Kenza eBookz

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 1

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 1

Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 1: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 1. [2/23, 7:34 PM] Nasma: Wata mace ce take kai kawo tsakanin falo da ɗaki…

4,965 words

[2/23, 7:34 PM] Nasma: Wata mace ce take kai kawo tsakanin falo da ɗaki cike da tashin hankali da fargabar abin da zai faru a yammacin yau ɗin. Yawan tunaninta da matsuwar son jin kyakykyawan labari daga Fanna ya yi mata yawan da ya haddasa mata ciwon kai na bari ɗaya. Kusan wata biyu kenan tana shirin da take fatan yiwuwarsa domin cimma ƙudurinta. Kuma nan da lokaci ƙanƙani ɗayan biyu zai faru, samun biyan buƙatar da zai zama mataki na farko wurin cikar burin nata ko kuma tonuwar asirin da zai janyo lalacewar komai. Tunowa ta yi da cewa Fanna bata da zaɓin da ya wuce yi mata biyayya ta samu kanta da sakin gajeren murmushi wanda ya kasance ɗabi'arta idan ta jiyo ƙamshin nasara. Duk da haka zama ya gagareta saboda rashin nutsuwa ta kalli agogon bango na rantsattsen gwal ɗin da yake ɗaure a tsintsiyar hannunta a karo na barkatai sannan ta sunkuya ta ɗauki wayar landline ɗin da ke kan wani teburin glass a gabanta ta danna wasu lambobi. A take kiran ya shiga kan wayar dake falon gidan. Wata siririyar mata ce ta ɗauki wayar ta kangata a kunnanta a ladabce tamkar tana gaban uwarɗakin nata ta ce, "Hajiya na shigo ne?" "Eh" Kaɗai ta iya cewa ta kife wayar tana jin kamar zuciyarta tana juyin waina a cikin kirjinta. Da hanzari Madam Zainaba ta miƙe domin cika umarni. Cikin sassarfa ta soma bin mattatakalar benen da zai sada ta da ɗaki na uku kuma na ƙarshe a saman. Hannu na rawa ta tura ƙofar ɗakin da tun safe yake a rufe ta shiga. Kamar kullum sassanyan ƙamshin turaren wuta da ya kama ɗakin ta fara shaƙa. Kai a ƙasa ta ƙarasa shiga ta sameta tsaye a jikin taga ta bata baya. Sassauta murya ta yi a ƙoƙarinta na son kwantar mata da hankali da tsoron ɓata mata rai. "Ki ƙara haƙuri Hajiya kinsan dole ne ta yi abin da kike so ko don gudun kada ki tona mata nata asirin" Cikin takunta na ƙasaita da isa ta juyo tana murmushi. Tun asalinta mace ce me dakakkiyar zuciya, wadda sanin ainihin abinda yake ƙunshe cikin tunani da zuciyarta abu ne mai matuƙar wahala. Ba domin komai ba sai saboda ƙwarewarta wurin nuna fuskoki mabambanta da suke dacewa da duk yanayin da ta sami kanta. Tana da tsananin wayo da dabara wurin samun abinda take so. Haj. Hafsatu Manga Bukarti kenan. Asalinta mutuniyar jihar Borno ce. A kamannin fuska ta ɗebo mahaifiyarta bafillatanar usul amma a ƙirar jiki da kuma launi dangin mahaifinta ta biyo. Tana da tsayi sosai wanda zai bawa me kallonta tabbacin ita ɗin ta raɓu ƙabilar Kanuri. Duk da kasancewarta baƙa yanayin rayuwa ya sanya fatarta gogewa tana sheƙi. Kasancewar ta tashi cikin arziki kuma ta yi aure cikinsa ya sanyata cikin sahun farko na matan da ake kallo a sake kalla saboda kyau da gayu. Zanen fuska da ta gada wurin mahaifinta bai rage komai na kyawunta ba sai ƙarin kwarjini. Tana da tsaga guda ɗaya daga tsakiyar goshi har ƙarshen hancinta sai bibbiyu a kumatu da wasu biyun a gefen kunne sirara. Mace ce mai kimanin shekaru arba'in gogaggiyar ƴar boko wadda ta karanci aikin jarida har zuwa matakin degree na biyu wato Masters. Sai dai bata taɓa aikin da ya shafi karatunta ba. Hasalima tana miƙa ragamar ilimin da take da shi ne wajen shirya abubuwa yadda take muradi kuma daidai da buƙatarta. Madam Zainaba amintacciyar mai aikinta ce, wadda za su yi kai ɗaya ta fanin shekaru saɓanin gogewa. Amma hakan bai hanata yi mata hidima cike da ladabi da biyayya ba. Asalinta mutuniyar Kogi ce ƴar ƙabilar Igala. Sun haɗu ne a wani asibitin kuɗi a Lagos wanda ya kasance wurin zuwansu indai suna Nigeria kasancewar nan suka zauna da mijinta na fari kafin su dawo Abuja bayan rasuwarsa. Ba wani sabo suka yi ba da farko saboda Madam Zainaba mai shara da wankin banɗaki ce. Wani abu mai girma ne ya zama silar amintarsu har ta kai Haj Manga kamar yadda aka fi saninta ta ɗaukota zuwa gidanta. Bata da matsalar zaman gidan saboda bazawara ce kuma ƴaƴanta suna wurin mahaifinsu sai dai ta kai musu ziyara. Tamkar waziriya take ga Haj Manga, ita ce mai sawa da hanawa idan bata kusa.

*** Tashin hankalin da Fanna take ciki bazai faɗu ba a wannan yinin. Tana cikin tsaka mai wuya domin gabaɗaya tun bayan da Haj Manga ta fada mata buƙatarta sannan ta haɗa da tsoratarwa, ta fahimci cewa tana cikin yanayin da bahaushe ke kira gaba kura baya sayaki. Zaɓi biyu ne rak take dasu, kodai ta tursasa Alh Audi ya saketa ta koma gida mahaifinta ya yi ƙuli-ƙulin kubura da ita ko kuma ta cigaba da zama da shi. Idan har ta yi hakan kamar ta ɗabawa kanta wuƙa ne, domin Haj Manga tana da ƙwaƙƙwarar shaidar da za ta zubar mata da mutumci da ƙima a idon duniya bayan ta kashe mata auren da ƙarfin tsiya. Duk mai hankali baya buƙatar neman shawara akan wadda ya kamata ya zaɓa, amsar a bayyane take. Sai yanzu ta gasgata zantukan da ta jima tana ji cewa Haj Manga tana da hannu wurin watsa duk wani neme-nemen auran Alh Audi yayan marigayi tsohon mijinta. Kamar yadda jita jitan yake yawo cewa ake yi, tun bayan rasuwar uwargidansa duk lokacin da ya nemi aure sai ta yi kutu-kutu ta shiga ta fita ƙarshe sai dai aji cewa ya fasa auren saboda an sami mishkila daga ɓangaren matar. Lokacin da nata mahaifin Manaja a reshen kamfanin Alh Audi da yake garin Maiduguri ya gabatar masa da ita akan ya nemi aurenta ko kaɗan basu sami matsala da Haj Manga ba. A takaice ma ita ce ta farko wajen bada gudunmawa ɗari bisa ɗari, ashe talala take yi musu. Aure shekara biyu ga ƙaramar yarinyar da ko yaye bata isa ba amma ana neman raba iyayenta. Murɗa ƙofar ɗakin nata ta ji anyi cikinta ya bada wani mahaukacin sauti saboda tsabar firgici. Yau ce rana ta ƙarshe da Haj Manga ta bata ko kuma ta tona mata asiri. Sake lafewa ta yi ta runtse idanunta daga kwance tana jin shigowar Alh Audi tsakar ɗakin. Ransa a matuƙar ɓace yake da sabuwar tsirfar Fanna a ƴan kwanakin nan. Fitsara da rashin kunya kullum sai ta tsiro da sabo gareshi ko girmansa bata gani. Bargon da ta rufa da shi ya yaye da ƙarfi yayi jifa da shi a kasa sannan ya kira sunanta da sigar gargaɗi. "Fanna" Ga tsoro a zuci amma haka ta dake ta ta shi cike da tsiwa "sunana kenan!" Kallon mamaki ya bita da shi. A zahiri faɗa yake son yi mata ko ya kamata ya fyala mata mari sai dai darajar mahaifinta a wurinsa yake dubawa da ƙuruciyarta shi ya sa ya canja akalar maganar da yayi niyyar yi zuwa lallashi. "Zauna muyi magana" Ya nuna mata bakin gadon shi kuma yana tsaye ya ɗora ƙafa ɗaya a kan gadon ya ranƙwafo daidai saitin fuskarta. Alh Audi Karam ba shi da tsaho sosai kuma babu kiɓa sai dai ba'a kira shi ramamme ba. Baƙi ne ba wuluk ba mai ƙaton tumbi da sanƙon da ya fara cinye gaban kansa. Fanna ta kawar da kanta gefe saboda tumbin ya matso gaban fuskarta sosai. "Kaga Alhaji babu sauran magana a tsakaninmu kawai ka sauwaƙe min na kama gabana ko ana aure dole ne?" "Ni kike faɗawa haka Fanna?" "Kai waye da baza'a faɗa maka ba? Kuɗi ne dai taƙamarka ni kuma basa gabana" Ta furta cikin sarƙewar murya, gabanta na dukan uku-uku saboda irin kallon da yake jifanta da shi kamar zai kai hannu ta ji saukar duka. 'Bani da lokacinki' ya ayyana a zuci saboda ya kula abin nata hadda alamun zuga saboda haka ya sauke ƙafarsa ya juya zai bar ɗakin. Tana ganin haka hankalinta ya sake tashi, bata san lokacin da ta danƙaro ƙaryar da take ganin za ta iya zama madafa ga tashin hankalin da ke bibbiyarta "Alhaji gara ka sakeni tun kafin na tona maka asiri duniya ta san sirrin da kake..." Maganar bata gama fita ba ta haɗiyeta tsaf saboda wani rikitaccen kallo da ya shiga jefa mata cikin ƙanƙanin lokaci sai ga wuyanta a tsakiyar hannunsa na dama ya kai mata mummunar shaƙa. Bakinsa har wata kumfa yake yi saboda kiɗima da ɓacin rai. "Me kika ce!? Nace me kika ce!!?Me kika sani!!?" Ya shiga jero mata tambayoyi bayan tuni ta yi nadamar amfani da tsoratarwar da aka yi mata a kansa. Kakari take yi idanunta sunyo waje saboda azabar riko. Hannuwanta biyu ta saka tana ƙoƙarin cire nasa guda ɗaya amma ta kasa. Alh Audi ya yi fushin da bata taɓa ganin irinsa ba. Idanunsa jajjurr ya sake cewa, "Me kika sani?" Fanna tana kakarin wahala domin ya sassauta shaƙar da ya yi mata. Ba abin da ke ta shi sai hucinsa kamar mahaukacin kare. Da alamu jira yake ta yi magana, murya can ƙasa ta ce, "Wallahi ƙarya nake yi saki na kawai nake so kayi na faɗi hakan" Sai da ya gama yi mata kallon tuhuma mai cike da zargi sannan ya yasar da ita a ƙasa ya fice daga ɗakin. Ajiyar zuciya ta soma saki da hawaye sai ga shi ya dawo ya jefa mata takarda akan fuskarta. "Saki kike nema ko? Gashi nan nayi miki uku kuma kafin a kira magariba ki tabbata kin fita daga gidan nan idan ba haka ba sai kin gwammace kiɗa da karatu. Kuma kada ki sake ki ɗaukar min ƴa ke kaɗai zaki fita shashashar banza." *** Ko da Alh Audi ya fita jiknsa sai tsuma yake yi, ya kai mari ya kai gauro. Tunani yake yi ya kasa gasgata shin shaci faɗi ta yi ko kuwa da gaske ne ta san wani abu. Sirrinsa a ɓoye yake yana da yaƙinin kuma waɗanda su ka sani harda ubanta Alh Ari basu isa su tona shi ba. A take hankalinsa ya fi kwanciya da gasgata zancenta yana mamakin me ya tunzurata yasa ta neman saki haka? Wata zuciyar ta raya masa bazai wuce yaro sa'anta take burin aure ba tunda dama tana da saurayi aka yi mata fin ƙarfi saboda babanta yana kwaɗayin karin matsayi a wurinsa. Wayar dake falon farko kafin a shiga katafaren ɗakinsa ya ɗauka da zummar kiran Alh Ari yaci masa mutumci akan sakacinsa da Fanna sai ya ji tana magana daga ɓangarenta kasancewar wayar landline ce, idan wani yana magana a kan ɗaya daga cikin kawunan wayar gidan wani zai iya ji. Wadanda suke ɗakinsa ɗaya tana kama duka gidan, ɗaya kuma lambarsu ɗaya da ta ɗakin Fanna sai kuma cellular da yake amfani dasu kawuna biyu masu masifar tsada. Shiru yayi hadda ɗora hannu ya toshe daidai bakin saboda kada su farga cewa ana sauraronsu. Muryoyinsu tartar ya gane kowa a ciki. Fanna ce take cewa "Ki fada mata ya bani takardar kuma saki uku ne." Madam Zainaba ta ce "kin kyautawa kanki, kada ki manta idan maganar nan ta fita kece zaki kwana a ciki" A tsorace Fanna ta ƙanƙame wayar daga nata ɓangaren, tana waige kamar wani zai ganta, "Madam Zainaba ki taimakeni ko nawa ne zan biya ki bani hotunan don Allah" Siririyar dariya Madam Zainaba ta yi kafin ta ce, "Hotunan haɗuwarki da tsohon saurayinki a Nicon Nuga Hilton garkuwa ne a wurin Haj Manga. Kamar yadda ta yi alƙawari ba za ta taɓa nunawa kowa ba cewa kina yawonki duk lokacin da Alh Audi baya ƙasar kema ki riƙe bakinki kada wanda ya san cewa da hannunta a mutuwar aurenki." "Madam Zainaba...", Sai dai kafin ta ƙarasa isar da muradinta kit Fanna taji shiru an barta da kan waya a hannu sai gumi da yake tsatstsafo mata kamar wadda ta yi tsere. Tana cikin mawuyacin hali a ɓangare ɗaya ga Haj Manga sannan ga mahaifinta sai kuma abinda ya tsaya mata a wuya yaki sauka wato tunanin wane sirri ne Alh Audi yake ɓoyewa wanda ya janyo sauyawarsa lokaci guda? A nasa ɓangaren kuma sai da ta ajiye wayar sannan shi ma ya ajiye ta hannunsa kansa gabaɗaya ya kulle. Me yasa Haj Manga take shiga tsakaninsa da aure haka? Idan sauran ta kawo kabali da ba'adin halayensu basu da kyau me yasa ta takura Fanna akan neman saki? Sannan ƙarin takaicinsa Fanna tana yawo da igiyar aurensa. Ji ya yi komai ya cakuɗe masa ya tashi ya buɗe firij ɗin ɗakin ya ɗauko kwalbar giyar gulder ya cizge murfin ya shiga kwankwaɗa batare da tunanin zubawa a kofi ba. *** Washegari Alh Audi Karam da kansa ya kira Haj Manga da Alh Ari ya nemi su zo yana son ganinsu kafin ƙarfe huɗu, saboda tafiya Japan da take gabansa akan harkar kayan wuta yana son buɗe wani sabon reshe mai suna Karam Electronics a ƙarkashin inuwar Karam Holdings Inc. Zuciyarsa ce ta kwana da zurfin tunani akan dalilin da yasa Haj Manga take yi masa haka. Ya sani cewa a halin yanzu babu yadda za ayi a ambaci mutum biyar da su ka fi kowa kuɗi a Nigeria sunansa bai zo a na biyu ko na uku ba. Shekara uku da ƴan watanni da rasuwar ƙaninsa Alh Ibrahim Karam amma ya bunƙasa kasuwancin nasu sosai fiye da lokacin da ƙanin nasa yana raye. Ribarsu ta habbaƙa arziƙi ya kama ƙasa. Mata rububinsa suke yi, shekaru ko cikinsa da yake ƙwajaja bai sagar musu da gwiwa ba indai zasu amsa sunan iyalinsa. Shigowar Tony PA (personal assistant) ɗinsa cikin falon da yake karɓar baƙi ce ta katse masa tunani ya sanar da shi isowar Alh Ari. Umarni ya bayar da ya shigo da shi saboda yana son su zanta kafin isowar Haj Manga, dalilinsa kenan na bada awa guda tsakanin lokacin da ya basu na ganinsa. Fuskar Alh Ari kamar wanda aka aikowa saƙon mutuwa yana cikin ɓacin rai mai tsanani ko hannun Alh Audi da ya miƙo masa su gaisa yaƙi karɓa. Tony na rufe ƙofar bayan ya jefawa Alhajin wani irin kallo tamkar zai kai masa duka ya soma magana. "Alh Audi ni za ka wulakanta ka sako min ƴa saki har uku?" Ya fada yana haki. Alh Audi bai nuna ɓacin rai ba ko kaɗan "ka zauna Alh Ari akwai abinda nake so ka sani" Baza hannuwan babbar rigarsa yake yi cikin yanayin ko in kula ya ce, "Babu wata magana tsakaninmu, kai ka san cewa a tafin hannuna kake billahillazi duk ranar da na buɗe wannan bakin" ya ɗora manunin yatsansa yana bubbuga laɓɓansa "sai ka ji inama baka..." "Kai ARI!" Alh Audi ya daka masa wata irin tsawa mai firgitarwa. Ba tare da ya jira ya amsa ba ya nunashi da hannunsa, murya a ƙausashe kamar wanda aka yi wa wahayin mutuwa. "Jiya Fanna ta kalli tsabar idona tana faɗa min cewa ta san sirrina yau kaima kana iƙirarin tona shi? Bani da niyyar tsawaita magana kai ka san waye Audi farin sani. Shiga gonata ba zai yiwa kowa kyau ba saboda haka ina shawartarka da ka rubuta ka ajiye duk ranar da ƙaiƙayin baki ya nemi kwasarka sai na nuna maka wannan Audin yafi wanda ka sani a da." Jikin Alh Ari sai ya yi sanyi laƙwas ba wai don ɓacin ransa ya sarara masa ba. Zama ya yi rigijif akan kujera ya cire hularsa yana fifita da ita ba don zafi ba sai don rasa abin yi. Daurewa ya yi kada ya nuna masa tsoron da yake cin zuciyarsa ya soma magana. "Alh Audi me yasa kayi min haka? Na taimaka maka lokacin da kake buƙatar taimako kuma na iya bakina akan sirrinka. Abu ɗaya na nema shi ne ka auri Fanna domin daga min darajata shi ne kayi mata sakin da babu gyara don ka nuna min iyakata?" "Ko ɗaya Alh Ari, mutuwar auren nan ba aikin kowa bane sai na Haj Manga" ya faɗa masa duk abinda ya ji a waya tsakanin Madam Zainaba da Fanna a yammacin jiya. Sai da ya sha ruwa rabin tambulan da yake gabansa ya ɗago kai yana kallon Alh Ari da ya zuba masa idanu, "Abinda ban fahimta ba shi ne dalilinta na hanani aure, kana ganin tana sona ne?" Ya kece da dariyar rashin yarda da abinda ya faɗa shi da kansa. Sai lokacin Alh Ari ya soma samun nutsuwa har ya iya kawo nasa hasashen akan dalilin Haj Manga. "Baka tunanin ko akan Arƙam ne? Shekara uku fa ba kwana uku bane." Idan akwai abinda Alh Audi ya ke gudu bai wuce a tayar da maganar Arƙam ba. Hannuwansa biyu yasa ya dafe kansa sannan ya ce, "Ban taɓa zaton abin alkhairi zai zame min sharri ba Alh Ari, yaron nan anyi neman har an gaji" Damuwa sosai ce ta bayyana a fuskar Alh Ari, "Indai haka ne ni ban ga laifin Haj Manga ba. Gani take yi kamar wani abu ka shiryawa ɗan nata ko ya mutu an ɓoye. Ko ni ne fa dole na ɗora alamar tambaya, ta yaya daga kai yaro karatu za a neme shi ko sama ko ƙasa kamar allura?" Ƙwafa Alh Audi ya yi yana kaɗa kai, "Tun ranar da aka bugo waya daga makarantar na nemi kwanciyar hankali na rasa. Ko sati bai yi ba ya gudu, ina raina shi ganin sanyinsa ya yi yawa ashe shaiɗanin kansa ne?" "To ko dai mutuwa yayi ne ba a ga gawarsa ba?" Cewar Alh Ari, maganarsa kuwa ta ƙara dulmiya Alh Audi cikin tunani wanda alhini ya bayyana ƙarara a fuskarsa. Sun koma tattaunawa akan ɓatan babban ɗan Haj Manga wanda ya kai wata makaranta a birnin Nottingham da yake Ingila domin ya karasa karatun shekara guda da ya rage masa na babbar sakandire sannan ya nema masa gurbin karatun a jami'ar garin. Lokacin tana takabar mijinta bata cikin nutsuwa da hankalinta ko kaɗan. Kasancewar tsakanin Arkam da ƙaninsa Jamal akwai tazarar shekara bakwai shi ya sa ba a sako shi ba a lissafin tafiyar ba domin ya yi ƙanƙanta. Amma a tsarin tun farko hadda nasa ɗan Shamsu sai shi kuma ya kamu da rashin lafiya yana kwance a asibiti har aka fara karatu da sati ɗaya. Gudun kada duka suyi latti sai ya fara kai Arƙam dama shi ne babba da alƙawarin Shamsu na samun lafiya zai kawo shi da kansa. Sai dai kuma hakan bata samu ba domin kwana huɗu da dawowarsa Nigeria ya sami waya daga makarantar wai Arƙam ya gudu. A daren ranar ya yi sa'ar samun jirgi suka ta shi da Tony PA sai da ya yi sati biyu ana yawon offishin jakadanci na Nigeria dake ƙasar da na ƴan sanda neman madafa. Kafin su dawo sai da ya rame cikinsa ya dan ja baya saboda tashin hankali. Bayanai daga airport sun nuna tabbas Arƙam matashi ɗan shekara goma sha bakwai bai bar ƙasar ba amma an kasa samunsa. Alh Audi ya kira Alh Ari tun a lokacin ya bada umarnin a tsayar da account ɗinsa ta yadda ba zai iya cire kuɗi ba dole wahala ta fito da shi idan ma ɓuya ya yi. Bankin da aka buɗe masa account a ƙasar ma a take yasa aka kulle shi amma har yau shiru babu shi babu labarinsa a idon duniya. Haj Manga tana gama takaba ko ta kan Alh Audi bata bi ba ta ɗauki Jamal suka tafi kaiwa Arƙam ziyara a nan ta haɗu da mummunan labarin da Alh Audi yake ta ɓoye mata. Da ta tashi sai ta kira shi tana tambayarsa yaya sunan makatantar da Arƙam yake shaf ta manta sai da suka je garin ta tuna bata tambaye shi ba. Alh Audi sai ya ɓuge da borin kunya wai tana son nuna masa iyakarsa akan ɗanta shi ya sa ko ta kansa bata bi ba ta tafi ganinsa. Ya gama bambamin faɗansa ya ce kuma ta dawo gida idan ya isa da ita domin ya riga ya canja masa makaranta ma sabanin wadda ya bata ta saka hannu a matsayin uwa. Daga ranar ta ɗora ƙatuwar alamar tambaya akansa na rashin faɗa mata gaskiya. Ta yi kuka ba kaɗan ba a hankali hawan jini ya sarƙeta ga mutuwar miji ga ɓatan ɗa. Yanzu an shekara uku tana neman Arƙam a gefe shima Alh Audi bai fasa ba kamar yadda makusancinsa Alh Ari da Tony suka sani amma har yau yaƙi faɗa mata gaskiya da bakinsa sai dai yayi ta hanya-hanya yana zillewa. Ƙarairayin nasa da dabaru tuni sun ƙare ƙarshe ya yi mata jan ido cewa a matsayinsa na wan uba ga Arƙam shi ya soke masa zuwa gida sai ya gama karatunsa gabaɗaya saboda soyayyar da take gwada masa ita ce take sangarta shi ya tashi da sanyi babu hayaniya irin ta matasa sa'anninsa. Wannan kenan. *** Shawara Alh Ari ya ba shi domin su san manufarta gara ya aureta kawai. Batun Fanna kuma zai yi mata auren kisan wuta da zarar ta gama idda sai a mayar musu da aurensu. Alh Audi yayi na'am ɗari bisa ɗari ko babu komai idan ya nunawa Alh Ari yana son zama da ƴarsa ya tabbatar sirrinsa zai cigaba da kasancewa a ɓoye. Batun yawon da take yi da saurayinta ta sha ruwa indai buƙatar su biyun za ta biya. Awarsu guda da rabi Tony ya zo ya sanar da isowar Haj Manga da waziriyarta Madam Zainaba. Ita kaɗai ta shiga falon aka bar Madam Zainaba tare da Tony a wani falon. Sai da ta gyara yanayin fuskarta ta yi alamun damuwa sannan ta shiga falon a firgice. Takun nan na ƙasaita babu shi ta kwantar da kai hadda guntun hawaye ta samu wuri ta zauna. "Yaya Audi me nake ji haka wai ka saki Fanna?" Ta ɗan muskuta tana kallon Alh Ari ta wutsiyar ido, "Kayi hakuri Alh Ari na tabbata kai da Haj. Kolo kuna cikin tashin hankali amma babu komai gara ayi sulhu yanzu ya mayar da ita" Saroro Alh Ari ya yi yana kallon rainin hankali na Haj Manga shi kuwa Alh Audi murmushi ma ya yi. "Babu sauran aure a tsakaninmu na riga na yiwa Alh Ari bayanin komai kuma shi ma ya fahimta" Kai kawai Alh Ari ya gyaɗa sannan ya ce "abinda ya faru laifinta ne saboda haka ba zai taɓa zumuncina da Alhaji ba" "Ni dai banji daɗi ba gaskiya, Yaya Audi saki uku ai sai yara manya masu hankali da zurfin bincike aka sansu" Magana ta faɗa masa a fakaice daga shi har Alh Ari sun fahimta amma sai suka ƙi nunawa. Ta zauna ta yi ta yabon Fanna da nuna tausayin Kulsum saboda ƙarancin shekaru. Ƙarshe kwabe fuska ta yi ita a dole tana cike da damuwa ta ce, "Yanzu waye zai kula da ita Kulsum ɗin Yaya Audi?" Danne ɓacin ransa ya yi ya ƙirƙiro mata murmushi mai nuna alamun kifi na ganinka mai jar koma, "Ke nake so na barwa wannan amanar idan zaki iya yi min alfarma" "Kamar yaya?" Ta tambaya da alamun mamaki duk da cewa tana murna ne ya faɗa tarkonta. Alh Ari ne ya bata amsa "Haj Manga auren Fanna ga babban mutum kamar Alh Audi kuskure ne daga gareni. Akwai ƙuruciya da zafin kaina tare da ita, Alhaji yana buƙatar mace mai nutsuwa da shekaru kamar naki wadda ta san yau ta san jiya. Yana buƙatar matar da za ta iya riƙe masa gida ta taimaka masa akan harkar kasuwancin nan" "Sannan ina buƙatar haɗe kan 'ƴa'ƴana wuri guda. Ina son Arƙam da Jamal su dawo ƙarƙashin kulawata kema ki taimaka min wurin kula da Shamsu da Kulsum" Shiru ta yi kanta a ƙasa taki basu amsa sai shessheƙar kukanta da suke ji. Alh Ari kamar ya ta shi ya shako wuyanta haka ya daure yana ta bata baki cikin minti goma ta amince da su nemi Baffanta ayi magana. Miƙewa ta yi za ta fita Alh Ari ya dakatar da ita da tsokanar ƙarfi da yaji "haba amaryarmu ki tsaya mana ku ɗan zanta da ango mana" Kawar da fuska ta yi alamun kunya tana dariya, "Kada muyi haka da kai don Allah". Tana fita suka ɗora zancen akan mamakin diramar da ta gama yi musu yanzu duka su biyun sun gaskata lallai neman Arƙam ne yasa take son auren Alh Audi domin ta san inda ɗanta yake. A hanyarsu ta komawa gida tsakanin Haj. Manga da amintaciyarta suka soma tattaunawa cikin magana ƙasa-ƙasa. "Ban san yadda aka yi ba amma jikina yana bani cewa sun gane akwai hannuna a cikin lamarin nan." Madam Zainaba ta murmusa "idan kuwa haka ne Hajiya ina tayaki murna domin buƙatarmu ta biya sai dai har yanzu na kasa gane me yasa kike son ya san cewa saboda neman Arƙam kike son auren shi?" Murmushin gefen baki Haj Manga ta yi, ta datse gefen leɓɓanta tana kallon titi, "Saboda neman Arƙam shi ne babban abinda yake gabana amma ba shi kaɗai ne a gaban nawa ba. Karam Holdings zuciyata ke hari, na kuma rasa dalilin faruwar hakan a gareni." Ta faɗa tana dunƙule hannu haɗe da kai wa iska wawwan naushi, kamar ita ta kashe zomon. Idanu Madam Zainaba ta ƙwalalo cike da mamaki "Hajiya kina nufin kamfanin gabaɗaya?" "Ko kina ganin bazan iya bane?" Ta kafeta da idanuwanta masu tsuma zuciyar mutane musamman na ƙasa da ita. Fahimtar cewa taso yin katoɓara yasata saurin gyaɗa kai kamar ƙadangaruwa cike da hanzari "ko kadan Hajiya, gani nayi abin ba na yau ko gobe bane" Murmushi ta yi mai cike da ma'anonin da ita kaɗai tasan manufarsu a ƙasan ranta, "Daɗina dake saurin fahimta Zainaba. Tabbas mallakar Karam Holding ba abu bane da zan iya yi yau ko gobe, aiki ne da zai ɗauki lokaci shiyasa ma na tura kaina jikin Alh Audi. Don ta Arƙam ko ban aure shi ba dole ne ya fito min da ɗana idan yana son kwanciyar hankali" [2/23, 7:34 PM] Nasma: *** Abu kamar wasa wata uku bayan sakin Fanna maganar auren Alh. Audi da Haj. Hafsatu Manga ta karaɗe lungu da saƙo na Najeriya. Wannan yamaɗiɗin ya faru ne ba don komai ba sai don kasancewar dama can ana raɗe-raɗin tana shiga ta fita ta hana shi aure a matsayinta na matar ƙaninsa da ya rasu. Kan kace mene ne wannan labarai kala-kala sun soma yawo ana tono rayuwarsu ta baya. Babban abin da ya fi ɗaukar hankalin mutane kuwa shi ne rasuwar Alh. Ibrahim mijinta da Tsaiba matar Alh. Audi a cikin shekara guda, a taƙaice ma dai tsiransu wata biyar ne da ƴan kwanaki. Shiyasa masu ƙarfin hali suka ɗora musu alamar tambaya ana ganin kamar akwai wata a ƙasa. Tun daga wannan lokacin kuma ita Haj. Manga ta fito da maitarta a fili take hana shi aure ga shi yanzu a cewar ƴan bani na iya sun gaji da ƙumbiya-ƙumbiya zasu yi auren. A wata majiyar ma cewa ake yi dama suna neman juna, wasu kuma sun tafi akan cewa kuɗi ne yake ruɗarta. To ko ma mene ne dai magana ba ta fitowa a jiki shiyasa ko a jikinta wai an mintsini kakkausa. Ta ɓangaren Alh. Audi shiri yake yi sosai saboda yana ganin wannan karon dai idan ya yi auren ya yi shi Kenan. Ko wane irin abu Haj Manga take tunanin shigowa da shi gidansa ya sani cewa ya fi ƙarfinta kuma aure ne za su yi babu yaji bare saki. Danƙarreran gida yasa aka gina masa na gani na faɗa irin wanda duk girman Abuja a wannan lokacin na shekarar 1999 babu kamarsa. Har tururuwar zuwa ganinsa ake yi, mutane da dama basu taɓa ganin gida mai kyau da tsarin Karam Mansion ba. Domin ba ƙaramin kuɗi ya narka ba kamar bai san ciwonsu ba, duk a ƙoƙarinsa na son ganin gidansa ya doke na mutumin da yake riƙe da ragamar lamba ɗaya a kuɗi a ƙasar. Karam Mansion katon gida ne wanda aka zube ƙarshen basira wurin gina shi. Mutumin da ya zana gidan har yau bai yi aikin da ya sama masa maƙudan kuɗaɗe kamar zane da tsara wannan gini ba. Katafaren fili ne da aka yi gine-gine a cikinsa. Banda ainihin gidan da yake daga ɓangare ɗaya akwai wani daga jikinsa, ta gefen swimming pool (wajen wanka) madaidaicin flat mai ƙofofi uku kusa da juna da su ke fuskantar ruwan. Kowace ƙofa idan an shiga ƙaton falo ne da ƙaramin kitchen sai ƙofar ɗaki da banɗaki a cikinsa. Ɗakunan anyi su ne domin ƴan mazan gidan, wato Arƙam Ibrahim Karam, Shamsu Audi Karam da kuma ƙaramin cikinsu Jamaluddeen Ibrahim Karam. Shamsu da Jamal ne kaɗai zasu amfana da nasu, tunda ba a san inda Arƙam yake ba har yanzu. Haka ma ɗiyarsa Kulsum duk da ƙuruciyarta ita ma an ƙawata mata nata ɗakin a sama, kafin a ƙarasa sashin da ɗakunan iyayan suke. Bayan ɓangaren samarin a can gefe kusa da katanga wani ginin ne guda biyu iri ɗaya, amma sun juyawa juna baya. Basu kai sauran gidan kyau ba amma suma sun tsaru daidai gwargwardo. Kai tsaye za a iya fasalta sashin da na masu aikin gidan, duba da yadda aka tsarashi ɗaki bayan ɗaki kuma kowane da makewayi cikinsa. Sashin farko na masu aikin cikin gidane, kama daga wanke-wanke da shara da kuma goge-goge. Ɗayan kuma na masu aikin waje wato masu gadi, direbobi, mai wanki da guga, mai sharar farfajiyar gidan da kula da shuke-shuke da aka ƙawata gidan dasu da kuma ƙaton ni'imtacen garden (lambu). Sai kuma wani ginin hawa biyu da aka yi musamman domin baƙi. Har ila yau akwai keɓantaccen wuri da aka ajiye namun daji irinsu barewa, jimina, ɗawisu da birai. Sai da aka gama komai na gidan aka zuba kayan more rayuwa kamar anzo duniyar kenan sannan Alh Audi ya je Maiduguri bisa jagorancin Alh Ari da wasu abokansu su biyu su ma masu kuɗi da faɗa a ji suka yi masa rakiyar neman aure.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull