Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 9
Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 9: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 9. Ya saka hannunsa ya kamo hannunta cikin nasa, wani irin sanyi ya ratso ta,…
3,369 words
Ya saka hannunsa ya kamo hannunta cikin nasa, wani irin sanyi ya ratso ta, tun daga tafukan hannayenta har zuwa ƙafafuwan ta. Ya kama gefen rigarsa ya goge in da ta shashshafa turare a hannunta. Ya saka hannunsa a gefen wuyanta, nan ma ya goge wanda ta shafa a nan. Na saman rigarta yake kallo, sannan ya kalli idonta. Ta yi tsuru-tsuru a ranta ta ce "Daga ɗan shafa turaren sa, shi ne yake mini wannan tijarar haka"
Idonta ta saka kwalli, bakinta kuma ta saka man leɓe mai kala, sai girarta da ta gyara. Ba ta gama zancen zucin ba, ya saka hannunsa ya fara goge man da ta saka a leɓenta. Riƙe hannunsa ta yi za ta yi magana, amma ya yi mata wani irin kallo da ta rasa na mene ne, babu shiri ta yi tsit. Ya goge leɓenta tsaf. Ya kalli idanunta da suka sha kwalli, ya mayar da hannun sa kan girarta, ya hargitse gashin girarta.
Ya zare mayafin rigar da ta ɗora a kanta, ya ciro hijjabin da ta shiga wanka da shi, ya hau saka mata.
Kamar ta rusa ihu ta ce "wanka fa na yi da shi, ba ka ga duk danshin ruwa a jiki ba?" Bai amsa mata ba, ya jefa mayafin rigar a kan katifa, ya koma gurin da yake zaune ya zauna. Wani irin takaici ya tokare Nana, kamar ta kurma ihu, saura ƙiris ta ce ta fasa fitar, amma ta tuna zaman shiru za ta zauna ta yi a ɗakin, ko ma shi ya fice ya bar ta. Ta ja takalmanta ta fice daga ɗakin tana haɗe fuska.
Fasalin gidan ya yi mata kyau sosai da sosai, sai da ta zagaya ta bayan wata baranda, sannan ta gano ƙofar shiga. Tun daga barandar take ɗan jiyo hayaniya sama-sama.
Ta buɗe ta shiga da sallama. Samari ne su kusan biyar a falon, su na kallon ball su na ta hayaniya. Sallamar ta ce ya sanya su yin shiru, suka amsa mata.
"Sannunku, dan Allah matar gidan nake nema"
Ɗaya daga cikin su mai riƙe da remote a hannunsa ya ce "Tana sama" ya yi maganar yana nuna mata upstairs.
A falon saman benen ta tarar da matar, babba ce mai jiki fara tas da ita, tana shan lemo a kofi tana danna remote.
Ta amsa sallamar Nana, tana yi mata kallon rashin sani.
"Ina wuni?"
Matar fuskarta babu yabo babu fallasa ta ce "Lafiya ƙalau, zauna mana ga kujera nan" Nana ta zauna, ta kalle ta ta ce "Dama ni ce matar mai gadinku, da muka tare, na ga tun da muka zo ba kwa nan, sai jiya na ji motsin mota a gidan, shi ne na ce bari na zo mu gaisa"
"Allah sarki, sannu ko? Da maigidan ya ce mini buzaye ne"
Nana ta ce "Maigidana ne buzun, ni bahaushiya ce"
"Ohh Allah sarki, ya sunan ki ne?"
"Nana"
Ta ce "Ma sha Allah, sannun ki"
Nana ta ce "Yauwwa, idan akwai wani aiki ma, idan ki na buƙata, idan bai fi ƙarfina ba, a yi mini magana zan yi in sha Allah"
Matar ta jinjina kai ta ce "To shikenan na gode sosai" Matar ta ɗan yi shiru tana kallon Nana. Ta yi mamakin yadda yarinyar mace kamar Nana, ta auri Buzu har yake yawon gadi da ita.
Sanin da Nana ta na idan ta koma, zaman tsuru-tsuru za ta yi da wannan kurman mutumin, ya sanya ta ja ta yi zamanta, ta ci gaba da kallon Tv. Matar kuma ba ta ce mata uffan ba. Can Nana ta ce "Hajiya ba ki da 'yan aiki?"
"Ina da su, ba na zama ne sosai a ƙasar, duk sun watse mun ma dai samu saɓani ne"
"Ke ki ke aikin da kan ki?"
"Ni da yara muke yi"
Nana ta ce "Allah sarki, idan kina buƙatar aikin ma, zan din ga zuwa ina yi miki"
Duk da tana basar da Nana, sai da ta yi murmushi ta ce "To in sha Allah" sai da Nana ta gama kallon, sannan ta tashi ta yi wa matar da ko sunanta ba ta sani ba sallama.
Ta sauka ta fita, sai dai tana fita ta yi kiciɓis da shi, sai da ta tsorata, yana tsaye a bakin ƙofar shiga cikin falon gidan, yana jiran ta
"Lafiya? Ya na ganka a nan?" Yana ganin ta fito kawai ya yi gaba ya bar ta a gurin. Ba ƙaramin ƙuluwa take yi da wannan dunkun-dunkun ɗin da yake yi ba na rashin magana.
*
Babbar mace ce a ƙalla za ta yi shekara talatin da bakwai zuwa da takwas, hannunta riƙe da waya take kaiwa tana komowa a ɗakin, ta sake kai wayar kunnenta.
"Hello Yaya kina ji na? Dan Allah maganar nan da gaske ki ke?" Ayshacool Daga ɗaya ɓangaren matar ta ce "Oho ban tabattar ba, amma kin san babu lallai a yi jita-jita da irin wannan maganar, amma abu mafi sauƙi ki saka lokaci mu je mu tabattar"
"Yanzu Yaya idan maganar nan ta tabatta, baban su Imaran ya kyauta mini? A yi auren yarinya ta amma a kasa gaya mini an yi mini adalci a haka? Ba fa shikaɗai yake da hakki a kan yarinyar nan ba"
"To yaya za ki yi maijidda? Kawai mu shirya mu je shi ya fi sauƙi"
Gyaran muryarsa da ta ji ya sanya ta kashe wayar babu shiri, tana faɗin sannu da zuwa.
Ya ƙura mata ido ya ce "Meye haka na ganki wani iri?" Ta so ta jure zuwa ya samu nutsuwa su yi magana ta fahimta, amma ta kasa. Cikin damuwa ta ce "Labari na ji wai an yi wa Nana aure, shi ne nake son in tabattar"
Nan da nan ya haɗe fuska tamkar tasowar hadari lokacin marka-marka. "Wato ba zaki fasa kiran tsohon mijinki ba ko Maijidda, ni fa na gaji ba zan lamunci wannan iskancin naki ba na shekara da shekaru"
Cikin ƙoƙarin kare kanta ta ce "Ka yi haƙuri, wallahi ba kiransa nake yi ba. Da Yaya nake waya wallahi"
"Bani wayar nan"
Ta ɓoye wayar a bayanta ta ce "Wallahi ba da shi nake waya ba, Yaya ce" za ki bani ko sai na ɓata miki rai. Ta miƙa masa wayar tana kuka ta ce "Dan Allah baban su Walida, ka bani wayar nan, hankalina ba zai kwanta ba sai na tabattar da gaskiyar maganar nan"
Ya tsaya cak yana kallonta ya ce "Allah wadaran halinki, ko kunyar Ubangiji ba kya ji, babu wata Nana da aka yi wa aure, tsohon mijinki ne ki ke bibiya, tirr da halinki" fashewa ta yi da kuka, tana sheshsheƙa mai cike da ƙunar rai.
*
"Zan yi wanka" ya yi maganar yana tsare ta da ido.
Nana ta ɗaga kai ta kalle shi, ta ce "To ka yi mana"
Ta yi magana tana ɓata rai, tare da mayar da hankalinta kan wayarta, da ta gano tarin fina-finai a ciki. Tun bayan da Hajiya Amina ta bata wayar, ta nunawa Nasiru, ya karɓi wayar ya fita da ita gurin abokan sa aka yi turi, ba ta taɓa sanin da su a wayar ba.
Shiru ya yi yana kallon Nana, ganin ba ta gane abin da yake nufi ba. Kawai ya shiga banɗakin.
Ƙofar banɗakin ta bi da kallo, gaba ɗaya ta kasa gane kansa, babu yadda za ayi ace mutumin da yake da taɓin hankali, ya din ga gudanar da al'amuransa cikin nutsuwa. Sai dai kuma wannan shirun nasa ma, yana ƙara tabattar da taɓin hankalin nasa. Duk da ma ba wannan ba, hankalinta ya fi karkata ga son sanin ainihin waye shi.
Ya shafe tsawon lokaci a banɗakin, dan sai da Nana ta manta da shi ma, sannan ya fito. Jikinsa sai tsuma yake yi.
Ya nufo kan katifar da Nana take kai tsaye, bai ce mata uffan ba, ya zazzageta ya janye bedsheets ɗin da yake shimfiɗe a kan katifar ya duƙunƙune a ciki. Galala ta saki baki tana kallonsa. Lallai babu alamar hankali a nan" ta faɗa a zuciyarta. Sai dai ta lura da yadda jikinsa yake ta tsuma da rawar sanyi.
Ga garin babu sanyi sam, ita gumi ma take yi, amma ta ga yana ta tsuma. Ya jima sosai a haka, daga bisani ya tashi tsaye, ya nannaɗe bedsheet ɗin ya ya jefe mata a ka, ya wuce gaban mudubin.
"Ya haka, me yasa ka jefo mini?"
Waiwayo wa ya yi mata wani mugun kallo, ya juya ya ci gaba da abin da yake yi.
Taɓe baki ta yi, ta tashi ta ɗaukko wani zanin, ta shimfiɗa ta zauna. Hannunsa ɗauke da robar mai, ya nufo ta.
Ya ajiye man a gefenta, ya zauna ya juya mata bayansa. Ƙuri ta yi wa bayansa da ido, daga bisani ta ce "Me za a yi ne?"
Ya ɗauki robar man, ya saka mata a hannunta, ya nuna mata bayansa da hannunsa.
A ɗan tsorace ta ce "Wai taɓa ka zan yi?"
Ya juyo gaba ɗayansa ya zuba mata ido.
Nana ba ta taɓa ƙare masa kallo ba, sai yanzu. A hankali ta fara jin sanyi yana ratsata, bugun zuciyar ta ya fara ƙaruwa.
Cikin sauri ta ce "To juya" ya juya mata. Ta ɗaga robar man ta na kallo, duk rubutun jiki da french ne, ba ta iya gane komai ba.
Ta tsiyayo man, sai ƙamshi yake yi, hannun ta har rawa yake yi, ta kai hannunta bayansa. Sai dai tana ɗora hannunta ta ji tsigar jikinta ta tashi, sanyi na ƙara ratsa ta. Ayshacool Ta ture gashinsa gefe, ta fara shafa man a bayansa, sai dai tana shafa masa, yanayinta yana canzawa zuwa wani abu, da ta kasa tantance mene ne. Tsayar da hannunta ta yi a guri ɗaya, ta ƙi gaba ta ƙi baya, jin zuciyarta na rayo mata wani abu a game da shi. Haushin kanta ne ya kama ta, kawai ta ja da baya ta haɗe rai. Ya sake waiwayo wa ya kalle ta. Kamar wanda aka yi wa dole ya ce "Sanyi nake ji"
Murguɗa baki ta yi, ta ja jikinta lungun katifa, ta yi masa shiru. Ganin ba ta da niyyar sake taɓa shi, ya sanya ya tashi ya nemi guri ya kwanta a ƙasa.
Shiru ta yi tana zancen zuci, iya tsawon rayuwarta, ita ba ta taɓa kai hannunta jikin wani namiji tana sane ba. Kuma ba ta taɓa jin abu makamancin irin haka ba, a tattare da wani ba.
'ki shiga hankalinki Nana, kar wannan farar fatar ta ruɗe ki" wata zuciyar ta gargaɗe ta.
Guntun tsaki ta yi, ba tare da ta shirya ba.
"Ya dai?" Muryar Ƙaisar ta dawo da ita tunaninta.
Ta kalle shi, yana ta haɗa wasu abubuwa a cikin kwalabe.
"Kai ne ko?" Ta yi maganar a ɗan ƙule.
"Na yi me?" Ya yi maganar ba tare da ya kalle ta ba.
"Ka fi ni sani ai"
Ƙaisar ya girgiza kai ya ce "Sanin gaibu sai Allah ai, ban san me na yi miki ba"
Nana ta ce "Ka sani"
Ya ɗan kalle ta, kawai ya bushe da dariya ya tashi tsaye yana faɗin "Kar ki damu, yanayi ne da bil adama su kan kasance a ciki, ai ba ki yi wani abu ba, ba abin damuwa ba ne ba. Kuma ni bani da hannu a wannan lamarin. Sai dai ina tunatar da ke, kafin ki yi aika-aika ki tabattar da wane ne shi"
Banza ta yi masa, ta nufi wata ƙofa da take buɗe.
A hankali ta buɗe idonta, tana kwance a kan katifarta, ta kalli gurin da yake kwance, yana nan kamar yadda ya kwanta. Ya dunƙule jikinsa guri guda, jikinsa ko riga babu. Ta shafa jikinta ta ji gumi take yi, amma shi alamu suka nuna sanyi yake ji.
Ta yinƙura da ƙyar ta tashi, ta ɗaukko bargonta a saman wardrobe, ta nufe shi.
"Ka tashi ga bargo ka rufa"
A hankali ya buɗe idonsa, ya kalle ta, kawai ya mayar ya lumshe. Ba ta haƙura ba ta sake cewa ga shi ka rufa tun da sanyi ka ke ji. Ta yi maganar tana ajiye masa bargon. Hankaɗe bargon ya yi gefe a zuciye, yana ƙoƙarin gyara kwanciyarsa.
"Me ya sa zaka jefar mini da abu, idan ba ka so sai ka jefar mini, haka ɗazu ma ka jefa mini bedsheet a kaina, ni ka daina yi mini haka. Kawai ya tashi zaune. Me Nana za ta gani, kamaninsa sun koma na tsohon nan da take gani a tare da shi. Ihu ta kurma da ƙarfi ta suma a gurin.
*
Sanye take da doguwar rigar bacci shara-shara blue black, ta yi mata kyau sosai, ga tsohon cikinta, tana gefen gado tana shan abu a cikin kofi.
Da sallama ya shigo ɗakin, ta amsa masa, ya zauna a kusa da ita. Ta ce "Ya yi baccin?"
Ya ce "Ya yi da kyar, ban da labarin Anty Nana, babu abin da yake yi mini, yana ta biya mini abin da take koya masa. Babu yadda za a yi ta dawo gidan nan ne ta ci gaba da kula da shi?"
Ta kwaɓe baki ta ce "Ta ina? Na gaya maka an yi mata aure da buzayen da suke gadin gidanmu"
Ya ce "Ikon Allah, to dama buzaye na auren wasu wanda ba irin su ba ne?"
Shukura ta ce "Waye ya san musu ma? Abin ne dai ga shi nan"
"Allah ya kyauta, ni dai Haidar nake ji, da alama sun shaƙu, wai me ki ke sha a cikin kofin nan ne?" Ya yi magana yana karɓar kofin.
Magani ya gani a ciki, ya tsuke fuska ya ce "Wai me yasa ba kya ji ne? Na hana ki shan wannan abubuwan, ya za a yi ki na da tsohon ciki ki din ga shan wannan abubuwan? Sai kin yi wa kan ki illa?"
Shukura ta ɓata fuska ta ce "Ba fa da yawa na sha ba, kuma ai duk dan kai nake yi"
"Kuma ni na ce miki ina bukatar wannan abin? Fruit bai ishe ki ba me ki ke nema kuma? Kawai sai kin illata mini yaro? Wallahi na kuma ganin kina shan wannan abubuwan sai ranki ya ɓaci" ya tashi ya fice ya bar mata ɗakin.
Haushi ne ya ishe ta, kawai ta nemi guri ta kwanta.
Girma da nauyin cikin jikinta, bai hanata yin gudun ceton ranta ba, tana gudun tana waiwaye, ga numfashinta na neman barin huhunta, saboda tsananin gajiya. Karo ta yi da wani mutum sanye da farar riga, miƙa masa hannu take yi, tana faɗin "Dan Allah ka taimake ni" Ayshacool Lokaci ɗaya abin da yake cikinta, ya yi wani irin dunƙulewa, ya na danno ta. Cikin gigita ta tsaya tare da durƙusawa a kan gwiwoyinta, tana jin nishi.
Mutumin da yake bin ta ya ƙaraso gabanta, ya saka hannu ya cire abin da ya rufe fuskarsa da shi.
Cikin tashin hankali ta ce "Daddy"
"Ki yi haƙuri Shukura, ni za ki taimaka, ki sadaukar mini da abin da yake cikin ki"
Jan jikinta ta fara yi, tana girgiza kanta, cikin kuka da azabar naƙuda take faɗin "A'a Daddy, dan Allah ka bar mini jaririna, na baka tawa rayuwar amma ka bar mini jaririna dan Allah"
Ya girgiza kai ya ce "Ba na buƙatar rayuwar ki Shukura, yaron nan kawai nake buƙata"
Mutumin nan mai farar riga, ya buɗe fuskarsa, sai ta ga doctor Sharif ne. Cikin kuka take ce masa "Dan Allah Doctor ka taimake ni, ka ba shi haƙuri".
Bai saurare ta ba, ya durƙusa ya yi mata wata allura, take ta yi wani irin nishi, jaririn ya faɗo.
Ya ɗauke shi har mabiyiyar, ya miƙa wa Alhaji Zailani.
Alhaji Zailani ya ciro wata 'yar wuƙa, ya ɗaga jaririn kansa a ƙasa, ƙafafuwan sa a sama.
Ihu take iya ƙarfin ta, tana yi masa magiya, amma ya ɗaga wuƙar nan zai caka wa jaririn, bai kai ga caka masa ba, ta ji an kira sunanta. Tana ɗaga kai ta ga Nana. Nana ta jefa mata wata sharɓeɓiyar wuƙa, a rikice Alhaj Zailani ya yi kan Shukura, cikin sa'a ta caka masa wuƙar da Nana ta jefo mata.
"Shukura lafiya? Me ya same ki? Me ya samu jaririn naki?" Ta buɗe idonta a hankali ta kalli fuskar mijinta da ke ɗauke da matsananciyar damuwa.
"Meya faru?" Ya sake tambayarta.
Jikinta ne kawai yake karkarwa, tana zare ido cike da matsanancin tsoro da tashin hankali. Ba ta iya yi masa magana ba, sai godiya da ta din ga yi wa Allah a zuciyarta, da ya zamana mafarki ne ba gaskiya ba.
*
Da safe Nana na ta karkaɗe ɗaki tana gyarawa, ko gaishe shi ba ta yi ba, dama ba amsawa yake yi ba idan ta gaishe shi. Sai dai fes take tuna abin da ya faru jiya da daddare, yadda fuskarsa ta canza baki ɗaya. Sai dai haryanzu tana ji a ranta, sharrin Ƙaisar ne ya sanya take ganin wannan abubuwan a tattare da shi.
"Zan yi wanka" ta ji muryarsa tana tsaka da gyara ɗakin.
Ta kalle shi ta ce "To banɗakin zan biyo ka ko ya za a yi?" Ta yi maganar cikin tsiwa.
Bakinta ya bi da kallo, rasa me zai ce mata ya yi, a wannan karon ma, ba ta gane abin da yake nufi ba, kawai ya wuce banɗakin. Yana shiga ta dira mitar abin da yake yi mata.
"Wai zai yi wanka, ko bin sa zan yi na yi masa wankan, ni ban gane ba"
Ta ci gaba da aikinta, yana fitowa bai tsaya wata-wata ba, ya sake yaye bedsheet ɗin da ta gama shimfiɗawa ya rufa yana rawar sanyi.
A hanzarce ta ɗago a ƙule ta ce "Lafiya, meye haka wai?" Ta yi maganar kamar ta fashe da kuka, saboda a lokacin ta gama sanya zanin gadon.
Jin ta tsaya masa a ka, saboda ya ɗauki bedsheet ya sanya ya miƙe, ya watsar mata da shi a gurin.
Ya ɗauki kayan da zai saka ya shiga toilet ya canza, ya fito ya bar mata ɗakin. Cikin hantsi ya fita ya zauna ya takure jikinsa, ɗumin ranar yana taɓa shi.
Nana ta ci gaba da mita tana ƙara gyarawa.
Muryar Habu ta jiyo, ta leƙa ta taga, ta gan su tare a zaune. Yadda Habu ya yi shiru ya nutsu ne, ya sanya ta gane mijinta magana yake yi, amma muryarsa ƙasa-ƙasa, ba a jin tasa sai dai ta Habu ake iya ji.
Ta saki labulen ta nemi guri ta zauna, Habu ya yi sallama a ƙofar ɗakin. Ta amsa masa. Ya ce "Na shigo?"
"Eh bismillah" sai ta ga ya shigo shikaɗai.
Nana ta ce "Ina kwana?"
"Lafiya ƙalau Alhamdilillah. Ya rayuwar?"
Nana ta yi murmushi, haryanzu hausar su wasu lokutan sai a hankali, ta ce "Lafiya ƙalau"
"Ga wannan" ya yi maganar yana ba ta leda.
Jiki a sanyaye ta ce "Malam Habu, abin da ya faru Allah ne ya ƙaddara, wannan ɗawainiyar ta isa haka, kullum sai kun kawo mana Abinci, ga ɗawainiya da ku ke ta yi. Zan fara girki in sha Allah"
Ya yi murmushi ya ce "Kar ki damu, ai dolen mu ne mu kula da ke. Kayan miya ne a ciki da sauran kayan amfani. Duk abin da babu, akwai lambata a rubuce a gurin mijin naki, sai ku kira ni" Nana ta jinjina masa kai. Ayshacool Sai kuma Habu ya yi murmushi ya ce "Amm amarya, mutumin fa ya kawo mini ƙarar ki, ya ce ki na yi masa rashin kunya, ki na ɗaga masa murya. Dan Allah kamar yadda na gaya miki ki yi haƙuri da shi dan Allah. A hankali za ki fuskanci yadda za ki zauna da shi, na san abin zai yi miki wahala amma dan Allah ki yi haƙuri hakan tamkar jihadi ne, ke ma Allah ya kawo ki mu yi tare"
Nana ta haɗiye maganganu da tambayoyi da ta so yi wa Habu, ta daure ta ce "Hmm ƙara ta ma ya kawo ko? To shikenan na daina"
"Ki yi haƙuri amma, yanayin ciwon nasa ne ba ya son hayaniya, shi yasa"
Nana ta ce "Babu damuwa in sha Allah, ina son ma na yi maka wasu tambayoyi, amma sai ka kuma dawowa"
Gyaran muryar sa su ka ji, Habu ya miƙe. Buzu ya juya yare ya yi masa magana, Habu ya jinjina kai.