Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 27
Cheaters club book 2 complete novel Chapter 27: Cheaters club book 2 complete novel Chapter 27. Duk dama yana Allah Allah ya bi bayansu amma bai hanashi…
3,325 words
Duk dama yana Allah Allah ya bi bayansu amma bai hanashi juyowa ya dube halisan ba. Har gabanta ya karaso ya dan tsuguna tare da mika hannu kamr zai tabata sai kuma ya fasa, wani irin sanyaya voice nashi yay cikin taushi snn yace are u okay..? Shessheka take ja ahnkli ta dago kai ta kallesa ahnkli ta gyada masa kai hawaye na sauka a idanunta, har ransa yakejin saukar hawayen nata dik dama baisan me zaice mata ba nan saiga uztaz ya shigo da bag din kayan da zata saka ahannunshi yanayin su ya bashi mamaki sosai yay musu sallama da sanyin murumya a hankli khaleel ya amsa shi snn ya mike tsaye yace masa pls make sure she get ready within 15 minute we r going to be late.
Yana fadin hakan ya fice a dakin agaggauce yabi bayansu meenal acan dakin meenal din ya same su suna cacar baki meenal ta birkice ta tutsiyeta akan ta gaya mata gaskiyar me taje yi a dakin halisan da har ta bari khaleel ya kamata..
Tafara maida mata maganan kenan sai ga khaleel ya doso wajen iya abunda kunnenshi yaji clearly shine datake rantsuwa tana cewa Wallh wallh meenal ba cutar halisa zanyi ba nide na saka maganin ne dan ta kai muku ke da mijinki kusha ku more aurenku to meyene lefina aciki da zaizo yahauni da fada kamr yarsa?
Suna jin motsin takunsa tay tsit shikuwa Ko sallama baiyi ba ya shigo ciki, kusan arazane hjy nadiya ta rufe fuskarta da tafin hannunta dan tsananin kunyar abun data aikatan dake damunta..
...meenal zatay masa magana kenan ya riko hannunta izuwa waje suka dan tsaya daga bakin kofa a mugun zafafe tace khaleel what is this..wann wani irin rainin wayone zaka dakawa uwata tsawa akan abunda bai kai ya kawo ba??? Jajayen idanunsa masu darsa fargaba ya zuba mata yanamai cewa be quiete a tsawace yace kikace bai kai ya kawo ba? For How long have she been planning all these nonsense, Dede nan hjya nadiyar ta labe tanajinsu..
Meenal ta zuba mashi ido sabida tsoratar datay Idun nata harya ciko da ruwa.. lura da hakan yasaka ya dan saussauto da muryansa ya fara mata magana da normal voice nashi..
Acikin abinda ya asalin faru be Boye mata komi ba face ta inda ya ganta tana zuba kwayar dan bayason ma susan yana da spy camera a dakin halisa..
Ita kanta meenal tasha matsanacin mamakin yadda akayi yasan komi harda sunan kwayar da amount dinta ta zuba snn yay threathing dinta da cewa in har uwarta nada gaskiya ta dauka coffe din tasha sugani
Meenal tay kifi kifi da ido tana kallonsa tarasa yadda zata fara masa bayani ita kanta she is confused dan Already hjy ta gayawa mata batun kwayar sede bata gaya mata cewa wa halisa take kkrin yiwa dure ba..
Dakyar ta iya danne zuciyarta ta fuskance shi Cmn Khaleel it must be a mistake, mum is old, she is kind of stressed nide koma miyene be kamata kamata irin wann tsawar ba, she is my mum for god sake...kai yanxu innayi ma mum dinka haka zakaji dadine?
Yace Allah ya kiyaye mama na tay wann abun and let me make on thing clear to u.. hakkin kare marar lfyata akaina yake dan haka no matter what games ur mum wanna play with her tabari tukun harse ta fice ahnnuna, all i knw is she is not helping u or me, ke ba mace bace da baki san ki gyara zamantakewar aurenki ba sai tazo ta sako marar lafyata aciki? Holding his grip tighty yace "she is too lucky dan ita din mahafyarki ce da wallh saina dauki mummunnan mataki akanta cos dis might have cause me alot on my reputation.
Kusan ihu meenal ta masa haba khaleel haba khaleel yanzu akan dan wann kuskuren datay shine kaketa masifa kamar hanjin halisan ta sata..what the fuck is wrong with u..ya ina binka ahankli zaka maidani yar iska..she was just trying to help u.
Yace help me?
Yes, tafa saka kwayar nan ne ma dan musamu kusanci da juna isnt that what u want? ure such an ungrateful fellow...
Cikin katseta da bacin rai da takaici a muryansa yace "well kigaya mata cewa nace bana bukatar temakon yarta bare kuma ita. Amina, ur body is not all i want. ba iska bane bare kice kin hanani numfashi har na damu, i can have thousands of u today in a blink if i want to bcos u aint all that inkuma hakan kike so i dare you to say it now.
Har cikin kokon ranta taji maganar tasa ya cakketa kamr kifiyar mashi, da wani irin bacin rai a muryanta tace "excuse me?..wani kake cewa haka khaleel..ohh u want me to say it so that u can go out der kana bin matan banza ko, i knw dats what ur mind is up to oloshi..to wallhi baka isa ba.
Idanunsa masu cike da kwarjini Ya juyo ya kalleta dashi cikin share ihun da takeyin, with a comanding voice yace "I do not want to come back and meet her in dis house kuma karki sake raina ya baci dake...Yana fadin hakan ya juya ya barta awajen tana tuma tana batsewa tana binshi da masifa kamr zata daga gidan.
Tin daga daki halisa takejin ihun da meenal din takeyi itade haryanzu bata gama tantance abunda ke faruwa ba.
Meenal na shiga dakinta ta sauke fushinta akan mummynta tana cewa ita take jawo mata raini da walaknci awajen khaleel dan haka tazo ta fita tabar mata gidan ryt this minute..haka hjy nadia tay fushi ta fita agidan agaggauce babu ko shiri tana kuka.
Rai abace meenal ta kammala shiryawanta itama ta wuce office dinta.
After few minutes bayan abun ya dan lafa wajajen 10.30 am Khaleel ya fito agaggauce sanye da true blue men suits da farar riga yar ciki da wata half cover shoe na gucci dik ilahirin gangan jikinshi na baza kamshin original mousuf wardi wanda ya gaurayeshi da qamshin bold rasasi daga shi sai hadadden wayarsa a hannunsa fuskarsan nan babu alaman rahama duk dakyan da kayan ta masa amma walwala ta dauke masa cakkk kamr ma baitama yin dariya a duniyan nan ba..
Gaban motarsa me taken DBX ya nufa ya bude ya shiga ya zauna aciki time to time haka yake dagawa yana duba royal oak watch dinsa dake daure da tsintsiyar hannunsa yana duban lkci.
After like 5 mint da fitowarsan sai ga nan Halisa ta fito tare da uztaz agefenta ya rike mata jakarta, khaleel tunda ya kafe ta da ido ta cikin madubin motarsa bai iya daukewa ba cikin tabe bakinsa yake mamakin yadda ta sauya shigatta da kwalliyarta atake zuciyarsa yahau nazarin mesa jinsin mata suke da tsinannen munafurci ne. Karamar Tsaki yay, Shida yake shirin kafa hujja da abunda take mishi agidan kwana biyu shine yau da zasuje gaban dr aseem din ne zata ta sauya shiga?? Ahnkli yay Kwafa aransa yanamai cewa matsoraciya kawai..
Kallonta ya dingai tana takawa ahnkli looking so calm and elegant kamar wani abu be faru da ita ba. Decent casual ne ajikinta me kafurin aji da tsada, formal coller borne shirt ne na original satin me tsantsi kalar burgendry daya wani irin fidda shape din tsayayun nonowarta, tay tucking din rigar cikin champaing golden straight skirt iya gwiwarta da wani haddden high heel na amina mu'adi shima burgendry colour exct kalar rigarta.
jakarta da uztaz ya riko kuma kalar skirt dinta sai agogon data saka smart watch baki dake stone din tsirin sarkan wuyarta akwai blck diamond stone ajiki.
Kallonsu yake ta mdubin motarsa har suka kai ga gaban motarsu dan sai yanzu ya lurada haddadiyar rolls royce sweeptail fara fat dake parke a kusa da nashi motar.
Yadda uztaz yake treating dinta kamar wata sarauniya wani abun har yana dan taba masa zuciya bude mata gidan baya Yay ta zauna cikin kankanin lokci suka doshi nisa premier hospital lagos.... Na kudine please dont share ..to subcribe chat surayyahms 08060712446 Tunda suka kamo hanyar asibitin Halisa batace komi ba,ahnkli ta jingina kanta akan kujerar motar tay wani irin shiru yanayinta na sanyi yana me nuni da alamar ta gaji da komi dake faruwa da ita.
Bata tabajin strong feeling din She wants to get away frm these ppl so badly kamar yadda takeji a yau ba..
Tunda suka dau hanyar asibitin Tunani take kode tafito filine ta gaya wa meenal din matsalarta dasu dan susan tasan komi arabu kawai kowa yay hanyarsa, ita bata damu ba koda zasu ce mata ta biyasu wani abu ne daga cikin dukiyarta a madadin tallafa mata adacan da sukayi lkcin datake matsatsin neman mafaka, a fahimtar ta da su zauna suna cutar da juna koma meye ne she is willing to give dan kar ya kasance da wata bashin alfarma a tsakaninsu nan gaba dik dama raya hakan nayi mata nauyi a zuciyarta bana kadan ba.
Silent Hawayen da ya zubo mata ta share jiki a sanyaye ta lumshe idanunta ahankli kirjinta na mata zafi sosai,cos No matter what da akwai wani bangarena zucyarta dayake son meenal talba, that love she have for her is natural badon komi ba saidan sabida Allah,taso ace meenal ta kasance mutumiyar kwarai me mutunci a idon duniya ba muguwar mace me fuska biyu ba.
For good 20yrs She loved her like her blood sister and more. Meenal was kind and generous to her da suke kanana, and dats why it hurting her too much data fahimce cewa meenal din nada wasu boyayyun hali kuma ita ba kalar macen datay tsammani bane. Yawan lokuta takanji kamar ta hadiye ranta ta mutu in ta tuna kalar munann halayyar da suke atattare da meenal da kyar ta iya shanye zafin da zuciyarta yake mata tabude lumsashun idanunta ahnkli tanamai sauke nannauyr ajiyar zuciya.
Idanuntan a bude suke sunyi sanyi kamar tana cikin nitsuwa amma ita kadai tasan kalar Kukan zucin datakeyi acikin motar..
Ata Fannin khaleel ma kusan tunanin daya shige ciki kenan, kusan dukkan wani abunda yake faruwa agidan sunakan dawo masa kansa and its just making him more tensed more confused and furious with everything.
He dont knw why yay ending up da mutanen da bai gane kansu ba, tin daga kan meenal din har halisan ya rasa gane kan bakin zarensu, deirs too much on his mind dan Auren meenal din ya kasance masa tamkr jarabawace daya rabashi da dukkan gatarsa da kwancyar hanklinsa tayau da kullum...
He misses his own family deeply and madly mamanshi da babanshi da kaninshi aliyu duk suna cikin garin lagos amma he cant be with them all the time duk sabida wann auren da yayi auren da haryau what he is gaining out of shine tashin hankli, idon shi ya ciko da ruwa tuna kalaman mahaifinsa na karshe dayace masa.." "kaje koma waye ya adora maka aure, amma ni babu hannu na akan wann auren naka...ƴa babu hankli uwa babu mutunci sune dede dakai. Inya tuna wann kalaman yakanji kamar tsine masa kawai mahaifinsa yayi ba fada kawai yay masa aranar ba. Altho he had this strong reason da yasaka yakejin baison yaje ya lallashe mahaifinsa.
Mahaifyarsa ce kawai sanyin idaniyansa sede kasancewa acikinsu yana yawan jawo ma mahaifyarsan damuwar ganin rashin jituwar dake tsaninsa da dad dinsa wanda shiyasa sam baifye son yana kai damuwarsa gidanba.
In damuwar rayuwarsa ta dameshi saidai yajeshi asibiti dashi, ko ya dawo gidansa shikadai amma bazai iya gayawa abokai ba, hakama meenal bata taba nitsuwa dan tagane halin da yake ciki ba.
Dik Ya rasa yadda zaiyi ya fara fixing rayuwarsa shidakansa kawai sai ya tarkata tunanin hakan ma ya aje agefe ya dawo kan na halisa wanda yake ganin kamar bazaifi karfinsa ba...
Acikin zuciyarsa ya dinga raya wasu abubuwanda ya fara fahimta bei bar me karatu ya gano wann sirrin ba. Dan Da can yana kokonta canza mata environment ne, amma ayanxu baijin hakan zaiyu, cos he need to find out the truth about sumting.
Ya lura rayuwar halisa da akwai abubuwa kala kala da basu bayyana masa ba musmmn tsakaninta da zach da kuma su hjy nadia, snn inhar be san wayann abubuwan ba hala bazai iya daukar hanyar kwaceta acikin halin kuncin datake ciki azcyarta ba.
Mintina sha biyarne ya kawosu cikin harabar nisa premier hospital tunda uztaz yay parking Halisa ta dan daga kai take kallon khaleel daga can nesa Lokci guda ta hango wann sauyawar san da tulin bacin ran dake tattare dashi..yana daga tsaye har uztaz ya bude nata kofa ta sauko kasa Kallo daya yay mata ta dauke kanta daga nan bai ce musu komi ba...
Wasu jakan files ne a hannun shi ya fitar ya doshi cikin asibitin kai tsaye suna binshi a baya Direct suka haura can sama inda office din Doc Aseem din yake..
Doguwar corridor ne me yalwataccen kwayayen wuta ga wani irin sanyin Ac dake busawa..
Wajen babu motsin kowa face karar Acn Isarsu kofa ke da wuya khaleel ya juyo a nitse snn ya dubi uztaz tareda nuna masa wajen zama a wani cushion dake waje daf da kofar, yace masa su zauna anan, he will send for them in few mins.
Babu musu uztaz ya amsa masa snn ya nuna ma halisa seat ta zauna
Tana zama aka bude kofar waje, nan sai ga Dr khalid bankole ya taho yana sauri sauri daga ganinsa kasan yan gulma ne suka sanar dashi cewa Halisa ta shigo asibiti.
aiki yakeyi ya bari marmaza yazo dan yaga yaya take dan kuwa saka idon zach akan harkokin sa da kasancewarta agidan magiyinsa khaleel bakaramin takamai burki yay ba.
Khaleel harya bude kofar office din De Aseem zai shiga caraf ya hango dr khalid nata sauri yana na zuwa kuwa ya tsaya yana kallonshi daga gefe...
Halisan batama lura ba tana zaune, caraf taji mutum ya fado gabanta da wani irin rawan jiki dr khalid din ta gani ya taho yanamai rike mata hannu casually da wani irin murnan ganinta a face nashi yace hi miss Halisa...oh my god its good to see u..
Murmushin bazata tay cos His happy gesture is almost infectious, duk da takwace hannunta anashi da dan sauri amma bai hana tay masa magana da tarba me kyau ba, da dan sakin fuska sosai tace..hi DR..? Whts that ur name again
Dariyar kirji yay ganin harta mance sunanshi Yace khalid..tace ohhh Dr khalid..wani janta yay ta mike tsaye yadan yi hugging dinta lighly yana cewa is soo good to see you pretygirl ya jiki?
Ta dan sake jikinta kadan snn Tace fine..
Wani jajjan ta Dr khalid din ya fara da wani irin dan iskan kallo yanata shishhige mata kamr zai cinyeta, wanda atake hakan yay annoying din khaleel to the core ahnkli ya firzan da zazzafar iskar dake bakinshi cikin kyabe baki ya wuce cikin office din Dr aseem kai tsaye.
Fannin vicky kuwa tun da ta kammalla waya da hadiza taji kirjinta na bugawa driving din ma a daddafe takeyinshi dan Allah Allah take ta isa office dinta ta zauna ta bude computerta danta turawa kayden sakon wasu files nata da gaggawa.
Hadiza ta gaya mata cewa thers been alot of competitions, mutane dayawa kuma na kai hari a wajen data samu, dadin karawa har da tawagar babban business rival dinta wato Mrs chimamanda onyeka chuku datake son taga bayanta a duniyar business din gaba daya.
Ata dayan bangaren kuwa dede gaban hadadden gate din pan athlantic unniversity Hadaddun Yan mata da samari sukayi cincirondo Tun daga gate din waje kansu nata kallon wani waje..
Vicky da already ta doso ta bakin gate da white mercedez benz dinta zata shiga sai taga student sunata kallon bayanta tun abun be darata ba harta fara tsarguwa daga bisani sai ta soma gane cewa ashe ba itadin ake kallo ba..
Wani hadadden koeniseg aqueira fancy sport car ce baka kirin irin matte black din nan daya kusa cin karo da ita tun a gate na farko aka tsaya anata kalla abayan ta, tsaki taja da tunanin cewa bazai wuce sabbin zuwan nan bane da kansu ke rawa a makaranta.
Ita haushi ma taji da motar yake jawo mata trfic duba da irin saurin datakeyi ta isa office..
Ahnkli motar ke tafiya akan titin schl duk inda ya wuce sai gayu sun ce "dammmnn" mata kuma suhau sumewar tsaye ana "wow wow" gashi tinted ce ba aganin kowaye ne aciki ba.
Wasu kywawan mata ne su ukunsu a tsaye kamar su suka kera kansu dan kyau dayan ta dafa dayan tace...
"Janis, Who ever is in that car must be the son of the president..
Ta biyun tace "No way nicole, he must be the son of a mafia.
Ta ukun tace I dont care, duk muninsa wallh saiya kulani. Cos damn he is soo wealthy duk schl din nan babu mai exotic cars kamarsa.
Hadaddun yan mata uku da ake mugun ji dasu a makrntar ke wann hirar agaban motocinsu suna tsaye daga cikin filin parking.Da karfi suke fadin hakan dan haka vicky take jiyosu tun kan ta iso..Kusan daf da gabansu tay parking Tana parking motar tan kuwa sai gashi nan ya doso yana biye da ita.
He is smooth and soo fast sabida sport car ce tunkan vicky ta gyara nata motar har cimmata Yay kamar ma tare suka iso.
Yadda yay parking nashi motar roughly daf da nata yasaka yan matan suka karajin ya mugun burgesu.
Ran vicky ya sosu bana wasa ba amma Tsabar aji daya gama ratsa jikinta yasaka ta kame kanta bata bude motar ta fito ba tana zaune a car din tana son taga wani isashen yarinya ko Yaron ne zai Fito aciki.
Nicole dija da janis sai rawan jiki suke kowacce tana famar gyara zaman nonowarta da matsatsen bombom dinta da hair dinta ana rigima ana kar kadasu..
Kusan five mint yaci snn motar tay blinking red light kafin nan murfinta ta budu, tun daga kan kafafunsa dake sakale cikin wata grey colour balenciaga booth da ya soma dorawa akasa suke kalla har izuwa kan hadadden fuskarsa data sha gyara sajen sa ta kwanfa luf, he is tall and dark shi ba fari bane but he is god damn young and handsome, asalin yanayin samari masu jini ajika yan gata yayan masu kudin gaske kuma sakaltattu wanda ake ji dasu sosai kayden yake dashi, wani irin shiga yay ta kamala, not the boyish swag u will expect to see frm a fresh young boy kamarsa yasaka white shirt me buttoran gaban adan bude da wata grey trouser me laushi ta kamfanin calvin klein.
manyan idanunsa har maiko maiko suke idan ya juyasu wani irin Sanyin nitsuwa da kamiyarsa tamkar ya hada jini da jinin sarauta. Kominshi a nitse He is so calm and collected.
Itakanta vickyn saida ta dau lokci tanata kallon sanyin kasaitar dake tafe da yanayin kayden duk dana bayau ta soma lura da hakan ba, yaron de haushi yke bata for no reason at all cos she feel like they are connected by heart sumhow..
Janis da dija kuwa atake suka yi sumewar tsaye ajikin nicole kusan atare suke cewa wowwww.. vicky ta kalle su tana jan tsaki jin takaicin su ya shakureta.
Daga zaune tafara mita tana cewa "Henry yana bawa yaron nan dama yay yawa, why wud he let him drive these fancy cars karatu yazo yi ko burge yan mata?
Kwarjininsa da wnn Calmness dinsan da nitsuwar tasa ya hana yan matan nan zuwa jikinsa dan sam baiyi kama da irin mazajen da suka saba cin karo dasu ba.
Allah Allah vicky take ya bar wajen sabida ta fito tawuce office dinta duk takaicin su nicole yasaka ki fitowa, daga zaunen ta dan lumshe idonta da zimman tana budewa zataga basu wajen dukansu, bata sani ba Kai tsaye wajenta ya doso ya tsaya ya zuba mata mayun idonsa daga cikin glass yanata kallon lumsashen idanunta yana murmushi me sanyi jin kaunarta yana me kara huda masa zuciya.