Kenza eBookz

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 30

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 30

Cheaters club book 2 complete novel Chapter 30: Cheaters club book 2 complete novel Chapter 30. Hajiya badiatu ta inda take shiga bata nan take fita ba.…

3,375 words

Hajiya badiatu ta inda take shiga bata nan take fita ba. Abun yabi ya ishe shi, bayan ciwon yay sauki ya lafa masa, daga asibitin ya kira shemau yace mata yanason ganinta amma tay burus bata yarda ta dawo gidan ba sai can da yamma kusan bayan ishai.

Lokcin ya fito daga masallaci kenan suka shigo cikin gidan tare tana huhhura hanci tana gatsine..

Tun daga babban falonsu sukaci karo da hajy badiatu na zaune fuskrta kamar bata taba dariya a rayuwarta ba, anan aka zauna yin sharia ta inda hajy take shiga bata nan take fita ba, dama can wann daman take nema da zata fidda abunda ke cikin ranta gaban idon shemau dantasan sun gaji da hqri ita akan dansu sosai.

wasu irin baqaqen maganganun ta zage ta gaggaywa shemaun babu sani babu sabo..

Kuma ba acikin balbalin masifa take maganan ba, ba akuma cikin sanyin nama ba, yin maganan take da dattako da nuna nitsuwar dayake cikin yawan shekarunta.. acikin ruwan sanyi take fiddasu manya manya

Lafuza masu cin rai da shiga jikin duk wani dan adam me busar nunfashi ita kanta shemaun sede tay hawaye dan babu inda yafi ci mata rai kamr inda hjy take ce mata

Ke ba yar uban kowa bace yikowar kashi nasan waye ubanki na kuma san uwarki ciki da bai, Dama ace bamu san asalin balbale bane da sai anuna mana farin kai ganan mahmud ki tambayesa kiji wallh nida ubansa sam bamuso ki kasance matarsa ba shine yace mana yaji yagani yanaso mukabar sa. Toh kisani alfarmar hakan ne yasaka mukayi shiri muka zuba maki ido badon kin isa ba.

kin taso gidn ubanki kina girki, kina wanki, kina kuma ibada sai auren dana ne zai sauyaki dankin raina mana wayo???? Toh Tir dake shemau..sam Albasa batay hannun ruwa ba, da can dana hadu da mahaifyarki naga tarbiyanta na dauka ke din yar mutunci ce hala zaki rikemin dana amma kincuci Uwarki shemau dakika dau rayuwar karya kika dorawa zuciyarki kina wasa da aurenki kamr ke ba yar musulma wanda iyayenta suka bata lokci wajen baki tarbiyan addinin islama ba.

Toh wallah Baki isa ki kashemin dan dana haifa ba kin yi kadan...banda ma qaddara mahmud ai ba sarar auranki bane..

Ta juya kansa shima ta wankeshi tacemai baida zuciya ya bari ya kare ya dauka akan shemau.. ..tace mai tura yakai bango tun zancen lafyarsa ake shikadai ta haifa bazata lamunci abunda zaizo ya rabata da danta kwalli daya ba

Agaban shemaun Tace masu kwana biyu ta bashi inhar bataga canji akan dabiun shemau ba duk hukucin data yanke masa karyaga lefinta yaga lefin kansa daga nan ta tashi tatafi ta barsu awajen dikkansu babu wanda ya iyayin motsi.

Kuka shemau ta dingayi kamar zata fidda ranta bawai dan nadama ba gani take lefinta ne data auri mahmd tazauna har wata gidahumar local tsohowa take mata zagin tas tasssssss...but enuf is enuf..yaune karshe!!!

Mahmud na shirin mata magana yaga ta mike tsaye kuma a mugun fizge kamar wata me aljanu ta haura sama tana shiga room dinsa ta kulle kanta ciki ta dinga kuka dan tasan dolene hanklinsa ya tashi sosai.

Tanajinshi yazo bakin kofar yana bugawa yay magiyar duniyan nan danta bude mishi suyi magana amma shemau bata tankasa ba barema harta bude masa..

Hakanan har ya gaji ya hakura ya kyaleta aciki karshenta a masallacin gidan nasu yay barci cikin damuwa da tunani.

Washe gari ana idar da sallahn fajr sassafe ya dawo cikin gidan ya nufi dakin mahaifyarsa da tsammanin zai lallasheta tay hakuri ta dena fushi amma koda yaje sai yaga itama ta tsananta bacin ranta, kwata kwata yau bata kulashi ba.

Dan gaisuwarsan ma da kyar ta amsa masa snn tun nan bata sake tanka masa ba bata kuma sakemai fuska ba, jikin shi a mugun sanyaye ya fito ya rasa abinda yake masa dadi.

Hanklinsa a tashe ya dawo wajen shemau da kyar ta kammala wayar datakeyi da alhaj shafiu kafin nan ta bude masa kofar ya shigo ciki.

Yana mata magana ko kulashi batay ba saima tsabagen baqar magana data dinga jefa masa daddaya...

A wann yanayin ya shirya yaje wajen aikinsa duk hanklinsa ba kwance yake ba da yanayin yadda yabarsu a gidan kowaccensu tahau dokin zuciya.

Abubuwa sun masa yawa aransa adan dolensa yau ya nemi shawarar Abokinsa duk dama bai mayar masa komi baa amma abokin ya jadadda masa cewa abinda ya dace yay shine ya saka shemaun agaba suje har daki subawa hajyarsa hakuri.

Wann shawarar dama tuntuni tana ransa Ynxu Babban damuwarsa shine yadda zai sako shemau agaba duba da irin izgilin data tareshi dashi da safe

Adan dolensa yay ta maza da yamma bayan ya dawo yazo ya samu bata gidan, tun safe ta fita tare da driver alhaj shafiu aka kaita aka mata visa na zuwa United kingdom akan zataje ta sameshi acan gobe.

Bai sani ba shemau ta riga ta shirya tarkon da zata kamashi dashi wanda take saka ran shine zai kawo silar rabuwarta dashi dan harga Allah bazata taba daurewa ta zauna dashi ayanzu ba, musmmn ma da uwarsa tafara saka ido akan auren nasu batason case din yakaiga iyayenta bare ajawo asata zaman auren dole agidan mahmud.

Ji take kmr in haka ya faru zata iya hadiye ranta ta mutu cos She just cant commit to him no matter what dan tafara son alhaj shafiu aranta sosai snn babu komi aranta game da mahmd din aynxu face nadaman aurensa datakeyi tun farko..

Hakanan mahmud yayta jiranta harta gama shirye shiryen tafiyarta awaje ta dawo gidan agajiye.

Bai hakura ba ya sameta a daki yahau mata nasiha wanda god knwa bama jinshi takeyi ba.. Bayan ya gama yace mata suje su bawa mamansa hakuri..

Shemau ta kalle cikin kwayar idanunsa tace masa bazataje ba ai ita aka ciwa mutunci aka zaga dan haka shi yaje yace ma mahaifyarsa tazo ta bata hakuri.

Ran mahmud da wuya ne yake baci amma data furta mai hakan saida yaji yawu ya dauke abakinsa tsabar bacin rai

Abunka da wanda bai saba masifa ba yau dayake mata masifar har muryansa na rawa rawa.

Yace mata Ki iye bakinki shemau duk abunda zamuyi dake banda kawo zancen raina uwata..

Tay banza dashi ya gama masifar ya fita yauma kusan a falo yay kwanan cikin kunci wani zucyar yace masa barinta yakeyi

Da sassafe yazo dakin ya sameta ta gama shirinta tasssss harta aika da jakarta waje an zuba matasu a motar da driver alhaj yazo daukarta dashi, ya sameta taci kwaras kamar wacce zataje gasar kyau babu komi nata a dakin face handbag dinta data aaje akan gado.

fuskarsa babu alaman wasa ya riko hannunta sukayo har waje sashen mahaifyrshi, shemau batace mai uffan ba ta bata ranta sosai.

Lkcin hjy ta gama gaiswa da hafsa daga can turkey kenan tanakan kunna turaren wuta sai ga nan sun shigo a rikirkice da juna kamar sun fito filin dambe .

Tana zaune tana kallonsu batace musu uffan ba ya dangwalata kasa a durkushe ransa a bace yace mata umarni yake bata data bawa maman nasa hakuri.

Shemau ta bushe idonta ta miƙe tsaye ta kalleshi tace wallah bazan bata hakuri ba..in kaga na bata hakuri to nima ta bani ne. Inba haka ba to zan bar gidan nan saidai ka zauna da uwar taka.

Baki bude mahmd yake kallonta dan tunda suke da ita bata taba mai irin wann tsangwaron rashin kunyar agaban mahfyarsa ba...

Idanunsa sunyi jaaa akanta yace shemau kika ce mene?mahaifyata ce zata baki hakuri ashe baki da hankli??

Tace masa eh ai uwarsa bata fita ba.. Da bori da hauka ta bangaje shi ta fuce waje fuuuuuu tay waje tana kananan maganganu masu zafi kafin ya fita daga shock din data jefasa aciki ya fito harta dauki jakarta ta fice acikin gidan..

For the first time in his life ya shigo dakin da mugun bacin rai yana ihun sunanta sai wayam baiga kayanta ba bare ita.

Da sauri sauri ya fito waje har bakin gate yana kiran sunanta, yana isowa dede bakin gate din lokcin yaga wulgawar wucewarta a wata kafurar jeep an wuce da ita tasha gilashi dauke kanta tayi danma wai karta kalleshi yabata tausayi idonshi da sukayi ja suka sauka akan deck din bayan motar yaga an rubuta A.A shafiu...haka sunan ya tsaya masa ransa batare da yasan meyasa ba.

Har ransa Yakeson shemau amma abunda tay ma mahaifyarsa yau yasaka wann karon be nuna damuwarsa akan tafiyarta sosai ba. Bai kirata ba baiyi yunkurin binta ba, Sai yabari kawai akan idan ta huce ai zata dawo mishi by then ma ya samu abunda yake so komi saiya tafi masa dadi.

Bangaren shemau kuwa daga nan babban airpot din Abuja aka wuce da ita kanta tsaye tashirya zamanta da saurayinta acan UK dan tasan mahmud bazai taba gayawa iyayenta abunda take masa ba..

Alhaj shafiu ya riga yace mata zai sakata a harka ko aikinta bata damu saita koma ba aganinta inma ta aureshi kawai irin rayuwar hadiza maitama zatayi na zamowa oga wife tayita wanka cikin dukiya da narkakken daula basai tay aikin gwamnati ba

a plan dinta shine daga anyi harkan sun samu nasara babu wani abunda zai kara hada fuskarta dana mahmud sai karban takardan sakinta daga gareshi...

***********

Bayan kwana biyun kusan kowani bangare abubuwa na tafiyane awani irin rudaddiyar yanayi, masu neman duniya sun sako duniyar agaba basaji basu gani masu neman mafita suma sunakan sakawa da warwarewa.

Mahmd ya jijirce wajen ganin design dinsa ya samu karbuwa dan ya samu kudin da zai shawo kan lalataccen alakar mahaifyarsa da shemau cikin gaggawa dan ya kimtsa aurensa da rayuwarsa.

Saidai kuma Tunda shemau ta bar gidan nasu kullum cikin masa nasiha iyayensa sukeyi hakama in babansa ya kirashi awaya haka zaita wayar masa dakai da kuma jan hanklinsa akan rayuwarsa me gabki daya dan ya nitsu yasan inda ya dosa yaji dadi sosai da mahaifinsan ya yabashi da bai bi bayan shemau akan rashin kunyar data ma mahaifyarsa ba duk dama basusan da cewa haryau yana sakawa a ranshi cewa in ya samu kwangilar can shemau zata dawo gareshi ba.

Cikin kwana biyun nan da kyar ya aje tunaninta ya maida hanklinsa gabaki daya akan harkan aikinsa

Shemau kuwa tunda ta isa united kingdom take buga rayuwarta cikin nishadi da kwanciyar hankli tama mance da caftan auren mahmud a duniyarta dan awani hadadden hotel da alhaj shafiun ya kamata ta sauka mostly suna tare da saurayinta suna hira ko suna zaga gari...

Ranakun zuba kudade a game din carlos yanata matsowa Meenal da uwarta sun gama sawa aransu zasuyi nasara dan haka yanxu dukkn hanklinsu ya raja'ane akan neman investors din da zasuyi tafyar atare dasu wanda yasaka sam basa zama.

Yanzu aiyyuka a kamfanin talba grp of companies ya fara tafiyar hawainiya dan kotaje aikin ma bata iya zama korafe korafe akan kamfanintan ya farayin yawa musmmn ma akan yadda abubuwansu suka rage kargo da daraja a idon yan kasuwa musmmn ma na kasashen waje.

Shiyasa Da zuciyarta ta zage take kokarin ganin sunyi game din nan sun same wasu kudaden da zata kashesu duka dan ta dawo da martaban kamfaninta lokci guda... TO BE CONTINUED.... SURAYYAHMS

Wani tukukin tsaki me sauti halisa taja daga kan gadon kusan shida yake bakin kofartata saida yajiyo sautinsa daga nan, saida taci kusan minti biyu akwance tana kkrin washe baccin dake idonta kafin nan ta sauke kafafunta kasa ahankli cike da kasala da saibin jiki ta fada bathrum ta watsa ruwan sanyi ajikinta snn ta fito..

Kamar yadda yay makansa itama haka tay sanda tasha ruwa me dumi sosai, sama sama ta shafa lotion just to keep her skin hydrated Sann ta shafa spray na musk muchio me zuba qamshin baby lavender a fatar jikinta, ta saka dogon bakin wandon sport kamfanin nike da rigarsa baki ta kama suman kanta sama duka snn ta dauresu kamar chuku.

Smart watch dinta da takalminta grey colour, sabida New clients masu yawan kirarta yasaka ta jona earpod a kunnenta ana neman 10 min past 6 snn ta fito ta sameshi a tsaye ya dake cikin scnds yakare mata kallo daga sama har kasa ganin yaddata cusa hannayen ta aljihu, baisan inda ta aje karar tabarta kawai take tabawa ba.

Kallo daya suka ma junansu kowa ya dauke kansa basuce makansu uffan ba, damacan in be mata magana ba ita bata fiye masa ba.

Shanye abunda ke ransa yay can kasar wuyarsa yace mata "lets go. Batace mai uffan ba ta dinga binsa abaya suka kai gaban motarsa ya bude ya shiga ya zauna snn ya bude mata taciki ta shiga ciki...

tsakaninta dashi bansan waye kirjinshi yafi na wani bugawa ba, dadin karawa da qamshin turarensu ya qamuso yake bada wani irin mayataccen qamshin dadin me masifar tada hankli...

A.C motarsa ya kunna ya barshi a low, snn yay winding up na class, tunda suka fara tafiya halisa ta maida kanta jikin mirror tanata kaallon buzzling street of lagos yadda masu sammako suke fafatawa wajen ganin sun isa wajajen aikinsu da sasssafe.

within seven minute suka iso wani quiet and serene area wanda babu yawan gidaje awajen sai sharararrun tituna da filayen wasanni, anan wajen ne dasuke gudanar da cognitive excersise dinsu sabida babu wani hayaniya snn akwai albarkatatun greeny vegetations na dogayen bishiyoyi atacan gabansa da akwai pools da ponds na ruwa ga nan sanyin iskan safiya me dadi na kadawa anan din sosai...

Sunakaiwa wajen bata san sanda murmushi me sanyi ya kwace mata ba Kallonta yakeyi harta bude motar ta sauka kukan tsuntsayen da kunnenta yakeji yasata sauke nannauyar ajiyan zuciya..

Yana kammala parking ya sauko ya sameta..

kai tsaye Ya fara gaya mata amfanin abunda zasunayi anan din Cognitive excersice atakaice anayinshi ne dan ya dedeta nitsuwarta da hanklinta waje guda.

To convince her soul to put its self back together, and to connect her mind and body tru excise da zai tura sako ma jijiyon kwakwalta dansu inganta aikinsu na yin tunani me kaifi...

Har ya gama bayanin sau daya ta gyada masa kai.

Snn suka fara 100mtr slow jogs daga wajajen bishiyoyin izuwa wajen Da pools din ruwan suke suna kaiwa suna dawowa.

Sanda sukayi kamr guda talatin tare snn ya tsaya agefe yabarta tana yi yana marking time din daga gefe..

Farko farko taji dadi ajikinta cos its make her thinks about nothing amma da sukayi talatin din nan Daga zarar ta kalli ruwan dake gabanta sai ta fara tuno da ranarda tay yunkurin kashe kanta da kuma dalilin dayasaka hakan

then She started to get tired jin abubuwa na dawo mata kanta kamr an zazzagosu sai jijiyar kafarta yafara mata alaman ya gaji.

A iliminsu na likitocin pschlogy suna kiran wann feeling din da emotional rush or E- reflux, inhar tay kkri ta cireshi aranta toh zaiyi wuya baqin ciki ya zauna atare da ita nan gaba..

Yana tsaye yana lura da yanayinta duk ya gane metake ciki shiyasa yaki ya bata hutu, she started to rember everything ruwan hawaye suka ciko idanunta suna kkrin zubowa kasa kirjinshi na bugawa har Allah Allah yake yaga tafara sauke hawayen dan ya saamun dalilin jawota off the track suyi magana, sai kwasam taji wayarta na beep beep beep bata tsaya wani neman excuse agareshi ba ta dau wayar tare da zuwa gefe tana amsawa..

Ransa sosai ya baci cos dat wud have been the perfect time da zata zama dede cikin yanayin da zai mata magana ta Kuma jishi basai sunyi hatsaniya ba..

takusa fin minti talatin tana wayan kafin can ta katse, tana juyowa taci karo dashi gabanta yay mummunan fadi da yadda taga ya mugun hade rai yana mata wani irin kallon da bai taba mata irinsa ba.. jikinta take ya bata hala wayar data amsan ne matsalar sa kanta na kallon kasa Ahnkli tace sorry, i have to pick dis"...tun bai amsa ba tazo zata bar wajen ji tay ya kamo hannunta da karfi ya dawo da ita baya suna masu fuskantan juna..

gabanta na faduwa sosai dan Jikinta ya riga ya bata akwai matsala ahnkli ta fixge hannunshi anata snn ta kallesa cikin ido tace "wann wani irin kallo ne haka and what exctly do u want from me hhun???

'yace "A talk."

Idonta a lumshe tace "i dont have time for talks..

Sautim Hmm ne ya kufce masa "I shud call u on ur phone maybe u will listen to me then..

calmy tace I am a business woman Doctor, And these calls are important to me.

Ya dada matsowa kusa da ita har suna shakar numfashin juna yace i knw,.. 'sexy girl, with the suit of wealth huhn, take that off,..what are u?

Cikin idonsa ta kalla snn tace "i am independent, "Strong, genious, succesaful super model and a multi Millionare business woman.

tsakar kanta ya kalla ya kyabe baki snn yace cud be self made or man made, so which one are u?Cos Nobody is strong witout his family..

take taji maganan ya cakketa. Ta tambaye kanta meye ke nufi???

Cikin katseshi tace I made myself. And, u knw nothing abt my family.

yace are u sure??..dan nasani cewa Ur dad got hit by a car while he was drunk, and ur mum died of blood cancer while ure 7,..And u knw u cud be a good girl by staying with ur uncle....i knw ur story!

Hawaye ya cika idonta muryanta na rawa rawa tace "that is good for you, and I do not want to be a good girl. Thank you!

shiru yay dan ya bata lokcin hatsala sosai dan akwai wani tactics da likitoci kamarsa sukeyi

Idan suna dealing da mutum me taurin kai ko girman kai kome ilimi dayawa they use to trigger him with bad words or accusations basu binshi da kalamai masu sanyi se masu cin rai da kuma zafi, Wanda ata hanyar nan ne kawai ake iya gane rauninsu dan kuwa kashi 99% na masu irin wann taurin kan zasu hatsala ne su fallasa kominsu acikin rauni dansu kare kansu.

Cikin lumshe ido da budewa yace i knw. Ur too stubborn..U dont want to be a good girl. Wann abune da kika zabar makanki aranar da kika bar gaban kawunki kika fara aiki cikin kazanta a inda ake.....

Daukewa cak numfashinta yay Cikin datsar numfashinsa tun be karasa ba tace...

"party da shan barasa?., ko a inda ake kwana da maza ayi zinace zinace? Kace nice na zabar makaina? ..

girarsa na sama adage Yace Ders no better way to say it..iyayenki sun rasu amma kina da gatan awajen kawunki toh me zai kaiki wajen? Neman kudi, ko kuma neman maza????

Muyyanta na rawa sosai tace ohhh.., and u think u knw evrything abt my life?..

yace "No i dont knw..why dont u tell me...why ure this arrogant,.defensive. U act like a good girl to ppl around you but to urself ure not..Deluded by men and fame.. after all dukiyar da kike takama dashi yanxun is not even ur own sweat baby girl.., is all built on the bid of ur self worth and dignity... thats why kika kasa rabuwa da wancan mutumin (zach) even after he used and break u, u think he wil mary a girl like u, but He just show u how empty ure when he dumped u on ur weding day, few days ago you wanted to kill urslf, bcos u saw him da wata ƴa macen irinki ko?..

Snn ynxu kuma Kinakan binshi kuna waya kullum kina kulashi and sumting is telling me he is happy seeing u get manipulated suffering all bcos of his money.

Hawayen datake dannewa ya kwace mata hawaye masu azaban ciwo da mahaukacin zafi ya fara zubo mata yarr hannunta dake dunkule da uban karfi ta bude tare da dora masa akan fuskarsa da wani irin karfin da saida yaja baya batare da ya sani ba.

Wani irin bacin rai da rauni takeji duk jikinta na bari idanunta na fiddda ruwan hawaye masu tsananin zafi Ji tadingayi kamarta harzuka ta gagaggaya masa baqaqen maganganun da harya mutu bazai manta dasu ba but she is not like him. Zatay fada akan komi amma bazata tsaya fada da mutumin da ya karance rayuwarta Abaibai ba dan ji take kamr zata bata makanta lokacine wajen masa bayanin gaskiyarta.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull