Kenza eBookz

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 3

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 3

Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 3: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 3. *** Duk wani abu da ya kamata a shirya anyi an gama. Wata biyu bayan zuwa…

12,778 words

*** Duk wani abu da ya kamata a shirya anyi an gama. Wata biyu bayan zuwa tambaya Maiduguri, su Alh Audi suka koma aka ɗaura aurensa da Haj Hafsatu Manga, akan sadaki mai tsada wanda ya biya da sulallan gwal. Taron ya sami halartar manya manyan ƙusoshin gwamnati, ƴan kasuwa da masu faɗa a ji a Najeriya da kewaye. Cikin kwana huɗu aka gama komai amarya ta tare a sabon gidanta dake unguwar Asokoro a birnin tarayya Abuja. Wata shidan farko Haj Manga ta sauke duka makaman yaƙinta ta nunawa Alh Audi kulawar da ta dace da ango irinsa. Shi kuma wannan kulawar ita ta susuta shi ya sami kansa da yi mata soyayya da zuciya ɗaya. Da yake abin da take so kenan sai ta ƙara bada himma wurin tattalinsa da na ƴaƴansa. Akwai mai reno da aka ɗauko musamman domin Kulsum, amma duk da haka kusan komai ita take yi mata. Tun yana zargin akwai ranar da zai kama ta da laifin cuzgunawa yarinyar a bayan idonsa har ya haƙura ya aminta da ita. Matsalarta guda ɗaya ce Shamsu idan ya zo hutun ƙarshen mako daga Gwagwalada. Kishi yake gwada mata na fitar hankali akan mahaifinsa. Shi ma kuma uban sai ta kula da takunsa, yana matuƙar gudun ɓacin ran ɗan nasa. Wannan abu bai ɓata mata rai ba ko kaɗan sai ma dariya da take yi a gefe. Wato shi da nasa ɗan suna son juna, ita da nata da aka rabasu ko su mutu ko suyi rai saboda kewa ba damuwarsa bace? Ta wannan fannin sai ta tattarasu ta watsar ta rungumi Jamal ɗinta. Makarantar kwana mai kyau ta maza ta samar masa saboda tana buƙatar nutsuwar aiwatar da abubuwan dake gabanta. Wata safiyar Asabar lokacin tana da wata bakwai a gidan ta fito ɓangaren dakunan samarin gidan. Abu take son tambayar Madam Zainaba dake ɗakin Jamal tana gyarawa saboda washegari za a basu hutu. Sanye take da wani lace ruwan madara mara nauyi anyi mata ɗinkin riga da skirt da suka yi wa jikinta kyau matuƙa. Haj Manga haɗaɗɗiyar mace ce wadda take bawa jikinta da suturunta mahimmanci kamar sauran al'amuran rayuwarta. Sassanyar iska ke busawa a hanyar saboda swimming pool da yake wurin tare da manyan bishiyun da suke gefe suna kaɗawa. Ɗakin Arƙam ne na farko idan an fito ƙofar ɓangaren nasu sai na Shamsu a tsakiya sannan na Jamal a ƙarshe. Cikin nutsuwa take tafiya har ta iso ƙofar ɗakin Shamsu, ba nufinta ta tsaya a wurin ba sai dai tashin muryoyin da take jiyowa yasa ta dawo da baya ta kara kunne. Alh Audi ne da ta yi tsammanin ya fita mintuna talatin da suka wuce da Shamsu suke sa'insa. Cike da zakuwa ta kalli hagu da damanta ta tabbatar babu kowa sai kawai ta buɗe ƙofar a hankali ta danna kai. Tana sanya ƙafa a cikin falon wata irin iska mara daɗi ta doki hancinta ba arziki tasa hannu ta toshe shi. Alh Audi da Shamsu suna daga cikin uwar ɗakin basu ji shigowarta ba ta lallaɓa ta raɓe daga bakin ƙofa yadda za ta jiyo su sosai. Daga yadda Shamsu yake magana za ka gane yana cikin fushi da ɓacin rai. "Kai fa ka ce min wannan maganin zai yi" Alh Audi ya miƙa hannu zai taba shi ya ja da baya, idanunsa sunyi ja sosai. Bai yi fushi ba ya sake miƙa hannu sai da ya riƙo hannun Shamsun na dama ya rufe shi da nasa biyu. "Kayi haƙuri, idan wannan bai yi ba zan sake neman wani." Dogon tsaki Shamsu ya ja Haj Manga a ranta ta ce 'ashe ba ni kaɗai ake yi wa ba?' Tana ji yana magana yana cin magani irin na marasa kunya "ni dai na gaji, saboda matsalar nan fa na yarda da karatu a kasar nan. Sannan duk yadda nake da abokai na amma na kasa barin kowa ya kwana a apartment ɗina. Wasu ma sun fara jin haushina ko ina wulakantasu ne saboda na rainasu" "Ka ƙara haƙuri Shamsu zan yi magana da Dr Madaki, idan maganin asibiti yaƙi sai mu koma na hausa" Alh Audi ya ce cikin rarrashi kamar yana tsoronsa. Wani tsaki ya sake ja zai yi magana Haj Manga ta tura ƙofar tana murmushi. So take idanunta su gane mata irin lalurar da ake ɓoyewa tsakanin uba da ɗan. Da murmushi a fuskarta ta dinga kallonsu tana ƙarewa ɗakin kallo. "Ashe kuna ciki ina ta sallama ba a amsa ba?" Rai a ɓace Alh Audi ya ce "mene ne ya shigo dake?" Shamsu kuwa fargaba ce ƙarara ta bayyana akan fuskarsa ya yi tsuru-tsuru dashi. Cikin halin ko in kula kamar bata ga sauyin yanayinsu ba ta bawa Alh Audi amsa, "Wani bashi-bashi nake ji daga waje shi ne na shigo in gani idan ɗakin ne babu gyara na turo Mercy" Ganin ƙofar rufawa kansu asiri ta bayyana gareshi ya yi saurin canja muhallin fushinsa zuwa ga Shamsu, "Kaga abinda nake faɗa maka ko? Saboda kawai kana taƙamar akwai masu aiki sai ka mayar da kanka ƙazamin ƙarfi da ya ji" ya shiga nuna kayayyakin da suke a yashe a tsakar ɗakin a wuraren da basu kamata ba. "Kinga fa yadda yake zubar da kaya kamar wani ƙanƙanin yaro." Dariya ce ta taho mata ta gimtseta da ƙyar. 'Wai ni zaku rainawa wayo' ta ce a zuci tana bin Shamsu da kallon ƙurilla. Sai da ta farga kamar su ɗin ma kallon da suke yi mata kenan ta yi saurin canja yanayinta zuwa na mai lallashi. "Kayi haƙuri Alhaji haka samarin suke yanzu. Zan turo Mercy ɗin ta gyara, sai ka fito." Ta juya tana aje takunta akan diga-diganta cike da ƙasaita. Ajiyar zuciya suka saki duka su biyun, hankalinsu ya soma kwanciya da Allah Yasa bata ga abinda basa so ta gani ba. Sai dai kafin su ankare ta kuma waigowa. Daga Alhaji har Shamsu sai da gabansu ya faɗi da inda ta kalla. Bata kula da yadda suka yi ba ta ce, "Uhmm! Alhaji, na ce fita kayi ka dawo ne ko kuwa tun sallamarmu ta ɗazu dama kana nan?" Haɗa kalmomi ya soma yi cikin gargadar harshe irin na marasa gaskiya "ni ko? Au ashe fa ban faɗa miki ba cewa naji labarin result ɗinsu ya fito shi ne nazo dubawa" Ta san sarai ƙwai ya saki sai ta dawo tana murmushi su kuwa gaba na faɗuwa "Shamsu ɗauko mu gani nasa albarka". Kawar da kansa ya yi gefe yana ƙunƙuni "shi ma Baban na faɗa masa bai fito ba." Dama bata sa a ka ba don ta san cewa ya dai faɗa ne domin kawar da hankalinta. Murmushi ta sake yi musu sannan ta kama hanyar fita tana jin muryar Alhaji yana sake nanatawa Shamsu wai ya dinga tsafta. Abinda ya fito da ita bata iya yi ba sai komawa da ta yi ciki tana tunanin me suke ɓoyewa? Wannan tunanin shi ya ɗauke mata hankali musamman ganin Shamsu ya bar gidan ranar da yamma maimakon Litinin da ya saba komawa makaranta. Maganar dawo da Fanna tana nan daram, Alh Ari ba da wasa yake yi ba. Ya aurar da ita har anyi sakin ta soma idda. Shi da Alh Audi suna ta ɓoyon shirinsu daga gareta sai gashi mahaifiyar Fanna ta tona. Haɗuwa suka yi a wani biki, irin abin nan na mata sai da ta bari wurin da mutane sosai ciki kuwa harda Haj Manga ta kada baki ta ce. "Daga wannan bikin kuma sai na komen Fanna fa. Ina gayyatar masoya, maƙiya da mahassada kowa yazo ya ga inda ake bikin ƴar gata." Matar wani minista sai ta kalli Haj. Kolo ta kalli Haj Manga cike da mamaki ta soma magana. "Aka ce saki uku ya yi mata har ta sake aure." "Inji wane sarkin maƙaryatan? Saki ɗaya ne jal!" Haj. Kolo ta bata amsa. Mata an sami abin da ake so cikin ƙanƙanin lokaci an kasa Alh Audi a faifai kowa tana tofa albarkacin bakinta. Babu wadda ta iya goyon bayan Haj. Kolo akan idon Haj Manga. To ai ido ba mudu ba ya san ƙima, laffayar jikinta kaɗai sai ta sayi suturar jikin wasu cikinsu harda jaka da takalmi duk da kuɗin mazajensu. Gefen bakinta ne kaɗai ya motsa ta yi murmushin nan nata sannan da ido ta yi wa Madam Zainaba alama. Sai da ta tabbatar ta fahimceta ta tafi isar da saƙo sannan ta ce da matan, "Ai mutuwar aure babu daɗi bare ga ƙaramar yarinya kamar Fanna. Shi ya sa saboda Kulsum na matsantawa Alhajina ya dawo da ita." Yabo ta soma sha daga matan nan aka bar Haj. Kolo da cizon yatsa. Takaicinta bai ƙaru ba sai da Madam Zainaba ta shigo da Kulsum a hannu. Bacci take yi a bayan mai rainonta ta karɓota tana kuka. Idanunta na sauka akan Haj Manga ta soma kokawar ƙwacewa daga hannun Madam Zainaba cikin gwarancinta take mika hannu. "Nanna za ta" Haj Manga ta tashi daga kan kujerarta ana binta da kallon burgewa, ta karɓota tana sumbatar kumatunta "waye ya saka babyn Nanna kuka?" Haj. Kolo dai tamkar ta haɗiyi zuciya saboda cin fuskar da taso yiwa Haj Manga kanta ya dawo. Ana ta faɗin maganganun da zasu yi mata ciwo kamar bata wurin. *** Saɓanin yadda ta nuna dakiya da halin ko in kula game da jin komen Fanna da Alh Audi ya dawo kuka ya sameta tana yi. Hankalinsa kuwa in ya yi dubu ya tashi ya yi juyin duniya ta sanar dashi damuwarta taƙi. Fita ya yi ya tura aka kira masa Madam Zainaba ta faɗa masa ƙarya da gaskiya. Nuna masa ta yi bayan Haj. Kolo ta yi maganar zai mayar da ƴarta sai aka haɗewa Haj Manga kai ana ta zaginta a bainar jama'a. Fuskarsa tuni ta kaɗa ta koma abin tsoro, a haka ya ɗauki waya ya kira Alh Ari ya sauke masa fushinsa tare da dogon gargadi. Ba don girman sirrin da Alh Arin ya sani ba da babu abinda zaisa ya sake auren Fanna. Duk abinda zai sosa ran Haj Manga baya ƙaunarsa. Burinsa ta kwantar da ranta su gina rayuwa mai daɗi fiye da wadda tayi da ƙaninsa. Idan zai sami haka babu abinda zai hana shi sake bada ƙaimi da jajircewa wurin nemo mata ɗan banzan yaron nan da ya jefa shi cikin zargin mutane. Ranar kwana ya yi yana lallashi tare da manyan alƙawarrurukana yadda zai fifita ta akan Fanna. Sai da ta yi nadamar fushin ƙaryar da ta tsira kuwa saboda yadda ta tsani ya dinga bibiyarta yana yi mata surutai. Da safe bayan ya fita ta kira Baffa Alƙali ta faɗa masa zancen auren da nuna rashin yarda da ta yi. Yana zaune a ofishinsa lokacin shi kaɗai ya yi murmushi, "Dama na faɗa miki akwai wata a ƙasa tsakaninsa da wannan Alh Ari, idan ba haka ba ban ga dalilinsa na goyon bayan aurenki bayan an sakar masa tasa ƴar ba." "To yanzu Baffa me ya kamata nayi?" "Kin yanke shawarar irin kasuwancin da zaki iya yi? Ko har yanzu kina tunanin cewa zaki iya tunkarar Alh Audi baki da kuɗi a hannunki?" Shiru ta yi bata amsa ba ya cigaba da cewa "Hafsatu da kuɗi ake neman kuɗi, you need power to face Alh Audi. Ki bar ganin ke da yaranki kuna da shares a Karam Holdings, wannan ba zai sauƙaƙa mana raba shi da kamfanin ba domin rama ɗaukan Arƙam." Har yanzu bai ji ta ce komai ba ya dan murmusa "Hafsatu kuka? Haba don Allah ki dena. Alh Audi ya yi kuskuren taɓa min jika har ya saka ki zubar hawaye. Amma a yadda lamura suke yanzu ko gawar Arƙam aka ɗauko a ɗakinsa ina mai tabbatar miki da cewa babu inda shari'ar za ta je bare a kai ga ƙwatar mana haƙƙinmu." Hawayen da take yi mara sauti ta goge da bayan hannunta tare da sake ƙanƙame wayar "Baffa lokaci ƙara ja yake yi..." "Kuma zai ƙara ja muddin baki sakawa zuciyarki haƙuri ba. Wallahi tunda aka kai yanzu Audi bai dawo da Arƙam ba kuma bai faɗi inda yake ba na tabbata ba za mu sami ganinsa nan kusa ba. You need to be strong Manga." Zuciyarta ke suya da ɓacin rai da tsanar Alh Audi, da ya zaɓi mutuwar mijinta a matsayin lokacin da zai rabata da ɗan da mijin nata yafi so sama da komai a duniya. Datse tunanin da ta san zai raunana mata zuciya ta yi ta tambayi Baffa matakin da za ta ɗauka yanzu. Cikin nutsuwa ya warware mata duka abinda ya tsara ta ajiye wayar tana murmushi. Alh Audi ya dawo da yamma ya sameta yadda ya barta a ɗakinsa. Babu wanka bare alamun ta fita ko wani ya shigo. Idanunta sunyi jawur ta yi kalar tausayi. Auren gabaɗaya yaji ya fice masa daga rai, ya saki briefcase ɗinsa a ƙasa ya tayar da ita daga kan gadon yana taɓa wuyanta ko akwai zazzaɓi. Bai ji komai ba don kuwa banda rashin wanka ƙalau take, abinci mai rai da lafiya ta take cikinta da shi tunda niyyarta idan ya dawo ko ruwa ba za ta sha ba. Ya shiga damuwa sosai da ganin yanayinta. Sai yanzu zuciyarsa take ƙara gaskata cewa hadda soyayyarsa ta hana ta aure ba saboda Arƙam kaɗai ba. Yafi kowa sanin abubuwan da suke gabansa masu girma amma tabbas mallakar zuciyar Haj Manga tana cikin sahun gaba. A wurinsa baki ya yi kaɗan ya kwatanta ta saboda duk inda ake tunanin mace ta wuce. "Tashi ki yi wanka zan kira Dr. Madaki yazo ya min duba ke" Tabe baki tayi tana ture hannunsa "ni ka kyaleni idan ma sonka da kishi zasu kasheni ai baka da asara." "Haba Hafsa me ya kawo zancen mutuwa kuma?" Ya ce a gigice. Hafsan da ya kirata da shi ya sake bata haushi. Duniya Ibrahim kaɗai yake kiranta Hafsatu sai ko Baffanta. Ba ta son jin sunan a bakin Alh Audi ko kaɗan. Fashe masa da kuka ta yi don ta sake ɗaga masa hankali. Tun yana lalashi da baki har ya gaji ya ɗauko cheque book ɗinsa. Zaman dirshan ya yi a gabanta a ƙasa cikin nan nasa shima ya samu wuri ya yi balance. "Nawa kike so na baki kiyi abinda kike so dabshi?" Fuskarsa ta kalla zuciyarta fal murna kafin ta nemi kuɗin da Baffa ya ce shi ya bata da kansa. Amma sai ta nuna kamar ya yi mata laifi da yake tunanin kwantar mata da hankali da kuɗi. "Ba kuɗinka nake so ba kaima ka sani." "Na sani to faɗi abinda ki ke buƙata" ya ɗauke littafin zai ɗora akan centre table ta yi saurin dakatar da shi. Wani irin kallo ya shiga jefa mata tamkar mai son karanto cikin zuciyarta. Yanayin kallon nasa sai ya takurata ta gane ta kusa bada kanta. Ba shiri ta wayance tana yi masa hararar wasa. "Ku maza yanzu haka ku ke yi ne? Idan kuna neman aure sai kuyi ta yiwa ta gida kyautar babu gaira babu dalili" Dariya ta bashi yadda ta yi da fuska ya ce "Ku ɗin ne sai ana lallaɓaku." Ɗan littafin ya sake buɗewa "blank cheque zan rubuta miki na san ba za ki rubuta abinda zai gurgunta ni ba" "Da gaske kake Alhaji?" Bai ce komai ba sai takardar da ya sakawa hannu ya yago ya miƙa mata. Karɓa ta yi tana masa godiya da ƙorafin kada ya ga ta karɓa ya yi murna. Tayi ne kawai saboda ta san cewa itama Fanna yana kashe mata kuɗi. "Mata sarakan kishi, tashi kiyi wanka mu ci abinci Hafsatuna" 'Wai Hafsatunsa? Allah Ya isa!' ta ce a zuci. A zahiri ta sakar masa kyakkyawan murmushi sannan ta mike zuwa banɗaki. Ita kanta yau taji babu daɗi saboda ta wuni ba wanka. [2/23, 7:34 PM] Nasma: Kuka Tauhidat ta saka Shalewa ta tafi domin taimaka mata, Susu da Minasco kuma su ka nemi hanyar gudu ashe health prefect Ganiyat Saliu ta ga abin da ya faru duk da bata alaƙanta abin da bambancin yare ba. Ita dai kawai abinda ta yi tunani cin zali ne da nuna iko tunda sun shiga senior class abinda makaranta take ƙoƙarin daoilewa saboda ƙorafin iyaye. "Kneel down there" ta ce da ƙarfi tana tahowa wurin da bulalarta a hannu saboda yau ita ce da duty. Susu da Minasco sun mugun tsanarta saboda itama bayerabiyar ce. Aƙida mara tushe su ka ɗorawa kawunansu saboda yanayin yadda garuruwan ƙasarmu su kan nuna naka-naka ne sauran ƙabilun ƙasar ba mutanen kirki bane. Da kanta ta ɗago Tauhidat daga cikin taɓon, sannan ta nemi jin ba'asi. Tashin farko Susu sai cewa ta yi bata kula bane ta tureta. "Ƙarya kike yi, saboda naga lokacin da kika daketa" cewar prefect ɗin sannan ta ɗaga hannu ta yafito Shalewa "ku je ta cire kayan ki kawo min su nan yanzu in bata ta wanke" ta ƙarasa furucin tana nuna Susu. Jin haka yasa ta ɓata rai, ta soma magana ciki-ciki tana murguɗa baki da juya idanu irin na tsagerun makaranta "tabɗi, ni zan wanke mata kaya? To wallahi gara ma ki min bulala na yi tafiyata akan na taɓa ƙazaman kayanta." Daga nesa kaɗan dasu Head girl Alawiyya ta hango abin da Susu take yi, ranta ya ɓacci kuwa. Da ita Suwaida take taƙama a matsayin yayarta saboda kasancewar iyayensu mata ya da ƙanwa ne. Sai dai kuma halinsu ya sha bambam, har ta kai Alawiyya lokuta da dama ta kan ji kunyar ace su ƴan uwa ne ma. Rashin kunya da gadara kamar ƴar wani hamshaƙin maikuɗi. Tahowa ta yi wurin gadan-gadan Susu ciki ya soma hautsinewa saboda Alawiyya bata da sauƙi akan bada horo ga masu laifi. Tana zuwa kuwa ta tambayi Ganiyat ta faɗa mata abinda idonta ya gani. Shalewa ma ta faɗa duk da mugun kallon da su ke watsa mata na zamu gamu dake. Alawiyya sai ta kama hannun Tauhidat ta saki fuska ita ma a zatonta bahaushiya ce ta ce "maza ki ciro kayan a wanke, kina da wasu ko?" Murmushin da ya bayyana kyakkyawar wushiryarta ta yi, har ta manta da abinda aka yi mata saboda yarinya ce mai saurin sabo da sakewa da mutane "eh guda uku Papa ya ɗinka min, kuma hadda wasu ance sai babu class in saka. Suna akwatina." Dariya Minasco ta yi a hankali a daidai kunnen Susu ta ce "mun sami story teller fa, irin wannan zubo zance daga tambaya daya?" Sunanta Alawiyya ta tambayeta ta faɗa har lokacin da murmushin nan a fuskarta ba ta ɓoye mamakinta ba kuwa ta ce mata "ashe yarenku ɗaya da Ganiyat amma kin fita iya hausa sosai". Suka yi dariya ita da Ganiyat ɗin. Kai ta gyaɗa cike da jindaɗi ta ce "Broda Shaheed ya fini iyawa, ni kuma na fishi iya yarbanci." Har zuciyarta Alawiyya sai ta ji yarinyar ta bata sha'awa. Ita da Ganiyat suka haɗata da Shalewa ta je ta cire kayan da su ka ɓaci. Susu kuwa kamar ta mangareta duk wannan murmushin da take yi har tana ayyanawa ko akwai taɓin hankali a tare da ita, idan ba haka ba babu wani alamun fushi akan tureta da ta yi sai sakin baki take tana faman zuba surutu. A ɓangaren Tauhidat tahowarta makaranta abu ne da ta daɗe tana mafarki. Kullum idan yayanta Shaheed zai koma makaranta ƴan kayan provision da ake haɗa masa sune suke tsole mata ido saboda akwaita da son zaƘi. Sai dai kuma duk soyayyarta da tafiya bodin ranar tahowa makaranta anyi daru da ita kamar me, taci kuka ta gode Allah. Tunda take bata taɓa barin mamanta ba kullum suna tare. Aunty Bimbo mai abinci kamar yadda ƴan unguwarsu ke kiranta ta yi ta fama da haihuwa yaran har uku na mutuwa tsakanin Shaheed da Tosin shiyasa ta ke shagwaɓata son rai tana yi mata gata. Sunanta ma Oluwatosin yana nufin kyautar Allah sai dai a gida kaɗai ake kiranta da sunan, a waje musamman makaranta Tauhidat ake kiranta. Duk abinda Bimbo ta samu burinta ta fito da Tosin dinta ta yi kyau, shiyasa ta ke tsaf da ita. Asalinsu mutanen Abeokuta ne ta jihar Ogun zama ne da neman arziƘi ya kawo iyayen Abayomi mahaifinta Gombe har aka haifeshi da ƙannensa. Lokacin da su ka tashi komawa gida shi kaɗai ne yake aikin direba a gidan wani Sanata sai yaƙi binsu. Ga shi anyi masa aure da Bimbo ƴar garinsu tana fama da tsohon ciki. A hankali ita ma ta saba da zaman. Bayan Sanata ya sauka ƙuncin rayuwa ya fara dukansa sai ya sallami da yawa cikin ma'aikatansa, azal ta faɗawa Abayomi hadashi. Da yake Aunty Bimbo akwai zafin nema sai ta buɗe gidan abinci a bakin titin unguwarsu. Tana yin ƙosai mai daɗi da safe da rana zuwa biyar na yamma kuma ta yi amala, tuwon semo, sakwara, teba da miyoyinsu kala-kala na ganye, kuɓewa, ogbono ta saka kifi ko nama da ganda. A gefen shagon Abayomi ya samu yake yin faci da buga iska sannan shi yake zagayawa bayan shagon ya daka mata sakwara. Da Shaheed ya kawo ƙarfi shi ya karɓi dakan. Tauhidat a shagon nan ta buɗi ido tun ƙananan shekaru ta goge sosai da irin girke-girkensu. Yarinya ce kyakkyawa wankan tawarɗa ga ɗan jiki irin wanda turawa ke kira chubby. Bakinta ɗauke yake da wushirya wadda da wuya take ɓuya saboda tsabar murmushi da yawan fara'arta. Idan ka ga fushinta to lallai abu ya yi tsamari. Bata da gashi sosai amma a cike yake ga wahalar gyara. Wannan dalilin yasa Aunty Bimbo ta yi masa kwas-kwas da za ta taho makaranta. Askewa mata kai ba komai bane a wurin cikakken bayerabe. Bayan ta cire kayan Ganiyat ta bawa Susu wankinsu, Minasco kuma Alawiyya ta haɗata da masu dawowa makaranta a makare aikin nome ciyayi. Wannan lamari shi ne matakin farko na assasa ƙiyayyar Susu ga Tauhidat. A ganinta ci baya ne da raini a saka ta wankin kayan ƴar jss1 kuma mutane da yawa sun sani. *** Kwanaki huɗu kenan da Alh Audi ya juya akalar ƙudirin Haj Manga ta hanyar yi mata bazata ya ƙwace plazar da ta wahala wurin ganin kafuwarta. A ranar da aka yi taron kafin a tashi taji kirjinta yana suya ga wani azababben ciwon kai ya far mata lokaci guda. Bata nemi kowa ba domin gabaɗaya duniya gani take babu wanda kuma ya cancanci ta amince da shi ɗari bisa ɗari sai ƴaƴaan cikinta. Jamal ta tura ya samo musu taxi drop zuwa airport. Shi ma ɗin ƙuruciya bata rufe masa ido ya kasa fuskantar cin zarafin da aka yi wa mahaifiyarsa ba. Ya so yiwa Baffa Alƙali magana kafin su tafi amma ta hana. Sun daki gurbi kuwa domin basu sami jirgi ba, aka sanar dasu jirage masu zuwa Abuja sun gama tashi a ranar sai washegari. A yadda Haj Manga take jin jikinta ya ɗauki zafi sake kwana a Lagos ba zai yiwu ba. Tasha ta umarci Jamal ya samo mota ta kaisu ya shiga roƙonta da ta yi haƙuri sai gobe. Cikin fushi ta hau shi da faɗa, dolensa ya bi umarninta awa guda basu rufa ba suka ɗauki hanyar Abuja a wata peugeot da ta yi musu shata su kaɗai. A baya ta zauna ta zurfafa a tunani har bata san lokacin da hawaye ya dinga ambaliya akan fuskarta ba. Rabonta da kuka irin wannan tun daren ranar da ta kudiri niyyar auren Alh Audi. Sai yanzu ma take ƙara godewa Allah da bata gayyato kowa daga Kano ba. Ta yi haka ne domin gujewa magana akan Arkam, amma da a gabansu aka yi mata wannan dibar albarkar bata san inda za ta saka kanta ba kuma. Tafiyar gabansu ba ta wasa bace, domin ba su suka isa Abuja ba sai ƙarfe biyar saura na asuba. Tana saka ƙafarta a cikin gidan da gudu-gudu ta hau sama zuwa ɗakinta. Ko takalmi bata cire ba ta tafi ta durƙusa a gaban wakekiyar wardrobe ɗinta. Wani akwati ɗan ƙarami ta janyo daga ƙasan ta buɗe cikin sauri. Gabanta ya yi mummunar faɗuwa kuwa, envelop ɗin da take ganin zai zame mata garkuwa wurin juyar da abinda Alh Audi ya yi mata babu shi babu dalilinsa. Zazzage akwatin ta shiga yi tamkar mahaukaciya tana barbaza sauran takardun. Komai nata yana nan, envelop ɗin mai ɗauke da takardun shaidar mallakar fili, takardar izinin ginin da ma ta rigistar sunan wurin a matsayin wurin kasuwanci shi kaɗai ne babu. A take zafin ƙirjinta ya ƙaru ta yi zaman ƴan bori tare da tuge ɗankwalinta, ƙananun kitson barebarinta suka bazu a gefen fuskarta. A hankali wani irin sanyi ya shiga ratsata ta sulale a wurin a sume. A can Lagos kuma ko minti biyar basu yi da barin wurin ba Madam Zainaba ta fara nemansu. Ta yi ta kiran wayoyinsu ita da Jamal duka a kashe sai hankalinta ya tashi. Tunaninta bai kawo mata komai ba sama da sun koma gida. Cike da tausayin uwarɗakin nata ta dinga kutsa kai tsakanin mutane zuwa inda ta hango Baffa Alƙali yana magana da ƴaƴansa. A ladabce ta faɗa masa Haj Manga ta tafi. Shi ma wayar ya kira yaji shiru ya cewa ƴaƴan nasa su zo su tafi wurinta. Suna zuwa tun a bakin gate ya tambayi masu gadi aka sanar da shi babu wanda ya shigo gidan tun bayan fitarsu ɗazu. Nan fa hankalinsu ya ta shi kafin magariba kowa ya san ba a gansu ba. Ana kiran isha sai ga motocin ƴan sanda sun shigo gida. Alh Ari ne ya ɗaukosu wai ana zargin an sacesu ne a wurin taro. Baffa sai ji ya yi Alh Audi yana musu bayani. Fuskarsa ta nuna damuwa sosai kana ganinsa duk ya firgice da alamun alhini ya ce "kwanaki uku kenan tana faɗa min idan ta fita tana jin kamar ana bin bayanta." Ya ja hanci harda kaki ya tofar da majina a gefe sanna ya cigaba "na ɗauki abin wasa har ina cewa ta fiye tsoro ashe gaske ne. Officer ko nawa ku ke bukata zan bayar ni dai kawai a nemo min matata da ɗana." Ana haka Alh Ari ya amsa waya ya fita, bai jima ba ya dawo tare da ma'aikatan gidajen talabijin na NTA, AIT da DBN sun zo neman rahoto game da sace matar Alh Audi Karam. Abin ma sai ya bawa Baffa Alƙali dariya. Zuciyarsa tuni ta ba shi komai lafiya sai dai ɓacin rai yasa ta yi nisa da gida. Ya tabbatar hakan ba dabara bace domin kuwa Alh Audi amfani zai yi da wannan damar ya turbuɗe fuskarta da ƙasa. Hakan ce kuwa ta faru aka saito kemara da loudspeaker daidai fuskarsa idanunsa jazur yana amsa tambayoyin ƴan jarida. Tambayar farko daga wata mace cikin masu ɗaukan rahoton ita ce "Sir, me za ka iya cewa game da ɓatan matarka Haj Hafsatu Manga Bukarti?" Daga shi sai ƴar ciki da dogon wando ya cire coat ɗin ya kalli kemarar yanayinsa abin tausayi yana sadda kai ƙasa ya ce, "ɗazu na yi tunanin ko wani mugun abu ne ya faru amma yanzu na fahimce kamar ba haka bane, ina zargin kaina da ɓata mata rai har ta yi fushi." Baffa Alƙali zama ya yi don ba shi da ƙarfin jure tsayuwa yana kallon ikon Allah. Da wani namji ya tambayi Alh Audi da ya yi musu fashin baƙi akan abinda ya ce sai ya duƙar da kai yana magana. "Kamar yadda ku ka sami labari yau ake bikin buɗe plaza da na gina da sunan ƴaƴana. Alal haƙiƙa komai na ginin nan kama daga sayen fili zuwa kammaluwar abinda kuke gani Haj Manga ce ta yi. A yadda na tsara komai zamu mallakawa ƴaƴanmu wurin ne." "Yallaɓai wadanne ƴaƴa kenan? Naka ko nata? Mun san cewa yaranta biyu na ƙaninka ne." Alamun ɓacin rai Alh Audi ya nuna kafin ya bada amsa. "Ƴaƴan ƙanina ba nawa bane? Ni idan ina ƙirgen ƴaƴana huɗu nake cewa. Duk da cewa nawa biyu ne ita ma nata biyu. Kamar yadda nake muku bayani niyyata na mallaka musu wurin su huɗun. Sai aka sami akasi wanda aka bawa kwangilar yin banner ɗin sunan wurin jin ance ƴaƴana sai ya saka farkon sunan Shamsu da Kulsum. Mun riga mun saba aiki da shi, cewa na yi kawai ya saka farkon harufan sunayensu." Katse shi aka yi daga gidan TV na DBN inda mutumin ya ce "amma kowa ya ji lokacin da ka ce S & K palace na ƴaƴanka ne." Ko ɗar bai ji ba ya ba shi amsa da cewa "nima ba ƙaramin mamaki na yi ba da Shamsu ya buɗe naga harufan basu cika ba. To amma abu na mutane da yawa ga ku ƴan jarida da na nuna kuskuren daga gareni ne ban sa an duba banner ɗin ba an tabbatar komai daidai kafin a fara taron sai ace Alh Audi is careless..." ya yi wata siririyar dariya. "Gudun haka yasa na gabatar da shi da sunan da yake jiki tare da niyyar gyarawa idan an gama. Na san dole ta ji haushi tunda tun farko na faɗa mata harda nata yaran. Kun san matan nan ba dai kishi ba, gani za ta yi kamar na ware nata" ya kuma yin dariya a zuwan wasa yake yi. "Haɗin gwiwa kenan ku ka yi na kuɗin da aka yi komai dasu?" Wani ya sake tambaya. Murmushi ya yi wannan karon, irin murmushin nan da yake nuni da mutum bai ɗauki kansa komai ba. "Ko kaɗan, kuɗi dai nine na bata domin kyautatawa da kuma ganin ita ce uwargida sai na bar mata ragamar a hannunta." Mutanen da suke wurin cikin ƴan uwansu Fanna da abokansu suka soma ƙananun maganganu. Alh Audi ya ƙare jawabinsa da ban haƙuri ga uwaigida sarautar mata. Jama'a sun jinjina masa yayin da ƴan jaridar duka suka matsa gefe domin ƙarƙare rahoton ta hanyar jawabin ƙarshe. Dukkaninsu sun ƙare bayanansu da nuna cewa Haj Manga bata kyauta ba saboda ta yi hukunci cikin fushi. Za su cigaba da bibiyar binciken ƴan sanda har zuwa lokacin da za a ganta. Bayan tafiyarsu Alh Audi ya ƙarasa inda Baffa Alƙali yake zaune ya durƙusa a ƙasa yana ba shi haƙuri. Takarda Tony PA ya miƙo masa ya warware a gabansa sannan ya nuna masa. Kallo ɗaya Baffa ya yi mata ya ƙaƙalo murmushin ƙarfin hali ya ajiye a saitinsa. "Allah Ya tayasu riƙo, haɗasu su huɗun zai ƙara musu zumunci ai." Daga haka bai ƙara magana ba ya ta shi su ka tafi masaukinsu shi da su Ali. Kafin gari ya waye duk wanda ya kalli AIT ko NTA a ranar da wahala idan zuciyarsa bata cika da tausayin Alh. Audi da jin haushin Haj. Manga ba. Da yawa kallon mace mai kishi da son kai suke mata. Saboda anyi kuskuren cire sunan nata ƴaƴan shi ne ta gudu daga wurin taro don baƙinciki. *** Wuraren takwas na safe ta buɗe ido ta ganta kwance akan gadonta, an ɗaura mata drip a hannu ga Jamal yana ta gyangyaɗi daga zaune akan gadon saitin kanta. Ciwon kan nata ya yi sauƙi sai nauyin jiki. Tambayar Jamal take shirin yi me ya sameta ya ta shi ya fita. Bai daɗe ba suka dawo tare da Dr. Samson Madaki da ɗaya daga cikin masu aikin gidan. Da taimakon Jamal ta zauna bayanta jingine da pillow. "Jamal bamu wuri ko..." Dr. Madaki ya ce da shi. Fita ya yi yana kallon mai aikin da nufin ta fito itama. Likitan sai ya girgiza kai ya nuna ba sai ta fita ba. "Doctor me ya sameni?" Haj. Manga ta tambaya a raunane. "Hajiya kina wasa da lafiyarki gashi cikin jikinki yana gab da zubewa." Wannan ita ce amsar da ya bayar wadda ta girgizata. Yana lura da yadda mai aikin tasu ta wangale idanu da baki don mamaki da gulma. Ita kuwa tamkar an watsa mata ruwan zafi ta ce, "Ciki ne dani? Garin ...." Bai barta ta ƙarasa ba ya katseta da sauri, "na sani muna iya ƙoƙarinmu domin ganin cikin nan ya zauna. Amma laifina ne, da na san cewa ba kya gari ba zan kiraki ba. An bani tabbacin cewa maganin yana taimakawa matan da ciki yake musu barazanar fita shi ya sa nace ki taho asibitin saboda aiki ya yi min yawa." Mamaki kasheni in ban mutu ba ta ce da kanta a zuci. Gabaɗaya maganganun Dr. Madaki babu wadda ta yi ma'ana bare ta fahimta. Mai aikin bata kula da ruɗanin da ya bayyana akan fuskarta ba ta fita bayan likitan ya bata umarnin taje ta kawo mata farfesu. Da azama don kada a ci gaba da bayani bata ji ba ta ce, "Akwai na kaza yanzu na gama dama." Dakatar da ita ya yi, "Ba shi ya kamata ta sha ba." Ta murmusa, "Akwai na kayan ciki dana kifi duka da safen nan muka yi saboda ance su Alhaji zasu iso da wuri." Sai da ya nemi wanda bata ce akwai ba ta ce, "Na kashin rago take buƙata. Kiyi sauri kinji, sannan ki tabbatar ya dahu sosai." Suna jin guntun tsakin da ta saki ta fita rai a ɓace. Ita ce babba cikin sababbin masu aikin gidan, saboda haka ita kaɗai ke da damar shiga dakunan matan gidan. Tana fita Dr. Madaki ya soma yiwa Haj. Manga bayanin da Baffa Alƙali ya yi masa tun daren jiya. Baki ta buɗe cike da tsantsakar mamakin ƙarfin halin Alh. Audi. Wato juya komai ya yi kanta don ya ɓata mata suna bayan rashin adalcin da ya yi mata? Da ya kula cewa ta shiga tashin hankali sai ya fara faɗa mata shawarar da suka yanke da Baffanta. "A labaran NTA naga komai lokacin kuna hanya ba sani zaki yi ba. Ki kwantar da hankali mun riga mun ɗinke duk wata ɓaraka da tahowar taki ta janyo. Abu ɗaya za ki riƙe shi ne cewa kina da ciki kuma yana baki matsala. Ni kaɗai na san da shi saboda kina gudun kada Alhaji ya ƙwallafa rai kuma ya zube. A jiya na kiraki na faɗa miki an kawo min maganin da nace zai taimaka miki wurin zaunar da cikin..." "Amma Doctor ka rasa abin cewa sai ciki? Da shekaruna ga kuma history na matsalar da na dinga samu bayan Jamal na rashin zaman ciki, gaskiya wannan shawarar babu mai karɓa." Ta ce tana girgiza kai. Ɗan dattijon likitan murmushi ya yi mata "waye yace miki mata basa haihuwa da shekaru arba'in da biyu? Ina da magani da aka kawo last week na matsala irin wannan. Ke dai kawai ki tabbatar kinyi abinda ya kamata a gaban ƴan jarida." Tana jin ya ce ƴan jarida ta yaye bargon da aka rufeta ta miƙe. Fita ya yi daga ɗakin tayi wanka da sauri ta yi sallolin da ake binta bashi. Bayan ta gama shiryawa ta kunna wayarta ta kira Baffa da Alh Audi wayarsu bata shiga, ashe suna jirgi sun taho. Saƙon text ɗin Baffan ta gani wanda yake yi mata bayanin shirinsu da Dr. Madaki. Abin sai ya ɗaure mata kai saboda a iya saninta likitan Alh. Audi ne kowa ya sani. Yaushe suka haɗa kai da Baffa da yake Maiduguri bata sani ba? Shaɗaya na safe gida ya cika. Alh Audi da muƙarraban Alh Ari sai su Baffa da wakilan NTA guda uku da aka turo domin jin ta bakin Haj. Manga. Fanna tana gefe tana cika tana batsewa tuni labari ya risketa cewa ciki ne da Haj Manga. Harara ta dinga jefawa ɓangaren da take zaune akan kujera sanye da jallabiya ta yafa babban mayafi ga fuska fayau. Tambayarta reporter ɗin ya yi dalilin biyo motar haya da yamma daga Lagos zuwa Abuja ba tare da sanin mijinta ba. Kallon fuskar Alh Audi ta yi ya kafeta da idanu babu fara'a ko kaɗan a tare dashi. Wani irin juya idanu ta yi ta murmusa kafin ta soma magana. "Jiya babbar rana ce a garemu da duka masu ƙaunarmu. Bayan shafe lokaci ina ta kai kawo wurin ganin komai ya tafi daidai kaga ba zan so saboda raina ni ɗaya taron ya lalace ba. Na tabbatar da na faɗawa Alhaji wayar da Dr. Madaki ya yi min shi ma ba zai zauna a wurin ba, ga baki mun tara daga wurare daban-daban. Tsoron da naji ni kaina bai wuce jinin da nake zubarwa ba sakamakon rashin hutun da aikin ya jawo min." Reporter ɗin ya ce "idan na fahimceki dai rashin fahimta ce ta jawo aka yi tunanin wani abu ne ya sameki jiya. To amma me ya hanaki sanar dasu a waya ko ki faɗawa PA dinki Madam Zainab sunanta ko?" Murmushin da yafi na ɗazu ta saki "Madam Zainaba tana da ruɗewa, idan na faɗa mata kana ganin ba za ta sanar da Alhaji ba? Wayata da ta Jamal duka ni na kashe. Kai namiji ne ba za ka fahimta sosai ba amma ga mace ta san cewa babu irin wahalar da bama jurewa domin kula da ciki da ƴaƴanmu." "Ko kina da saƙo na ƙarashe ga mutanen da suka shiga tashin hankali a daren jiya?" "Ƙwarai kuwa, nagode musu Allah Ya saka da alkhairi. Ina kuma roƙon afuwarsu saboda naso kaina batare da bayar da gamsashshen bayani ba na kamo hanya. Saboda kada na bata taron shiyasa ko direba ban nema daga gidan ba. Ka san idan mace ta daɗe bata haihu ba sam bata ji bata gani." Ta share ƴar ƙwallarta tana yamutsa fuska kamar wadda take cikin ciwo "ban san da cikin da wuri bane ina ta faɗi tashi akan aikin nan da zan kula da jikina yadda ya kamata." Kafin a ɗauke kyamarar daga kanta ta riƙe ciki tana jujjuya idanu. Dr Madaki ya taho da sauri yasa aka kamata.Ƴan jarida dai hankalinsu a tashe suna biye da motar da aka sakata zuwa asibiti. Alh Audi da Alh Ari basu da zaɓin da ya wuce bin bayansu. Su duka biyun an rasa me yin ko tari a motar saboda mamakin da suke ciki. Wannan shi ake cewa reshe ya juye da mujiya. Zaman rabin awa suka yi sannan Dr Madaki ya fito ya sanar dasu cewa, sai dai ayi haƙuri ta yi ɓarin cikin wata uku na ƴan biyu. Zuwa yanzu ƴan jarida sun ƙaru ana ta yabawa jarumta irin ta Haj Manga. Tana cikin wannan yanayi amma saboda kada ta ɓatawa mijinta shirinsa ta yi ta dauriya gashi cikin da take ta wahala a kansa ya zube. To yanzu kwanaki huɗu kenan ƙura ta lafa. Takardun plaza har yanzu babu su babu dalilinsu. Baffa ma ya koma Maiduguri bayan dogon jan kunne gareta akan ta kiyaye daga nuna wani canji ko yaya a fuskarta. Ya kuma ƙara mata da ta dena komai ta yi zaman jinyar barin karyar da ta yi kafin ya san me ya kamata su yi a gaba. Game da alaƙarsa da Dr. Madaki kuwa ya sanar da ita cewa ta kwantar da hankalinta. Duk abinda yake da yaƙinin zai yi mata wuya, zai tsaya mata akansa. Ya ƙara tabbatar mata kada ta manta, tana da uban da zai yi komai domin ganin walwalarta. Maimakon hakan ya kwantar mata da hankali sai ta sami kanta da yawan tunani. A iya saninta babu wanda ya san inda ta ajiye takardun nan sai Madam Zainaba, idan kuwa haka ne kenan da ita aka haɗa baki wurin cutar da ita. Sai dai kuma silar haɗuwarsu tun farko ta sanya mata wasiwasin anya kuwa za ta cuceta? Da abin ya isheta bayan ƴan kwanaki sai ta yi mata izinin zuwa garinsu ganin ƴaƴanta da ƴan uwa. Da yake bata nuna mata cewar maganar ɓarin ƙarya bane sai ta so kin tafiya a cewarta za ta buƙace ta. Haj Manga sai da ta yi da gaske wurin nuna mata cewa ta warke ta bata sati uku taje ta zaga dangi. Ranar tafiyar bayan Madam Zainaba ta gama shiryawa ta sauko wani ni'imtaccen falo a ƙasa inda Haj Manga take zaune. Sallama tazo suyi Haj Manga ta ce ta koma ɗakinta akwai atampopi a wata leda ta ɗauko. Tana hawa saman ta janyo jakarta ta ɗauke mata waya ta mayar da ita inda ta ɗauka sannan ta kashe wayar. Da ta dawo sai ta bata guda uku a ciki ta kaiwa ƴan uwanta mata. Godiya Madam Zainaba ta yi sosai saboda irin shatara ta arzikin da ta haɗa mata. A hanya ta farga da rashin wayar tana isa gidansu ta karɓi wayar babbar ƴarta ta kira Haj Manga. Bayan sun gaisa take faɗa mata an sace mata waya. "Wani tsinanne ne ƙila ya ɗaukar min a mota. Yara za su yi ta gwadawa ko zamu same shi" ta ce cike da takaici. Tsinuwar nan har zuciyar Haj Manga sai cewa take ba dai ni ba. Haƙuri ta bata da alƙawarin saya mata sabuwa idan ta dawo. Cikin aminci suka yi sallama. Da daddare misalin shabiyu da rabi ta tashi ta kunna wayar ta shiga dube-duben sakonnin da suke ciki. Idan ka cire nata sauran yawanci daga yaranta ne. Duka nambobin Alh Audi da ta Alh Ari ta saka a wayar ta gwada kira amma suna bai bayyana ba. Alamu sun nuna babu hannun Madam Zainaba, to waye kuma yake bibiyarta? Gari na wayewa Alh Audi ya shigo kamar yadda ya soma tunda aka ce ta yi bari wai ya zo dubiya. Kadaran-kadahan ta amsa ya tashi ya fita yana yi yana waigenta. Gabaɗaya ta zame masa abar tsoro tunda ta iya mummurɗa magana yanzu har yi ake dashi wai ya yi amfani da ita kuma don wulakanci aka saka sunayen nasa ƴaƴan kaɗai. Sai da ya tafi ta sauka ƙasa sanye da riga da zani na atampa ta yi ɗaurin ture ka ga tsiya. Fanna tana zaune da Kulsum amma ganinta yasa ta tashi da ƴarta tana buga tsaki. "Ba kya gabana ƙaramar alhaki." Haj Manga ta ce bayan ta zauna a falon ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana karkaɗata. Kana ganinta tamkar wata jinin sarauta tana riƙe da waya a hannu. Minti biyar bai cika ba da fitar Fanna taji motsi kamar mutum yazo bayan ƙofar falon. A hankali gefen bakinta ya motsa ta murmusa sannan ta ɗauki waya ta ɗora a kunne a zuwan da Madam Zainaba take yi. Doguwar hira ta rinka yi ita kaɗai kafin daga bisani ta ce, "Yauwa maganar file ɗin nan na takardun filaye a ina ki ka ajiye min ne?" Jim ta yi kamar tana sauraron amsa sannan ta sake cewa, "Okay suna cikin akwatin nan ko? Nagode Zainaba." Ta sake yin shiru na ɗan lokaci ta kuma ɗorawa "kada ki damu har yau ko Jamal bai san inda nake ajiye akwatin ba. Alhaji kuma zan bashi mamaki tunda suna hannuna dasu zan yi amfani wurin kwato plaza ɗin." Rifkatu mai aiki ta naɗe komai ta garzaya ɗakin Fanna ta kai mata rahoto. Gigicewa ta yi tunda ta san sun ɗauke takardun plaza ɗin. Idan akwai wasu Alh Ari sai ya ci mata mutumci yace bata aiki da nutsuwa. "Maza jeki ki ɗauko min akwatin da sauri kafin ta hawo." Da Rifkatu ta tafi kai gulma Haj Manga ta koma ɗakinta. Banɗaki ta shiga ta ɗan buɗe ƙofar kaɗan, yadda za ta hango cikin ɗakin. Can sai gata ta shigo kai tsaye alamun ba yau farau ba ta nufi gaban wardrobe din ta durƙusa. Sai da ta janyo akwatin sannan Haj Manga ta fito gadan-gadan ta yi kanta. Idanu a waje, ciki ya ƙulle kamar ta saki zawo, ta tashi jiki na rawa za ta gudu. Kafin ta yi taku uku Haj Manga ta damko wuyan rigarta ta juyo da ita ji kake tas, tatas...tas tana surfa mata lafiyayyun maruka. A gigice take kurma ihu saboda azaba sai ga Fanna ta shigo dama tana kusa. Idanun Haj Manga da ta gani ita kanta sai da nata cikin ya tsirga kafin ta fara tambayar me ya faru. Cikin ƙaraji Haj Manga ta haɗasu da Rifkatun ta ƙare musu tanadi. "Kun ajiye ɓarayi a gida ba dama na yi ajiya sai an ɗauka. Wannan wace irin masifa ce?" Rifkatu ta rufe bakinta da yake zugin mari a tsorace ta nuna Fanna "Maman Kull..." Caraf Fanna ta kama yatsan da yake nunota ta hanata ƙarasa magana "dan ubanki ashe kece barauniyar gidan nan ban sani ba? Ina awarwarona da nake ta nema?" Haj Manga sai da ta yi dariya duk yadda taso daurewa. Da gaske Fanna take jibgar Rifkatu kada ta tona musu asiri. Ƙyalesu ta yi sai dare da Alh Audi ya dawo ta tayar da zancen bayan tasa an kira sauran masu aikin. Nuna su ta yi ɗaya bayan daya "Alhaji ina so yau a gaban kowa ka shata mana layi ni da duka masu aikin nan kada wadda ta sake kusanto ɗakina." Kamar bai sami labari daga wurin Fanna ba ya ce tayi masa bayanin laifin me suke yi mata. Rifkatu mai fasasshen baki da kumburarren ido sakamakon dukan da Fanna ta yi mata ta nuna masa da baki "ita na kama a ɗakina taje yi min sata kamar yadda ta saba." "Me? To ba dai a gidan nan ba, Fanna ki sallameta ta kama gabanta" ya ce yana kumfar baka. "Ni ban ce a koresu ba sai dai ni ma zan ɗauko nawa da kaina. Zan sa a nemo min direba da mai girki da yi min shara. Kafin su zo bana buƙatar ganin kowa a hanyar ɗakina." Tashi ta yi sai kuma ta koma ta zauna ta sallami masu aikin ta gyara zama. "Abu na gaba shi ne ina so a biyani duk abinda Rifkatu ta ɗauka zan baka list tunda matarka ce ta kawo su sai ka ɗauke mata nauyin biyan. Sannan ta sanar dani wanda ta kai wa takardun plaza, satar ashe mai lasisi take yi." Tana kaiwa nan ta tashi ta barsu. Alh Audi ya buɗe baki ya fi sau biyar amma ya rasa abin cewa. Anya baiyi kuskuren auren Hafsatu Manga ba kuwa? *** Tauhidat ta sha wahala sosai a hannun Susu. Tun bata jin komai har ta koma ko muryarta taji sai ta kusa sakin fitsari. A haka aka gama zangon farko ranar hutu murna a wurinta ba'a cewa komai. Ta fito da ƴan kawayenta suna ta hira kowacce da kayanta a gefe tana jiran azo a ɗauketa. Suna tsaye ta hango Susu ta nufosu tana murmushin mugunta ita da Minasco. Aisha ta gaji da hanasu cin zalin Tauhidat ta zuba musu ido kawai. Jikinta ne ya hau ɓari da ta ganta sai Allah Ya taimaketa kamar daga sama taji muryar mamanta. "Oluwatosin" ta ce cikin murna tana dariya. Wani irin ihu ta saka ta kwasa a guje ta rungume Aunty Bimbo. "Maami" ta ce tana ta murna da mamakin zuwanta. Ta yi zaton babanta ne zai zo. Sai da su ka gama rungumar juna ta durƙusa ƙasa ta gaisheta ita kuma tana tambayarta karatu. Duk hirarsu da yarbanci su ke yi Shaheed yana gefe yana yi musu dariya saboda ƙorafin Maami ɗinsu wai ƴarta ta rame. Duk abinda su ke yi a idon Susu da ƴar korarta don Aisha ko kai bata ɗaga ba. Dariyar shaƙiyanci su ka hau yi suna kallon daurin zanin Aunty Bimbo da ta yi iya ƙwauri bisa al'adar yarabawa. Minasco ce ta fara nuna mata, "Mutuniyas ba za ki je kwasar gaisuwa ba wurin babarku?" Kafaɗarta Susu ta kaiwa duka da ƙarfi "amma kin cuceni, me zai kaini gaishe da dangin Oduduwa masu ɗagaggen ɗaurin zani?" Maganganun da ɗan ƙarfi su ke yi da gayya tunda sun san cewa Tauhidat tana ji. Hankalinta bai kai garesu ba sai da taji suna binsu a baya duk takun Aunty Bimbo ɗaya sai Susu ta ce, "Tsingil..." Minasco kuma ta ce, "zanin babarku" suna dariya harda tafawa. Karaf a kunnenta kuma ta san da wa su ke duk da ƙuruciyarta don lokacin shekarunta goma sha ɗaya. Amma hakan bai hanata fahimtar munin a yiwa mahaifiyarka dariya ba. Ƙwace hannunta ta yi daga cikin na Aunty Bimbo ta dumbuji ƙasa hannun hagu da dama ta yi kan Susu kamar wata zakanya. Kafin mutane su gane me yake faruwa ta bangajeta duk tsayinta sai da ta kai ƙasa saboda abin yazo mata a bazata. Tauhidat ta haye ruwan cikinta ta soma tula mata kasa a baki da fuska tana ihu cikin yarabanci tana cewa kada su sake zagin mahaifiyarta. Aunty Bimbo da Shaheed da sauran mutanen wurin da su ka haɗa da prefects, iyayen yara da malamai aka soma kici-kicin rabasu amma Tauhidat taƙi tashi. Minasco da ta kawowa aminiyarta agaji ma tunkuɗeta ta yi ta faɗi ta fasa baki. Nan da nan wurin ya rikice aka samu aka kwashesu sai ofishin shugabar makarantar. Idanun Tauhidat a soye Aunty Bimbo tana yi mata faɗa amma ko gezau sai ajiyar zuciya da take yi. Principal tana tare da wasu malamai da prefects aka tambayi me ya faru Tauhidat ta labarta musu harda kwatanta muryoyinsu. Nan fa malamai da prefects su ka shiga kare mata domin kuwa zuwa yanzu da yawansu sun san irin cin zalin da Suwaida take yi mata. Amma duk da haka sai ta ƙaryata. "Idan ƙarya nake yi mata a rufeni ni kaɗai a makaranta kada naje hutu" cewar Tauhidat hawaye na zubo mata. Principal ta janyota "babu mai rufe mana Tauhidat a makaranta amma ranar da aka dawo za kiyi aikin wanke toilet saboda kinyi laifin dukan babba, gashi har kin jiwa Amina ciwo" ta nuna Minasco. Godiya sosai Aunty Bimbo ta yi mata tana jaddada cewa za ta ƙara jan kunnen Tauhidat idan sun je gida. Bayan fitarsu Susu da take tsaye jiki duk ƙasa da Minasco mai kumburarren lebe takarda aka basu su zo da iyayensu ranar da za'a dawo makaranta idan ba haka ba kada su dawo gabaɗaya ta gaji da ƙararsu da ake kawowa. Zumbura baki Susu ta yi ta karɓi takardar a wulakance. Displine master na gani kuwa ya hau jibgarta da dorina amma da yake tsagera ce idonta babu ko ɗigon hawaye bare ta bada haƙuri. Haka ta dawo harabar makarantar har mahaifinta yazo ɗaukarsu ita da Aisha da Minasco da yake unguwarsu ɗaya a cikin Gombe. Iyayen Suwaida ƴan Gombe ne gaba da baya. Su biyar ne a gidansu ita kaɗai ta biyun ƙarshe ce mace. Babban yayansu sunansa Salihu sai Imam, Ridwan, Suwaida da kuma Habibu. Mahaifiyarsu Talatu mutuniyar kirki ce ba sawa ba fitarwa. Babansu tsohon ma'aikacin gwamnatin tarayya ne daga baya ya dawo gida yake aiki da hukumar zabe ta ƙasa reshen jiharsu. Suna da rufin asiri bakin gwargwado basu rasa kuɗin ɗauke buƙatun yau da kullum ba. Suwaida yarinya ce mai son a yaba mata tun ƙuruciya, ɗabi'ar da ta samo asali daga yawan kambamata da kakarsu Iyalle take yi. Komai sai ta ce Suwaida tafi kowa, kama daga kyau, ƙoƙari ko hankali shiyasa bata ganin girman yayyenta ko kaɗan. Idan ta yi abu aka yabeta gobe dan uwanta ya yi aka yaba sai ta kusa kwana tana kuka. Wannan halayyar tana ɓatawa Talatuwa rai ta yi ta faɗa amma Iyalle da take gidan sai ta hana. Duk wata tsiyar Suwaida da sa hannun kakarta. Ta tashi da son ganin a komai ita ce ta yi zarra shiyasa ƙawaye ma sai da ta duba a unguwarsu waɗanda nata iyayen su ka fi nasu kuɗi, ta fisu kyawun fuska da ƙoƙarin karatu saboda ko kwatance za'ayi a ambaceta da matsayin tana gaba dasu. Ta sami yadda take so kuwa bayan haɗuwarta da Aisha da Amina (Minasco), sai da suka koma ƴan koranta saboda suna cin arziƙinta. Minasco tafi Aisha kwantar da kai tamkar wata baiwa sai abinda Suwaida ta ce, Aisha kuwa kafin tafiyar ta yi nisa tana soma wayo ta fuskanci inda ƙawancen yasa gaba sai ta soma ja baya dasu. Kasancewar nata mahaifin yafi na sauran ƙaramin ƙarfi bai sa ta amince da ƙawancen mulkin mallaka ba, sa'arta ta dinga juyata kamar waina. Idan ka ga sunyi wani abu tare harda ita to tabbas tasa kanta ne ba wai son burge Suwaida kamar Minasco ba. Ajinsu ɗaya tun firamare har zuwa yanzu komai nasu tare ne. A hanyarsu ta komawa gida Susu kamar yadda ta mayar da sunanta, tana gaban mota tana kuka saboda faɗan da Alh Musa yake yi musu akan abinda su ka yi a makaranta. Minasco da Aisha suna baya sunyi shiru. Maimakon faƊan ya yi tasirin sanyaya mata zuciya sai ya zamana cikin hutun nan bata da aiki sai tsara yadda za ta kaya tsakaninta da Tauhidat idan an koma makaranta. Da anyi magana kowa sai ya kare mata harda Principal, ƙudurin hanata jindaɗin karatun tayi idan ya so a koreta bayan buƙatarta ta biya. *** Gidan Abayomi sun sha hutunsu cike da ƙaunar juna da haɗin kai. Idan ba ka nufin kowa da sharri, sai Allah Ya buɗa maka a inda kake Ya yi ta sanya maka albarka. Hutu ya ƙare Aunty Bimbo ta kashe ɗan abin hannunta wurin yiwa Tosin ɗinta siyayyar komawa makaranta. Sai dai babu abinda yake birgeta saboda kusantowar kwanakin haɗuwa da Susu. Aunty Bimbo tana lura da ita ta kirata ɗaki ana gobe zasu koma, ta bata shawara akan haƙuri sannan idan anyi mata ba daidai ba ta sanar da malamai. Da kuka su ka rabu washegari Tauhidat ta shige banɗaki ta rufe kanta. Aunty Bimbo sai da ta yi ta rarrashi ƙarshe ma dai goyata ta yi har bakin motar da Abayomi ya yi musu shata. Shaheed ya gama karatu lokacin sai zaman gida kafin a sami kuɗin tura shi Unilag ya fara karatun jami'a. "Maami bana son komawa a sakani a day" ta ce tana sharce hawaye. "Ki gama js1 in dai har lokacin ba kya so In sha Allahu zan mayar dake day kinji Oluwatosin ɗina" ta shafa kanta sannan ta soma kwararo mata addu'a su na cewa "Amin" ita da Shaheed da babansu. Satinsu ɗaya da komawa har ta soma sakewa, saboda Susu ɗauke kai take yi idan sun hadu. Wata Asabar da safe ta gama wankin kayanta ta shanya sai ga Minasco an turo ta kirata. Tun a hanya jikinta yake rawa Minasco ta soma dariya. "Yau Susu sai ta yi kilishi dake a makarantar nan." A gaban gadonta ta sami Susu ta ɗora akwatin Tauhidat ɗin akan gadonta ɗakin babu mutane yawancin ɗalibai sun fice. Fuska a murtuke ta nuna mata akwatin. "Bude ki bani duka madarar da take ciki" Kai a sunkuye ta ce "senior Susu bani da madara." Minasco ta yi saurin cewa "Ke, ashe rainin wayon naki ya kai Susu ta saka ki abu ki ki yi saboda kina taƙama da malamai ko? To bari kiji na faɗa miki ko sau nawa zaki kai ƙararmu sai mun ci moza mun ci faza dinki ehen." Rantsuwa ta fara cewa babu basu ankara ba Susu ta ɗaga tsohon akwatin ta buga shi da ƙasa sai da ya tsage tana harararta "malama bude ki bani ina da abinyi." "Eh, eh a buɗe a bamu ko mu ƙarasa shi" cewar Minasco. Durƙusawa Tauhidat ta yi tana duba inda ya tsage sannan ta ce "ni bana shan madara tana saka ni amai shiyasa Maami bata sako min ba" "Da me ki ke shan cornflakes?" "Ban iya sha ba, kin gani ma" ta buɗe musu akwatin nata tana zubar kwalla. Susu bata haƙura ba ta dinga dungure mata kai tana lakace mata hanci "ƴar matsiyata akwatin ma babu wani abin arziki ashe?" Minasco tana ganin samu da rashi domin kuwa akwatin makare yake da provision ta kasa haƙuri "Susu ga sadin (sirdine) fa. Ki ɗaukar mana da gesha ko gwangwani bibbiyu ne mu raba." Ita ma hararar ta samu daga Susu, "jiya ban baki gesha ɗin ba?" Shiru Minasco tayi ita kuma ta mayar da hankalinta ga Tauhidat, "rufe akwatin ki zo kwanata." Suna tafiya ta fashe da kuka amma ta san zuwa ya zame mata dole. Da jan ƙafa ta isa kwanar tasu ta yi kneel down tun kafin a saka ta. Aisha tana kwance tana karanta littafin Wedlock of the Gods da aka basu assignment na literature ta ganta ta tashi zaune. "Ke kuma lafiya?" Ta kalli ƙawayenta sai suka ɗauke kai. "Tunda baki da madara shiga nan kiyi min ƙwai shi nake son ci" Susu ta nunawa mata ƙarƙashin gadonta. Aisha da sauri ta tashi daga kwanciyar da tayi "Susu me yarinyar nan ta yi miki kuma? Har kin manta me ya faru ranar hutu?" "Wallahi Aisha baki da kirki, Susu tayi miki komai amma duk motsinta sai kin saka ido kin nuna ba daidai ta yi ba. Idan baki da niyyar tayata ki ɗauke kai mana" inji Minasco mai ƙarin neman fada. Aisha sai kallon ikon Allah tana gani suka tura Tauhidat ƙarƙashin gadon Susu wai ba za ta fito ba sai ta yi mata ƙwai guda biyu. Da kuka ta shiga suna mata faɗan idan wani ya ji gobe a store zasu kulleta. Store ɗin da kowa yake tsoro dole ta kama bakinta sai ajiyar zuciya. Bayan kimanin minti goma Aisha ta ce su fitar da ita Susu ta hau ta da faɗa ta kuma ƙwace littafin don dama nata ne wai za ta ga da yadda Aishan za ta yi assignment ɗin. Wannan bai bata haushi ba kamar gorin da su ke yi mata da Minasco. Cikin ɓacin rai ta fita daga hostel ɗin gabaɗaya ta barsu. Ba daɗewa aka kaɗa ƙararrawar cin abincin rana suka ce kada ta kuskura ta fito. Tana takure a kasan gado taci kuka ta ƙoshi fuska ta dame da hawaye da majina har suka dawo. Suwaida ta manta da ita saboda sun rufe gefen gadon da zanin gado da bargo. Minasco kuma tana tsoron magana ta kwaɓe mata kamar yadda aka yi da Aisha ɗazu. Tun shaɗaya da rabi na safe har akayi la'asar tana ƙasan gadon baccin wahala ya kwasheta, jiki kuma ya yi tsami. *** Kwana biyu kafin ranar da Susu ta tura Tauhidat ƙarƙashin gadonta Aunty Bimbo ta tafi Abeokuta matar ƙaninta ta haihu. Da tunanin Tauhidat ta kwana ta tashi, gari na wayewa ta bawa Abayomi dubu goma wai yaje makarantar ya biya kuɗi a rabata da wannan yarinyar da su ka yi faɗa. Ƙin karbar kuɗin ya yi yana murmushi "Abimbola kina da saka abu a rai, irin wannan ke saka yara su goge da zaman duniya fa." Damuwa ce kwance a fuskarta ta girgiza kai "ni dai zan fi jindaɗi idan aka raba musu ɗaki. Please Papa Shaheed ka je." Domin ya kwantar mata da hankali ya amince "zani amma ki riƙe kuɗin nima akwai a wurina. Sannan ki fara mana addu'a kinsan Malam Sani ɗinnan direba mai zuwa shagonmu cin abinci?" "Eh, na gidan Haj Lami da ake bikin ƴarta ko?" "Shi fa, wai aikin direba ya yi min tayi a gidan Karam" gani ya yi tayi masa wani irin kallo na rashin fahimta ya soma dariya "gidan Alh Audi Karam." Idanu Aunty Bimbo ta zaro "Karam fa kace? Papa Shaheed masu kuɗi ne sosai, ance da dollar ake biyan masu aikinsu. Da gaske zai samar maka aiki?" Abayomi ya dinga dariya saboda yadda ta ruɗe, burinta mijinta ya sami wani aikin saboda yadda yake yawan damuwa kusan ita ke riƙe da gidan. "Matar Alhajin ce take neman direba da kuma mace mai girki. Ya ce min ta hanyar kamfaninsu su ke ɗaukar masu aikin gidan amma wai ita tana neman mace mai hankali wadda za ta iya yarda da ita. Ban gama gane zancen ba amma na faɗa masa muna so. Ya yi min alƙawarin idan ki ka amince Hajiyar za ta bani aiki a gidan saboda ta fi son masu aure ma." Aunty Bimbo sarkin addu'a nan ta shiga jero yabo ga Allah tana yi musu addu'ar dacewa da aikin nan. Sai shaɗaya ta tafi tasha bayan sun haɗu da Mal Sani sun nemi alfarmar ya faɗawa Haj. Manga cewa suna son aikin kuma za ta same su da rikon amana. Suna tafiya ya kira Haj Lami ƴar kanwar mahaifiyar Haj Manga ya faɗa mata. Dama ita ta baiwa cigiyar masu aikin ita kuma ta faɗawa direbansu saboda yana da mutane. Washegari za ta iso Gomben bikin ƴar Lamin. To da yake kana naka Allah na nasa kuma ta Allah ita ce daidai. Aunty Bimbo ta tafi da farincikin samun aiki da zai ƙara musu samu ta yadda rayuwar ƴaƴanta sanyin idaniyarta zata inganta, har tana hango Shaheed ya tafi makarantar da yake mutuwar so wato Unilag ya fara karatu. Oluwatosin ɗinta kuwa jeka ka dawo za ta nema mata a kusa da gidan aikin nasu a Abuja sai hankalinta yafi kwanciya. Mijinta Abayomi zai ware ya dena yawan damuwa. Ko yaya garin Abuja yake? Ta dinga rayawa a ranta tana murmushi da yawan cewa "Alhamdulillah". Sun kusa shiga gari bayan awanni a motar wani abu ya soma ƙauri daga gaban bonnet direban ya tafi ya duba. Yana buɗewa daidai da yin bindigar motar gabaɗaya ta kama da wuta. Da shi direban da fasinjojinsa babu wanda ya tsira dukkansu sun ƙone sai fatan Allah Ya jiƙan musulmi baki ɗaya. Abayomi yana ta jiran wayar Aunty Bimbo saboda basu daɗe ba da ta ce sun kusa isa idan ta je gida nan da awa ɗaya za ta kira shi. Shiru babu wayarta sai ya soma gwadawa amma ya kasa samu kuma cajinsa ya yi kasa sosai. Sai ya soma danganta shirun nata da hayaniyar ƴan uwa ƙila bata sami zama ba. Abu kamar wasa awa biyu ta wuce a lokacin da yake tsammanin kiran nata sai ya ɗauko wayar da niyyar kiran yayanta aka yi rashin sa'a cajinsa ya ƙare. Zuciyarsa ke matsanancin bugu hankalinsa ya kasa kwanciya ya tada Shaheed suka tafi shagon wani mai renting din CD ya roƙi alfarmar a jona masa chajin amma mutumin ya ce tashi zai yi sai dai ya kawo da safe. A gidansu Aunty Bimbo su ma hankali ya tashi wayarsu ta karshe ta ce sun kusa shigowa gari. Yayanta ne yake ta kiranta yana kuma kiran Abayomi basa samunsa. Daga baya su ka sami labarin mota kirar J5 ta ƙone a hanya. Tashin hankalinsu bazai faɗu ba ƴan uwa aka tafi wurin ƴan sanda domin bincike. Da numbar motar aka kira tashar da ta taso cikin dare ƙarfe ɗaya lokacin an gama kwashe abinda ya yi saura a motar. Ma'aikatan union na tashar sun bada shaidar tabbas wannan mota mai lambar da aka faɗa daga wurinsu ta taso. Wadanda 'yan uwansu ke tsumayin isowarsu su ka nemi a duba sunaye sai gashi a ciki an sami Abimbola Hafsat Abdulwasiu. [2/23, 7:34 PM] Nasma: Kwanaki sunyi ta tafiya har lokacin da Fanna ta sake dawowa a matsayin matar Alh Audi. Ta sha huɗubar zama da Haj Manga a wurin iyayenta saboda haka da shirinta ta zo gidan. Abu ɗaya ne yake damunta shi ne waɗannan hotuna da Haj Manga ta yi mata barazana dasu. Kwananta ɗaya a gidan ta sallami mai rainon Kulsum aka kawo mata wata daga gidansu. Bayan sati ɗaya kuma aka sallami sauran masu aikin gidan gabaɗayansu aka zuba wasu. Madam Zainaba dai bata taɓuwa duk da ita Alh Audi yafi tsana saboda mugun kusancinta da Haj Manga. Sannu a hankali Haj Manga ta kula cewa, idan ta sakasu aiki basa yi sai Fanna ta basu izini. Wannan mulkin mallakar sai ya zame mata sabon jari, inda ta yi katari aka yi irin haka akan idon Alh Audi. Ranar Fanna tasha faɗa kamar zai cinyeta ɗanya. Haj Manga kuma domin ya kwantar mata da zuciya, ya ce ta kawo cheque ɗin da ya bata kwanaki saboda ya kula bata yi amfani da shi ba. Wannan kuma huɗubar Baffa ce da ya ce kada ta nuna zalama akan kuɗin. Tana kawowa ya rubuta mata maƙudan kuɗade da ya san cewa idan it ace za ta cike ba za ta dauki rabinsu ba. Ba ƙaramin girgizata kuɗin suka yi ba, saboda bata san darajar Karam Holdings har ta kai ayi kyautar zunzurutun kuɗi irin waɗannan ba batare da asusu ya girgiza ba. Bata yi ƙasa a gwuiwa ba ta nemi izininsa akan fara kasuwanci ya kuma amince mata. A satin suka tafi Lagos ita da Madam Zainaba. Wani tsohon yaron da suke harkar filaye ta nema akan ya samo mata katon fili a unguwa mai tarin jama'a kuma bakin titi. Harka ta kuɗi sati bai zagayo ba ya kaita wata unguwa Ikoyi. Filin ya yi mata ta kira Baffa Alƙali suka gama tsarin komai sannan ya turo mata hotunan tsarin gini irin na plaza kala goma. Wanda yafi kyau da tsari ta zaɓa ta saki kuɗi aka fara gini. Mr Bankole yaron da ya nemo filin ne yake kula mata da komai, kafin isowar Kashim sa'anta ɗan gidan Baffan. Su ta sakarwa ragamar ita da Madam Zainaba suka wuce China. Da yake da shirinta dama, shi ya sa basu ɓata lokaci ba. Cikin wata guda aka gama haɗa mata order na kayan gado, kujeru, kayan yara, kayan ado da ƙyale-ƙyalen mata da kuma kayan wuta na kitchen. Duk wannan abu ba wai ta yi wa Alh Audi dogon bayani bane. Iya abinda ya sani shi ne za ta fara kasuwanci, kuma ta tafi sayen kaya. Amma sauran bayanai ta nuna masa cewa ya jira ta gama, domin tana son ta ba shi mamaki ne. Bai matsa mata ba ya ƙyaleta. Kafin ta baro Chinan ma ya je ya yi sati guda ya dawo. Rashinta a gidan da kuma rashin bayani daga Alh Audi ya ɗagawa Fanna hankali sosai. Bata san me yake faruwa ba, amma zuciyarta tana raya mata cewa ko mene ne ba alkhairi bane gareta. Kasa haƙuri ta yi ta sanar da Alh Ari shi kuma ya yi amfani da matsayinsa kafin su dawo daga China ya tura canjin masu aiki a gidan Lagos ɗin. Da suka dawo taga sababbin fuskoki bata damu ba. Kwanansu uku suka wuce Abuja. Fanna ta matsu ta san me Haj Manga take yi wanda ya sa bata damuwa da duk wani hari da take kawo mata na kishi. Harkokin gabanta kawai take yi sai zuwa ziyartar Jamal a makaranta. Watanin da suka gabata Haj Manga bata hutawa ko kaɗan. Baffa yana Maiduguri yana faɗa mata abubuwan da za ta yi. An gama gini cikin nasara ga kayanta sun iso daga China suna warehouse. Plaza ɗinta kuwa tun kafin a buɗe zancenta ya zaga garin saboda girma da haɗuwa. Hawa shida ne ginin anyi masa ado da gilas. Shaguna biyar ne a sama da ƙasa, bakwai a hawa na huɗu da na biyu sai goma a biyun tsakiya. Yanayin ginin ya bada fasalin ficika mafi karancin coin kafin a dena amfani dasu gabaɗaya. A shaguna goma take son zuba kayanta sauran kuma ta bayar haya. Tun kafin a kammala mutane da dama sun cike form na neman shagon haya a wurin. Duk abinda ya kamata ayi anyi har an saka ranar bikin bude A & J Palace kamar yadda ta saka masa suna da farkon sunan ƴaƴanta. Ana sauran kwana biyu su tafi Lagos bikin Alh Ari ya je ofishin Alh Audi. Sun jima suna tattaunawa wanda duk Alh Ari ne yake ƙoƙarin ankarar da shi manufar fara wannan gagarumin kasuwanci na Haj Manga. "Idan baka manta ba kwanaki na nemi izininka akan canja ma'aikatan gidanku na Lagos. Ba wani abu ya janyo haka ba sai zargin cewa akwai wata maƙarƙashiya da Haj Manga take ƙulla maka" Katse shi Alh Audi ya yi ta hanyar ɗaga masa hannu, "Dakata malam! wai ni mene ne gaminka da iyalina ne? Ina ce Fanna ka ke so na aura kuma na aureta to kuma sa idon na mene ne?" Ransa ne ya soma baci shima, "ka tsaya na dire kafin ka tari numfashina mana." "Kai nake sauraro" Matsowa Alh Ari ya yi ya ranƙwafo kusa da kujerar da Alh Audi yake zaune sosai. "Yarinyar da na tura mai girki ita na bawa aikin saka ido akan duk wani motsin Haj Manga a cikin gidan. Direbanta shima ni yake yi wa aiki". "Ba ka ganin kana wuce gona da iri akan lamarin gidana Alh Ari? Ba fa tsoronka nake ji ba don ka san sirrina, na rantse maka abu ne mai sauƙi a wayi gari a nemeka a rasa" Alh Audi ya ce rai a matuƙar ɓace ya tashi ya juya masa baya, "kana iya tafiya ko ma mene ne bani da buƙatar ji. Abu ɗaya nake so da kai, ka ɗauke ido daga duk abinda ya shafi matata". Zuciya ce ta ciwo Alh Ari ya tashi shima "kudi da ka ke taƙama dasu na fa san tushensu saboda haka kai ba kowan kowa bane Audi." Ƙofar ofishin Alh Audi ya kalla da sauri ya juyo a fusace "kana hauka ne? Idan wani ya shigo fa?" Dariyar ban haushi Alh Ari ya yi, "sai su san kallon kitse suke yiwa lalataccen rogo" Motsi Alh Audi ya ji saboda tsoro ya tafi da sauri ya buɗe ƙofar. Wurin zaman sakatariyarsa ya kalla ya sauke ajiyar zuciya domin ba ta wurin. Dawowa ya yi ya gwara ƙofar ya koma ya zauna, yana huci kamar wani matashin ɓauna, "Me Haj Mangan ta yi?" Sai da Alh Ari ya yi murmushi sannan ya zauna shi ma ya soma faɗa masa maganganun da masu aikin suka kawo masa rahoto. A ciki akwai yawan wayarta da wani Baffa wanda su biyun sun san waye shi a wurinta. Akwai kuma batun idan kasuwa ta buɗe a hankali ta sa Alh Audi ya ƙara mata kuɗi ta buɗe wasu rassan. Ƙarshen jawabin dai shi ne cewa duk abinda take yi tana yinsa ne domin ta samu ƙofar mallakar ko da rabin Karam Holdings ne sannan ta shigar da ƙara akan ɗanta da ya ɗauka da sunan zai kai shi makaranta. "Idanunka sun makance da soyayyar ƙarya da take nuna maka. Matar nan bayanka take son gani. Ka taimaka ka faɗa min inda yaron nan yake a bata abinta kowa ya huta." Alh Audi ya tashi daga kujerar da yake kai ya tunkuɗata baya sai da ta kifa. Zuciyarsa sai tafarfasa take da ɓacin rai ba akan kowa ba kowa sai Arƙam. Datse haƙoransa ya yi yana magana da ƙyar. "Wannan tsinannen yaro idan bai riga ya mutu ba ni zanyi ajalinsa. Wace irin masifa ce wannan yake neman janyo min. Me zan ci da shi da har ake zargin ni ne na ɓoye shi? Abinda yafi bakanta min rai bai wuce na rashin samun damar aiwatar da nawa kudurin a kansa ba. To ko wannan ne abinda Oga ya gargade ni a kansa?" Alh Ari yaji daɗi haƙansa ya cimma ruwa ran Alh Audi ya ɓaci. Gyara zamansa ya yi ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tare da kunna sigari yana dariya. "Ba wannan bane kaɗai matsalarka mutumina, wato na ji daga majiyar da bata ƙarya cewa Haji Lawalli yana ingiza Dada su ma su shigar da ƙara akan yaron nan dai." Ya tashi ya daidaita hannuwan babbar rigarsa, "Ni nayi nan sai mun haɗu." *** Cikin rashin sanin kwaɓarta ta yi ruwa Haj Manga ta cigaba da shirye shiryenta. Da kanta taje makarantarsu Jamal ta dauko shi saboda shi take so ya buɗe wurin a madadin kansa da yayansa. Duka gidan a safiyar Asabar suka wuce Lagos. Abin da ya bata mamaki bai wuce haɗuwa da iyaye da ƴan uwan Fanna ba a airport. Daga Maiduguri ma Baffa Alƙali da matarsa Umma sun wuce Lagos ɗin tare da dukkan ƴaƴansa su biyar da matansu. Cikin dangin Innar Haj Manga mutum shida aka tura su wakilcesu domin tayata murna. A can gidansu matan suka sauka gabaɗaya mazan kuma aka kama musu masauki. Bayan sun yi sallah ko abinci bata iya ci ba ta kira Madam Zainaba zasu je taga decoration da aka yi wa babban ɗakin taron da yake hawa na uku a ginin inda za su yi event ɗinsu washegari. Ɗakin Alh Audi taje ta ƙwanƙwasa masa ƙofa, saboda tana tunanin ko Fanna tana ciki. Ilai kuwa ita ta buɗe tana ta yatsina da karairaya. Daga ciki Alh Audi ya ce ta shigo tare da sallamar Fanna. "Alhaji sauri nake yi, kaga gobe ne gashi ban je na duba shirin da aka yi ba" ta faɗa daga bakin ƙofar bayan fitar Fanna. A tsanake ya zo ya ja hannunta cikin ɗakin "ke da fita sai gobe, kinga yadda ki ka soma yin ɗan wuya kuwa? Kullum kina fama kusan shekara baki da nutsuwa. Idan baki huta ba yau goben ba lallai ki moro a wurin ba." "Don Allah kada ka hanani zuwa, aski ya zo gaban goshi ka haƙura a ƙarasa. Gobe so nake idan kaga abinda nayi ka yaba." "Ko a haka ma na san cewa na tsinci dami a kala. Masu shirin nan experts ne saboda haka ki kwantar da hankalinki zasu yi abinda ya dace." Gani ta yi kamar da gaske baya son ta fita ta nuna bata san zance ba, shima kawai sai ya haɗe rai ya soma faɗa. A babu yadda zata yi ta haƙura. Da safe ma ta so ko yaya ta leƙa ya hana dole ta haƙura zuwa ƙarfe huɗu da rabi da zasu tafi. *** A limousine din Alh Audi zasu tafi wurin taron da matansa. Ya fito sanye da suit ruwan ƙasa wadda ya gagara balle maɓalli saboda tudun cikinsa. A gefensa Fanna ce ta ci ado da wani rantsattsan leshi an zuba gwal sama da ƙasa ana ta firirita. Sai da suka zauna da minti goma ƙwarara sannan Haj Manga ta fito. Atampar aura ce a jikinta wadda ba a gani sosai domin ta lulluɓeta da haɗaɗɗiiyar laffayar da tasa aka yi mata musamman daga Dubai. A babarbariyarta sak ta fito duk ƙyashi da hassadar mutum ya san ta wuce sa a. Mutum uku ke kokawar buɗe mata ƙofar ɓangaren dama na motar Jamal ɗinta ya riga su. Ya ƙara tsayi da kyau kamanninsa da mahaifinsa kullum ƙaruwa suke yi. Shekarunsa goma sha shida a lokacin ya soma tara siririn gashin baki. Hannu ya ɗora a kafaɗarta ya miƙawa Madam Zainaba digital camera ɗinsa. "Daukemu da Nanna kafin ta shiga taro ganinta ya yi min wahala. Kinsanta da sabga ganinta sai an cike form." "Ƙaniyarka" Haj Manga ta ce tana rungumo shi jikinta tare da dariyar wai har yanzu ta kere shi a tsayi. Shamsu da ya ke tsaye a gefe ya yi sana'arsa, wato tsaki ya shige motar da zasu bi. Su ma ana yin hoton kowa ya shiga mota suka mika zuwa mall ɗin. Ƴan jarida da mutane sunyi tururuwar cika wurin anata hayaniya, da ƙyar ƴan sanda su ka zagaye iyalin suka sami damar wucewa cikin gate ɗin. Nan suka yi ta zagayawa gaisawa da manyan baƙi sannan aka taru a gaban wani ƙyalle mai kyau da ya zagaye farfajiyar wurin. Haj Manga ta matso riƙe da hannun Jamal domin karɓar almakashin yanke ƙyallen ya zamana an buɗe wurin sai Alh Audi ya rigata ƙarasawa. Karɓar almakashin ya yi ya miƙawa Shamsu sannan ya karɓi Kulsum da tasha ado sosai ya ce, "Ɗauketa ku yanke tare." Tamkar saukar aradu maganar da shiga kunnuwan Haj Manga domin dena ji ta yi na taƙaitaccen lokaci ma. Ta ɗaga ƙafa kenan cikin wani irin ɓacin rai mara misaltuwa ta ji anyi mata ƙaƙƙarfan riƙo. Juyawa ta yi da niyyar zagin uwa da uban koma waye idanunta suka sauka a cikin na Baffa Alƙali. Kai ya girgiza mata yana mata nuni da ta tsaya a inda take. Kamar wata mai ciwon wuya ta juya da ƙyar tana kallon Shamsu ya saka almakashin a cikin hannun Kulsum sannan ya yanke ƙyallen ya faɗi a ƙasa aka ɗauki sowa da tafi. Mai gabatarwar ya nuna musu wani ƙaton abu da aka lullube. Alh Audi ya gyaɗawa Shamsu kai bayan ya karɓi loudspeaker ɗin. Shamsu na yaye lulluɓin wurin rubutun da yake ƙarƙashi ya soma walƙiya. Alh Audi ya ce, "Welcome to S & K Palace, kyauta ce ga ƴaƴana Shamsuddeen da Kulsum wanda matata abar alfaharina Haj Hafsatu Manga Bukarti ta taimaka min wurin assasa komai." Kuka mai tahowa daga ƙasan zuci shi ne ya tasowa Haj Manga, amma duk faɗin wurin Baffanta kaɗai ta yarda yaga rauninta. Saboda wannan dalilin ta maye ɓacin ranta da murmushi a lokacin da Alh Ari ya tako gabanta yana mata godiyar ɗaukar dawainiyar kula da koma na ginin tun daga farko har ƙarshe. "Tabbas na yarda idan mutum ya yi dacen mace ta gari irinki sai dai ya yi fatan cikawa da imani" ya ce da murmushin mugunta a fuskarsa. Murmushi itama ta yi sannan ta ja hannun Jamal "muje ka taya ƴan uwanka murna". Jikinsa ya yi mugun sanyi saboda ya fahimci me ya faru a wurin. Murya na rawa ya ce "Nanna are you ok?" Bata ce masa komai ba sai ƙarfin riƙon hannunsa da yaji ya sake ƙarfi. Can cikin zuciyarsa ya ce 'Arƙam kana ina?' *** FGGC Bajoga Gombe State.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull