Kenza eBookz

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 26

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 26

Cheaters club book 2 complete novel Chapter 26: Cheaters club book 2 complete novel Chapter 26. Around 6.56 am ya kamo hanya izuwa gidan lkcin gidan babu…

3,321 words

Around 6.56 am ya kamo hanya izuwa gidan lkcin gidan babu motsin kuwa koina shiru..yana bude kofar dakinsa direct ya nufi kan gadonsa ya dauki wayar yy sliding screen Tun baikai ga budeta duka ba yaga notifications with 3 miscalls da 1 text message 56min ago akai da alama da karfe 6am dede aka kirasa wanda koda bai sani ba na ogansan ne.

Zama yay abakin gadon snn ya bude text din ya karanta yaga ya rubuta masa cewa jiya cikin dare jirgi ya taho dashi daga abujan snn 10am sharp yake son ganinsu a NISA premier hospital din tare da patient din sa.

Reply ya tura masa snn ya mike tsaye dan yaje ya sanar da ita danta shirya akan lokaci,da can har ya bude kofar sai kuma ya tuna kalar wahala datake cusa ma gangan jikinshi inyaje wajen hakan yasaka ya fasa zuwa saikuma yay fowarding sakon izuwa wayar uztaz Kai tsaye..

Bacci ne a idanunsa amma haka ya fasa iya komawa kan gadon ya koma kan computersa ya bude ya fara duba file file na gamsashun progress report din dayay guda daya ne ya ragemai da bei karasa ba yake kan yi

Idanuwansa duka nakan aikin yana typing yana editing da sauri sauri duk dama kwakwalsa da zuciyarsa duka basu tare da shi. Haka kawai yake jin wani matsanancin haushi na tason masa daga kasar zuciyarsa cos he cant belive wai yau halisa zata gama cinye week din da aka debe mata agidansa batare da ya gane komi gameda rayuwarta ba. Is like he expect to see sumting more not these tons of confusing dramas and talks. Har ya kammala typing din yay editing yay documenting dinsu hanklinsa baya kan abun sosai. Kafin nan ya kammala already karfe takwas da minti arbain yayi, dede lokacin hjy nadiya ta farka ganin meenal na zaune akan table da nitynta tana Danna wayarta hankli kwance, gabaki dayan su babu wacce tay sallahn jiya bare na yau dan basu tashi dawowa daga club meeting din nasu ba sai wajajen sha biyun dare

Da tsananin kishi hade da haushin halisa hjy nadiya ta kwana aranta.

Abun takaicin ma duk sanda tataso da maganan wa meenal sai meenal dinta fusata ta haura mata da mugayen maganganun banza tana maicewa ita bataga wani aibu a dressing din halisa ba kawai khaleel dinne me shegen jaraba da baida kamun kai shiyasa yake yawan kallon jikinta.

Sunyi musu akan hakan yafi sau akirga haryakai ga meenal tafara cewa mummynta tana fadin hakan ne danta hadasu fada da halisa agidan snn dantana son ta cusa mata son kwana da namiji kamarta.

Ita sam batason ta rika bawa khaleel jikinta anyhow saboda ji da kanta datakeyi sosai tafiso taga ya wahala yana binta kafin nan intay raayi tabashi ya lasa.

Daga kan gado tay shiru tana kallon meenal in her heart She kept wondering a wann zamanin wani irin wayewa ne da har zai saka meenal rufe idanunta akan mijinta da rayuwar aurenta?..

Dan daga masu ilimin har izuwa kan jakkunan matan duk sunsan suyi kishin mazajen su amma haryanzu batasan awani jinsin mata yarta meenal ta fito ba tukuna..

Shin ita "Tinkiya ce ko me kwakwalwar kifice ko kuma me kan dusa ce da bata ganin zazzafar sha'awa karara acikin kwayar idanun mijinta akan wata ƴa macen?

Jiyan kawai da tazo gidan amma saida taji kishin hakan ya hanata samun nitsuwa aranta sam sam dan haka tasa aranta cewa ko meenal tanaso kobataso yau din nan saita hada tarzoma me zafi agidan wanda zai jawo ayi tashin hankli me yawa da sai saka halisar ta kasa zama.

Jiyan ita tay Convincing in yarta akan su kwana tare agidan sudan huta zuwa 10 am kafin suje office, badon komi ba sedan ta tsaya taga irin hukuncin da khaleel zai dauka akan halisa in ita tahada mata nata kalar makircin data kumso aranta dan bazata bari halisa ta kwacewa yarta tauroronta a idon mijinta ba..

Tabe bakin datay yasaka meenal din ta juya ta kalleta "mummy kece haka kika tashi da wuri i tot kince sai 10am zamu fita? Saukowa tay daga kan gadon snn tace ba dole na tashi ba nasan ko mijinki zaai leko dubaki da safe

Takaitaccen Dariya meenal tayi mummy kenan ciwo nake da zaizo dubani? Hmm ai inkinga khaleel anan dakin da safe to jarabar sa ya kawosa ko yazo ya matsamin nayi sallah sai kace washi aka bawa sallahn ya kawo duniya

Hajy ta taɓe baki batace komi ba harsaida ta sauka akan gadon,hm Ke kuma babu ruwanki da zuwa duba shi ko??..

Ko ajikinta tace ye, Most at times..in inaso ya samin abun wuya ko wani magana haka But not alwys..why are u asking me kuma,hmm zaki fara wa'azin auren nan naki ko mummy... Comn marriage is not built on sex bansan sau nawa zamuyi magann ba

Agajiye hjya tace I knw..niyau bani da karfin musu dake karfe nawa ne zanje nayi wanka??

Meenal ta duba screen din wayarta tace to 9 nima bari na tashi na farayi kafin kidan gyaramin kan gadon mummy yunwa nakeji toh ko coffe mana ki hada mana kafun na fito daga wanka..

Hjya na kallonta batace mata komi ba har ta zari towel dinta ta shiga wanka, da kyar ta mike ta jajja bedshet din sama sama ita kanta bawai ta iya gyaran bane dama can masu aiki ko halisa ce meyi musu daga ita har yarta basu iya komi na tattalin gida ba bansa harkan office dana hutu

Duk da haka hjy nadia ta ga duniya snn tay girman da tasan what is right from wrong.

Kasar zuciyarta bawai haka kawai takijinin halisa ba. Tun zaman datay dasu suna yan mata ta gane cewa halisa is 1000 times and more better than daughter ata kowani bangare na rayuwa. Tun sa can Bataso kawancen sun ba sabida tana ganin kamar duk inda suka shiga halisa zata zama tauraruwa ba yarta ba.

Amma Dake taga meenal dinta tasone tana kaunar kawarta shi yasaka ta boye nata tsanar har saida wann abu na batun auren zach ya bayyana ta gane cewa ashe meenal din ma tanada nata shirin nadaban.

Ji take kamar lalata halisa a idanun khaleel is not enuf dan Tsoro takeji na musammn dasuka kasnace a inuwa guda.

Dan yau akace khaleel ya karanto asalin waye halisa tasani sarai babu mafaka yarta meenal zata dawo tamkar shara a idanunsa...

Wani lalatacen coffe me shegen daci ta hada wa meenal din a cup ta aje mata akan table, meenal na fitowa daga wankan itama ta shiga tay sharp sharp ta fito ta samu meenal ta zubar da coffe din akasa tana jajjan tsaki...dauke kai tay batace mata komi ba suka hau shirya kansu Hajya nadiya tana sauri sauri ta gama dan Allah Allah take ta fito ta same halisa da irin tsinanniyar shigar da tay jiya sabida plan dinta ya tafi mata dede dan bakaramin bomb yauta shirya cinnawa agidan ba

Bangaren halisan kuwa tun 8am ta farka ta hau kimtsa room dinta murna fall ranta da jin yau zata rabu da meenal da khaleel. Kayanta kaf ta shiryasu acikin jaka musammn ma wanda jasmine ta aiko mata da yaune amfaninsu ya kare agareta duk ta tarkatasu acikin box din ta kulle, iyakar bunch din cigarete dinta ne kawai tabari a jaka.

Tun tanakan aikin uztaz ya kirata ya sanar mata da sakon da Dr aseem ya turo murna kamar zai kasheta, 9 ta shiga wanka ta fito ta zauna gaban madubi ta tsarawa fuskata simple make up ta shafa nude janbaki daya sakata ta fito so natural and elegent yalo yalon suman kanta ta kamashi in a pony tail style snn ta saka gel ata gaba gaban bakaramin bata innocent look yay ba...

Wayarta ta dauka tana latsawa tayi shiru tana zaune da farin bathrobe agefen gadonta tanakan jiran shigowar uztaz da kayan ta na mutunci da zata saka ajikinta yau domin zuwa ganin doctor aseem. COMENT AND DONT SHARE.

LITTAFIN NA KUDINE NE TO JOIN US CHAT 08060712446

THANK U

Meenal nakan shiri taga wai har mumnynta ta gama saka kaya harta zari mayafi...tace mummy ina zakije haka saurin me kikeyi? Tana murmushin makirci tace Kitchen zanje na dauki abu na share coffen da kika zubar but kafin nan can you do me a favour?

Meenal ta kalleta wani iri tana danna sponge a fuska sama sama snn tace what favour??

Wani serious magana ta taho ta gaya mata a kunne can sai meenal din ta mike ta fita a dakin da wani golden key a hannunta ta haura can can sama inda ma'adanan kudadenta na gida suke wajen nada dan nisa dake bata fiye shiga wajen ba...

Meenal na ficewa hjy nadiya ta bude jakarta da sauri sauri ta dauko wata hamshakiyar kwaya ta sha'awa kusan four good tablets ta debo masu kyau aciki snn ta wuce kitchen ta juye sauran ruwan coffe dinta akan cup uku Cikin sauri ta gama ta nufi room din halisa dashi da kwayar boye a hannunta

Halisa Tana daga zaune a dakinta taji karar knocking abakin door duk ta dauka uztaz ne sai ta bada izinin shigowa kai tsaye, kafin ta gama daga ido sama sai taga hjy nadia a tsakyar dakin tana washe baki da tray din coffe a hannunta..

Mamaki ya cika halisa ta dan daga kai."Au hjy kece yau kuma da ssafen agidan nan?"

Da mamaki halisa taga yau bata zageta kota harareta ba Tana washe mata baki tace eh nice, kin ganni da sassafe ko hmm dama wata yar magana ce nazo namuku da ke da meenal, gshi naje room dinta naji shiru kamar bata tashiba ko zakije ki kirawo min ita

Being respectful yasaka halisar mikewa izuwa dakin meenal din dede lokcin khaleel ya taho gaban computersa zaiyi shuting din cameras dinsa down kenan sanin cewa amfaninsu ya kare caraf sai idonsa yagano masa ficewar halisan da bathrobe ajikinta alaman ko shirya kanta batayi ba gashi time nata tafiya

Tsiririn tsaki ne ya kufce masa yana daf zai dann button sai idanunsa ya sauka akan hjya nadiya ta zazzare idanunta kamar munafuka a dakin halisan ita kadai..

Mamakin ganinta ayanayin daya gantan ne ya tsandarar dashi dan kwata kwata baida wata masaniya akan zuwanta gidan ayau bare kuma sanin cewa ta kwana masa agida. Idanunshi da dukkan nitsuwarsa ya zuba akan cameras din yanamai lura da abunda take shirinyi ganin yadda take mika wuya tana leke leke duk alamun rashin gaskiya ya gama bayyana atattare da ita.

Kansa sosai ya daure sanin cewa basa wani jituwa da halisa infact kullum acikin kusheta takeyi tome zai kawota room din halisan yanata wondering hakan a mind dinsa, Yanadai kallonta harta ajiye cups din coffe din akan table snn ta ware hannayenta biyu ta hau fidda kwayar daya bayan daya har su hudu da wani irin speed yay capturing kan hannun nata dede kan kwayoyin Da can yana dga tsayene ahujajan ya ja kujera ya nemi wajen zama, babu bata lokci yaga ta zuba kwayar guda uku acikin cup daya, saita saka daya acikin cup na biyu ta girgizasu sosai sai cup na ukun dake kurkusa da ita bata saka komi aciki ba.

Dannen dannensa yay within some minutes yafara scanning capture din daya dauka yana kammala scanning din ya nuna masa sunan kwayar kai tsaye da wasu relevant information akan aikin sa..

Yana karantawa shikansa baisan sanda ya rike bakinshi ba...

Dan Tsabar karfin kwayar sha'awar kwata kwata rabi ake sawa a drink asha ahakan ma me karamin brain baya shan irin wann,its moslty used by drug addicts who are addicted to maniacal sex sukan sha ne dan su kwana suna cin mace basu gaji ba, ko ire iren professional rapist, ko sex trafficker lords.

marmaza yay unmuting din voice din computer dan yaji metake cewa kuma me zatay da shi..

Yaganta tana murmishi harta dauki book din halisa tana dubawa..

Jim kadan saiga halisan ta dawo cikin dakin ita daya batare da meenal ba, hjy nadia naganin hakan tahau washe mata baki, ita kuwa halisa tunda ta shigo dakin kallonta takeyi dan sosai tsikar jikinta ya tashi duk dama bata kawo komi aranta ba.

Khaleel ya mike tsaye idonsa da hanklinsa nakan su at same time yana kulle butoran rigar sa na ciki, ji yay halisa tana cewa hajy banga AMINA a room dintan ba fa..

wani wuf hjy nadian tay tanamai dafa kafadun halisan da wani irn sigar makirci..its okay halako taje wajen mijinta na

..nan ta jawo hannun halisa tana cewa okay come i made this coffe for us, ga naki nan ta dauki wanda ta zuba one tablets ta mikawa halisan na dole, daga nan khaleel ya bar gaban computer ya fito cikin sauri sauri kirjinshi na bugawa dan ko aron takalmi bai saka akafafunsa ba ya nufo hanyar room din halisan agaggauce..

Meenal ta fito kenan da damin dollar a hannunta sai ta hangeshi yana tikan sauri abun ya daure mata kai musmmn ganin datay yay hanyar dakin halisa, aggauce ta sauko Ta nufi room dinta da niyyar kai gulma da dumi dumi ma mummynta sai taga wayam babu ita..

Aje kudaden tay akan gado tafara kwalla mata kira mummy mummy can ta duro bayan gida waiko zata ganta ciki SHARE UR VIEWS AND DON'T SHARE TO GRPS DAN ALLAH MESON SIYA YA CHAT DIN 08060712446...

Daga nan kuma halisa na rike da cup din hjya nadiya sai famar lallabarta takeyi akan takai bakinta ta shanye.

Nasan kina jin yunwa bakici komi ba pls take it quick quick kafin duniya suce bantaba kulawa da ciwonki ba, drink it so that u can go and call her for me kinga aini surkuwace bazan je dakin suruki na ba, tunda suna can kuma ke patient dinsace pls go along with the other cup inkin buga kofarsu sun fito sai ki bashi coffe din ita kuma ki karawota nan kuzo tare..

Cike da rashin aminta da zancen nata halisa tajanye jikinta gefe snn tace hjy ki kirata awaya mana tazo nan se muyi maganan gaskiya nifa bazanje harcan ba am sorry but is not even proper kaje dakin miji da mata kanamai katsesu..

Cikin katseta tace Iyye kaji manyan yan bariki masu sanin laduban zaman aure..toh uban me za'a katse musu ehh ,komame zasuyi ai sun riga sunyishi jiya cikin dare ..ko kin medani bansan menakeyi bane?

Halisa ta turo baki gaba amma hajyaa ya za'ayi kice sai naje har dakin sa na bashi coffe dan kawai na kirata,..cant it wait..?

Da mummunan harde rai tace No it can't, inkuma ban isa na aikeki kije ba ne saiki fito fili ki gayamin mara kunya kawai...dama can nasan baki kallona a matsayin uwarki sam Bansan ma mesa ƴata meenal ta dauki son duniya ta dora akan macen da bata san darajar uwarta ba...

Kafin halisa tace zatace wni abu hjy nadia tay wuf ta wawusho hannunta da karfin tsiya tana cewa Naga alama ciwon nan naki yamaidake karamar yarinya ne sai anmiki dure...

cup din ta kama tana kkrin kai mata baki Ran halisa ya baci tafara turewa hjy me haka dan Allah ko kyaleni nace bazan sha bako..sai cewa take saikin sha kuma dolene kije aikana ko atunaninki ban raineki bane agabana kika tashi yarinya bazaki fi karfina ba..hawayen bacin rai harya fara cikowa idanun halisa tana kkrin danne zucyarta karta ture hjya nadiya kasa ta karya mata kunkumi, kusan kokqwa suka shigayi ta damke bakinta sam taki budewa. gashi zuciyrta yaki sam ya kwanta da coffe din, kkrin cusa mata da hjya takey ya dada sata jin bata aminta da coffe din ba.

Ganin halisa ta turje taki shan coffe yasaka takai hannunta waists dinta zata mata cakulkuli tana kaiwa halisa ta firgita tay wani irin ihu daf zata juye mata abki kenan kwaf taji anbuge cup din kasa da wani irin karfin da saida mug din ya rabe biu. Noise din ya janyo hanklin meenal agurguje tayo dakin halisa cikin sassarfa.. hjy nadia kuwa na hade ido da khaleel tay saurin sake Halisa ta zube kasa tafara kuka.

Matsancin tsoron ganin idon khaleel Yasa hajya nadiya tsadarewa bakinta na rawa rawa ta kasa cewa komi sai rarrraba idanu data farayi..

Ko tambayarsu meyafaru beiyiba yay sauri zaiyo kan halisa dake tsugune tana kuka Da sauri hjy nadiyar ta turesa ta isa gaban halisa har jikinta na rawa tafara cewa toh yanxu ni menamiki anan kike kuka neman ki tara min mutane? Oh my god Are u seriously crying dan kin gansa? Hmmm khaleel kaga sakarci ko daga cewa tasha coffee dan kar ta zauna da yunwa shine zata kama dambe dani ganin idonka sai ta hau kuka...

Haushi ya kamashi baisan sanda yay mata magana cikin tsawa ba.

Yace bangane me kika mata ba i just saw u trying to force her to take that dirty coffe nida hannuna na bugeshi kasa.

Da wani irin bari barin rashin gaskiya cikin sauri ta mike tsaye ganin yadda ransa ya baci har idanunsa sunyi jaa..

Tafara barin baki subhanallah wani coffe wani coffe..lahaula wa la kuwwata.

Kusa daf da ita ya matso Dan kar halisa taji ahnkli yana kallon cikin idonta yace coffen da kika zuba kwayar sha'awa aciki inkuma kin musanta i will call ur doter to give u the oda cup agabana in oder to prove ur innocence

Kusan karkacewa baya tay kamar zata zube kasa matsancin mamakinsa da tsoron abunda yace din shine ya turnuke atake kafafunta suka fara rawa lar lar kar

Tun bata budi baki ba Saiganan meenal talba ta wantsalo cikin dakin a rikice ta kallesu sai taji ta rude gabaki daya ganin ran khaleel ya tafasa ya kone yakai matakin no control dama kuma danyen kaine dashi in ransa yana bace, ga nan kuma alamun Guiltness kaca kaca a yanayin mummynta ta rasa meye mum dinta tayi anan din daka turketa, halisa kuma na zube akasa tana kuka dan ta mugun tsanar amata cakulkuli .

Kusan a rude meenal tace "Mummy meyafaru..

Tun Kafin ta amsa tay wuf zatayo kan halisa Khaleel yasha gabanta da wani irin miskiliyyar harara ta tsaya cak. sai cewa take cikin rawan murya halisa halisa Innalillahi halsy halisa ..halisa halisa why are u crying? Is evrthing okay? Meya faru, what...

Fixgota gefe khaleel yay cikin bacin rai yace Dont fucking ask her ask your mum what she is doing here with that poisonous coffe.

Kusan a tsandare meenal ta juya ta kalle hajya nadia lkcin tay lumi lumi da ido kamar baqar munafuka tace mummy poison kuma??? A rude tace wai meyafaru ne.

Hajya nadiya Tana daga ido suka hade idanunsu waje guda da meenal take ta fashe da wani irin Gawurtaccen kukan makirci "yeee yeee yee ohni yau na shiga uku ni nadiya daga abun arziki anzo an maidashi na mugunta...yeee yee yee

Hanklin meenal yay mummunan tashi khaleel sai kallon mamaki dayakebin hjy nadiar dashi ganin yadda take neman sauya salon zancen gaba daya

Meenal ta rikota tana jijjigata tanacewa Mummy what now meyafaru? Tell me pls

Hajya nadiya tay da fuskrta narai narai kamar wacce aka ciwa mutunci Snn ta fara magana cikin murya me tattare da kuka..

Wai dukkanku da halisan naga ƴaya na ne, coffe din nan dana hada miki shine nace bari itama na kawo mata tasha, fashewa da kukan tay, yeee yee..yee..snn taci gaba da magana tace "daga nan fa bansan meyafaru ba saiga nan mijinki ya shigo a fusace ya hau kaina da fada ya fara min tsawa kamar ban haifesa ba har yana cewa na zuba mata wani abu aciki. Inbanda renin wayo ta ina yaganni ina zuba mata abu yeee yeee yee Allah wadar naka ya lalace..yeee yeee nayi nadaman zuwa na gidan nan tana kukan tana fyace hanci kmar dagaske

...duk son danake miki ya jawomin inbanda rashin sanin darajar uwa har yaushe mijinki zai daka min tsawa, akn wani dalili..tana fadin hakan ta mike a fusace ta fita tana kuka kamar an daketa

Meenal tabi bayanta da sauri suka fita..

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull