Kenza eBookz

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 4

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 4

Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 4: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 4. "Susu. Ke Suwaida Musa fito fito da sauri" cewar wata ƴar siririyar…

9,800 words

"Susu. Ke Suwaida Musa fito fito da sauri" cewar wata ƴar siririyar matashiyar budurwa a bakin ƙofar hostel ɗinsu. Cornflakes wadda aka kira Susu take sha a lokacin ta miƙawa ɗaya ƙawar tasu da suke group tare su uku ta fito tana murmushi. "Minasco ta samu ne?" Hannunta Minasco ta damƙo ta kuma buɗe murya domin dayar ta ji "Aisha ke ba za ki fito ba?" Aisha din tafi alamun nutsuwa da salihanci cikinsu. Tasowa ta yi ta fito bakin ƙofar ɗakinsu ta samu har sun ɗan yi nisa suna uban shewa da karaɗi irin na ƴan matan da ke tashen girma. Ware ƙafa ta yi ta cimmasu lokacin da Minasco take cewa. "Kun manta ma mun ce muna shiga senoir class zamu yi school daughter? Wallahi na hango ƴan kyawawa a sababbin nan muyi sauri kafin a rigamu." Ai fa sai murna kowacce tana faɗin yadda za ta ɗinga kulawa da school daughter ɗinta, yadda yaran ba za su dinga ƙyuyar yi musu aiki ko zuwa aike ba. Jin kawunansu su ke yi a sama an gama junior class su ma yanzu manya ne a makaranta. Sun doso wurin da sababbin ɗaliban ƴan JSS 1 su ke sai su ka tsaya, daga gefe suna jiran Senior Mistress ta gama yi musu magana ga prefects da zasu tafi dasu zuwa hostels da aka basu. Fuskokin ƴan matan da yawa babu fara'a wasu ma da gani sun ci kukan rabuwa da iyayensu. Su Minasco yanke shawarar komawa harabar hostel ɗinsu suka yi, idan ya so cikin waɗanda aka turo nan sai su nema saboda sauƙin mu'amala. Basu daɗe ba da komawa sai ga Labour Prefect da yara suna biye da ita. Wasu cikin ƴan manyan aji musamman jss2 sune masu taya yaran ɗauko kayansu. Hannun Minasco Susu ta ji a kafaɗarta tana cewa "ke ce mai son ƴan kyawawa Susu kallo gefen famfon can ki ga wadda na gano miki." Aisha murmushi ta yi "kuna da matsala ni zan koma na kwanta kafin a sakani ɗaukar kayan kowa na fasa daughter din." Babu wadda ta amsa mata tsakanin Minasco da Susu, domin kuwa hankalinsu yana gun wata ƴar kyakkyawar yarinya mai ɗan jiki da kumatu. Kallo ɗaya za ka yi mata ta burge mutum. Uniform ɗinta ya yi mata kyau saɓanin sauran ɗaliban ita sai washe baki take yi tana yiwa wata ƴar js2 magana. "Ke Minasco gano min waccan banzar uwar shisshigi da neman s." Cewar Susu a zafafe. Minasco itama ta hangota ta yi gaba Susu na biye da ita zuwa gaban yaran, ransu a haɗe kamar waɗanda aka yi wa wani abu. "Ke Shalewa waye ya baki damar kula school daughter ɗin Susu?" Cewar Minasco ƴar kanzagin Suwaida da gurɓataccen turancinta saboda ba wani isarta ya yi ba. Shalewa ɗan ja da baya ta yi a tsorace. Susu da kawayenta basu da sauƙi don tasha wahalarsu suna js3 ta shigo js1 kawai saboda yarenta suka kafa mata kahon zuƙa. Tana tsoron yin magana kada su saka ta aikin wahala da ta tambayi yaushe ta zama daughter ɗinta yarinyar da shigowarta kenan makarantar. "Sorry Senior Amina" ta ce da Minasco tare da taɓa kafaɗar yarinyar "greet them." Ɗan murmushi yarinyar ta yi ta ce "good evening" Susu sai kai ya yi wani gingirim, daɗi ya kamata saboda muryar yarinyar da salon turancinta ya burgeta sosai. "What is your name?" "Tauhidat" Minasco ta dara "Susu kin dace wallahi, ke kinji wani rantsattsen suna irin na ƴan gayu. Ƙila ma fa ƴar masu..." Harara Susu ta jefa mata kada ta zubar musu da aji, ta kama hannun yarinyar har ƙasan zuciyarta tana fatan kada Allah Ya kawo wata cikin ƴan ss2 ko ss3 su ƙwace mata daughter. Hanyar shiga hostel su ka nufa Minasco ta kwaso kayan nata tana cewa Shalewa ta tafi tunda ba hostel ɗinsu bane. Tsayuwar dole ce ta kama Susu ba shiri, lokacin da sabuwar daughter ɗinta ta ɗagawa Shalewa hannu. "Odabo sister mi" Wani horrified look ta wurga mata "na shiga uku kema ƴar gidan su oloshi ce?" Minasco ta zubar da kayan a ƙasa ta ruga gabansu "wai kina nufin bayerabiya ce?" "Baki ji me ta ce ba? Ke ya sunanki na gaskiya?" Susu ta ce da Hausa. "Oluwatosin Tauhidat Abayomi amma Tosin ake kirana a gida." "Kan babban bala'i. Susu kinji wani uban suna? Wato da fakewa zaki yi da hausa ki liƙe mana ko? Sarakan gulma a ɗiba a kaiwa ƴan uwa" ta dungure kan Tosin. Rikicewa ta yi ta kasa fahimtar laifinta, ta kalli Shalewa wadda ta yi tsuru itama. Ita kuma mai yi mata murmushi ɗazu yanzu kallon ƙyama take yi mata. Duk da ba wai ta gane hakan bane amma ta fuskanci cewa basa sonta kuma kamar yadda su ka nuna da farko. Tana wannan tunanin Susu ta talle mata ƙeya sai da ta hantsila ƙasa fararen kayanta su ka dame da tabon da yake wurin inda ruwan sama ya kwanta a wani ɗan rami. [2/23, 7:34 PM] Nasma: Abayomi ya manta rabon da ya raba dare bai runtsa ba sai a wannan ranar. Aunty Bimbo ta kan tsokane shi cewa da ya ɗora kansa a pillow yake fara minshari, sai gashi yau yadda ya ga rana haka ya ga dare saboda rashin samunta. Zuciyarsa a cunkushe tunaninsa ya tsaya cak. Gabanin asuba wani irin bacci mai nauyi ya ɗauke shi ba shi ya farka ba sai goma na safe da matsananincin ciwon kai kamar zai rabe biyu. A kiɗime ya tashi ya fara danna wayarsa da ya bari a jikin caja ko an kawo wuta bai sani ba amma taki kunnuwa. Jiki babu ƙwari ya yi sallar da ta kubuce masa ta asuba sannan ya yi wanka. Ƙaramin falonsu ya duba ya sami bread da flask ɗin tea wanda Shaheed ya ajiye masa. Tunda ya ji gidan shiru ya san ya tafi wurin facinsu a bakin titi. Ko ruwa bai iya kurɓa ba ya fita. Allah cikin ikonSa lokacin Mal Sani ya karyo kwanar layin kenan ya ɗauko Haj Manga daga airport na Bauchi saboda rashinsa a Gombe a wancan lokacin. Rage gudun motar ya yi ya sauke glass ɗin domin su gaisa ya kare da tambaya da fatan Aunty Bimbo ta isa gida lafiya. Cikin hausarsa mai saurin tona masa asiri a gane ba asalin yarensa bane ya ce, "Mallam Sanni tun jiya na kasa samunta ga rashin caji, ka taimaka min na saka sim card ɗina a wayarka na kirata" damuwa ƙarara a fuskarsa, abinda bai sani ba yana fara maganar hawaye ya soma sauka akan kuncinsa. Wani irin yanayi yake ciki mara daɗin fasaltawa shiyasa yake ta ambaton Tawakkaltu Alallah a zuci. Alamar juyawar Mal Sani bayan motar inda Haj Manga ke duba wasu takardu cikin nutsuwa ta ji. Yana son neman izinin tsayawa ya saka sim ɗin da Abayomi ya riga ya miƙo masa amma yana gudun ɓacin ranta. Madam Zainaba da ke zaune a gefe ita ma kallonta take yi. Tana jin idanuwansu a kanta tayi murmushin gefen baki ba tare da ta ɗago kai ba. "Ashe har yanzu ana soyayya a duniya? bashi ya kira ko hankalinsa zai kwanta." Muryar da Abayomi ya ji ne ya fargar dashi cewa akwai mutum a bayan motar. Dan duƙawa ya yi duk da ba ya hango komai ta duhun gilashin ya gaishesu sannan hannu na rawa ya karɓi wayar. Tashin farko matarsa ya kira sau biyu shiru sai ya kira yayanta wanda dama gidansa ne za ta je. Yadda yanayin fuskarsa ke sauyawa Haj Manga ta ke karanta tana girgiza kai ta zurfafa cikin tunanin lamuranta da Alh Audi sai ji suka yi Abayomi ya ce, "(Kana hauka ne)?" da yarensa da babu wanda ya fahimta a cikinsu. Wata maganar ya kuma saurara daga ɗaya ɓangaren lokaci guda ya faɗi ƙasa kansa ya bugu da mudubin gefen direba. Cikin sauri Mal Sani ya fito haka ma Madam Zainaba, Haj Manga bata motsa ba amma gabanta ya yi mugun faɗuwa. Mutanen kusa dasu sun fara tahowa Mal Sani ya kara wayar a kunnensa. Da yarbanci mutumin ya soma yi masa magana ya yi saurin sanar da shi halin da Abayomi yake ciki da turanci. Muryar yayan Aunty Bimbo dama rawa take yi jin haka ya kama kuka ya faɗa masa halin da ake ciki. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Mutane su ka ji Mal Sani ya faɗa. Sai aka fara tambayarsa ko Abayomi ne ya cika. Fuskar Aunty Bimbo yake hangowa mai yawan murmushi a kwanakin da ya haɗu da ita da jiya, da ƙyar ya iya haɗa kalmomin da ya ce, "Matarsa ce da ta tafi gida jiya motarsu ta ƙone a hanya ta rasu." Zance ya riga ya kai bakin titi cewa Abayomi ya suma saboda haka a kunnen Shaheed ya faɗi wannan magana. Yaro ya faɗa kan mahaifinsa yana kuka yayin da ake kokarin samun farfaɗowarsa. Alhinin mutuwar ya ratsa jama'a, kusan duk waɗanda su ke wurin idan ka cire Haj Manga da Madam Zainaba babu wanda bai san Aunty Bimbo ba. Da aka samu Abayomi ya farfaɗo tashi ya yi yana hawaye mutane suna masa ta'aziyya amma ya kasa cewa komai sai Shaheed ya yiwa nuni da gidansu ya umarce shi da ya hada musu kaya su wuce Abeokuta. Bayan an rirriƙe shi zuwa gidansa Mal Sani ya koma mota yana yiwa Haj Manga bayani. "Ita ce mai girkin da na samo miki...Allah mai iko, jiya mun rabu tana ta murnar samun aikinsu ita da mijin ashe ko haɗuwa babu rabo tsakaninku." Wani irin sanyi ne ya ratsa Haj Manga da jin wannan batu. Hankalinta ya tashi matuƙa ta ji tausayin mutumin ya yi mata wani irin kamu a zuci. Cikin rabin awa Abayomi da ɗansa su ka fito ƙofar gidan jama'a sunyi dafifi ana ta gaisuwa. Wani maƙocinsu ne ya ɗaukesu a babur ɗinsa zuwa tasha su ka ɗauki hanyar Abeokuta uba da ɗan suna hawaye. *** A ranar da gidan Abayomi su ka tashi da wannan tashin hankali ne kuma Susu ta tura Taihidat ƙarƙashin gadonta ta ce ta yi mata ƙwai. Har akayi la'asar sun manta da ƴar mutane sai bayan magariba ɗalibai da yawa sun dawo daga cin abincin dare ta farka. Bata sani ba bacci ne ta yi ko suma na tsayin lokacin nan amma da ƙyar ta iya buɗe idanuwanta da su ka yi nauyi. Miƙe takurarren jikinta ta so yi amma babu wata gaba da ta bata haɗin kai sai ma wata irin azaba mai raɗaɗi da take bin sassan jikinta. Mahaifiyarta kawai take buƙata a wannan lokaci shiyasa cikin wata irin dasasshiyar murya da bata fita sosai ta soma kuka tana magana da yarensu. "Maami kizo, Maami ki kawo musu ƙwai su fito dani, Maaamiiiii." Kamar wasa wasu ƴan mata huɗu suna ƴar hayaniyarsu daga ɓangaren daman gadon wata ta dan daga hannu ta ɗora akan laɓɓanta. "Shhhhh." Ta kusa da ita ta firfito da idanu a tsorace "gardi ne?" "Maaammmiiiii" Sai akayi sa'a akwai wata yarinya da ake kira Mami a wurin. Idanuwa kanta su ka dawo jikinsu duka a sanyaye. "Mami kamar fa ke ake kira." Rai a ɓace cike da tsoro ta ce "inji uban wa? Ance muku sunan gaskiya ne Mami ɗin?" Wata da cikinta ya kaɗa don tsoro baki na rawa ta ce "amma dai kowa a ɗakin nan ya san sunanki ne. Wallahi ki ɗaga hannu idan aka sake kiran." Mami sai ta soma ja da baya da baya tana neman hanyar gudu kada a sake kiran sunan sauran su miƙa ta. "Maaamiii" Tauhidat ta sake kira a wahale. Da su ka tabbatar dai magana su ke ji kamar daga ƙarƙashin kasa da murya can ƙasa ba bata lokaci su ka soma rige-rigen fita daga ɗakin wasu na faɗuwa wasu na take su. Gudun kafa me naci ban baki ba ake yi cikin kiɗima ana kiran aljanu ne a hostel ɗin su na neman Mami. Susu da su Minasco suna bakin ƙofa dama tare dasu ake gudun gabaɗaya sun manta da wata Tauhidat. Ƙawayenta guda biyu ne ma rashin ganinta ya dame su tun a wurin shanya. Abinka da ƙuruciya sunyi tunanin aiki seniors ko prefects su ka bata shiyasa basu nemeta ba kada a haɗa dasu. Da aka kaɗa ƙararrawar zuwa cin abincin rana har aka gama basu ganta ba sai su ka fara nema. Sun wahala sosai ga rashin wayo sai ƙarfe shida na yamma ɗaya ta takura akan su faɗawa prefect ko rijiya ta faɗa wurin ɗebo ruwa. Tun kafin su faɗa ɗin su ke kuka, sai da suka yi mai isarsu sannan zancen ya kai kunnen dinning prefect ita kuma ta faɗawa malamar da take da duty ranar aka fara nemanta. Duk inda ake tunanin ganinta an duba amma babu alamunta. Malamar nan hankalinta yayi mugun tashi bata san me za ta faɗawa Principal ba sai gashi ta hango ɗalibai yuya guda anzo faɗa mata akwai aljanu a hostel dinsu. Salati ta yi yau sai godiyar Allah daga wannan sai wancan. Ɗaya daga cikin masu gadin da ta sa aka kira ta cewa ya nemo masu aikin rijiya a duba ko ta faɗa sannan tabi yaran saboda dare ya soma yi ina za ta kaisu. Cincirindon ɗalibai ne a bakin hostel ɗin an kasa shiga. Ƴan manyan aji sun tabbatar mata da cewa tabbas akwai aljana tana kiran Mami, ga kuma Mami a gefe tana kuka kamar ranta zai fita don tsoro. Malamin Qur'ani da yake limanci ta sa aka kira da wasu malamai biyu su ka shiga ɗakin ana addu'a da karatu. Tauhidat ta galabaita ƙarshe ɗan motsin da take iya yi ta ƙasa. Muryar Liman ta ji yana karatu sannan ya ce, "Su waye ku? Me ku ke nema?" Da ƙyar ta dan ɗaga murya "Sir nice Tauhidat ku fito dani don Allah." Sai kallon kallo tsakanin malaman da metron ɗin hostel. "Kina ina ne?" Ya tambaya jikinsa na bashi mutum ce. "Kasan gado, Senior Susu ta ce na yi mata ƙwai ne" ta ja ƙarshen tana fashewa da kuka. Malamar nan mai duty jikinta har tsuma yake yi ta ruga waje ta kira Suwaida saboda ita ta sani mai wannan sunan. Hankalinta a tashe ta biyota za ta ja Minasco ta kwace hannunta ta yi baya. Gaba na faɗuwa ta shiga ɗakin sauran malaman suna tambayar malamar da ta kirawota dalilin kiran ba'a gano matsalar ba. Bata amsa musu ba sai fatan yarinyar da take ta nema ta kasance a wurin. Ɓangaren gadonsu mai hawa biyu ta nuna mata. "Daga min bedsheet din gadonki." Dammmm! Ta ji zuciyarta na barazanar fasa mata ƙirji. Sai yanzu ta tuna abinda ta yiwa Tauhidat tun kafin azahar. "Na shiga uku na" ta ce murya a sarƙe. Zargin malamar ya tabbata ta haɗe rai, "Za ki shiga dai mutuniyar banza, daga min nace!" Hannunta yana rawa ta yaye zanin sai ga alamun yarinya a durƙushe ta cure wuri guda. Liman da wani malami cikin sauri su ka kama gadon gabaɗaya su ka ɗaga shi sama. "Subhanallahi, Tauhidat ce fa" cewar Metron ɗin ta tafi wurin ta miƙa mata hannu "sannu ƴar nan tashi kinji." Tana jan hannun ta saki wata razananniyar kara har waje inda daliban suke suna ji. Ɗaya daga cikin malaman maza ya kalli Suwaida idanunsa zallar ɓacin rai. "Tun ƙarfe nawa take nan?" Fitsari ta ji zai zubo mata saboda tsabar rudewa "na..naaa...na manta" A take malamar nan mai duty ta sambada mata bulalar darbejiyar hannunta a baya ta soma faɗa, "kin manta?" Gantsarewa ta yi azaba na shigarta tana kai hannu bayanta, "kafin ayi lunch ne Ma." Sake harzuƙa malamar ta yi. Awanni sama da biyar ta tura 'ƴar mutane ƙarƙashin gado, ga wahalar da ta sha wurin nemanta tun ɗazu suke yawo sun karaɗe makarantar. Bulalar ta shiga jibgawa Suwaida iya ƙarfinta tana ta kururuwa. A gefensu kuma Tauhidat ta kasa juya hatta wuyanta sai mamanta da take ta kira. Liman a dunƙulen nan da take ya ɗagata su ka yo waje za'a kaita clinic ɗin makaranta. Minasco ta kusa sakin zawo da ta ganta a hannu sai yanzu ta gane dalilin ihun kukan Susu. Da rawar jiki ta matsa kusa da Aisha, "In kina yiwa Allah kice banda ni aka turata ƙasan gadon." A kunnenta wata ta faɗa ashe, yarinyar ta riga ta san yadda su ke azabtar da Tauhidat ta kwasa a guje ta shiga ɗakin. Malamai mata biyu ta tarar suna ta yi wa Susu faɗa kamar su cinyeta. Tana sauke nishi ta ce, "Ma harda Amina Falalu" Suwaida taga haske ko dukan zai ragu ta ce, "eh wallahi mu biyu ne." Minasco ta kama hanyar banɗaki sai jin kira ta yi kamar daga sama ga mutum biyu sunzo kamota. Rantse-rantse ta soma yi har aka direta gaban malaman nan. Bulala dai a wannan dare anyi musu tafi talatin. Sunyi kuka har sun gaji ga sauran ɗalibai su na ta aibata su. Nos ɗin da take clinic ɗin a lokacin allurai ta fara yiwa Tauhidat sannan ta sa aka samo ruwan zafi aka tubeta Metron ta dinga gasa mata jiki. Kukan ma babu sai gurnani kawai na tsananin ciwo da kiran Maami ta zo ta ɗauketa. An riga an sanar da Principal a daren ta baro gidanta can ɓangaren gidajen malamai ta taho ganinta. Kallo ɗaya ta ganeta, yarinyar da ta yi dambe ce saboda an yiwa mamanta dariya. Zama ta yi aka gama gasa jikin ta tura aka karɓo abinci a gidanta tasa Metron ta bata, sai dai ko rabi bata iya ci ba ta shiga kwara amai a wahale. Yunwa ta ci ta cinyeta ga jiki ko ina yana ciwo abin tausayi. *** Manya-manyan mutane ne maza masu faɗa aji a cikin Najeriya, saboda ƙarfin arzikinsu da muƙamai aune a wani madaidaicin falo. Su talatin da shida ne cif-cif, mutum ɗaya daga kowace jiha. Zaune suke a kan kujeru na alfarma sun zagaye ƙaton zagayayyen teburin da yake gabansu. Shugaban tawagar ne akan kujera mafi girma da kyau. Jibgegen mutum ne baƙiƙƙirin mai baƙar aniya. Bayan sun gama tattauna abinda ya zaunar dasu meeting ɗin ranar zasu tafi ya dakatar da Alh Audi. Ba shi da aka tsayar ba, sauran ma gabaɗaya hankulansu sun tashi. Komawa ya yi ya zauna a ɗofane yana jiran yaji me Ogan nasu zai ce. Sai da ya yi gyaran murya sannan ya ce dashi, "Audi ka tuna shekarun baya da na faɗa maka cewa babban ɗan Ibrahim zai zame maka barazana a gaba ko?" Wani irin sanyi da firgici ne ya kama Alh Audi domin kuwa saɓanin kawar da Arƙam da aka ce ya yi bai ma san inda yake ba. A take gumi ya shiga tsatssafo masa ko ta ina tsigar jikinsa ta mimmiƙe. Oga tabe baki ya yi, "ina fata ka yi yadda nace da shi." Cikin sauri ya ce, "ƙwarai. Sosai kuwa. Oga ai don bana son yawan damunka da surutu ne da tuni na sanar da kai. Shekaru shida kenan tun kafin uwarsa ta gama takaba." Kai Oga ya gyaɗa, "ka taimaki kanka, yanzu ma akwai wani abin da ya tunkaro ka wanda zai iya rusa duka shirinmu." Jiki na rawa Alh Audi ya ce "wane iri?" "Mace ce, macen ma kuma yarinya. Ban san yaushe bane za ta shigo rayuwarka ba." "Oga to me ya kamata na yi?" "Shigowarta wajibi ne amma zamowarta sillar tonowar asirinka wannan sai ka so." Dam! Dam!! Dam!! Gabansa ya tsananta faɗuwa. Tashi ya yi zai fita, cikin tashin hankalin da ba zai faɗu ba. Duk irin taɓargazar da ya aikata a rayuwarsa babu wadda yafi jin tsoro kamar wannan babban al'amari da yake da yaƙinin shi Oga yake nufin yarinyar za ta tona. "Ka nutsu ka yi abinda ya dace, idan ba haka ba komai da ka sani zai lalace." Oga ya ce da shi lokacin da ya kama hannun ƙofa zai murɗa. Bai san lokacin da zuciya ta ciyo shi ba ya ce, "don gwafar ubanta me na yi mata to? Saboda gudun ɓacin rai ni fa ko mata ba na bi duk yawo na." Wata muguwar dariya mai fitar da razanannen sauti Oga ya yi. "Banyi tsammanin zan ga alamun karaya a tattare da kai ba Audi." "To ai, to.. to ai, Oga idan sirrina ya fito fa shikenan tawa ta ƙare" cewar Alh Audi a raunane. Cikin dakakkiyar murya Oga ya ce "sai kayi abin da ya dace." [2/23, 7:34 PM] Nasma: *** Abayomi ya yi kukan rashin matarsa har ya ji babu daɗi. Bai san da wace kalma zai kwatanta Abimbola ba. Matar da duka neman kuɗinta akansa da ƴaƴansa yake ƙarewa. Bata da ƙyashi kuma bata taɓa yi masa gori ba, sai ma dai ta ce lokacin da yake cikin wadata yana direban Sanata meye bai yi musu ba. Zuciyarsa wani irin ƙunci take shiga idan ya kalli yadda Shaheed ya zabge yini guda, bai san yadda zai yi da Tauhidat ba. Yana tausayin yadda rayuwarta za ta koma babu uwa. Ƴar gata ce a wurin mahaifiyarta abar tattali yanzu za ta soma sabuwar rayuwar maraici. Iyaa Bayo ita ce surukarsa maman Aunty Bimbo. Tun shigowarsa gidan take suma tana farfaɗowa. Yanzu ma da gari ya waye kwance take cikin mawuyacin hali ta tayarwa da kowa hankali. Suna zaune ana karɓar gaisuwa Bayo yayan Aunty Bimbo wanda ya kira jiya a waya ya ratso ɓangaren dangin Abayomi ya yafito shi da hannu zuwa cikin gidan. Iyaa Bayo tana kuka tana kiran sunan jikarta Oluwatosin ya zauna daga gefe yana jiran bayani. Bayo ya kalle shi da tausayawa "jiya a wayar wani ka saka sim ɗinka ka kirani?" "Oluwa mi o (Wayyo Allah na)" Abayomi ya ce da ya tuna bai karɓi sim din ba ya taho. Bayo ya katse masa tunani, "Yanzu na gama waya da mutumin ya ce wai Principal ɗin su Tosin ta kira shi cewa bata da lafiya kuma tana ta kuka." Matar Bayo ta shiga girgiza kai, "ba dole ba, mahaifiyarta ce fa ta rasu. Taji a jikinta ne" Wani sabon tashin hankalin, da ƙyar ya tambayi Bayo yanayin jikin nata ya ce shi ma bai sani ba amma da mutumin ya kira ya gaya masa Principal ɗin ta nemi da su je su ɗauketa ta bata hutun sati ɗaya. Karɓar wayar ya yi ya kira Mal Sani ya roƙe shi ya turo masa nambar Principal ɗin ta layin Bayo. Ba jimawa ya turo Abayomi ya kira ya buƙaci ta haɗa shi da Tauhidat. "Mr Abayomi idan mamanta tana kusa ka fara bata saboda tun jiyan ita take nema. Kuma ina so inyi mata bayanin abinda ya faru ne" ya ji ta faɗa a dan tsorace kamar akwai abinda take son ɓoyewa. Yawu ya haɗiya sannan ya faɗa mata zancen rasuwar. Principal sai da ta kusa kaiwa ƙasa saboda gigicewa. Ranar hutu fa su ka haɗu ashe shi ne farko kuma ƙarshen ganinta da matar. Ga kuma ƴarta gaɓoɓinta sun kumbura musamman ƙafafu yaya za ta yi da yarinyar alhali likitan nasu da yazo da safe yace lallai a kaita babban asibiti. Sai ta shiga haɗiyar yawu, ta tattaro ƙarfin hali ta faɗa masa abinda aka yiwa ƴarsa. Tun yana tsaye sai da ya zube a ƙasa saboda wani irin baƙinciki da ya saukar masa. Da mahaifiyarta tana nan yaya zata ji an yiwa ƴarta abu irin wannan? Tambayoyi ƴan uwa su ke ta yi masa ya dakatar dasu cewa su jira ya sami mafita. Mal Sani ya sake kira dai saboda ba shi da lambar kowa sai tasa ya roƙe shi akan cewa akwai maƙocinsa wanda ya kaisu tasha jiya, ya taimaka ya faɗa masa ya ɗauko Tauhidat zai yi ƙoƙarin dawowa shi kuma ana kwana bakwai. Domin su gaggauta ɗaukota ma ya labarta masa abinda Principal ta ce. Yana yi ƴan uwansu musamman Iyaa Bayo kukanta ya tsananta ga nisa bare su ɗauko ƴarsu. Mal Sani tausayin yarinyar ya kama shi, cikin gidan bikin ya shiga ya faɗawa mai girki ta sanar da Hajiya Lami zai ɗan fita. Jiya bayan suman Abayomi bai san inda ya jefa nasa sim ɗin ba sai da Principal ta kira shi sannan ma ya farga da cewa ba nasa bane a cikin wayar. Taron da aka yi jiya a gidan kuwa yawancin ƴan unguwar da dama basu je ba musamman ƴan cikin layin. Sun taru ne a gidan maƙocin Abayomi suna nasu zaman makokin. Babu alaƙa ta jini amma akwai kyakkyawar mu'amala tsakanin Aunty Bimbo da maƙotanta, kowa alkhairinta yake faɗa. Mai girkin sai ta tsayar da Mal Sani ta shiga cikin gidan bayan ɗan lokaci ta dawo ta kira shi wani falo inda Haj Manga take hakimce akan kujera. Gefenta kuma Haj Lami ce. "Yauwa don Allah Mal Sani me ya sami Tauhidat ɗin?" Haj Lami ta tambaye shi yana shigowa. Yadda Abayomi ya faɗa masa ya maimaita. Haj Manga bata san lokacin da ta yi jifa da takardun hannunta ba, "Kace me?" Duk da ya ɗan tsorata saboda ya kula ita yanzun nan take canjawa. Ana abin arziki ta rikiɗe idan abin nata ya motsa, ya lanƙwasar da kai ya kuma koro mata bayani. Goshinta ta shafa cike da damuwa kamar ta san yarinyar, "This is serious, yanzu cin zalin da ake yi a boarding schools har ya kai wannan matakin?" Yunƙurin tashi Mal Sani ya yi saboda isar da saƙon Abayomi ga maƙocinsa, domin yadda yake ta kiran wayar tun zamansa a falon. Haj Manga ta dakatar da shi ta hanyar ɗaga hannunta. "Kira min mahaifin nata." Idan ma ya yi mamaki bai nuna ba ya ce mata gashi yana kira ma. Ɗauka yayi ya faɗa masa Haj Manga za ta yi magana da shi sannan ya miƙa mata. Ta'aziyya ta fara yi masa tana iya jin rawar muryarsa sannan ta ɗan dake, "Mr Abayomi za ka karbi aikin da ku ka yi magana da Mal Sani a gidana?" Shiru ya yi ƴan uwa suna ta tambayarsa da hannu me ake cewa a zatonsu da Principal ɗin su Tauhidat yake magana. Ɗan guntun haƙurinta ya nemi ƙarewa, "Na ce za ka karɓi aikin direban ku dawo Abuja da ƴaƴanka?" Ƙwaƙwalwarsa ba wani dogon tunani za ta iya ba matsawar bai ji halin da Tosin ke ciki ba ya amsa mata da "eh". "To madallah, ka kira makarantar yanzu ka faɗa musu cewa zan tura a ɗaukota saboda kada su hanashi." "Da kanki?" Ya sami kansa da tambayarta cike da mamaki. Shi da yake jiran wayar maƙocinsa da zai ɗaukota. Tamkar bata ji me ya ce ba ta ɗora ta cewa, "Gobe zamu koma Abuja zan tafi da ita idan ka gama shiryawa bayan an gama zaman makoki ka samemu a can. Sani zai turo maka kuɗin mota da kwatancen gidan tare da numbar da za ka same ni sai ka turo accout number". Mal Sani ta miƙawa wayarsa ya tsaya galala don bai taɓa tsammanin haka za ta ce ba. Haj Lami kanta ta yi mamakin ƴar uwarta balle Madam Zainaba. Buɗaɗɗuun bakunansu ta kalla ta dan taɓe baki ta ce, "Ka jira zan kawo kuɗin da za ka bayar idan an buƙata a makarantar ina so ka taho mata da takardun transfer" sannan ta bar falon. Tana ɓacewa Madam Zainaba ta kalli Mal Sani da waya a hannu "ka yi masa magana kada dama ta wuce shi mana" Saurin ɗora wayar ya yi a kunnensa ya ce, "Abayomi kada ka yi wasa da damarka, aiki tare da Haj Manga ba ƙaramin abu bane. Zan ɗaukota zuwa gidan aikina gobe su wuce." Ji ya yi abin yayi masa yawa lokaci guda amma kuma yana ganin da gaske dama ce bata kufce musu ba da zai samu inganta rayuwar yaransa musamman Shaheed da ya kasa fara jami'a. Haka nan zuciyarsa kuma ta yarda dasu da yake ya san gidan Haj Lami sun jima a unguwar tun kafin haihuwar Tauhidat. Amincewa ya yi ya kira Principal ɗin ya kwatanta mata Mal Sanin. Haj Manga kudi ta kawo kamar yadda ta ce ta miƙawa Mal Sani sannan ta umarci Madam Zainaba da ta bishi saboda basu san a halin da zasu riski yarinyar ba. Bayan fitarsu Haj Lami ta nuna jindaɗinta sosai na wannan sauyin hali da ta gani a wurin ƙanwarta. Tashi su ka yi daga falon zuwa wurin sauran danginsu aka cigaba da sha'anin biki. *** An wayi gari makarantar ƴan mata dake karamar hukumar Bajoga ta jihar Gombe babu walwala a cikinta sakamakon abinda ya faru jiya. Tun sassafe Susu da Minasco su ke durƙushe akan gwiwoyinsu a ƙofar ofishin Principal ɗin suna jiran matakin da zata ɗauka akansu banda dukan da aka yi musu jiya. Bata bi ta kansu ba tana jira azo a ɗauke Tauhidat domin ta sami kulawar ƴan uwanta. Ga daɗin tashin hankalin jin rasuwar mahaifiyarta. Ta kira meeting na gaggawa ta sanar da malamai tare da neman shawarar hukuncin da yafi dacewa da masu laifin. Malamar da ta yi duty a jiyan ta yi saurin cewa a koresu saboda a ganinta yin haka zai tsoratar da sauran ɗalibai akan cin zalin na ƙasa dasu wato bullying. Basu tashi daga meeting ɗin ba su Mal.Sani suka iso cikin wata haɗaɗɗiyar mota. Masu gadi suna gani ko tsoron miyagun mutane babu suka wangale musu gate. Mal Sani ya faɗa musu aike ne daga Hajiya Manga matar Alh Audi Karam. Sannan ya tambayi hanyar ofishin Principal aka nuna masa. Kafin su ƙarasa yawancin ɗaliban makaranta kowa ya ga wannan haɗaɗɗiyar mota mai matuƙar kyau kirar jeep saboda an tara su a gaban assembly dukkaninsu. Madam Zainaba dama idan ka ganta babu yadda za a yi a kirata mai aiki saboda gidan da take ciki ya amsa sunansa, biyanta ake yi da kuɗi masu tsoka ba kowa yake samun wannan alfarma ba. Maigadin da ya biyosu har cikin staff room ya kaisu inda ake meeting. Kada ma wani ya riga shi faɗa ya yi saurin cewa Principal ɗin, "daga gidan Karam ne, Karam dai da muka sani na ƙasar nan." Ya juya ga Madam Zainaba a lokacin Principal da malamai sun fara miƙewa tsaye "uhmm Hajjaju ziyara ku ka kawo mana ko yara za'a saka a makarantar?" "Baba Maigadi" Principal ta kira shi ganin yana ta rawar ƙafa "je ka abinka zanyi magana dasu." Haɗe rai ya yi bai iya ɓoye ɓacin ransa ba, dama haka manyan nan su ke idan sun ga masu kuɗi sai su kankane komai su hana na kasa samun romon arziƙin ya ayyana a ransa kafin ya fita. Iyakarsa bakin ƙofa idan sun fito ya yi niyyar ya kuma rakasu bakin gate kamar wasu makafi. Ƙofa Principal ta nuna musu, "Muje office ɗina ko" "A'a muna sauri ne Tauhidat mu ka zo ɗauka ba zama zamu yi ba" cewar Mal Sani. Irin kallon mamakin da su ke jifansa da shi sai kayi zaton wani abu mara kyau ya fada. Oluwatosin dai yarinyar da kana ganinta ka san gidansu babu maiƙo ita ce mutane daga gidan Karam su ka zo ɗauka. Hankalin Principal kuwa ya tashi da ta tambayi sunansa ya faɗa ta gane shi ne Mr Abayomi ya faɗa mata zai zo. Yau sun shiga uku ashe yana mu'amala da manyan mutane. Duk ta diririce sai mataimakinta ne ya kaisu nasa office ɗin aka tura malamai mata biyu su ka ɗaukota. Madam Zainaba jikinta sanyi ya yi da aka kawo Tauhidat. Idanu sun faɗa saboda yunwa gashi duk abinda aka bata sai ya dawo. Sai kuma jikinta da ta kasa taka kafafu ga wuya bata iya karkata shi ko yaya sai taji kamar zai balle. Miƙewa ta yi ta rike kafaɗunta ta ce, "Mal Sani zamu jiraka a mota ka karɓo takardar da Hajiya ta ce." Ya so mantawa kuwa ya tambayi nawa ake biya idan za'a bada takardar transfer. Nan fa Vice ya soma bashi haƙuri akan cewa zasu ɗauki mataki akan yaran domin sallamarsu ma za ayi daga makarantar. Idan sun cire Tauhidat me aka yi kenan? Principal tana tsaye tana jinsu ta ce dama Papa Abayomi ya faɗa mata. Sai dai basa karɓar komai, ko ana karɓa ma duba da yanayin da ƴarsu ta tsinci kanta a ƙarƙashin kulawarsu ba za ta karɓa ba. A take aka ɗauko takardar transfer aka yi cike-cike sannan ya yi musu sallama ya fita. Har bakin mota aka biyoshi suna kara yiwa Tauhidat sannu. Kayanta duk an saka a boot tun safe Matron ta haɗo komai. Tafiyarsu ke da wuya aka koma kan su Susu. Nambar iyayensu ta cikin file ɗinsu na makaranta aka nema Principal ta ce tana buƙatar ganinsu a ranar ko washegari. Daga baban Susu har na Minasco kasa haƙuri su kayi saboda haka a ranar su ka taho tare tunda dama basu da nisa da juna. Anyi assembly Principal ta ja kunnen ɗalibai akan yi wa juna sata, kwace, fin ƙarfi da zallunci. Ta sanar dasu irin matakin da zasu dinga ɗauka yanzu babu sassauci sannan a gaban kowa ta miƙawa Suwaida da Amina takardar sallama daga makaranta. Minasco ta saka kuka Susu kuwa zuciya kemas.Baƙincikinta bai wuce ace saboda Tauhidat aka koreta ba. Tana cikin ayyana irin tsanar da ta yi mata a zuci muryar Liman ta katseta. "Mu yiwa Annabi SAW salati...." Ɗalibai su ka yi shiru suna sauraronsa yana ta kwararo addu'a da larabci a ƙarshe ya kare da cewa "Allah Ya jiƙan mahaifiyar Tauhidat da sauran musulmi." Sai a lokacin wata mummunar faɗuwar gaba ta saukarwa Susu saboda sam bata ji lokacin da aka fara zancen rasuwar ba. Me yake faruwa? Bata sami amsoshinta ba sai da Babanta da na Minasco su ka zo aka mayar musu da jawabi. "Abin baƙinciki Alhaji a lokacin da su ke azabtar da yarinyar nan Allah Ya karbi ran mahaifiyarta, ta yi tafiya motarsu ta kama da wuta babu wanda ya tsira. Yanzu haka da aka tafi da ita sai dai taje ta tarar da babu uwa ga rashin lafiya" Alh Musa sai ya kalli Principal da ta gama yi musu bayanin komai ya kalli yaran. Ɓacin ransa ba zai kwatantu ba ya ɗaga hannu ya kwaɗawa Susu mari ta ƙanƙame kumatunta da take jin kamar zai zazzago don azaba. "Ke har kin iya gwadawa na ƙasa dake mugunta ko? Muje gidan zaki ga yadda zan yi dake." Mal Falalu shi ma ransa a bace don ma bashi da zafi kamar Alh Musan ya ce "saura ɗaya shaidaniyar ita ma ka bata nata rabon." Kunyar idon mahaifi tabbas ita ta hana Alh Musa haɗawa da Minasco, domin shi yana da saurin fushi. Matsalarsa dama bata wuce Iyalle mahaifiyarsa wadda bata yarda a yiwa Suwaida faɗa. Minti goma ya baiwa yaran su tattaro komatsansu su taho. Bayan fitarsu su ka sake bada haƙuri har nambar Papa Abayomi Alh Musa ya karɓa da alƙawarin zai kira shi. Susu da Minasco sun zama abin kallo da zunɗe a makaranta. Tun da su ka fito zuwa hostel ake kallonsu sai harara da habaici. Yawancin kowa karin tausayinsa ga Tauhidat ya samo asali ne da jin labarin rasuwar mahaifiyarta. Suna haɗa kaya Aisha ce kaɗai me tayasu Minasco na ta zubar hawaye don yau me rabata da Ummansu sai Allah. Susu kuma tana hango Yaya Salihu yana jibgarta don ta tabbatar dole yana daga cikin masu horata a gida. Rasa makamin dogara ta yi ta yankewa kanta shawarar da take jin za ta fissheta ta daidaici kan gadonta ta yanke jiki ta faɗi tana girgiza jiki da surutai. Ɗalibai an sami abin yi aka sami masu zuwa sanar da malamai Suwaida Musa tana da aljanu. Da mahaifinta ya ji ransa ya kara ɓaci don ya tabbata ƙarya ne. Cewa ya yi a taimaka masa a kawo ta su tafi. A mota bai ce mata komai ba ta kwanta sharaf tana numfarfashi. Sai da su ka je gida ya sauke su Mal Falalu a farkon layin ya shige cikin madaidaicin gidansa da motar sannan ya fizgota ya shiga duka kamar an aiko shi. "Ni zaki rainawa wayo?" Ya faɗa yana ɗaga murya abinda ya fito da jama'ar gidan. Alh Musa baza babbar riga yake yana dukanta. Iyalle ta soma faɗa yaƙi sauraronta. "Musa zan saɓa maka wallahi." Mama Talatuwa ta ce "haba Iyalle a gaban yara? Baki san me ta yi ba." "To ba sai ya faɗa min ba, ina cikin gidan saboda ya nuna min shi ne ubanta ya ke dukanta ba tare da wani bayani ba" Yau ɗaya dai bai saurareta ba sai da Susu ta dena motsi bare kuka sannan ya shige cikin gidan a fusace. Iyalle ta kama ta amma ganin ta kasa tashi ta ce da Mama ta kama mata ita ciki. Dakin Iyallen aka kwantar da ita sannan ta ce lallai Alh Musa yazo ya faɗa mata me Suwaida ta yi. Kafin ya gama faɗa Mama hadda hawayenta na tausayin Tauhidat amma Iyalle sai cewa ta yi wai su basu san sharrin ƙuruciya bane da su ka kasa yi wa Suwaida uzuri. Takaici bai bar Alh Musa ya ce komai ba. *** [2/23, 7:34 PM] Nasma: Kuka haiƙan Tauhidat take yiwa su Mal Sani a mota tunda aka buɗe gate din gidan Haj Lami. Dama tunda ta hango shagon abincin mamanta ta ce ya sauketa a wurin yaƙi yana bata haƙuri akan ta bari su je gida. To gashi an shigo layin nasu kuma yana cewa mota zai ajiye ya rakata da kansa. Kukan da take yi ko kusa bashi da alaƙa da tsatstsaman jikinta, haka kawai zuciyarta take wani irin nauyi da raɗaɗin da bata san yadda za ta kwantanta shi ba a kananun shekarunta. Tausayinta sosai ya sake shigar Madam Zainaba ta kamota ta fito da ita daga motar a hankali. Dingisawa ta soma yi ta nufi gate za ta fita harda yi musu godiyar ɗaukota da suka yi. Madam Zainaba ta ce da ita ta shiga gidan su gaisa da Haj Lami. Duk da ciwon da take ji hankalinta ya yi gida tana ta zubar hawayen da bata san dalilinsu ba ta ce, "Anti idan naje gida zamu zo tare da Maami." Wannan abin tausayi da yawa yake Madam Zainaba ta aiyana a zuciyarta. Kasa cewa komai ta yi ta juya da nufin neman agajin Mal Sani sai ganinsa ta yi tare da Haj Manga suna ƙarasowa bakin gate ɗin. Tun kafin su ƙaraso Haj Manga ta ƙurawa Tauhidat ido tana kallon yadda take kokawa da sakatar gate ɗin. Bayanta take iya gani ta gane yarinyar tana da ɗan jiki ba ramammiya bace. Sauri ta ƙara ta isa kusa da ita ta kama hannunta ta riƙe. Wani irin abu ne ya soki zuciyarta a lokacin da Tauhidat ta dago suka haɗa ido. Tana da son yara sai dai Allah bai bata da yawa ba. Kallonta take yi babu ko kiftawa, fuska ce mai nuni da yarinta da shiga rai. Manyan idanuwanta da suka yi jazur suka ƙanƙance sune suka fara ɗaukar hankalinta kafin ta ji ta yi magana da muryar kuka. "Anti ina wuni, Anti ki ce su buɗe min in tafi wurin Maami." Tauhidat ta ce duk da tsayi da kwarjinin Haj Manga yaso bata tsoro. Ga mamakin duka mutanen wurin harda Haj Lami kuwa sai gani suka yi Haj Manga ta rage tsayi ta durƙusa a gaban Tauhidat tare da juya mata baya. "Hau muje in baki abinci da magani sannan in faɗa miki inda Maami ɗin ta tafi." Ita ma kanta mamakin kanta ta yi shi ya sa ta saki murmushi ba shiri. Tauhidat kuwa kallonsu Mal Sani ta shiga yi sai ta ga suna mata nuni da ta hau. Abinka da ƙuruciya da kuma halinta na saurin sakewa da mutane ba musu ta ɗare ta riƙo wuyan Haj Manga da ta miƙe tsaye da ita. Kanta ta tura daidai kunnenta ta ce, "Maamin ta yi tafiya ne?" "Eh shi ne ta ce a kawo min ke" cewar Haj Manga tana tafiya muƙarrabanta suna biye dasu a baya ana kuskus. "To Anti ke friend ɗinta ce?" "Nanna zaki dinga ce min, haka ƴaƴana suke kirana." Ta bata amsa cike da kulawa. Tauhidat ta karɓi gyaran ba musu "Nanna ke friend ɗin Maami ce? Ban taɓa ganinki ba. Seat ɗin ku ɗaya a aji? School ɗin su fa a Abeokuta ne ke kuma ga ki a Gombe." Murmushi mai sauti Haj Manga ta yi. Rabonta da nishaɗi har zuci an kwana biyu. Tana son inquisitive kids (yara masu yawan tambaya). Samun kanta ta yi da cewa. "A'a amma ni sabuwar mamanki ce, suna na Hafsatu Manga." Sake ƙwaƙumar wuyanta Tauhidat ta yi tana dariya "na yarda! Sunanku ɗaya da Maami amma ita ba sunan babanta Manga ba." Bushewa Haj Manga tayi da dariya daidai lokacin da ta sauketa akan doguwar kujerar falo. "To ita Maami ɗin yaya sunanta?" Tauhidat tana son komai na mahaifiyarta. Cike da shauƙi ta ce "Abimbola Hafsat Abdulwasiu". Kallon Haj Manga ta yi ta ja da baya kaɗan akan kujerar tana yi mata kallon tuhuma "ki ka ce friend ɗinki ce amma baki san sunanta ba?" Zamowa ta yi daga kan kujerar tana tunanin fita Haj Manga ta zauna ta mayar da ita zaune kusa da ita. Hannu ta ɗora akan kafaɗarta kamar wasu ƙawaye. Hakan ya yi sanadiyar sanya Tauhidat jin nutsuwa da ita. A hankali daidai fahimtar yaro ta ce, "Tauhidat, Maami ta yi tafiya ne ta ce ni na koma mamanki. Kafin ta tafi ta ce duk abinda kike so in dinga yi miki. Kuma wai idan kika ki zama a wurina ba za ta dawo ba." Idanu raurau da hawaye ta shiga girgiza kai tana cewa mamanta ba za ta je wani wuri ta barta ba. Rikice musu ta yi sai da Haj Manga tasa Mal Sani ya kira mata Abayomi a waya. Kwantarwa da Tauhidat hankali ya yi ta hanyar rarrashi. Da ya ce ta bita Abuja gobe zai taho tare da Shaheed nan da kwanaki kadan sai ta ƙara sautin kukan. Tambayarshi ta yi ko zai taho da Maami sai ya kasa bata amsa saboda kukan da ya taho masa ya kashe wayar. Kafin Tauhidat ta iya magana sallamar mata kusan shabiyar ta ɗauke musu hankali. Akan idon wata cikinsu suka shigo gidan kuma ta hango Tauhidat a bayan mota shi ne ta faɗawa sauran makotan. Mai aiki ce ta kaisu falon inda suka ga Tauhidat tare da matar da ta ɗauki hankalin dukkansu. Yanayin shigarta da komai nata ya nuna musu ba ƙaramar mace bace. Wadda suka zo dominta ta ganesu duka shi ya sa ta zuba musu idanu itama ganin suna yi mata wani irin kallo. Wurin zama aka nuna musu suka hau koke-koken tausayi da jajantawa juna tare da ta'aziyya gareta. Da farko bata fahimci me ake yi ba sai da wata ta ce, "Allah Sarki, shikenan yaran nan sun zama marayu. Tauhidat nafi tausayawa ita ce mace." Fuska a haɗe Haj Manga ta tashi ta kamo hannunta kafin su fasa ƙwai. Maimakon su fara neman jin ba'asin ko an faɗa mata, kawai sun kama maganganu. Takaici sosai ya kama ta yadda wani zubin mata basa lissafi kafin su saki magana. Tauhidat da wayo ba jimawa ta gano me suke nufi da zantukansu. Jikin matar wanda ya kai su Abayomi tasha ta faɗa a gigice. "Anti Ma'u ina Maami ta tafi?" "Tosin sai haƙuri, Aunty Bimbo ta rigamu gidan gaskiya", cewar wata daban tana sharar ƙwalla. Razananniyar ƙara ta sakar musu lokaci guda jikinta ya saki ta faɗi ƙasa. Ba yau ta fara jin kalmar gidan gaskiya ba. Ta riga ta san meye mutuwa tun bayan rasuwar kakanta na wajen uwa shekara ɗaya da rabi da suka wuce. Mata sun fi biyar a kan ta suna salati da kiran sunanta. Ran Haj Manga kuwa in ya yi dubu ya ɓaci. A ganinta rashin hankali ne zai sa a faɗawa yarinya ƙarama rasuwar mahaifiyarta ta wannan sigar. Ko minti goma bata yi da haɗuwa da ita ba amma tana jin kamar akwai wani al'amari mai girma tsakaninsu. Yarinyar ta shiga ranta fiye da zatonta. Da ƙyar suka samu ta buɗe ido tana kuka mai ban tausayi. Cikin fushi kuwa Haj Manga ta soma yiwa matan faɗan abinda suka yi tana janyeta daga jikin wadda ta tallafe mata kai. Su kuma jin haka ya sa suka fara tasu masifar don a iya saninsu dai sun ma fi wannan matar mai ji da kai kusanci da Tauhidat. Shiru ta yi musu kawai ta naɗe hannuwanta a ƙirji tana kallonsu daidai. Kaf ɗinsu tana jin babu wadda ta wuce matsayin ta ɗauketa ƴar aiki. Madam Zainaba ta aika ɗakin da ta yi masauki ta haɗa mata ruwan zafi a banɗaki sannan ta cicciɓi Tauhidat duk nauyinta ta bi bayanta. Habawa, ganin haka wasu mutum biyu suka hau faɗan wace ce wannan mai son nuna musu iyakarsu akanta. Ƴar da aka haifa a gabansu kuma ta tashi cikin ƴaƴansu. Idan akwai mai iko da ita duk falon ai bai wuce su ba. Haj Lami na ganin yadda ƴar uwarta ta juyo a fusace lokacin da suka yi wannan magana ta soma bata haƙuri. "Jeki ki kula da ita Haj Manga zan yi musu bayani." To ashe cikinsu akwai wadda take da labarin Haj Lami ƴar uwar Haj Manga ce. Sunanta ya jima da karaɗe ƙasar saboda arziƙinsu tun ba yau ba. Jiki a sanyaye ta dafa wadda ta fi zaƙalƙalewar. "Maman Faruku yi shiru haka Haj Manga ce." Wadda aka kira Maman Faruku wata siririyar mace ce da goyon ɗanta. Yatsina fuska ta yi tana yiwa wadda ta yi mata magana kallon biyu ahu. "Mangooo, nace Mangooo ƙarewar Manga" ta dinga jan karshen harufan a wulakance. Irin kallon da Haj Lami ta yi mata ne ya rage mata ƙwarin guiwar ci gaba da abinda ta yi niyya. Ita kuwa mai magana ta farko bata fasa ba ta ɗora bayani domin sauran su gane da kyau. "Matar Alh Audi Karam ce ko Hajiya?" Ta nemi ƙarin haske daga wurin Haj Lami. "Ita ce, ƙanwa take gareni. Iyayenmu mata ciki ɗaya suka fito." Wata irin murɗawa cikin Maman Faruku ya yi a take saboda tsabar ruɗewa. Sauran ma jikinsu ba ƙaramin sanyi ya yi ba aka soma rige-rigen saka takalmi. Babu ɓata lokaci kowacce ta fice, Maman Faruku ce a gaba. Tana shiga gida ta roƙi mijinta unguwa saboda tsoron kada a turo kama ta. *** "Hajiya zauna inyi mata wankan" cewar Madam Zainaba bayan sun samu kan Tauhidat da ƙyar ta dena kuka sai ajiyar zuciya. Harararta ta yi ta sake janyo hannun Tauhidat kusa da ita tana kallon kumburarriyar fuskarta. "Yi tafiyarki ni ki take so na yi mata ko ƴa ta?" Bata iya buɗe baki ba sai gyaɗa kai. Kukan da ta yi ya janyo mata ciwon kai ga zazzaɓi yana neman rufeta saboda dama ba lafiya ce ta isheta ba. Duk yadda take ƙin ayi mata wanka saboda ganin ita ma fa yanzu ta girma bata iya yiwa Haj Manga musu ba. A da duk juma'a Aunty Bimbo sai ta yi mata da kanta suyi ta rigima. Su cika gidan kuwa da ihunta tana magiya da cewa ta iya. Ita kuma maman tana cewa danƙararriyar daudar sati za ta wanke mata. Haj Manga a gefen bahon ta zauna ƙafafunta duka biyu suna ciki. Idan ka ganta sai ka rantse ba ita bace wannan matar mai tarin damuwa da abubuwa a gabanta. Zagewa ta yi ta gasa mata jiki da gabobi sosai sannan ta yi mata wanka. Hatta askakken gashin kanta ya sha wanki da shampoo mai kamshi saboda ya soma cika. Wani irin farinciki ke ɗawainiya da zuciyarta tana ganin tamkar cikar burinta ne na samun ƴa mace. Shuɗaɗɗen mafarkinsu ita da Ibrahim ta hasko bata san lokacin da hawaye ya ziraro daga idanunta ba. Lokacin tana gogewa Tauhidat jiki ne da ƙaton tawul ɗin da ya naɗeta gabaɗaya. Hawayen da ta gani a idon babba sai ya bata tsoro. Jiki na rawa tana daga cikin bahon ita kuma Haj Manga tana ciki har lokacin Tauhidat ta ɗora kanta a kafaɗarta wani kukan yana taho mata. Murya na rawa duk ta dusashe ta ce, "Nanna kema kukan tafiyar Maami ki ke yi? Ba kin ce mu haƙura ba zamu haɗu watarana." Sake ƙanƙameta Haj Manga ta yi tana jin sabon ciwon mutuwar tsohon mijinta da ɓatan babban ɗanta. Kuka sosai ta fashe da shi daga ƙasan zuciyarta. Irin kukan da ta daɗe tana son yi amma taurin zuciya da kafiya sun hana. Haj Lami na shiga ɗakin ta jiyo alamun suna cikin banɗakin sai ta leƙa. Yadda ta gansu rungume da juna suna kuka ya taɓa mata zuciya sosai. Ita ma hawaye ne ke barazanar fito mata ta juya a hankali ta fita tare da rufe musu ƙofa. Addu'a take yiwa ƴar uwarta da fatan Allah Ya kawo mata sanyin zuciya dalilin wannan yarinya. Sauran ƴan uwansu da ke ƙoƙarin shiga ɗakin ganin yarinyar da aka ce mamanta ta rasu ta hana shiga. "Ku bari ta shirya su fito." Shi ta iya ce musu kawai. Tsoron kada sanyi ya kama Tauhidat a cikin banɗakin yasa Haj Manga fito da ita suka koma ɗaki. Ko nauyinta bata ji. Mai ta shafa mata suna hira kamar sun daɗe da sanin juna. Tambayoyi Tauhidat ke yi mata cike da zallar ƙuruciya. "Dama babba yana kuka Nanna? Ko kema mamanki ta tafi gidan gaskiya ne?" "Tun ina baby ta tafi" ta bata amsa da murmushi a fuskarta. Mamaki ne ya bayyana a fuskarta ta ce, "Kai, hmmm to kuma waye ya zama mamanki?" "Wata ce zan kai ki wurinta ki gaisheta." Tauhidat ta tuna yadda take kaunar mahaifiyarta sai ta ɗan tura baki, "To ni dai na girma bana son wata maman, nafi son Maami." Kaɗa kai da murmushi Haj Manga ta yi tana mamakin kanta da yadda ta yi saurin sakewa da yarinya ƙarama, "Tunda ke ba kya so ni ina son ki zama mamana." Kunya ce ta kama Tauhidat ta rufe fuska da tafukan hannayenta tana murmushin da ya sake shigar da ita zuciyar Haj Manga. Ina ita ina zama maman babba? "Ke ce maman ni daughter dai." Haj Manga ta girgiza kai "ban yarda ba. Ni ce daughter ke kuma mamana." Tauhidat ta sake cewa "a'a kece". Ita ma taƙi yarda. Haka suka cigaba da yi suna ta dariya tamkar uwa da ƴar da suka shaƙu da juna. Madam Zainaba ce ta hawo da akwatinta aka bata kaya a ciki ta saka sannan Haj Manga ta sa aka kawo mata abinci ta ci ta sha panadol. A wurin ta ɓingire bacci mai nauyi ya ɗauketa. Papa Abayomi sau biyu yana sake kira Mal Sani ya kwantar masa da hankali da cewa komai lafiya. Ana can ana cigaba da biki da shirye-shiryen kai amarya banda Haj Manga. Zamanta ta yi a wurin Tauhidat ta rufe taga saboda shigowar sautin kiɗa. Da za'a tafi kai amarya kuɗi mai kauri ta bata a envelop tare da nasiha amma taƙi binsu. Haj Lami dai kamar wadda aka yiwa bushara saboda canjin da take gani ƙarara a wurin ƴar uwarta. A wuni ɗaya ta koma Mangan da ta sani, Mangan da take so, Mangan da suka tashi tare. Washegari suka kama hanyar Abuja. Airport ɗin Bauchi Mal Sani ya kaisu suka hau jirgi zuwa Abuja. Tsoro a wurin Tauhidat ba zai faɗu ba. Cikin lafayar Haj Manga ta shige tana cewa kayan cikinta zasu zube lokacin da jirgin ya tashi. A firgice take hannunta ɗaya ta tallafe ƙasan cikin nata da shi. Dariya a wurin Haj Manga harda hawaye. Neman damuwar da ta dade da kewaye zuciyarta ta yi ta rasa Madam Zainaba tun tana gimtsewa ita ma sai da ta dara. Ta kuma sanya wannan rana a tarihi domin uwarɗakinta tamkar an sauya mata ita ne. *** Kwana biyun da Haj Manga bata nan Alh Audi ya yi su ne cikin damuwa da tashin hankali. Maganar da Oga ya faɗa masa game da zuwan yarinyar da za ta taka muhimmiyar rawa wurin watsa lamuransa ke ci masa tuwo a ƙwarya. Idan ya ce ya sami baccin cikakkun awanni goma a cikin kwanakin nan ya yi ƙarya. Fanna ta yi iya yinta wurin son jin damuwarsa babu biyan buƙata. Mahaifinta ta kira ta tambaye shi ko yana da masaniyar abinda ya ke faruwa. Alh Ari da ba ya son ace ga wani abu game da Alh Audi da bai sani ba da hanzarinsa yazo bugun ciki. Da yake mutum ne mai shegiyar kisisina kamar tsohuwar karuwa, da wayo da dabara sai da ya fitar da maganar Oga daga bakin Alh Audi. Sai da maganar ta riga ta fito ta yi rijista a ƙwaƙwalwar Alh Ari sannan nadama ta dirar wa Alh Audi. Ya rasa garin yaya ya ke bawa Alh Ari makaman da zai iya amfani da shi wurin cin amanarsa ta hanyar faɗa masa sirrukansa. Babu wani abu nashi da ke buƙatar ɓoyo da Alh Ari bai sani ba. Kodayake Alh. Ari shi ne silar haduwarsa da Oga saboda haka damuwa ba tasa bace. Dariyar riƙaƙƙun yan duniya ya yi sannan ya kada baki ya soma magana "banda abinka tunda dai ya ce zuwanta dole ne meye na tayarwa da kanka hankali? Ai kawai Alhaji ka jira ka ga ɓullowarta sai mu san irin matakin da zamu ɗauka." Ɗauke kai Alh Audi ya yi saboda ya kula Alh Ari ya na cikin farincikin sake samunsa a tafin hannu. Giyarsa ta gulder ya ke marmarin korawa ko zai ji sa'ida. Ƙarar shigowar mota suka ji daga wurin da suke zaune a cikin ƙawataccen lambun gidan, wanda aka wadata da wuraren zama har biyar kowanne da fasalin bukka daga sama. Ta ƙasan kuma zagayayyen tabur ne da kujeru huɗu sun kewaye shi. Ya manta da batun dawowar Haj Manga saboda ruɗanin da ya ke ciki sai da ya hangota ta cikin kofar gilas ɗin wani falo ta buɗe da nufin zuwa wurinsa. Tun daga nesa ake iya hango fara'ar da ta mamaye fuskarta. Cikin takun nan nata na isassun mata ta tunkaro su. Alh Ari ya murmusa ganin irin kallon da Alh Audi ya ke mata. "Ka ga wadda ya kamata ka sanyawa ido ba wata ƙaramar yarinya da baka san lokacin zuwanta ba." "Ka cire kan ka daga harkar iyalina Ari bana son irin haka" ya amsa masa murya ƙasa-ƙasa saboda ta kusa isowa. Duk irin kyawun da ta yi masa bai mantar da shi cewa ita ɗin kunama ce mai jiran saransa ba. Sakin fuska ya yi yana mayar mata da murmushi har ya rage taku kaɗan ta isa gabansu suka ji wata daddadar murya ta ƙwala mata kira. "Nanna?" Ta ce a tsorace saboda barinta da Madam Zainaba ta yi a falon bayan Haj Manga ta fito. "Gani nan Tauhida, come." Ta miƙa mata hannu tana jiran ta karaso. Ai tunda ta buɗe ƙofar har dan gudun da ta yi zuwa wurinta da Alh Audi da Alh Ari bakunansu a buɗe suke cike da mamaki da fargaba. Tana isowa Haj Manga ta tsayar da ita a gabanta ta ɗora hannuwanta a kafaɗunta tana sakar musu murmushi. "Alhaji ga ƴar da Allah Ya bani amana. Ka tuna na faɗa maka an samar min direba da mai girki a Gombe ko? To Allah Ya yiwa matar rasuwa shekaran jiya. Wannan ƴarsu ce Tauhida." Yawun da ya haɗiya mai masifar ɗaci ne ya kusa ƙware shi saboda tambayar da ya ke son yi mata. Murya a kausashe ya ce "ban tari numfashinki ba, ita wannan ɗin a gidana za ta zauna ki ke nufi?" Gira ɗaya ta dage da yanayin rashin damuwa sannan ta nunawa Tauhidat ɓangaren dabbobi ta ce taje ta kalla. Sai da ta tafi ta kalle shi "haka nake nufi, idan tsarin bai maka ba sai mu koma nawa gidan." A gigice yake ta kula sannan ya kasa ɗauke ido daga kan Tauhidat. Hannayensa jike da gumi ga laɓɓansa a bushe ya buƙaci Alh Ari ya basu wuri. Ba dai haka ya so amma dole ya miƙe ya koma falon. Wuri ya nuna mata ya ce ta zauna ta yi masa bayani sosai. Ko motsi bata yi ba daga tsayen nan ta faɗa masa abinda ya kamata ya sani. "Ki ka ce Babanta da yayanta suna tafe ko?" "In sha Allahu." "Ɗa na kowa ne, ta zauna a wurinki ɗin kafin su iso. A ɓangaren masu aikin na san akwai spare room da zai ishesu." Ko sake kallonsa bata yi ba kira Tauhidat suka hau sama ɗakinta. Ranar tare suka kwana don bata yarda da a kaita ɗakin masu aiki ba. Bacci ta yi cike da nutsuwa da mafarke-mafarken da suka sanya zuciyarta jin kamar ana warware mata wani ƙulli. Rayuwarta da uban ƴaƴanta ke yi mata gizo. Irin zamansu da shi da tsantsar fitina da sangartar Arƙam. Kaifin tunani da karambanin Jamal sai kuma kyakkyawar fuskar Sa'adiyya ma'abociyar dariya. Ƴarta mace da ta biyo bayan Arƙam wadda ta rasu tana da shekara ɗaya da kwanaki. Da ta farka cikin dare janyo Tauhidat ta sake yi jikinta tana fatan Allah Ya sanya alkhairi da albarka a haɗuwarsu. Sai bayan kwana goma Papa Abayomi da Shaheed suka iso gidan. Yanayin da ya ga Tauhidat ɗinsa ya faranta masa rai matuƙa. Girman Haj Manga ya ƙaru ninkin ba ninkin a zuciyarsa. Farinciki ne ya kusa yi masa yawa a lokacin da Haj Manga ta kawo kuɗin registration da accomodation (wurin kwana) na Shaheed ta ce ya je Lagos ya ji matsayin admission ɗin da aka bashi bara. Idan gurbinsa yana nan ana soma sabon zangon karatu nan da watanni kaɗan sai ya koma. Idan kuma da matsala ya dawo sai ta sake nema masa. Bayan doguwar addu'ar da suka yi mata da godiya Shaheed ya tafi Lagos. Mutumin da ta ce ya nema idan ya je shi ya taimaka masa aka sake masa alƙawarin samun gurbi a zango mai zuwa. Da murnarsa ya kira mahaifinsa wanda ya fara aikin da aka dauko shi dominsa ya sanar dashi. Washegari ya dawo kuma a ranar ne Alh Audi ya aiwatar da nasa ƙudirin bisa shawarar Alh Ari. Kamar wasa da kansa ya cewa Shaheed ya kawo masa takardunsa ya gani. Da ya ɗauko ya kai sai Tony ya tarar ya karɓi takardun wai Alhaji ya hau sama. Bai kawo komai a ransa ba ya koma ɓangarensu. Bayan wata guda ya soma shirin tafiya Lagos. Lokacin Haj Manga ta saka Tauhidat a wata private school mai kyau da tsada sannan ga islamiyya tana zuwa idan ta taso. Kulawar da ta ke bata ita ta rage yawan kiran mahaifiyarta da ta ke yi. Kwanaki kaɗan suka ragewa tafiyar Shaheed wata Talata sai ga kira daga Alh Audi. Shi da mahaifinsa ya nema a gaban Haj Manga tana zaune a falon. Mamaki ta yi tunda kuwa ta faɗa masa waɗannan mutane a ƙarƙashinta suke bata so shi ko Fanna su shiga sabgarsu kamar yadda ita ma ta janye kanta daga garesu. Girkinsu Madam Zainaba ke yi yanzu. Papa Abayomi a tsorace ya shigo suka gurfana a gabansu yana jira ya ji ance ya yi laifi sai Alh Audi ya miƙo masa wasu takardu fuska a sake.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull