Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 9
Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 9: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 9. "Breath taking..." ya ce kamar wanda ya kai tsere saboda irin bugun…
1,739 words
"Breath taking..." ya ce kamar wanda ya kai tsere saboda irin bugun zuciyarsa. Ba wai kyau tafi kowa ba amma ya rasa me ya taba shi tun ranar da yaji muryarta. Washegari da ya kira Haj. Manga sai da ya nemeta suka gaisa. Yau kuma daga ganin hoto tana neman kurdawa inda bai sani ba a cikin jinin jikinsa. Gaba ya yi da sauri amma bai tsira ba. Duka hotunan fuskarta a sake kamar gonar auduga. A wurin Jamal ya fito ya same shi. Bai san muryarsa ta shake ba can kasa ya tambaye shi meya sa basu zo tare ba. Kafin ya bada amsa Haj. Manga ta kwankwasa musu kofar ta shigo. Ko zama bata yi ba ta hango hoton da yake kallo. "Ka ga Tauhidan Nanna ko Arqam? Yarinyar nan ta rage min kewarka fiye da zato." Jamal ya ce "To dai kada kiyi mana kuka." Ya juya yana kallon Arqam "in fada maka ko kai da ake ta nemanka baka kai Tauhida matsayi ba fa. Ita ce number one a zuciyar Nanna." "Na bar mata indai ba kai tafi so ba." Cewar Arqam yana murmushi. Zama tayi ta fada masa yadda ta hadu da Tauhidat ta kare da cewa "a matsayin 'ya na dauketa kuma Jamal yana mutunta min ita kamar jininsa. Don Allah kaima kada kayi mata wani abu na kaskanci saboda tana 'yar direba. Na dade da son ya bar aikin amma yaki. Ni kuma ina tsoron matsa masa ya ce da ita zai tafi." "Jamal da gaske ta fi sonta. After all these years baki tambayeni komai ba sai hirar Tauhida" Arqam ya ce yana sake kallon hotonta. Dariya suka yi sannan aka koma falo inda aka baje kolin hirar yaushe gamo. Abu Usama da iyalinsa sun tafi. Haji Lawalli ma sai ya fake da gajiya ya gudu hotel dinsu ya bar iyalin su kebe. Arqam bai boye musu komai ba na rayuwarsa tun ranar da ya baro England. Haj. Manga tun tana kuka sai ta koma gyada kai kawai. Babu abinda yafi bata tausayi kamar irin rayuwar da ya yi ta kunci kamar mara gata. Batun waka kuma tunda ya ce ya dena taji dadi sosai. Sana'a irin wannan a kasar da addini ba shi da mahimmanci sai wanda Allah Ya tseratar. Rayuwa ce bahaguwa mara alkibla akeyi. Babban abinda ya tayar mata da hankali kuwa bai wuce sunan Madam Zainaba da ya ambata a matsayin mai daukar wayarsa ba. Rike baki tayi cike da matukar mamaki tana kuka "Baffa ka ji abinda yake cewa? Zainaba fa..." kasa karasawa tayi saboda ranta ya kai kololuwar baci da wannan cin amana. Lallai Alh. Audi ya nuna mata har yanzu bata kama kafar yakarsa ba. Shekara da shekaru tana tafin hannunsa a dalilin Madam Zainaba bata sani ba. Wannan abu ya yi mata mugun ciwon da ya sanyata tafiya daki ba shiri ta banko kofar. Allah Sarki rashin sani... Jiki a sanyaye su ma suka shiga daki. Dare ya yi sosai saboda haka Arqam sai ya barwa Jamal da Baffa dakinsa shi kuma ya dawo falo. Da suka damu da ya dawo dakin ko a kasa Jamal sai ya yi shimfida sai ya ce shi karamin sauti ke tada shi bacci. Bai dade da kwanciya ba akan doguwar kujera Haj. Manga ta fito ta ganshi. Ta riga ta yanke hukuncin yadda zata yi da Madam Zainaba shi ya sa ta saki ranta. Akanta ba za ta kuntatawa zuciyarta a lokacin farincikinta ba. "Kana nan da rashin son kwana da mutane ko?" Dago kansa ya yi daga kan throw pillow din kujerar yana sosa keya "I don't feel comfortable (takura nake yi)." Zama ta yi a wata kujerar suka dasa hira. Idonta ya soye saboda bambancin lokaci. Ba su suka kwanta ba sai bayan sunyi sallar asuba. Daga ranar aka ajiye kuka da bakinciki suka sake suna jindadin kasancewa da juna. Kullum sai Arqam ya kaisu yawo. Aminansa Tomaz da Josh sun zo har gida gaishe da iyayensa. Jamal ya sha mamaki harda sakin baki da ya ga video din wata waka da yake yawan sauraro a gida ashe su suka yi. Nan fa ya makalewa su Josh. Barkwancinsa yasa suka saba cikin kankanin lokaci. Bayan sati daya Arqam ya koma aiki. Amma yana dawowa gida zai tare a wurin mahaifiyarsa. [2/23, 7:34 PM] Nasma: Yau kwanansu goma kuma suna shirin tafiya idan sun cika sati uku. Tafiyar tasu dole ce saboda wata shari'a da dole Baffa ne zai yi zaman karshe da mutanen ya yanke hukunci. Babu dalilin ace wanda tazo jinya ya koma gida ita tana nan sai zargi ya shigo tsakani. Arqam tun yanzu ya fara damunta kuwa akan yadda zai cigaba da rayuwa idan sun koma. "Nan da wata biyu in sha Allahu zan dawo. Ka kara hakuri har mu san abinda ya kamata muyi. Nima ina son kaje gida ko don Dada." Suna wannan hirar waya da shigo mata da sunan Haj. Lami. Murmushi ta doka saboda tun dazu take kira yau bata ji muryar Tauhidat ba. Kememe taki yarda idan sun je Gomben ta kwana a gidan abokin babanta makocinsu. Bata son 'yarta ta takura. Haj. Lami ma tana shan kashedi akan a kula da abincin da za a bata. Ita dai dariya take yi akan wannan uwa da 'yar. Sai da suka gama gaisawa Haj. Lami ta tambayi jikin Baffa sannan ta soma tsokanarta akan Tauhidat kafin ta bata. Arqam dake gefe yana ji ta soma hira da ita ya kwabe mata fuska tare da tara hannuwa kamar mai roko.
Dariya ma ya bata kamar wani dan almajiri ta mika masa. Yana karba ya zame daga zaune ya kashingide akan kujera ya saka speaker. Kai tsaye sai cewa ya yi, "Nayi miki laifi ne you don't even ask for me (ba kya nema na)." Da muryarsa ta gane shi duk da sau daya ta taba ji. Murmushi Tauhidat ta sami kanta da yi. "Laahhh, Dayan kayi hakuri. Ina cewa Nanna da Jamal su gaisheka." "Meyasa ba za ki gaisa dani ba sai sako? Bana so." "Kayi hakuri" Tauhidat ta ce a sanyaye. Haj. Manga kuwa dukan kafadarsa tayi ta mika hannu "kai bani wayata. Ya za ka tsare min yarinya da rigima saboda ka dawo gida a gajiye? Rabu dashi kinji ko." Sai da ya matsa can gefe rike da wayar ya ce "nima ki dinga kirana. I am your brother too. Zan karbi number dinki wurin Nanna." "Ai bani da waya, ka bari ta dawo sai na dinga kira da wayarta har sai ka gaji." "Seriously? Nanna wai bata da waya?" Kai ta gyada masa tana cewa sai ta kare secondary ya ce da Tauhidat "I'll send one for you with Jamal okay? (Zan bawa Jamal ya kawo miki guda kinji.)" Ba wai turancin bane Tauhidat bata ji sai dai accent dinsa (fitar sauti) ya bambanta da irin turancin da ta iya. Ko kadan bata gane me ya ce a karshen maganar ba. Kasa tayi da murya "ko me ya ce?" Sai kuma ta daga muryar yadda zai ji ta ce "uhmm" alamun bata ji me ya ce ba. Haj. Manga ta tuntsire da dariya "kana magana da hanci yaushe za ta gane? Muma nan wahalar damu kake yi. Hausa da turancin duka da hanci suke fita." Dariyar Tauhidat ya ji ya bata fuska ya ce "me nayi?" "Tauhidat wai waya zai saya miki." Cewar Haj. Manga. "Ba kin ce sai..." "Kada ki ki karba ai yayanki ne. Kai kuma bani wayar kayi naka wuri." Sosai ya hade rai "ni ban gama ba." Murmushi tayi tana jindadin yadda yake nuna damuwarsa akan kanwar tasu tun kafin su hadu. A haka aka kare hirar su uku. Tauhidat ta sake sosai saboda tana jin muryar Nanna. Shi kuma Arqam yadda suke hirar ne yake burge shi. Haka kawai yake son muryarta...da fuskarta. Laifin dadi karewa. Kamar kifta ido da budewa haka sati uku suka wuce. Arqam tun asuba ya koma dakin Haj. Manga ya hanata komawa bacci. Gani yake kamar idan sun tafi shikenan zai koma gidan jiya. Da wannan tunanin yake kwana yake tashi. Tayi iya bakin kokarinta wurin kwantar masa da hankali da alkawarin ba za ta dauki lokaci ba zata dawo amma jikinsa ya yi matukar sanyi. Kansa ya dora akan cinyarta tana jin saukar hawayensa akan rigarta. Namijin kokari tayi bata son ta karasa karyar masa da zuciya ta hadiye nata kukan. "Kada ki manta da yi min addu'a kullum." "Wannan dole ne, kana kasar nan da ba mafadi ga Kawunku Audi ai dole na zage dage." Dago kai ya yi ya kalleta "Nanna me ki ke gani reason dinsa na yi min haka? Its not like muna neman wani abu a wurinsa" sannan ya kara da cewa "Idan kin koma ki kashe auren fa." Sama ta kalla tana kokarin mayar da kwallarta "ban sani ba Arqam, deep down ina ji a raina kamar akwai wani abu tsakaninmu dashi da bamu sani ba. Kaina a kulle yake. Dubi dai yadda ya lalata min yaro. Haji Lawalli ya ce Tony da bakinsa ya fada masa shi ya sa shi koyawa Jamal shaye-shaye. Zuwanmu nan ne ya hana shi yi saboda ganin ido. Amma kaninka ko kashin awaki aka ce zai bugar dashi fes zai tura a baki." Wani dadin abin haushin kuma da yake damunsu shi ne ganin ko kadan Jamal yaki yarda da cewa Alh. Audi baya son su. Jiya kamar ta doke shi da safe har ya yi fushi. Sai da suka yi la'asar a gida sannan suka kama hanyar airport. Abu Usama da iyalinsa sun zo sunyi musu sallama aka rabu ana kewar juna. Bayan sun isa an gama duba kayansu Arqam ya shiga mugun tashin hankali. Yau da yake ya saka hula ya kuma rufe rabin fuskarsa ya tsira daga mutane kuma ya sami damar kukansa na zuci da na zahiri a boye. Rabuwa ce mara dadi cike da tsoro da fargabar ko za'a sake haduwa. Duk wanda ya ga yanayinsu dukkansu sai sun bashi matukar tausayi. Tsayuwa ya yi yana daga musu hannu har suka bacewa ganinsa. *** Kauyen Dakasoye Mace ce durkushe a gaban murhu tana ta hurawa da baki da kasan zaninta amma wutar taki kamawa sai uban hayaki. Dududu ba ta haure shekaru ashirin da biyar amma wahala ta yankwaneta tamkar wadda ta baiwa arba'in baya. Dago kai tayi idanu jajir hanci na yoyon tsinkakkiyar majinar wahala ta kira kaninta dake yashe akan wata guntuwar ragowar tabarmar kaba.