Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 1
Cheaters club book 2 complete novel Chapter 1: Cheaters club book 2 complete novel Chapter 1. Book21️⃣▶️2️⃣ Bismillah rahmneeraheem. Wani irin mahaukaciyar…
3,372 words
Book21️⃣▶️2️⃣ Bismillah rahmneeraheem. Wani irin mahaukaciyar duhu duhu halisa take kallo agabanta idanunta sun rufe kirif zuciyarta da kanta na wani irin sarawa da azaban radadi mai tsanani ayayin data fito cikin sarari kusan a gigice da alaman bata cikin hayyacinta tabar musu kofar gate dinsu a bude dan ahalin datake ciki batacikin yanayin da zata iya juyowa bare kuma ta rufe musu shi.
Tafiya take kamar wanda Aljanu ke fixgarta kirjinta na bada wata zautcciyar sauti kamar na wanda zai faso waje .
Kafafuwanta da sukenan sulbabbu take dorawa bisa kasa batare da ta damu da inda take takawa ba cikin wani iriyar ragwababbiyr yanayi na gushewar hankli da rauni irin wanda bata taɓajin launinsa arayuwarta ba.
Amon Muryan meenal tareda kalmominta da yake dawo mata akai yanamai zubowa mata a zucya tanajin tsananin kunarsa tamkar wuta da ake zubowa mata a gangan jikinta.
hanyar kan titi tadosa ita kanta batasan inata zataje ba dan tamkar iska yanajanta hakanan take tafiya fuuu saidai ba acikin sauri ba.
ji take kmr Kwakwalwar ta gabaki daya ya toshe ya dena aiki lunshe ido take tana budewa dan bawani ganin gabanta takeyi ba.
gata nan ne kawai a tafe amma komi nata ya tsaya mata cak baya motsi taciki,mutaccun hawaye masu tsananin yawa da zafi sune suke sauko mata yuuuu bisa kan fuskrta hakama bata iya jan wani kwararren numfashi bare kuma tay wani tunani.
kafafunta da babu aron takalmi naɓari tare da harhadewa gabanta kawai to dosa batare da tasan inda zata tsaya ba face saida tayi nisa da anguwar takai wani waje.
Dada rikecewa tasoyi dataga idanun mutane na dawowa kanta....
Wasu har sun kura mata idanu alamar suna son su tabbatar ko itace da sassafen nan take gantali akan titi da hawaye taff a ido babu takalmi dake labarinta da zach jiyan ya zaga media babu laifi masu jiran kiris dansu caccakarta sun caccaketa masu ganin lefin zach din suma sunatayi acan.
Tsakanin jiya dayau da safen dukkan wani shafinta a social media babu matsaka tsinke..
Juyowa tay da sauri tun kan mutane su iskota tay wufff kamar wata wanda aka tsikereta tasaka hannu ma comercial rider dake tahowa. yana tsayawa batay wata wata ba ta haukai ta zauna batare da tagayamai inda zataje Ba suka dauki hanya cikin gaggawa suka fara tafiya can can gaba gaba...
Tun basuyi wani nisa ba Yaketa tambayarta inda zai kaita amma sai shiru dan Tsabar ta shiga wani mayuwacin hali na tunani batama jin shi Har sukayi neeesa sosai.
Adan dolensa ya rage gudun ride dinshi jin yadda nunfashinta yake sama sama kamr zata mutu masa..kuka nason ya kwace mata amma zuciyarta da kirjinta yay mata nauyi dayawa wanda koda zatayi kukan abayyane bazata iya kwato muryanta waje ba.
A dame rider yace Madam u neva talk ooo wher i wan drop you?. Madam u sure say u okay???.. Saidai ya memeta hakan kusan sau uku kafin nan Da kyar ta iya gaya masa sunan anguwar Banana island inda jasmine take zama.
Daga Wajen da suke babu wani nisa da anguwar amma gani tay kamar shekara guda sukayi suna tafiya dan acikin dakikanin lokacin nan dukkan wani nazarin rayuwarta data keyi ya gama birkita mata kwakwalwa, sosai ta galabaita ta zamo soo weak and shaky, baqin ciki da rauni marar misaltuwa shiya nakasa mata dukanin gabobin jikinta gabaki daya. Har ride dinta yazo zai wuce gidan bata sani ba.
Godiyan Allah da securityn dake gadin gidan jasmine din ya hangosu,ganin zasu wuce yay sauri ya tsayar dasu, kusan a ragwabe ta sauko kasa jikinta na rawa rawa ta amshi aron kudin mai gadin ta biya mai ride dukansu basuce ma juna komi ba sai kallonta kawai sukeyi da mamaki ayanayin fuskokinsu.
Shiga gidan tayi a birkice dan lokacin sosai kukan datake dannewa yake kkrin fasa mata kirjnta sai taji ta kara birkewa cikin baqin ciki da rauni...
Kusan a rikice ta burmo cikin falon jasmine muryanta dake sarkafe cikin jajjan numfashi da kuka ta fara kwalawa jasmine kira dashi da iya karfinta danji take kamar in bata fidda abunda ke ranta ba hala kwakwarlta bazai iya daukawa ba. Jas..jass...mine... Jas...m...jasmine.
Tun a bugu na biyu jasmine ta shako muryan halisar daga kasa,dirowa tay daga kan gadonta atake batare da ta sako takalmi ba tasauko kasar da mugun gudu da tunanin ko wani abu ne ya faru da halisar dan bakaramin damuwa ta shiga ciki akan abunda ya faru jiya ba.
Jiyan ma dakyar ta samu bacci, duk atunaninta itace ta jawo ma halisa komi dan da bata matsa mata sunje event din nan ba toh da hala bazata tozarta a wajan zach ba.
Babu takalmi akafarta ta sauko kasan...Muryanta na rawa rawa tace Halisa halisa are u alright???
Yanayin dataga halisan ya kangarar da ita ta tsaya cak batare da ta iya karasowa gareta ba, kallon jikin halisa dake abirkice yana rawa rawa takeyi dan bata taɓa ganinta a wann yanayin ba itama kusan tsoron ne ya soma mamaye mata zuciya..
muryanta a rarrabe kuma atsorace ahnkli take kallonta snn ta kangaro tace whats wrong
H..A..L..IS..A Are u okay????..
Cikin jan wata nannauyar ajiyar zuciya mai tafe da karsashi halisa ta daga kafafunta zata karaso wajen da jasmine din ta tsaya tana daga kafarta jiri mai tsananin ƙarfi ya fyetar da ita tay kasa a mugun ragwabe.
Tamkar kukan nata na jiran ta fado kasar ne dan kuwa tana jinta akasa kuka mai tsananin karfi ya kwace mata tabi ta dafe tile din da hannunta kanta na kallon kasa cikin rauni da dukkan idanuwanta alumshe suna zubda ruwan hawaye masu tsananin ciwo da zafi.
yadda kasan an kashe mata iyayenta gabaki daya haka taji zafin abunda meenal tay mata na shigarta dan bata cire tsammanin cewa har duniya ta nade bazata taɓa iya mancewa da wann rana ta yau ba.
Kafin kace wani abu har jasmine ta fado bisa jikinta ta rungomata. Dukansu basu iya cewa juna komi ba dan wani Kuka mai tafe da rurin tsananin baqin ciki halisan takeyi yadda zakasan zuciyarta na tafasa gabaki dayane gangan jikinta ya dau zafi kamar an jonata da wuta.
Idanun jasmine take ya soma kawo ruwan itama Acikin tsananin damuwa da rudani ta rungumeta tana tambayarta meke faruwa cikin muryanta dake rawa rawa sosai.
Da kyar Halisa ta kwaco hanklinta daya gushe a cikin dedeta nitsuwarta ta kalle jasmine cikin idanunta ayayinda hot tears ke zubowa mata uncrtrobly wanda yasaka jikin jasmine din mutuwa acikin karkarwa da yanayin bugun zuciya mai tsanani.
Acikin sauke nannauyr nunfashi Halisa ta riko ta Tace jasmine...meenal Meenal...mm...Meenal...meenal talba has She...she....lumshe ido tay agajiye kafin nan kuka ya kuma kufce mata ta rike zucyarta tay tsam idanunta dake lumshen sosai..
Kusan Arazane jasmine take kallonta,ahankli cikin lallami tace Talk to me halisa meyasa me meenal din what happen ure driving me crazy
Runtse idonta ta kumayi cikin tsananin zubda hawaye dan tunawa take da cewa tun bayan mutuwar iyayenta a duniya babu wani dan adam wanda ya jawota jikinshi snn ya sata a inuwa face meenal talba So how is this day even possible.?? Kenan Ashe wanda ya baka ruwa kasha wata rana zai iya baka guba kasha???
A rikice Ta shiga girgixa kanta tana cewa wayyo Allah na, Na shiga uku jasmine...na shiga uku.... na shiga uku da rayuwata i just cant belive this is happening to me..
A birkice Jasmine tace mutuwa meenal din tayi kome??
Batare da ta amsata acikin hayyacinta ba, frustration yasaka ta fara fiddaa maganan cikin ihu da zafin rai tana cewa "jasmine Am going crazy,.inason in tuna meye nakeyi marar kyau, menake ma mutane marar kyau, am i this very very bad..? ...Am i dis sooo sooo unfortunate. ..how comes duk wani wanda nayi tarayya dashi sai yaci amanata,..sai sun zalunceni, sai sun neme suyi shrinking dina su kuntatamin sun cusamin baqin ciki, What have i ever done in this life to desrve dis kind of pain?? Dan Allah menayi? menayi?...menayi....menayi jasmine? Ta karashe cikin ragwabbyar kuka.
Hawayen jasmine ne suka sauko kasa ta rikota jikinta tana kkrin rungumeta seidei a lkcin Wani irin Juyawa kan halisan yake tanajin rayuwar kwata kwata ya fice mata akanta sosai.
Kuka kawai takey muraran Muryanta harna sarkafewa cikin kukan mai tafe da karayar zuciya mai tsanani ahnkli take cewa jasmine ban taba cutar da kowa ba,.All i ever want is to survive.."i tried my best.,i fell and rise,i feel again and rise again..how many more trial is it bayan ban taɓa shiga hakkin kowa ba..
Jasmine ta kasa cewa komi hawayenta nata sauka tsabar tausayin da halisan tabata jikinta sosai yay sanyi yana rawa dakansa shikadai dan ko amakance kake zakasan cewa halisa is seriously hurting and in pain..koma me aka mata ynxu toh yaci mata ranta bana wasa ba, dan kamar Ba a cikin hayyacinta take maganan ba.
dada rikota jasmine tay dan turirin zafin dake huruwa ajikinta kadai ya isa ya baka tausayi, cewa take.. "My only crime was coming to do this world, and my daddy died, my mummy also died, and my uncle raped and hate me, The man i soo much love ditched me on our weding day..and ...and the only best friend i had is now stabbing me at my back.
Acikin tsananin rudewar tunani jasmine ta dada rungumota tanacewa Halisa ban fahimceki ba pls what are u talking about..talk to me halisa... wani irin Rungumar junansu sukay a ragwabe cikin tsumayi sunata kukan atare sai can snn halisan ta Riko hannun jasmine din tana kuka ahankli cikin nitsuwar da batasan ina ta samoshi ba tafara gaya mata Abubuwan da meenal ta faɗawa hajya nadiya akanta..
Yadda take maida maganan zaka san Har ga Allah sam bata wani damu dan meenal ta hana yiwar auren ta da zach ba, iya abunda yay mata ciwo ya kuma sakata acikin rauni shine data san asalin Dalilin dayasaka meenal din tayi mata haka..
Ji take aranta a yadda ta dauke meenal tamkar jininta koda zata rabata da soyayyar zach bai kamata ya zamo akan dalilin mugunta,kyashi da hassada ba. Dan babu wanda zai maka wayann abu ukun face babban MAQIYINKA.
Tayaya kenan zata iya sake Aminta da meenal musamn datajiyota tana cewa bazata taɓa kyaleta ta samu wani cigaba arayuwarta ba dan kawai itace ta taimekata a lkcin datake cikin tsanani??
Babu wani tantama ko shakku yau din tasha mamakin sabuwar fuskar meenal daya bayyana mata a sarari, tsananin mamaki... irin wanda dakyar kwakwala yake iya daukawa.
Aragwabe jasmine ta sake hannunta ta koma da baya baya cikin wani iriyar mamakin dayaso ya taɓa mata kwalkwarta acikin dakikanin lkci.
Bata iyacewa komi ba face memeta kalamn da halisar ta gaya mata cikin rawan murya duk dama tay harsashen hakan tin farko amma dataji abun ya faru sai kuma brain dinta ya rude bana wasa ba.
Kuka kawai Halisa takeyi tana cewa nifa bansan meye amfanin rayuwata ba..ina zanje inji sanyi, yaushe baqin ciki zai rabu dani jasmine? Musammn ma idan ina zagaye da mugayen maqiyana masu fuska biyu?...Duk abunda nayi na adalci makaina its alwys come back only to hurt me... Like i dont derseve peace of mind..like i dont derseve to be happy...nobody really care about me,so i dont get what am i doing in this world if its just gonna be this cruel to me...inhar meenal taymin haka a duniyan nan who did u think i will ever trust now???? Ta nuna min so da amana na fitar hankli And...i treated her like my own bloood har raina nakejin meenal kamar yar uwata. This is too much for me.. Kinsan zafin da nakeji araina yanzu kuwa???? Wai Duk inda na shiga neman soyayya ko wata alaka sai yaxo ya zame min ciwo me radadi ne? banyi zaton maqiyana zasu fito daga cikin shakikaina ba.
Ta riƙe zuciyatta jin yana raya mata abubuwa dayawa...
kafin kace wani abu numfashinta ya fara kwacewa hartakai kasa ahaka tari me tsananin karfi ya turnuketa..
tsorata jasmine tay ta miƙe tsaye jikinta na ɓari kamar mazari dan Gani take kamar Halisa zata amayo jini dan ba acikin hayyacinta take tarin ba.
iska gabki daya baiya kai mata har ramin hancinta, domin kuwa kwakrlta tunawa yake da dukkan wani abu daya wakana a rayuwarta marar kyau tun tun tana karama past miseries and traumas zallan marasa kyau da irin tarin mutanen da ta asalin amincewa dasu snn sukazo suka tozartata suka yaudareta har izuwa yanzu.
She just tot she is suppose to be dead. Batacanci tay rayuwa ba sabida duniyan nan bai dace da ita ba, bata shigo cikinsa a sa'a ba.
Ace tun tana yarkarama babu wani rayuwa me dadi da zata iya tunawa mai yawa saina yawan baqin ciki?
Death is just the answer, maybe then she will rest from traumas and all these miseries dan Batajin nan gaba zata iyayin adalcin barin kanta cikin wann irin gurbataccen rayuwar..
Tasani nata ya kare tunda har kawunta dayake jininta na asali ya mata ciki snn ya tozarta da zach daya nuna mata amana da tsaftacciyar soyayyar da ko a korean film albarka ya zo ya walakantata da meenal data zame mata tamkar gangan jiki ta koma bayan idonta tana munafurtanta..
Mutane na kusa da ita sosai sun taru dukansu sun cutar da ita toh duk duniya babu wanda bazai iya cutar da ita ba.
Koda ta rayu Tayayama zata iya sake amincewa da wani Dan Adam ynxu??Wani abin baqin cikin ma baya taso mata sai ta tuno da irin fuska biyu da meenal din take sakawa agabanta. Cos This even hurts her more than words can say...
duk wani tare mata fada da mata kuka da nuna damuwa tare da daga jijiyar wuya dominta dama duk na karyane kallon ta kawai takeyi kmr marar hankli?
She felt too stupid right now datasha yin kuka akafadar makashiyarta datake zuwa mata da fuska biyu.
Kanta ta cusa atsakanin kafafuwanta tanajin kamar ta hadiye ranta ta mutu cos Her brain is compltely detached from anything positive tabi ta cire ranta akan komi. Dan har jasmine din dake gabantan ma gani take kamar itama wata rana zata yaudareta, ta tuno da uztaz..sai kuma tsoron cin amana ya fara shigarta tasoma jin kanta kamar zomo a gaban zakuna a tsakar jeji.
Wani iriyar tarine ya turnuketa harta fadi kasa tanayinshi cikin gigicewar tunani...
a mugun rikice jasmine ta haura step dan taje tadauko wayarta ta kira ambulance for quick emergency intervention
Haurawarta saman ke da wuya halisa ta mike da kyar tafara bubbude drawers din jasmine din inda tasan tana aje guns danta kashe kanta bata samu ba, tabi ta birkita ko ina bata gani ba sai key din mota data dauka ta dunkulesa a hannunta.
Babu inda ya fado mata akanta face tajeta third mainland bridge.
Batare da bata wani lkci ba tabar mata palonta awargaje Snn ta fita, tabi ta kulle jasmine din da lock ta waje..
Kusan ince idanunta a rufe ta danna key din motar Data dauka ya budu da kansa sport car ce mai kyau, daga ita sai yar rigar baccin dake jikinta babu takalmi ta fada ciki ta danna horn ma mai gadi ya bude mata gate din acikin gaggawa dan amatse ta danna horn din sosai
Wani irin Murza motar tay tunma Kafin me gadin ya kammala wangalewa Harta fixge motar da mugun gudun ta bar arean wajen daga nan hanyar third mainland bridge din ta dauka inda babban tekun lagos yake wucewa..
Haka jasmine ta sauko kasa a rikice da waya a hannunta kusan a rikice take dannawa sai bata ganta anan ba, katse kirar tay tahau dube dube tana kwala mata kira...
Gabaki daya ta bata lokcinta wajen dubata harsu cikin toilet da bathrum duk bata ganta ba, kirjinta na buguwa tayo kofa a guje tana tabawa nanma taji an kulleta aciki dam dam.
Girgizawa tay cikin tsananin damuwa tace "Damn it" kira ta dinga dannawa me gadinta amma dake gidan babba ne sai baijita ba.
Saida ta hakura ta kirasa a waya snn yake cemata ai yaga halisan ta fita a mota agurguje bata tsaya karasa jinshi ba tacemai yazo ya bude ta.
Yana budeta A rikece ta yo waje itama bawani suturar kirki ajiknta dan Duk ta Tsorota bata san ina halisa zataje awann yanayin ba bata kuma san mezatay ba
Me gadi yana budewa Itama motar ta dauka ta shiga gari neman halisa sede hanya daban daban sukabi atunanin jasmine hala ko wajen meenal din halisa zataje.
Ita kanta driving take tana hawaye musammn inta tuna irin dankon so da shakuwa da halisa suka nuna ma junansu ita da meenal na tsawon lokci tamkar yan uwan jini.
Ita sam batasan wata irin bahaguwar mace bace meenal amma koda ba a fada ba tasan this particular issure yay ma halisa ciwo harma fiye da yadda taji alkcin da zach ya rabu da ita.
Halisa consider meenal as her own blood sister dat she neva had,komi ta samu na duniya meenal ce farko,arayuwa da wuyane ka gaya mata abu akan meenal ta amince maka muddin abun mai munine.
She can do anything for meenal's sake dan matsayin data aje meenal din aranta is truly undecribable. .gani take kamar wann karon kam halisa bazata iya daukar abun aranta cikin sauki ba.
Itakanta Jasmine datayi harsashen hakan farko daya faru kuma sai taji abun ya mugun girgizata...she fear for halisa.. gudun motarta ta kara kodama za ta cimmata cos she knew halisa will need sumone to hold on to her titely duba da jiya jiyan nan zach ya gama mata nashi ga kuma na meenal yau da safe.
Sosai Tsoro yacikawa jasmine zuciya tana tukin amma gabaki daya hanklinta baya jikinta sai juye juye take tana duban hanya koda zataga kawarta amma ina batagan ko me kama da ita ba..
Dagata dayan bangaren kuwa zaune meenal da mahaifyarta hajya nadia suke acikin fankacecen bedroom dinta dayaji kayan duniya Ac na busowa takotaina hanklinsu kwance da tunanin Halisa tana daki tana bacci.
Suna zaunawa Hajy nadia ta sauke murya kasa kasa snn ta kalle meenal din tace babyna ince mijinki yayi nisa bazai dawo ynzu bq dan bana son nakawo miki zancensa yazo yajiyo mu yace nice nake lalata muku aure...
Meenal tay murmushi tace kai mumy kin cika tsoro toh inma yaji sai me???..me ya isa yayi, cikin kyabe baki tace hmm ni de wallah bana jin tsoron khaleel Nikaina ina da tarin abubuwan da zan gaya maki akansa dan kwana biyun nan ya canza min gabaki daya kuma ina tsammanin uwarsa ce take cusa masa wani ra'ayi akaina
Cikin sauke ajiyar zuciya hjy nadiya tace ke da Allah bar wann maganan agefe, wake maganan mallakar namiji bayan ana zancena nemen kudi, kinga Amina.. da Akwai wani babban dalilin dayasa na ce miki kijirani kawai nazo lagos din nan mu hadu dan kona gaya miki awaya bazaki fahimceni dakyau ba.
Acikin matsuwa meenal ta gyara zamanta tana kallon hjy nadiya snn tace toh menene ƙhaleel din kuma yay a Abuja mummy..?altho naga ya dawo da wani tsinannen girman kai.. ina magana yana magana he has no regard for me now.
Hajya tace hmmm Amina kenan ai dole yaron nan ya fara miki girman kai...ke Wasu abubuwa ne suketa faruwa acan Abuja kuma bana son mutattauna shi a inda khaleel zai jiyomu. Are we safe to talk here ko zamuje wani wajene??
Meenal batace mata komi ba ta dauki wayarta tayi dialling after some time aka dauki wayar.
Muryanta a kisininance tace "Hey Khaleel are u almost done with ur gym hours..? Muryansa kasa kasa kmr baison amsawa Yace nop meya faru and Why are u asking me. Sama da kasa tay rolling idanunta adan fixge Tace ohhhh, nothing. Amma inka gama zaka dawo gida yanzu ne? Ammm..you see..mum and i..cikin katseta alamn baison ma yaji zancen yace is okay dont stress.. badawowa zanyi ba, daga nan zanje wajen abokina engr Hafeez ne a site din aikinsu..
Tace ohh okay..in zaka dawo gidan just alert me.
Baice mata komi ba ya katse wayarsa yabi yasaka wayar a silent. Haushi hakan ya bata taja tsaki, shikuwa Ya sauka akan trade mill machine dayayi gudu akai ya jawo towel din dake cikin bag dinsa ya goge zufan jikin shi ya wuce washroom ya cire gym singlet dinsa ya watsa ruwa akansa ahankli yana sauke ajiyan zuciya.