Kenza eBookz

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 69

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 69

Cheaters club book 2 complete novel Chapter 69: Cheaters club book 2 complete novel Chapter 69. Tace zata maida mata kamfanin amma meenal tace sam bata so,…

1,292 words

Tace zata maida mata kamfanin amma meenal tace sam bata so, ita iyakan abinda take so shine gidan mahaifinta da suka siyar ma yan caca da mummynta, tanason ta kara siyenshi dan shikadaine abunda bataso ta rasashi ba amma kamfani gani take kamar inta koma harkan neman kudi da wann kamfanin zata dawo kamar wacan meenal din ne da bata da hankli.

atake Halisa tay mata alkwarin siye mata gidan mahaifin nata tare da mata nasiha sosai, suka yafe juna,..Meenal bata damu sosai da jin cewa khaleel baison ganinsu atare ba dan tasan ko yaya zatay khaleel bazai taba aminta da ita ba.

A wani bangaren kuma taji matsanancin dadin jin cewa da akayi wai shemau is back tare da nata iyayen.

koma miye ya faru itade Taji farin ciki sosai cos since they cant be best friends with halisa anymore but they can promise to be each others sisters keeper and thats enuf for her.

Halisa ta dau duka wasu abubuwan ta data amso matasu awajen hukuma including credits cards da sauran 75million naira dake acct dinsu ta bata abubuwanta.

Lokcin bikin aurenta haka tamata komi kamar yadda dan uwanka na jini zai maka ga mota ga kudi And she also try her best to invite all her friends dan su kara mata karfin gwiwa sukuma mata ta'aziyar mumynta.

a Karo na farko da shema tazo garin lagos da kwarin gwiwa kenan

ranar meenal batay tsammani ba tagansu dukansu kama daga kan vicky, halisa, hadiza, da shema, kowa ya hallci bikinta sun mata goma na arziki an mata jajen mutuwar mummynta haduwar tasu was very emotional dan akallo daya kamasu zaka san kowa ya sauya.

Vicky da halisa kowa yazo da yaransa duk da ma halisa na fama da cikin na biyu yanzu.

They talked abt thier life yadda kowa zai kama abubuwanda ke gabansa but still keeping in touch in terms of needs, sisters spirit, and empathy.

When best freinds become foes evrything bcm like burn castle dan cikinsu babu wanda bai canza ataciki ba cos nothing can ever be the same anymore.

cuta, rashin gaskiya, Hassada, kishi, kyashi, jahilci, cin amana duk sun gani atare amma bashine ya hana hakuri, juriya tausayi imani da tuna alheri ya dawo da su cikin yan uwansu ba.

Daga nan wajen meenal taronsu na kawaye biyar din nan ya tsaya na har Abada kowa ya cigaba da rayuwarsa da wanda yaga zai iyayin hulda dashi...

****** sabon Rayuwar Auren baizo ma meenal da sauki ba sabida karancin ilimin addini da na rayuwa, amma dake Allah ya hadata da kishiya me imani within no time suke gudanar da rayuwarsu cikin sanyi tana koya mata abubuwa kamar girki da aikin gida duk dama suna da masuyi amma she do help meenal with the knwlge alots.

Tana ganin halima tana soyayya da mijinsu ashraf amma Ita bata taba sakawa aranta cewa ma zatay soyayya da ashraf din ba dan yanzu soyayyar ma tsoro yake bata duk dama duk wani hakkinsa na aure tana kkrin bashi, amma kuma data fara sallah tafara gudanar da addini bisa qaida saitaga deirs more to married life dan sadness and fears.

tun Suna zuwa islamiya ita da kishyrta halima, hartazo ta samu ciki dake haliman Ita bata taba haihuwa ba sai kuma cikin yay sanadyar da kusanci ya shiga tsakanin meenal din da ashraf sosai suka fara gudanar da soyayyarsu me sanyi.

Iyaka dan abunda baza a rasa daga kishi na mata be ke giftawa tskaninta da haliman amma dake tana samun ilimin addini da nasiha sai kwata kwata bata haukar kishi da halima, yanxu ko sun dan samu sabani zakaga ita zata fara bada hakuri Har Allah ya sauketa ta haife da namiji aka samai sunan mahaifinta Aliyu..halisa bata samu zuwa sunan ba sabida wann karon a saudi ta haihu kuma bata wani jima da haihuwar ba itama ta ta haifi namiji me suna _Sa'ood_ ..

Rayuwa ta cigaba musu ahaka saida aka dan jima sann shema ta auri wani gangariyar alhaj a bauchi yana da mata uku amma kuma yana da kudi sosai, dan gidanta ma daban ne irin ryuwar daula dataso adacan din ayanxu da bata damu dashi ba sai gashinan yazo ya sameta a sama haka kowa ya mata murna, as time goes on Meenal ta fara daga business din kayan gona da babanta yakeyi tun dacan, da kudaden da halisa take turo mata ta dingayi har Allah ya bata saa business din ya fara flourishing ahnkli ahankli

After 4 years *********** abubuwa da yawa sun faru harda kammala karatun kayden a US tare da bude babban private asibiti me sunan hafsa agarin lagos mahmud da matarsa suna da yaransu uku, zumunci tskaninsu da familyn shema yay karfi dan Babban dansu muhammad kowani hutu awajen shema yake zama a garin bauchi..

..meenal kuwa saida ta sake haihuwa kafin nan kishiyartan itama ta haihu, duk dama yanxu ashraf yafi kaunar meenal amma kuma suna zamnsu lumui tana agro business dinta data sake maida masa suna talba enterprises daga ita har halisan sun gina sadaqatul jariya ma iyayensu da suka rasu.

jifa jifa suna ziyartan junansu amma meenal bata iya zuwa gidan halisa sabida khaleel

Yawanci saidai su hadu a office shidinma baifi sau daya ko biyu a shkra ba but still suna kula junnsu like true blood sisters no matter what u cannot separate the natural bond..meenal haryau tana kaunar halisa sosai.

Halisa ne ta dan dauki hutun haihuwa bayan ta haifi saood kusan saida tay 2 gud years kafin nan ta sake daukar wani cikin

Hadiza da shema kusan alkci guda suka haihu shema ta samu ƴa mace hadiza ɗa namiji duk dama dakyar hadizan ta sha wajen haihuwa sabida tanada hawan jini me tsanani.

Kawaye biyar dinnan basu kara hadewa da juna ba saida mijin hadiza ya tsaya takarar zabe dake awann shkran ne za'ayi zaben Dukansu they contributed in their own ways har Allah ya bashi nasara.

Wajen waliman ne kowa tazo da ahalinta, wasu da mazajensu aka yi taro aka watse. All these year saiyau meenal ta ga khaleel da idonta dayazo daukar halisa suka gaisa And he wish he well with her new life harya bawa yaranta kyautar kudi.

Daga nan tunda aka rabu da juna sai haduwa kuma ya dawo da kyar dan kowaccensu ta shiga tsbgr sabuwar rayuwrta ne cikin kwanciyar hankli da aminci tare da kyautatawa.......

Dukkan godiya ya tabbata ga Allah madaukakin tsarki daya bani ikon kawo wann karamin labarin domin in nuna illar maraici ga ƴa mace, illar bacin zuciya, "fuska biyu, hassada, illar rashin ilimin addini, da yadda Amana, hakuri, juriya da yafiye ke yin alfanu ga rayuwar alumma gabaki daya. Babu wata Qaddarar da badaga ubangiji take zuwa ba, dan adam yasani addua ce kawai maganin qaddara ba wani boka ko malami ba Iyaye nagari sune tushen al'umma, idan zaka gina ramin mugunta Kagina shi da dede dan wata rana kai zaka rufta aciki, acikin labarina na kawo concept of Generational trauma iyayen da ke tsaurara hukunci akan yayansu misali akan khaleel da mahaifinsa, homosexulity lesbianism da sodomy wato harkan gay, da kuma feminism da kuma fornication and adultery, samari, yan mata da matan aure masu buri da kwadayi dake fadawa acikin munannan qaddara hattara dai duniya budurwan wawa...

Dis book is also for Thos of u that think age and religioun is a barrier to marriage, humanity and kindness, sann akarshe muddin bawa bai fidda ransa da niimar ubangji ba toh tabbas tsira bazai nesa da shi ba.

ALHAMDULLHI RABHIL ALMEEN THIS COMES TO THE END OF THE *"CHEATERS CLUB" BY SURAYYAHMS* COMPLETE BOOK DOCUMENT *#800* CHAT ME AT 08060712446

DUK WACCE TA KARANTA BATA BIYA BA BANAJAN ALLAH YA ISA AMMA DAI KUSAN HAKKIN WANI YANNA HANA WANI KWANCIYAR KABARI KO??

Toh bissalam.. #Surayyahms/2024

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull