Kenza eBookz

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 8

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 8

Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 8: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 8. Shi ya katse shirun ta hanyar cewa "thank you Tauhida. You have won my…

2,583 words

Shi ya katse shirun ta hanyar cewa "thank you Tauhida. You have won my heart (kin saye zuciyata) tun kafin mu hadu." Zaro idanu tayi a tsorace "Eyye?" Cigaba da magana ya yi abinsa don bai ganin ya fadi karya a maganarsa. "Kin bawa Nanna waya when I asked. Hakan ba karamin abu bane a wurina. Kuma ta ce ke sister dina ce. Can't wait to meet you." "Nima haka" ta ce a kunyace. To me za ta ce sama da hakan? Haj. Manga ta sake karbar wayar ta cigaba da yi masa tambayoyi. Nan ta zauna tayi kuka tayi dariya kamar yadda yake yi a nasa bangaren. Sun kwashi awa guda kafin hirar ta karkata zuwa bayanin cewa Baffa da Haji. Lawalli ne suka zo gidansa. Daga nan Baffan ya karba ya mata takaitaccen bayani da kwabarta akan kada kowa ya san sun ganshi a gidan. Da ta tambayeshi ko zasu taho gida tare ya ce a'a. Ya bata yau zuwa gobe ta san yadda zata yi ta nemi izinin mijinta ta taho batare da ya zargi komai ba. Ya yarje mata ta ce shi ne bashi da lafiya ya tafi check up bai sanar da kowa ba sai yanzu. Da kyar suka ajiye wayar ita da Arqam sannan ta kira Jamal da kyakkyawan albishir. Shi kuma Arqam tsare su Baffa ya yi da tambayar wa take aure yaji ance mijinta. Ai sai da ya yi dana sanin tambaya kuwa domin Baffa na cewa kawunsa ne Audi yaji kamar duniyar ce ta kife dashi. Bai taba kaunar Kawun nasa ba tun fil'azal jininsu bai hadu ba. Sai kuma wani abu da ya taba gani wanda ya tsaya masa a kokon rai. Tsautsayin da ya sami Abbansa a ranar ne ya mantar dashi abinda ya gani. Wane irin mutum ne zai daga hannu ya shake wuyan kanin mahaifiyarsa? Babu magana guda da suka yi da ya iya ji sai wannan shakar da ya hango da dan manuninsa da ya nuna shi dashi yana masa gargadi da kakkausan harshe. Girgiza kai ya yi bayan Baffa ya fada masa cewa dalilin nemansa ne ta aure shi. "Tunda an ganni sai ya saketa. Kuma guda ukun zaiyi mata." Ya ce a kufule. "Arqam ka bari a nutse idan ta iso za ka ji komai. Kai da ka ke farincikin haduwa da ita kada tunanin Audi ya dameka." A tsorace ya ce da Baffa "Allah Yasa dai ba ta son shi." "Bata son shi kaji. Bata taba son shi ba kuma ba za ta taba ba. Ka sa ranka a inuwa." Baffa ya amsa masa da murmushi. *** Alh. Audi ya gama jin bayanin Haj. Manga tsaf ya kwantar da murya kamar gaske.

"Yanzu shi Baffa sai ya tafi har America check up bai fadawa kowa ba?" Tabe baki tayi ta gyara kwanciyar Tauhidat da tayi pillow da cinyarta tana sharar bacci. "Kaima ka fada, ya kasa gane cewa ya tsufa dole ya nemi mataimaki. Yanzu gashi ya je ance sai an ajiye shi for observation. Yayun nawa kuma babu mai visa shi ya sa nake son tafiya." Kwalbar giyarsa ya daga ya ga babu saura a ciki ya mike zuwa fridge din dakin hotel din da ya yi masauki a kasar Japan ya dauko wata. Sai da ya kurba ta sauka a tulelen cikinsa sannan ya bata izinin tafiya harda alkawarin kara mata guzuri da shawarar ta tafi da Jamal. Dama ko bai fada ba ai dole ne zuwa dashi. In don karatunsa ne carry over yana da ita tafi cikin kwando. Zuwa ganin dan uwansa ba zai rage masa komai ba. Ajiye wayar tayi ta buga tsaki shi kuma yana jin ta kashe ya soma dariyar mugunta. "Shegen tsoho, Allah Yasa daga nan ka sheka kowa ya huta." *** Jirgin safe Jamal ya biyo daga Adamawa zuwa Abuja washegari. Haj. Manga ta hada shi da Tauhidat ta ja musu kunne akan ko da wasa kada su taba zancen ganin Arqam da akayi da kowa. Shi dai yana mamakin yadda take yiwa baban nasu boye-boye tunda har yau idan ka cire kwace plaza bai ga aibunsa ba. Tauhidat kuwa bata taba yi mata musu. Shi ya sa ma bata ji bacin rai ba da ta bata hakuri akan soke zuwansu Turkey. "Bazan yarda bane ki tafi ke kadai tare da Fanna ta bar miki raino. Da ace rainon ma da zuciya daya ne bazan damu ba. Amma ba kirki gareta ba. Sai ta kuntata miki kafin ku dawo." Jamal da ke sharce cukurkudadden gashinsa mara aski da gyara ya ce "to mu tafi da ita mana." Cike da damuwa ta ce "bata da visa, da na sani lokacin da muka je renewal kema na nema miki." Murmushi tayi ta ce "Nanna kada ki damu,tunda za ki da Tarantula ai sammakal." Dariya Jamal ya kwashe da ita ganin Haj. Manga ta zaro idanu tana harararsa. "Kanwata bani da ta biyunki. Ashe kina gane yaren."

Kunnuwansu ta kama tana ja "don kaniyarka bata min yarinya za ka yi? Ke kuma kiyi ta makale masa ke mai dan uwa. Na sake jin kuna min yaren 'yan kwaya sai na gwara kawunanku." Tana fada suna hada ido suna dariya. Tun tana masifa ta koma dariyar ita ma. Kwana biyu a tsakani suka kaisu airport. Ta sha kukanta kuwa saboda zaman kadaici da zata yi. Madam Zainaba tun jiya ta tafi garinsu za ta kwana biyu sai ana gobe zasu dawo ita ma ta dawo. A hanya Papa Abayomi yake fada mata cewa gobe ta hada kaya zai kaita Gombe suyi zumunci da tsofaffin makotansu. Ya riga ya baiwa Shaheed hakuri akan uzurin rashin lafiya da ya tasowa Baffa. Kuma Alh. Audi zai je daga Japan sannan Fanna da bata gajiya da yawo ita ma za ta je. Baccin da Tauhidat tayi a hanya ne ya bashi damar cigaba da tunanin yadda Alh. Audi ya mayar da Shaheed jikinsa sosai. Yana yawan kai masa ziyara gashi wai ya biya masa ya dora Masters kafin ya dawo gabadaya. Hutu kawai zai zo idan an fara karatu ya koma. A bangare guda Haj. Manga ta tsare kofar bar masa 'ya tayi maraicin mahaifiyarta. Zuciyarsa ta kan raunana da tunanin kada wani abu ya bullo nan gaba da zai sanya shi zama maci amana ga wadannan mutane. Yadda suka dauke shi da zuciya daya haka yake fatan su rabu cikin aminci. *** Daga uhm sai uhm-uhm Haj. Manga take iya yi a jirgi idan Jamal ya sako mata hira. Hankalinta kamar ba ya jikinta sai hasashen yadda za ta ga Arqam take yi. Gajiya ya yi da hirar ya kunna TV din gabansa yana kallo har bacci ya kwashe shi. Tun safe Arqam yasa housekeeper dinsa Mrs Brown ta gyara ko'ina na gidan. Dakuna biyu ne ya siyo sababbin bedsheets da kayan bukata na mata ta jerawa Haj. Manga a daki daya. Dakinsa kuma sai su kwana da Jamal tunda su Baffa suna hotel. Abu Usama da mutane da yawa na masallacinsu sun san mahaifiyarsa za ta zo yau. Sauran basu san me yake faruwa ba amma duk da haka suna taya shi murna saboda tsananin farincikin da ya kasa boyewa. Abinci kala biyar ya ce Ruksana ta dafa saboda bai san wanda zasu so ba. Abin mamaki ga shugabansu a asibiti da kansa ya nemi hutun sati guda. Babu bata lokaci aka bashi. Kowa yafi jindadin mu'amala da wannan Arqam din mai yawan fara'a da jan mutane da wasa. Jirgin nasu sai biyar na yamma zai sauka amma a airport din hudu ta riski Arqam. Awannin da zaman ko kadan basu dame shi ba. Shi kadai ya zo don su Baffa sun ce ba da su ba wannan zama. A gidansa ya baro su ya taho a hadaddiyar motarsa kirar chrysler convertible ruwan toka. Wurin parking ya nema a hawa na biyar ya ajiye motar. Sai da ya dan jira mutanen da suke wurin da za a iya ganinsa sun ajiye ko kwashe ababen hawansu ya fito. Sanye yake da bakin jeans da bakar turtle-neck top wadda ta kama shi, ya yi zanzaro da ita. Ya dora sky blue din blazer. Kansa a saisaye ya rage gashin fuskarsa. Ba karamin kyau ya yi ba musamman da ya dora gilashin ido kalar blazer din wato sky blue ya rufe idanuwansa. Kallo daya ya ishi duk wanda ya san kungiyar 3ripleA ya gane mawakin cikinsu Arqam. Wata magazine ya samu ya kare fuskarsa lokacin da ya shiga lift. Ya zo fita a inda zai jira isowarsu wata ta bangaje shi da gangan. Magazine din ta fadi ya bita da sauri, kafin ya dauko yaji an rungume shi. Ihu matan wurin suka saka manya da yara. Concerts din da yake zuwa mata na suma yau gasu ga shi. Wurin nan da nan ya cika da dandazon mutane masoyansa ana ta kiran sunansa da daukar hotuna. Duk wanda ya amsawa musabaha kuwa ya mika nasa hannun sai ya yi da gaske suke saki. Security ne suka bambare mutane daga jikinsa ya samu ya sulale. Wani office aka kai shi na VIP ya zauna. A nan din ma bai tsira da signing autograph ba. Kamar wanda yake kan kaya biyar na yi ya tashi ya ce wadanda yake jira sun sauka. Ba a barshi ya fita shi kadai sai da aka hada shi da security biyu hagu da damansa. Saboda matsayinsa a garesu da son takaita hayaniyar da kasancewarsa a wurin ta kawo aka kai shi daidai wurin fitowarsu. Yana kallo security din ya radawa wani maaikacin kamfanin jirgin da suka biyo wata magana. Bai san me suka ce ba sai ga mutumin ya zo gabansa yana murmushi ya tambayeshi sunayen wadanda yake jira. Ya fada da minti goma aka bude jirgin dake jone da jikin ginin airport din ta yadda mai fitowa ko shiga ba zai ga jikin jirgin ba. Haj. Manga da Jamal na zaune suka ji sanarwar ana kiransu su. Ai sai suka tsure gabadaya har tana yiwa Jamal fadan ko ya hado da kwayoyinsa a cikin kaya. Gani suka yi a mutumce an zo an karbi kayansu su suka fara fita daga jirgin. Arqam yana tsaye ya zura hannuwa a aljihu a daidai inda zasu ganshi idan sun gangaro. Zazzafar kwalla ce ta cika musu idanu duka su ukun a lokacin da idanuwansu suka hadu da juna tun kafin su iso inda yake. Mahaifiyarsa sanye da navy blue din laffaya mai rangwamen ado ya fara kallo sannan ya kalli rabin jikinsa Jamaluddeen. Kasa tsayuwa yayi kamar yadda Jamal din shi ma ya debo a guje tare da riko hannun Nanna don ta kara sauri. A tsakiyar wurin suka hadu kwallar idanuwansu duka ta fara wanke musu fuskoki. A tsorace Arqam ya mika hannuwansa garesu. Jamal ya rike daya Haj. Manga ta rike daya. Wata irin ajiyar zuciya ya saki domin ya tabbatar da gaske ba mafarki yake yi ba. Duka su biyun ya keresu a tsayi. Haka ya rungumesu da iyakar karfinsa su ma suka kankame shi kamar za a rabasu. Kuka suke yi sosai babu mai bawa dan uwansa hakuri. Kafadarsa aka taba ya juya wurin daya daga cikin securities din. Inkiya aka yi masa da cewa su bar wurin saboda an fara fitowa. Tsayar dasu ya yi ya dauko trolley ya dora kayansu. Wanda aka yi checking-in Jamal ya tafi daukowa ya barsu su biyu a wurin. Haj. Manga da take jin kanta kamar a gajimare ta daga hannuwa ta rike fuskar Arqam a tafin hannunta. Cire hannuwan ya yi ya sumbaci tsakiyarsu sannan ya dago da sababbin kwallarsa "Nanna ki kira sunana please." Hawaye ya goge mata da yatsansa tana masa murmushi ta ce "Arqam yaron Abba." Sake rungumeta ya yi yana jin jikinsa gabadaya tamkar ana warware masa wasu igiyoyi da suka yi masa dabaibayi. A haka Jamal ya samesu suka kama hanyar wurin parking din karkashin jagorancinsa. Mutane ne jingim a wurin suna jiran fitowarsa. Haj Manga da Jamal sai mamakin yadda ake ihu a kansa da yadda securities suka wahala kafin su sama musu hanya suka shiga ya tayar. "Yayana celebrity ne ga dukkan alamu. Ka shiga hollywood ne?" Cewar Jamal abin yana kara burge shi. "Nope" ya ce da murmushi. Haj. Manga ta girgiza kai na rashin yarda "Anya Arqam? Ji fa yadda wata ta kusa shidewa da ihun ganinka." "Haduwa ce kawai suka gani tsagwaronta ko Bros?" Jamal ya ce yana leko da kansa gaba tsakaninsu. "ActualIy I used to be a singer amma yanzu na dena." Idanun Haj. Manga kamar su fito "Waka Arqam? Wace iri? Irin wadda 'yan mata ke yanyameku kamar kyankyasai?" Dariya suka yi shi da Jamal ya roketa da ta bari su isa gida. Tafiyar minti arba'in da biyar ta kaisu gidan nasa. Abu Usama da matarsa da dansu suna gidan ta jera komai akan dinning table ana jiran isowarsu. Tarba mai kyau ta yiwa Haj. Manga kamar sun dade da sanin juna. Irin gaisuwarsu ta rungume mutum a sumbaci kumatu hagu da dama tayi mata. Kayansu Arqam ya kai daki tunda duka yunwa suke ji suka zazzauna kewaye da table din. Arqam ya sake gabatar da Abu Usama, Usama da Ruksana ga iyayensa. Da turanci suke maganar yadda kowa zai fahimta. "Abu Usama ya taimaka min sosai a lokacin da rayuwata take cikin mawuyacin hali. Na daukesu tamkar jinina saboda sun cetoni daga mummunar rayuwa." Baffa ya gyara zama ya kalli kowa a wurin da murmushi "Duk wanda ya taba taimaka maka ko na rana daya ne Arqam ya cancanci mutumtawa da karramawa daga garemu. Ni da 'ya'yana da jikokina muna farincikin samunku cikin ahalinmu." Abu Usama hannu ya sake mika musu suka gaisa. Ruksana kuwa hawayen dadi take yi saboda yadda fuskar Arqam ta cika da annurin kasancewa wuri guda da iyalinsa. Suna gama cin abinci Haj. Manga ta ce za ta yi wanka. Arqam ya kaita dakin da ya tanadar mata ya sami wuri ya zauna. "To fita mana in shiga wankan ko." "Zan jira ki Nanna. Ban gaji da kallonki ba." Ya kashingide akan gadon. "Yi hakuri nima ba gajiya nayi ba. Ina shiryawa zan fito." Tana fama dashi sai ga Jamal. Da zuwansa tsalle ya daka ya fada kan gadon. "Don Allah ku fita jikina har kaikayi yake min." Babu wanda ya motsa. Idanu suka zuba mata tana ta fada suna dariya. Gani tayi abin nasu harda zolaya ta dauki tawul ta bude kofar bandakin za ta shiga Arqam ya ce, "Nanna ina Tauhida? I was hoping to meet her." "Zo muje na nuna maka hotonta." Cewar Jamal yana jan hannun yayansa. "Hamdan, katheeran, dayyiban, mubarakan fihi. Allah Ka cancanci kadaita da bauta Ya Zhuljalali wal Ikhram" Haj. Manga ta fadi ta kai sujjada ga Sarkin Sarakuna tana mika godiyarta da ya nuna mata wannan rana. Laptop Jamal ya dauko daga jakarsa ya kunna ya bude wata folder da ya sakawa sunan Tauhidat saboda hotunanta ne a ciki. Wanka ya shige bayan ya tura laptop din gaban Arqam. Zama ya yi ya tankwashe kafarsa daya akan gadon dayar kuma tana kasa ya bude hoton farko. Tana tsaye a jikin mota ita da Papa Abayomi zai kaita makaranta aka dauka. Murmushin nan da baya rabo da fuskarta take yi wanda ya bayyana siririyar wushiryarta. Kasa yin gaba ya yi yana ta kallon kyakkyawar fuskarta. Hoto na gaba da ya danna sai da zuciyarsa ta tsaya cak na wucin gadi. Tsigar jikinsa ce ta tashi lokaci guda. A tsaye take a bayan Nanna ita kuma tana zaune. Tauhidat ta zuro hannuwanta ta wuyanta ta dan kwanto tana dariya.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull