Kenza eBookz

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 5

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 5

Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 5: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 5. "Abayomi kayi haƙuri nayi muku karambani irin namu na tsofaffi. Ga wannan…

1,361 words

"Abayomi kayi haƙuri nayi muku karambani irin namu na tsofaffi. Ga wannan admission na samarwa Shaheed a Turkey. Zasu fara karatu nan da sati uku saboda haka gobe Tony zai kai shi ayi masa passport a nemi visa." "Me ka ce?" Haj Manga ta mike tsaye rai a ɓace. Ran ta har wani makaki ya ke yi mata saboda tana da tabbacin da biyu Alh Audi ya ke son shige musu. Buɗe baki ta sake yi da niyyar soma faɗa sai idanunta suka sauka akan Abayomi da Shaheed. Kallonta suke yi a tsorace saboda basu saba ganin fushinta haka ba tun zuwansu. Abayomi ba zai so mata da miji suyi rigima a kan iyalinsa ba. Fasa maganar ta yi don dole ta zauna zuciya na tafasa. Alh Audi ya yi dariya a ran sa sannan ya langaɓar da murya ya karyar da kan sa. Yanayinsa irin na mai son bada haƙuri ya ce, "Ki yi min haƙuri na san tun farko munyi maganar zan ɗauki nauyin karatun ƴaƴan ƴan uwanki biyu ne a ƙasar waje. Kada ki ga na ƙara da Shaheed ki damu, ba zai hana ni cika miki alƙawari ba kinji Hafsatu." Ashar ne ya subutu daga bakinta ba tare da ta yi niyya ba. Wai ita Alh Audi zai yiwa duniyanci. Wato ya fente ta baƙa a gaban direbanta da ɗansa ta yadda ko a gaba ya nemi haɗin kansu zasu bayar da gudu. Idan bata gyara lamarin da wuri ba tabbas zuwan Abayomi da iyalinsa zai koma kamar ta ɗauki wuƙa ne ta dabawa cikinta. Ita da ta fi shi sai ta hau muryar kuka tana mammatse idanu "Alhaji ka bar batun waɗancan yara duka basu ci jarabawa ba. Ba komai ya sa ka ga na nuna ɓacin rai ba sai tunanin kada Papa Abayomi ya ga kamar muna son nuna masa iko da ɗansa. Kada ka manta bai daɗe da rasa matarsa ba. Yaran nan biyu su ne yake gani yaji daɗi. Amma me ka ce?" Ta yi tambayar ga Abayomi. Idanunsa cike da ƙwallar godiya ga Allah da Ya haɗa shi da mutane masu kirki da son cigaban iyalinsa ya ce a raunane, "Ba na son ɗora muku nauyi. Lagos ɗin ma ya isa Alhaji." Ɓacin rai Alh Audi ya nuna "saboda ita ka ke yiwa aiki shi ya sa ni za ka watsa min ƙasa a ido? A wurina ɗa na kowa ne. Yadda zan kula da nawa haka zan yiwa duk waɗanda suke ƙarƙashina." Da sauri ya girgiza kai yana bashi haƙuri. Alh. Audi ya ce "In dai haka ne to ya fara shiri. Ga wannan Shaheed ka sayi kayan sawa. Idan bai isa ba ku yi mata magana zan ƙaro" ya miƙa masa kuɗi. Kin karɓa Shaheed ya yi sai ya ajiye a cinyar Haj Manga ya tashi ya basu wuri. Alh Audi ya kasheta da mamaki. Yanzu kuskure guda za ta yi ya janyo rashin yarda tsakaninta da Abayomi. Ba don yadda take jin Tauhidat ba da babu abinda zai hanata sallamawa Alh Audi su, domin har kasan zuciyarta tana jin wani abu mara daɗi zai biyo bayan wannan alherin da ya yi musu. Kuɗin ta miƙa musu ta bi bayansa. A falon ɗakinsa ta same shi yana kora giyarsa don yanzu ba ya kunyar uban kowa. Tsayuwa ta yi a gabansa ta soma faɗa akan wannan shigar sauri da ya ke shirin yi mata. Tana masifa yana lumshe idanu saboda daɗin da ya ke ji na abin shan sa. Tuna masa ta yi da haƙurin da ta yi lokacin da ya ci zarafinta ya kwace plazarta ta Lagos. Ƙarashe zancen ta yi da cewa, "Ka sauwaƙe min na kama gabana" Gama sauraronta ya yi sannan ya tashi ya tsaya a gabanta ya turata ta zauna daɓas a kujerar bayanta. Yanayinsa abin tsoro don bata taɓa ganinsa a haka ba. Nuna ta ya yi da yatsa yana ƙankmƙance idanu. "Manga a tafin hannuna fa ki ke. Na daɗe da sanin zaman me ki ke yi a gidana sai dai ina son sanar da ke cewa shigowa ce ganin damanki amma fita sai na so." Tashi ta yi da ƙarfinta ta tunkuɗe shi baya ya yi taga-taga kamar zai faɗi. Ita ma nuna shi ta yi yana tsaye bayan ya dafa wata kujera ya tsaya, "Baka isa ba tunda zaman aure babu dole a cikinsa." Ran Alh Audi ya sake ɓaci dama yana jin haushin kawo Tauhidat da ta yi gidan. Fincikota ya yi ɗankwalinta ya faɗi ƙasa. Jelar siraran kitson kanta ya damƙo na tsakiyar da ƙarfinsa yana ja. Saboda azaba ta kusa sakin fitsari amma taki roƙonsa da ya sakar mata kai. Duƙar da kansa ya yi daidai kunnenta tana jin numfashinsa mai haɗe da warin giya ya ce, "Namu auren zamansa wajibi ne a gareki indai da gaske kina son wannan shegen yaron naki Arƙam." Da sauri ta ɗago kai ya yi murmushi ya cigaba da magana "ƙwarai kuwa Hafsatu. Ni kaɗai na san inda Arƙam yake. Ina so ki zubar da makaman yaƙinki ki bini a sannu domin na haɗaki dashi." Sakar mata kai ya yi da ya ke mata azababben zugi ya ƙara da cewa "kada kiyi tunanin haɗani da hukuma domin bana jin akwai dan sandan da idonsa ya yi tsararon da zai ɗaura min ankwa a hannu. Ni ne Alh Audi Iro Karam! Shaheed zai tafi karatu kamar yadda na tsara sannan ubansa da ƙanwarsa su cigaba da zama da mu." Haj Manga ji ta yi kan ta ya kulle ta kasa dogon nazari. Da ƙyar ta iya cewa "mece ce manufarka a kaina da su?" Dariyar mugunta ya yi mata kafin ya riƙe habarta a tsakiyar hannunsa "da sannu idanunki zasu gane miki. Ke dai ki zame min mace ta gari a idon duniya ni kuma zan kawo miki Ibn Ibrahim Al- Karamawi, hahhh hahhh" ya kece da mahaukaciyar dariyar da bata san ya iya ba. Jiki a sanyaye ta fice zuwa ɗakinta ta faɗa gado tana wani irin kuka mai ban tausayi. Duk wani makaminta a lokacin ta ajiye shi saboda bata hango komai sai duhu a gaba da bayanta. Washegari ko ruwa ta kasa kurɓa saboda tashin hankali ya tura Fanna ta kira masa ita saboda ta kashe wayoyinta. Shiryawa ya ce ta yi kafin shabiyun rana sun sauka a Kano gidan Dada. Kwantar da kai ya yi a gaban dattijuwar nan ya faɗa mata ƙarya da gaskiya akan dalilinsa na ƙin barin Arƙam ya zo hutu. Ba tun yau take jin tsoronsa ba shi ya sa bata ja zancen ba har ya yi ya gama. Bayan sun fita idanunta na zubar da hawaye ta ce, "Allah Ya jikanka Arƙam." Ta riga ta yardar ma zuciyarta cewa lallai asiri Alh Audi ya yi da shi saboda yadda dukiyarsa ta kara haɓɓaka. Tausayin surukarta ne ya dirar mata tana ganin ƙila ita ɗin ma bisa tursasawa suke zaman auren. Da wannan tunanin ta tara sauran ƴaƴanta na wurin mijinta na biyu su biyar ta ja musu kunne da babbar murya cewa kada wanda ya sake tayar da zancen Arƙam. "Rana dubu ta ɓarawo ce, rana ɗaya ta mai kaya. Idan dubun duk mai hannu akan salwantar jikana ta cika ina mai tabbatar muku da cewa duniya za ta yi atishawar ƴan tsaki. Za'ayi walkiya mu gansu. Ban lamunce ku yanke zumunci da Jamalu ba ko bayan raina. Wannan yaron (baban su Jamal) yayanku ne kuma dukkaninku daga arziƙinsa ku ke ci saboda haka zare hannu daga kan abinda yayi saura daga zuri'arsa ba naku bane. Allah Ya yi muku albarka." Wannan su ne kalaman Dada na ƙarshe ga Nana, Safiyanu, Garba, Rabi'a da Usman akan lamarin Arƙam. [2/23, 7:34 PM] Nasma: *** Tun daga waje ake jiyo hayaniyar matasa tana tasowa daga wani wuri da aka rubuta cafeteria da manyan harufa. Wannan wurin cin abincin da ya ke cikin Medical College reshen Johns Hopkins University matattarar malamai ce da ɗaliban makarantar. The Johns Hopkins Medical College tana cikin manya manyan makarantun karatun aikin kiwon lafiya mafiya girman daraja a duniya ba ma ƙasar Amurka kadai ba. Yankin Baltimore na garin Maryland suna ji da wannan makaranta shi ya sa ake ganin girman ɗalibanta.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull