Kenza eBookz

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 33

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 33

Cheaters club book 2 complete novel Chapter 33: Cheaters club book 2 complete novel Chapter 33. Ta fannin khaleel yana farkawa masallaci ya nufa har saida…

3,358 words

Ta fannin khaleel yana farkawa masallaci ya nufa har saida yay sallah ya dan Zauna yay bitan karatun qur'ani sama sama daga masjid din ya dawo gida ya hau shirya kansa shima, yau all black ya saka ajikinshi bai mixer da wata kala ba ya dauki phone dinsa 5 min to 6 ya taho kofar dakintan ya tsaya tare da kwankwasawa after a while ta fito ta same shi atsaye suka kalle junan su kowa nashan qamshi kusan yauma basucewa junansu uffan ba har suka kama hanyar field diin atarre.

suna isa babu bata lokci suka fara, tasha mamki yadda taga yau yanayi dgske bakamar can baya ba,Babu yanayin fushi ko murmushi ,but he seem to be intrestd now, Bai barta ta huta ba yana ta sakata tana motsawar dayasan zasu saka ta zamo strong and confident woman in the face of adversities.

Wasu abubuwan tanayi tana Sauke raunattun hawaye, tana kuma lura da yadda ya dauke kansa akan hawayen nata dum dama suna damunsa acikin ransa, her mind is really getting fussy and distracted now, kusan ma dakanta take kkrin dawowa da tunaninta bia hanya wanda ya kasance wani babban cigaba ne agareta da lfyarta batare da tasani ba..

jiya Cikin dare meenal suka isa capital city of south africa tare da mummynta acikin wata luxurious hotel aka kama musu suke zama, they spend the night in a bar chating about business da wasu mutane da suka kasance abokanan mummynta saidai gabaki daya nitsuwarta da hanklinta yaki sam ya dedetu da gangan jikinta

Zargi da baqin xcya irin nata sai raya mata yake cewa khaleel bazai iya kama kansa da kyakkwa kuma balaggiyar mace agidan kamar halisa ba, maganan mummynta da batason jin adacan yafara damunta aranta sosai gashi batason ko kadan mumyn nata ta gane hakan ayanyinta tasan zata zugata ne kawai tay abunda batay niyya ba.

she is really suffering in silence da tunaninsu dakyar ma take hadiyar drink dake gabanta, kuma bawai dan bata aminta da tarbiyan halisa bane, ita khaleel din ne ma bata yarda da shi ba sam sam, aganinta babu abunda namiji bazai iya yi akan sex ba musmmn ma nata daya nuna mata yanaso.

Hakanan tay dakon wann damuwar har safiya at around 7;40am wai ahaka ma tay kkri ta farka da wuri kenan tana bude ido ko tunanin sallah batayi ba ta lalume wayarta ta hau kiran khaleel din. Sau uku yana ringing ana hudun ne ya dauka wani tukikin ajiyar zuciya ta sauke masa a kunne as usual bata san me ake kira da gaishe da miji ba, kai tsaye ta fara tambayrsa inda yake wanda bai san ma'anar tambayr ba kawai amsawa yay..

Sama sama sukayi magana ganin bata da abun fada yasaka yace mata yana field ne yana aiki inya dawo zai kirata.

Tana son tay mai shagwaba da kisisinan nan irinta mata amma kuma bata iya ba, bata masan ya akeyi ba.

Bai gama rufe baki ba sai yaga kirar uztaz na shigowa Wayar tasa, katse wayar yay kai tsaye ya dauka abunsa suka gaisa a mutunce cikin minti biyar uztaz ya sanar dashi abunda ake ciki, shikansa sai yanzu ya lura da cewa halisa tabar wayarta agida ne yau shiyasa basu sameta kai tsaye ba.

Tanakan share hawaye tana abunda ke gabanta taga khaleel din ya tun karota fuskarsa wani iri...suna hade ido ta taya cak ganin yana mika mata wayarsa, yace mata Sumone want to talk to you is urgent.

yanayinsa yasaka batay masa musu ba ta karba wayar ta kara a kunnenta ganin lambar uztaz ne yasaka bata matsa gefe ba atunanin ta busines call ne, agaban khaleel din tace "hey, uztaz is evrything alryt.. dagata dayan bangaren uztaz yace "Boss u need to go to the university teaching hospital now yanzu aka kirani daga can cewa basu sameki ba. I think they have found a dead body that is related to u

wani irin sarawa taji kanta yay tace 'a dead body..? Bakinta na rawa rawa tace related to me...a lagos state university teaching hospital kuma?.

Uztaz yace student ce boss...Inaga yarinyar can ne da..

Tun be karasa Taji kanta yay hiting sai ta tuna da grace, in shock tace..oh my god its grace...lokaci guda kuma sai tafara panicking tana jefa ma Uztaz tambaya daya akan daya harya rasa na amsawa aciki ganin ta rude yasaka kawai yace mata taje wajen dakanta da gaggawa..

tana mikawa khaleel wayarsa taji kuka me yawa na shirin kwace mata, irin feeling din nan na tsananin fargaba da nadamar rashin zuwa ganin grace na nemn raunata, girgiza kanta tay hankli in a complte sober mood tanaji aranta kamr bata kyauta ma grace ba duk dama ta guje ma rayuwar grace din ne sabida batason abunda zai jonata da matsalar kawunta saya zame mata trauma a aryuwrta harynzu toh gashi grace din ta mutu basu ga juna na karshe ba..

kusan a rude ta juya zata tafi da kafa batamasan inata ta dosa ba tana juyawa taji khaleel ya fixgota ahnkli ta juyo suka hade idanunsu waje guda. Yay kamar besan meke faruwa ba Ahnkli Yace "hey, ina zakije" Hawayenta ne suka fara sauka masa akan hannu lkcin idanunsa akan nata yake aransa yanaji kamar ya karba mata kukan yay,

cikin wata Iriyar ragwbbyar murya tace masa i want to go to hospital now pls doctor, a dead body was found... Grace is..kukan datake dannewa gabansa yaki barinta ta karasa maganan dan sosai ta rude..

Ji tayi ya kamo hannunta cikin nashi sigar lallashi suna kallon junansu awani irin yanayi kalaman dake wanzuwa cikin idanun nasu kadai suke iya fassarawa, babu shiri yaji ya jata suka doshi gaban motarsa yanamai cewa lets go i will take u der. Batace masa komi ba harya bude mata gaba ta zauna tana zama ta rungume kanta cikin yanayi me saka tausayi ,

yana tukin ne amma Hanklinsa rabi da rabi nakanta suka kama hanyar asibitin cikin gaggawa.... Brown colour Flat shoe ne mai kyau marar kara daya kara haskaka kyawun smooth dark skin na fatar kafafunta ta fito sakale dashi.

a hnkli take takawa akn matakalar tana saukowa cikin saibin jiki da kasala dan tamkar wacce kwai ya fashe mata aciki haka take sauke kafafunta akan kowani step tare da saukar numfashi jin jikinta take yanayi mata wani iri a daddaure haka takejin kanta duk dama bata jin ciwo akoina.

Kaucewar ciwon kai da yawan jin gajiya dasu suke bala'in addabarta sukesa ta jin tagaji da komi kamar rayuwan ne kwata kwata baiya mata dadi sune yanxu suka sakota agaba.

da dar dar ta sauko jin yadda waje yy shiru yasata kara wara Fararen idanunta tana mai zubasu cikin sashen tana dan waige waige koda zataji motsin su Hajiy

Ganin shiru yay yawa yasa ta kara kutsowa ciki sai can ta hangosu kan wata katuwar turkish capert milk colour kalar manya manyan kujerun dake wajen suna zaune akai suna hira da kayan karyawa agabansu ga wani irin luxurious golden colour incense burner agefe na tashi da hayakin original Sandal flakes da sanyin dadinsa ya kama koina musmmn ma da Ac yake dada hurashi yanamai kama har jikin labulayen wajen

right from her eyes zakagane yadda yanayin sun yay affecting mind dinta yasakata jin sun mugun burgeta sosai, wani sanyi da sakewa ta soma ji aranta dan hafsa tana mugun son harkan gayu da tsafta arayuwnta bana wasa ba,..

Kanta ta sauke kasa tana boye sautin ajiyar zuciyar daya kufce mata ta iso gabansu da sassnyr sallama abakinta

abazata Suka juyo suna masu amsa ta da sakin fuska da murmushi me sanyi.

Bayan sun gaggaisa sun ji lafyarta Kai tsaye hajiya binta ta mata bayani snn ta gaya mata cewa nan da sati uku ne zata fara schl din sabida anje hutu fresg session ne zasu fara da ita..

Inna hajiya ta sauke boyayyr ajiyar numfashi bata sake ce mata uffan ba sanda tanemi waje ta zauna snn tace mata tna son magana da ita

..duk da nauyinsu datakeji batayi musu ba ta zauna adan rakube agefe dan duk halin da ake ciki alredy hjy binta ta zayyana mata komi.

..wani shirun minti biyu ne ya gifta a tsakanin su nan inna hjya tay gyaran murya ta juyo ta fuskan ce hafsa snn ta soma ma hafsa din magana cikin tausahiyar muryan ta wanda yy kama dana fada tare da lallami, tace mata kaf duniya babu maraya sai rago dan haka dagewa take son taga tay dan ta kwaci mutuncinta da darajarta akowani fanni na rayuwarta da cewar suna nan su zasuna dorata bisa kan hanyar samun hakan akan lkci.

Addini, Ilimi, tsafta, juriya, hakuri, iya girki, da rike darajar miji da iya kula dashi shike bambamta tsakanin cikakken mace da wacce ta rako mata.

Acewar inna hajiya su dacan ma auren kawai aka musu basu san mijinsu ba saida aka kawosu dakinshi dan haka yanayin auren da aka mata da mahmud ba dalili bane da zai sakata tay sanya wajen kintsa kanta da rayuwarta na nan gaba da zatay dashi.

Duk wani raunin da hafsa ta cusawa ranta akan aurenta mahmud saida inna hjiya ta warware mata kashi 70% daga ciki a zamansu na farko.

Tace mata qaddara ce ba komi ba, dan haka itace zata jajirce tay shaping din qaddarar yadda Allah zai ji dadi ya saka musu albarka aciki..

Inna hjiya tace mata mace itace jigon da namiji ko mata dari mahnud yake da shi idan har ta jajirce wata rana sai labari.

kaifin nasiharta tuni ya hau shigar zuciyarta ta yanaimata debi da soyayya irin na uwa zuwaga yarta datake matukar kauna da kuma jin tausayi..

Maganganun inna hajiya sosai yasata tuno da nata mahaifiyar hawaye ne suka kwace da qarfi acikin idanunta sukahau zubowa, ta tuna tunda tazo duniya tsakaninta da ita kullum nasihace

saurin share hawayen da sukekin dena zubowa tayi dan ta saurari inna hajya da kyau

A hankli harta dan samu nitsuwa, sosai ta gane cewa akwai masu kudin da sukagaji ilimi kuma sukeyin amfani da ilimin zaka samu sam basada matsala wajen muamala dana kasa dasu sam sam.

Maganganun da take mata a fayyace suke babu wani boye boye

Tunda akace mata hafsa marainiyace babu uwa babu uba Hakan yasa tahau gaya mata gaskiyar rayuwar aure a tsirarsa, Babu wani boye boye ko sakayawa straight to point take fayyacewa, in tay mata waazin sai tace toh ga abunda ya dace dake ga abunda bai dace dake ba

Snn tabi ta cusa mata jin cewa sun daukota nan ne donsu tayata yaki da maraicin rayuwarta amma badon su tallafa mata kadai ba sun san hakanne zaisaka ta dena kallon kanta a matsayin banza, kaskantaccya ko raunataccya wanda bata da gata.

da haka ta rinka karfafa mata jin cewa zatafa iya yin rayuwa mai dadi fiye da wanda take tunanin bazata taba samunshi ba

She stressed dat she must try and put her fears behind her back kuma a shirye suke da su riketa anan din kamr yar cikinsu.

Godiya hafsa ta rinka musu har tana sake sheshhekar kuka dum hawayen da suke kan sauko mata sun wanke mata fuska da alaman maganganun sun shige jikinta ta kuma ji dadin yadda inna hjiya ta mata filla filla, kusan zuciyarta a shirye yake data bi wannan salon nasu don itakanta harso take taga ta dawo kamar yadda inna hajiyan taje fada wati cikakkiyar mace data san kanta.

Alokaci kalililan taji xuciyarta ya wani cikke da shaukin hakan .

Suna cikin tattaunawar hjy binta ta umarceta da akan ta karya kafin nan su san me zasuyi acikin satin ukun nan

Bawani sha'awar cin abincin takeji ba yanayin sakewar su da ita yasa ta daure ta ci abincin fiye da na kullum.

Bayan nan hira kadan sukayi snn ta koma room dinta tanata tunani akan abubuwan da inna hjya ta gaggaya mata...

Cikin sassanyar nitsuwa da samun cikakken gamsuwa acikin zuciyarta take sauke nannauyar ajiyan zuciya

She will try and be that great woman, koda ma ace mahmud ba mijnta bane anan gaba, itade zatay kkri dai taga ta cire kanta a cikin salon matan da basu da class wanda tsabar rashin darajars maza ke iya dauke ido akansu cikin gaggawa.

Bayan kwana biyu koyaushe takan fito da safe su gaisa suci abinci yau bayan sunyi sallan ishai hajy binta tay hamdala Alhamdullhi ya kamata hafsa ta soma shiga kitchen dan itama ta koyi Abincin zamani da kyau it wll be better for now sabida babu batun xuwa makarnta ana hutu.

Inna hjiya tana murmushi tace "aiko ban dan haka bama kinsan gidan mijinta zata wuce daga nan, kamata yay in zata koma ta koma mishi da makaman yaki..Ko yaya kikagani hafsatu?

Tsabar kunya kanta ta sunkuyar can can kasa ta gyada ma inna hjya kai a hankli tana murmushi.

Hajya binta ta riko hannun surkuwanta dake tashi dakyar tace mama tashi muje room ki kwanta yau kingaji fa just leave evrything to me..

yadda inna hjy take nishi nishi dakyar tana surutan tsufa yasa dukan su sukahau dariya.

Suna mugun jin dadi aransu sukaga hafsa tana kkrin yin dariyar duk dama alamar dariyar kawai zaka gani ayanayinta bawai takan sake tayishi bane har can can.

Kafin hjy binta ta dawo ta samu har hafsa ta tattara empty dishess din dake dining ta goge wajen yayi fesss da mamaki ta shiga kitchen ta bude kofar a hankli ta shigo bata lura ba.

Samunta tay agaban sink taba wanke wanke.

Da gyaran murya hjy binta ta karaso Cikin jin kunya da tsantsar yanayin girmamata hafsa ta ja baya.

Hjy binta ta amshe aikin kitchen din dakanta tanayi suna magana tana gayamata abubuwan da zasu nayi kowani rana

Washe gari da safe hafsat ta fito dan yau wekends ne tamkar house sanitation sukeyi cikin haka ta soma janta da hirarra ki, tana dan sakata kana nan aiki miko min kaza aje min kaza goge nan share nan har hafsa ta sake jikinta daa gidan da haka da haka taci nasarar jefa kanta cikin aikin kitchen din sosai.

anan ne ma hjya binta tasoma fahimtar me ta iyada dame bata iya ba fannin abincin gayu.

Babu laifi Hafsa ta iya girke girke dayawa musamman wanda ake koya musu sabida aikin su na house girl.

wasu kuma ta iya amma bata taba gwadawa ba.

Haka hjya binta ta sakata agaba sukayi doguwar list na kyafaffun abincin da zata koya masu rai da lafiya, kama daga kan girkin abinci, izuwa grills da small chops, kai harma da drink kala ka hade da few inter continental dishes.

Bayan sun kammala da wann suka fito cikin gidan nan ma hajy binta ta hau gwada mata yadda ake yi in za'a tsaftace manyan faloka da sauran wajaje har suyi kyalli suna Baza qamshi me kama zuciya da jiki irin na isasshun mata.

Sosai hafsa ta bada hanklinta tanamai kallon Salon da hjy kebi wajen kunna incense dan ya kama waje, suna da special mopping humra da suke zubawa a floor na rooms dinsu har toilet da kitchen wanda daga ka shigo dai zakaji kamar ginin gidan ne akayishi da qamshin turare.

Kokadan hafsa batajin gajiya aranta dan abubuwane da suke mugun burgeta.

Kwana biyu abunda suka dingayi agidan kenan iyaka intan gaji a kunna mata kallon fina finai masu dadi ta dinga kallo wasu sukan sakata taji ta karu da ilimin rayuwar aure wasu su sakata jin tausayi.

Bayan yan kwanaki A gidan kowani rana musamman da safe akeyi ma hafsa kitchen classes na musammn

Hajya dakanta take shiga kitchen tana koyama mata varieties na kalolin abinci na zamani, small chops with evry delicious recipes na daidai da ajinsu na masu shi har a internet takan bibiye shafukan da suke sarrafa abunci just to learn sumtin new...

Inna hjya tay ta basu dariya kenan dan itace me judging din duk wanda aka kammalashi

Kafin sati ukun nan ya cika saiga fuskar hafsa yay bul bul ya ciko ta dadayin wani irin smooth jikinta na dawowa ahnkli

rayuwarta agidan tamkar mafarki dan bakaramin dadin zama dasu takeji aranta ba, Babu abunda ke burgeta kamar yadda ake koya mata tsafta da girki, Wasu abubuwan girkin ma anan kawai ta soma sanin cewa akwaisu kuma suna existing a duniya..

Wata rana kawai bayani hjy binta take mata na yadda akeyin abu saita kyaleta dashi, to kafin ta leko zata samu hafsa ta dage hartayishi zak koma fiye, sumtimes kuma sai inna hjya taci gyaranta kadan.

intaje gyarawa inna hjiya daki haka zata yi ta bata labarin yadda dacan suke kwalliya ma mazajensu a zamanin dacan, yadda take ganin yawan suman kan hafsa masha Allah babu irin recipe da bata bata na gyaran gashi ba.

Ana daf za'a fara azumi Yau Tun Karfe bakwai na safe hafsa ta fito kitchen din tana famar aikace aikacenta na karshe dan baifi saura kwana uku tafara zuwa schl ba.

Yaune ranar koyan abincinsu na karshe inna hjya tace mata tay local kunu kala kala one one cup, aka siyo mata hardasu cow milk, gari gero dana dawa da sauran cereals.

Bayan ta gamashi aka sake bata wasu kayan shayi kamar kala takwas kowanne tayishi shima

gefe taja tana zufa tana fifita da hannu, Hular kanta ta cire kanta babu dankwali gashinta mai cika da tsahon gaske ya bayyana ta nannade shi acikin ribbon satan kallonta hajya takeyi tana murmushi ganin yadda suman ya wani kwanto mata agaban goshinta musamman sabida hamamin turirin ruwan shayi data hada Tana kashe last tea pots ta juyo a takaice tace" mama na gama.

Hjya tace jeki kira inna hjya tazo ta gani, tace toh snn tafita.

Har iyanzu kirjinta bugu yake tana ta tsamamnin jin coments dinsu

Jiya da sukayi judging din smoothie dinta they were tough though, dan Da kyar ta samu making 99.99%..

Inna hjy na zuwa suka hau tattabawa, sai bin reaction dinsu take da kallo kirjinta na bugawa, bayan sun gama duk sun gamsu suka mata nasiha atare hjy binta tace mata ba iya abincin bane kawai nasarar mace a gidan mijinta

Halin kyautatawa da tsafta da kuma riko da Addini uwa uba sanin daraja da bukatar namiji sune mabudin samun hasken zamantakewa.

Inna hajiya tace mata kafin taci nasara a rayuwa sai ta nitsu ta san waye kanta waye kuma mijinta meyake so meye baiyaso da kuma triggers dinshi .Tace mata duk yadda akayi tay kkri ta iya kalami, dan duk dadin gindin ta, da dadin girkinta if she have no respect for her man bazata je koina a rayuwar aurenta ba.

Sosai hafsa ta gamsu da bayanansu Cikin gamsuwa da jin dadii suka mika mata wani box me dauke da kyautar abun hannu da abun wuya aciki..

inna hajya tace mata congratulations,infact Ure the best cook ive ever seen..

Wani Washe bakin bazata hafsat tayi kamar tayi cillo can sama dan dadi...

Tace nagode sosai inna hjya Allah ya kara lfya ta juya wajen hj binta tace nagode mama Allah ya saka da alheri.

Dukansu murmushi sukayi tare da saka mata albarka.

Dama wannan ajin shine karshe ko?gyada kai tayi tana murmushi sosai

Hajya binta Tayi dan jimm kamar mai shirin tuno wani abu can tace Cikin azumin nan babu wani aiki sosai dan haka daga kin dawo schl zamu na zuwa Spa. Dake duk suna sane da cewa mijinta zai iya zuwa lokcin sallah sunaso yazo yaganta cass cass

Da tsallen farinciki hafsa ta amsasu cos she is dying to becme clean itama she really want to have her confidence too kwata kwata bata kawo tunanin mahmd a duniyarta ba...PLS DONT SHARE, NAKUDI NE TO JOIN CHAT ME ON *08060712446* FOR DETAILS. Wani irin tsorata taji tay gashi nan da danbanzan nauyi da kyar Da wuya ta karasa dashi kan kujera ta shimfidasa snn tay noticing cewa yana dan numfashi..

tafi minti biyar tana kallonsa cikin rasa abunda zatayi masa gashi ruwan sama ake shekawa harda bakin kwarya...

Taje bakin kofa yafi sau goma koda ma me gadi zaiji muryantaa ya fito amma sai shiru, haka ta haura sama ta dauki wayarta duk likitan datake kira sai yace mata bazai samu fitowa cikin ruwan nan ba dan ruwan is heavy ga storm.

Tana dawowa falon tazo ta samu har hancinshi na zubda jini tsabar jikinshi yay mummunan zafi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull