Kenza eBookz

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 6

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 6

Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 6: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 6. Yau ta kama Valentine's day saboda haka cafeteria ɗin ta sha ado da…

9,293 words

Yau ta kama Valentine's day saboda haka cafeteria ɗin ta sha ado da jajayen fitilu, balan balan da banner waɗanda aka yi rubutun kalaman soyayya. Samari da ƴan matansu ne suke ta kai kawo, wasu na raye-raye wasu kuma suna cin abinci ko shaye-shayensu ana raha. Cikin wannan hayaniyar wani matashi ne zaune akan kujera mai tsayi da ta daidaita kirjinsa da dogon teburin gabansa. Hannuwansa ya saka ya dafe kunnuwansa sakamakon ihun kiran sunansa da wasu gungun ɗalibai suke yi suna bubbuga tebura da kofuna. "A.I.K! A.I.K!! A.I.K!!!" Suke ta maimaitawa ana ingiza shi da ya tashi ya hau stage ɗin da aka tanada musamman dominsa a wannan rana. "I've got a cold (mura nake yi)" ya faɗa cikin wata siririyar murya, mai nuni da an kusa galaba a kansa. "NOOOOO" ita ce kalamar da suka haɗa baki wajen furtawa da karfi, amon muryoyinsu ya sake karaɗe wurin. Ya yi ɗan murmushi "not in the mood today (bani da ra'ayin yau)." Maimakon su rabu dashi sai suka ƙara ƙarfin bugun teburan da kiran sunansa. Wani babban mutum ne ya taso ya zo gabansa, ya ja hannunsa sai da ya tayar dashi tsaye ya yi masa magana da turanci. "Kayi na minti goma kacal. Ranar ba za ta cika ba idan ba ka ƙawata mana ita ba" Matashin turo baki ya yi sannan ya miƙe tsayinsa sosai. Dogo ne sosai mara ƙiba sai dai alamu sun nuna yana motsa jiki. Fatarsa baƙa ce irin ta mutanen da duniya ta yi musu daɗi. Ta murje ta yi kyau. Kyakkyawar fuskarsa tana ɗauke da madaidaitan idanu, hanci mai dan faɗi da tsini ta gaba sai bakinsa da siririn gashin baki ya ƙawata. Arƙam Ibrahim Karam kyakkyawan saurayine ta kowace siga. Kallo ɗaya za ka yi masa indai ka san Haj Manga ka gane cewa tsatsonta ne. Yadda ya ɗebo mahaifiyarsa a komai haka ƙaninsa Jamal ya ɗebo mahaifinsu. Wannan dalilin ya sa a lokacin ƙuruciyarsu akan tsokane su da Telu fari da Telu baƙi. Sanye yake da dogon wandon chinos ruwan ƙasa mai duhu ya yi zanzaro da farar vest ɗinsa. A sama kuwa t-shirt ce baƙa wadda ya buɗe maɓallanta daga sama har ƙasa. Kansa ya sha rangaɗeɗɗean kitso guda takwas wanda tsagar ta fito raɗau, ga jelunan sun dan zarta kafaɗunsa. Yana tafiya kan stage ɗin ana ihu ya ƙarasa ya tsaya a gaban loudspeaker da take kafe a wurin. A gefen hagunsa wani bature ne mai suna Josh zaune a gaban piano. Daga ɓangaren dama kuma mutumin ƙasar Philippines ne Tomaz zaune da guiter a hannu. Sipikar ya zaro daga marikinta ya soma rera waƙar soyayya cikin harshen turanci cikin wata daddadar murya mai ratsa zukatan masu sauraro. Irin ihun da aka saka a wurin sai ka rantse rabon arziƙi ake yi. Masoya su ka shiga filin rawa wasu hadda hawaye saboda irin kalaman da ya ke amfani dasu masu tsuma zukata. A can ƙarshen wurin mutumin nan ne da ya tayar dashi zaune da wasu mutane su biyu suna magana. Arƙam da abokansa ya nuno musu ya ce, "Me kuke tunani akansu?" Ɗaya daga cikin mutanen ya kaɗa kai, "ka ce medical students ne, ta yaya ka ke ganin zamuyi signing ɗinsu a agency ɗinmu?" "Yaran nan da kuke gani suna da basira sosai. Shekararsu biyu da fara waƙa a nan kuma ban taɓa jin Karam ya yi waƙar wani ba. Shi ne shugabansu kuma shi ya ke rubuta waƙoƙinsa." Ya gyara zama sosai "ɗan baiwa ne don yanzun nan sai ya haɗa waka ka ji wurin nan ya ruɗe da ihu saboda daɗinta. Idan duka ku biyun babu mai son ɗaukarsu zan nemi wasu." Mutumin da yaki magana tun zamansu ne ya ɗauke ido daga ɓangaren da ake waƙar, ya dubi shugaban cafeteria ɗin da ya kira su. "Sun san kana nema musu agency?" "Ko ɗaya, ina dai son taimaka musu ne saboda na san waƙa tana kawo arziƙi fiye da tunani. Ka duba da kyau mutumin Africa ne ɗan Nigeria kuma musulmi da wannan basirar." Duka mutane biyun kowannensu kalmar musulunci sai ta zaburar da zuƙatansu. Na farkon da ya fara nuna rashin ra'ayi bai yi wata wata ba ya yanko wasu makudan kuɗi a matsayin abinda kamfaninsa zasu biya mawaƙan a shekara. Manufarsa a zuci bata wuce ra'ayinsu na ɗauke hankulan musulmi daga addini ba. A ganinsa addinin musulunci naƙasu ne ga rayuwar mabiyansa musamman matasa maza da mata. Da irin haka suke yiwa mutane shigo-shigo ba zurfi. Son kuɗi da burin yin suna a duniya yana taka rawa sosai wurin lalata tarbiyar mutane musamman musulmi. Kan kace meye wannan zuciya ta karkata sai haram ta koma halal. Kuɗin kawai ake hange ban da lahirar. Bayan ya faɗi kudin Raymond mai kula da cafeteria ya yi murmushi da zummar amincewa, sai ɗayan ya ruɓanya kuɗin da wancan ya faɗa sau biyu. Jin haka shi kuma ya mayar sau uku. Wancan ya mayar huɗu...A haka sai da suka yi ta jayayya inda kuɗin ya koma daidai da ruɓi takwas kuma na farkon ne ya yi nasara. Bayan sun gama waƙar Raymond ya kirasu teburin da suke zaune. Ɗaya mutumin ya tashi cikin ɓacin rai ya tafi. Zama suka yi a gajiye ya gabatar musu da shi. "Ga Mr Darcy shugaban Ace Entertainment yana son ɗaukarku contract ɗin waƙa a ƙarƙashin kamfaninsa." Arƙam ne ya fara tashi fuska a tsuke "Raymond tun yaushe na faɗa maka cewa waƙar da nake yi ba sana'a nake son mayar da ita ba?" Lallashin sa Raymond ya soma yi "ka zauna ka ji nawa zai baku a shekara." "Bana so kuma kada ka sake yi min irin haka." A fusace ya tashi ya bar wurin. Waje ya fita yana shaƙar iskar wurin hannuwansa a aljihu. Bai daɗe da tsayuwa ba Raymond ya fito. Cikin laluma ya dinga nuna masa irin alkhairin da zai samu a dalilin waƙa. Misali ya bashi da Westlife da Backstreet boys saboda yanayin waƙarsu ta Pop music ɗaya ne. Sunyi kuɗi sunansu ya zaga duniya. Sannan ga Tomaz aiki wurin kala huɗu yake yi saboda kufin makaranta. Josh kuma daga gidan marayu wasu suka yi adopting ɗinsa. Yanzu sun mutu basu bar masa komai ba sai tulin bashi. "Kai maikuɗi ne amma indai abotarka dasu da zuciya ɗaya ne ba za ka so zama sanadin shiga tsakaninsu da arziƙi ba." Ya dafa masa kafaɗa da hannuwansa biyu "kaine mawaƙin, su kiɗa kawai suka iya. Idan baka shiga ba su ma sai dai su ga samu su ga rashi." Daga haka ya koma ciki ya bar shi da tunani. Washegari da safe a ɗakin karatu ya haɗu da Josh da Tomaz fuskokinsu babu yabo ba fallasa. Tabbas abokan nasa suna buƙatar taimako. Takaici da ƙuncin zuciya ke nuƙurƙusarsa. Shekara shida da watanni kenan da mahaifiyarsa da wan babansa suka raba shi da mahaifarsa. Bakin gwargwado yana ta ƙoƙarin tsayawa a turbar addini amma abin da wahala. Babu mafaɗi sannan Nanna da ta rage masa ta yi rantsuwar muddin ya sake sauke ƙafafunsa a Nigeria batare da kwallin shaidar ya zama cikakken likita ba sai ta yi masa baki. Ya rasa me yake faruwa, kuɗi dai bai taɓa rasawa ba tun bayan Tony PA ya ɗauko shi daga makarantar da Kawunsa Audi ya kaishi ya dawo dashi America kuma shi ne ya yi masa waɗannan bayanai game da mahaifiyarsa. Tun yana buga numbar gidansu bata shiga har ya haƙura. Daga baya Tony ya bashi ta Nanna amma har yau idan ya kira wata Madam Zainaba ke ɗauka ta ce masa Nannansa bata son magana dashi saboda laifin da ya yi mata. Ranar farko cikin tashin hankali ya tambayeta laifin ta faɗa masa wai makarantar da aka kaishi nan mamansa taso ya yi amma shi ne ya koma inda Alh Audi ya zaɓar masa. Ya so yi mata bayani cewa Tony ne ya canja masa kuma ya ce inda ya kaishi nan Nanna ta zaba saboda duka takardun ya ga sa hannunta da idanunsa. Wasu maganganun sam baya gane ma'anarsu ma. Abu ɗaya ya fahimta shi ne, Nanna tana fushi kuma ba za ta yafe ba sai ya gama karatu. Tun yana son sanin me yake faruwa har shima tasa zuciyar ta kangare ya dena damuwa. Wurin Raymond ya tafi batare da sanin abokansa ba aka kaishi ofishin Mr Darcy. Takardar contract ɗin ya sakawa hannu an ɗaukesu shekara biyu. Banda zunzurutun maƙudan kuɗaɗe ga gida da mota da aka haɗasu dashi. Sai da aka kammala komai sannan Raymond ya yi kiransu Tomaz zuwa ofishin. Sunyi mamaki da matuƙar farinciki ganin cewa Arƙam ya damu da rayuwarsu. A matsayinsa na shugabansu dai kuɗinsa yafi nasu amma hakan bai dame su ba. Dukkaninsu sunyi bankwana da fatara da shiga aljihunsa, kodayake yanzun ma alfarmarsa suke ci. Bayanin ƙarshe a contract ɗin shi ne basu yarda a saka su waƙa a lokutan karatunsu ba. Suna buƙatar a dinga basu isasshen lokaci saboda su ukun duka cikar mafarkinsu shi ne zama cikakkun likitoci. Da wannan ne *3ripleA* suka samu kafuwa. Sunan nasu inkiya ce ta nahiyar da suka fito. Africa ta Arƙam, Asia ta Tomaz sai America ta Josh. Sati guda da gama jarabawarsu ta ƙarshe wadda a ƙa'ida bayan fitar sakamako zasu fara internship ne suka yi reporting a Ace Entertainment. Waƙoƙi takwas Mr Darcy ya buƙaci suyi domin fitar da album ɗin farko. Watanni uku garesu kafin fara zuwansu asibiti saboda haka nauyin kacokan yana wuyan Arƙam. Ba dare ba rana ya duƙufa wurin rubutun waƙoƙin, rerawa da kuma gyare-gyaren da Mr Darcy ya ke ganowa. Rashin bacci, ƙara taɓarɓarewa da raunin ibada da rashin walwala saboda ƙarancin hutu ne suka sarkafi wuyansa. A ƙoƙarinsa na ganin ya kammala rubuta wakokin a wata uku sai ya zamana ɗaukar video ne ya rage ko sun fara zuwa asibiti ya jefa shi cikin takura. Cikin sati goma ya gama haɗa komai. Wannan ƙwazon nasa ya sake tafiya da imanin Mr Darcy. Sun fara zuwa asibiti aka nemi sulhu da ƙyar da siɗin goshi da hukumar asibitin wurin samar musu lokutan zuwa shooting. A tsukin wata biyu sun soma fita hayyacinsu sai da afa ƙwayoyi suke iya wasu ayyukan. Idan za'a fara recording sai an tabbatar sunyi akalla baccin awa takwas sannan a basu maganin wartsakarwa. Daga nan sai masu kwalliya su gyara musu tun daga kai har kafa sannan designers su kawo kayan da suka dace. Hauka ne kawai basu yi ba saboda mugun stress a dalilin haɗa gudu da susar duwawu. Arƙam ya fi kowa jigata shi ya sa ma ya fisu shan ƙwayoyin. Ranar da aka gama ɗaukar tamkar sallah take garesu. Sai dai suna komawa asibiti aka sanar dasu sai sun sako wata biyun nan saboda basu taɓuka abin kirki ba. Ba haka aka so ba amma sun san anyi musu adalci sosai. Koyon aiki suke yi ka'in da na'in. Wata guda bayan an gama shirin komai aka saki album ɗin 3tripleA na farko. Cikin sati guda Mr Darcy ya mayar da kuɗaɗɗen da ya kashe harda mahaukaciyar riba. Ba jimawa album ya zaga ƙasar Amurka da kewaye babu zance sai na sababbin mawaƙan nan. Sunyi suna saboda daɗin murya da waƙoƙin Arƙam. Kyawun samarin ya ƙara rura wutar samun alkhairinsu. Kuɗi kam tashin farko suka yi na ban mamaki. Tun ba a gane ba kuwa har aka waye dasu a asibitin da suke. Mutane suka dinga tururuwar zuwa ganinsu. Idan aka hanasu shiga sai suyi ƙaryar cuta. Hanyar kuɗin shiga ta ƙaru ga asibitin duka darajar waƙoƙin ɗan Haj Manga. Ga kudi ga suna amma duk waɗannan basu hana rayuwar Arƙam shiga wani irin yanayi na dimbin damuwa da kaɗaici ba. A zahiri kullum ya fito sai sakin fuska da yawan murmushi saboda faranta rayukan masoya. Babu wanda ya san irin ƙuncin da yake tattare dashi na rashin ɗumin mahaifiya da ƴan uwa. Privacy tuni ya yi ƙaura. Yanzu bai isa ya shiga wuri mai mutane ba indai ba cikin asibiti ba sai da masu tsaronsu. Idan ba haka ba kuwa mutane ke kewayesu ayi ta ɗaukar hoto ana rungumarsu. Ƴan mata da dama suna cikin gararin soyayyar waɗannan zaratan matasan. Bayan an gama cin kasuwar album ɗin farko da wata biyar Mr Darcy ya buƙaci su fara shirin na biyu da za a saki a shekara mai zuwa. Arƙam da ya tabbatar da cewa kansa zai iya bugawa bai yi wata wata ba ya nemi a soke contract ɗin tunda basu karɓi wasu kuɗi na shekarar ba. Mr Darcy ya yi tsallen daka yaƙi amincewa saboda shi ya san me ya samu a dalilinsu. Abu dai ya kusa zama rikici ana batun zuwa kotu tunda sun sa hannu. Sai da aka kai ruwa rana Arƙam ya yarda da album na biyu amma ya jaddadawa su Josh daga wannan ba zai ƙara ba. Rayuwarsa gabaɗaya a ƙuntace yake jinta. Babu wata walwala ko manufa. Irin rayuwar da ke samun akasarin mutanen da suke harkar entertainment industry dai. Waɗanda suke bibiyarka da dama saboda suna ƙaruwa da kai ne, karancin kusanci da mutane saboda tsaro, shaye-shaye saboda yawan damuwa da stress da sauransu. Mafiya yawansu a haka rayuwarsu ke lalacewa suyi ta yawo tsakanin asibiti da rehabilitation centres. Idan damuwa ta yi yawa tare da ƙarancin imani sai ka ga mutum yana harin rayuwarsa da kansa. Wa iyazu billah! Kwanaki na ƙara tafiya al'amura suna ƙara rikicewa Arƙam. Sun cika alƙawarin contract da blockbuster album wanda ya sama musu kuɗi fiye da zato da tsammaninsu. Mr Darcy ya so matuƙa ko shekara su ƙara yarda ayi amma fafur Arƙam yaƙi. Hargitsin rayuwarsa shi ne babbar damuwarsa. Shekara da shekaru uwa taki nemansa. A ɓangare guda kuma masoyansa sun hana shi mayar da hankali akan karatunsa sosai. Daga ƙarshe asibiti daban ya nema inda zai yi residency ɗinsa duk don ya sami nutsuwar zuciya. Sai da ya rage tsayin gashinsa ya dena kitso sai barin afro da ya ke shan gyara. Ya kuma ƙara da tara kasumba kuma ya yi sa a ba kasafai ake gane shi ba. Wata rana ya dawo daga asibiti a gajiye zuciyarsa ta kwaɗaitu matuƙa da son gida. Numbar Tony ya nemo a tsohuwar wayarsa ya kira. Bugu biyu Tony ya ɗauka a gigice don rabonsa da Arƙam yafi shekara uku. Ƙarya ya ke yiwa wanda ya sa shi ɗauke shi a kodayaushe ya ce a bashi kuɗi yana damunsa da son zuwa gida. Kuɗin makarantarsa tuni aka gama biya duk don kada ya sami damar cewa zai zo gida. Muryarsa ya canja kamar mai shirin kuka, "Arƙam kaine?" [2/23, 7:34 PM] Nasma: Mutumin da bai iya faɗa ko ɗaga murya ba yau ɓacin rai ya sanya shi yiwa Tony tsawa. A wannan lokacin babu abinda Tony ya hasko sai fuskar Haj Manga, ya haɗiyi yawu da ƙyar. Arƙam ya cusa yatsunsa cikin tulin gashinsa wanda na gaban yafi tsayi da cika, "ka haɗani da Nanna yanzu." Cikin rawar murya Tony ya amsa da cewa, "Arƙam ka kara haƙuri ka gama karatun kafin ka nemeta." Yadda zuciyarsa ta raunana bai san lokacin da ya sake ƙanƙame kan wayar yana zubar da zafafan hawaye "Tony! I am not happy. I need my mother, am so lonely." A karon farko da tausayin Arƙam ya ɗarsu a zuciyarsa kenan. Yana da kyakkyawar masaniya akan manufar mutane biyu akansa. Alh Audi da wanda ya ke yiwa aiki a bayan fage, idan ya barshi ya koma gida yanzu yana da yaƙinin zai iya rasa rayuwarsa. Bayan gajeren tunani kawai sai ya katse kiran. Matarsa da take amsa waya a matsayin Madam Zainaba ya kira daga ɗaki. Umarni ya bata cewa idan Arƙam ya kirata ta katse wayar kada ta yarda ta yi masa magana. Abin ya bata mamaki tunda ta san komai akan abinda maigidan nata yake yi. Ba jimawa kuwa ya kira ta ɗauka taƙi amsa tarin tambayoyinsa sai ma kashe wayar da ta yi. "Tony meye manufar yi masa haka?" Da dukkan gaskiyarsa ya ce "ina ganin lokaci ya yi da zai dawo wurin mahaifiyarsa. Na gaji da yaudararsa da ƙarya. Zuciyata tana bani shirunmu zai tunzura shi ya kamo hanyar gida. Ki zama cikin shiri garin zamu bari." Shi kuwa Arƙam shirun nasu ba komai ya ƙara masa ba sai hasala da mugun bacin rai. Wayarsa mai tsada ya rotsa da ƙasa saboda takaici. A take ya ƙudurtawa zuciyarsa ba zai kuma neman Nanna ba sai ta neme shi da kanta. Ya sha yin kuka, ya yi roƙo da magiya ga Tony da wadda ta kira kanta da Madam Zainaba duk a banza. Tabbas kafin tahowarsa Madam Zainaba ta koma gidansu. Ko fuskarta ba zai iya tunawa ba bare murya, amma ya tabbatar da kusancinta da Nanna shi ya sa bai taɓa ƙaryata ta ba. *** Kwanci tashi Tauhidat ta shiga js3 yayin da Jamal ya fara Abti America, jami'a me zaman kanta a garin Adamawa. Soyayya da gatan da Haj Manga ke nuna musu babu kama hannun yaro. Zuwa yanzu Tauhidat ta san matsayinsu a gidan saboda haka take ƙoƙarin kamewa daga wasu abubuwan kada a dinga ganin zaƙewarta. Hakan yana ɓata ran Haj Manga amma mahaifinta yana yawan ja mata kunne da cewa ita ɗin ba kowa bace face ƴar Abayomi direba. Yawan nasihunsa a gareta ya sa ta iya riƙe matsayinta duk da tana da ƙarancin shekaru. Girma ya fara zuwa ta zama ƴar budurwa mai shiga rai da wuri saboda halinta na surutu da yawan tambaya. Iyakar surutun nata dama daga babanta sai Nanna da Madam. Idan taje hutu wurin danginsu sai ka gani a yanayin Haj Manga. Gidan gabaɗaya dena yi mata daɗi ya ke yi sai ƴarta ta dawo. Jamal tun yana cewa ta yi masa ƙwace har ya dawo ya zama basu da sirri ga juna. Babbar matsalarsa ita ce zamansa riƙaƙƙen ɗan ƙwaya da shaye-shayen kayan maye. Kunnuwar wannan masifa cikin rayuwarsu ba ƙaramin tashin hankali yazo wa Haj Manga ba. Alh Audi ne da wannan aikin kamar yadda ta gano daga baya. Shi ya umarci Tony ya ƙulla abota da Jamal ya dinga jansa a jiki. A haka rayuwarsa ta ɗauki turba daban har ya sauya suna zuwa Tarantula a wurin abokan shashancinsa. Haj Manga ta yi kukan ta yi faɗan sai daga baya ta fuskanci Alh Audi da gangan ya yi mata haka. Bai ji kunya ba ranar da ta tunkare shi ya ce yana son nuna mata cewa ƴaƴanta basu isa komai akansa ba. Duk wani shiri da ta fara akan gina Jamal dole ya rushe. Mutane suna ganin baƙinta akan rashin nuna ƙyama akan halin ɗan nata sai ma ƙara jansa a jiki da take yi. Ita kuwa ta fi kowa sanin idan ta bar Jamal gabaɗaya tamkar ta amince Alh Audi ya yi galaba akansu ne. Tauhidat tana daga cikin mutanen da suka san ɓoyayyun halayensa don ta sha kama shi a wurin dabbobi yana yi. Kullum roƙon rufin asiri yake yi a gareta yana nuna mata zai dena. Damuwarsa bata wuce yawan kukan mahaifiyarsa akan yayansa ba da sababbin halayensa, sai dai kuma duk yadda ya so denawa abu yaci tura. Gashi har yanzu bai san takunkumin da Alh Audi ya sanya mata ba. Hasali ma jansu yake yi a jiki sosai da shi da Tauhidat ɗin. Shamsu a lokacin yana bautar ƙasa bai fi a kirga ba ta taɓa ganinsa tun zuwanta gidan. Yau ta kama Asabar Jamal ya zo hutun ƙarshen mako gida. Yana zaune a ɗakinsa ya ji bugu haɗe da sallamar Tauhidat. Da sauri ya kashe tabar wiwi ɗin hannunsa ya tura kwalaben benelyn ƙarƙashin kujera ya tashi yana layi. Airfreshner ya dinga fesawa sai da ɗakin ya yi ƙaramin hazo sannan ya buɗe. Sanye take da kayan islamiyya riga ta dan wuce gwuiwa da wando sai hijab. Rinannun idanunsa ya sauke mata ta ja da baya. Dama ba shiga zata yi ba don Papa da Madam Zainaba suna mata gargaɗi sosai akan haka. Tsabar wayonta yasa ta gane ya sha wani abu ta taɓe baki "Tarantula ne ko Jamal?" "Ke. Fa. Akwai sa ido" ya ce murya na rarrabewa Murmushi ta yi masa wanda ya hasko siririyar wushiryarta ya kara mata kyau "na dai gane Tarantula ne. Nanna ke kiranka dama." Gabansa ya ɗan faɗi don ko yaya ya sha wani abu tana saurin ganewa. Cewa ya yi ta faɗa mata yana wanka zai shigo idan ya fito. Dariya ya bata ganin bai yi tunanin Nanna za ta iya gano ƙaryarsa ba, ta ce, "To waye ya faɗawa Tauhidat ɗin yana wanka?" "Eh to kuma da ƴar gaskiyarki. To jirani minti goma, a'a biyar ma ya isa." Ya koma cikin ɗakin da sauri duk da yadda take faɗa masa islamiyya za ta tafi. Tsayuwa ta yi a bakin ƙofar saboda muddin ta koma sai Nanna ta tambayeta ina yake. Idan ta yi mata ƙarya kuma za ta yi saurin gano cewa ya yi halin ne ta shiga damuwa. Ƙarar buɗewar ƙofar ɗakin Shamsu ta ji ta kawar da kan ta gefe. Tun zuwanta gidan bata taɓa ganin ya sakar mata fuska ba. Wani wari da bashi da ƙari ne suka haɗu suna silalowa daga ɗakin nasa zuwa hancinta. Cikinta ne ya soma yamutsawa amma maimakon ta ja baya sai ta tunkari ƙofar hannunta akan hanci. Ko wani abu ne ya mutu a ɗakin ta tambayi zuciyarta. Niyyarta ta rufe ƙofar ta sanar da mai yi musu shara ya duba sai ganin mutum ta yi tsaye ƙiƙam a bakin ƙofar. Da saurinta ta ja baya a daidai lokacin da ya watsa mata wani mugun kallo ya rofo ƙofar garam akan fuskarta. Jiki na rawa ta juya za ta bar wurin kiran da Jamal ya yi mata ya ƙarasa gigita ta. Ganin yadda tsoro ya bayyana a fuskarta ya sanyaya masa jiki. Ƙofar ɗakin ya kalla ya bita da kallon tuhuma. Tambayoyi ya dinga jero mata yana bin ƙofar ɗakin da harara tamkar ita ce Shamsun. "Kin haɗu da Shamsu ne? Ya yi miki wani abu?" Gaba ta yi da sassarfa kafin ta iya bashi amsa "mu tafi Jamal na san Nanna ta gaji da jiranka kuma nima na makara islamiyya." Zargi ne ya ɗarsu a ransa game da Shamsu saboda ganinta da ya yi a bakin ƙofar dakin. Nan da nan kuwa zuciyar ƴan kwaya ta tunzura shi ya kama ƙofar ya murɗa a fusace. Ko gezau bata yi ba alamun an rufe da mukulli. Bai tsaya tunani ba ya shiga bugun ƙofar da ƙarfinsa. "Kai dalla Malam ka buɗe ƙofar nan idan ka cika namiji." Mugun tsoro ne ya sake kama Tauhidat ta dawo tana roƙonsa ya bari saboda babu abinda ya yi mata. Kallon da ya yi mata da jajayen idanunsa da mayen wiwi ya fara saki ya sata yin baya. Bata bar magiyar ba shi ma ya cigaba ƙofar. Daga shi sai tawul a kugu ga danshi a jikinsa da gani daga wanka ya fito. Abinka da dama ta ciki na ciki ga kan ba daidai ba ƴan abubuwan da ya sha sun fara yi masa karo kawai sai Jamal ya kai masa naushi a baki. Tauhidat cikin gida ta ruga a guje lokacin da Shamsu ya shararawa Jamal mari rai a ɓace. Sa'ar ganin Haj. Manga ta yi a ƙasa za ta fita ta riƙo hannunta da sauri tana faɗa mata me yake faruwa. Ita ma nata hankalin tashi ya yi suka dunguma harda Fanna da suke kallo ita da Kulsum da ƴarta ta biyu Aimana. Turus kowa ya yi musamman Haj. Manga da suka fito. Shamsu ne da hannu ɗaya ya shaƙe Jamal ya manna bayansa da bango. Yanayin jikinsu dama ba ɗaya ba. Shamsu ya ɗara shi tsayi sannan kana ganinsa ka ga ƙaƙƙarfan namiji. Jamal kuwa ɗan hutu ne daga sama har ƙasa. Wai amma duk wahalar nan da yake sha yana kakari bata hana shi magana ba. "Ko kallon banza ka sake yiwa ƙanwata sai naci b...." Haj. Manga ta daka masa tsawa "ya isa haka". Ta kalli Shamsu da ko kunyarta bata sa ya sake shi ba ta ce masa "sakar min ɗa kai kuma." "Idan na ƙi fa?" Ya ce a wulaƙance yana taɓe baki. Furucinsa ya ɗaurewa Tauhidat kai. Fanna ma duk tsagerancinta sai a bayan ido take iya yiwa Haj. Manga maganar banza, shiyasa yau daɗi ya kama ta. Faɗan da babu ruwanka dadin kallo ne da shi. Cikin takunta na matar da bata ɗauka bare jurar raini ta isa gabansu ta ɗauke Shamsu da marin da ya yi sanadiyar sanya shi sakin Jamal. Wurin tamkar ɗaukewar wutar nepa don kowa shiru ya yi. Ransa ya yi matukar ɓaci ya dago ido ya na kallonta, "Ki ka mareni?" Ta cikin zagayayyen farin gilashin idanunta ta zuba masa nata idanun sannan ta nuna shi da yatsa, "ko za ka rama ne?" Rai na ƙuna ya shige ɗakinsa ya bugo ƙofar da ƙarfin tsiya. Juyawa ta yi ta kalli Jamal takaicinsa yana mamayarta. Cikin faɗa ta ce, "me ya haɗaka dashi? Ban gargaɗeka akan iyalin Audi Karam ba?" Mamakin maganarta ya saka kowa mutuwar tsaye banda Jamal da ya daka tsalle yana ɗaga hannuwa irin na jinjina, "wooo Nanna, wooo Nanna kina fire my sweet..." "Shut up!" Ta daka masa tsawar da ta sa ya kama baki ya bame kamar ba shi ba sannan ta sake tambayar me ya haɗa su. Zumburo baki ya yi ta ɗago hannu za ta make shi ya yi saurin mayar da shi sannan ya nuna Tauhidat, "fitowa nayi naga ƙanwata a tsaye a ƙofar ɗakinsa jiki na shaking." Haj. Manga ta gyaɗa kai tana jiran ya ɗora bayanin ta ji ya yi shiru. "Daga nan sai aka yi me? Ta ce ya yi mata wani abu ne?" Sosa keya ya kama yi yana ɗan murmushi "Eh to gaskiya bata ce ba, amma yanayinta yasa naji gara na tauna aya ko don tsakuwa taji tsoro." Fanna kasa daurewa ta yi saboda yanayin maganarsa ta kwashe da dariya. Ita fa saboda shirmensa shi ya sa take ɗan dasawa dashi. "Jamal ba tauna tsakuwa kayi don aya taji tsoro ba?" Yana tsaye gaban mahaifiyarsa ya ɗago mata hannu da ƴar dariya "sammakal Anti Fanna tunda kin gane." Ita ma Haj. Manga dariyar ya so bata ta riƙeta tare da kama kunnensa "gashi nan an tauna ka ai kafin ka tauna ayar. Tauhida ya taɓa ki ne?" Girgiza kai tayi idanunta akan Jamal da ta ke jin takaicin ya janyowa kansa duka a dalilinta. "A'a Nanna kawai fa war..." Kafin ta ƙarasa Haj. Manga ta ja hannunta suka koma ciki saboda hasashen me za ta ce. Fanna ta so samun kanun labarai ta samu ta haɗa gulmar da za ta kaiwa mahaifinta. Haj. Manga ta ja ta har ɗakin farko idan an shiga falonta kafin babban wanda ta barwa Tauhidat. Nan suka shiga tana riƙe da hannunta har lokacin. Ita duk tsoro ya kama ta. Jamal na isowa Haj Manga ta tura ƙofar. Ransa kuwa ya ɓaci ya soma ƙunƙuni. "Not fair Nanna, ni ne fa na fara shigar mata. Ya ci ace dani aka ƙarasa komai. Sai da aka zo wurin dadin za ki koreni" Kama ƙofar ya yi zai buɗe yaji ta ce, "Jamal" da muryar gargaɗi. Ba don ya so ba ya haƙura amma sai da ya manna kunnensa a jikin ƙofar. Ganin yadda Tauhidat ta tsure yasa Haj. Manga sakin fuska tana murmushi, "ni kam abar a tausayawa ce! Daga ke har Jamal din babu wani jajirtacce. Yara sai kace ƴaƴan tsintuwa ba raino na ba." Dariya ce ta so suɓucewa Tauhidat ta sa hannu ta danne bakin. Daga waje kuwa muryar Jamal suka ji yana ce wa "Nanna ya haka ne, sai ki sa ta raina ni. Namiji kamata kina zubar masa da aji a gaban ƙanwarsa." Dama ta yi zargin ba zai tafi ba. Taɓe baki ta yi "Namamajo dai." Tana jiyo takunsa ya bar wurin yana mita suka yi murmushi ita da ƴarta. Tambayarta ta yi ko wari taji a ɗakin Shamsun ta amsa da eh duk da kasancewarta a waje. Gargaɗi Haj. Manga ta yi mata sosai akan ko hanya kada ta yarda ta dinga haɗata da shi. Babu doguwar tambaya ta yi alƙawarin bin umarninta. Duk da muguwar makarar da ta yi kuwa a haka ta wuce islamiyya. Shi kuwa Shamsu tunda ya koma ɗakin zuciyarsa take tafasa da ɓacin rai. Yadda ba ya son mutane ko shiga shirginsu haka ya ke so shi ma kada a shiga nasa. Duk faɗin gidan kuwa ba shi da abokiyar hamayya kamar Haj. Manga. Wayar mahaifinsa ya kira yana kumbure-kumbure ya faɗa masa cewa matarsa ta mare shi sannan wannan ƴar aikin ta ta wato Tauhidat ta ji warin ɗakinsa. Da farko Alh Audi sai da yaji tsoro ya sarƙafi zuciyarsa saboda sanin wace ce Tauhidat a gareshi. Haƙuri ya baiwa Shamsun akan zai yi mata magana idan ya dawo sannan ya ajiye wayar. Hularsa ya cire ya soma shafa sankon kansa yana faman tunani. Sai ga shi yana murmushi bayan mintuna kalilan daga baya ma ya kwashe da wata muguwar dariya. Jinjinawa ƙwaƙwalwarsa mai zurfin tunani da hango mafita a lokacin da ya dace ya yi. Daki-daki zai bi komai har ya samu biyan buƙata. Koda ya dawo da daddare bayan ya ci abinci ya tara iyalin nasa gabaɗaya banda Haj. Manga. Lokacin da saƙo ya risketa na kiransa waya take yi. Hannu ta ɗagawa Madam Zainaba alamun kada ta dameta da kiran nasa. Sai da suka yi jiran kusan rabin awa sannan ta iso tana zuba wani irin ƙamshi mai ratsa zuciya. Jamal kallonta ya yi tare da yin alamar ta yi kyau da hannun damansa. Kan sa ta shafa cike da kulawa ta sake ƙular da Alh Audi da Shamsu. Zama ta yi ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan ya soma magana yana ta ƙoƙarin danne ɓacin ransa. "Hafsatu me ya kai ki shiga rigimar yara harda marin Shamsu? Gidan nan kaf kun san cewa shi ba mai son hayaniya bane shi ya sa yake ƙoƙarin nesanta kansa daga kowa." Ɗago kai ta yi cike da isa ta ce "ka tara mu ne ka ji abinda ya faru ko ka tarewa ɗanka? Idan na farkon ne na riga na yiwa Tauhidat faɗan kada ta sake bari wani abu ya haɗata dashi. Sannan kuma na mare shi saboda rashin kunyar da ya yi min. Idan kuma na biyun ne to sai in ce asuba ta gari don ina da abinyi kafin na kwanta." Tashi ta yi abinta ko waige babu ta ƙara gaba. A yadda Alh Audi yake jan Jamal da Tauhidat a jiki kuwa sai kunya ta rufesu. A fahimtarsu suna da laifi suma bai kamata ta bada wannan amsar ga mijinta ba a gabansu. Shi kuwa Shamsu da igiyar saki a hannunsa take da ta daɗe da bar musu gida. Fanna dai nata ido ne take ta rarrabawa a tsakaninsu. A kunyace Jamal ya ce "Baba kayi haƙuri" ya kuma juya ga Shamsu shi ma ya bashi haƙurin. Tauhidat ma sahunsa ta bi. Alh Audi kuwa ya dinga rangwaɗa kai gefe kamar tsohon ƙadangare yana cewa babu komai tare da saka musu albarka. Kuɗi ya kawo masu tsoka ya damƙawa Shamsu. "Gobe ka ɗauki ƙannenka kuje shopping kowa ya sayi abinda yake so." A take ya raba kuɗin gida huɗu ya miƙawa Fanna kashi biyu na Kulsum da Aimana sannan ya bawa Jamal kaso ɗaya ya miƙe. Alh Audi kuwa ya nuna kamar ransa ya yi masifar ɓaci ya daka masa tsawa "ba na son rashin hankali. Ina na Tauhidat? Ita da yayanta ƴaƴa Nannanku ta ɗaukesu saboda haka a wannan matsayin kai ma za ka mu'amalance su. Sannan cewa nayi kuje shopping ba a raba kuɗin ba." Miƙewa Jamal ya yi da ido ya yiwa Tauhida inkiya ita ma ta tashi. "Baba sammakal fa, no worries. Ni da ƙanwata zamu raba wannan. Ke muje." Ita dai duk abinda aka yi babu wanda ya ɓata mata rai domin ta san matsayinta kuma ta riƙe shi. Tsoronta ɗaya bai wuce rigimar da ta janyo ba. Tun zuwanta gidan ta san Nanna da Baba da wuya su kwana uku ba ka ji tana maida masa magana ba. Tana matuƙar ƙaunar Nanna amma ta kasa fahimtar me yasa tsakaninta da mijinta ba irin yadda yake da Anti Fanna bane. A koridon da zai sada Jamal da falon hanyar ɓangarensu ya tsaya ya bata kuɗin ko ɗaya bai zara ba. Girgiza kai ta yi ta ja baya. Ya murtuke fuska kuwa. "Ina wasa dake ne? Come on karbi ki ware dare ya yi aje a kwanta." "Nanna za ta yi faɗa fa." "Ki ce mata yayanki ne ya baki." "Yau kuma?" Ta ce da murmushi a fuskarta. Ƙememe yaƙi yarda ta kira shi Yaya ko Broda yadda take kiran Shaheed. Wai kara masa tsufa za ta yi ya tashi daga autan Nanna. Duk abinda suka yi a idon Haj. Manga, har kullum wadannan hallaye na Tauhidat su ke ƙara mata matsayi a zuciyarta. Lokacin da Tauhidat ta shiga aji huɗu a sakandire ya yi daidai da kammala digiri ɗin Shaheed daga Abdullah Gül University a ƙasar Turkey. Zuwansa gida sau ɗaya tun bayan tafiyarsa. Duk lokacin da ya yi waya da mahaifinsa ko Tauhidat zancensa ba ya wuce na matsananciyar kewarsu da take damunsa. Su ma ɗin hakan take a wurinsu. Papa Abayomi ba ya gajiya da yiwa jama'ar gidan nan hidima musamman Haj. Manga da Alh Audi. Sunyi masa komai a rayuwa. An raba ƴarsa da maraicin uwa ga makaranta mai kyau tana zuwa. Babban ɗansa kuwa sai son barka. A nasa ɓangaren shi ma Shaheed ɗin ba ƙaramin ƙoƙari ya ke yi a makaranta ba saboda kada ya bawa waɗannan mutane kunya. Burinsa ya dawo ya sami aiki mai kyau domin mahaifinsa ya huta. Yau ta kama Juma'a shabiyu da rabi Tauhidat ta dawo gida. Tun a mota take yiwa Papa kuka yana bata haƙuri. Speech and Prize giving day ɗinsu zai kama ranar hutu ne suna ta shirye-shiryen gabatar da drama. An yi rehearsal (gwaji) na sati uku sai da ya rage kwanaki goma aka cire sunanta daga ƴan dramar wai ta fiye murmushi. Da yarbanci suke magana a motar hancinta ya yi ƙato saboda kumburi. "Papa meye laifin yawan murmushi?" "Babu" ya ce da taushin murya. Ya tabbatar da wuya idan Haj. Manga ba ta ɗora masa laifin saka ta kuka ba. "A drama ɗin taku amma wane matsayi aka baki? Ana buƙatar yawan murmushi ko kuwa?" Kai ta duƙar a hankali ta ce "ɓarauniya zan fito. Sata zamu je gidan soja a kama mu." Abayomi ya kashe motar yana dariya "banda abinki ɓarawo ina ya ga ta dariya. Yana dariya fa za'a kama shi da sauran abokan sana'ar tasa." Yadda taci burin dramar nan dole ta yi kuka. Jan hanci ta yi ta ce "to su bani police mana." Dariya maganar ta bashi "kiyi haƙuri kawai, Police ɗin ma ai ba a son wanda basa iya rufe bakinsu. Sai a raina su." Fushinta ta ƙaraci yi saboda ganin ya goyi bayan abinda aka yi mata ta haƙura. Alƙawarin tafiya da ita wurin Iyaa Bayo hutu da ya yi mata ne ya sanyaya ran ta. Ta saɓi jakarta za ta shiga gidan ya sake kiranta. Fuskarsa kaɗai ta sanar mata magana ce da ya ke so ta ɗauka da mahimmanci. "Hajiya ta faɗa min zaku je a nema miki wata takarda da zaki iya zuwa wurin Shaheed jiya. Wai tana so muje graduation ɗinsa. Ni dai na faɗa mata ba zan je ba." Tauhidat ta ce "Papa me ya sa?" Murmushi ya yi mata ganin tana neman tayar da hankali "duka irin kyautatawar da ake yi mana a gidan nan kada ki manta matsayina bai wuce direba ba. Bai kamata na saki jiki nayi ta ƙara musu nauyi fiye da wanda suka ɗauke min na karatunku da ciyar damu ba. Kema ba don Hajiya ta nuna ɓacin rai ba da kinyi zamanki. Bana so a kwaɗaita miki rayuwar da ba taki ba." Maganganunsa sun sanya jikinta yin sanyi. Nuna masa ta yi ita ma za ta cewa Nanna ba za ta ba ya ce kada ta soma. Ya gwada kuma tabbas ba ƙaramin ɓacin rai ta nuna masa ba. Nasiha dai ya dora mata irin ta uban da ya ke tsantseni da ƙoƙarin kare martbar iyalinsa a idanun masu kyautata masa. Ɗakinsu da Nanna ta wuce kai tsaye da zummar kai mata ƙarar malamin da ya cireta daga drama. Ta yi sallama ta kai sau biyar a ƙofar ɗakin babu amsa. Nata ɗakin ta shiga da yake jikin na Haj. Manga ta cire uniform ta yi wanka. Sai da ta gama shiryawa ta shiga ɗakin da sallamarta. A zaune ta ganta bayanta jingine da gado da alamun sallah ta idar bacci ya ɗauketa a wurin. Fuskarta ta yi shatin hawaye da ya bushe ga hoto ta damƙe a hannunta. Ƙwalla ce ta cikowa Tauhidat ta fita daga ɗakin da sauri. Bata da buƙatar neman bayani ta gama gane hoton da ya ke yawan sanya Nanna kuka. Hoton Jamal, babansu da ɗayan kamar yadda take kiran Arƙam. Tun bata daɗe da zuwa gidan ba ta san babbar damuwar mariƙiyarta. Nata ɗakin ta koma ta ci kuka ita ma har bacci ya ɗauketa. [2/23, 7:34 PM] Nasma: Sai dare suka haɗu da Haj. Manga wadda ciwon kai ya hana fitowa. Kamar babu abinda ya faru haka ta sakarwa Tauhidat fuska tana ta tsokanarta akan cireta daga drama da aka yi ita kuma tana mita. Madam Zainaba sai kallonsu take yi ɗaya bayan ɗaya suna ta dariya cike da nishaɗi. Abu ɗaya ne zai tabbatar da farincikin Hajiyarta, bayyanar babban ɗanta. To ita ma Tauhidat ɗin abinda yake damunta kenan. Kwanaki ma sai da tayiwa malamin islamiyyarsu tambaya akan addu'o'in biyan buƙata. Amsar da ya bata take son faɗawa Nanna yanzu da ta ga hankalinta a kwance. Jira ta yi sai da Madam Zainaba ta tafi kwanciya sannan ta matsa jikinta. Shafa kanta Haj. Manga ta yi tana murmushi, "Akwai magana a ɗan bakin nan namu ko Tauhida? Ya aka yi?" Kai ta sunkuyar saboda nauyin abinda za ta faɗa. Sai da Haj. Manga ta sake tambayarta sannan ta faɗa mata malaminsu ya ce duk mai son biyan buƙata ya yawaita sadaka da sallar dare. Farinciki ne ya mamaye fuskarta bayan ta gama sauraron bayanin. Ko a mafarki bata tunanin akwai wata rana da za ta yi dana sanin sanya Tauhidat a ƙarƙashin inuwarta. Yarinya ce mai kyawawan hallaye da ɗabi'u, ga ta sam bata iya fushi ba. Fuskar nan kamar gonar auduga. Sai ayi abinda ya kamata taji haushi ta bar Nanna da ɓacin rai ita kuwa tana murmushi. "Kin ga muna sadaka sosai Tauhida, kuma sallar ma ina ƙoƙarin yi cikin dare." Ƙeya Tauhidat ta sosa da ɗan murmushinta "Nanna harda kuka fa Malam ya ce. Muna addu'a muna ƙanƙantar da kai da kukanmu." Haj. Manga bata san lokacin da ta rungumeta ba. Ba wai don bata yin ƙiyamul laili ba, sai dai maganar Tauhidat ta ƙara mata ƙaimi sosai. Sun ɗauki lokaci suna hira mai daɗi tsakaninsu, tana son ta tambayeta wannan ɗayan na jikin hoto amma kuma tana gudun ƙara mata damuwa. Da haka suka yi sallama, har ɗakinta ta rakata tana tunatar da ita yin alwala da kuma addu'a kafin ta kwanta ta ja mata ƙofar. Koda ta koma ɗaki zurfi ta yi cikin tunanin maganganun Tauhidat. Ƙarfe ɗaya da rabi na ranar kuwa alarm ɗin gefen gadon Tauhidat ya buga ta tashi daga bacci sosai a idonta. Ɗakin Haj. Manga taje ta tasheta. Alwala suka ɗauro suka tayar da sallah akan ƙatuwar dardumar da ta shimɗida musu. Tun a raka'ar farko ta soma gyangyaɗi saboda bacci. A daddafe ta karanta suratul A'ala a ta farkon da Nas a ta biyu. Tana sallamewa ta zauna kamar mai addu'a, nan bacci ya sake awon gaba da ita. Haj. Manga da ta yi kusan rabin awa a biyun farko tana sallamewa ta kalleta da tausayawa. Kafaɗarta ta dan bubbuga a hankali. "Tashi ki hau gado kinji Tauhida." Firgigit ta buɗe ido ta ce "Nanna kada mu manta da kukan, it is very important." Ta ɗaga hannuwa tana cewa, "Ya Allah Ka bayyana mana ɗayan." A haka akayi sallar rabi gyangyaɗi rabi ibada a gun Tauhidat har ukun dare sannan suka kwanta akan gadon Nanna. *** "Dr. Karam idan baka yi hankali ba depression zai kama ka." Cewar babbar likitan ɓangaren Psychiatry na cikin asibitinsu. Maimakon ya nuna damuwa ko tashin hankali sai ya gyara zamansa kamar wanda ya ke kallon ƙayataccen shiri a TV. Ta san za a rina, patient ɗin nata ba ya jin magana bare shawara. Dama can da ƙarfin tsiya Tomaz da Josh suka kawo mata shi. Abokin nasu ya canja sosai. Babu wani abu da yake burge shi yanzu, kullum cikin ƙunci zuciyarsa take. Ba don aikin da yake zuwa ba ma da al'amarin nasa sai ya fi haka ɓaci. Yanzu ta kai ta kawo ko bacci ba ya iyawa sai ya sha magani. Kuma sau tari kafin huɗu ya farka. Ya mayar da asibitin gidansa saboda ba kasafai yake tafiya gida ba. Duk likitan General Surgery department inda yake residency mai neman a kama masa aiki musamman call (aikin kwana) Arƙam yake bawa. Wuyarta ka ce masa yau kana da uzuri, ko tambayar ƙarin bayani ba zai yi ba saboda tuni ya gano ƙarya suke yi da yawansu. Aiki yake yi tuƙuru shi ya sa duka resident doctors ɗin ya fisu experience da gogewar aiki. "Doctor da kai nake fa." Cikin yanayin ko in kula ya kaɗa kafaɗunsa "ke ce likitan saboda haka ki faɗa min abinda ya kamata nayi?" Girgiza kai tayi ta ɗauki waya ta kira shugaban General Surgery ɗin. Arƙam yana zaune ya lumshe idanunsa ya ji shigowar dattijon likitan. Ya riga ya san komai daga wurin matar shi ya sa bai ce masa komai ba ya kama hannunsa suka koma ɓangarensu. Ofishin Arƙam ɗin ya buɗe da ID card ɗinsa ya shiga ya ɗauko masa mukullin motarsa ya damƙa masa a tafin hannu. "Dr. Karam na baka hutu, bana buƙatar ganinka a harabar asibitin nan sai na nemaka da kaina." "Idan ka bani hutu me kuma ya rage min da zanyi da rayuwata?" Ya ce da wata irin murya mai nuni da ɓoyayyan ciwo a zuciya. "Kaje club, ko wurin budurwarka ko kayi tafiya wani garin. Kawai ka nemi abinda zai baka nishaɗi. Arƙam rayuwarmu ta wuce zaman asibiti kawai. Kana da abokai da ƴan uwa. Ka nemesu kuyi wani abu na shaƙatawa." "Patients ɗina fa?" "Ni da kaina zan yi taking over." Gajeriyar dariya ya yi saboda yadda ya ga babu fuskar musu. Shiga office din ya yi ya ɗauko ƴan tarkacensa ya zuba a jaka ya fita. Garin da alamun hadari duk da dare ne ana iya ganin yadda sama ta yi baƙi. Maimakon ya je kasan wurin parking ya ɗauko motarsa sai ya zabi yin tafiyar ƙafa saboda rashin nisa tsakanin gidansa da asibitin. Tafiya yake cikin nutsuwa yana faman kwaɓar zuciyarsa daga karkata zuwa tunanin Nanna. Wannan hutun dolen ba komai zai janyo masa ba sai tunani. Ya zo daidai wani gidan sayar da abincin 'yan Pakistan daga gefe ya ji kamar ana kabbara. Tsayuwa ya yi cak ya dan koma baya yadda zai sake ji saboda ba a bari su saka spika su dami mutane a cewarsu. Ai kuwa Ladanin kamar ya sani cikin zazzakar muryarsa ya ce, "SAMI'ALLAHU LIMAN HAMIDAN" Wani irin gudu jinin jikinsa da ya tsinke a take ya soma yi. Dan leƙawa ya yi ko zai hango masallatan amma bai gano ba saboda sai an shiga wata ƙofar. To sallar me suke yi shaɗayan dare? "Ohhh Shit!" Ya ce tare da sakin siririn tsaki. Shaf ya manta tun satin da ya wuce ake cewa watan Ramadan ya kusa kamawa. Har ga Allah Ya so yin azumin sai dai rashin mai tuna masa da kuma shi kansa da bai bawa addini mahimmamci ba ya sa shi mantawa. Juyowa ya yi da sauri da zummar barin wurin ya ji ya yi karo da wani. "Subhanallah" Mutumin ya ce lokacin da ya riƙe hannun Arƙam don kada ya faɗi. Kallon da yaga Arƙam din ya yi masa ne ya sa shi saurin bashi haƙuri "sorry, it is a Muslim expression (kayi hakuri, kalma ce da musulmi suke a amfani da ita.)" Gyara zaman jakarsa ya yi a kafaɗa ya ɗago idanunsa ya zubawa magidancin mutumin da kallo ɗaya za ka gane ɗan ƙasar Pakistan ne "kada ka damu, na san ta. Nima musulmi ne." Murmushi ne ya mamaye fuskar mutumin "Oh Masha Allah, mu shiga ciki. Kaima sallar taraweeh ka zo yi ko?" Hannun Arƙam ya ja suka shiga ya kai shi har wurin alwalar maza. "Idan kuma kayi alwala a gida ka wuce ciki nima zan shigo yanzu idan nayi." Kamar wanda aka ɗaurewa harshe sai ya kasa cewa komai. Jakarsa ya ajiye a gefe ya yi alwalar sannan ya jira mutumin suka shiga masallacin tare. Ni'ima, salama, farinciki, tsoro da tararrabi ne suka dirar masa a lokaci guda. Yaushe rabonsa da shiga masallaci? Yau fa sallar safiya kaɗai ya yi don ba zai kirata asuba ba. Jiya bai yi azahar da la'asar ba. Shekaranjiya...lissafin bashi da daɗi. Mutumin na ƙoƙarin jansa sahun ƙarshe su tsaya kusa da mutane sai yaƙi binsa. A can ƙarshe ya tsaya ya kawo sallolin da ake binsa cike da wasi wasin samun karɓuwarsu. Yana masallacin aka idar da sallar taraweeh. Matsawa ya yi kusa da mutumin da ya janyo shi da sauri ganin ya miƙe. Tambayar da ya yi masa shi kansa sai da yaji kunya. "Yau azumi na nawa aka yi?" "Biyar" ya bashi amsa yana ƙoƙarin danne mamakinsa. Duk yadda aka yi yaron nan yana neman taimako. He looks lost. Wurin zama ya nuna masa "ka jira ni a nan na gama karatu don Allah." Shi da ba gida yake son zuwa ba bai ga dalilin ƙi ba. Zama ya yi ga mamakinsa Limamin sai ya tashi mutumin ya maye gurbin zamansa. Dan matashin da ya yi ladanci ya turo masa speaker gabansa. Bayan sallama da ambaton sunan Allah ya soma tafsir na Suratul Isra'. Kamar ruwa ya cinye Arƙam haka ya zauna yana jin kalaman da suke fitowa daga bakin mutumin nan. Minti talatin da biyar da farawa matashin ya nuna agogo. Nan mutumin ya ƙarƙare karatun da doguwar addu'a kowa ya watse saboda dare ya yi sosai. Daga shi sai matashin sai Arƙam ya taso ya iso gabansa ya miƙa masa hannu. "Suna na Luƙman amma anfi kirana da Abu Usama, wannan ne Usaman babban ɗana" ya nuna ladanin. "Arƙam" ya ce a takaice. Sai da ya sallami ɗan nasa ya ce ya jira shi a waje sannan ya ce "Na kula baka yi sallah tare damu ba. Sallar jam'i tana da lada mai yawa musamman ga shi watan azumi." "Banyi azahar da..." "Garin ya ya?" Abu Usama ya katse shi cike da mamaki. "Ba matsalarka bace" Arƙam ya ce tare da juyawa ya fice abinsa. Ajiyar zuciya Abu Usama ya yi saboda ƙarfafar zarginsa. Lallai yaron na tare da damuwa. Ya rasa dalilin da yake sa mutane sakaci da sallah kuma su nuna rashin damuwa akan girman laifinsu. Sai ka ga al'amuran rayuwarsu suna taɓarɓarewa su rasa gane dalili. Da sauri ya fita ya umarci Usama da ya bishi har gidansa saboda yana tunanin a kusa yake. Ya taɓa ganinsa har sau biyu. Arƙam bai san ana binsa ba har gida. Abin mamaki condo (condominium jerin gidaje ne iri ɗaya hawa hawa. Ya kan kai hawa 20 ko sama da haka, kowanne hawa da gidaje aƙalla biyar) ɗinsu kusa da na su Abu Usama ne don gate dinsu ma daya. Sai dai shi nasu ya fi kyan tsari da tsada. Hankalin Arƙam din yana kan wayar da yake yi yana bayanin maganin da za a bawa wani patient ɗinsa bai kula da shigar Usama lift ɗin da ya tsayar ba. Shi kuwa yaro ya kare fuskarsa da hannu yana biye dashi har ƙofar gidansa a hawa na sha bakwai. A gida ya sami mahaifinsa ya faɗa masa. Da ya tambaye shi dalilin son sanin gidan sai ya yi murmushi. "Nima ban sani ba Usama, haka nan nake jin ina son sanin damuwarsa." Ƙarfe huɗu da rabi assalatu take yi a ƙasar a lokacin, shan ruwa kuma takwas da arba'in na dare. Haka yake kasancewa a sauran ƙasashen duniya. Lokaci da yanayi suna canjawa tare da lokutan sallah. Uku daidai Abu Usama ya ƙwanƙwasa ƙofar Arƙam tare da sallama. Idonsa biyu lokacin ya kasa runtsawa duk da tarin gajiyar da ya kwaso. Kamar daga sama ya ji bugu da sallama. Abin ya ɗaure masa kai amma haka ya je ya buɗe saboda kada maƙota su fara ƙorafi. "What the fuc..." Kasa ƙarasawa ya yi saboda kwarjinin Abu Usama. Mamakinsa ƙaruwa ya yi da ya ga shigo masa falo riƙe da wani abu kamar jaka ƙarama. "Kayi haƙuri naga baka yi kama da mai aure bane shi ne nasa matata yin abincin sahur da kai. A block B gidana yake." "I don't care, please get out!" Cewar Arƙam kamar ya sa ihu. Abu Usama sai ya nemi wuri ya zauna "kawo plate na nuna maka yadda ake ci. Beef Mandi ce da curry (wata na'u'in miya ta mutanen ƙasashen Asia). Ko ka taɓa ci?" Rai a ɓace Arƙam ya ce "wai me ka ke nema a tare dani?" "Abota." "Ba na abota da waɗanda suka girmeni." "Sai ka fara da ni. Yauwa me ya hana ka bacci?" Ya ma dena mamakinsa sai ɗaure fuska da ya yi ya zauna. Abu Usama ya buɗe jakar ya zaro ƙananun robobi da matarsa ta zuba komai na haɗin abincin. Haɗaɗɗen ƙamshin na shiga hancin Arƙam wata muguwar yunwa ta dake shi sai da cikinsa ya yi ƙara. Abu Usama ya buɗe duka robobin ya tura masa gabansa. Ɗage gira ɗaya tare da nuna abincin da hannu Arƙam ya yi "me ka ɗauke ni ne? Mara hankali? Ka shigo min gida da tsakar dare daga haɗuwar da bata wuce awa biyu ba ka ke tunanin zan ci abincinka." Dariya ya bashi domin kuwa kallon yunwa sosai ya ga yana yiwa abincin. Cokalin da aka sako cikin jakar ya ɗauka ya ci daga cikin kowacce roba. Arƙam na ganin ya ci ya ɗauko wani cokalin a kitchen ɗinsa ya soma ci. Idan ka ga yadda yake yi sai ya baka tausayi. Da gani rabonsa da abincin kirki an kwana biyu. Damuwa taci ta cinye shi daga coffee sai dan abinda ba a rasa ba kamar biskit ko ƴaƴan itatuwa yafi ci a wurin aiki. Sai da ya gama tsaf ya tashi zai ɗauko ruwa ya yi kicin-kicin da fuska yana kallon Abu Usama. "Bana son asarar abinci shi ya sa naci." "Ka ji nayi magana ne?" Cewar Abu Usama yana ɓoye dariyarsa. "Kafin kayi ne na faɗa maka dalili. Kada ka fara tunanin wani taimako kayi min babba, kai na taimakawa saboda matarka." "Naji, yanzu dai kayi alwala mu tafi masallaci Usama ya kusa kiran farko." Ɗan jim ya tsaya daga baya kuma yaje ya ɗauro alwalar ya dora jacket akan rigar jikinsa saboda sanyin asuba. Ba ya son faɗa amma yaji daɗin kasancewa da Abu Usama. Ashe haka ya yi kewar kusanci da musulmi ɗan uwansa bai sani ba. A hanyar masallacin babu abinda suka cewa juna. Bayan sun shiga ne Abu Usama ya ce suyi nafilar tahiyyatul masjid raka'a biyu. Idan Arƙam ya taba jin sunan wannan nafilar to ya daɗe da mantawa. Da suka idar ya kuma saka shi yin ra'atainil fajr bayan kiran farko. Daga nan masallacin ya ɗan cika Limamin ɗazu wanda ya kasance ƙani shaƙiƙi ga Abu Usama ya ja su sallar asuba. Ana idarwa aka gaggaisa da gajeriyar hira kowa ya fita sai su biyu. Nutsuwar da yake ji ce ta sa ba ya son barin masallacin. Da wannan ɗaure fuskar don kada Abu Usama ya ce yana jindaɗi ya ce masa yana son zama a ciki. Zai jira zuwa wayewar gari har azahar idan sun zo sallah sai ya fita. "Nima karatu zanyi sai na dan yi bacci zuwa safiya." Ba haka ya so ba amma sai ya ce "idan ka san kana juye-juye ko minshari ka faɗa min nayi tafiyata gida. Bacci yana yi min wahala kuma motsi kaɗan ke tayar dani." "Kada ka damu, karatun ma a hankali zan yi." Can jikin bango Arƙam ya samu ya ɗan kwanta. Tun yana jin sautin ƙira'a mai daɗi daga Abu Usama har bacci mai nauyi ya ɗauke shi. Rabonsa da bacci irin wannan ba zai iya tunawa ba. Minsharinsa saboda rashin daɗin kwanciya ne ya ankarar da Abu Usama gare shi. Ya zura hannuwansa a cikin aljihu ya cure wuri guda kamar ƙaramin yaro. Ji ya yi yana son sanin sa. Yana son jin damuwarsa idan wadda zai iya ce sai ya taimaka masa. Bacci ya yi daɗi ba shi ya farka ba sai da Abu Usama ya yi gyaran murya a spika zai kira sallar azahar saboda Usama na makaranta. A zabure ya tashi ya ga mutane uku a zazzaune suna karatu. Agogonsa ya kalla da sauri ya kalli lokaci, bai san sanda murmushin farinciki irin wanda ya manta yadda ake yi ya kwanta a saman kyakkyawar fuskarsa ba. Kana ganinsa ka san yana cikin farinciki. Mutumin farko da ya miƙo masa hannu su gaisa ya cewa "Bacci nayi na awa takwas, awa takwas ko motsi ban yi ba." Murna mutumin ya taya shi duk da mamakin da ya bashi. Sai da aka idar da sallah Abu Usama ya ce su zo su tafi gida kafin la'asar. Ƙiri-ƙiri ya ce ba zai tafi ba ai ba gidansu ɗaya ba. Sai da ya yi dariya yace masa saboda suyi wanka ne, yau ya janyo masa bai yi wanka ba har azahar. Haka nan ya bi bayansa yana ɓata rai. A masallacin Abu Usama ya same shi kafin la'asar don ya riga shi zuwa. Magrib a nan ta riske shi. Ana buɗa baki lokacin ƙamshin girke girken restaurant ya cika harabar wurin da kewaye. Maza da mata haka aka yi ta tururuwar shiga. Ruksana matar Abu Usama ita ce ke shugabantar komai. Ita da matar ƙaninsa da wasu maaikatan ke girki, samarin ƴaƴansu da masu tayasu aiki su rarraba zuwa kowane tebur. Musulman kusa da na kewayensu haɗa kudi suke yi domin ciyar da junansu da azumi. Wadataccen abinci Ruksana ta zubawa Arƙam ta ajiye masa a gabansa tana murmushi. "Yau abincin daban aka yi saboda kai. Ina fata zai yi maka daɗi." Ba ƙaramin daɗin karramar da aka yi masa ya yi ba "Nagode, amma ya akayi ki ka san zan zo?" "Duk masu zuwa masallacin nan ƴan uwan juna ne a musulunci. Muna maka barka da zuwa Brother Arƙam" cewar wani dattijo da ya fi kowa tsufa a wurin. Idanunsa ne suka ciko da ƙwalla da irin kulawar da mutanen suka bashi. Daga ranar ya mayar da masallacin nan gidansa na biyu. Kamar haɗin baki da shugaban sa a wurin aiki bai neme shi ba har sallah ta gabato. Tsakaninsa da Abu Usama kuwa tun yana sharewa har sabo mai ƙarfi ya kƙƙullu ta yadda kullum suna tare. Duk tsahon lokacin nan bai taɓa tambayarsa labarin komai a kansa ba har aka yi sallah. Ibada musamman nafila da karatu su ya dinga nusar dashi da dabara ta hanyar cewa suyi tare. Sun idar da sallar idi yanayin wurin na haɗuwar musulmai ya ƙayatar da shi matuƙa. Hawaye ya goge a fakaice wanda Abu Usama ya gani. Daren ranar fa kansa ya je gidansa ya bashi labarin irin rayuwar da ya yi a ƙasar da banzatar da rayuwarsa da mahaifiyarsa ta yi. Abu Usama shawara ɗaya ya bashi "Ka yi ƙoƙarin daidaita tsakaninka da Mahaliccinka Shi kuma zai daidaita maka duk wani abin da ya shige maka duhu game da ƴan uwanka"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull