Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 32
Cheaters club book 2 complete novel Chapter 32: Cheaters club book 2 complete novel Chapter 32. Na maza yay ya daure ya dagota yanamai bata hakuri, harya…
3,363 words
Na maza yay ya daure ya dagota yanamai bata hakuri, harya bata phone numbersa. Labarin na cinshi aransa kamar karsashin wuta amma hakanan ya daure ya dauke alaman hakan akan fuskansa Adan dolensa yay calming inta kafin nan ya fito ya same hafeez awaje..
Yanayin yadda ya fito jikinshi a sanyaye ya jingina bayamsa da kofat yasaka hafeez din kallonsa...
Guy is evrything okay?
Bai bari sun hade ido ba Yace yeah i need to use the rest room.
Wata nurse ce ta nuna masa male side din yana shiga ya jingina bayansa da bango yana sauke ajiyan zuciya me nauyi karamin hawayen daya ciko idanunsa suka sauko ahnkli yabi ya lumshe idanunsa..
...ya jima baiji maganan da ya dagamai hankli ya kuma damesa aransa kamar wann ba.
"He Just cant belive Halisa went tru dis..". sosai hanklinsa yay mummunan tashi Ya rasa inama zai fara aje tunaninsa..
yafi minti goma atsaye cikin rudani tunda ya shigo jikinsa a muce take Baiyi komi ba ya kunna sink ya tare ruwa ya dinga watsawa akan fuskrsa yana sauke ajiyan zuciya har sanda ya danji dama dama aransa snn ya fito..
Yazo ya samu hafeez ya gama daga hanklinsa, suna hade ido ya sake tambayarsa ko lafya baice masa komi ba da murmushi ya boye nashi damuwar snn yace masa babu komi kawai yagaji ne kuma kansa na masa ciwo.
daga nan Hafeez bai sake gane kansa ba dan A tsatsaye sukayi sallama da Dean student affairs yanaji khaleel din yace masa zai kirashi awaya gobe..
suna zama a motar maganganun grace ya soma dawowa masa kansa yarike stiring kenan sai yaji hannunsa ya fara bari bari, hafeez dake lura da hakan a hujajan yace guy barmin driving din kawai zan iya kaimu gida....
Baice komi ba ya sakar masa wheel din ya dawo dayan seat din ya zauna..
tunda hafeez ya amshi tukin khaleel ya bata cikin shiru tareda tsunduma kansa cikin wata duniyar tunani wanda bai fito aciki ba saidai suka kai gidan hafeez din. Jikinshi a sanyaye ya nemi waje ya dan kwantar da kansa.
Maganin ciwon kai yasha ya kwanta cikin son yasaka kansa baccin dole, da kyar baccin ta dauke sa, after like 2hrs ya farka jin zucyrsa ta rage nauyi, bai tsaya cin komi agidan hafiz din ba ya kamo hanyar gidansa kai tsaye.. DONT SHARE NA KUDI NE INKUNASON KUBIYA CHAT 08060712446 salam alaikum Gud evening sisters and others. Idona yadan kumbura shiyasa jiya banyi ba but i visted the clinic today kuma da sauki in sha Allah zuwa gobe we will continue posting as much pages as we can.
*NEW COMERS SHUD CHAT ME KAR YA WUCE BY 8.30PM ZANZO NA TURA MAKU A PRIVATE*
*DOS DAT ARE SAYING AN WUCESU KO SUN YI MISSING PAGES NA BAYA SABIDA BASU SAMU SUN KARANTA BA KO MATSALAR WAYA PLS ASK OTHERS TO SEND IT FOR U NOT ME OR OTHER ADMINS*
MASU TURO SAKO DA AUDIO PLS KUDAN RAGE BANA IYA NITSUWA IN JI MOST OF THE TIME KUMA YANA CIN LOKACI Da murmushi me sanyi akan fuskar vicky ta sauka daga kan gadon cikin xcyarta babu komi face godiya datake mikawa Allah daya bata wann dama, minti sha biyar kawai take dashi dan haka ta fada bathrum tay wanka sharply ta fito ta shafa mai koina yaji ta gyara fuskarta da light make up, bata tsaya styling sumanta ba kawai ta tattarashi baya ta dauki bone straight wig cap baki me shegen tsada ta kifa akan gashin kanta ta kimtsashi tabi ta gyara gaban da original curling gels na mielle,nan da nan looks dinta ya zamo dan dede kuma natural bakaramin kyau simple looks din yayi mata ba.
Walk in closet dinta ta shiga ta zabo wasu hadaddun kaya ɗa akay mata odernsu daga thailand kwanan nan ta zuba su akan gadonta
gaban mirror ta wuce ta dasu tsaya tana kallon kanta a sannu a hnkli ta dafe kirjinta tay ajiyan zucya wanda har acikin ranta tanajin sarraƙewar da numfashin ta yakyi wajen tunanin yin zaben kalar dressing din da zaifi dacewa da ita intaje event din nan, sanin kanta ne manyan mata masu international connection da suke business na cosmetics masu ji dakansu zasu hallara wajen, she is anxious and nervous, dan bata tabajin looks dinta Wil matter alot kamar na yanxu ba, dik a tunaninta shine acan kano state inda zasuy progrm din zata hadu da ceo na kamfanin datake chatting dashi akaro na farko, and She is already crushing on him babu karya, jikinta na bata cewa ya mugun haduwa sabida yanayin aji da kasaitace dake tafe da sassanyar kalaman sa, he most be a king dan har wani Allah Allah take harsashenta akan kyan fuskansa ya zamo gskia, dan har ranta takejin shaukin son tagansan, duba da yadda shaukin kalamansa ya mamaye mata zuciya yake hanata sakat cikin bacci, mararin son hade ido dashi ya samu wajen zama na musmn acikin zuciyarta da ita kanta bata isa ta fassara manufar hakan
Kankararun kaya masu ma'ana da aji wanda basu baiyana tsaraici ta dauka cos the last thing she want os to look like an attention seeker, tana mugun son taga ta kama ajinta koma yaya ne, duk formal suits ne amma daya collar gown ce ta gucii,daya skirt din aldo bianchi, daya kuma suite me dogon wando ne na french designer zegner.
make up dinta ta dada gyarawa tayi touching kwalliyar fuskrta da light powder mai haske danya kara ma yanayinta haske da annashuwa.
Jim kadan ta kammala shirinta tsaf ta fito cikin hadaddiyar french grey zegna suits dintan mai tsinannen kyau irinta sophiscated rich ladies, yasha madaran design din botora daga wuyarsa har kan breast bone yana zuba kyalli,grey colour ne kayan dan haka da jaka da takalminsa baki ne na channel mai balain tsada kominta to match.
Tun kafin ta fito mai aikinta suzan ta shigo tafitar mata da dan karamin trolley dinta izuwa harabar gidan,for a moment vicky ta tsaya a dakin tay shiru with the feeling of.. "This is huge for her"... abune wanda batay tsammanin sa ba kwata kwata ba dan tay tsammanin zata sha baqar wuya kafin ta samu shiga wajensa duba da cewa kowa dayake irin business din datakeyi na cosmetics idanunsa nakansa ne
Daga tsayen Ta rike wayarta tana kokonton wanda zata kira ta sanar dashi game da tafiyar tata daya tason mata acikin gaggawa kuma bazata, cikin lumshe ido da budewa ta raya aranta cewa mijinta prince femi wud have been the perfect person to knw all her achievements, cikin sauke ajiyan zuciya ta bude wayartan har tay dialling lambarsa sai kuma ta katse da sauri tanamai sauke raunataccen ajiyan zucia tunawa yau satinsa biyu kenan harda dori bai nemeta ba sann baixo gida ya duba yadda take ciki ba, he left her like a log of wood wanda bata da feelings ko wani bukata ko iko,infact inba abakin nile ko lucio ba bata sanin halinda femi yake ciki yanxu.
Rolling idanunta tay cikin jan tsaki to mutumin da bai damu da existance dinka bama meyene na cusa masa kai mtsss..
Wa nile ta turawa text cewa zataje kano, irin dai hira ta shakuwa tsakanin yan uwa, sai bata boye masa komi ba, nan ta gaya masa cewa Hadiza maitama ce ta taimaka mata ta samu private email din elmario har kuma tana chating dinsa kamar da wasa gashi abun ya soma zamowa mata reality harya dorata shugaba akan babban commisioning event dinsa da za'ayi na kwana uku a kano state.
Text dinta ya shiga wayar nile dede lokcin sunakan shirya breakfast lkcin abokinsa lucio yanakan waya da femi nile baima sani ba sabida ahnkli lucion yake magana dake yanxu lucio ya mugun sabawa da femin sosai sabida yana bashi kudi kamar na banza.
nile najin karar shigar sako awayrsa ya wanke hannunsa ya dau wayar yana budewa yaga vicky ne da sauri ya Bude ya karanta sakon, murnan ganin yar uwarsa ta samu babban cigaba yasashi ambatar sunan ta karfi freaking out a bit yaje har gaban lucio da murnan a muryansa bai ma lura da wayar dake kunnensa ba yana dariya yace...mehn kaga magic din mata ko, women they are alwys lucky with male ceos, kaga fa sister vicky Ta samu wani huge oppurtunity a kamfanin elmario cosmetics the new one in singapore..
cikin kwalo ido da matsancin mamaki Lucio yace "what? Are u kidding me..aawww congrat to her, wayarsa ya fitar fili yana cewa awww brother femi shine baka bamu labari ba.
Nile ya tsaya cak yana kallonsa da mamaki he was like dama waya kakeyi...
Lucio baice masa komi ba ya saka handsfree yana jiran jin amsar da femi zai bayar
Atake Femin yay kamar yasan da zancen yafara kawo musu bayanai cewa komi tare da vickyn sukayi 100% yana sane, zancen nasa sosai ya bawa nile mamaki duba da vicky ta ce masa hadiza metama tay mata hanyar ba femi ba.
shiru yay Baice komi akai ba wanda hakan yajawo femi bai iya shan bakinsa jin sauran labarin ba..
Shi Dadajin dadi ma yay hanklinsa ya kwanta da yaji ance vicky ta maida hanklinta kan business ba akansa ba badon komi ba saidan yana son yaga yacika babban burinsa akan nile..
Saidai duk da haka rashin nemansa da rashin kirinsa awaya datakeyin nan na dan damunsa aransa badon komi ba saidan baison yaganta tana cigaba ko tana cikin walwala da farinciki inba shine zai sakata aciki ba.
dat narssicistic and selfish behaviour kusan wani dabia ne na maza irinsa which most of them Bazasuyi providing peaceful life ma mace ba amma kuma baso son suga tasameshi ta wni waje musammn ma ace tanayi ne dakanta batare da ta nemi taimakonsu ba..
Lokacin da suke zaman dadi da vicky babu kalar connection din datake so akan business dinta da bazai iya samo mata ba.
harcikin ransa yanason yaji sauran labarin yadda akayi ta samar makanta shiga wann babban kamfani batare da saka hannunsa ba, sede kuma baison su nile su fara gane cewa da akwai matsala tsakaninsa da vicky dan haryau basu san ma baya komawa gidansa ba dake yanxu wknds kawai yake zuwa yay dasu.
ta fannin vickyn kuwa batare da bata lokci ba ta kammala shiryawanta tayi waje harabar gidanta anan taci karo da wasu kankanrarun lexus guda uku da akazo dashi sun sha tinted bataga kowa aciki ba, sai da aka bude mata taga wasu mutune su biyu baturai dayan me suna james wanda ya gabatar mata dakansa a matsayin shine assistant dinta, sai dayar me suna anita ita kuma cosmtics enteprenur expert ce ,suna da saukin kai sosai dan haka bata ji dar dar nakansacewa cikinsu ba, tare dasu aka wuce da ita aiport, private plane ne yakaisu daga lagos har izuwa kano state wanda kafin isansu wasu kyafaffun motocin ne na daban suke jiransu anan din ma, sede wnn karon ita kadai aka dauka acikin wata hadaddaiyar motar daga ita sai driver sai escort dake bin bayansu har izuwa masaukinsu..
masaukinsu cikin Bristol palace hotel aka wuce dasu with tight security, sede progrm din gabaki dayansa a tahir quest palace za'ayi dan haka baqinsu da duk wani shirye shirye acan akeyi
Vicky na isa Master bed room dinta aka biyota da tarkacen abubuwan da zata bukata na gudanar da aikin kamfani, Files, da gadgets kamr su macbook, laptops da sauransu. Wani irin karramawa na musmmn ake mata tamkar matar sarki, duk da ma bata saka komi aranta ba duk a tunanin ta kodan an bata shugabancin wajen ne yasaka kominta ya zamo na alfarma..
Duk wann bashine agabanta ba babban burinta shine tay ido biyu da wanda take chating dashi, ayayin da take hutawar ne ta kira hadiza maitama suka sha hira hadizar ke dada gaya mata tay hankli sbida kala kalan mutanen da zasu halarci taron duk rivals dinta ne kuma babbn burinsu shine su shafe kamfaninta acikin manya ya zamto su kadai ake harkan dasu.
Dagata dayan bangaren kuwa kayden na kwance kan makaken gadon sa na cikakken dan gata agidansu dake banana island na lagos, daga shi sai white throbe na hutu, yau baije schl ba, almost evry now and then ya kan kira james daga kano domin ya tambayeshi lafyar vicky, bai nitsa ba sanda ya tabbata ya sanar musu cewa baison kowa yasan kamaninsa bare asan cewa shine me kamfanin and he made it clear to most expecially vicky. su duk sun dauka gwadata kawai yakeyi akan dukiyarsa daya dorata akai.
awajensa kuma hakan ba gwaji bane face wani babban hanya data budu masa na samun daman dada janye tunaninta akan mijinta femi gabaki daya. Saida vicky ta samu isashen hutu kafin Program din ya fara da opening dinner na dare.
simple black flowinv gown ta saka for the dinner event bata tsaurarawa a komi ba.
Anan ne ta hadu da few of her business rivals mrs toyin,mrs karimat da babban cikinsu very stern and greedy igbo lady wato mrs chimamanda da bata iso Kanon ba tukuna.
Ganin vicky wajen ya basu mamaki sede ko kulata basuyi ba a tunaninsu kawai batawa kanta lokci takeyi anan din babu abunda zata samu cikin harkan da suka sako agaba sanin cewa kamfaninta yaja baya..
Wajen dinner din banda gulmanta babu abunda sukeyi suna yi suna kuma jefa mata habaici musmm akan business dinta daya koma baya.
Aganinsu ko su din da suke fafutukar tashi tsaye bazasuyi risking jawota cikin business dinsu Ba bare kuma babban kamfanin na elmario da suke masa kallon babban Tudun sa'a kuma mabudin hanyar yin suna da arziki.
abubuwan da suke gaya mata masu cin rai amma hakanan ta daure ta nuna bata damu ba, kuma bata bayyana musu sabuwar matsayinta wajen ba, aranta jira take sai gobe in anzo hidima lokcin kowaccensu tana nan kafin gani zai kore ji... ********
ata fannin su halisa sai can Da yamma lis bayan sun gama yawonsu na shakatawa sun ci abinci sun dawo kafin nan jasmine take gayawa halisar cewa zata bi jirgin sassafe ta koma london dama dan ta duba jikin tan kawai tazo.
Halisa bata ji dadi ba at same time kuma taji dadi sabida Tasan bakowane abokiya bace zata iya secrificing kudinta da lokacinta domin ta taho daga wani duniyar dan tazo ta dubata.
abataso ba haka ta raka jasmine har gidanta suka suka sha hira kadan jasmine tanamai dada nutsar da ita akan abubuwanda suka tattauna dazu dik dama ta lura halisa nada taurin kai akan lamarin khaleel duk da haka she make sure to make her understand that bazata ci nasara akan jinyarta ba har sai ta bude ido akan makircin meenal snn tayi hakuri dashi..
10;30 pm na dare suka rabu da jasmine bayan sunyi sallama ta dawo gidan duk ta gaji, ahnkli ta bude kofar falo sanyi Ac me gauraye dana qamshin turarensa ta faracin karo dashi, koina yay shiru wanda inba ka lura ba bazaka ce da mutume rai zaune aciki ba, nan tasameshi a falonsa yana zaune jikin shi sanye da wata white armles shirt da blue colour thr qrtr ya nade kafafunsa innocently
Idanunta daga can masu kama dana mejin bacci ta darsa akansa lkcin hanklinsa rabi da rabi nakan system yana aiki akan project dinsa wani bangaren kuma tunanin sa dika nagakan abubuwan da yaci nasaran samun su a yaune game da ita.
Tun da sukayi magana da gracy bai samu wani cikakken sukuni aransa ba. Duk Ya rasa me zaiyi, dan juyi yay kadan sai halisan ta fado masa cikin ransa ayanayi me kashe masa gabobin jiki.
he is not sure how to contain the feeling dan akaro na goma sha babu adadi kenan yanamai sauke ajiyan zuciya me nauyi hade da karsashi, dan Kusan dk wani abunda ya shige masa duhu akanta They all came in to him at once yau a sigar da bai taba tsammani ba.
tana shigowa suka hade idanun su waje guda, yadda tay saurin dauke nata anashi da dauraren fuska yasaka wata sihirtacryar ajiyan zuciya ya kufce masa..
Wasu abubuwa masu rikita tunani ta dingaji aranta datake kallon kyaywar fusknsa jin tana bukatar duk wani hanya da kuma dalili da zai saka ta dandana masa irin zafin daya dandana mata aranta ata inda zai fahimce rayuwa.
Gabobin jikinta har wani mutuwa sukeyi ayayinda haske da kuma kyan fuskansan yake piercing cikin kwayar idanunta yanamai aika mata sakonni tare da sakar mata kasala da sacewar jiki daga tsaye.
He can't be this cute and dump at same time, hade rai tay za ta wuce shi batare datace masa komi ba harsanda tay dan nisa snn ya dago idanunsa yabi bayanta da mayun idanunshi da suke haskawa ta cikin farar gilashin dake sakale akan idanunsa yana sauke ajiyan zuciya.
irin kallon Kurilla dayabi bayanta mata har Ji tay gabanta na mugun faduwa, take jiyo muryansa cikin sanyin dakewa yace "Halisa" ..batare da ta juyo ba cikin lumshe ido da budewa tace 'what?
Ya kyabe baki, kamar zai ce wani abu sai kuma ya girgiza kai yace 6.am sharp pls. Ahnkli ya fada
itama ahnkiln tace "Anything else?
Ya jinjin akai snn Yace uhum, dan shiru ne ya ratsa wajen tana jiranshi ya furta abunda yake son furtawa amma sai shiru.
Kallonta yake koda zata dan juyo ta kalleshi ita kuma kallon nasa ne bataso, bayan ta bashi while She waited to hear him speak harsaida ta hakura dajuya mai bayan ta juyo zata kallesa sai ta ga shidin ma ita yake kan kallo..
Kusan atare suka sauke wata sihirtacciyar ajiyan zuciya cikin bude ido da lumshewa tace "I am listening. Har cikin kwayar idonta yake kalla Da muryansa me taushi cikin kyabe baki yace gud nite...
Tay saurin kwace idonta anashi batace mai uffan ba ta juya ta haura sama tana tafiya ahankli.
mamakin ganin kalar sauyi tare da tsananin shaukin tausayinta datake kallo acikin kwayar idonsa da bata kammala fahimtarsu ba takeji har ta isa cikin dakin. Bude kofar tay ahnkli tana shiga ta fada akan gadonta tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya..ta jima a kwance batare ta kawo tunanin komi ba jim kadan ta muke tay wanka ta fito
Yaudin Kamar yadda bai same nitsuwa aransa cikin daren ba itama kusan hakan ne ata fannin ta, dan kusan kwana sukayi cikin juyi da tunanin juna, sama sama baccin yake daukar ta. sai Wajen karfe biyu na dare kafin ya dauketa me gabaki daya.
Tana rufe idanunta bata jima ba taga kanta da bakaken kaya a wani babban makabarta tana durgushe mutane dayawa sun zagayesu tare da mamanta da babanta sun rike hannu suna mata murmushi ita kuma na durkushe agaban wani kabari tana zuba kasa aciki tana binnewa cikin baqin ciki da kuka.
5:am Dot ta farka a mugun razane tana haki sanadiyar wannnn mummunan mafarki datayi wanda ta rasa dalilinsa, tafi minti biyar zaune akan gadon bata iya motsawa ba, Addua tay ma iyayenta, da tunanin ko itace zata mutu tabiyosu suke nuna mata alaman hakan a mafarki, har sai can da tsoron data kwaso a mafarkin ya saketa snn ta sauko kasa ta fada bathrum tay wanka sama sama ta dawo cikin room din sanye da kakkaurar bathrobe duk da haka taji kmr tana barin sanyi kai tsaye ta rage gudun Ac snn ta zaune tsantsane sumanta ta fara bushar dashi ta shafa masa mayukan gyaran kai ta kamashi in a messy bun dede inda face cap dinta zai zauna.
bayan lotion data shafa ma fatar jikinta bata kara komi ba sai body mist da musk oils masu qamshin lavender notes da african oranges which make her to be smelling as fresh as clean air. Banda oil din hana fuska tsufa data mutsika bata shafa komi ba tabar fuskarta ahaka a natural dinshi.
pants kawai ta saka snn ta jawo bakin wandon sport na kamfanin jordan me stripes din Red colour ajiki da rigarsa me kamar t shirt amma sakakke bai mata yawa ba kuma be kamata ba ko breziya bata saka ba ta zurashi
5;45 ta fita taje kitchen tay makanta green tea ta dawo room dinta dashi tanasha tana tura text wanda zata kirasu duk ta kira sun magantu dan yau batason ma taje ko ina da wayarta bare ya zamo mata silar wani hatsaniya tsakaninta da khaleel..