Kenza eBookz

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 18

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 18

Cheaters club book 2 complete novel Chapter 18: Cheaters club book 2 complete novel Chapter 18. Kalolin kayan take kallo badai daukar idanu ba, dake…

3,361 words

Kalolin kayan take kallo badai daukar idanu ba, dake kaloline masu haske kamar lush pink, peach, sky blue, alots of whites, lavender purple, da uwa uba pepper red, tan and winery gold.

Tarkata kayan tayi ta shiryasu da kyau acikin closet for easy access. Daga nan tay gaban madubi ta tsaya cak tanamai kurewa kanta da kallo sosai kamar wacce take son taga wani abu acikin, nannauyar ajiyar zuciya take saukewa a karo na babu adadi dan Har yanzu kallon kanta takeyi kamar ba ita ba dan abubuwa dayawa sun sauya mata a kamaninta da kuma cikin zucyarta sosai. She is in a stage where she cant recognised herseld anymore, irin ka dingajin kamar brain din ka da jikinki banaka bane din nan.

Daga tsayen ta Lumshe idanunta tana tunanin yadda zata tursasa kanta yin abubuwan da jasmine ta kayyada mata domin samun sauki dan bata da wani babban buri aynzu da ya wuceta bar musu gidansun ta koma ga hidimar rayuwarta data saba koyaushe.

Bata bude lumsashun idanunta nata ba har saida tay convincing kanta cewa lallai zata iya kwaco kanta daga hannun khaleel din acikin sauki, Juyawarta ke da wuya taji wayarta na kara dacan kamar bazata dauka ba tahakura ta taho bakin gadon dede yana daf da yankewa ta dauka kafin nan ta dora bisa kunnen ta tana mai sauke boyayyar ajiyar zuciya, a hnkali cikin sanyin murya tace Helo sir good morning.

Daga ta dayan bangaren Dr Aseem yay murmushi yace Hello dear. Hope ban tasheki a bacci ba?

Babu yabo babu fallasa Tace Na tashi.. daga nan suka gaisa, ta lura ya damu da lamarin ta sosai, na musmn takejin ajikinta kamr yafi kowa fahimtar metakeji aranta game da rayuwarta, snn ya fahimce cewa tana cikin halin kadaici duk dama bakowa ne ya ke mata kallon cewa tana missing din familyn ta ba.

No matter how rich or succesful u are dole ne ka bukaci makusantar ka na jini ko iyayenka atare dakai dan dole ne akwai gurbin kewar su da wasu mutanen bazasu taba cike maka su ba.

Cikin tausashiyar muryansa me saurin kara mata nitsuwa ya tambayeta ya take ji yanxu a jikinta...

Bata boyemai komi ba ta gayamai cewa she is feeling empty tanajin kamar ba ita din bace wata ce daban. Sann ta kara jadadda masa cewa bata son zamanta anan gidan duk dama taki sam ta gaya masa dalilinta game da hakan.

Murmushi yay mai sanyi Cike da lallami Yace karki damu zanzo na dubaki dakaina sai mu tattauna sosai amma sai bayan kwanakin dana deba makin ya wuce atare da Dr khaleel.

Shiru tay Batace masa komi ba ya sauke ajiyan zuciya ya fara advicing inta yanamai cewa Halisa ki sake ranki, kiyi min alkawarin zakiyi kkri wajen Taimakawa kanki, rmebr, untill u make the unconsious consious, it will direct ur life and u will call it fate. Get up and do sumting karki na zama cikin kadaici da tunani..

Ya fada mata ire iren wayann kalmomin sunfi sau biyar acikin yanayi me tattare da hikima da kuma ilimi.

Hakan dayace din sai ya bata daman tambayarsa ko zata iya fita cikin gari

Shikam bai mata musu ba dake kwararren likitar kwakwalwa ne yasan idan ya hanata motsa jikinta zai kara mata damuwa sosai, take sai yace mata zaiyi ma khaleel din bayani game da bukatun nata snn zai shawarce shi tunda ayanzu shine yake da iko da case dinta ba shiba dan haka dolene sai khaleel din ya bada amincewarsa kafin nan sai ta fita, acike da lallami yake mata magana, shikam bazai iya hanata zuwa inda take so ba but he want to make sure ta nemi shawarar khaleel akan hakan dan kar su shiga hurumin aikinsa.

Halisa ta tsane ace wai sai an nemi izinin khaleel kafin nan tay wani abu daya dangance rayuwarta.

Sede yanayin yadda dr Aseem yake tausasa lafazinsa yasaka batay masa musu sai kawai ta Amince cewa duk sanda take son ficewa wani waje zata nemi izinin nasa babu damuwa

Bayan nan sosai ya kara mata karfin gwiwa akan data warware jikinta ta dena zama a daki ita daya musammn ma intanason taga ta warke da wuri. Sosai yake nuna mata cewa yana tare da ita dari bisa dari dan har cikin ransa yakejin tausayinta sosai

Tun da ya soma mata ire iren wann maganganun masu cike da ilimi da karfin gwiwa sai taji kamar an yashe mata dar dar din datakeji ne na aikata abunda yake ranta cikin sauki da kuma nishadi. Aranta taji dadi sosai har suka katse wayar tana murmushi.

Daga nan wanka ta tashi ta shiga tanamai tunanin abunda zata soma yi inta fita duk ranta a dagule musmmn inta tuna wai sai ta nemi izini.

Kallon fatar jikinta ta dingayi taga kamar duk ya jejjeme yay baki da alamar dai bai mata kyallin data ke bukata ba.

bayan ta fito daga wankan batay wata wata ba ta shirya kanta da normal kayanta riga da wandon jeans dayay mata kyau ya kuma nuna karamin ramar datayi kwana biyu, fuskarta yay fayau yay haske bakinta ya dadyin pink dake bata shafa komi a fuskrtan ba face man baki da turare.

Khaleel na Kwance shiru a fankacecen dakinsa me dauke da huge glass windows da home office yay lumui ya kuma hade ransa cikin takaicin meenal akan shirgegen burgendy red colour italian bed wanda yaji kwalliyar bedsheets deep orange da layi baki baki..

Sanye yake da lallausan black napoliana shirts da wandon burbery baki da fari mai laushi Kana ganin yadda yayi cross acikin comfotersa zaka dauka baccin yakeyi amma idanunsa biyu babu abunda yake yi sai ambatun Allah wai dan zuciyarsa tay sauki snn ya samu sassauci bisa desires din dayakeji aransa kar shedan ya fara kitsa mai wasu tunani na daban a wann yanayin dayake ciki.

Idanuwanshi a lumshe wet and sumptuos lips dinsa ne yake motsawa ahankli yadda zakasan ba bacci yakeyi ba, mika hannunsa yay ya dauki wayarsa dayaji tay kara acan gefen pillownsa ya bude jajayen idanunsa ahnkli yay scrolling sai yaga text messages ne har guda biyu dana uztaz ne dana kuma ogansa dr Aseem.

Na ogan nasa ya soma budewa agaggauce cikin nitsuwa snn ya hau karantawa, iyakar duk wani abunda suka zayyana da halisa ya fayyace masa tare da rokon alfarmsa akan da ya sassauta ma halisan

Amsar sakon khaleel ya tura ma sa atakaice dan ya san ya ga sakon nasa duk dama baisan meyasa har ya amince akan abarta tafara fita waje ba dan shidai haryanxu aransa tsoro yakeji yana ganin kamar pretending to be fine kawai takeyi dan abarta taje ta kashe kantan amma ba lallaine tana cikin hayyacinta ba.

Can sai kuma ya tsaya cak da tunanin, jin kansa ya cirke, take Yabi yarasa meyasa ma ya damu sai halisa mansa ta rayu, dat insane feeling of care and obsession..kwata kwata ya nemi dalilin su na wanzuwaa acikin ransa ya rasa. Abun dai na mugun hatsalashi bana wasa ba.

Wata hatsalallen tsakin dayaja aransa me zafi saida ta fito fili a zafafe ya dada harde ransa kamar ma halisan ce take gabansa ayanzu.

Badon ogansa ne yace abarta ba da shikam da bazai taba amincewa taje konan da bakin gate din gidansa batare da ta kammala dukkan wani treatemnt dinta ba.

Watanni shida na cikakken jinya ne cas cas wa'adin lokcin da ake tsammanin zata iya warkewa daga ciwon nan na depression din nata kwata kwata.

Tun da suka fara jinyar bai taba sawa aranshi cewa bazai iya kwaco Halisan daga ciwon nan ba infact he thinks is easy to dealt with her musammn ma daya san cewa suntsane junansu sosai duk dama bai san meyasa ya damu da ita aransa ba.

Da wann rudadden yanayi na muhawara da bangaren zucyarsa da yakejin he dont care abt her a wani bangaren kuwa zucyarsa baiya neman izini inzai aikata wasu abubuwan akan halisan sede kaga kawai yayi wanda shikansa baiya ganewa, ahakan ya zauna abakin gado yay shiru cikin tunani.

Can ya jawo wayarsa ya bude Ya karanta tex din uztaz tsaf, ya rasa me zai ce, dan gani yake kamr inhar ya bashi go ahead yaje ya siyo abinci hala ra'ayin halisan kawai zai bi.

Abincin da zata ci na safen yay odering ta wayar sa as usual salads, fruits and omaletes with one piece of probiotics. Yana kammala odering duka duka abincin ya turawa uztaz tex na sunan restaurant din akan yaje kawai ya amsa.

Uztaz kuwa na ganin sakon baiyi tunanin komi ba ya fice abunsa ya nufi wajen domin karbo sakon akan lokci dan ya samu ya gama kulawa da lfyar halisa ya nufi office dan abubuwa sosai suka fara musu yawa yanxu sabida karuwar sabbin client da suke samu tako ta ina.

Hakan ya bada khaleel damar kimtsa kansa a nitse, yafi minti talatin a gaban mirror trying to perfect his breathtaking looks, within no time ya saka pure white shirt mai dan sharara me three qtr sleeves, Da gucci write my paper brown shots sai takalmin sa mai laushi ta kamfanin massimo dutti iri daya zak zak da kalar wandon sa da hadadden royal oak agogonsa gabaki daya jikin shi na baza wata iriyar sassanyar qamshi na sabuwar turaren da yaune ya fara shafata.

ya san yarinyar da girman kai,aransa yasaka in har bata budi baki ta tambaye sa izini dakanta ba bazai taba nuna mata yasan da maganan fitar tan bama..wayarsa ya jefa a aljihunsa snn ya fito daga dakin nasa ya nufi inda taken straight...

Tafiya yake a nitse looking dashing tamkar wanda bai taba saka irin wann suturar ajikinsa ba. LITTAFIN NA KUDINE #SURAYYAHMS

TO SUBCRIBE CHAT SURAYYAHMS @ 08060712446

DO NOT SHARE.....

A cikin sanyin aji mai tafe da nitsuwartasa ya iso har bakin kofar dakintan yay kncking yana daga tsaye sai bayan kamar mintina biyar ta bashi izini ya shigo daga ciki...

Yana turo kofar Wani takurarren Kallo ya bita dashi tare da darsa mata ruwan idanuwansa masu tsananin kwarjini da rikitarwa daya kusan rudata atake tayi saurin daidaita kanta ta tattaro nutsuwarta da ƙarfin halinta tanamai dauke kanta daga kansa gabaki daya tare da sauke tsiririn tsaki..

Qarasowa yayi cikin yanayin sanyin nitsuwa yanamai lura da abunda takeyi dan already ta riga ta shirya kanta cas cas tay fes tana zaune akan kujera, wata hadaddiyar boot din paco rabanne daya mugun dacewa da kalar rigarta take kkrin sakawa akafafunta ahnkli kamar bata san da idanuwansa daya zubo akanta ba.

Hular face cap ne akanta ta dunkule suman kanta aciki fuskarta a tsime batace dashi uffan ba shima baice da ita uffan ba yanayinsu kowa naji da dagon kansa da alamar kowa yana jiran dan uwansa ne ya fara gaishesa.

Tunda ta sunkuyar dakanta kasa babu abunda xuciyarta ke rayawa face jin takaicin wann lokcin da Allah ya kawota dahar saita nemi izini daga wajen sa kafin nan ta aiwatar da komi.

Shidin ma Kallonta yake cikin ayyana wasu maganganu aransa game da hakan, har saida ya gaji snn ya kyabe bakinsa slowly and mischiveously yanajin aransa yanzu fa ya in yace bazataje ko ina ba haka zatay hakuri.

Kuma Babu tantama shaukin hakan yake ji akasar ransan sabida sam baison ma ta fita ko nan da waje gani yake kamr za ta iyacin karo da saurayintan can dayake son ya fara rabata dashi kwata kwata sede bazai iya aiwatar da komiba dan baison ogansa ya farayin masa wani tunani na daban.

Leaning back a bit ya dago glassy eye balls dinsa ya kure ta wani irin piecing looks directly looking at her cute natural beauty Calmy Snn yace "how you feeling? "Ya jiki?..

Bazata ta Lumshe idanuwanta dasuka fara canxa kala snn ta budesu jin yadda yay maganan cikin nutsuwa da taushi.

cike da dakewa muryan ta ciki ciki tace masa, "good" snn ta gyara zamanta akan couch din tadan dago kai sama sede jin ta kasa iya hade ido dashi yasaka ta dadayin shiru....

Batare da ya kulata ba ya tabe baki snn ya taho ya dan dudduba vitals dinta nan yaga har sun dan soma dawowa normal dan zafin jiki dayake damunta kwana biyun ma ya sauka da degree daya, hawan jinin nata ne dai sai ahankli gashi shikansa baison ya dorata akan maganin hawan jini.

Wani abu ya daddana ajikin system control dayake monitoring din lafyartata yana kan dannawar ba yabo ba fallasa yaga Induction dinta ta ma duk sun kare izuwa ynxu allurorin ta ne kawai ya rage shidin ma once in a day ranar da zata cika sati agidan nan shima zai kare.

Wani abu fari me press buttons kamar head light ya dauko tare cream kamar maclean dan karami da ya dosho ta dashi baice mata komi ba ya dan tsaya daf da inda take Yanamai satar kallonta Dan banda latsa wayarta babu abunda takeyi, Miskilallen kallo yke binta da shi ganin bata san ma yanayi ba ya hakura yace..

"Xcuse me Can i see yr hand?

Tanajin shi batace uffan ba har saida ya sake memetawa snn ta dago kai suna hade ido taga girarsa na sama a dage Yanamata wani irin kallo.

Dada harde ranta tay kamar yanda yay snn ta bashi hannun kamar bazata bayar ba ji kawai tay ya dan fixgo hannun da dan karfi sai da ta gyara zaman dole tana mai kallonsa ganin baiya ma kallonta tsirin tsaki ya kufce daga bakinta dada harde ransa taga yay da alama ya tsani ajamai tsaki.

Dede inda yake yawan mata Alluran ya zuba cream din yana saka yatsar shi akai zai shafa mata ta yi kicin kicin zata janye hannunta jin ya rikeshi dam dam yasaka ta hakura jin kirjinta na bugawa da dan karfi ta runtse idonta gam gam ta rike jikinta dake neman yay rawa rawa, wani yarrrrr din laushin hannunsan kawai ta keji na mata yawo ajikinta uncontrobly, ido ya kura ma lumsashen idanunta yanamai sauke boyayyarr ajiyan zuciya da alama kyaun fuskarta na balain rikita shi komin haushi datake bashi sai yaji ya gushe atake dan Saida yaci minti uku rike da hannuntan a shagale yanamai karewa fuskar nata kallo while her eyes are closed.

Ganin kamar bazata bude idanun nata nan kusa ba ya kyabe bakin sa ahankli yy murmushi me sanyi data kufce masa abazata.

ahankli ya fara shafa mata cream din a dede wajen yana lailaya mata jijyoyin dake wajen dake duk sun kumbura sabida anan kullum suke allura,.

Ahnkli yake mata yawo da yatsunsa awajen at same time yana dubar yanayinta ko zatay reacting dan sumhow akwai wani bangare na zucyarsa dayake mata kallon watsatsiya sanin cewa yanayin addininta da rayuwarta na zamani bai lallaine ya zame me doka me tsanani akan zina ba.

Halisa taki sam ta bude ido bare ta nuna masa yanayin datake ciki, iya dauriya tay dan har ji take kamar zata saki fitsari ajikinta yanayin dayake shafa mata man akan wajen.

Tun yanayi dan ya gwadata har abun ya soma tabashi batare da ya shirya ba dan abazata shima yabi ya lumshe idanunsan jin yadda tsantsi da laushin jikin nata ke jansa duk ya kasa iya dena kallon fatar ta dayake nan soo shiny and smooth kamar kullum gogeshi akeyi da ruwan zuma da madara..

atake idanunsa suka sauya kala sosai yafara jin wani iri iri aransa da gangan jikinsa wani abu yadingaji na masa yawo tun daga tafin kafafunsa har tsakar kansa..

Sihirtaccen ajiyar zuciya ya dinga saukewa ta ciki yana kkrin ya calming zucyarsa cikin kwatar makansa nitsuwa da karfi ya bude idonsa tare da sake wata nannauyar ajiyar zcya taciki sai gani yay har halisa ta bude idon nata tanata kallon yanayinsa suna hade ido yay sauri ya kawar dakai dan kuwa ji yay kamar ya nitse kasa dan kunya sai kuma yabi ya fuske yay kmr baisan me yayi ba kuma bai sake hakan ya nuna akan fuskarsa ba.

murmushi kawai halisa tay aranta tanamai cewa "namiji kenan" kallonshi ta dingayi dagangan dan mugunta sanin sarai kunyar yanayin data gansa ya lullumesa, cike da basarwa ya dauke kansa akanta da dan sauri ya dora headlight din akan hannun nata wani farin haskene ya bayyana akan dede inda ya shafa man ko minti daya baiyi ba tajiyo wani sauti daga cikin system control din kusan atare suka daga kai suna kallon screen din dayake nuna hoton wajen a screen din monitor din.

Its so amzing to see how her veins are arranged wansa shine ya janye hanklnta daga kansa dan bai dauketa wani lokci ba itama tagane wajen daya dan kumburar yay jaaaa kafin khaleel yace wani abu sai ga nan uztaz ya dawo da ledojin abincin da khaleel ya aikesa ya karbo

Yana qarasowa ciki ya taho kusa da ita ahnkli dan ya duba me ake mata itakuwa dadi taji dataga uztaz da abinci dan yunwa na damunta bana wasa ba, yana tsayawa ta pointing masa screen ahnkli tace mai look, uztaz yay murmushi, "ur veins? Ta gyada kanta."i wish i can see my head.. dariya uztaz yay sosai. khaleel na jinsu baice musu komi ba. Ya gama danne dannen sa ajikin system din kafin nan uztaz har ya zubo mata abincin a plate ta saka hannu ta karba tana yatsina fuska dan harga Allah sam bata son cin wayann abincin itakam sede daga zarar ta tuna maganansu da jasmine sai taji karfin gwiwa dan haka ta dau fork din dake kai ta fara cakalawa har ta yanki kadan ta kai bakinta ta fara taunawa Ahnkli kamar bazata ci ba.

Tanakaiwa loma biyu taga uztaz ya mike tsaye yana duban agogonsa. Ji tay abincin ya tsaya mata a wuya..yace "Boss, u need anything?

Hadiye abincin dake wuyarta tay snn Tace yeah, I need you.

khaleel yaji kalman har ransa batare da yasan meyasa ba.

Sauri kakeyi ne?

Aladabce yace " Eh muna da bakin da zasu zo snn muna series of meeting yau din nan Yawwa boss did Rembr those...Tun bai karasa ba cikin katsesa tace no no don't tell me anything bana son kaina yay ciwo. I just want to go with u..tunda yanzu zaka tafi ga abincin nan sai ka ajiye ni na koshi..

Batare daya kalleta ba ya dubi khaleel snn ya juyo ya dan kalleta..da ido ta masa alaman akan ya gayawa khaleel zasu fita uztaz ya rasa me zaice ganin ta dage tana masa signal da ido ,ya lura kawai de girman kai da qwuiwar masa maganan ma takeji snn inya biye nata zasu iya bata lokaci anan sosai

hakan yasaka ya dan dago kai ixuwa kan khaleel yana juyowa kuwa suka hade ido caraf, kafin yay magana Yaji khaleel din na cewa malam idriss ice cubes pls, Akwaisu acikin freezer a kitchen pls kataimaka mana dashi

..da sauri uztaz yace okay sai ya juya cikin sauri sauri ya fice ya je daukowa ya kyalesu subiyun a tunanin sa hala kafin ya dawo sun sasanta...

Bayan fitar uztaz Direct khaleel ya dosho kanta cikin nitsatsen takunsa aransa yana mamakin yadda halisa take iya kare masa takadadarren kallo, sau tarin yawa yakan ji aransa kamar kwarjininta girman kai ne, hakama wann rashin tsoro da boldnes dake cikin kwayar idanunta taurin kai ne bakomi ba.

Bai dena raya hakan aransa ba Har sanda ya iso daf snn ya tsaya ya riko hannun nata da karamin plaster a hannun sa duk ta sakankance zai manna ne ya tafi sai taga ya dan dofano da jikin couch din kurkusa da ita sosai ya zauna, gefe ta matsa jin Wani yarrr trr tsigar jikin ta na tashi musmn da qamshin turaren nasa ke neman shake mata numfashinta gabaki daya.

Ahnkli ta dada kau da kanta har ma bata so ta dubi meyake yin gabaki daya..

Idanuwansa nakan abunda yakeyin but deep within him he's battling with his self control dan duk wani motsin datayi sai ya duba, wai shin ma wani irin tsana ne yake mata da har yau bai gane kansa ba??? Da duk wani karamin motsin datayi in discomfort sai yaji zafin abun har cikin kokon zuciyarsa. A lissafin sa Halisa bata cancanci ya kulata da ita ba sedei a lissafin zucyarsa kuma jiyake kamar shine dan Adam na farko daya fara jin shaukin kulawa da matar daya tsana.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull