Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 31
Cheaters club book 2 complete novel Chapter 31: Cheaters club book 2 complete novel Chapter 31. Waye shi da sai ya fahimceta, shidin waye ne da zai ta gaya…
3,332 words
Waye shi da sai ya fahimceta, shidin waye ne da zai ta gaya masa labarin rayuwarta kafin nan ya yadda da ita, she dont care what he say tunda shi ba Allah bane how he think of her doesnt matter.
Tana kuka ahankli harta kammala ayyana haka aranta ta juya kanta a fixge zata koma gida yy saurin kamota ta baya
"Where are u goin?
Lumshe idonta tay hawayen ta na zuba dan bata tabajin kanta so irritated with him kamar na yau ba. she just cant believe he think this low of her da har zai kalleta a matsayin karuwa wacce ta bar gaban familynta ta fito duniya dan ta gina dukiyatta da arzikin wani ɗa namijin.
Haushi da hatsala yasaka ta juyo kansa da fusata take tureshi tana mai kai masa duka akan kirjinsa har sanda ya rike hannunta dam dam snnn ta nitsu, muryansa wani iri yace "why are u soo furious with me, is it bcos i told u the bitter truth"?
He expect yes from her teary eyes sai yaga ta kalle tsakar idanunshi tace masa "No, am furious bcos i am going to watch u regret saying dat to me doctor.
yace regret what?
Raunatattun hawaye suka kara bulbula daga idonta muryanta na rawa rawa ahankli tace masa I get ure a pyschologst, its ur job to knw ppls mental issure and emotions and treat them. Amma Inde haka karatunka ya rawaito maka akaina then i am glad to let u live it with it, cos am neva gonna defend myself to u bcos ure soo irrelavant and nothing to me.
Wani irin kallonta yakeyi tana hawaye zuciyarta a mugun karye dan baiyi tsammanin zatace masa hakan ba ko kadan.
He neva even saw guilt and weakness in her teary eyes, he just saw anger And disspontment in him datake kallonshi dashi.
ACikin fushi ta kwace hannunta anashi zata juya yay wuf zai juyo da ita hanklinsa yay mugun tashi da yanayinta..
Halisa listen..i just say this so that we can talk about it. I really want u to tell me the truth by urself Duk abunda na gaya maki abunda naji ne kuma na gani da idona ..its is only u i wanna hear it from..
Batasan ya akayi ta juya da muryan kuka me yawa ta kalleshi ba..
Kusan ihu ta masa tana cewa "You din't see anything, u just assummed the worst of me..seeing is believing but ure soo dump u dont even knw that seeing cud be deceiving too.. ...i swear ure going to regret saying this to me...
Ya tsaya cak yanata kallonta idonshi suna masu bayyana tsananin tashin hanklin daya shiga ciki musmmn ganinta a wann yanayi..ya jima yana son ya ga wann ranan amma gashi ranan yazo masa wani iri tun ba aje ko ina ba yafarajin danasanin gaya mata abunda ya fada mata yanxu...but how else wud he say it..she appear to him as rude, arrogant not easy to talk to..ta yaya zai gaya mata maganan ta inda bazai hurting dinta haka ba..
duk jikinshi yay sanyi yanajin duk be kyauta mata ba, ganinta tana share hawayenta ahankli tana gama share hawayenta fara tafiya da kafa zata nufo kan titi ta wuce gida
Binta ya fara abaya yana kiran sunanta
Bata ko amsa shi ba saida taji ya kamo hannunta tajuyo asalin zage karfinta tay ta nausheshi acikin shi har saida ya rusuna kasa damke da cikin.
Ahnkli tace mai "Don't touch me again".
Tabi kansa Taja masa hatsalallen tsaki snn ta juya aguje tabar wajen tana kuka ahankli ta doshi hanyar gida batare da ta sake kallon inda ta barsa ba.
Maganganun daya gaya mata da wanda ta gayan masa suke damunsa fiye da zafin da cikinshin yake masa, memekon yaji sanyi aransa yau dayay jarumtar confronting dinta da abunda yake ji akanta sai kuma yaji kansa ya dada kullewa zuciyarsa ta dada tsumuwa acikin matsanancin damuwar yanayin dayaga ya jefata aciki yanxu, ya jima anan a zaune a cikin yanyin da shikansa bai gane ba
Wani bangaren xucyarsa already harya fara jin nadamar gaya mata hakan,wani bangaren kuma baiya nadama ko kadan dan yasan inda bai furta wayann zafafan maganganun ba da bazai gane wani abu Aciki ba..
atleast hanklinsa ya kwanta da bata bude baki tay admiting komi gameda accusation dinsa ba dats means ders another truth to the story Wanda dolensa ne ya samosu cikin gaggawa..
Da sauri ya tashi ya shiga motarsa ya fara bin ubern daya dauketa abaya tunanin duniyar nan yayi na inda zai samo dayan gaskiyan har suka isa gate din gida kusan atare bata juyo ta kalleshi ba bare ta kulashi ba..
Tabarta ta kunna tana sha tana tafiya tana tuna yanayin kalamansa.
Bashine mutum na farko daya gaya mata bakaken magana irin haka ba amma sosai nashin yay mata zafi fiyeda yadda take tunani..
First time da megadin gidan ya gaisheta bata amsa ba kawai ta shige cikin gidan...
khaleel yanayi parking ya biyota cikin gidan agggauce domin kuwa yana da abubuwa da yawa da zai tambayeta akai mostly abunda meenal ta gaya masa..
Daf zata haura kan steps din kenan taji ya kamo hannunta ta juyo a hatsale ta kalleshi" muryansa kasa kasa yace "pls listen"..hayakin taban ta dinga hura masa a fuska tanacewa i dont want to talk to u pls ure irritating me,.. zata turashi kenan sai ga meenal tana saukowa ta wajensu da sauri sauri tana kkrin rabashi da jikinta kenan wayoyinsu suka zame suka fado kasa.. kusan atare suka kai hannu ya dauki nata ta dauki nashi tana dagowa ko dubawa batay ba ta saka wayar a aljihunta tare sa shanye hawayenta cikin sauri.
Shikuwa yana mikewa tsaye da wayar atake ya gane banashi bane duk dama komi da komi irin dayane har model din da kalar wayar...
Da sauri Batare da ta lura ba yay swiping din wayar ta budu dan kar ya shiga lock, ayayinda hanklinta ya koma kan meenal shikuma hanklinsa nakan wayar ne dan baiyi wata wata ba kai tsaye ya shiga call log dinta ya fara dubawa ahankli... SHARE UR VIEWS bfr next.....
#Love indeed speaks in volume# SURAYYAHMS FANMILY OYA TAKE UR FLOWERS❤️❤️❤️❤️ MY HUMBLE LOVE, AND EARNEST APRECIATION GOES TO ALL THE KIND AND LOVELY PEOPLE THAT TOOK OUT THEIR PRECIOUS TIME ANS EFFORT TO CELEBRATE ME YESTADAY ON MY BDAY, PLS EVEN IF I DINT ANSWER UR TEXT OR CALL, KNW DAT UR REACH OUT MEANS ALOTS TO ME...LOVE U LOADS.
*DONT FORGET TO CHECK THIS LOVELY PAGE ON TIKTOK AND IG @ MUM RAMLAT COLLECTION FOR UR TIMELESS, ELEGANT AND LUXURIOUS LAFAYAS, ORIGINAL LACES, BE SPOKE JEWERIES AND MORE...*
Khaleel yana shiga motar engr Hafez ma ya bishi ya shiga nan suka kama hanya zuwa university of lagos, acikin motar yake dan tsakura masa iya abubuwan da yake son suce in sunje, shide hafez kwata kwata bai gane komi ba amma dai yake amsa shi,isarsu lasu ke da wuya ya kira sctaryn office din basu wani jima awaje ba aka basu izinin shigowa ciki domin ganin student dean affairs din kai tsaye..
daga cikin babban office din wani Dattijon bayarbe ne zaune akan chair yasha medicated glass manya da tarin takardun makrnta a gabansa yana dubawa, ganin hafeez a office dinsa da safe ya mugun bashi mamaki.. Tun basu karaso ciki ba ya ambace sunansa yanamai musu lale marhaba da sakakken fuska..
Dn rusuna kai hafez yay cikin girmamawa snn yace Salam alaikum sir Ladipo lawal akintola ..can we come in??
da sakakken fuska Bayarben yace Wa'alaikslm cikin kwalo ido yace haaaaa Afeezz is dat you? Oya come in come in pls shigo mona..
Khaleel ya cire face cap dinsa ya rike hannu sanin cewa yarbawa nada son respect dan haka suka ma mutumin gaisuwar dattako da nitsuwa.
Bayan sun gaisa ya kallesu cikin gyaran murya" eeermm afeez i hope deirs no problem dis one dakazomin da sassafe...
Hafeez na murnushi yace no sir..babu wani prblem fa dama yar wata alfarma muke nema..
daga nan ya nuna mishi khaleel yace this is my friend. Dr khaleel, he is a pyschlogist. Dean ya kalle khaleel Nan take sukayi exchanging respecful glances tsakaninsu.
Engr Hafeez ya cigaba da cewa 'We r here to incur abt one of ur student and kuma frm his source yaji ana cewa kaine quardian dinta.
Dean ya jinjina kai snn Yace okay..Doctor khaleel pls can u explain the issure here kasan security na yaran nan duka suna hannuna ne evrything is on me ina fata ba matsala bane oo
Da sakakken fuska khaleel yace babu wata matsala sir..ni likitan sister din student din ne..which i think dazu da safe kunyi magana da ita awaya, so, ders these personal stuffs da zamu tattauna da yarinyar and it wont take us like 10 min amma nafison ace kanada masaniya akan zuwan mu tunda abune da aya shafi health na familyn su kuma yarinyar a hannunka take.
Cikin nuna gamsuwa da bayanin khaleel din dean yace Dats tru, okay.. thank u for acknwlging that part dan da wasune da saidai suje su nemeta a schl hostel suyi abunda ya kawosu su tafi bamu sani ba yana kan mita ya jawo computersa ya bude sashen student row snn yace menene sunan student din?
kai tsaye Khaleel yace Her name is grace, her sister's name is Halisa mansa.
Da mugun mamaki mutumin ya dago kai ya dada kallon khaleel, oh my god kana nufin kai likitan miss halisa ne.. Ahhhhhh u shud ave just tell me eveything da zan makashi yanxu ynxu, ai halisa tamuce dat lady is very very kind and generous May god almighty reward and lighten her paths kawai.
Sassanyar murmushi ya kufce ma khaleel bazata.
Tun baiyi wata magana ba mutumin yahau cewa Hmm thnk god ure here ooo cos Jikin grace babu dadi ciwon nan ya kusa cinyeta, gashi taki sam taje babban asibiti and she have been pressing me akan saina kira mata halisa...so how can a big woman like halisa leave her business to come and babysit her in the university yaran nan fa basu da hankli.
yanata surutunsa khaleel da Hafez suka kalle juna basu ce komi ba suka zuba masa idanu
kirar sectarynsa yayi snn hadasu da shi...pls take them to the sick bay sugan jikin grace mansa sudin bakine daga wajen halisa..
Take sctry ya amsa
cikin jinjinawa kai Dean yace Allah sarki ure wclm err..Dama nasan halisa zatay responding sakona da wuri,she is very kind and her sister have been demanding to see her tun last week sabida ciwon nan i hope tunda kazo yanzu nima zan huta
tarin magana abakin khaleel amma haka ya danne baice komi ba har Sectary ya kaisu sick bay din, dats wajen da ake aje marasa lafya da suke jinya akarkashin kulawan hukumar makaranta.
Suna shiga cikin wajen akabi dasu wajen wasu dakuna, acikin na hudu direct mutumin yakaisu tare da bude musu kofar dan su karaso ciki.
..tun daga nan suka hango grace din a kwance kmar wata mutacciya, daga ita sai blue yar din nan da ake sawa matsayin rigar asibiti,an makale mata ruwan drip a hannu..
Kallon tsaf khaleel ya mata ganin tsayinsu da yanayin jikin su iri dayane dana halisan amma ita bakar fatace snn basu kama a fuska dan tanada faffadan fuska zak irin ma mamanta mama G...
kamannin jinin nan ne kawai baiya boyuwa cikin sauki.
hafeex ya juya yana gode ma mutumin daya kawosun har sukayi sallama, Motsinsu kawai gracy taji kanta ya fara motsawa nan fa fara motsa busashen labban bakinta ahnkli wanda duk yay farau farau yay fari fatt ya kuma kankare kamar wacce ta jima bata gana da ruwa da abinci ba.
bakinta na rawa rawa cikin sarkaafaffen nunfashi take cewa "nna anty Halisa, nna anty halisa, Saida ta memeta hakan kusan sau uku cikin harshen yarensu tana wasu maganganu masu ban tausayi snn ta fara cewa pls pls hold my hand and tell me u forgive me for all the evil we have done to u.
Kan hafezx ya mugun daurewa duka suka zuba mata ido suna kallon yanayinta, kallo daya khaleel yay mata ya gane cewa ba acikin hayyacin ta take ba.
Tahowa yay bakin gadon ya tsaya akanta snn ya kira sunanta ahnkli yace "grace..can u hear me?
Kamr me aljanu ta dan firgita sai kuma ta asalin farkawa adan daburce ta kalle kyakkwan fuskaraa dake kallon nata, ahnkli tace masa Yes yess, muryanta na rawa tace pls who ..who are u sir.??
Khaleel yace pls calm down, hadiyar yawu tay yana kallonta har sanda ta dan nitsu snn yacee mata "my name is dr khaleel..i am ur sisters doctor..tanajin hakan ta firgita ta damke masa hannunsa ta mike da kyar kuma firgit cikin karfin hali kamr ba itace take kayi kamr zata mutu ba bakinta na rawa ta soma tambayarsa ko tare da halisan ne su kazo? Hawaye na sauka a idonta abun tausayi ta rikeshi dam dam dan tana matsancin son taga halisa aynxu bana wasa ba.
A matsayinsa na likita bai daukesa lkci waje calming inta ba, yabarta da tunanin cewa halisan bata da lfya ne shiyasa ta turosu wajenta.
Jin hakan yasaka ta nitsu Harta gaishesu suka mata ya jiki, kafin nan khaleel ya ce ma hafezz din yadan basu waje su tattauna.
Fitarsa ke da wuya khaleel ya tambayeta meke damunta aka bata gado a sick bay kuma mesa bataje babban asibiti agari ba.
Hawaye na zuba idonta yanayinta kamar na wacce ta gama cire rai ga rayuwa, nan tace mishi kwananta bakwai kenan anan akwance.. Dama kuma halisa ce take biya mata kudin makrnta dana Abinci duk dama basu taba haduwa ido da ido ba.
..cikin son ta boye mashi asalin damuwarta na ciwon cancer datake fama dashi tace, tay bincike ance mata wani ciwo ne ke damunta a hanjin ta amma bata gaya makowa ba snn ta kira iyayensu acan benue sunki daukar wayarta haryau da tunanin ko kudi zata rokesu itade ta tura musu sako akan suzo.
shikansa Ya lura dik wann bai dameta ba itade babban burinta shine taga halisa agabn ta koda sau daya ne kafin ta mutu tabar duniyan nan
khaleel duk ya dauka zafin ciwo ne yasa take kiran mutuwa makanta hakan yasa mammata nasiha masu shiga jiki snn ya kwantar mata hankli da maganganu masu saka nitsuwa..
tun yana maganan take kuka harya gama bata dena ba...
Tana dago kai still tace masa ya mata hanya taga halisa Ido da ido pls ta rokeshi..
Shikansa yana da manyan dalilinsa na zuwa nan din amma ganin yanayinta yasaka ya rasa ta ina ne zai fara Gashi bazai iya mata alkwarin kawo halisa ba sanin cewa halisan ma batasan yazo nan ba kuma intasani wani sabuwar draman ne.
Cikeda da son fahimtar da ita yace mata shidin likitan halisa ne kuma yanxu haka halisan is not in ryt state of mind da zata na fita shiyasa batazo ba, kawai ta gaya masa sakon inyaso shi zai isar mata. Snn Inhar halisan tace tanason zuwa shi yay mata alkwarin zai kawota nan dakansa suga juna.
Sosai furucinsa ya kara mata karfin giwa saidai rauni da zafin ciwo hade da nadaman rayuwa yasaka bata wani ja dashi ba.
kirjinshi har bugawa yakeyi ganin yadda yarinyar ta goge hawayen ta tare da taro makanta nitsuwa dantayi magana dashi...
kanta na kasa cikin rauni sosai tafara cemasa tanaso ne ta nemi gafarar halisa wa iyayenta akan abunda iyayentan sukayi da rayuwarta a baya..
cikin karantar yanayin tunaninta ahnkli Khaleel yce mata tagaya masa menene iyayenta sukayi da rayuwar halisa abaya Dan ya zafafa abun sai ace mata aiyana daya daga cikin abunda yake saka halisan ciwo yanxu.
hanklin grace sosai ya tashi dataji hakan sai kuma ta kara rushewa da wata raunatacciyar kuka me sanyi..
"I am sorry.. i knw im asking for too much. But pls you have to tell me..meyasa mutane sukacewa halisa ta gudu ne agaban uncle dinta babu dalili, or is it bcos she want to..
cikin katseshi da muryan kuka tace Bata gudu ba fa duk Karya ne wannan..
Nannauyar ajiyan zuciya ya kufce masa ahnkli cikin taushin murya yace pls tell me..what happen
babu wani bata lkci ta share hawayenta snn fara gaya masa yanayin yadda suka taso suna yan yara, tace masa Ankawo halisa gidansu while she was 8yrs old Dan babanta ya rasu tana shekara bakwai mamanta bata jima ba tabi baya. lokcin ita kuma grace din kwata kwata batafi shekara 5 ba dan haka takan iya tuna komi daya faru da suke kananan yara..
Labari tafara bashi Tun daga ranar da aka kawo halisan gidansu aka mikawa iyayenta she dint forget any details.
Tacemai tun a ranar halisa bata sake hutawa araywrta ba, dan tun aranan mama g ta fara korafi Cewa halisan zata zame musu karin nauyi dan haka aka cireta a schl aka fara turata talla akan titin kasuwanni, tun washe garin da aka kawota tana cikin danyen makokin mutuwar mahaiyfrta basu barta tay makokin ta bama.
Nan Ta bashi labarin irin dukan mutuwa dana tozarci da ake mata cikin dare, musmn ma in taje talla ta dawo da daren batay isashen ciniki ba, da kalar horon yunwa da hanata abinci da zagi na cin mutunci da tursasata da sukeyi akan saitayi karuwancin dole ta kawo musu kudi in taki su taru su daketa kamar zasu kasheta,.. tun anan ya fara sanin inda halisa ta kwaso taurin kanta..
wasu abubuwan ma grace bata iya gaya masa ba kawai a misali ta bashi amma bai iya daurewa ba idonsa saida suka tara ruwa sosai tsabar zuciyarsa ta raunatu da tausayi.
Dede part din daya matsu yajin anan ta tsaya tanata kuka tarasa me zatace masa, badon komi ba saidan tana jin matsancin nauyin tafurta masa cewa babanta ne dakansa yay raping din halisa agidansu ciki ya shigeta yace banashi ba snn suka zubar mata dashi Bayan nan Suka taru shi da mama g suka mata dukan tsiya suka koreta agidan suna masu ce mata karuwa wanda shine yay sanadiyarta barin gida tana kwana agidan rawa tana musu goge goge suna biyanta kudi a walaknce amma haka take karba dan taci tasha snn ta koma makarnta..
Dan Gadonta daya ragen kaf sun kwamushi sunyi caca dashi sun hanata komi sun tozarta ta.
khaleel yay ma grace wayon duniyan nan danta fayyace masa komi game da barin halisa gidan kawunta amma haka taki sam, sai ce masa takeyi ai babanta shine silar fitowar halisa duniya sabida yana neman yay abusing dinta sexually amma bata gaya masa meyafaru sa halisa a ranar ko ga yadda abun ya faru ba..
gani take kamar inta fada masa hakan kamar asirin yar uwanta take tonawa snn mutuncin halisan zai iya zubewa.
Hakazalika babban stigma ce agareta ace babanta ya aikata ma yar dan uwansa haka. Its already a very bad story to tell ji kawai tay bazata taba iya fayyace masa ba.
duk matsawar dayay taki gaya masa komi Sede tace masa mahaifinta ne ya cutar da rayuwar halisa snn abunda suka mata shida mamanta Allah bazai yafesu ba dan da halisa tabarsu ita kanta tasha yin munanan mafarkai akan cewa babanta tun a nan duniya zai kone da wutar azaban Allah sabida irin cin amanan maraicin halisa da sukayi..
Itama tsoron hakanne ya dada sata ta gudu tanar gida tazo birni ta shiryu snn ta nemi taimakon halisa amma halisa bata taba zuwa inda take ba sede ta mata aika..infact ita ta biya mata kudaden karatunta tun daga na scndry schl har izuwa university komi da kominta ita ke biya mata.
tay kuka harta gaji Ta daga ido tana kallon khaleel da ta lura hanklinsa yay mugun tashi jikinshi duk yay sanyi...
yanayin sanyin jiki da magiya sosai tace masa ciwonta fa bana tashi bane kawai yay kkri ya cika mata alkwarinta na kawo halisa nan gobe sabida ta nemawa iyayenta gafara.
har kasa ta rikota ta kama kafafunsa ta dinga rokonshi tanata kuka har jikinta na rawa rawa tsabar matsanancin damuwar datake ciki...