Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 7
Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 7: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 7. [2/23, 7:34 PM] Nasma: *** Anyi sallah da sati ɗaya Tauhidat da Papa suka…
3,778 words
[2/23, 7:34 PM] Nasma: *** Anyi sallah da sati ɗaya Tauhidat da Papa suka dawo daga Abeokuta. Lokacin saura kwanaki shabiyu tafiyarsu Turkey, duk wani shiri da ya kamata sun gama yi sai jiran rana. Washegarin dawowarsu Baffa Alƙali ya sauka a garin Kano batare da sanin kowa ba cikin ƴayansa. Motar da aka turo ɗaukarsa kai tsaye Kano Tropicana Hotel ta wuce dashi. Direban motar ya faɗa masa lambar ɗakin da zai je. Da sassarfa ya shiga aka karɓi jakarsa. Bayan ya faɗi sunansa a ƙagauce ya ce akwai mai jiransa a ɗakin da ya basu lambar. A reception ɗin an riga an sanar da zuwansa su ma basu ɓata masa lokaci ba aka yi masa jagora. Girma da shekaru basu rage masa kuzari ba. Da zafinsa yake tafiya har ya isa bakin ƙofar ɗakin. Yana murɗawa cikin Tony PA ya karta saboda tsabar tsoro. Baffa na shiga kuwa ya yi kansa gadan-gadan ya zaro kwalin DVD ya cilla masa a fuska. Muryarsa har korido ɗin waje ana ji lokacin da ya ce, "Tony nawa na baka akan Arƙam? Nawa na kashe iya ni da kai da kuma a gaban Haji Lawalli akan yaron nan? Amma shi ne ka kasa cewa komai sai da al'amura suka ɓaci gabaɗaya ka turo min wannan abin. Arƙam ya zama mawaƙi ya gama zaga duniya." Zuciyarsa tamkar ta buga haka yake ji. Haji Lawalli da ke zaune a kan kujera ya dafe kai ya taso ya riƙo hannunsa "Baffa kayi haƙuri, yanzu abinda ya kamata mu sani shi ne ko Haj. Manga ko Jamal sun taɓa gani." "Manga bata sani ba domin ko da wasa idan ta sani ba za ta ɓoye min ba." "To yanzu me ya kamata muyi?" Cewar Haji Lawalli. "Idan kana da visa to a shirye nake mu bar ƙasar nan jibi don na riga na sayi ticket ma." Baffa ya ce tare da hararar Tony wanda bakinsa ya yi nauyi saboda firgici. "Saura bai fi wata biyu ta yi elapsing ba. Ina fita daga nan zan fara processing ticket ɗin ko ba rana ɗaya da kai bane dole nima na je." Yadda Tony ya tsorata yasa Haji Lawalli ƙarawa da cewa ya kwana da shirin sai sun ɗaure shi. Baffa kuwa ji yake kamar ya tashi ya shaƙo wuyansa don baƙinciki. "Wane irin rashin imani da rashin tausayi gareka da ubangidanka? Ashe hawayen da ƴa ta take zubarwa bai isa ya sa ku tausaya mata ba? Musamman ma kai Tony. Na daɗe da tunanin lallai Alh. Audi ne ya ɗauke min jika. A matsayinka na PA ɗinsa ba irin kyautar da bana yi maka da roƙo guda ɗya tak, idan ka ji labarin Arƙam ko nawa ka ke so zan baka ka sanar dani." Haji Lawalli fuskarsa ta yi rauni matuƙa ya ce "kayi haƙuri Baffa, ko babu komai mun san inda zamu same shi yanzu." "Bayan ya zama mawaƙi? Mawaƙin ma a ƙasa kamar America. Lawalli ɗan Ibrahim ne fa da kitso a kansa. Ya ya Manga za ta ji?" Baffa ya ce muryarsa na rawa ga ƙwalla ta ciko a idanunsa. Tony dai nasa ido ne. Bayan ya ji shiru Arƙam bai zo ba hankalinsa ya ɗan kwanta. Sai kwatsam satin da ya gabata yaci karo da album ɗinsa a DVD ana saidawa a junction. Ba don ya san shi da kitso ba da ba zai gane shi ba. Mafita ɗaya gare shi wato neman Baffa tunda ya daɗe yana bibiyarsa akan jikan nasa. Ko ba komai zai roki alfarmar su yi masa hanya shi da matarsa su bar ƙasar kafin asirinsa ya gama tonuwa. Abu ɗaya yake son warware musu saboda tarar Alh. Audi da rigima sai mutum ya yi shirin gaske. "Ranka ya daɗe wallahi Alh. Audi bashi da masaniya akan inda Arƙam yake. Shi ma nemansa yake yi." Baffa ya ji kansa ya kulle "to wa kake yi wa aiki?" "Ba zan iya faɗa ba domin makusanci ne ga Alh. Audi and he is very dangerous." Da sauri Haji Lawalli ya ce "Alh. Ari? Lallai amma mutumin nan baƙin munafiki ne." "Bani da tabbacin ko shi ne. Ni kaina ko wuƙa za a saka min bana ce gashi ba. Amma na tabbatar yana tare da Alhaji." Ɗaukar maganar tasa suka yi a matsayin salon rainin wayo. Abinda ke gabansu yafi ƙarfin lallaɓa Tony ya haɗasu da ɓoyayyen ubangidansa. Cheque Baffa Alƙali ya damƙa masa sannan suka fita shi da Haji Lawalli zuwa Central Hotel inda zaiyi masauki kafin shi kuma ya sayi ticket. Bayan tafiyar Haji Lawalli da daddare ya dlɗauko wata jaka da yazo da ita ya baje takardun cikinta akan gadonsa. Duk wani abu da ya kamata ayi na cike-cike akan su anyi an gama saura sa hannunsa ya rage. Takardu ne na dukiyar gadon amanarsa Hafsatu Manga. Bayan rasuwar ƙaninsa da matarsa shi ya ajiye mata gadonta daga baya ya saya mata hannun jari dasu. Tsautsayi ya sa kamfanin ya kusa durƙushewa mutane suka ɗibga asara. Da yawa tun a lokacin an biya su kuɗaɗɗnsu. Baffa Alƙali kuwa duk da mutum ne mai zafin zuciya yana da kawaici. Shugaban kamfanin amininsa ne. Nauyin neman a biyasu ya ji ya kasa cewa komai. Bai ɓoyewa ƴar tasa ba da mijinta Ibrahim a lokacin. Alfarma ya nema da su ƙarawa mutumin lokaci tunda ya ce yana jiran kammaluwar wani contract domin tabbatar da asara ta hau su da gaske ko akwai kofar farfaɗowa. Allah Rahimi kamfanin ya farfaɗo da ƙarfinsa bayan shekaru sai ga dukiya ta haɓɓaka na ban mamaki. A lokacin da ya ke shirin mallaka mata komai ne Alh. Audi ya shammacesu ya kwace plaza ɗin da ta gina. Ya san irin yadda ta shiga tashin hankali ga rashin nutsuwa saboda Arƙam. Wannan ya sa ya dakatar da bata kuɗin tukunna saboda gudun kada Alh. Audi ya sami kmƙofar wawashe mata dukiya a yanayin da take ciki. Yanzu kuwa da ya ke da yaƙinin gano jikansa ya tabbatar zai iya bata kuɗinta ta juya yadda ya kamata. Ya duƙufa yana ta rubuce-rubuce wani tunani da shi ko wani nasa a iya saninsa basu taɓa yi ba ya ɗarsu a zuciyarsa. Ina dukiyar Manga, Arƙam da Jamal ta gadon da Ibrahim ya rasu ya bar musu? Yaushe dukiya da gumin Ibrahim Iro Karam ta koma ta Audi Iro Karam? Zumbur Baffa ya tashi daga kan gadon ya ɗauko wayarsa da ke caji hankali a tashe. A shekaru goma sha ɗaya da watanni da rasuwar uban ƴaƴan Manga amma ba a raba gado ba. Yana ina haka ta faru? Ko shi ya sa suka damu da ƙwace kamfanin daga hannunsa batare da sanin ƙwaƙƙwaran dalilinsu ba? Sun dai san kawai kamar haƙƙinsu ne. Tunowa ya yi da kaɗan cikin maganganunsu da Alh. Audi ranar da aka taru da sunan rabon gadon ya dafe kansa. Akwai wata a ƙasa! Lambar babban ɗansa Ali ya kira amma abin mamaki sai ya nemi dalilin kiran ya rasa. Tamkar wanda aka shafewa kai ko kaɗan ya kasa tuna me yasa ya kira. Karshe sai gaisawa suka yi ya tambayi lafiyar iyalinsa ya aje wayar. Da mummunan ciwon kai ya kwana a daren. Washegari da yamma Haji Lawalli ya sayi ticket suka shirya komai na tafiya. Ba za su sanar da Haj. Manga ba sai sun ga ga su ga Arƙam ba wai wai ba. A ranar da suka tashi zuwa USA daga Lagos a ranar ne kuma Oga wato shugaban su Alh. Audi ya tashi daga bacci a firgice. Mafarkin wata guguwa ya yi wadda ta nufo Alh. Audi da ƙarfinta. Karfin wannan guguwar har ya fi irin wadda ya gani game da Arƙam da Tauhidat. Tashi ya yi a hankali ya sauka daga kan gadonsa. Wata durowa ya buɗe ya ɗauko wani ƙyalle wanda yake ɗauke da jinin Alh. Audi da ya yi masa aiki a kai shekarun baya. Bayan ya gama aikinsa akan idon Alh. Audi jinin ya rabe kashi uku. Oga ya fassara masa wannan rabuwar a matsayin mutane uku da zasu iya zama barazana gare shi. A haɗuwar farko lokacin ta'aziyya ya gane Arƙam. Guguwar Tauhidat ita ta sanar da zuwanta. To waye ko wace na ukun? *** Ranar talata su Baffa suka bar Nigeria suka sauka a Baltimore/Washington International Airport. Ba don dare ba a ranar za su wuce Johns Hopkins Medical School inda Tony ya faɗa musu Arƙam na karatu. Baffa bai iya runtsawa ba sai addu'ar da ya kwana yana yi domin komai ya zo musu cikin sauƙi. Gari na wayewa kuwa ko karyawa basu iya yi ba suka tafi makarantar. Ɗalibin farko da suka tambaya abin mamaki garesu ya san Arƙam. Da initials ɗinsa ya kira shi wato AIK. Yanayin tsayinsa da na Baffa duk da tsufa ya kama shi ya sa shi gaskata maganarsa ta cewa shi kakansa ne. Sun kawo masa ziyara amma sun kasa samunsa a waya shi ne suka zo makarantarsu. Cafeteria ya kaisu wurin Raymond ya ce babu inda zasu sami cikakken bayani akansa sama da nan. Addu'a takobin mumini, duk tsirfa irin ta bature amma Raymond bai iya yiwa su Baffa tambayar kwakwa akan Arqam ba ya basu nambar wayarsa, adireshin gidansa da sunan asibitin da yake residency. Ya sha godiya kamar su ari baki. Bayan fitarsu ya kira Arƙam don ya faɗa masa kakansa ya zo amma bai ɗauka ba. Josh ya nema ya sanar da shi cewa daren jiya ya yi call bai daɗe da tafiya gida ba. Indai bai amsa waya ba ta yiwu bacci yake yi. Kafin a barsu su shiga security ya tambayesu wurin wa suka zo da nambar apartment ɗin. Sun bashi suna sa komai amma duk da haka sai da ya kira gidan Arƙam da layin da ake kiran mazauna condo ɗin. Cikin bacci ya ji waya da ƙyar ya iya buɗe idanunsa. Yanzu kam Alhamdulillah ba kamar da ba yana samun bacci. Kara wayar ya yi a kunne aka sanar da shi yana da baƙi. A tunaninsa su Abu Usama ne har yana jin haushin me ye kuma na tsare shi bayan shi ma a daya block dɗn yake. "Na san da zuwansu ku barsu su hawo." Ya ce ya ɗauki pillow ya danne kansa yana ihun an hana shi bacci. Yau sai ya yi wa Abu Usama bore ko ya saka shi zaman gadinsa a masallaci ya runtsu ko na awa ɗaya ne. Haji Lawalli da Baffa sai baki ya mutu a lokacin da lift ya buɗe a hawa na sha bakwai. Jikinsu sai ya soma sanyi da fargabar rashin sanin irin tarbar da zasu samu. Kada ya watsa musu kasa a ido ya nuna bai san su ba. Hannun Baffa dai tuni gumi ya jiƙe shi a haka ya soma ƙwanƙwasa kofar tare da sallama. Wata doorbell nan da ya gani bai ma yi tunanin dannata ba. Allah Ya so kan Arƙam babu kitso sai uban tulin gashi da kasumba da ta sha gyara. Tarawa yake saboda ɓoye kansa daga mutane masu hana shi nutsuwa ya yi aikinsa a asibiti. Daga shi sai wando 3-quarter baƙi da farar vest ya zo ya buƙe ƙofar. Da farko juyawa yaso yi tunda gidan ba baƙon Abu Usama bane sai kuma ya juyo da sauri yana kallon mutanen da suke tsaye a bakin ƙofar gidansa. Wani irin kallon tausayi, kewa da dumbin soyayya suke yi masa. Tsohon kuwa ƙwalla ta cika masa idanu har ta fara gangarowa kan kumatunsa. Shi Arƙam yafi kallo gabansa yana faɗuwa sosai. Ya gane su sai dai yana gudun ko mafarki yake yi. Jiki a mace ya dafa bango da hannunsa ɗaya tare da runtse idanu shi ma yana hawaye. Cikin yaren hausa da ya kwashi shekaru rabonsa da wani ya yi masa magana dashi Baffa ya yi masa magana muryarsa na rawa. "Jikana Arƙam Ibrahim Karam muke nema." "Baffa..." Arƙam ya ce kamar me raɗa kafin ya ankara Baffa ya janyo shi jikinsa sun rungume juna. Sun ɗauki kusan minti uku kafin ya iya sakin Baffa ya koma kan Haji Lawalli. "Baba Lawalli ashe baku manta dani ba?" Koke-kokensu suka sha a bakin ƙofa sannan suka shiga ciki. Arƙam gani yake kamar mafarki ne ba gaske ba. Suna zama ya ce "Baffa ina Nanna? Me na yi bata son ganina kuma?" Abinka da rashin samun wanda zai yi magana da yarensa da shi, gabaɗaya bakinsa ya juye. Hausar ta sa a turance take fita kuma a birkice. "Nannanka tana nan lafiya. Bayanin namu da tsaho ba maganar da zamu yi a tsaye ba ce." Haji Lawalli ya bashi amsa. "Na zauna. I am listening (ina sauraronka)" ya faɗa lokacin da ya zauna a kusa da Baffa da ya kasa cewa komai sai kallonsa kawai. Murmushi Baffa ya yi, "har yanzu baka girma ba, ji yadda kake hawaye kamar wani yaro." Goge hawayen ya yi da saurinsa "Am sorry, now please tell me about Nanna and Jamal." Bai barsu sun yi motsin kirki ba sai da suka faɗa masa abinda suka sani game da ɓatansa. Mamaki sosai ya kamashi shi ma ya faɗa musu yadda Tony ya rabo shi da waccan makarantar da wayoyinsu hadda zancen Madam Zainaba. Kansu kullewa ya yi saboda abin ya ƙara rikice musu. Baffa ne ya ce su kwantar da hankulansu da sannu zasu binciko komai har ƙarshe. Arƙam na jin haka ya ce bari ya shirya ya kaisu su ci abinci sai ya duba ko akwai jirgi su yi booking zuwa Nigeria a yau. Haji Lawalli ya ce masa "Yi hakuri Yallaɓai, kai da zuwa gida sai mun gane waye yake harinka kuma me ya sa." Kallon wasa ku ke yi ya musu kafin ya ce, "Nanna kuma sai na haƙura da ita?" "Nanna za ta zo gareka" cewar Baffa. A lokacin ya buƙaci su bashi nambarta ya kira. Baffa ya soma ja masa rai yana cewa shi fa yunwa yake ji. Kamar yasa ihu ya ɗauki waya ya kira Abu Usama. Order ya yi musu na special abincin wurinsu sannan ya ce duk wanda yake cikin restaurant din a lokacin a maida masa kuɗinsa a haɗa masa bill. Da aka kawo abincin ya biya yaron da ya kawo ya jera musu komai akan dinning table suka zauna. Hannu ya miƙa musu "please ku bani phone number ɗinta." "Sai ka zauna mun ci abincin tare" Baffa ya kuma tsokanarsa. Haji Lawalli yana dariyar yadda ya ɓata fuska ya miƙa masa tasa wayar bayan ya danno sunanta. Yana faɗa masa cewa bashi da sim din kasar a ciki Arqam bai saurare shi ba ya shige ɗakinsa zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri. *** Tazarar awa bakwai ne tsakanin America da Nigeria. Ƙarfe shabiyu saura na rana a wurinsu Arƙam ya yi daidai da bakwai saura a Nigeria. Haj. Manga da Tauhidat basu daɗe da shigowa gida ba. Siyayyar kaya ta yi mata na tafiyarsu Turkey akwati guda. Tauhidat ta riga idar da sallar Magariba tana azkar wayar Nanna ta fara ringing. Ita kuma lokacin raka'ar farko ma take. An kira sau biyu a jere a na ukun sai ta ɗauka domin ta bawa mai kiran hakuri. Baƙuwar namba ta gani ta kasar waje kamar kada ta dauka sai wani kiran ya sake shigowa ta kara wayar a kunnenta. Alamun numfashi kawai Arƙam ya ji cikin wata irin murya da ta yi sanadiyar tayar da tsigar jikin Tauhidat ya ce, "Nanna, ni ne?" A hankali Tauhidat ta ce, "Nanna tana sallah. Ka kashe idan ta idar sai ta kira ka. Wa zan ce mata?" Yadda muryarsa ta janyo gudun jinin jikinta ya ƙaru haka shi ma ya sami kansa da shiga wani yanayi na takaitaccen lokaci a dalilin jin ƙaramar muryarta. "Wa zan ce?" Ta sake tambaya da dan ƙarfi jin ya yi shiru. Tsoron kada a sake maimaita masa irin yadda matar da ke kiran kanta Madam Zainaba ya sa shi cewa, "No. Wait. Please don't disconnect the call (A'a, tsaya, don Allah kada ki katse kiran)!" [2/23, 7:34 PM] Nasma: Ya faɗa da sauri. Yadda ya yi magnar tsoro ya bata, a ɗarare ta sake cewa, "za ta kira idan ta idar." "Kiyi min hira kafin ta idar kinji. Ya sunanki?" Ya sami kansa da cewa da taushin murya. Haka kawai ba zai kuma yarda da irin excuses ɗin da aka dinga bashi ba a shekarun baya ba. Idan zasu kwana akan waya a shirye yake har sai Nanna ta idar ta karɓa. Tauhidat gabaɗaya sai ta rasa abin cewa. Kallon Nanna ta yi ta ga a raka'ar ƙarshe take sai ta murmusa. Ko waye wannan ita dai bata son tsawaita magana dashi saboda yadda ta tsinci kanta a wani baƙon yanayi. Kuma ma bata san sunansa ba shi zai nemi sanin nata? "Kai ya ya sunanka?" "Arƙam" ya bata amsa a takaice. Bata san lokacin da ta sake ƙanƙame wayar ba hankalinta a tashe tana kallon Nanna da ke zaman tahiyya ta sake tambayarsa sunansa domin tabbatarwa. Muryarta har rawa take yi alamun ta soma kuka. "Me ka ce? Sake faɗa don Allah" Yanayin tambayar ya tabbatar masa da ta ji abinda ya ce da farko. "Do you know me (kin sanni ne)? Nanna tana yin maganata dake?" Fashewa kawai ta yi da kuka "tana yi, kullum sai ta yi. Da gaske kai ne?" "Kuka ki ke yi? Kema kin damu dani ne?" Ya ce da mamakin ita wace da ta damu dashi haka. "Sosai!" Nanna ta sake kallo lokacin ta sallame sallar ita ma ta ƙura mata ido. Suna haɗa ido kuwa ta yi mata alama da ta kashe wayar. Ko waye bata ga dalilin da zai saka mata ƴa kuka ba. Maimakon ta kashe sai kawai ta saka wayar a speaker ta ƙure sautin sannan sannan ta rarrafa kusa da ita tana murmushi haɗe da hawaye. Kamar daga sama, tamkar saukar ƙanƙara a zuciyar da wuta take ruruwa a cikinta Haj. Manga ta ji muryar Arƙam ta doki kunnuwanta. Muryar da daɗewar shekaru da ƙaruwar sautinta ba zai sa ko a mafarki ta manta da ita ba tana cewa, "I miss her so much. Ki faɗawa Nanna ta yafe min ta yi magana dani. I have a lot to say." A hankali Tauhidat ta gyaɗa kai kamar yana kallonta yayin da wasu zafafan hawaye suka shiga kwarara daga idanun Haj. Manga. Runtse idanu kawai ta yi tana fatan idan mafarki ne Allah Ya tsawaita mata shi. Kukan da Haj. Manga take yi ba karamin tsayawa Tauhidat a rai ya yi ba. Ga muryar Arqam tana ji yana ta cewa "hello" cikin tashin hankalin rashin amsa masa da aka yi. Dora mata wayar tayi a tafin hannunta kamar mai bada umarni ta ce, "Ki yi masa magana." Kai ta gyada kawai ta sake fashewa da wani kukan a lokacin da Tauhidat ta tashi a guje ta fita daga dakin. Nata dakin ta shiga ta dauko wani envelop a cikin tsohon akwatin mahaifiyarta. Hotunansu ne da Aunty Bimbo da yawa ta rungume daya tare da fashewa da kuka mai tsuma rai. Haj. Manga kuwa kasa motsa bakinta tayi sai kukanta da ya tsananta. Jin muryar Arqam ya wanke mata damuwa sannan ya dawo mata da wata damuwar. Rayuwar da a da take ta ganin za ta dauwama a ciki ke mata gizo a kwakwalwa. Lokutan da take tare da Ibrahim da irin dumbin soyayyar da yake nuna musu ita da 'ya'yanta. Saboda irin abin nan na dan fari da take gwadawa Arqam yasa shi jansa a jiki sosai. Yadda Ibrahim dinta ke da sanyin hali haka dansa yake. Duk wannan tunanin tana yinsa ne yayin da hawaye ya jike mata fuska da hijabi. Shi kuma jin shiru yasa shi komawa falo zai roki su Baffa da su taimaka su bashi lambar da zai sameta sai ji ya yi cikin dasashshiyar murya ta ce, "Sai yau Arqam?" Duk girma da ji da kan namiji, karamin yaro yake a wurin mahaifiyarsa. Tsigar jikinsa gabadaya ta mimmike saboda yadda muryarta take kwarara tana bin sassan jikinsa. Jagwab haka ya zauna akan kujerar da tafi kusa dashi yana zubar da hawaye masu zafi. "Ba za ka yi min magana ba Yaron Abba?" Ta ce da wata irin murya mai cike da shaukin tuna baya. Rabon da yaji wannan suna tun ranar da mahaifinsa zai rasu yana bar masa wasiyar kulawa da Jamal da Nanna. "Nanna kinyi fushi ko? I am so sorry." Ji tayi inama za ta iya zura hannu ta finciko shi daga wayar ta rungume. Rarrashinsa take so ta yi "Banyi fushi ba, ka daina kukan haka." "I am sorry, anyi min karya da yawa but still I should have come home (duk da haka ya kamata ace na dawo gida)." Bata son jin wani dogon bayani yanzu. Lafiyarsa ta damu ta sani tukunna. Suna kukan farinciki a gefe Baffa da Haji Lawalli na kallonsa. Haj. Manga ta shiga jero masa tambayoyi wata na bin wata ko amsa ba ta jira. "How are you? Kana cin abinci? Kana karatu ko ka gama? Kila ma kayi aure har matar ta haihu? Allah Yasa musulma ka kwaso dai. Ka kara tsayi kuwa? Lokacin da ka tafi ba ka da wani jiki... " Dariya ya yi ga hawaye "all these questions Nanna na dade ba a yi min su ba. Ina lafiya. Ba na cin abinci sosai. I am taller dan Baffa (na fi Baffa tsaho)." Baffa ya share kwallarsa yana murmushi ya dawo kusa dashi ya zauna. A razane Haj. Manga ta ce "auren fa? Kada kace min da gaske kayi kuma ba musulma bace." Bai san lokacin da dariya ta kufce masa ba "babu mata Nanna, ni kadai ne. And am a third year resident doctor." "Masha Allah" take ta cewa ta mike da sauri ta tafi dakin Tauhidat. Tambayarta yake yi ina Jamal ta ce yana makaranta amma ga kanwarsa da bai sani ba. Akan gado ta sameta tana risgar kuka amma ganinta yasa ta boye hoton saboda kada taji ba dadi. Bata rasa komai na soyayya da gata a wurin Haj. Manga ba. Shi ya sa bata cika son tayar mata da hankali ba. Gani take yi kamar za ta ga ta raina kulawar da take bata ne. Wayar ta dora mata a kunne bayan ta rungumeta suna kukansu. Cike da murna ta ce "kin ji Tauhida Dayan ne ya kirani. Ashe bai manta dani ba. Ashe ina ransa." Farincikin da take ji yayi mata yawan da ita kadai ba za ta iya rikonsa a zuci ba. Haka nan saboda doki ta manta ma Tauhidat din ce ta amsa wayar. "Arqam ga Tauhida." Muryar da tayi masa sallama dazu da ta dauki wayar ita ya sake ji ta daki dodon kunnensa. Daga sallamar sai ta rasa abin fada musamman saboda ganin yadda Nanna ta tsareta da idanu tana ta zuba murmushi.