Kenza eBookz

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 8

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 8

Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 8: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 8. Ya yi murmushi ya ce "Sweetheart, Allah ya amsa mana, ɗan duba mini…

3,367 words

Ya yi murmushi ya ce "Sweetheart, Allah ya amsa mana, ɗan duba mini paracetamol idan ki na da shi, kaina yana ciwo, ina so na je asibiti ma a duba ni ko bp na ne ya hau"

Cikin damuwa ta ce "In sha Allah ba shi ba ne ba ya hau, dan Allah ka kwantar da hankalinka, mu na buƙar lafiyarka just recently fa kai ne ka ke yi mini nasiha a kan yadda da ƙaddara"

Ya girgiza kai ya ce "A'a ba ma damuwar na saka a raina ba, kawai jikina ne babu daɗi"

Ta tashi ta ce "Bari na ɗaukko maka" ta nufi bedroom ɗin ta.

*

Alhaji Zailani ne zaune a gaban malam Gambo, sai gumi yake yi kamar ya yi wa sarki ƙarya.

"Na rasa gane abin da ya faru gaba ɗaya, ni dai na san mun yi da kai za mu yi magana da wanda ta aura ɗin, na ba shi kuɗi ya sake ta, sai dai ban san meyafaru ba na kira shi ɗin a zahiri, ban kira shi ba na kasa tunawa, ni dai kawai na ganshi a mafarki ban ma san meyafaru ba kawai na farka na ji tamkar an shaƙe ni, da ƙyar nake numfashi" Ayshacool Ta tashi ta kwance kayan da Ummi, ta yi mata sayayyar su. Ɗan kayan shafe-shafe ne, da turaruka sai under wears, duk da masu arha ne Nana ta ji daɗi sosai da sosai. Duk da tana jin haushinta, amma ta san idan ba Ummin ba, babu wanda zai tsaya tsayin daka ya yi mata wannan abin. Ta haɗa da na gurin Hajiya Amina, duk ta jere. Ta janyo drower mudubin, ta ga burshes ne da comb a ciki. Ta mayar ta rufe.

Ta janyo jakar kayanta, ta buɗe wardrobe ɗin, ta ga ɓangare ɗaya shaƙe da kayansa, sai da abin ya bawa Nana mamaki. Ɓangare ɗaya ta jere kayanta, ta tsaya tana kallon kayan, duk da galibi wanda hajiya Amina ta ba ta ne, ba ta san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba. Ta daɗe tana burin ganin kayanta a cikin wardrobe. Dan a gida, a wata tsohuwar adakar kakar su take zuba su, ƙarewa wataran talauci ya ishi Baba ya ce ta zazzage kayanta, ta ba shi. Haka ta ba shi ya sayarwa 'yan gwangwan ya sayo mata viva ya bata wai ta zuba kayan a ciki, tun da tsummokaran nata ba su da yawa. Daga baya ta koma zubawa a kwalaye, daga ƙarshe dai Jamila ce ta samo mata ghana must go ta bata, take saka kayan ta a ciki. Amma yau ga kayanta a wardrobe, kuma kaya kusan set goma sha uku, sababbi da tsofaffi, ga atamfofinta uku da ba a kai ga ɗinkawa ba. Ta ninke bargonta, da bedsheets da Shukura ta bayar a bata, ta saka su a saman wardrobe ɗin. Drower ƙasan wardrobe ɗin kuma, ta saka takalmanta guda biyu, da jakar gidan sarkin baka, da pad ɗin ta. Ta gyara kan katifar ta ɗame ta da bedsheets. Ta tashi tsaye tana kallon katifar, ita ma tsawon rayuwarta a kan wani tsohon bargon Baba take kwana, shi ma dai na kakar ta ta ne, bargon nan tamkar ya koma audigarsa saboda tsufa, amma yau albarkacin aure, ga ta da ƙatuwar katifa.

Wani murmushin ne ya sake suɓuce mata, ta juyo kawai ta yi karo da shi a tsaye a bayanta.

Ba ta san lokacin da ta ƙwala ihu ba, dan sam ba ta ji alamun mutum a bayanta ba. Kuma kasancewar ta ƙure da jikin katifar, razanar da ta yi, sai ta faɗa kan katifar.

Taku ɗaya ya ƙara, ya tsaya a kanta yana kallonta.

Ayshercool 08081012143 Ayshacool 29

Ƙara rikicewa ta yi, ta kasa tantance abin da take gani daga cikin idanunsa.

Ya sauke rawaninsa, ya saka hannu a aljihunsa, ya ɗaukko wayarta ya ajiye mata a gefen ta. Tashi ta yi zaune tana kallon wayar, gaba ɗaya ta manta ma tana da wata waya, a ina ya samu wayata? Ta tambayi kanta.

Ta bi wayar da kallo, ta kasa taɓa ta. Ya sake zura hannunsa a cikin aljihunsa ya ciro wata roba, ya ajiye mata, ya juya ya fita. Sai da ya fita ta ɗan samu ta nutsu, ta kai hannunta ta ɗauki wayar ta duba ta ga a kashe take, sai ƙamshi take yi. Ta kalli robar da ya ajiye mata, dabino ne fal a cikin robar lubiya.

Gefe kuma ga kwanukan abinci, fulasan kawai ta kalla ta san daga gidan Hajiya Amina suke.

Tana cikin tunani, ta ji sallamar mace. Ta amsa tare da kallon ƙofar ɗakin. Wata mata ce ta shigo, Nana ta yi mata maraba, ta shimfiɗa mata sallaya ta zauna.

Bayan sun gaisa Nana ta ce "Ban gane ki ba"

"Eh ai ba ki sanni ba, a nan baya muke, aka ce ai an kawo amarya na ce bari na zo mu gaisa"

Nana ta ce "Allah sarki, dama da mutane a nan haka? Shiru nake jin unguwar duk da jiya na zo"

Matar ta ce "Eh, ai a nan baya nake, sunana na Haulat, amma kin je kun gaisa da mutanen gidan"

Nana ta girgiza kai ta ce "Ai ban san da mutane a gidan ba"

Haula ta ce "Ai ba su fiye zama bane ba, kullum cikin yawo suke, amma yau ko gobe za su dawo."

Zuwan Haulat sai ya ɗebe wa Nana kewa, su ka yi ta hira.

Sun daɗe su na hirar, sannan ta yi wa Nana sallama, ta rako ta har bakin ƙofar ɗakin ta ce "Idan na fara fita, nima zan kawo miki ziyara"

"To shikenan, ai a nan baya muke"

Nana ta ce "Kuma da gidaje a gurin? Na ga duk kangwaye ne?"

Haula ta ce "Gamu kuwa, akwai gidaje a gurin"

"Allah sarki, to na gode sosai ki gaida gida"

Yana zaune a kan benci, yana shan shayi a cikin ɗan ƙaramin kofin nan nasu, Nana ta jima tana mamakin kofin da suke shan shayin nan, tamkar wasan yara. A ganinta sai mutum ya sha goma bai ƙoshi ba. Tana hango shi su na fitowa da Haulat, ya rufe fuskarsa. Ta zo za ta fita ta tsaya tana gaishe shi, amma ya yi shiru, kuma bai ɗaga kai ya kalle ta ba, ta fita.

Sai da Nana ta ji babu daɗi, haryanzu ita ba ta ga wata alama ta hauka a tare da shi ba, kuma jiya ya yi magana ba kurma bane ba, tsagwaron wulaƙanci ne ya sanya sai a yi masa magana amma ya yi shiru.

Da daddare ma, zuwa ya yi ya saka ta a gaba, yana kallonta yana kallon kwanukan abincin da ba ta san waye ya kawo ba, ta san dai na gidan Hajiya Amina ne.

Haka ta zuba masa ya ja gefe ya sauke rawaninsa ya ci abinsa, sai dai da ya gama ci, yake ɗaukar kwanon da ya ci abinci ya fita ya wanko ya zo ya ajiye. Abin da ta lura da shi, shine mutum ne mai tsafta sosai. Ita dai tana gefe sai dai ta saci kallonsa, sai dai ƙasan zuciyarta tana mamakin yadda yau ba ta jin bugun zuciyar, sai dai sanyi da take ji.

Bayan ya ajiye kwanukan, ya tashi ya kwance rawanin sa, duk da wayarta take ɗan dannawa, sai da ta saci kallon gashin kansa, kawai ta ji tana son ya ware shi, ta ga adadin tsawonsa. Ya rage kayan jikinsa, ya ɗauki radion sa, da kayan shayinsa ya fice daga ɗakin. Yana fita ta ja ajiyar zuciya, ta tashi ta shiga banɗaki, ta yi wanka ta wanke bakinta, tayi alwala, ta fito ta shirya ta kwanta.

A iya saninta, wayarta take ɗan duddubawa tana tunanin yadda aka yi ya samu wayarta.

"Amarya ba kya laifi, ko kin kashe mai gida?"

"Meye haka wai?"

"A ina?"

"Ni fa yanzu matar aure ce, ya zaka din ga kawo ni nan, duk lokacin da ka ga dama?"

Ya ajiye littafin hannunsa ya ce "Ina ruwana da auren ki? Auren jeka na yi ka? Auren da haryanzu ba ki da tabbas a kansa? Haryanzu ba fa ki san me ki ka aura ba, kuma kamar an ce ma mahaukaci ne ko?"

A ƙule Nana ta ce "Ko ma dai mene ne ina ruwan ka? Zan gano da kaina, koma wane ne, idan ma mutum ɗin ne ko akasin haka"

Ƙaisar ya ce "Jiya fa ki ka zo nan ki na yi mini kuka, ki dai san iya abin da yakamata ki yi, da inda yakamata ki tsaya kar allura ta tono garma"

"Eh, haushi ka ke ji na yi aure, ba tare da tsammaninka ba, balle ka sake hanawa" Ayshacool Kawai ƙaisar ya bushe da wata irin dariya, da sai da ta tsorata ya ce "Ke haryanzu ba ki san ina ki ka dosa ba, ni ba jinnil ashiƙ bane da zan hana ki aure, na baya ma mazan naki ne ba su yi mini ba, duk da wannan ma da na farga da wuri sai na ruguza shi, sai dai idan na matsa za ki iya rasa rayuwar ki baki ɗaya, shi yasa na ƙyale"

Nana ta ce "Saboda me?"

"Kawai" ya bata amsa.

"Amma wai da gaske aljani yana auren mutum?"

"Eh"

"To ku ina naku matan ku ke auren na mutum?"

Ya ce "To ai ni ba aljanin soyayya ba ne ba da za ki tambaye ni."

Nana ta ce "Amma ka hana ni aure? Me yasa ka saka Saleh ciwon ciki?"

"Ke ko duk matan bil'adama sun ƙare zan auri masifaffiya ne mai azabar taurin kai kamar ke ne?"

"Eh abin nan ne, da ake cewa makaho ga ido, ya ce wari yake, na fi ƙarfin ka ne kawai"

Ya ce "Ko?"

"Eh mana, dan Allah ka gaya mini ya ake yi ku ke auren bil adama"

"Ni ma ban sani ba, sai dai zan baki wani littafi ki karanta, soyayyar Aljani Ridwan, da bil adama" Nana ta zabura ta ce "Dan Allah, ya sarkin baka, a wane hali yake yanzu? Kuma ni ba littafin soyayya nake so ba, wannan littafin na Jaddul jinn nake so ka bani na ƙarasa karantawa"

"Ba zan bayar ba, kuma ba wannan ne ya sanya na kira ki ba, duba jikin mudubi, ki zo ki gaya mini abin da ki ka gani"

Nana ta ce "Wallahi ba zan kalla ba, masifa da bala'i kawai ka ke nuna mini a cikin mudubin nan, Allah ya sa ya tarwatse...

"Wallahi sai kin kalla, wataƙila zuciyar ki ta saduda, ki yi abin da ya dace"

Kawai ta ganta a gaban mudubin, Jamila ta gani a kwance tsirara, Hajiya Sa'a na ta tsira mata allurar nan. Tsigar jikin Nana ta tashi, ta rintse idanunta ta ce "Dan Allah me take yi mata? Jamila ce fa"

"Ƙwarai ita ce, Matar ta umarceta ta kawo mata jininki, ta ce ba za ta iya ba, shi ne ta bi ta bayan gida, yanzu haka ta gama mallake ta, duk abin da ta ce ta yi shi za ta din ga yi, ba za ta taɓa kaucewa maganar ta ba"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, yanzu ya zan yi, kar ta cutar da Jamila, shiyasa ni tun farko ba na son yawon maƙwabtan nan da take yi. Wannan matar ba ita ta bayar da Muhsin ba?"

Ƙaisar ya ce "ƙwarai ita ce, kuma ba wannan ba, bayan cin moriyar ganga, yada ƙwauron ta za ta yi. Ba wannan ba bayan ɗalibin ki da ki ka rasa, babansa ma an sako shi gaba, wataƙila nan kusa ko nesa kaɗan ya bi ɗan nasa".

"A'a ba gaskiya ba ne ba Ƙaisar, hakan ba zai taɓa yiwuwa ba"

"Dama ai ba gaya miki nake yi domin ki yadda ba"

Ta ɗan yi shiru cikin jimami da tashin hankali, ta ce "Yanzu meye abin yi, ba na son Jamila ta faɗa ga halaka" ta yi magana cikin kuka.

"Kin fi ni sanin abin yi ai Nana Asma'u"

"A'a ban da wannan, wannan ba mafita ba ce ba, na gaya maka ba zan yi wannan ba"

Ya ce "To shikenan, sai ki zura ido mutane na cutuwa alhalin ki na da yadda za ki yi, ki taimaka musu"

"A'a ƙasair" kawai ta ga tamkar ya wurgota waje.

Ihu ta saka ganin tana faɗowa daga sama, za ta faɗa cikin ruwa. A razane ta tashi tana faɗin "Ya Allah" ta dafe saitin zuciyarta tana haki.

Ita kaɗai ce a cikin ɗakin, ta janyo wayarta ta duba lokaci, ta ga uku da rabi na dare. Ta yi shiru domin tuna abin da ya razanata daga baccin, amma ta kasa, kawai faɗowarta daga dogon tsaunin da libararyn Ƙaisar zuwa ƙasan ruwa ta iya tunawa.

Ta kalli ɗakin, fitila a kunne, amma ba ya ciki.

Ta tashi a hankali, ta nufi ƙofar ɗakin, ta leƙa harabar gidan.

Yana kwance a kan benci, yana bacci ya tada kansa da hannunsa. Gabansa ɗan murhun dafa shayinsa ya mutu, ga butar shayin da kofinsa.

Wasi-wasi ta shiga yi, a kan ko tashin sa za ta yi. Wutar gurin ce ta ɗauke gaba ɗaya, gurin ya gauraye da duhu, aka yi wata irin walƙiya mai hasken gaske, kawai ta ga wannan tsohon a tsaye a kansa. Tamkar an dasa ta, ta kasa motsi ta kasa gaba ta kasa baya, aka sake walƙiyar nan, ta sake ganin tsohon nan a tsaye a kansa, sai dai wannan karon ya feso wani irin tartsatsin wuta da ya tilasta mata yin baya cikin matsanancin tsoro. Ayshacool A hankali ta buɗe idonta, kawai ta ganshi a tsaye yana kallonta, kamar taɓaɓiyya haka ta zura da gudu, ta koma kan katifa ta kifa kanta tana haki, saboda tsoro da razani. Maganganun Ƙaisar suna nema su fara zama gaskiya a kan mutumin nan. Tabbas ta fara tantamar kasancewar sa mutum. Duk da ta san ba ta da cikakkiyar lafiya ƙaisar ya saba tsorata ta, amma ya za a yi a ce mutumin da ta hango yana bacci, cikin abin da bai fi ƙifta ido sau biyu ba, ta gan shi a gabanta. A ɓangaren sa shi ma mamaki yake yi, me take yi a tsaye a bayan labule a wannan tsohon dare haka?.

* Hajiya Sa'a ce take kallon Jamila, tana wani irin mugun murmushi ta ce "To jamsy me ki ka ce yanzu?"

Jamila ta ce "Ta yaya zan samo miki jinin nata?"

"Yauwwa Jamila, ba wani abu ne mai wahala ba, magani zan baki a abinci, ki kai mata ta ci, sai kuma abin da za ki ajiye mata a ɗaki"

Jamila ta ce "To shikenan, babu damuwa an gama"

"Kin tabattar za ki iya?"

"Eh mana, me zai hana?"

Hajiya Sa'a da Maman Khairat suka kalli juna, suka sheƙe da dariya, Hajiya Sa'a ta ce "Yauwwa jamcy, zan gaya miki duk yadda za a yi " Jamila ta gama wuninta a gidan, sannan ta tafi gida. Sai dai gaba ɗaya ta din ga jin ta wani iri, tamkar akwai wani abu da ba dai-dai ba a tattare da ita.

**** Tamkar bakin mama ya taɓo ƙeyarta, haka take washe baki, a gaban malaminta. Ta ce "Anya ka taɓa yi mini aiki mai zafin wannan? Komai ya tafi yadda ake so, wallahi yadda na tsara masa komai haka ya bi, dama abin yana cin sa a rai ƙiri-ƙiri mai kuɗi ya zo ta ce ba ta so"

Ya yi dariya ya ce "Mu ɗin na wasa ne? Gangaran ne ni fa, ai duk taurin buƙata muka ɗauki allo muka hau kan buzu mun gama da ita"

Mama ta ce "Ai kuwa na ga zahiri, malam saura na 'yan matana, a bamu na farin jini. Wallahi duk samarin nasu ba na arziki sai tarkace babu wata mamora a tattare da samarin nasu, ni kuma masu maiƙo nake so, inda zamu jingina mu huta, ka san rayuwar ce sai a hankali, ba zan so mu dauwwama a talauci ba, su yi gadon masifa ba"

Yayi murmushi ya ce"Tabbas wahala abar gudu ce, za a san abin yi, ki bayar da kuɗi, za a sai binta sudan, da ma'u wardi, sai farin goro zan yi musu wani aiki"

"To kamar nawa ka ke ganin zai isa?"

Ya ɗan yi shiru ya ce "Ba da dubu goma sha biyar, akwai turarukan da zan haɗa da su ma, da wasu saiwoyi." Ganin buƙatar ta ta biya a baya, ya sanya babu fargabar komai ta amince ta ɗebo kuɗi ta ajiye masa, ta yi masa sallama ta tafi.

**** Bayan sallar asuba kallonsa Nana take yi, tana tuna abin da ya faru jiya da daddare. Fuskarsa daina zahiri ba ta yi kama da ta miyagu ba, ta kalle shi daga sama har ƙasa, babu wata alama da take nuna ba mutum bane, a suffar sa ta zahiri.

Amma dole tana buƙatar tabattar da waye shi, ta kalli inda yake zaune yana ta fama da radio. Akwai aikin jin radio, sai dai magana ce aiki a gurinsa.

"Ina kwana?" Ya ji muryar Nana babu tsammani. Ya ɗago ya kalle ta domin ya tabbatar idan da shi take.

Ta sake cewa "Ina kwana?" Ɗaga mata hannu kawai ya yi, tare da jinjina kai.

Takaici ya kama Nana, maganar ce dai ba zai yi ba.

Kawai ta ga ya tashi ya ɗauki ɗan kurfotin dafa shayinsa, ya zuba ruwa a cikin butarsa. Ya ɗauki wata baƙar leda ya tashi zai bar mata ɗakin. Cikin sauri ta tashi ta ce "Kawo na dafa maka" ya kalle ta ya girgiza mata kai.

Ta miƙa hannu za ta karɓi butar, ya janye ya ce "A'a"

Ya juya zai fita, kawai ya ji ta biyo bayansa. Ya tsaya ya waiwayo, tana ƙoƙarin tsare shi da ido, amma ta kasa. Ya kuma yin gaba ta sake bin sa.

Sai ya fasa fitar, ya dawo ɗakin, ita ma ta biyo shi ta dawo.

Ya samu guri ya zauna, yana kallon butar shayinsa yana kallon Nana, da ta maze.

Bayan wani ɗan lokaci ya tashi ya fara shirin shiga wanka. Nana ta maze ta ɗauki wayarta tana dannawa.

Sai da ya shiga banɗakin, ta bi bayansa da kallo.

Hajiya Amina ta kira a waya, cikin ikon Allah kuwa bugu biyu ta ɗaga tana "Amarya kin sha ƙamshi"

Cikin jin nauyinta Nana ta ce "Hajiya ina kwana?"

"Lafiya ƙalau Nana, ya ki ke fatan kina lafiya? Ina ta kiran wayar ki a kashe" Ayshacool A nan Habu ma ya karya, ya zauna su ka yi hira da Nana, shi kuwa da ya gama cin abincin sa, ya koma gefe ya yi musu shiru.

Shi ma bai wani jima sosai ba, ya tafi. Gaba ɗaya zaman shiru ya ishi Nana, shi ba kula ta yake yi ba, sai dai ta wuni a ɗaki shiru, shi kuma yana waje, yana jin radio da aikin dafa shayi kamar ibada, ko hutawa ba ya yi, har mamaki take yi idan yana gane abin da ake yi a radion.

Bayan azahar yana kwance, a ɗakin, radion ta cika wa Nana kunne, ta dube shi ta ce "Dan Allah zan shiga cikin gidan nan, na yi musu sallama, tun da na ga alamar akwai mutane a cikin gidan" ya gyaɗa mata kai kawai.

Ta ɗumama ruwa a kan gas, ta shiga ta yi wanka ta fito, sanye da dogon hijjabi. Ta ɗauki kayan da za ta saka, ta koma banɗaki ta canza ta fito. Doguwar riga ta sako, hannunta riƙe mayafin rigar. Ta cire hular kanta, ta tsaya a gaban mudubi tana shafa mai. Abin ka da mace, kuma amarya, sai ta tsaya a gaban mudubin tana gyara fuskarta.

Ta tsiyayo humra ta shashshafa a jikinta. Ta janyo drower mudubin, inda yake ajiya kayansa ta buɗe a hankali, ta waiwaya ta kalle shi, ta ga idonsa a rufe, ta ɗauki turaren sa, ta tsiyaya a hannunta, ta shafa a wuyanta.

Yana daga kwance yana kallonta, ta ƙasan idonsa. Sai da ta gama tsaf, za ta fita kawai ya yi gyaran murya. Ta tsaya ta waiwayo tana kallonsa. Ya yinƙura ya tashi, ya nufe ta, ta tsaya ƙyam tana kallonsa. Gani ta yi tamkar zai shige cikin ta, babu shiri ta fara ja da baya, sai da ta dangana da jikin bango.

Ayshercool 08081012143 Ayshacool Page 30

Zazzaro ido Nana take yi, numfashin ta na neman sarƙewa, saboda tsoro da fargaba.

Readers Also Read