Kenza eBookz

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 10

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 10

Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 10: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 10. "Mammalo agaza min da kirare ko na samu wutar nan ta kama mana." Ta ce…

10,397 words

"Mammalo agaza min da kirare ko na samu wutar nan ta kama mana." Ta ce tana mikewa tsaye da kyar. Siririya ce sosai ga rashin tsayi tana sanye da dankwali da zanin atampa daban daban da tayi daurin kirji dashi. Hakan shi ya kara bayyana tudun cikin jikinta da ya kusa cika watannin haihuwa. Yaron da ta kira Mammalo shi ma babu jikin. Zafi ya ishe shi daga shi sai dan buje yake kwance. Cikinsa a dame kamar zai hade da bayansa saboda tsabar yunwa. Bata fuska ya yi ya soma magana da kunkunin da ba ta iya jiyowa. "Dan gwafar ubanka baka ji ni bane? Idan wutar ta kama na dafa waken ba har da kai za a ci ba?" Dogon numfashi ya ja sannan ya tashi zaune yana numfarfashi "ke kuwa Yaya Uwani babu lamuni cikin lamuranki, banda rashin tausayi ina ni ina neman kirare yanzu?" Waken da ta zuba a tukunya ta kamfato a tafin hannunta ta watsa masa "sai ka ci a haka tunda ba za ka iya fita ba." Tausayinta ya ji ya mike ba don yaso ba ko riga bai saka ba ya fita. Cikin kankanin lokaci ya hado kananun itatuwa ya kawo. Da kyar Yaya Uwani ta samu wutar ta kama ta dafa musu waken da aka basu zakka daga gidan Sarkin noma. Man kwanturola ta diga musu a kai ita da kanin nata da guntun gishiri suka hau ci hannu baka hannu kwarya. Wata muguwar gyatsa Mammalo ya saki bayan ya gama kora waken da ruwan da ya sha daga wata tsohuwar buta. "Alherin Allah Ya kaiwa Sarkin noma da iyalinsa. Rabo kuma Allah...." Hannu ta dago masa da sauri "to mara mutumci za ka fara diban albarkar ne saboda ka koshi ko?" Dariya ya yi kamaninsa da ita na kara bayyana. Dan jikinsu iri daya. Bakake, sirara marasa tsaho. "Diban albarka ko fadin gaskiya? Yasin kwana biyun nan da babu abin dorawa a gidan nan na galabaita. Ko kinsan ko ga'idi ba na iyawa idan naje tsuguno? Haka zan gama nishi na tashi. Babu komai a cikin to me zan fitar? Tusa wannan hegiya haka nake fitar da sautuka kamar busa sarewa amma babu hamami don bala'i." Harara ta maka masa duk da ta san gaskiya ce yake fada "idan ba ka iya zaman gidana ai muna da yawa yayun naka. Ka koma gidan masu arziki inda ba'a kwanan yunwa." Ba nufinsa ya bata mata rai ba. Duniya kaf yanzu ba shi da kamarta. Sauran 'yan uwansu suna gudun ya zauna musu a gida saboda kiriniya da daukar magana. Uwani kuwa da suke sakwanni dashi ta ce taji ta gani. Innarsu ta so autanta don bata raye bai kamata zumunci ya yanke ya rasa wurin zuwa ba. Matsalarta guda a gidan aurenta, mugun talaucin da ya yiwa maigidanta kawanya. Da babu ta addabe shi ya sayar da kazarsa ya je gidan wani Malami neman sa'ar arziki. Malami ya dafe 'yan canjin ya ce masa iyalinsa ce mai farar kafa sannan ya hada masa da wuridin arziki. Rabo na jin haka bai kara sati ba ya dankara mata saki ya kuma tattara komatsansa ya bar garin. Gidan ma bar mata ya yi tunda yana hasko arzikinsa. Wuyarta dai ya yi nesa da ita ya sami damar yin wuridinsa. Idan arziki ya zo sai kowa ya yi mamakinsa. Daga ita sai kaninta a gidan, sai kuma cikin da ya bayyana bayan tafiyar Rabo. Su kam sun wuce ajin talauci sai fatara. Basu da komai sai abinda Allah Ya hore musu a rana. Tun suna yawon zuwa gidajen 'yan uwa da tsakar rana daidai lokacin cin dumame har dai gori ya hanasu fita. Uwani akwai bakar zuciya. Habaicin 'yan uwanta ya sanya ta dena zuwa duk da yunwar dake sasakarsu. Mammalo kuma dama malalaci ne. Bai iya komai ba sai yawon gidan kallo. Ya dane bishiyar darbejiyar wajen wurin yana kallo a bagas. Shekarunsa ashirin da biyu. Yana son yayarsa kamar rai duk da fada suke kullum kwanan duniya. Hakuri ya bata ta kuwa sauko tunda tsakaninsu ba ta baci. Sako mata zancen tafiyarsa birni ya yi a karo na biyar cikin satin nan ta kuwa sake hade fuskar nan kamar bata taba dariya ba. "Yadda Rabo ya guji mai farar kafa kaima guduna za kai ko?" Kwantar da murya ya yi kamar jikan maroka ya soma magiya da ban baki yana nuna mata alfanun tafiyar. "Ni fa na gama tsara komai. Gidan kallon nan da nake zuwa ba banza ba. Kamar yadda na gani a wani fin nima ina zuwa zan sami arniyar motar gidan masu kudi ta bige ni." Da sauri ta dafe kirji jin wannan rashin hankali "idan ka mutu fa?" "Za su biya diyya sai ki rike duka ki kula da kan ki da jaririn da za ki haifa. Ko kwandala ki ka baiwa wani cikin su Yaya Talle Al-Qur'an ban yafe ba kuma sai nayi muku fatalwa." "Ba ka da hankali. Idan kuma ka hada da 'yan yankan kai fa?" "Kurwata kur...ke da nake miki bayanin masu kudi zasu bigeni. Daga nan muje gidan sai 'yarsu ta makale min, a kai ruwa rana karshe ayi aurenmu ni da ke mu wataya me ya kawu zancen 'yan yankan kai kuma?" Dariya ya bata kuwa "ashe harda aure, eh lallai. Har an daura ma ta tare. Mammalo mijin Hajiya ranka ya dade." Bai ji haushi ba ya cigaba da bayanin yadda zai je birni neman auren 'yar masu kudi. Ya tabbatar kyaunsa kadai ya isa ya janyo masa soyayyar yarinyar ko 'yar waye. Kuma a shirye yake da ya jure duk wani wulakancin mahaifinta a dalilin talaucinsa kafin karfin soyayyar tasu ya sa a bashi ita. Tashin farko gida zai dankawarawa Yaya Uwani. Ya wadata ta da abinci ita ma ta dinga bayar da zakka duk shekara. Abinda za ta haifa kuma zai kaiwa matarsa har ma ya ja mata kunne cewa idan ta wulakanta jinin Yaya Uwani ta wulakanta igiyar aurenta ne. Wata irin zabura da tsallen murna ya yi bayan ya gama shirya komai a cikin kwanyarsa. Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba. Cikin wata guda sai da abokan huldar Mammalo suka san zai je birni. Karya ya shata musu wai ya sami aiki ne a birnin tarayya Kaduna. Wadanda suka san karya ne suyi ta dariya suna zuga shi. Bayan 'yan kwanaki kawai ya hada 'yan kayansa ya yiwa Yaya Uwani sallama. Ranar tayi kuka tayi roko harda fada amma ya dage cewa shi fa zuciyarsa tana bashi lallai da arzikinsa zai dawo kauyen nan. Babu irin fadi tashin da bata yi ba wurin hana shi amma ya tubure. Babban yayansu ya ce a barshi ya tafi ai bari ba shegiya bace da ubanta. Idan ya kwana biyu kacal a birnin da kafarsa zai dawo gida. Tana ji tana gani abokan arziki masu jindadin shaftarsa suka hada masa kudin mota ya samfe... *** Ana sauran kwana biyu su Haj. Manga su dawo Abayomi da Tauhidat suka dawo Abuja. Madam Zainaba tana garinsu babu lafiya. Ashe tana da ciwon suga sai yanzu aka gane. Ga damuwar rashin waya daga uwardakinta ta saka a rai. A zatonta jikin Baffan ne ya yi tsanani tunda bata fada mata gaskiya ba kafin tafiyar. Sun saba duk inda ta je tana kiranta ta bata lambar wayarta. Jikinta har lokacin babu kwari shi ya sa danta ya ce ta zauna idan sun dawo zai kira ta ya sanar da ita. Bayan dawowarsu Tauhidat washegari ta gyara dakin Haj. Manga da nata. Babu inda bata share ta goge ba. Tun daga falo har dakunan da bandakunan biyu. Abinka da dakin mutanen Maiduguri ba sa rabo da kamshin turaren wuta. Na safe daban na yamma daban. Su kansu uwa da 'yar sassanyan kamshi ya ratsa jikinsu. Tauhidat kam sai dai a kirata babarbariyar bayerabiya kuma bahaushiya a baki domin yaren gidan kenan. Da wuya ka ji Haj. Manga na magana da yarenta indai ba da Baffa ba. Jamal ba wani iyawa ya yi ba bare kuma Arqam da ya dade ba ya nan. Karfe bakwai suke sa ran saukar jirgin kamar yadda ta sanar da Papa Abayomi a waya. Shida da rabi suna airport shi da Tauhidat a cikin sabuwar motar Haj. Manga Element. Basu wani jima ba kuwa suka sauka. Jamal ta fara hangowa ya taho a guje harda bude hannuwa. "Oyoyo Tauhidat.." ya tafi kamar zai rungumeta Haj. Manga ta janyo kwalar rigarsa ta baya. Dariya ya saka yana kyakyatawa saboda yadda ta hade girar sama da kasa tana fada. "Kwana biyu mun yi missing wannan Nannan ko?" Ya tambayi Tauhidat dake taya shi dariyar. Girgiza kai tayi ta kama kunnuwansu tana cewa suna son mayar da ita kakarsu ta karfi da yaji. Baffa yana kallon yadda take fadan amma kana ganinta ka san cewa tana tattare da babban farinciki. Shi da su Papa Abayomi duka murmushi suke yi lokacin da take korafin wai Tauhidat tayi duhu kuma ta fada. Ba za ta kara turata Gombe ba tunda babu kulawa yadda ta dace. Mota suka nufa Tauhidat ta daukar mata jakar hannunta sauran akwatunan kuma ana tura musu. Baffa motar Haji. Lawalli ya bi washegari zai wuce Maiduguri. Tun a gidan Arqam ya riga ya baiwa Haj. Manga takardun da za ta karbi kudadenta dasu. Anzo shiga mota tunda Jamal ya kyalla ido ya ga wadda aka zo da ita ya shiga rokon a bashi ya tuka. Magiya yake yi Tauhidat na taya shi Haj. Manga ta ce basu isa ba. Tunda bai gaji ba idan sun isa gida ya dauki tasa motar ya wuce Adamawa amma ba ta ta ba. Basu fasa rokon ba har Papa Abayomi ya taya su cewa a bashi dani. Ashe kaddara ke kiransu. Ranar kwanan Mammalo daya a tasha ya rasa inda zai sa ransa yaji dadi. Shi dai ya fadawa direban motar da ya biyo cewa birnin tarayya zai je. Direba kuwa ya caje shi kudin zuwa Abuja. Duk lissafinsa Kaduna zasu je domin nan ne yaji ana cewa garin Gwamna. Sai ya zata nan din ne birnin tarayya. Da isarsu kowa ya sauka Mammalo ya shiga raba idanu ga yunwa. Kure aljihunsa ya yi ya sayi kosan hamsin aka zubo masa su a leda kamar ya hada ya tura duka lokaci guda. Ya ga tashin hankali muraran domin a iya saninsa kosan hamsin a garinsu duk yunwar cikinsa ya yi masa yawa. Tijara ya hau Mai kosan da ita ya ce ko ta kara masa ko a bashi kudinsa. "Wake abin banza shi ne za ki zuba min wannan abu kamar za a baiwa dan yaye? Ni da Yaya Uwani dan talatin muke ci mu gyatse a garinmu" "Nan Abuja ne ba garinku ba" wani a kusa ya bashi amsa. Ita kuwa Mai kosan harara ta doka masa ta cigaba da juya wanda yake cikin mai. Mammalo ya kara harzuka kuwa yana ganin kamar rainin wayon 'yan birni ake neman yi masa. Wanda ta soma kwashewa ya dumbuza a hannu ga zafi ya kwasa a guje. Bai je ko ina ba wasu karti suka damko wuyansa. Nan aka nada masa na jaki ana kiransa barawo. Abu dau baiyi dadi ba. Da tsattsaman jiki ya kwana akan wani benci a tashar ga yunwa kamar ya ci babu. Tunda garin Allah ya waye ya koma bakin titi yana jiran motar masu kudi tazo ta bige shi ko ya samu su daidaita da budurwar da wuri ya koma wurin Yaya Uwani. Da yake da wayonsa ya kula motocin nan sharo gudu suke yi, idan ya yi gangancin hawa titi mitstsike shi zasu yi tas a kasa gane shi a kan kwalta. Tafiya mai dan nisa ya yi zuwa bakin junction inda ya kula da mai bada hannu ga kuma wata fitila mai canja kala. Gaban motoci biyar ya sha daga safe zuwa yanzu amma duka bai ga alamun nasara ba. Na farko fitowa ya yi ya zabga masa mari yana ta magana da yaren da bai ganewa. Na biyu sai da yellow fifa ya sa baki har aka ce ana kallon lokacin da ya kwanta a gaban motar don ya kulla musu sharri. Wahala idan ta auri mutum sai hakuri. Isha ta kawo kai yanzu babu wata alamar sa'a a tare da shi. Hanyar tashar ya soma nema ya koma amma ya kasa ganewa. Kamar da wasa ya dan juya gefen titin kuwa ya hango wata bakar mota mai masifar kyau tana tahowa. Hasken fitilun titin sun sake kawata ta tana ta kyalli. Babu mai bada hannu yanzu kuma dai ba sanin kan fitilar nan mai canja kala ya yi ba. Haka ya yi shahadar kuda ya jefa kansa a tsakar titi daidai lokacin da Jamal ya taka wani mahaukacin burki. Haj. Manga da Tauhidat sai salati don sun saddakar ko waye an gama taka shi. Jikin Jamal na rawa Papa Abayomi ya fita da sauri. Mota dai bata taba Mammalo ba sai firgitar da ya yi. Ganin babban mutum a kansa sai ya ji tsoron kada a maimaita irin na dazu a mare shi. Tashi ya yi zai bar wurin salin alin sai ga Haj. Manga da Tauhidat sun fito daga motar suna tambayar ko yaji ciwo. Ai yana kyalla idanu akan Tauhidat sai ga shi ya fadi wanwar a kasa yana kiran bayansa ya karye tare da kifta mata idanu yana mata kallon notice me. Haj. Manga ta soma yiwa Jamal fada shi kuwa duk ya rude yana tsoron ko da gaske ya ji masa ciwo sai ga wasu masu cin kasuwar bakin danja. Wani cikinsu ne ya gane Mammalo ya tona masa asiri cewa tun dazu yake shan gaban motoci. Suka tarar masa don son burge Hajiya mai alamun naira a jikinta ai kuwa sai gashi ya mike garau. Wannan abu ya batawa Haj. Manga rai kuwa. "Idan kudi kake so ka nemi aiki mana. Kai ko bara ai ta fiye maka da wannan gangancin da kake da rayuwarka." Idanu akan Tauhidat har lokacin Mammalo ya shiga bata hakuri tunda ya ji ance a kira 'yan sanda su tafi dashi. "Ka wuce ka koma gida zaman yaro kamarka a nan da wannan sana'ar babu abinda zai ja maka sai wahala" cewar Papa Abayomi. "Kwarankwatsa bani da wurin zuwa a garin nan. Birnin tarayya na ce a kaini can Kaduna shi ne aka kawoni nan. Aiki nazo nema in sami kudi in koma wurin Yaya Uwani." Haj. Manga tace "daga ina kake?" "Dakasoye, alkarya ce mai kyau a birnin Kano." Ya bata amsa yana dan hura hanci kada a raina shi. Ah to shi da zai zama surukinsu gara a fara mutunta juna tun wuri. Murmushi tayi ta tambaya shi sunansa. "Mammaloncy ne da turanci" Jamal da Tauhidat me zasu yi in ba dariya ba. Mammalo zuciyarsa har wani shiga shauki take yi ganin ya fara samun kan budurwar da yake da yakinin idan har ba aurenta yazo yi ba to tabbas akwai wani al'amari tsakaninsu da ya kawo shi Habujan nan. Ita kanta sai lokacin ta dan kalle shi haka nan ta ji kamar jininsu zai hadu saboda yanayin barkwancinsa. Bayan doguwar muhawara tsakanin Papa Abayomi da Haj. Manga akan rashin gaskiya na mutane da kuma tausayin yaron da ya mamaye zuciyarta a lokacin aka ce ya shiga gaba. Papa Abayomi ya karbi tukin su kuma suka koma baya su uku. Yana zama a motar ya dan waiga baya "Hajiya nace ba, shin yarinyar nan taki kinyi mata miji ne?" Wata muguwar harara da ya samu daga Papa Abayomi sai da hanjin cikinsa ya karkada. Jamal na dariya ita kuma Tauhidat ta hade rai. Haj. Manga ta kalleta tana murmushi don zancensa ko kadan bai bata haushi ba "Tana da miji idan ma saboda ita ka biyomu tun wuri a tsaya ka sauka." "Ai ba za ku rasa 'ya'yan 'yan uwa da abokan arziki ba. Mace dai indai ta birni ce kuma gidansu akwai get ina so." Kafin su isa gida hatta Papa Abayomi sai da ya dara. Gaskiyar dalilin zuwansa birni ya fada musu abin tausayi abin dariya. Haj. Manga ta ce indai zai dan nutsu to za ta bashi aikin yi ya samu kudin sayawa Yaya Uwaninsa abinci. Girman Karam Mansion ya matukar tsorata Mammalo har ya tuna da 'yan yankan kai da Yaya Uwani da fada masa akwai. Jikinsa a matukar sanyaye ya fito daga motar bayan kowa ya fito. Bakinsa yana rawa ya ce "kaddai har na cika?" Jamal yana nunawa wani yaron gidan jakarsa da zai kai masa daki ya ce "Me ka cika?" "Na cika da imani mana an kawoni aljanna. Idan kuma gidan yankan kai ne to na rantse fatalwa zanyi muku na hanaku rawar gaban hantsi." Dariyarsu ce ta janyo hankalin Alh. Audi da Shamsu da suke ta magana cikin bacin rai tun dazu basu ji shigowarsu ba. Murmushin dole ya dauko ya yabawa fuskarsa ya karaso inda suke. Wata mummunar faduwar gaba yaji a lokacin da ya hada ido da Mammalo da Tauhidat da tafi kusa dashi. Bai san kuma ya akayi ba haka nan ya tuno da Arqam yaron da yake ta nema ruwa a jallo a boye. [2/23, 7:34 PM] Nasma: Dauriya ya yi suka gaisa Haj. Manga tana ƙoƙarin sanar da shi baƙon da ta taho dashi ya kasa nutsuwa ya saurara. A zuciyarsa kuwa fargaba ce take masa kai kawo. A cikin shekaru sama da goma sai yau ya tuna cewa banda Arƙam da Tauhidat tabbas Oga ya faɗa masa mutum uku ne manyan ƙalubalensa a rayuwa. Abinda ya kwantar masa da hankali shi ne sanin da ya yi cewa Oga yana faɗa masa duk lokacin da suka tunkaro shi. Tunda bai sake jin gargaɗi ba daga gareshi tun wanda ya yi masa gabanin zuwan Tauhidat, ya tabbata wannan ragowar yunwar ba ya cikinsu. Sakin fuska ya yi ya nunawa Haj. Manga ta kyauta wurin tunanin taimakon mabuƙaci. Daga nan ta roƙi Papa Abayomi ya tafi dashi ɗakinsa kafin a bashi wani da safe. Suna tafiya hanyar ɗakunan ma'aikatan daga ɓangaren dabbobi jimina ta yi kuka sai birrai daga nasu kejin suka soma. Mutuwar tsaye Mammalo ya yi jikinsa ya saki sai gumi kamar anyi masa feshin ruwa. "Fafa" ya kira Papa Abayomi kamar yadda yaji Jamal da Tauhidat suna kiransa da murya can ƙasa. "Taho mana mun kusa. Yanzu Hajiya za ta aiko da abinci sai kaci ka yi wanka da sallah." Maƙalewa ya yi a wurin yaƙi ƙwaƙƙwaran motsi. Papa Abayomi sai ya dawo da baya ya riƙe hannunsa ya ji ya turje. "Meye haka ne?" Wani siririn hawaye ne ya silalowa Mammalo ya ce "Gidan zoo ku ka kawoni daga neman taimako?" "Gidan zoo kuma?" "Kada ka ce komai nima da kake ganina wayis ne. Gidan zoo ɗin Kano zuwana ɗai-ɗai har huɗu saboda haka na waye da kukan birai da damisa." Sai da Papa Abayomi ya gama dariyarsa sannan ya kama hannunsa yana jansa tare da yi masa bayanin cewa wurin shaƙatawar masu gidan ne. Lallai ba don dai har yanzu yana jin tsamin jiki daga dukan da ya sha a tasha ba da ya yi rantsuwar cewa ya mutu ne. Yanzu a gidan duniya don tsabar jindaɗi mutum sai ya kewaye kansa da namun daji? Ba komai yake jiye musu ba sai ranar da dabbobin zasu tsinke. Watanda sunan wani abu. Indai aikin da za a bashi ya danganci zuwa zoo ɗin ne ya yanke shawarar kama gabansa a gobe goben nan. Da suka shiga ɗaki bayan ya gama santin wuri ya tambaye shi garinsu. "Na ji hausar taka ba irin tamu bace." "Bayerabe ne ni." Mammalo ya riƙe baki, "kuma musulmi? Ikon Allah. Yasin in ka barni duk duniya daga mu Hausawa sai Larabawa ne kaɗai muke sallah." "To yau ka haɗu da bayerabe wanda aka haifa cikin musulunci" Papa Abayomi ya ce da sakin fuska. Mammalo ya washe baki "ni kuma Badaƙasoye ne, ai ka ji lokacin da nace sunana Mammaloncy ko?" Dariya bata barshi ya iya amsawa ba kuwa. Haka suka kasance, sunata wasa da dariya abinsu. *** Kulsum da Aimana suna ta murnar dawowar Nanna. Yaro ba ruwansa da kishi balle kuma ga mai kyautata masa. Suna daga cikin dalilin da ke daƙile rashin kunyar Fanna yanzu gareta. Sun gaisa a mutunce suka wuce ɗaki Jamal shi ma ya nufi ɓangarensu. Ya fito daga wanka kenan Arƙam ya kira yana mitar rashin samunsu tun dazu bayan ya san sun sauka. Jamal ya zauna bashi labarin guntun hatsarinsu da Mammalo, hankalinsa kuwa ya tashi ya shiga kiran Haj. Manga ba ji ba gani. Sallah take yi ya kira ya kai sau biyar ya kuma kiran Jamal yace ya kai mata wayar. Ya kusa isa ɗakin ya ji ya ce, "Ka bata wayar da na baka?" "Wa kenan?" Ya tambaya duk da ya riga ya san da Tauhidat yake. Dan sosa kai Arƙam ya yi sannan ya ce, "ƙanwarka." "Kulsum ko Aimana?" Ya tambaya yana dariyar tsokana a ciki. "The other one (ɗayar)" "To ko autar Nanna kake nufi?" "Jamal" Arƙam ya ce da alamun gargaɗi. Ya kuwa sa shi dariya hadda yi masa tsiyar ko har yanzu yana tsoron mata kamar yadda yake a da. Lokacin idan ka ga fushinsa a makaranta an haɗa shi yin wani abu da mace. A gida kuma idan suka fita indai gidan akwai mata da yawa kasa shiga yake yi. Ya ce da Haj. Manga wai tsoronsu yake ji. Sai su dinga kallon mutane suna jujjuya idanu baƙin kwayar yana shigewa sama. Ranar da ya faɗi haka ita da babansu sun sha dariya. Ashe wata ƴar ajinsu ke son shi da aka faɗa masa ya ce ba ya yi shi ne fa ta koma harararsa. Ya gaisa da Nanna ya tabbatar da lafiyarta sannan hankalinsa ya kwanta. Da Jamal ya tambayeshi ko ya kaiwa Tauhidat ba musu ya amince. Yana mamakin yadda yake jindaɗin hira da ita duk da ba ta sake masa saboda rashin sabo. Washegari da wuri Alh. Audi ya nemi Oga a waya ya tambayeshi ko mutum na uku cikin waɗanda ya gargaɗe shi a kansu ya tunkaro shi. Oga ya yi murmushi don ya tabbatar abin da ya sami labarin faruwarsa ya riga ya faru. "Ka kwantar da hankalinka har yanzu ko waye mace ko namiji lokacin zuwansu gareka bai yi ba saboda babu wani canji da na gani." Sai a lokacin hankalinsa ya kwanta ya ja gwauron numfashi. "Ba ka ga yaron da Manga ta kwaso min bane jiya. Muna haɗa ido sai jin numfashina na yi yana neman tsayawa. Yadda ka san yana gani na tsirara haka na ji." Sake kwantar masa da hankali Ogan ya yi suka yi sallama. Ko da wasa ba shi da niyyar sanar dashi hatsarin da yaron zai zame masa a nan gaba. Ba komai ya janyo hakan ba kuwa sai nasa ƙudirin da yake ɓoyewa game da Alh. Audin. Tauhidat da shirin komawa makaranta sati mai zuwa ta tashi bayan ta gama duka aikace-aikacenta na ɓangaren Haj. Manga. Dama an riga an saya mata litattafai da sababbin kayan makaranta tun ranar hutu na shiga SS3. Zaune take a falon Haj. Manga tana rubuta sunanta a jikin litattafan ita kuma tana bata labarin Arƙam. Wani abin ta maimaita mata sau uku ko huɗu saboda tsabar farinciki ita kuma ko sau ɗaya bata nuna ƙosawa ba. Babban abu irin wannan ya faru na murna amma tsoro ya hana ta raba farincikinta da makusantan ta. A wannan yanayin Jamal ya shigo anyi abin arziƙi yau ya taje tulin gashinsa da gayu yasa ya barshi a cukurkuɗe babu kyawun gani. Manyan kaya ya saka, shadda anyi mata ɗinkin tazarce yana ta zuba ƙamshi. "Sai ina wannan ƙure adaka don na tabbatar ba don zuwa gaisheni ka yi ba." Cewar Haj. Manga bayan ta amsa gaisuwarsa. Dan sunkuyar da kai ya yi Tauhidat ta dinga leƙen idonsa shi kuma yana mata nuni da baki akan ta yi bayani. "Uhmm Nanna tsaraba zai je kai mata." Ta ce kai a kasa saboda har ta fishi jin kunya. "Ita wa? Kada kice min da wannan sheƙar ungulun gashin nasa akwai budurwar dake sauraronsa." A take su biyun suka ɓata fuska. Tauhidat ce mai kare masa "akwai Nanna kuma ƴar islamiyyarmu ce. A wurin kaini suka haɗu kuma kyakkyawa ce sosai." Murmushi ta yi. Ita dai haɗin kansu yana matuƙar burgeta bata fatan wani abu mara daɗi ya gifta tsakanin ƴaƴanta. Yadda Tauhidat ta ɓata fuska ne yasa ta cewa "Maida wuƙar ƙanwar Jamalu. Tunda bokon yaƙi idan auren yake so sai na yi masa ai." Zai yi magana Tauhidat ta riga shi. "Nanna Jamal fa zai baki mamaki." Ta juya tana kallonsa yana zaune ya tallafi fuskarsa da tafin hannayensa yana kallonsu "kai kuma idan ka cigaba da bin su Mannirun nan ni ma ba ruwana da kai." Da sauri ya soma bata haƙuri hadda alƙawuran maida hankali a karatu kamar gaske. A gaban Nanna ta yi masa a bayanta idonta ma haka. Shi fa idan za ka ƙure shi akan su wa yafi so a rayuwarsa daga Nannansa to tabbas Tauhidat sai ta zo a ta biyu sannan Arƙam ya biyo baya. Shaƙuwa ce mai ƙarfi sosai a tsakaninsu tamkar da gaske cikinsu ɗaya. Yana fita sim ya fara saya ya saka mata a wayar da ko yau da safe Arƙam ya sake masa tuni da ya bata kuma ya tabbatar ya saka mata kuɗi. Katin dubu goma ya loda mata sannan ya wuce gidansu budurwa. Haj. Manga gudun tone-tone tunda ta ce dubiya za ta je shi ya sa Kulsum da Aimana kaɗai ta sayawa riguna da takalma. Ƴarta kuwa akwati guda ne da kaya da tarkacen ƴan mata na kwalliya. Turarakan jiki da na kaya masu ɗan karen ƙaamshi kuma saƙon Arƙam ne a wata ƴar jaka mai kyau. Murnarta ba a cewa komai. Tun tana godiya ta koma ƙwalla. Sai da Haj. Manga ta soma faɗa ta dena kukan. Ko gama ganinsu bata yi ba ta tashi zuwa dakin mahaifinta ta faɗa masa tunda ido ba zai bari ta kinkimi akwatin ba. Daga bakin bene tun kafin ta gama saukowa take jin sautin dariyar Fanna. Ta soma saukowa ta hango Papa da Mammalo ya taƙaƙare yana bayani. Takunta Fanna ta ji ta ɗago idanunta hadda hawaye don dariya ta ce mata ta kirawo Nanna baƙonta na jiranta. Komawa ta yi ba jimawa suka sauko tare. Papa Abayomi ne ya musu bayanin cewa daga fitowarsu zai nuna masa gidan ya rikice masa wai a saita shi gabas zai koma ƙauyensu. Girma da haɗuwar gidan sun matuƙar tsorata shi ya soma kokwonton ko cinikin kansa zasu yi da turanci tunda ba ji yake ba. Sai da Haj. Manga ta yi da gaske wurin kwantar masa da hankali sannan ta ce daga yau Papa Abayomi ya soma koya masa abubuwan mota. Ya san sunan kowane bangare da amfaninsa sannan a kai shi makarantar koyon tuƙi. Tana so kuma duk inda aka aike shi su je tare saboda ya gane gari shi ma wata ran a aike shi. Bayan ta gama duka bayananta Mammalo ya muskuta gaba a hankali sai ga shi a kusa da kujerar da Haj. Manga take. An gama magana bai ji an sako batun abinda ya kawo shi birni ba. "Hajiya sai maganar albashi na ko." Gyara zama ya yi saboda abinda zai faɗa ya ƙudurta a ransa yadda gidan yake da girma to fa ba zai musu lamuni wurin albashi ba. Da yatsun hannuwansa ya shiga lissafi. "To da farko dai shinkafa kwana uku idan ƴar hausa ce, kwano biyu idan ta gwamnati ce. Sai wake da gero suma kwano bibbiyu. Kwantirola kwalaba ɗaya amma kwalabar seben o (seven up) don tafi girma. Sai gihiri da mai tauraro ƴan hansin-hansin. Da kuma kuɗin motar da zan kaiwa Yaya Uwani." Ya kare maganarsa da haɗe fuska don tun yana lissafin ya kula kamar suna mamaki. Shi kuwa ko yi ko bari ba zai rage ba. "Yanzu Mammalo da wannan ka ke so a biyaka?" Fanna ta tambayeshi don har ga Allah ya bata tausayi. Duk a lissafinsa nan fa ya ƙure su kenan. Ita kuwa Haj. Manga cewa ta yi yaushe yake son a kaishi wurin yayar tasa za ta so ganinta. A zatonsa ko so suke ita ma a taho da ita gidan. Nan ya fitittike musu ya ce shi yayarsa tafi ƙarfin aikatau. "Ah to, irinsu Yaya Uwani fa sai Kansila ba don ƙaddarar auren matsiyacin nan ta gitta mata ba da yanzu ana kiranta Hajiya." Haj. Manga ta sanar da shi cewa albashinsa na farko za ta biya shi saboda haka take son yaje gida ya kaiwa ƴar uwarsa nasa rabon. Daga jin haka Papa Abayomi ya riga ya san uwarɗakin nasu alkhairi take nufin Mammalo da shi. Godiya ya ta ya shi yi mata ta ce washegari sai a kaishi gida saboda ita ta fi gane duk wanda zama ya haɗasu to ta san asalinsa. Suna wannan tattaunawar Jamal ya dawo. Da hannu ya yafito Tauhidat suka hau sama zuwa falon Nanna. Wayarta ya nuna mata ƙirar Nokia mai matuƙar kyau daidai ƴan mata. Ta saki baki ta ma rasa abin cewa ya ɗauko tasa da zummar saka mata nambar Arƙam sai ya ga suna ya bayyana kafin ya kai ƙarshe an rubuta Karam 1 a jiki. Ɗan murmushi ya yi da ya ga tasa numbar da Karam 2 ya mata saving. Miƙa mata ya yi, "Arƙam ne ya saya miki, ki kira shi yanzu don ya dameni akan na baki wayar. Da kuɗi a ciki na san zai isheki." Sai da ta gama godiya ta koma yi masa mitar yadda ya hanata kiransa da Yaya ta kula haka yake kiran ɗan uwan nasa. "A wurin wa na koya ni ma? Shi ne fa mai ƙorafin wai sunansa is too sweet bai yarda a ɓoye masa da wani Yaya ba. To ni ma nawa da daɗi ga gudun tsufa so kawai sammakal ki kiramu kai tsaye." Kai ta gyaɗa kawai tana biye da shi, "muje na nunawa Nanna." "Ta gani tun a can, please ki kira shi yanzu na huta da mitarsa." Kitchen ɗin ɗakin ya shiga neman abinda zai ci ita kuma ta shige ɗakinta. Sunan ta ke ta kalla tana murmushi kafin ta tattaro ƙwarin gwiwa ta danna kira. Farar safiya ce a can ƙarfe shida da ƴan mintuna. Yana cikin cire scrubs ɗinsa (kayan aikin asibiti) bayan sun fito daga wata emergency theatre wayar ta shigo. A gajiye yake sosai idanunsa da ƙyar yake iya buɗeu saboda bacci. Gida yake son ya tafi ya kashe waya ya kwanta sai azahar. Baƙuwar number da ya gani kuma daga Nigeria sai kawai jikinsa ya bashi ita ce. Tana jin alamun ya ɗaga ta yi masa sallama a ladabce kuma ta kara da, "ina wuni?" Earbud ne a kunnensa irin wanda ake amsa waya da kunne ɗaya mai dan girma saboda haka ya cigaba da balle maɓallan rigarsa yana mai jindaɗin muryarta. "Bamu wuni ba Cuddles." "Cuddles?" Tauhidat ta ce da mamaki. "Yeah" ya amsa a lalace saboda wata muguwar gajiya da ta sake saukar masa. "Me yake nufi?" Sautin murmushinsa har kunnenta sannan ya fassara mata kalmar tana nufin mutum mai jiki irin wanda ake son rungumewa ko a kwanta a jikinsa. Kafin ya gama dogon turancin nasa ta buɗe baki yafi a ƙirga saboda kunya da mamaki. Yanzu ita ɗin ce za ta yi daɗin runguma sai kace wani pillow? Tana can tana tunani har ya gama shiryawa ya rataya jakarsa bayan ya fito da mukullin motar daga ciki. "Uhmm bari na kashe maybe yanzu ka tashi daga bacci." "Zan tafi gida ne nayi call yau." "To sai anjima" kit ta kashe wayar. Kafin ta fita daga ɗakin ya sake kira. Hira ya buƙaci ta yi masa wai yana jin bacci sosai saboda haka yana buƙatar abinda zai ɗauke masa hankali har ya isa gida. A zahiri muryarta kawai yake son ya cigaba da ji ba wani abu ba. Shiru ta yi ita ma saboda rashin sabo ta rasa abin cewa. So yake ta saki jiki da shi kamar Jamal. "Bani labarin Nanna. Yanzu na manta things about her (abubuwa game da ita)." "Faɗa min waɗanda ka tuna tukunna." Tuƙi yake cikin nutsuwa yana ta murmushi. Wai shi za ta nunawa tana da wayo. "Lokacin Abbanmu yana nan tana yin baki-baki da baka-baka." Allah Ya sa ta taɓa jin wannan sunan a wurin Jamal ta soma dariya "burabusko da miyar kuka!" Ɗan zaro idanu ya yi "don't tell me (kada ki ce min) har yanzu tana yi." "Idan za ta zo wurinka zan tuna mata ta taho da tsakin da kuka ta yi maka." Ta tsokane shi. Har ya hango abin a idonsa kuwa ya kyaɓe fuska da sauri "No, ba na ci fa! Amma ba tare za ku zo ba?" Shiru ta yi. Ita fa ƴar direba ce kuma ba ta son zaƙewa akan matsayinta. Yanzu ma wayar nan a takure take jin kanta. Tana gudun ce masa ba tare zasu zo ba kada ya je ya yi wa Nanna magana a haɗa da ita ko ba niyya. Basu taɓa yi mata wani abu na ƙasƙanci ba amma kamar yadda babanta ke ja mata kunne a duk lokacin da suka keɓe, yana da kyau ta dinga sara tana duban bakin gatari. "Kafin mu zo tare nake nufi." "Kamar baki son ganina Tauhidah. Ni kuma ina son ganin ƴan uwana da yawa musamman ke." "Ni kuma? Me yasa?" "Honestly I don't know. I just want to know you (zancen gaskiya ban sani ba, kawai ina son saninki ne)." Shiru suka yi har ya ajiye motar ya shiga gida. Sai da ya gama shirin wanka ya faɗa mata ta kife wayar ko sallama babu saboda nauyin da maganar tayi mata. "What's her problem? (Meye matsalarta?)" Ya tambayi kansa. Tunda babu mai bashi amsa shi kaɗai ya ke ayyana ko don basu saba bane. Alƙawari ya ɗaukarwa kansa kafin su haɗu sai ya sa sun saba ta sake dashi sosai. Bayan ya gama waya da Haj. Manga da daddare kuwa ya sake kiranta. Wayar tana ɗaki ta manta da ita saboda rashin sabo. Ta Nanna ya kira ba kunya yace ta faɗa mata ta ɗauki wayarsa. Murmushin manya ta yi tana fatan Allah Ya kai damo ga harawa. Duk duniya bata jin akwai wanda zai kaita farinciki. Haɗuwar waya da hoto kawai ɗan nata yana wasu abubuwa da ita kanta ta yi imanin bai san girmansu ba ga mace. Ta yarda da ƴarta, rashin samu ne kaɗai zai sa mutum kusheta don ya huce ɗacin rai ba don tana da makusar ba. Wa yafi cancanta da morar rainonta sama da jininta? Waye za ta iya haɗawa da ƴar da take jin ta har ranta ya riƙe mata ita amana sama da jinin nata dai? Kiranta ta yi tana falo ta ce ta ɗauki wayarta ana kira. Missed calls uku ta gani da ta duba. A take wani kiran ya sake shigowa. Sunan ɗazu ya kirata dashi ta zumɓura baki kamar yana ganinta. "Na fa duba dictionary. Ashe mutum ɗan lukuti ake kira haka? Ni dai ba lukata bace." "Lukuti fa yana nufin fat, ke kuma you are not fat, just chubby." Buga hannu ta yi akan pillow ta ce "Ni dai gaskiya..." "Cuddles" "Na'am." Ta amsa ba shiri Ya yi dariya "kina son sunan kenan, ni kuma ba zan canja ba." Maganarsu da Jamal ta rana ta tuna "to kai kuma sunanka Yaya ko Brother." A take ya faɗa mata yadda Jamal ɗin ya ce mata kuwa. Shi yana son sunansa sosai bai yarda ba. Ta ce wato nata sunan babu daɗi ya ce a'a yana son sunan amma ta yi haƙuri tunda dai gaba yake da ita babu canjawa. Alƙawari dai zai mata shi ne ba kullum zai kirata haka ba. Wani lokacin Tauhida zai ce. Sai da suka kwashe wurin awa guda a rigimar suna har ta fara hamma sannan ya ƙyaleta. Kafin sati kuwa Fanna ma sai da ta fara zargin ko saurayi Tauhidat tayi. Daga waya sai text. Sai tana zaune ka ga ta tashi tana murmushi. A nasa ɓangaren da ya sami break a wurin aiki ko ya tashi ya koma gida bashi da aiki sai kiran gida. Daga ya gama da Nanna to kunnen Tauhidat bashi da sakat. Ba ta taba kiransa da kanta amma har tsumayin ya kira take yi. Kwana tara da dawowarsu Haj. Manga ta yanke shawarar zuwa wurin Dada ta faɗa mata gaskiya game da jikanta. Lokacin Tauhidat sun koma makaranta Mammalo kuma an zama ɗan gida saboda bai iya baƙunta ba. Sati na gaba Shaheed zai dawo tuni an bashi wani ɗakin amma kullum yana jikin Papa Abayomi yana bashi dariya. Saboda a kaishi gida ta yanke shawarar tafiyar mota. Mammalo ya fito lokacin sun shiga baya ita da Tauhidat. Ƴar jakar kayansa Papa ne ya saka a boot da kansa saboda haka duk tunaninsa bai wuce gida zasu mayar dashi ba batare da an biya shi ba ma. Zamansa ke da wuya a mota Fanna ta aiko Kulsum da envelop ta bawa Haj. Manga wai a ƙarawa Mammalo guzuri. Godiya ta yi mata sosai kuwa, ya baza kunnuwa yana jiran a ce ya miƙo hannu ya karɓa yaji shiru. Haka nan aka yi tafiyar jikinsa a saɓule. Yanzu haka zai koma gida bai samo komai ba ƴan garin ya san za su saka shi a gaba da surutu. Hanyar gidansu ba ta mota ba ce saboda haka da ƴar tazara tsakanin gidan nasu da inda aka ajiye motar. Papa Abayomi ya ce masa ya samo masu taya shi kwashe kaya a boot. "Fafa kenan, miƙo min jakata kawai na saba a kafaɗa. Me za a zo tayani ɗauka kamar wanda aka bawa kwanon shinkafa da wake bibbiyu kamar yadda na kwantas da kai na roƙa." Da yake akwai zulumin yadda Dada za ta karɓi maganar Arƙam sam Haj. Manga ta kasa sakewa sosai. Tana cikin damuwa ta ki faɗa. Shi ya sa Tauhidat ta jefa wayarta a jaka yau taƙi biyewa hirar Arƙam sai janta take ta hanyar bata labarin makaranta da suka koma ranar litinin. Bude boot ɗin Papa Abayomi ya yi Mammalo ya tafi da niyyar ɗaukar jaka ya yi arba da buhunhuna da kwalaye ga galan ɗin manja da na man gyaɗa. Dariyar farinciki ce ta mamaye fuskarsa da ta soma cikowa saboda cima mai kyau. "Ha in ruga bakin titi na karɓo laidos a wurin Ɗanasabe mai kiyos. In haɗo da kwano ko kuna dahi?" "Meye laidos kuma?" Inji Papa Abayomi. Tafa hannuwa ya shiga yi yana kaɗa kai "ledoji da turanci. Ka san fa na soma firamari, da dan boko na ma na san idan gayu yayi gayu ana kara cyyyyyy a ƙarshen suna." Ya fitar da kalmar tamkar sakin takurarrariyar tusa. Sai ga Tauhidat da Haj. Manga suna dariya hadda hawaye. Balle da ya ce zai karɓo ledar ne su aunar masa komai kwano kwano aka ce masa duka na Yaya Uwani ne. Ya kusa suma ya shiga far-far da idanu yana neman faduwa. Irin addu'ar da ya jerowa Haj. Manga sai ta ji inama ta ƙara masa fiye da haka. Buhun shinkafa da na wake bibbiyu ne sai na gero karami. Ga kwalin taliya da macaroni da na maggi da gishiri. Mai kowanne galan guda da omon wanki, sabulun wanka da man shafawa. Kuɗin da Fanna ta bayar ya karɓa ya ƙirga sai ya zari biyu ya maida mata. Shi tsoron kuɗin ma yake ji. Dubu ashirin zuwait kamar wanda yaje fashi? Sai da ya gama ƴar diramar tasa ya ruga gida a guje. Yaya Uwani hadda hawayen murnar dawowarsa. Da ƙyar take ɗaga ƙafa don ma ta roƙi wata Gwaggonsu ta dawo gidan saboda haihuwarta da ta matso. Haka ta daure zuwa inda aka ajiye motar ya gabatar dasu Haj. Manga da abin arziƙin da aka basu. Kuka hadda majina suna ta godiya ta roƙi Haj. Manga da ta dinga haƙuri da Mammalo. Shi kuma a gabansu ta rantse idan yaci amarsu kwarankwatsa sai ta kama shi. Da taimakon wani abokinsa suka kwashe kayan Haj. Manga ta bata sauran kuɗin sannan ta ce ya shirya ranar Lahadi zasu tsaya su ɗauke shi su wuce. *** Dada bata ce komai ba har Haj. Manga ta gama yi mata bayanin komai. Su kaɗai ne a ɗakinta. Babu hawaye ko ɗigo a idanun baiwar Allahn nan sai murmushi cike da jindaɗi. "Hafsatu ki sani cewa a tare da addu'a akan sami jinkirin ganin biyan buƙata amma tabbas a duk lokacin da ka ɗaga hannu kana tare da samu. Yanzun shi ne lokacin da Allah Yaso mu san inda Arƙam yake." Wani hoto Haj. Manga ta ɗauko wanda tun bayan dawowarsu take fargabar kada ya faɗa hannun da zai tona asirinta a gidan. Saboda gudun tsautsayi ko Tauhidat bata bari ta san da zamansa ba. Miƙawa Dada ta yi wadda ta saka kuka a lokacin. "Da gaske shagwaɓaɓɓan yaron nan likita ya zama." Ta ce tana shafa hoton. Yana tsaye sanye da kayan likitoci na asibitinsu ya ɗora labcoat ga stethoscope zagaye da wuyansa. Sun gama jajantawa juna Dada ta ce ita ma bata yarda ya dawo ba. Idan mahajjata sun dawo zuwa ƙarshen shekara ya tafi umara su haɗu a Saudiyya. Haka ya yiwa Haj. Manga daɗi sosai. Haɗasu ta yi a waya, Allah Yaso yana gida ya sakankance yana gwada mata halinsa da ta san shi dashi tun ƙuruciya. Tsohuwar nan ta yi kuka ta yi dariya ta kuma tsinewa Alh. Audi sau babu adadi. Biye masa ta yi suka sha hira sosai. Burinta ya cika. Su kaɗai suka rage mata tsani tsakaninta da Mal. Iro Karamci. Mahaifinsu ya rasu sune take gani su sanyaya zuciyata. Tauhidat ta kira ta zo kwashe kwanukan da aka ajiye musu na abinci kamar daga sama ta ce "ni kuwa Hafsatu an raba gadon yaron nan kuwa? Ba wai don na damu da a bani wani abu ba, ko kaɗan. Kawai kinsan shi gado nauyi ne ga mamaci." Shiru Haj. Manga tayi mamaki kamar ya danneta a wurin. Ashe fa duk tsayin shekarun nan ba a taɓa zama da sunan raba gadon mijinta ba. Zabura ta yi ta miƙe "Tauhida ɗauko min wayata da sauri na kira Baffa." Bayan ta tafi falo har lokacin tana jiyo muryar Nanna tana faɗawa Dada cewa tunanin bai taba zuwa kanta ba. Kuma bata san inda komai yake na shaidar abinda ya bari ba. Dada ta ce ita ma sai a ƴan kwanakin nan abin ya faɗo mata. Ta ɗauko mata wayar a cikin jaka ta kawo ta miƙa mata. Ko da ta karɓa sai ta hau dudduba sunaye ta rasa me take nema. Dada ta kalla ta ce "Dada zancen me muke yi ne ma?" Ƴar tsohuwa ta murmusa "maganar zamu haɗu da Arƙam a Saudiyya mana. Ba don Hajji ba da gobe goben nan zan bar ƙasar nan." Kan Haj. Manga sarawa ya soma yi da ta matsawa kanta da tunani saboda ta tabbatar cewa sunyi wata magana mai matuƙar mahimmanci amma kamar an shafe mata ƙwaƙwalwa. Wayar ta miƙawa Tauhida kana ganin yanayinta ka san bata ji daɗin wannan mantuwa ba. "Jeki da ita na manta wa zan kira." Jiki a sanyaye Tauhidat ta karɓi wayar ta fita. A bakin ƙofar ɗakin ta tsaya tsoro da fargaba na cika zuciyarta. Wannan wane irin abu ne haka? Yanzu suke zancen ba a raba musu gado ba amma cikin abinda bai fi ƙiftawar ido da buɗewa ba duka sun manta. Ita kuma da bata manta ba ɗin wani irin tsoro ne na ban mamaki ya kama ta ta yadda take jin ko da wasa bazata iya faɗawa Nanna ba duk son da take mata. Damuwar da take gani a fuskar Nanna tasa ta yakice tsoron ta yi nufin tuna mata. Sai dai kuma da ta buɗe baki sai ta ji harshenta ya yi nauyi. Abin ya ɗaure mata kai fiye da zato da tsammani. Ga magana a saman harshenta amma taƙi fita. Hankalinta ya tashi matuƙa. Wayarta ta ɗauko za ta rubuta a ciki sai ta tura mata nan ma abu yaci tura. Tun tana daurewa kuwa sai ga hawaye. Ga abu yana cin ka a rai amma ka kasa faɗa. [2/23, 7:34 PM] Nasma: Banɗaki ta shiga tasha kukanta son rai ta fito. Ranar bata iya bacci ba duk da gajiyar da suka kwaso ta hanya. Sau biyu tana tashin Haj. Manga idan ta gama karantawa zuciyarta dauriya. Tana farkawa sai ta kasa motsa bakin. Kafin asuba sai zazzaɓi mai zafi. Ko kaɗan zafin jikin ba shi yake damunta ba kamar wannan abu da ta laƙabawa tashin hankali. Kuka ta saka da abin yaci tura tana ta addu'a domin neman samun sauƙi. Ƙarfe tara a wani asibitin kuɗi ta yi musu aka zurkuɗa mata allurai da magunguna. Haj. Manga duk ta tashi hankalinta ganin tana share hawaye. Ta zata zafin zazzaɓi ne ita kuwa Tauhidat ba ta shi take yi ba. Bayan sun dawo tana ta lallaɓata ta ci abinci sai ga wayar Arƙam. Bayan sun gaisa ta faɗa masa Tauhidat ba lafiya. Ta san ko bata faɗa ba sai ya tambayi ina take tunda ya kira bata ɗauka ba. "Nanna ki bata wayar." "A kwance take ka bari ta huta." Ya tabbatar ba zai iya bacci ba idan bai ji muryarta ba. "Please just a minute na ce ya jikinta." Dada tana kallonta ta yi murmushi "ki bata mana su gaisa." Ɗakin da suka kwana ta bita ta bata sannan ta fito. Dada ta ce tana fatan dai abinda take zargi ne tsakaninsu. Gara a haɗa shi da ta gida kafin ya ɗauko musu baturiya. Suna hira suka ji sallamar Alh. Audi. Tauhidat tana ɗaki idanunta jazur saboda hawaye ta ma kasa amsa ya jikin da Arkam yake mata kawai ta jiyo muryar da ta saka ta kusan sakin fitsari a kwancen. Wuntsilowa ta yi a firgice ta fito daga ɗakin. Tamkar ita yake jira kuwa tana fitowa suka haɗa ido. Irin kallon da ya yi mata sai da ya tsinka mata jini saboda tsabar firgici. Bata taɓa jin tsoronsa ba sai yau. Jikinta ke bata ya san me yake faruwa shiyasa babu wani dogon lissafi don bata ma san ta yi ba ta maka masa wata uwar harara ta saki laluben ta juya. Gumi ya shiga tsatstsafo masa da ganin dahir game da abinda Oga ya faɗa masa a daren jiya cewa sirrinsa daya ya shiga kunnen Tauhidat. Bai san wanne bane cikin sirrukan amma ya kiɗime don gabaɗaya duk abinda ya kira sirri to ba ya fatan duniya ta taɓa ji. Da yake babu wanda ya ga leƙowa da komawarta basu damu ba. Wayancewa ya yi da cewa yaso tahowa jiya tare da Haj. Manga gaishe da Dada aiki ya riƙe shi. Babu wata magana daya da yake faɗa wadda ta ƙara masa daraja a idanunsu sai dai a bishi da to. Tauhidat sai taji girmansa gabaɗaya ya zube a idanunta. Sai yanzu wasu abubuwan ke dawo mata kamar uban kudaɗen da yake bawa Jamal duk kuwa da an san me yake da kuɗi. Nanna ko ƙwandala bata bashi saboda shaye-shayen da yake amma saboda taya ɓera ɓari a irin kuɗin da Alh. Audi ke bashi har kyautar motarsa ya bawa wani abokinsa ya sayi sabuwa. Wunin ranar a ɗaki ta yi shi, saboda rashin ƙwarin jikin da ya same ta. Babu yadda Haj Manga da Dada basu yi da ita ba, amma taƙi fitowa. Haka shi ma ya dinga zuba, yana daɗin baki. Har dai ya gaji da zaman munafurcin ya tafi. Washegari suka ɗunguma sai Abuja, tare da Mammalo da aka ɗauka a hanya. Rayuwa ta cigaba a inda Haj. Manga ta nemi contractors aka tsantsara mata zanen makarantar primary irin wadda ake haɗawa da karatun arabiya da Qur'ani sosai. Makarantar aji ɗaya zuwa shida ce, wadda take burin wadatawa da abubuwa na zamani. Sosai take burin ginata, domin taimakawa yara wajen jindaɗin karatunsu. Babu abinda ta faɗawa Alh. Audi don wannan karon taci alwashin ko me zai yi ya yi ƙarya ya rabata da abinda yake mallakinta. Ana wannan tsarin a gefe ta gama da cinikin fili da komai, ranar wata Laraba sai ga Madam Zainaba ta shigo gidan lokaci ɗaya. Koda suka haɗa ido ta ji ba daɗi, domin wata guda da dawowarsu daga wurin Arƙam ko sau ɗaya bata nemeta ba. Bata yi tsammanin ma za ta dawo ba. Ɗauke kai ta yi ta shige gida. Madam Zainaba ta rame sosai saboda ciwo. Rashin ji daga Hajiyan ya sa ta kasa haƙura ta gama samun lafiya ta taho. Ɗakinta na ɓangaren ma'aikata taje ta fara ajiye kayanta sannan ta shiga cikin gidan. Tauhidat tana makaranta haka su Kulsum. Tunda bata da shamaki kai tsaye ta shiga falon Haj. Manga wadda take ta safa da marwa tana jiran shigowarta. Yanayin fuskarta kaɗai ya ishi Madam Zainaba sanin cewa babu lafiya. Jikinta a sanyaye ta daure ta ƙarasa ciki sannan ta gaisheta. Auna ƙarfin hali irin na Madam Zainaba ta yi kafin ta sake haɗe rai bayan ta zauna tana fuskantarta sosai. "Zainaba wace irin zuciya ce a ƙirjinki da ta baki damar iya daurewa ganin hawayena tsayin shekarun nan amma baki taɓa tausaya min ba? Wace riba ki ka tsinta a sakamakon cin amanata?" Bata gane kan maganar ba amma ta tabbatar cewa ran Haj. Manga ya ɓaci da ko ma mene ne. "Hajiya me na yi?" Madam Zainaba ta tambaya a tsorace. Haj. Manga tana son sanar da ita cewa haƙansu bai cimma ruwa ba amma tana tsoron abinda zai faru "ba zan ja magana dake ba ki kwashe kayanki kafin gari ya soma duhu ki koma wurin waɗanda ki ke yi wa aikin. Ki faɗa musu cewa Allah ba azzalumin Sarki bane inji ni." Tashin hankalin Madam Zainaba ba zai faɗu ba. Haƙuri take son badawa amma babu ƙofa, domin irin maganganu masu zafi da take faɗa mata sun tsaya mata a zuci. Bata rabe ɗayan biyu, shiga tsakaninsu aka yi. Ta riga ta san halin Haj. Manga tunda take ganin kamar taci amanarta ne to fa sai ta yi da gaske za ta fidda kanta. Zaman shekara goma shaɗaya cikin rabin awa ya ƙare tsakaninsu. Haj. Manga ta yi fushi sosai, babu kuma laifinta domin ko waye zai yi haka ko ma fiye. Arƙam da ya kama sunan Madam Zainaba ɗin shi ma abinda ya sani ya faɗa ga Tony ya bar ƙasar. Alh. Audi kansa ya gaji da nemansa ya ɗauki wani da Oga ya haɗasu ya maye gurbinsa. Duk yadda ta roƙeta akan ta bari ta kwana abu yaci tura. Yadda ta shigo haka ta fita, ita ɗaya sai guzurin barazanar hawan jini bayan diabetes ɗin da take fama dashi. Tasha ta wuce kai tsaye don ba ta da wani wurin zuwa a garin kuma. *** Yanzu da Mammalo ake kai Tauhidat makaranta a ɗaukota. Bayan dawowarsu daga Kano ta yi ƙoƙorin cire damuwar maganar da taji daga ranta. Duk wanda taso faɗawa ta kasa, sai ya zamana ta sake saka ido sosai wurin ganin tana kula da Nanna yadda ya dace. Iya mafitar da wayonta ya hasko mata kenan tunda abin yafi ƙarfin tunaninta. A yau suke shirin tarbar Shaheed. Haj. Manga ta tada hankalin masu aiki, sai ka rantse ɗan cikinta ne a hanya. Ba ta gajiya da cewa tana son zuri'ar Abayomi domin mutane ne na ƙwarai. Tana yawan jinsa yana yi wa Jamal faɗa akan shaye-shaye da rashin mayar da hankali akan karatu. Abinci da snacks kala-kala tasa aka yi sannan aka gyara masa wani ɗakin don ta ce zamansa da mahaifinsa takura ne garesu. Shiri sosai ta yi ta tura direban gidan ɗauko shi daga airport tare da Tauhidat da Mammalo. Papa Abayomi ta umarta da ya zauna a gida ya tarbi ɗansa. Idan yaje da kansa tamkar yaje a bakin aiki ne kuma ba za ta so hakan ba. An jere duka kayan abincin a ɗakinsa, komai na mutum uku ta tsara wato su da babansu. Lokaci ne da zasu keɓe na taya juna farinciki. Da gudu Tauhidat ta isa gareshi, ta rungume shi tana murna. Shi ma ya rasa inda zai sa kansa don farinciki. Da yarbanci ya ce "Tosin kece kuwa? Yaushe ki ka girma haka kin zama ƴan mata." Kunya ya bata ta sunne kai a ƙirjinsa "Brother kaima ka yi kyau sosai kamar ba kai ba." "Ina Papa?" "Yana gida yana jiranka. Mammalo an ga ɗan ƙasar waje, jiki na rawa ya dinga kinkimar akwatunansa yana sakawa a boot. "Wannan fa? Ban san fuskarsa ba." Shaheed ya tambayeta. "Mammaloncy kenan" ta amsa da murmushi. Jin an ambaci sunansa ya taho da sauri "Allah e sa yayan naki iya jin hausa. Kin tuna na faɗa miki iyakata firamare ba wani nisa na yi ba a turanci." Zancen kenan iyakarsa firamare. Daga ita har Shaheed dariya ya basu. Hannu Shaheed ɗin ya miƙa masa zasu gaisa idanunsa suka sauka akan wasu maza biyar ƴan ƙasar China. A iska ya barwa Shaheed hannunsa ya juya kallon ikon Allah. Yarfe hannuwa kawai yake yi yana ɗaga kafafu ya dire kafin ya sandare a wurin. Direban da ya kawosu dama ba hausa yake ji ba amma yanayin da ya ganshi ya bashi tsoro. Tauhidat da Shaheed ma sun zata wani abu ne ya same shi. Kaɗafarsa Shaheed ya ɗan doka ya kuwa saki ihun murna yana jijjiga Shaheed ɗin da ƙarfinsa. "Wohohooo, eh na yarda inda rai da rabo. Ƴar gidan Nanna duba min ki gani Brut Li nake hangowa ko gizo yake min?" Sai da ta toshe bakinta don dariya shi kuwa sai cewa yake "aka ce mana ya mutu ahe duk ƙarya ne Yasin." Cikin sauran mazan akwai wanda yafi gajarta ya nuno shi da hannu harda ɗan hawayensa na farinciki "kinga ga ƙaninsa can Jenti Li, na san cikin waɗancan da suka bada baya ba'a rasa Jaki Chan." Shaheed dariya, Tauhidat dariya aka rasa mai gyara masa a cikinsu. Mammalo daɗin ya masa yawa ya kasa haƙuri su dai sai hango shi suka yi a gaban mutanen nan. Irin gaisuwar da akan yi a finafinan China, na zamanin da za ka ga mai koya faɗa da ɗalibansa suna bashi girma haka ya yi musu. Kansa a ƙasa ya dunƙule hannu ɗaya, ya saka cikin ɗan uwansa ya ce musu. "Shan kwenkwen chizo fa." "Kut...Brother ku sameni a mota, ba za ayi wannan abin kunyar dani ba." Inji Tauhidat ta ruga ta shige mota tana dariya sosai. Ta tabbata cigaba da tsayuwarta tana kallonsa zai iya sawa a ɗauko musu ƴan sanda saboda dariyar da take yi. Mutanen birnin Sin sai suka hau yare suna tambayar juna ma'anar abinda yake cewa. Shi kuma sai ya zata amsa masa suke yi ya hau gyaɗa kai, "yes yes shanwe shanwa." Shaheed ya daure ya yi ta maza ya matsa gabansu, ya basu haƙuri da turanci. Sun amsa masa a sake ya nuna musu Mammalo mai son finafinan ƙasarsu ne shi ya sa. Ransa ne ya soma ɓaci da ya ga kamar ƙwacensu Shaheed zai yi masa ya ɓata rai "Me ku ke cewa? Ka barmu mu masu jin yaren muyi a junanmu ba sai kunyi turancin ba." "Muje mota sun ce zasu kira security ne a tafi da kai wai ka dame su." A guje ya bar wajen kafin Shaheed ya gama magana ya shige motar. Suna tafe a hanya ana maida zance da dariya Arƙam ya kira Tauhidat. Dama ta faɗa masa zasu je ɗauko yayanta yau. Kunyar ɗauka taji kada Shaheed ya ce meye tsakaninsu. Sai kuma ta tuna ita kaɗai ta san ko waye shi bisa amanar Nanna. Ya kuma kira sau biyu tana tonawa kanta asiri ta hanyar kallon wayar da ta kashewa fitar sautin kara. Kamar daga sama ta tsinci muryar Shaheed, ya matso kusa da ita "indai ni ki ke jin kunya ki ɗauki wayarki amma fa sai kin faɗa min ko waye idan na huta." "Ba fa abinda ka ke tunani bane" ta furta maganar tana tura masa baki. Ya yi murmushi "to ɗauki ki bani mu gaisa. Kinsan dole a kama ƙafa dani." Sai kuma ya kawar da zancen ganin da gaske kunyar ɗauka take ji. "Wai ina amininki ne Jamal?" Kafin ta bashi amsa da cewa yana makaranta, Mammalo ya juyo daga gaba yana rarraba idanu tsakaninsu. "Nace ba, ko za ku yi firar da hausa yadda zan iya tofa albarkacin bakina nima? Da shike ina yawan faɗa ban yi nisa a boko ba. Iyakata firamare da munyi da turanci ko don mai tuƙa motar nan." Ya ɗan kanne ido, "kunsan ba daɗi na kama sunansa bai san me nake cewa ba." Shaheed ya fi kowa dariyar shirmen Mammalo. Hirar ƴan China ya sako musu motar ta kaure da dariya kuwa. Alamun shigar saƙo Tauhidat ta gani a wayarta ta duba. Murmushin da ta yi ne ya ƙara ƙarfin zargin da ɗan uwanta ya ke yi, na cewa ko waye yana da babban matsayi a wajenta. Saƙon text ne daga Arƙam da harshen turanci kamar haka. (Hey Cuddles, yau na yi kewarki. Ki kirani idan kun isa gida. Nanna ta ce baku dawo daga airport ba. Ina gaishe da Brother Shaheed kuma ina fata ni ma idan na dawo dake za a zo ɗaukata?) Kalamansa sun yi nasarar kashe mata jiki, ta yadda ta kasa rubuta masa amsa sai juya su da take yi a cikin zuciyarta. Sabonsu da Arƙam yana bata tsoro, saboda yanzu kusan komai na juna sun sani. Da wuya su kwana uku basu ji muryar juna ba. Tun yana hirar tana bashi amsar kurame har ta sake ta fito masa a Tauhidat ɗinta sak. Yarinya mai surutu da yawan abin dariya. Tuni ya waye da halinta na rashin saurin fushi da yawaita uzuri. Ya ɗokantu da haɗuwa da ita domin yadda suka shiga rayuwar juna yanzu shi kan sa ya san rabuwarsu ba abu bane mai sauƙi. Nanna idon manya ta saka musu suna bidirinsu tana addu'a a gefe. Fatanta yadda suke yanzu kada ya kama ƙafar yadda zasu kasance duk ranar da suka ɗora ido akan juna. Wani saƙon ya sake turowa wanda yasa ta bashi amsar dole. (Ina fata dawowar Brother Shaheed ba za ta shafi Karam1 ba?) Baya saka suna saboda gudun ɓacin rana kada wayar ta faɗa hannun da ba nata ba. (Ƙanwar Jamal, Tosin ɗin Shaheed, Tauhidat ɗin Nanna, Cuddles ɗin Doctor. A ciki babu wanda ya taba ta kowa.) Amsarta har ya kwanta a ranar ita zuciyarsa take karantawa. Cuddles ɗin Doctor. How he can't wait to cuddle her! *** Bayan fitarsu daga gida Alh. Audi ya kira matansa ɗakinsa. Babu wadda ta san me yake ƙullawa tun jiya. Sun dai ga yana yawan waya da wani daga office ɗinsu wanda ya baiwa ragamar ganin kammaluwar shirin da ya yi wa yau ɗin. Dama yana ta addu'ar kada Haj. Manga ta yi shigen abinda ya yi niyya domin hakan zai ɓata masa wasa sai gashi kuwa ko kusa bai ga alama ba. Yau zai ƙara kusanto da iyalin Abayomi gareshi domin ya samu kan Tauhidat cikin sauƙi. Yana da yaƙini kan talaka da zuri'arsa babu abinda za ka yaƙe su dashi cikin sauƙi kamar kuɗi da kuma jansu a jiki. Ita ma Haj. Mangan ya fahimci kuɗinta ne ya ɗauresu gareta. Kaya ne a leda ya miƙa musu. A ledar Fanna guda uku ne, ɗaya nata wani irin lace da bata taɓa gani ba a ɗinke sai na yaranta iri ɗaya shi ma mai matuƙar kyau. Iri ɗaya ne da na Haj. Manga da ta buɗe nata sannan kayan Tauhidat babu bambanci da na su Kulsum sai a mayafi da jaka da takalmi. A take tasha jinin jikinta da cewa akwai abinda zai biyu baya mara daɗi. Alh. Audi bai bata kunya ba kuwa. Wani shegen murmushin ya yi kawai saboda jindaɗin yanayin da ya gani a fuskarta na fargabar me zai biyo baya. Sai da Papa Abayomi ya shigo ya miƙa masa tasa ledar sannan ya faɗa musu shirin nasa. "Duk wani mazaunin gidan nan ba zai rasa jin labarin babban ɗan Hafsatu ba da na kai karatu UK ba." Ya ja gwauron numfashi kansa na yawo hagu da dama irin na masu alhini "to yaro dai tamkar ɓatan allura an neme shi an rasa ba amo ba labari. Saboda haka na kasa cewa zan kai Jamal. Idan na yi haka ma sai duniya ta zargeni da raba uwa da ƴaƴanta." Fanna ta gyaɗa kai "Wannan gaskiya ne Alhaji. Ta wannan fannin ni kaina ina jinjinawa Hajiya. To amma Shamsu kuma fa?" Ƙarya ya yanko musu Haj. Manga tana kallonsa, ko kunya babu ya ce wai ba lafiya ce ta ishe shi ba. Fanna da bata shiru ta ware murya tana tambayar cutar da take damun Shamsun suna matsayin matansa basu da labari. Da yake ɗan duniya ne sai ya bagarar da zancen. "Yanzu ba maganarsu ake yi ba. Shaheed ya dawo cikin ikon Allah da sakamako mai kyau. Domin taya mahaifinsa farinciki Hajiya sai kiyi haƙuri na muku karambani. Surprise party na shirya masa da ƙarfe bakwai na dare." Yadda yake maganar duk mai hankali ya san ba da zuciya ɗaya bane. Sai nanatawa yake ai ɗa na kowa ne. Wannan magana ya yi ta lugwigwitawa kamar mangwaro a hannun yara, har zuwa lokacin da ya ji muryar Shaheed da Tauhidat suna sallama. Daga nan ga mamakin duka mazauna falon sai cewa ya yi, "Abayomi na sani sarai tamkar bawa kake ga Hajiya sai abinda ta ce. Amma ka sani ba zaman kanta take yi ba. Saboda haka na gama magana kowa ya shirya ana sallah za mu wuce venue ɗin." Fuskokin ƴaƴan mutumin da aka kira bawanta domin cin zarafi ta fara kallo, kafin ita da su duka su raka Alh. Audi da idanu. Jikinta ya yi mata nauyi da sanyi ganin irin kallon da Shaheed yake mata. Wane ɗa ne zai so a kira mahaifinsa bawa a zamanin da babu bauta? Ledar kayan da ya bata ta ɗauka ta yi sama batare da ta tankawa kowa ba. Tauhidat na ganin haka tabi bayanta da sauri. Fanna ma dai a saɓule ta tashi tana kawo tunani barkatai a ƙwaƙwalwarta da zai sa maigidan nasu wannan furuci a gaɓar da bata dace ba. Papa Abayomi da aka yi domin a nunawa ƴaƴansa cewa shi ɗin wulaƙantacce ne a gaban uwarɗakinsa, bai tsaya ba ya kama hannun Shaheed suka fita zuwa ɓangarensu. Muryarsa a kausashe saboda ya ga irin kallon da ɗan nasa ya yiwa Haj. Manga ya soma magana da yarbanci.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull