Kenza eBookz

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 19

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 19

Cheaters club book 2 complete novel Chapter 19: Cheaters club book 2 complete novel Chapter 19. Yana kkrin kammala manna karamin plaster din bakinsa ya…

3,252 words

Yana kkrin kammala manna karamin plaster din bakinsa ya furta.. "U need to rest' ahankli sosai.

Ta rasa me zata fara cewa tay shiru for some time yana daf zai mike tsaye ta dago kanta da niyyar kallonsa sai caraf idanuwansu ya sarkafu cikin na juna small cute pouts din datay kamr na yar 4yrs ya daskarar dashi batare da ya motsa wani gaɓa daga jikinsa ba jin yadda zuciyarsa take harbawa da wani irin karfin tsiya. She is indeed effortlessly beautyful duk shirmen datay seyay ma fuskar tata kyau, is like duk sanda ya kalleta sai ta sauya masa da wani kamanni na daban, she have dis one sided dimple wanda inba ka kalleta da kyau bane bazaka gane tana da shi ba ma, ajiyar zucya me nauyi ya sauke ta ciki ganin ta kafe sa da ido kamr yar yarinya karama dan ji tay Ta kasa dauke idanunwanta acikin nashin itama da suke nan cike da wasu kalar sakonni da sam ta kasa iya tantance su, lkci guda taji kanta ya cirke ganin irin kallon kurilla dayake ma kyakkwar fuskarta kamar be taba ganinta a rayuwarsa ba.

Wani abu kamar sihiri ke fizgarsu tare da nanar dasu acikin wann yanayi Da kyar yay Rolling din idanuwansa calmy tare da sauke mata double smirks fuskarsa babu yabo babu fallasa kusan atare suka budd baki zasuyi magana shiya rigata da sauri yace "kinji me nace miki? Ta girgiza kai alaman bata ji ba...

Ahankli ya rangwafo Daf kan fuskarta yanamai kallonta cikin wata murya me kamar whisper yace i said , u need to rest ...cikin lumshe ido da budewa jin bugun kirjinta na tsanantawa kai tsaye tace "i know, "am going out too...ya kureta da ido sosai cos dis sentence bai yi kama da na me neman izini ba but she is boss lady sai abun bai basa mamaki.

Boss ladies neva ask for permission, idan mace ta kai ta cika all her words are bold and elegant they don't out needy... Ko Meyasa ma yake tsammanin jin sumting as little as please daga bakinta oho, aransa yasan ma hala bazata taba furtawa ba.

Yana kammala raya hakan aransa ahnkli yaji tace "pls" din duk dama a kasae wuyrta ta furtashi

Girarsa na sama adage da mamaki ya kalleta ganin ko kallonsa batay Yace mmm, to where? Ina zakije..

Kafin ta amsa ya dan bata ransa yana me cewa wann satin gabaki dayansa na hutunki ne i hope you knw dat u have more to do next week wanda zai shafe motsa jiki dan haka baki bukatar zuwa ko ina hutu kawai kike bukata yanxu.

Muryanta adan shagwabe ya fito badon taso ba, Tace ba ko ina nake zuwa ba dama Kuma ba dolene bane in gaya maka sunan wajen okay, U can't keep me here like i am your prisoner, i am looking soo unkept or i am not allowed to my personal self care?...,

Tana kammala furta hakan at same time tay Scoffing ganin irin kallon daya karewa jikinta dashi agaggauce..

She had to relax giving him dat perfect i dont care mood har yagama checking inta out da idanunsa shidai baiga ta inda maganan nata yaje ba bcos her skin isnt looking bad at all a wajenshi wani self care kuma take bukata kuma,

ita kuwa gani take kamar kwana biyun nan data kumshu a daki duk ta dishe ta dawo wani abu na daban sabida tsanar zamanta datayi agidan sai tana ganin kamar jikintan ma ya dishe ya lalace duk dama ba hakan bane kai tsaye.

Its just the environment she hates and she is not comfortable with....

Yanayin fuskarta ya kalla yadda ta harde hannu ta bata ranta sosai Sann ya dan mike tsaye cikin tabe baki.

Okay fine.. i need to knw the name of the place and time..

Ta dauke kai cikin sauri ganin yadda ya furta maganan da iko kamar irin shine mijintan nan. wani tukikin tsaki tay aranta batare da ta kallesa ba snn tace "My assistant will tell u Everything" Ta fada cikin jan aji sosai.

Shiru yay baice mata komi ba tukun ya xuba hannuwansa acikin aljihu

Shiru ne ya gifta tsakanin su can sai ga uztaz din ya taho da ice packs a wani bowl da ya zuzzubasu.

Kallon yanayinsu yay ya rasa meke faruwa a dakin ganin halisa ta dauke kai khaleel din kuma ya zuba mata idanunsa daga tsaye.

Saida yay Gyaran murya kafin nan suka dan juyo dukan su suka kalleshi kusan atare.

Yace Dr ga ice din.

Khaleel ya amsa yace thanks

Agaggauce ya dawo gabanta cikin nitsuwa ya kamo hannayenta biyu tare da nashi snn ya dubeta yace Breath in and out, ahnkli taja numfashi ta fetsar waje snn yasaka ta memeta hakan sau uku bayan tay hakanne ya saka hannun nasu acikin ice din atare yanamai daddanawa kan jijiyoyinta aciki ahankli.

Jin sanyin abun ta dingayi har cikin kanta sai kuma taji kamar an yaye mata wani abu akan nerves dinta sosai suka zamo calm ko minti uku basuyi ahaka ba ya cire mata hannun ya rike a nasa, kafin nan ya zaro hankynsa na calvin clein fari me dan kauri daga aljihunsu yabi ya Dora hannun nata akan hankyn dan damshi damshi da sanyin ruwan dake hannun nata ya tsantsame tasss ajiki.

Uztaz dake sauri dan ya fita ya kalle khaleel fuska ba yabo ba fallasa ya fara masa bayanin inda zasuje da Halisan kai tsaye.

Yanxu da halisa bata nan aikin managing kamfanonin su sosai yake neman yasha masa kansa duk dama lafyar tan yafi masa komi amma baison yay wasa da aikin sa ko kadan dan haka yake son yakaita ya wuce office da gaggawa.

Duk bayanin kyale kyalen matar da zatayi baji khaleel yake ba, abu daya ne kawai intrest dinsa yake kai shine How private is that place? Dan Baison taje inda akwai maza ko taron mutane Ya tambaye uztaz game da hakan.. nan ma yay masa cikakken bayani cewa private body shop ne na business organisation dinsu na mata masu kudin kansu a garin lagos so zallan members din kungiyar ne Kadai suke iya shiga wajen snn babu abunda babu aciki.

Hanklin khaleel ya kwanta sosai dayaji hakan ya kalleta ganin ta gama qakuwa yace mata su tafi caraf sai taji yace "In taci abinci zaku iya tafiya. 2hrs is enuf? Da wani irin gatse Tace "No, is not enuf, i need like 10hrs..har zai amsa ta kenan uztaz yay saurin katseshi "sir, i promise zamu dawo on time snn zata ci abincin...karka damu.

Yay sauri ya dauko abincin ya mika mata ranta a bace dan ta tsani renin hankli ta karba ta rike cike da taurin kai taki ci ganin khaleel nata kallonta Shima Allah Allah yake takici yace mata bazataje ko ina ba.

Nan uztaz ya deba mata a spoon zai mika mata khaleel ya saka hannu ya karbe "pls let her eat by herself..ya dangwala mata spoon din a hannu taja mai tsiririn tsaki ya hade rai kamar zai fashe dan Badon yanayin magiyar dake bisa kan fuskar Uztaz ba da sai ya hanata zuwa yaga ta fadin.

da kyar ta dauka ta fara ci ahnkli, gabaki daya saida ta bata musu lokci kafin ta gama cinyewa tasss tasha ruwa after relaxing for 3 mint Ta mika mai plate din ta mike tsay Ko wayarta bata dauka ba uztaz din ne yabi ya tattaro mata da dan karamin side bag dinta ya rike zai sakata agaba tace nop ta dawo tsakiya shi yana gaba khaleel na tsaye daga bayanta yana kallonta bai hankara ba yaga ta cire Face cap din kanta da niyyar ta cillo shi baya, suman nata yololo ne baki sidik kamar na sadaka yalla Dan haka yanayin da suka ziriro gadon bayanta ya mugun tafiyar dashi bai hankara ba yaji saukar face cap din fuskarsa kwafffffffff ganin bata juyo ba yasan da gangan ta jefeshi dashi yay kwafa baice komi ba har suka fita....

Kan computer ya koma yabi ya tattaba snn ya dawo kan cameras din ya cire wanda yake saman gadonta dana can sama yabar wanda yake jikin mirror dake miirorn na iya haska gadon nata directly shima.. LITTAFIN NA KUDINE #SURAYYAHMS

TO SUBCRIBE CHAT SURAYYAHMS @ 08060712446

DO NOT SHARE..... #SURAYYAHMS

Harsaida ya kammala abunda zai a dakin snn ya fice ya koma sashen sa, yana shiga ya aje wayar sa akan table snn ya rage buttons din gaban rigarsa sa kamar guda biyu ya bude cabinet inda wasu manyan manyan text books da journals suke. Tsayawa yay idanunsa stiff akansu cikin tunani wanne littafine zai taimakesa akan bisa lokacin daya rage masa ynxu.

sai can ya zaro wata katuwar littafi wanda girmanta zai kusan kai oxford dictionary gaban ta an rubuta "the law of human nature" by Roberts greene. Littafi ne dayay exploring 18 universal laws dat gorvens human behaviour and pschology

Yana daukawa ya aje shi akan table snn ya zaro wani madaidaci an rubuta the evolution of human behaviour 1982, By helen .E. fisher duk ya hadasu waje guda snn ya tarkatosu tare da hanklin sa ya zauna agaban computera yanamai tsunduma akan aikin project din nan nasu na larabawa da suka sako agaba.

Bangaren halisa kuwa Tunda suka fito batace ma uztaz uffan ba shima baice mata komi ba har suka isa gaban lexus din daya parker a tsakiyar gidan cikin sauri ya bude mata owners coner ta shiga ta zauna sann ya aje mata wayarta da jakarta agefenta ya rufeta ahnkli.

janyo jakar tay ta budeshi ta fidda karar tabarta data boye aciki ta kyasta lighter akai ya kama ahnkli tay relaxing bayanta akan seat sann tafara xugar hayakin ahnkli tana fetsarwa waje.

Langwamar dakant tay cikin seat ruwan dake kwayar idanunwanta atake sukayi luf kamar na me jin bacci dan kuwa sassanyar qamshin turaren khaleel data kwaso daga jikin hankynsa daya goge mata hannu dashi ya kama mata hannuntan harma yafi kaurin tabar tata tashi wanda shine yake kashe mata jikinta a yanxu bana wasa ba.

zagowa uztax yay ta dayan bangaren driver ya bude snn ya shigo shima yana zama ya bude gaban motar ya dauko wata golden and black card acikin tarkacen da jasmine ta zuba mata a podcast dinta.

Address din club house din ya kalla snn ya kunna motar suka kama hanya izuwa victoria island after few minutes suka iso gaban wata sharbebiyar gate da gabanta yaji security duk sun saka uniform me kama dana sojoji suna tsaye da bindigogi a hannayensu suna gadin wajen.

Card din kawai ya ciro ya nuna musu abakin gate din snn aka barsu suka shigo har ciki.

Wani irin serene and secure contemporary 3 level building ne ata ciki dats located in the heart of victoria island.

Wajen shakatawa da relaxation ne na aiwatar da abubuwa da yawa kamar business meeting, conference, treats, round table discussions, arts/fashion, exbihitions da abubuwa dayawa wanda hamshakan manyan matane zalla suka taru suke juyashi Domin kuwa an kirkiresa ne dan yay serving 5% na top african female business excutives,Ceo, business owners, senior professionals, officers da business founders..

practically duk wata macen datake kawo cigaba ma kasa da kuma bunkasuwar kasuwanci tsakanin mata a kasa tana ciki dan Is a top premier private business women club u have to be a member kafin nan ka samu shiga wajen.

Uztaz ya sauko agaggauce ya bude mata kofar motar ta sauko tare da daukar jakarta ta rataya a kafadunta dayan hannunta na rike da karar tabar tana zuka a hankli tana kuma tafiya cikin kamiya da nitsuwa.

Zai magana cikin katseshi tace kaje aikin ka kawai Inna gama zan iya komawa gidan dakaina. Waje ya gwalo idanunsa Yace boss no am sorry. Doctor khaleel yaban strict oder Akan hakan..batace komi ba ta gyada kai aranta tana jinjina ma iyeyin khaleel tare da cin alwashn zata ladabtar dashi. Yadda tay shiru tana sake sake aranta Shikansa uztaz ya kasa fahimtar abunda zuciyarta yake ayyanawa a dede wann lokaci.

toh ka rakani ciki kasan yanzu ana hutu da wuya ne kaga wasu member din anan.

Bai mata musu ba ya fara binta abaya hannun shi rike da wayarta aka bude musu wata sharbebiyar glass door Wata receptionist na tsaye tana murmushi uztaz ya nuna mata card

Aladabce tace Ure welcome to the club house maam how can i serve u..business? Meetings...cikin katseta halisa tace "De-stress."

Matar ta gyada kai cikin girmamawa ta danna wayar dake gabanta take take sai ga wasu sun fito namiji da na mace sanye da uniform din aikinsu ajiki ta gaban rigar an rubuta Amalfi wellness

Nan da nan suka musu jagora zuwa amalfi wellness area inda akwai steam room, massage spot, fitness area da duk wani abunda ake bukata na tattalin jiki da kara lafya ma gabban jiki.

Suna shiga wajen fiye da yan mata hudu suka iso dansu serving inta cos they have this tasty snacks, high teas, mocktails acikin famous gaby bistro bar dinsu anan ma babu abunda basu zagaye table dinta dashi ba, nan uztaz ya bata wayarta sukayi sallama ya fita ya wuce office kai tsaye.

Bayan ta sha ruwa taci salad ta dan huta suka bata kaya ta sauya snn namijin ya wuce da ita fitness center dan ta motsa jiki ta kuma dada toning shape inta while matayen suna kan har hada massage therapies Da haven wato inda zata relaxing kanta sosai bayan angama komi.

Kafin kace wani abu Har halisa ta fara samun kalar kulawar datake bukata ma jikintan....

Ata dayan fannin kuwa wani babban conference hall ne cike da manyan mutane maza da mata majority awajen suna sanye da bakaken suits sai dedeku da suka sako native da hula anata famar tattaunawa.

Amina Ali talba ce zaune akan babban kujerar dayake fuskartan na kowa sanye da dark green classy suit dinta ta hakimce.

Daya daga cikin manyan sectaryn ta Rukayya ce agaban ta da wasu bunch of files ta dan rangwafo suna magana da meenal din kasa kasa wanda daga ganin idanun meenal din kasan ranta a mummunan bace yake, Wasu files take dubawa kamar kanta zai kama da wuta tanamai cewa "How comes? Ina tender of agreements dina?? Baki na bari rukayya tace Ma'am.. Cikin datsar numfashinta tace Shuttt up bitch kina haukane in babu shi fa bani da contrcs they will terminate it all... My tenders are my evrything babu wani kamfanin da zata saka sabuwar hannun jari dani in babu su... Go and Find them nowwwwww. Tafada a hatsale kamar zata hadiyeta dan fushi.

sectaryn duk ta rikice ta kasa barin wajen bayani take mata dan ita tun da ta fara aiki anan ma bata taba cin karo da files din ba bare taje ta dubosu.

Kusan Musu suka dingayi tsakanin ta da meenal din dan meenal tasan fadila tana amfani da tenders of agreement sosai wajen kwamuso musu contract masu tsoka kuma akan lokci tayaya kenan za'a ace mata yanxu babusu?.

kusn A hatsale cikin mutanen meenal ta daka mata wani kaskantaccen tsawa" keeee kina cika min kunne na just Get out...incompetent whore. Da yanxu bibiyar maza nace kiyi da tuni kin iya just get lost...ouuutttt

Da sauri rukayya ta tattara file din har jikintaa na ɓari idanunta sun ciko taff da ruwan hawaye looking soo embrassed ta fice awajen da sauri sauri...

Kusan Kowa sai da yaji mata kunya bacin meenal din da bata ko daga ido ta kalleta ba bandama tsakin datakeja mai sauti dan sosai ya ranta ya baci bata da yadda zatayi hakanan ta danne zuciyarta taciki

Tashuwa tsaye tay kamar wani abu beifaru ba taje gaban majigin ta tsaya tahau bayani acikin jiji dakai kamar yadda ta saba nuna ita watace.

Bayan Alot of them sunsan bata da wani abu ynxu da zata nuna musu akasa dan tun da fadila tabar wajen babu wani sabuwar ci gaba da talba grp of companies suka samu dan haka ba wani bata attention dinsu sukeyi ba.

Harta kammala proposing din new business project dinta babu wanda yace mata uffan ba just few of them suka mata tambaya akan financial investments amma bayan haka basu ce mata komi ba, diff ta tsaya tana kallonsu tana murmushin karfin hali while ranta na tafarfasa tanajin kamar ta zazzagesu ta huta.

Mamaki take sha ganin babu wayanda take tsammanin zasu zuba kudadensu ayi abun atare duk sun nade hannu sun zuba mata idanu. jim kadan wasu suka tashi kai tsaye suka tattara files dinsu suka fita batare da sunce mata uffan ba.

Dedekun da suke ganin mutuncin ubanta suka barta da kalman they will get back to her on this.

Few of them da basu da wani mutunci bayan anwatse suke ce mata inhar zata arranging musu night shift da sectarynta dansu kwana da ita a hotel toh babu shakka zasu saka mata hannu.

Meenal ta rasa meke mata dadi sam, ganin komi na kamfaninta na neman rugujewa, yaune karo na babu adadi a rayuwarta data ji kufcewar fadila a kamfanin ya taɓa mata zuciyarta bana wasa ba.

Fadila has neva been dis slow. Komi takanyi shi ne akan lokaci kuma bisa qa'ida dan sosai suka kure wajen bata ilimin kasuwan ci a kasar waje wanda yasaka data dawo bata rike musu kamfanin su da wasa ba.

It kills her to rmber dat A karkashin fadilar manyan contract har saima ta zaba gashi bata komi hatta presntation da meeting fadila ce take yawanyi..

bada son ranta ba tay tagumi tay shiru, jin gashi yanzu ko daya bata kama ba bacin tsoffin datake dasu.

Gashi Bacewar tenders din ya saka kowa yaa tsame hannunsa daga kan sabuwar harkan business data bude. All she have now is her shares, and old contracts new ones din dai duk sunki kankama

Kasa zama a office din tay ta dau jakarta cikin yanayin takaici da damuwa ta fice fuuuuuu bata tsaya ko ina ba sai wajen mummynta hajiya nadia a gidanta dake anguwar banana island.

*********** The same day.

Yau ranar monday karfe 8 na safe prince Femi ya bude kofar dakinsa ya fito looking all glam acikin wata bakar yadi sharara da aka yi masa dinkin elegant half jumpa na kamfanin Marks weber me guntun hannu yay pairing look dinsa da hularsa me tsada original jan Dara data haska sulbabben farar fatarsa,..

black sandals na Dior ne akafafunshi jikinshi ya dau qamshin turaren versece eros da notes of licorise daya saba shafawa akowani fita.

Yana takunsa a nitse cikin girman kai da jiji dakai hade da shan qamshi yanayinsa kamar bazai koma ga Allah ba

Kayan ta masifar haske sulbabben farar fatar sa da tsabar tana samun kulawa har yellow yellow takeyi dakanta, Bakin nan tasa tayi wani irin dark pink colour mai daukar hankli femi bakaramin kyakkwan saurayi bane me jini a jiki ire irensu ke saka yan mata sumewar tsaye Dan Allah ya zuba masa kirane me asalin daukar hankali.

Bisa Gawurtaccen kwarjini mai tafe da jiji dakai yake dora takunsa mai tafe da sanyin kasaitar dake wanzuwa acikin yanayin hadadden shigar tasa.

Sashen vicky ya nufa kai tsaye dan Tun jiya da bai gane mata ba sai bai sake lekowa tanan ya dubata ba..a tunanin sa izuwa yanxu hala ta gama fushin ta sauko dankanta.

Acikin nitsuwa ya tura kofar dakin mamaki yaji dayaga kofar a bude ba rufeshi ba, kai tsaye ya shigo ciki yatsaya cak ganin ko ina fess fesss kamr ba nan ne jiya yaga ta kawata da decorations din anniversary dinsu ba, shirun dayaji yasaka sanin cewa bakowa A dakin hakan yasaka ya fara tunanin ko harta fita office ne bata nemesa ba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull