Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 2
Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 2: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 2. Kai tsaye suka nufi gidan Justice Umaru wanda dangi suke kira da Baffa…
2,237 words
Kai tsaye suka nufi gidan Justice Umaru wanda dangi suke kira da Baffa Alƙali, shi ne kawun Haj Manga wanda ya riƙeta tun bayan rasuwar iyayenta. Alƙali ne a kotun (ɗaukaka ƙara) court of appeal. Yana daga cikin masu kuɗin da Jihar Barno take ji dasu. Dattijo ne kaifi ɗaya kusan halayensa kaf Haj Manga ta ɗebo tamkar ya yi kakinta ya tofar ta wannan fanin. Idan suna yi da kai to fa ka ciri tutar gata da soyayya amma muddin ka shiga bakin littafinsu to sai ta Allah. Wayau ne dasu da dabarar iya ƙulli, shi Alƙali ita kuma karatun aikin jarida saboda haka ake gwaren ideas (fikra). Yawancin duk abinda take yi yanzu na hana Alh Audi aure shi ne yake kitsa mata tare suke shirya komai. Allah bai ba shi ƴaƴa mata ba sai ita kaɗai tilon ƴar ƙaninsa shiyasa yake matuƙar ji da ita. Dansa na uku Kashim shi ne sa'anta. Sauran akwai Ali, Babagana, Kachalla da Bukar. A rayuwarsa indai Hafsatu zata ce wash to Baffa Alƙali ya dinga tambayarta kenan, "Manga me ya sameki? Manga me ki ke so?" Cikin wannan gata ta tashi bata da uwa da uba amma Baffa Alƙali bango ne madogara a gareta. Bayan gajeriyar tattaunawa da su Alh Audi ya ce ya ba shi aurenta sai su faɗi lokacin da suke ganin ya yi musu a zo a ɗaura aure. Alh Ari ne ya yi uwa ya yi makarɓiya shi yake bada amsa akan komai tamkar babu wata ɓaraka tsakaninsu. Hankalinsa a kwance yake, ya riga ya daidaita da wani yaronsa zai aura masa Fanna sati ɗaya bayan ta gama idda. Amma da sharaɗin zai sakota bayan wata uku. Ya gama lissafa komai a cikin ransa sai jiran lokaci. Sun kammala komai suna shirin tafiya Baffa Alƙali ya sako zancen Arƙam cikin wasa. "Wane course yake karantawa ne ɗan naka?" Alh Audi da bai fahimci inda ya dosa ba ya yi murmushi a zatonsa tambayar akan Shamsu ne, "Business Admin". "Amma shi da ya yi science (kimiya) me ya kai shi karatun Business (kasuwanci? Kodayake na ji ance karatun turai babu tsauri kamar namu, suna iya canja masa idan ya sauya ra'ayi" Gaban Alh Audi sai da ya faɗi da ya gane da wa ake. Sunkuyar da kai ya yi yana ƙaƙalo murmushin jin kunya ya yi saurin gyara zancen, "Shamsu ne ya fara level one wannan shekarar, Arƙam yana level two ne dayake ya wuce shi da shekara ɗaya." Kallon ido cikin ido Baffa ya yi masa fuskarsa a tamke tamau, "A wace makaranta Shamsun yake?" Cikin Alh Audi ya tsirga, indai ba yana hauka ba ga kowa ya saka masa ido akan rashin sanin ina Arƙam yake yaushe zai sake tura wani ɗan kasar waje. "Gwagwalada yake, University of Abuja." Babu wani ɓoye-ɓoye Baffa ya ce, "Shi nawa jikan ne ka kai wata ƙasar har yanzu ka kasa kawo mana shi mu ganshi? Duk karfin dangin uba fa Alh Audi ka sani cewa uwa ma tana da nata haƙƙin." Ya gyara zaman gilashin idonsa sannan ya cigaba da cewa "Magana ce ta aure a tsakaninku shiyasa nake mai baka shawara, da ka fitowa Manga a mutum sak ka bata ɗanta ko da rai ko a mace. Na san ba kasafai ake so mutum ya dinga karewa ƴaƴansa ba amma magana ta gaskiya ta yi haƙuri na ban mamaki akan yaron nan." Yana kaiwa nan ya tashi abinsa ya shige ciki ya barsu su huɗu zaune kamar ruwa ya cinyesu. Ɗaya daga cikin abokan nasa da suka zo tare mai suna Haji Lawalli ne ya soma magana bayan ya dena jin alamun tafiyar Baffa. Kai tsaye ya aje kallonsa a saitin Alh Ari sakammakon sanin duk cikinsu ya fi su kusancinsu da Alh Audi. "Kaga maganata ta jiya ta fito ko?" "Wace magana kenan?" Cewar Alh Audi yana bin su da idanu ɗaya bayan ɗaya. "Alhaji gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, INA ARƘAM yake?" Haji Lawalli ya jefa masa tambayar da ya riga ya gaji da jinta. Bai jira amsarsa ba ya ɗora a zafaffe da cewa, "Ko da bani da masaniya akan komai amma ina da yaƙinin babban abin da yasa Haj. Manga amincewa aurenka bazai wuce saboda rashin sanin ina ɗanta yake ba. Mu ɗin ma idan mun tambayeka sai dai kayi ta kauce-kauce. Saboda Allah jama'a an taɓa haka?" Ya yi tambayar yana raba idanu tsakaninsu. Abin mamaki garesu duka bai wuce hawayen da suke zarya a kumatun Alh Audi ba. Abin da zai girgiza wannan mutumin ya wuce raini amma yau akan ɗan ƙaninsa yake hawaye gidan surukai? Zubar hawayensa nasa ya tayar da hankulan sauran abokan nasa biyu amma Haji Lawalli tsaki ya doka saboda takaici. Wannan tsakin ne ya ƙular da Alh Ari har ya shiga yi wa Haji Lawalli tonon silili a wurin. "Haji Lawalli idan dai da gaske ka damu kai kanka ka sani ba nan ne muhallin kawo maganar nan ba amma saboda baƙin cikin Haj. Manga bata karɓi tayinka ba shi ne kake neman kunyata abokinka a gidan surukansa." Ai fa an taka jelar miciji ran Haji Lawalli ya sake dugunzuma ya tashi a fusace ganin Alh Audi da Alh Hadi suna kallonsa da mamakin jin wannan magana. "Ko da aure ko babu ni mai kulawa da Haj Manga da ƴaƴanta ne domin amintarmu da Ibrahim ta wuce duk inda kuke tunani." "Don Allah ku tashi mu tafi, wane irin abu ne haka da girmanku a gida irin wannan kuke mana tashin hankali?" Cewar Alh Hadi ya mike tsaya yana jira su tashi. Haji Lawalli ne akan gaba ya fice ko sake kallonsu bai yi ba. Alh Audi kuwa sai da Alh Ari ya taimaka masa ya iya miƙewa jiki a saɓule. Gidansu na garin su ka wuce wanda aka gina shi tun bayan auren Ibrahim da Hafsatu Manga kasancewar suna zuwa garin akai-akai shi kuma da kuɗinsa bai yarda da zuwa hotel ba kodayaushe ko zaman gidan surukai. Suna isa kowa ya sauka banda Haji Lawalli ya ƙwame a bayan mota yace airport za a kaishi ba zai kwana a garin ba. Duk yadda suka kaɗa suka raya ya dage yace bazai zauna ba, yana da abin yi. Bayan ya tafi sun shiga gidan masu aiki suna ta karakaina ana ƙoƙarin haɗa musu abinci su Alh Ari suka dinga bawa Alh Audi haƙuri. Alh Hadi ya ce, "Kada ka manta Haji Lawalli tare suka girma da marigayi saboda haka yana ganin kamar yafi kowa kusanci da cancanta ya auri Haj Manga ya riƙe mata ƴaƴa shiyasa" Alh Ari uban kauɗi ya yi saurin tarewa amininsa, "Idan yana taƙamar abota shi kuma Alh Audi da suke jini ɗaya fa? Har akwai wani kusanci sama da na ka haɗa uba da mutum? Kawai ka yarda kishi ne yake ɗawainiya da shi" sai kuma ya dan kwantar da kai ya rage murya "amma Alhaji wai da gaske ba za ka dawo da yaron nan gaban uwarsa ba ko don ka kubuta daga zargi ba?" Jiki ba kwari Alh Audi ya sake labarta musu abinda ya faru domin Alh Hadi bai san komai ba. "Har yanzu da nake muku maganar nan neman yaron nan ake yi ban taɓa hutawa ba. Kuna tunanin da gangan zan boye shi na janyowa kaina zargi da zagi ne?" Cikin ƙunar rai yake magana idanunsa sun sake ƙanƙancewa, "da na san cewa haka zata faru ko don kuɓuta daga fushin Dada da maganganun da ake jifana dasu da tuni ko ba shi da rai na kawo gawarsa na huta" kwalbar giya ya ɗauko ya shiga ɗaɗɗaka sai da ta kusa ƙarewa ya direta yana cije leɓe ya nisa a tunani. Daga ƙofar falon Tony PA ne ya gama sauraron hirarrakinsu ya murmusa "hmm dama ni ku ka kama da kun daɗe da mantawa da Arƙam ya taɓa ɓata." Wayarsa ya lalubo ya rubuta sakon SMS da turanci wanda fassararsa take nufin (Ina buƙatar ƙarin kuɗi saboda ya soma tayar min da hankali cewa yana son dawowa gida). Sai dare amsarsa ta shigo inda aka rubutu masa (Ok) kawai. *** Saukarsu Haj Manga kenan a birnin Dabo, Kano ko da me kazo an fika. Cikin shigar da aka fi gani a jikinta kodayaushe ta lafayya. Atamfa ce super exclusive a jikinta mai adon fari da koren ganye ta naɗe jikinta da lafayya ruwan madara mai adon bakin leshi. Yatsun hannuwanta sun sha jan lalle, wanda ya soma baƙi ga zabban gwal reras. Ƙafarta kuwa irin jan lallen nan ne wanda ake saka salatif ayi ado daga samansa, ya yi mata kyau sosai. Ƙunshi a wurinta wani ne yake tarar da wani ta riga ta saba. Sassayan ƙamshin turarukan humra da ya jima da kama jikinta ke ta shi fuskarta babu wata kwalliya sama da hoda da kwalli sai mai a leɓenta amma ta yi wani irin kyau. A gefenta yaro ne ɗan shekara goma sha uku cikin ɗinkin tazarce da hula. Babu ta inda ya ɗebo mahaifiyar tasa a kamanni domin kuwa shi fari ne mai ƙaramin jiki idan an kwatanta da yanayin nata jikin. Kai tsaye motar da take jiran ƙarasowarsu ta nufa an riga an buɗe mata ta shiga ta zauna Madam Zainaba ta zaga ɗaya ɓarin riƙe da jakar Hajiyar. Shi kuma Jamal ya shiga gaba. Wani ma aikacin filin jirgin kuma ya ɗauko akwatunan kayansu ya saka a booth (bayan mota). Madam Zainaba ce ta biya shi ya dinga zuba godiya kamar ya ari baki har su ka isa unguwar Yakasai gidan Dada mahaifiyar marigayi Ibrahim. Sai da suka yi sallah da cin abinci sannan Dada ta zauna tare da Haj Manga. Farar dattijuwa ce mai ɗan ƙaramin jiki alamu sun nuna a wurinta Jamal ya yi gado. Girmanta ya yi kyau domin da hankalinta sannan tana da ƙwari don har yanzu bata ranƙwafa ba. Idan ka cire ƴan ciwake-ciwaken da kan kama masu shekaru irin nata bata da wata matsala sai ta raunin idanu shiyasa take amfani da gilashin ido. Hira take yi da jikan nata yana ta zuba mata surutun wai saboda tace ya yi kyau ya sako manyan kaya. "Ai kuwa kayi kyau wannan auren namu ya kamata na sake biyan sadaki saboda ya ƙara ƙarko." Jamal ya kwashe da dariya, "Dada maza ne suke biyan sadaki fa ko Nanna?" Ya tambayi Haj Manga da take shirin zama akan wata dadduma ruwan zuma. Murmushi ta yi kawai ta kaɗa shi waje saboda amsa kiran Dada. Yana fita kuwa Dada ta haɗe fuskarta tamkar ba ita ta gama wasa da dariya da jikanta ba. Maganar ɗaya ce ta sani dama shi yasa bata ji mamakin fitowarta daga bakin Dadan ba. "Audi ya zo nan shekaranjiya ya faɗa min zasu je neman aurenki." Sunkuyar da kai ta yi batare da ta amsa ba. Dada ta ji wani abu ya taɓa mata zuciya sai dai kuma bata da hurumin hanata aure don ta taɓa auren ɗanta. "A matsayin ƴa na ɗaukeki Hafsatu ba don lamarin Arƙam ba babu yadda za'ayi na zuba miki ido kiyi ta zama babu aure." Ta numfasa sannan ta cigaba da magana "Audi ma ɗana ne idan kun haɗa kanku bani da abin cewa sama da yi muku addu'a da fatan alkhairi." Kai a sunkuye Haj Manga ta ce, "Dada nagode." "Idan kin gode Hafsatu to ku fito min da jikana." Dada ta ce lokaci guda tana fashewa da kuka mai tsanani. Dam! Haj Manga ta ji zuciyarta ta buga da ganin hawayen Dada. Ƙwarai tana jin tausayinta amma zuciyarta ta riga ta bushe ta yadda kukan ma sam ta kasa yi sai haƙuri da take ta bata. Sai bayan kimanin minti goma Dada ta sami nutsuwa, amma muryarta ta yi rauni sosai tana rawa ta kama hannuwan Haj Manga ta riƙe gam, "Kamar yadda na roƙi Audi kema ina roƙonki don Allah kada na mutu ban sake saka yaron nan a idona ba. Idan mutuwa ya yi ku faɗa min, na iya haƙura da iyayena, kakansa da mahaifinsa ma me zai hana ni haƙura idan shi ma ya koma ga Mahaliccinmu?" "Dada wallahi..." Girgiza kai Dada ta shiga yi "uhmm uhmm na gaji da rantsuwarku daga ke har Audi. Ba don mutuwa ta ɗauke min Ibrahim ba baku isa ku gwada min iko akan ƴaƴansa ba." "Ba haka bane Dada" Haj Manga ta sake jin wata muguwar tsanar Alh Audi zuciyarta ta cigaba da saƙa mata yadda za ta mayar da rayuwarsa abar kwatance idan ya kasa bayyana mata Arƙam, a raye! Washegari ta koma Abuja tare da Madam Zainaba, ta bar Jamal a wurin Dada. Sai dai gaba ɗaya tafiyar bata yi mata daɗi ba, bayan artabun da suka sha da Dada nan ma bata sake zani ba. Wata ƴar ƙanin Dada ce ta zo gidan ta sauke mata kwandunan rashin mutumci kala-kala. Ɗan uwanta daya kasance bangon jinginarsu take tayawa kishi ga zargin ta haɗa baki da Alh Audi sun ɓatar da Arƙam. Bata tanka mata ba ko sau ɗaya, sai ma Dada ce ta dinga ƙoƙarin tsawatarwa, ga kuma Madam Zainaba dake ƙoƙarin kare mata abin dai ya so ya koma rigima sosai. Tana daga gefe tana sakin murmushi, sai dai kowane furuci na matar tana ajiyeshi a mizanin da ya dace kafin ta waiwaye shi. Koda wasa bata bada ƙofar da za a fahimci maganganun sun taɓa ba, sai ma ƙoƙarin maida abin wasa da dinga yi. Sosai hakan ya ƙara mata martaba da ƙima a idon surukarta ta.