambaya ne, kin san yanayin abin, kar garin magani mu kauce hanya na je na mutu a mummunan tafarki, ya zamana na kasa jure ƙaddarata na kauce hanya"
Fadila ta ce "In sha Allah ba zaka mutu yanzu ba, za ka samu lafiya"
"To ki yi haƙuri, na ga kin ji haushix
Ta girgiza kai ta na ɗan murmushi ta ce "A'a ban ji ba"
"Kin ji mana, kin tura baki gaban ne ba ki ji haushi ba?" Sai kuma suka yi dariya a tare.
Ya ce "Ki yi haƙuri, in sha Allah ba zan sake magana ba, na yarda da ke, ba zaki cutar da mu ba"
Hajiya Suwaiba ta shigo ɗakin, tana basarwa jin yadda ɗakin ya ɗume da ƙamshin jan almiski, da ƙaurin hayaƙi. Ta ɗan taɓa baki a ranta ta ce watakila ma a cikin wannan tsiyatakun take mallake ka.
Ta ajiye masa kwanukan Abinci, ta juya za ta fice.
Ya ce "Ba magana ne?"
"Sannu ya jiki?" Ta faɗa a daƙile.
"Jiki Alhamdillah, a hankali ji nake jikina ya yi daɗi, na ɗan samu sassauci daga abin da nake ji kamar an ɗaure ni, ba na iya motsi sai da ƙyar da dabara, da ƙirjina da yake yi mini nauyi nake jin kamar an toshe mini baki da hanci da kokowa nake numfashi" Duk da tana jin haushinsa sai kuma ta saki fuska ta ce "Alhamdillah, sauƙi ƙazanta, duk ba wai duhu ne da ita sosai ba.
Shiru Hasna ta yi ta kamo wata hirar, ganin alamun idan ta matsa Nana za ta yarfa ta ne a gaban baƙuwarta. Ba a taɓa ma'aikacin da ba ya shakkar ta ba sai Nana. Duk abin da ta saka ta na aiki za ta yi, amma ba ta son rainin hankali.
Bayan sun fito Asal ta tsaya ta kalli Hasna ta ce "Hasna"
"Na'am"
"Ina ga yarinyar nan ta yi dai-dai da abin da nake nema"
"Wace yarinyar?"
Asal ta ce "Wannan 'yar Nigeriar, ina buƙatar za ki ba ni ita"
Ayshercool 08081012143