Kenza eBookz

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 39

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 39

Cheaters club book 2 complete novel Chapter 39: Cheaters club book 2 complete novel Chapter 39. Yace kar ki damu zan gaya mata komai kafin na bar gidan nan…

3,348 words

Yace kar ki damu zan gaya mata komai kafin na bar gidan nan i promise..

Tace Allah yasaka inka dawo ma kuje hutu gida taga badiatu lkcin nasan an bata hutu ma.

Batare dayayi dogon tunani ba ya amsa da cewa eh ba matsala ahakan haka har suka karkare maganan ya tashi ya koma dakinsa domin shiryawa.

Bayan ficewarsa hafsa ta shigo dakim bayan sun gaisa da hajya binta tace kar ki manta ki kai masa abun karyansa yanxu zai wuce...

..Tace toh Turarenta dan fetsa sama sama snn ta kamo hanyar sashen dayake din hannunta dauke da tea flask da kuma cinnamon pancake.

She looks very sexy in trousers dake yau wando da riga ne dai dai kan cikin ta me laushi all in light pink colour har da dan hular da ta rife kanta wanda shima dark pink dinne sharara dashi duhun suman kanta kawai ake gani aciki.

Tana yin sallama da daddan qamshin turaren na ya soma tuamali.. hakan ya sa ya juyo da kyau yana bin kofar da ido har ta shigo ciki..

Wani irin sunkuyar da kai tayi gaban ta nadan faduwa gamshin turaren ta da nasa sai ya hadu ya gamutsa ilahirin yanayin atmosphere dakin da wata sassanyar qamshin dadi

Kanta akasa take satar kallonshi dan He looks so dashing casuals ya saka fari da baki na girgio armani kafarsa sanye da wata sandal Hannun sa dauke da wata shakikiyar royal oak wristwacht fuskarsa yai fresh kamar dan zamansa anan din yanayin garin ne kawai ta amshe shi sosai.

Tana ajiye dan karamin s tray din Tace ogah mahmud ina kwana... Ya amsa ba yabo ba fallasa ya tsaya kallonta

Dan shiru ne ya kifta wajen kafin nan yace hafsat??? Chak ta dakata da nazarin datake na abunda zata tarar cikin sauke ajiyan zuciya a hankali ta amsa da naam ta dago ta dan kallesa

Zama yayi abakin fankacecen gadon sa ayayinda ta rusina a kasa agefen sa..

Yace ta serving masa break fast din..

Ba musu ta mike ta dauko tray din ta ta kawo gaban sa Baice komai ba ya tsaya kallon ta tana zubawa ko rabin cup din bata kai da shayin ba yace enough ta ajiye ta dauko ta mika masa haar da pancakes din idanun sa take kaucewa don sosai take jin fargaba a duk sanda suke inuwa daya taga ya kureta da idanu.

Sai da ya kai kurbi kusan sau uku sannan ya dago ya dube ta yace Dauko min wancen abun ya mata nuni da wata brwn envelope ba musu taje ta dauka masa ta Ya amsa yace thnks Sai ya ajiye cup din akan table envelope din Ya mika mata yace idan kin tashi anan ki kaima mama

...tace toh..yayi shiru Kamar bazai sake furta komai ba yace" zanyi tafiya mai dan neesa it depends amma hala bazan dawo Da wuri ba so idan akwai matsala ki gaya ma mama zata fada min..

Tayi shiru daga bisani tace toh Allah ya kiyaye hanya..yace thanks..

Maganan schl so please behave urself bana son yawo, snn no male friends dan Allah mutuncinki zakina dubawa

kanta na kasa Tace toh zan kiyaye..Yace good!

Toh shikenn dauke abunki ki fita da shi babu jira Ta mike jiki babu kwari tattara tayi waje..

Sauke ajiyan zuciya yayi Ya jawo dan karamin troleyn sa ya fito gaba daya daga dakin

Wani irin damuwa ke dawiniya da zuciyan ta amma ta kasa bari ya fito fili Tana ji suna sallama da inna hjiya ya dau kudi ya basu sunata godiya

har kofa suka rakosa lkcin hijabi ne dan karami ajikinta yana isa bakin car dinsa hjya binta ta dau wani box na cookie datay da hannunta tace hafsa kinga na manta ki bishi dashi da sauri kafin ya fice kice masa tun jiya namasa na manta ne in bashi.

Karba tay ta biyosa har bakin motar dashi tana cewa oga mahmud cikin katseta yace wai wayene ogan naki ? Shiru tay tana wasa da yatsunta

Yace u dont knw my name? Tamasa shiru can ta gyada kai alaman ta sani yace to say it ina son ji. Ahnkli tace oga mahmud, bazata taji ya jawota kusa dashi har suna shakar nunfashin juna wani irin damke rigarsa tay tsabar tsoro batasan ma tay hakan ba

Light peg taji ya sauke mata agefen kuncinta yabita kunnenta yace in baki fada sunana ba sumtin is going to happen to u today.

Muryanta na rawa rawa tace zan fada.Yace i am running late..da kyar ta daure tace sunan ka yaya mahmud"..dariya yay sosai yace waye yayan ki? hmm toh i wll accept that for a bit amma zaki canjashi Itako Bakaramin nauyinshi takeji ba, nan ta gaya mai sakon hajua snn ta nuna masa. Yace toh bude mana ingani. ..Tana budewa yace mata taste it mana koni kadai kikeson naci, a hankli tabude snn ta kai bakinta, kirjinta na dan tsananta bugun ganin irin kallon kurilla dayake bin bakin nata dashi yace da dadi? Ta dan gyada kai sai ya matso kusa da ita daf kamar zai rungume ta, Hijabin nata ya dada gyarawa zama tana dan satar kallonsa kamar zatayi exploding tsaban bugun zuciya..

Yace inason irin wann cookies din fatan dai kin iya ko?? Tayi shiru sabida bazata iya bari yaji rawan da muryan ta yake yi ya fito fili ba. kan ta hankara sai ga sasaayar lips dinsa a dai dai saitin nata cak nunfashinta ya dauke tanajin kamar zata suma awjan Wani irin damke masa hannuns sa tayi batare da tasan tayi haka ba..ta rufe idanun ta gam gam.

A hankali yay making wani irin moves da Soft lips dinsa akan nata yana wani irin bata hot flash feeling din kisses din duk dama tasan bazai yi ba amma saida taji kamar zata saki fitsari ajiki..

Yana gamawa ya bita da sassanyar kallo kamar baisan me yayi ba..ya kare ma jikinta kallo yarinyar full option ce.

babu karya tsafta da kuma gyara yayi dan kuwa ya fito masa da full package na macen da idanunsa ke son gani ajikinta shikansa kishin abunsa yasan yanayi yanxu yana mata kallo da kima fiye da nacan datake nan a wargaje.

Yace "Hafsat No male friends... ahnkli cikin sanyin murya Tace ai kafada min yace just want make sure u heard me, kanta ta sauke kasa tanasha mamakin sa sosai aranta dan batasan haka maza suke ba.

dacan dai tasan hala tausyinta kawai yakeji amma yanxu dayaga ta wanku tay fess tay wayo then he automaticly bcm more protective of his space, Kodan yasan bazata sake ganin sa bane oho, Nan Ya juya ya shiga motar kamar bai damu ba ya ja ya rufe ana juyawa da shi ya sa ido yana kallonta har sai da ta lume sannan ya dawo ya sauke ajiyan zuciya,..

Tun bayan tafiyarsa take jin kanta wani iri aranta kamar she's missing him already wani karsashi ne azuciyan ta wanda itama bata san na miye bane

Haka ta shirya zuwa schl ta daure fito falonsu Ta shigo ta same hjy binta tana zaune da bunch na kudade agefen ta.

Da tayi tunanin kawai ta bata abubuwan ta amma tasan hala akwai dalilin daya sa bai mika mata

Tace har ya tafi ko? Ta gyada kai adan sanyaye tace kema sai ki saka himma yanzu zaki tafi shl

Tace toh ta snn fita..

After few hours.

Hafsa taje schl ta dawo jikinta na dan tashin zazzabi sabida surutun datasha shi a schl wajen su yasmine akan batun aurenta, suna hirar ne da mamaki amma basu san dada cusa mata tunanin mijintan kawai sukeyi ba, hakuri ta babbasu tace musu auren nasu na hadine shine kawai ta kashe musu baki.

Anxiety data ganji yasaka period dinta yazo mata da yawa kuma bazata tana cikin wnn yanayin iarnnd 11pm in the night sai ga hajiya binta da waya tana zuwa ta dan makela mata a kunne.. Tace yi magana Mahmud ne, gabanta taji yadan fado ta dan mike zaune,

Sai yanzu ta tuno ashe dazun hjy binta tace mata mahmud ya aje mata kudaden kashewa da duk dan abunda take bukata tasan lallaine sai tayi masa godiya..

Dan shiru tayi har saida hajya tabar dakin snn tay masa sallama tace Ina wuni jin bai amsa ba tayi saurin cike gaisuwar da yaya mahmud din

Kamar yana jira ta cikan kuwa Yace lpya ya schl din tace fine alhamdull Tace dama ..uhmmm cewa zanyi nagode..

Sai da ya lumshe ido yana jiwo uneseness dake tafiya da nufashin ta snn Yace ok bazaki tambaye ni na isa lpya ba? Batasan sanda ta dan shagwabe murya kamar zatayi kuka ba tace kayi hakuri tayi shiru kadan can tace ka isa lpya? Yana murmushi Yace "Lafiya, but im tired zan yi bacci, i wll call you back again ko..Ta gyada kai tare da cewa uhmmm itama..Yace toh gud nit. tace ba waya ta bane zan kai mata ..yace ok me nace, tace kace gudnite ..dama abunda yake jira tace masa kenan yay karamin murmushi Ya katse wayarsa..kallon wayar tadingayi can sann ta yi murmushi me sanyi ta tashi da kyar ta kaiwa hajiya binta wayarta a daki.

Bayan nan bai sake kiransu ba dan har dan zazzabin kwana biyun nan sai da tayi bata fara zuwa schl ba sai da tay 2 days snn ta dawo normal da activities dinta.

*********

Ata dayan bangaren kuwa rayuwar victoria da secret boss dinta Kayden ya sauya gabaki daya ya zamo wani abu daban duba da yanzun bata da wani sauran shauki akan mijinta femi, rayuwarta kawai take zubawa ta inda zai kawo mata farinciki da nishadi shiyasa ma bata damu da komi ba.

Tun bayan abunda ya faru tsakaninta da femi data zo ta nitsu they had a deep conversation da kayden a chat ranar tun da yamma suka fara magana har tsakiyar dare and its all about ther lives, irin dai random hira na rayuwa, saidai she was suprise dataji yadda ya nitsu har ya fahimce kalmominta ya gano wasu matsalartan lkci guda kamar yadda take fama da boyayyar depression da kuma lonelines da wnn weight din betrayal din dake zucyarta da femi ya lakaba matashi...

He ask to be her friend officially. They spend time talking abt it, kafin nan tazo ta amince, so After she accepted.. in the morning irin da sassafen nan aka buga musu gate then she got a huge gift of bonquet of gifts with dollars in it frm him.

wani irin kinky and petty soyayyar gayu masu kudi da bata taɓa tsammanin a age dinta zata samu irinshi ba ta soma gani..

Sosai hakan yake sace mata zuciya dan wani abun yana sakata taji kanta so young and special, tana ganin gift din ta turomai sako, the conversations start with banters, a wasa Ya fara gaya mata how he can spend on her..

Duk ta dauka wasan ne face saida ta soma ganin yaana mata abubuwa a zahiri kawai abunda yake katse mata jn dadin nata shine da haryau bata san shi a fuska ko taji muryansa ba.

He startrd to give her alot of attention to the point that tafara amincewa dashi, inta tuna baqin cikin femi tasha giya ranar toh she will tell him her marital issures few of it, She ask him weda he gats a girl yace mata da batay aure ba she wll be his first girl kuma be damu yanxu ba If she wll like to date him..

Batadai bashi cikakken green light ba amma bakaramin shakuwa sukayi da junansu ba dan kuwa fiye da yadda femi yakan iya kashe mata kudi shima hakanan yake spoilng nata da kudi sedei nashi salon daban ne, dan kuwa ko awasa tace tana son abu toh washe gari zai aiko mata dashi komim girmansa gashi bei taba kuskuren tambayarta nudes dinta ko wani abu na zubar da mutunci da zai nuna alaman yaudararta yake sonyi ba.

Tun bayan rabuwarta da femi rayuwarta yay wani irin dadi da sauki, they are engrossed soo much in love bombing. Yana ta son ya bayyana mata kansa sarari amma kuma yana tsoron ko kawai tana bashi lkci snn ta na nuna mai soyayyan ne dan ta rasa mijinta femi,

Hakan yasakashi cikin damuwa dan baison garin bayyana mata kansa yazo ya rasata na har Abada, daga karshe wajen baban sa ya nemo shawara dake baiya boye ma baban nasa komi baban yace masa hanya daya kawai ake gane soyayyar mace according to the law of phsycology and human nature, idan kana son kasan mutum yana sonka da gaske ko baya sonka, kabari sai kuna tsaka da soyayya sai ka janye komi ya neme ka ya rasa for sumtimes shikansa he wll figure it out weda the feelinng is true or not and wat is meant to be wll alwys be.

Baida choice hakan yabiye ta babanshi, dan yana matukar kaunar yaga ya bayyana mata kansa akan lkco, Saida ya bari shakuwar tasu ya shigeta sosai then he disapper until she felt it so badly,.. yau kusan sati guda kenan babushi kuma har yanzu bata san inda zataji labarinsa ko ta samesa ba hakan yasaka bakaramin cikin damuwa vicky ta shiga ciki ba.

***************

Bangaren Femi kuwa tun bayan rabuwarsa da vickyn baida wani abun yi sai dai yaje shi gidan abokai ko yaje wajen chief okoro, yana gama yawace yawancensa ya dawo lagos ya sauka a gidan nile yay shame shame yana foaming sickness, haka zaita ɓari yana birgima da dare ana rireikkiesa kamar me jariran aljannu just to sleep in his room domim ya samu daman taba mai jiki, and hugging him in the name of high fever

abun ya fara isan Nile ranar ya tashi da safe ya bashi drugs da tea yace masa lallai suje asibiti kawai a dubasa ko akai sa therapy. Femi najin haka ya susuce a Take take ya sauya fuska ya fara kawo wata magana na daban, saying he just wants him to be free with him, saidai duk iya dadin bakinsa bai ganekan nile din ba he even tried spending several wknds exposing himself to him amma shiru harya gaji ya fara jan abokinsa lucio ajikinshi sosai a tunanin sa in suka saka lucio a harkan zai musu saukin jawo nile ciki... If u dindt see me pls dont panick is a busy week ahead. #SURAYYAHMS

Montcalm royal london house 5-star luxury hotel ne dake zaune daram a tsakiyar garin united kingdom Kusa da filin finsbury square wanda daga nan kuma tafiya kadan zakayi ya kaika har cikin moorgate underground station.

Wajajen motsa jiki, dakin gyaran fata da wajajen shakatawa dana cin abinci kai hatta rooftop restaurant akwai wann hamshakin hotel din.

Kimanin Dalar amurka dari biyu zuwa dari uku ake kashewa akan kowani kwana daya tal wanda a kudin najeria ta yanxu zai kama kusan Dubu dari uku zuwa dubu dariya biyar wanda badon komi ake biyan wnn maqudan kudin ba sai dan sabida harkallan su ta manyace, suna da stylish bedrooms dinsu na zamani da abubuwan dake ciki na more rayuwa

Yau watan shema'u biyu kenan a wann kasar amma acikin wann hamshakin hotel din take zama tana baza life tana kuma holewa, shiyasa koda acikin wasa bata taɓajin tana son ta kalle baya ba bare ma ta tuno da wani abu waishi auren mahmud dake yawo akanta.

Kusan dukkan wani abunda take so a duniyarta ta sameshi wajen saurayinta ALHAJ shafiu, Ga soyayya, ga ruwan kudi ga rayuwa mai cike da kyale kyalen duniya azagaye da ita, kusan babu abunda takeyi anan kasar face juyi cikin nishadi da more rayuwa cikin jin dadi....

kullum suna tare dashi suna holewa suna kuma yawon bude ido agari izuwa yanxu shemau ta masifar amincewa dashi dari bisa dari sabida duk tsananin soyayyar nan tasu basu taɓa kaiwa ga yin wata harkallan sex tsakaninsu ba saidai ayi taɓe taɓe da shafe shafe.

Saidai tun bayan sallah Abubuwa suka fara sauya musu dake an riga an saka ranar gabatar da contract previews din da suka ci burinsa a london wanda tamkar birni ne a cikin UK din da suke zaune acikin ynxu.

Tunda aka fara wann shirye shiryen shema'u take cikin yanayin ɓarin jiki da zumudi dan kuwa alhaj shafiun nata yariga yagaya mata cewa tasha kuruminta ta cigaba da hutawa kusan komi shi zai musu in maqudan kudin ya sauko kuma hamshakin aure zasuyi kalar wanda ba ataba irinsa a nigeria ba snn ya maidata sarauniya.

Alkwawuran kyale kyalen duniya da mutumin yay mata izuwa yanxu ita kanta bazata iya tunowa da wasunsu ba, bakomi ke rudarta ba face sake mata kudaden dayake yi tana danashanta dasu kamar wanda baison su.

Yanayin yadda rayuwa ya kasance musu kenan har izuwa yanxu da sauran baqi suka soma hallarowa domin fafatawa.

Acikin baqin kuwa har da mijinta mahmud daya iso kasar london din da wuri ya kama hotel dinsa kusa da inda za'ayi hidimar ita kuma da saurayinta suna can UK ranar gasar suke saka ran tahowa filin gabatarwa.

Tunda ya kasance musu saura sati hudu aje filin gabatar da project saiya zamto kowani enginer da dan siyasa kansa ya dau dumi babu lkcin wasa ita kanta shema'un ynxu holewarta kawai take ita kadai dan bata fiye samun lkcin alhaj shafiu a wayann kwanakin ba.

All her tots was yana musu shige da fice ne dan kominsu ya zo musu da sauki gashi yace zai sakata acikin harkan idan komi ya samu tazo hannunshi, tun zuwan su nan ya tabbatar mata da cewa babu tantama shine zai samu wann project din sabida kaf mutanensa nacikin alkalan hidima Hankllinta a mugun kwance take rayuwa aganinta rana kawai suke jira da zaa damka musu project din a hannunsu babu wani tantama tsabr ta aminta dashi ko sau daya bata taɓa duba jerin sauran engners din ba bare ma tasan ko mahmud zai samu shiga ciki.

Ayayinda mahmud din ke shirinsa a birnin london da zimman kawo karshe ma matsalolin rayuwar aurensa dana iyayensa

Shema'u anan kuma yan kudaden cikin acct dinta take ta kashewa tana zuwa wajajen bude ido da siyayyan kayan duniya da sukafi karfin arzikin ta, yo babban arziki zaizo musu ita da saurayinta kwanan nan shiyasa bata damu da yawan wanda take kashewa ynxu ba.

Tun daya shiga hidima ta zamo bata da aiki sai daukar wanka da yawo acikin motocinsa tana zuwa shoping agari

kayayyakinta dana nan dana gida duk tay kasafi wanda zata kyautar dasu sabida tsarin rayuwarta gabaki daya zata sauya ya dawo irinna hadiza maitama koma fiye dashi

She made a long list of the cars, the houses and the luxury datake son ta mallaka ita kanta dan rayuwar hadiza maitama kusan shine mata tamkar madubin dubawa.

** Ata daya bangaren Bugun Sautin Wakar sa'adu bori aka kunna wata hamshakiyar dattijuwa tana tikar rawa cikin hayagaga tana kuma rausaya kanta dake kaduwa kamar tsohowar kadangariya.

chan ta kunna hayakin tsadadden tabar nan na marlboro ta bula masa wuta tana busa shi yana fadada hayaki da gayya tana hura hancinta ita kadai tana huci tana kuma yatsinawa ...

Wani katoton Samsung laptp ne agabansu ta dauki pen dinsa tana rubutu aciki da alaman tracking ranakun da za'a gabatar da hidiman project din nan itama takeyi..

Tun daga ranar da za'a gabatar da bikin project din ma wanda suka ci nasara har izuwa sati guda dake bayansa ta ja ma ranakun jan layi da pen din hannunta. Tana yi tana busa hayakin tabarta ajiki daga ganin fuskarta kasan babu mutunci a lamarinta kwata kwata.

Dayan hamshakiyar matar dake gefentan ma kusan abunda takey kenan da alama abun ya shige ta giya mai zafi ta kwalkwala a wine glass shima ta masa zuka daya sanda taji tayi nak.

suna cikin hirar abubuwan dake gabansu aka kira babban cikin sun a awaya, dacan kamar bazata dauka ba sai can snn ta dauka muryanta a mugun dake tace fadi abunda yake tafe da kai ina jinka. Snn ta jefa wayar a handsfre ta aje musu ita da yar uwarta sunajin muryan me magana.

bayani aka hau yi mata dalla dalla cewa tun data tafi kasar dubai business ake ganin mijinta Alhaj shafiu ta da wata mata a hotel.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull