Kenza eBookz

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 2

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 2

Cheaters club book 2 complete novel Chapter 2: Cheaters club book 2 complete novel Chapter 2. Daukar goran ruwansa yay yasha sosai yaji sanyi aransa.

3,367 words

Daukar goran ruwansa yay yasha sosai yaji sanyi aransa.

Bayan nan yabi ya ciro wata sabuwan farar rigar ta kamfanin calvin klein dede da kalar sneakers din dake kafararsa marar nauyi yasaka ajikinshi..ya dauki jakarsa ya rataya ya fice yay gaban motarsa atake.

Danna key yy motar ta budu dakanta yabi ya aje wayarsa da jakarsa abaya batare da ya lura ba.

Driving ya somayi izuwa third mainland bridge nan inda abokinsa engr hafeez suke aikin gyaran babban gadar legas dake connecting kusan kowani kusurwa na garin da gwamnatin tarayya ta basu kwangila. KAR KIYI SHARING, IS NOT FREE, DAN ALLAH DONT READ IT IF U DINT PAY FOR IT. THANK YOU #SURAYYAHMS. *TO SUBCRIBE* *500 VIA 0152983148* *MOHD SULE SURAYYA* *GTB* *CHAT 08060712446*

4️⃣▶️5️⃣ #SURAYYAHMS

#PAID NOVEL

Khaleel bai daddara ba ya cigaba da kkri wajen ceto ranta,..karshe juyata yay da baya kamar yar paper ya shimfidata akasa da baya, in oder to stimulate her brain he needed to massage her veins thru her spinal cord. Wann din yana daya daga cikin lucky trick dinshi dayake yi musmn in marar lapyrsa yaki responding to any form of treatment.

Zame figgagiyar rigar tata yay ahankli ta baya snn ya saka dogayen yatsun hannunsa a dede setin layi kashin bayanta idanunshi a lumshe ya soma daddana mata wajen yana massaging dinsa gently ahankli ahankli daga sama izuwa kasa dede bayan keyarta inda jijiyar kwakwrla mai raunatuwa da stress din yake just in between d neck line, dan karamar space haka daya raba tsakanin kan mutum da wuyarsa, anan ne ya aje hannunsa yana dannawa ahnkli yana zamerwa har ta gadon bayanta har izuwa dede kan kugunta tare da bada muhimnci a setin cikinta ta baya.

Kusan sau biyar yakai hannunsa wajen yana dawowa kasa yana daddanawa kafin nan Halisa tay wani irin kaƙari snn ta fuzgo wani irin shakurarriyar aman ruwa daga can cikin cikinta tanamai fetsarwa waje cikin tari me balain karfi da gigitarwa.

Ba acikin hayyacinta ba cikin bala'in tsorata ta rike rigarsa dam dam kamar zata ballashi jikinta na kyarma sabida tsananin gigita da brain dinta ya shiga ciki.

Kusan Idanuwan rescure team din gabaki dayana xube akansu, hanklin khaleel ya mugun tashi yanata kkri wajen temaka mata tana amayo ruwar duk ta galabaice bata cikin hayyacinta ta kame masa jikinshi dam dam. har aka fidda su sama kan titi halisa tana amai bata dena ba,.. sai kafin nan can tay doguwar suma ajikinshi bata ko motsi amma bana mutuwa ba, duk da haka saida ya tattaba pulse dinta yajisu suna dan responding kafin nan hanklinsa yadan fara dawowa jikinshi yabi ya sauke sihirtaccen ajiyan zuciya yanamai furta hamdala cikin lunshe ido da budewa.

ganin har polisawa sun iso wajen yasa yabi ya cire farar rigarsa daya gama jikewa da ruwa da sauri ya saka mata ajiki yabar kansa da singlet aka basu life jackets da blanket ya rufeta dashi baki daya.

Da mugun gudu Hafeez ya iso wajensa yaname jajantawa duk ya rikice ya rasa mema zai soma ma khaleel tambaya akai dan abun ya matukar bashi al'ajabi da mamaki da khaleel ya jefa kansa a hatsari mai tsanani domin ceto rayuwar wata wanda a tunaninsa basu ma santa ba tukuna.

Duk yawan question mark din dake fuskarsa Khaleel dai baice masa komi ba dan kusan atare suka dorata akan Emergency wheel converyor aka jona mata engin taya numfashi sann suka shige motar emergency khaleel yana zaune agefenta yana zukar oxygen din shima dakadan kadan dan ya samu isashen karfin da xai kula da ita.

Duk dama motar emergency na babban asibiti wato LUTH ne yazo amma asibitin dayake aiki din kawai yace akaisu atake.

tare da yi musu bayani cewa halisar patients dinsa ne, kuma bayason tayi going tru any media publicity anan a babban asibiti... yadai musu bayanin situation dinta sama sama yadda zasu fahinceshi sosai subashi ita.

Dakema yanzu kowa yasan yanayin media da son yaɗa labarai barkate batare da sun damu da condition din mutum ba hakan yasaka ogogin suka Amince masa dan sunsan muddin aka akaita can toh da wuyane baza'a karasata da wani baqin cikin ba..

Lokacin ana neman karfe 10:30 na safe aka nufi hanyar NISA premier hospital dasu hafeez kuma na biye dasu abaya.

******* Ata fannin su meenal kuwa tunda suka shari zama a daki nan hajiya nadiya ta fara bude mata shafuka shafuka na Abubuwan data gano ma idanuwanta A abuja.

Tace meenalyn mumy ki yarda dani i was part of that project seminar da mijinki yay attending a Abuja kuma na nemo mana wasu relevant information akansa.

Sounding unintrested meenal ta aje kanta akan pilow tana gatsine fuskarta cikin muryan kasala tanamai cewa

"..mum wai dama akan project din nan nasa ne kika wani takuramin, ni wallh na dauka wata babban harka na billions ya bude acan..ahnkli taja tsuka, mtchew" mum amma ai kinsan babu wani kudi a harkan asibiti musmmn ma irin wanda khaleel yakeyi, he is just a normal doctor and i dont even knw what he specializes on, ..uhmmm gashi nan dai..

tana maganan ne tana jan jan nunfashi a kasale, hajy nadia sai kallonta take sakaka.

"mumy nadai san akasar waje yay duka karatunsa na likitanci...ko ma wani irin project zaiyi bafa zai fini arziki ba. So just chill lets talk about oda things.

Murmushin takaici hjya nadiya tay tace ure wrong my Dear...totally wrong, dan anan kasar ne kawai kike ganin kamar harkan likitanci is nothing..go to developed countries or even kenya zaki gane cewa medicine in a multi billion naira business all over the world.

Ashashance Tace Uhmmm mumy toh menene??? whats popping nassan khaleel baida tulin kudin sakawa acikin multi billion naira deal wai mesa kika damu da wann zancen ne...its really sound boring to me

Cikin katseta hajya nadia tace zaki saurareni ne ko sai na cimaki ba gashi? Akace miki zan zo nan da maganan banza ne?

Turo baki meenal tay a shagwabe snn tace sorry mummy toh ai inajinki...

Hajya Taja tsaki cikin mita tace sam sam bana son wann attitude din naki na ko inkula din nan...ure too stubborn to see what is coming to u...ko bakisan dan hakin dakika raina wata rana shine zai tsole miki ido ba????...

Ahankli meenal ta mike zaune batare da tace mata komi ba..

acikin yanayin jadaddawa hjya nadiya tace Amina ki nitsu kiji ingaya maki, Conference dinnan fa nawasu hamshakn kusosine na duniya da suka shiryashi acan saudi. a group of 7 billionaire investors frm arab worlds sune suke son subude wata hamshakiyar project akan lamarin human phsycology and mental therapy dan a samu mafita wa ciwon tabun kwakwalwa dake yawan damun sojojin kasashensu da kuma tsoffi masu rikicewa kinsan cewa alzhemeir ya zamo musu ruwan dare, ga kananan yara da suke tashi da mental traumas, da mata masu ciki masu yawan mutuwa da pre and post partum depression and anxiety.

Meenaal kam ba fahimtar komi take ba dake ba field dinta bane ita sam ma likitanci baya burgeta arayuwa tafiso ta tsoma biyar ta samu goma a harkan business dinta.

Nan hjy ta bude zip din katoton fashion bag dinta na michael kors ta ciro wasu takardu hilimi guda ta bazasu agaban meenal din duk da logon tambarin masarautar saudi arabia ajiki snn tace Ceo na King faisal speacialist hospital and research instutite sune suka shirya taron tareda riyadh millitary hospitals dake saudi arabiya.

Snn sun gayyace saka hannun babban asibitin john hopkins na America da toronto medical service. Daga nan saudi arabiyan kuma sun hadakaine da suleiman Al habib medical service group tare da mouwasat medical service, and mind u, professor Ahmed harshi frm medical city of king saud is the father of the entire project...

Anan nigeria muna da lagoon hospital tanan lagos amma anayin hidiman ne tare Da national hospital abuja.

kuma a boye akeyinshi sabida halin da kasar nan ke ciki basu san kowa da kowa yaji me suke kullawa dankar ashigo musu da zancen siyasa aciki..

The good news is Dr asim khan mentor na mijinki shine chairman na wann babban harka

My baby ki kalle takardun nan da kyau, ki mance da Abubuwanda suka saka agaba, just think about the money Amina.. its a huuuuuge investment. Ta karashe maganan tana murmushi ayayin da ko daga kai sama meenal batay ba bare tay murmushin itama.

Wani gullutun abu taji ya tsaya mata akan kirji, nan ta debi takardan ta bude tana karantawa da idanuwanta dake cike da tsananin baqin ciki da kishin ganin tsabar narkakkun kudade da aka zubasu anan gashi ba field dinta ba bare ta mora.

Tunda ta gane cewa is legit Batama kai karshe ba ta Dangwala takardan akan gado a shashance dan Arayuwa in Abu is not in her favour to bala'in haushi yake bata.

Hajy nadiya batama san metaciki ba cikin karasa mata bayanin ta dada hatsalata data kuma cewa Dr asim khan ya riga daya jona mijinta aciki, And he is among the lucky five doctors around the world da zasu fafata a wann hidima.

Da ɓarin jiki Tace Inhar mijinki yaci nasara project dinsa yay mugun kyau toh babu shakka zasu daukeshi aiki awajensu,Qaddara Wann Harka zai iya sauya ma mijinki duniyarsa gabaki daya bama rayuwarsa ba dan Idan kika cire sauran manyan kusosin,toh iyakan sulemain alhabib ma kawai is a capitalist medical investor group with worth 20.3 billion us dollar investment in medicine.....

Wani irin nannauyar numfashi meenal taja mai nunnuke da baqar hassada dake kwalala aranta. Tay rau rau da idanu Tanajin kamar ta shakure wuyar mahaifyr tata tace mata tay mata shiru.

Cikin lumshe ido da budewa tace mumy bangane ba fa, wai shin zancen khaleel ne kawai ya kawoki lagos ba zancena ba? I mean how is dis even a news to me...to ni kuma ina ruwana da cigabarsa mtsw..

Shiru hajy nadiya tay dan atake ta gane cewa meenal ta hatsalene dan taji baqincikin wann zancen, hmmm ita knta tarasa wani irin nau'in hassada da baqin hali Allah ya dora a zucyar yarta meenal dabaiji baiya gani.

meenal ta ɓata shiru aranta babu abunda take kullawa sai lissafe lissafen mugunta da fatar kar Allah ya bawa khaleel sa'a akan project din nan kwata kwata.

Tuna cewa bazata taɓa amincewa khaleel yayi gaba ya haura can sama daita a arzirki a duniyan ba yasaka ta fashe da dariya mai karfi irin abun baije mata inn nan ba.

Mummy Wann ai mafarkine da bazai taɓa zamowa gaskiya ba cos i knw khaleel bazai taɓa cin nasara akan wann hidimar ba, he is just a normal doc...mutane nawa ne suka fishi ilimi a duniyan nan? Nikuma Sai nazauna rayuwarsa ya sauya nawa na nan waje guda??? hahaha Noo... khaleel bazai taba yin arzikin dayafi nawa ba dan banga ta inda hakan zaiyu masa ba,..snn kekanki kinsan in hakan ya faru it must be by mistake and i will corect that mistake for him by bringing him down, Kema ai bazaki so ace khaleel yafini arziki ba dan walaknta ni kawai zaiyi yafara neme neman matan banza na zame masa kamr shara agidan nan....abar zancen sa kawai...Lets do sumting and forget abt him cos he will neva win that contract ina da tabbaci akan hakan.

Cikin katseta da wani irin kallo hjya nadiya tace "ohhh harkina da tabbaci..mmmm na manta dawa nake magana ashe..the great superior Amina talba datakejin komi a hannunta yake ba a hannun Allah ba. Ke Toh bari in gaya maki wann tsinannen feeling na superiority complex din naki shine zaikaiki ya baroki,.. baida ilimin cin project din suka zabeshi??? Kaji maganan banza rikemin tsuliya nayi kashi..

Cikin turo baki Meenal ta budi baki zatai magana ahatsale hajya nadiya ta mike tsaye cikin katseta Da cewa Amina bana son naji wata magana daga bakinki...kisani Tun da hantsi ake kama fara ba sai dare yay ba. Ni anan na dauka kedin me wayoce shiyasa har na bata lkcina ina miki bayanin harkan arziki ashe kwakwalr kifi ne dake....To Bari kiji Amina, niba zuwa lagos nayi domin nayi shawara dake ba. Nazo ne inkaiki gidan Alfa Oluwalekan abamu magani me karfi da zaki rike mijinki dashi a tafin hannunki just incase ya samu abun duniya kema ki yaqe rabonki anan..

I want to see u build talba's empire all over arab countries dan nasan bazama zaiyi anan cikin nakasashen kasartaku ba musmmn ma idan harkan arziki tazo masa idonsa ya budu da kudi. Kisaka aranki cewa Harkan nan tana tsaya masa zaki lallaba kisamu ki haihu masa ku haifo ɗa namiji, kinga Khaleel na mutuwa arzikinsa kafff sai ya dawo hannunki.

Da wani irin giggiwa da jiji dakai me tsanani meenal ta mike tsaye Tana kumbure kumbure.

Mumy haihuwa fa kike cemin nayi da khaleel, ewww akan me zan haihu dashi? Akan kudin da ubana yabarmin tulinsa sai na jefa kaina a irin wann azabar?...and beside akan abunda bai faru bane zakice nabiki muje wajen wani matsafi a mallakemin shi toh nide wallah bazanje ba ..khaleel din shi waye da zanje wajen boka akansa god forbid wallah nafi karfin naje wajen malami akan namiji dana fishi dukiya..he can go to hell. Dan nasan ko wuta tusarsa zai hura bazai yi arzikin da zai doke nawa ba.

Shut up ur mouth amina Cikin tsawa hjya nadiya ta dakatar da ita.

Marar kunya kawai...ina magana kina magana?

Idonta a bushe sigar rashin tarbiya Tace mummy sorry mana amma ai kece kike fadin abunda bazai taba yuwa ba. Haba dan Allah I will neva ever stoop dis low musmn wai dan na same kan khaleel wallh nafi karfinsa...qaddara ma ace nayi miki biyayya munje wajen boka amma aikinsan khaleel will loose this project he wont even win, gayen Baida sa'a, baida farin jini Bazaiyi arziki irina bafa.

Cikin tsananin bacin rai hajya nadiya tace okay fine ooo,..foturne teller naji..Komawa tay ta zauna ta dafe kanta "Oh my god kaina ma ciwo yafaramin, Allah na gani ni Bani da wani abunda zance miki yanzu, amma kisani karda ki sake nan gaba kizo kinamin kuka akan Abunda nake gaya miki yanzu.

Da sauri ta tsuguna tare da riko hannun mahaifyrtata sigar lallami tace haba mummyna nifa na ke zama da khaleel ninasan halinsa inda ace zai yi wani abun arziki da nice zan gaya maki..trust me he will fail. Cos he is meant to..ni fa bansan mesa kika saka rai akansa ba he is looser Baki gani ko magana mahaifinsa baya masa har yanzu? Allah yasan abunda yasaka ya dorani a samansa, he is evil...all what i need now is more money more fame ahakama sai kiga na mallakesa gabaki daya.

Agajiye da zancen hajya nadiya tace You're too sure of urself Amina. Ke matsalarki kenan wallah gani kike kamar u can control evrything kamar u know it all.. amma bakomi ba..ai namiki alkwari cewa bazan takura maki ba. Dan haka lets talk about oda things. Yanzu ya maganan zaman aurenku dakike complain da kuma maganan sectaryn? U said she is useless ko, to Yaushe kikeso akawo sabuwa.

Bata amsaba ta zubawa mummyntan ido Ganin kamar bata wani ji dadin rashin amsar tayinta na zuwa wajen Alfa datayi ba.. in oder to make her happy tace mummy am fine now..khaleel din ay dawo...snn kibar mgn sectaryn kawai nafasa korarta..i can manage her. Kawai de asamamin wata hot marketer wacce zata iya aikata komi dan insamu biyan bukatata.

Tare da sauke ajiyan zuciya akarona sau ba adadi Hajya nadia tace toh bakomi hakan ma yay..kafin na koma Abuna za'a samo miki new marketer.

Ahnkli Meenal tace thanks mumy..zancen business dinfa..u knw im dyieng to knw wani harka ne ya rikeki a dubai.

Ajiyar zuciya Hajy nadia ta sauke tace kedai bari Wani babban kamfanine da suke harka da crypto amma sun maida tsarin su kamar caca in ka ci sa'a zaki samu ninkin baninkin abunda kika zuba idan kuma bakici sa'a ba saikiga ya rufta dake.

Witout thinking for abit meenal tace okay i am in Kihadamu kawai zan yi sabida nasan zanci...But like how much are we talking about?

Hajya nadiya tace hmm We r talking about euros..thousand of millions of it..ko 4 million euros kika samu ai duk kasar nan sai anjiki.

Cikin rawar jiki meenal ta zauna daf da ita tanamai cewa woww Wow mummy shine tintini baki gayamin wann zancen ba Kudin da baba yabarmin a dayan bank acct dinsa na America is almost 2million dollars sai kawai na zubasu a harkan duka. Kuma kinga dama wacan jakar fadilar ta tara min aiki wallah tana tafiya dukan investors dinmu suka farajan baya sabida aiki baya sauri..nasan ina samun kudin nan dik zasu dawo jikina

Cikin katseta hjy nadiya Tace 2mill dollar yay yawa Amina, but be careful kila wa kala ne Idan asara tazo zakifi kowa jin zafin rashin kudin nan dan gumin mahaifinkine.

Tace karki damu mmy kawai ki hadani dasu.

Hjya nadiya tace naji amma saikin Amince munje wajen alfa ko da sau dayane ko irin wankan farinjini dana kore idon maqiyan nan amiki uhmm meenalyn mummy.

Rau rau da ido meenal tay dan tasan hjyrta akwai kafiya suna zuwa wajen zata mata wayo akan batun khaleel gashi ita she is not ready ta saukar masa dakanta musm yadda feminism ya shige jikinta sosai din nan..

Cikin karntarta tace mumy pls noo..inde akan khaleel kike so muje nayi miki alkwari zan gyara halina, zan yi irin rayuwar dakike so na aure. Cmon mumy Im a woman, zan iya jawo hanklinsa gareni basai na kaisa wajen boka ba. kede Kawai kisamar min harkan nan dat way i wont even feel like zai zo kusa dani a arziki kinga sai bazamu dinga fada bama..

Cikin sauke ajiyan zuciya Hajy nadiya tace toh shikenan..amma aidacan cewa kike yana miki kaza yanamiki kaza..komi ma lefinsa ne ..ynxu harkin manta ko.

Tace hmm mummy just calm down nifa yanxu harkan samun kudin yafi damuna ba khaleel ba.

Hjy na shirin budar baki saiga sautin sallama daga kofar sashen.

Shiru dukansu sukayi har Saida akayi sallaman kamr sau uku kafin nan meenal taja wata arniyar Tsaki ta fito waje.

Sama da kasa ta karewa me gadin kallo kai kuma uwar me ya kawoka.

Kansa akasa yace Dama kinyi bakuwace a waje nace bari nazo na sanar dake..

Adan mamakance tace bakuwa kuma???

Meye sunanta???

Bai samu ya amsata ba saiga hjy nadiya ta fito dauke da iphone a hannunta yanata ringing tace Amina ur friend shemau is calling.

Share me gadin meenal tay ta amshi wayar cikin gaggawa tace helo yan mata..how far.. baki wuce Abujan bane?

Daga ta dayan bangaren muryan shemau wani iri tace meenal where are u dan Allah?

Meenal Tace ina gida mana..whats up

Da tashin hankli a muryan shemau tace meenal Kina gidan shine kika bar Halisa ta fita taje zata kashe kanta??

Tare da bugawar zuciya meenal tace mene?...Ke shema tsaya..wata halisar..halisa...is in the room sleeping, kuma dazun nan na dubata..

Rai abace shemau tacee Ohh my god meenal cam u just check online and see for urself Labari da dumi dumin sa ya baza ko ina...Can you just...

Meenal Bata karasa jin maganan ba ta katse wayar jikinta na wani irin ɓari ta kunna data straight taje poplr Twitter blog tana hawa taga post akan halisa mansa breaking news halisa mansa attempted suicide at mainland bridge ko minti biyar ba'ayi da sakawa ba.

Hannunta na bari dan Bata san sanda ta Jefar da wayar ba, da sauri ta nufi dakin da halisan take ciki tun daga ganin yadda kofar yake a wangale kirjinta ya soma dukan uku uku...ta fito a rikice kamar zaty kuka mummy na shiga uku dagaske ne...Halisa is not here, taje ta kashe kantan me dagaske..

Da sauri hjya nadiya ta karaso tana lekawa ganin dakin wayam yasa itama tace innalillahi wa inna ilaihi rajiun..

Kusan a rikice suka sauko ta dau wayarta hannunta na rawa raw tay dialling lambar shema dana hadiza baije ba saita kira vicky itace ta gaya mata cewa har yanzu ba asan inda aka kai halisan ba amma ance musu motar LUTH wato lagos state university teaching hospital ne ya dauketa

Duk da son gayun meenal yau bata tsayayi ba,abaya kawai ta jawo ta saka ajikinta duk ta rikice..

Mummy kije gida zamuje luth dani da vicky mu duba halisa acan.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull