Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 11
Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 11: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 11. "Aderemi Shaheed Abayomi waye ya kawoka gidannan?" Ɗan jim ya yi kafin…
6,055 words
"Aderemi Shaheed Abayomi waye ya kawoka gidannan?" Ɗan jim ya yi kafin ya ce, "Nanna ce." "Yauwa na ji daɗi da baka manta ba. Ina so ka riƙe a ranka cewa kuɗi ko wani ƙyale-ƙyale da wani zai nuna maka kada ya canja maka tunani a kanta. Mace ce mai matuƙar kirki da hangen nesa. Ban san meye tsakaninta da mijinta ba amma ban yarda ka canja mu'amalarka da ita ba akan abinda kaji ɗazu kana jina?" Sakin fuska ya yi domin kwantarwa da mahaifinsa hankali duk da wasi-wasin da yake masa kai kawo a zuci ya ce, "Na ji Papa kuma zan kiyaye." Murmushi Abayomi ya yi shi ma ya rungume ɗansa, yana mai farinciki da dawowarsa. Tarin kayan abincin da ta aiko musu ya nuna masa da kuma kuɗi dubu ɗari wanda ta ce su tafi Abeokuta cikin dangi ayi walimar gama karatunsa lafiya. A ranar da ta bashi kuɗin tana ta nanata masa kada a wuce sati da Tauhidat tunda an koma makaranta. Dan abinda Shaheed ya riƙe a ransa sai ya nema ya rasa. Ba wai kuɗin bane ya sauya masa ra'ayi, ko kusa, mutuntawa ga mahaifinsa ya fiye masa komai. Haj. Manga kuwa ɗaki ta shiga ta kwanta, zuciyarta tana tafarfasa. A yanzu da ta ga Arƙam shi ne daidai lokacin da ya kamata ta nemi Alh. Audi ya sahale mata wannan aure da suna kawai ya tara. Ya rabata da Madam Zainaba bata fatan ya yi nasara akan su Tauhidat. Tana cikin tunanin bata ji shigowarta ba sai kwanciya da ta yi a bayanta ta saƙala hannu ta rungumota yadda take yi da ƙuruciya. Tana ji lokacin da ta kama hannuwan ta riƙe sosai a cikin nata masu ɗumi. Cikin ƙanƙanuwar murya ta ce, "Nanna kada ki yi kuka. Idan ki ka yi kuka za a gane, idan aka gane kuma anyi nasara a kanki." Da sauri Haj. Manga ta tashi zaune ta tambayeta dalilin faɗin haka. "Saboda bana so kowa ya raina min uwa." Ita ce amsar da Tauhidat ta bata Rungume juna kawai suka yi, wani abin ba sai an fada ba. Allah ne Ya amintar da zukatansu suka zama wani bangare mai mahimmanci ga juna. *** Taro ya kasance fiye da zato da tsammaninsu. Alh. Audi amfani ya yi da dawowar Shaheed wurin ɗaga martabarsa a idanun al'umma. Ya aikawa ƴan uwan Abayomi da na matarsa ashe kwanansu ɗaya su goma sha uku a guest house ɗinsa bai sanar da kowa ba. Su ma kuma ya nuna musu ba ya son Abayomi ya sani ne saboda haka suka yi shiru. Wannan kirki nasa da suka gani yasa suka ɗaukake shi da girman daraja. Ga abokansa da Alh. Ari wanda ya bayar da shawarar yin wannan taro. Yadda ya ɗinkawa kowa leshi domin dacewa da taron yarbawa shi ma haka ya saka nasa da babbar riga da hular kayan ya karkata. Gefe ɗaya kuma ga ƴan jaridar da Alh. Ari ya ɗebo ana ta ɗaukar hotuna da video an yiwa taron laƙabi da Karamcin Karam. Mutane suna ganin wane mai arziƙin ne zai yiwa ɗan direban matarsa abu irin wannan. Don gwaninta ya haɗa ƴaƴansa da na direba ya yi musu kaya iri ɗaya don ya nunawa duniya cewa babu bambanci tsakaninsu. Sun dai bi yarima sun sha kiɗa ko ba komai zuwan kawunnai da gwaggwanninsu ya faranta zuƙatansu. Haj. Manga sai ta shige cikin taron ta saki ranta sosai, abinda ya tunzura zuciyar Baba Audi. A can gefe Shamsu ya tsaya yana mai takaicin haɗa shi da wannan taron matsiyatan kamar yadda ya karantawa zuciyarsa. Da gayya Alh. Ari ke tambayar Alh. Audi wai ina Jamal shi kuma ya wani karkata kai yana cewa ayi sha'ani kawai. Waɗanda suka san mashayi ne ɗan ƙwaya suka dasa faifansa ana ta bawa ƴan rahoto kanun labarai a fakaice. Bayan taron ya watse sai su da ƴan uwansu Haj. Manga ta zauna cikinsu ana ta hira da raha. Alh. Audi bai daddara ba ya taho inda suke Fanna tana mara masa baya. Bayerabe akwai girmama mai kyautata masa. Nan fa suka shiga yi masa godiya da fatan alkhairi akan ɗawainiya da ɗansu. Ya murmusa yana duban Abayomi, "Duka yi wa kai ne saboda mun riga mun zama ɗaya. Na so Hajjin bana ma ayi da kai to amma sai na tuna yadda uwarɗakin naka ta ɓata rai lokacin da na ce zan tura Shaheed Turkey karatu." Ba ɓata lokaci wurin ya kaure da ƙananun maganganu. Masu jin turancin cikinsu suna fassarawa sauran. Idanu suka yi caaa akan Haj. Manga. Tauhidat ta kalla wadda ta ɗage mata gira irin na muna da namu makamin, ta saki murmushi sannan ta ce, "Alhaji mungode sosai amma kada ka damu. Maganar Hajji in sha Allahu ana fara ɗiban Alhazai za ka ji sunan Alhaji Abayomi." Fanna bata iya ɓoye farincikinta na ganin wannan karon bai sami damar tozarta kishiyarta ba. Ba wai zaman dadi suke yi ba, amma ta gama gane cewa akwai ta inda Alhajin nasu yake tauye Haj. Manga wanda shi ne dalilin shigowarta gidan. Sauran mutanen hadda Shaheed aka shiga yi mata addu'a suna yaba kyautatawarta garesu. Ƙwafa Alh. Audi ya yi a zuci ya bar wurin da murmushin yaƙe. Yana isa gaban motarsa Haj. Manga tana isowa. Kallonsa take ido cikin ido. "Ina roƙon Allah Yasa ba takalmin kaza ne tsakanina da kai ba, domin na ji daɗin rangaɗa guɗa ranar da za ka ciji yatsa." A fusace ya ce, "me kike nufi?" "Ina nufin Allah Yana sane dani da ƴaƴana a duk inda suke. Mahaifinsu har ya koma ga Allah bai da abokin adawa balle ace ya cutar da wani. Nayi imani cewa da izinin Allah zuri'ar Ibrahim ba za ta wulaƙanta ba duniya da lahira." *** A kwana a tashi rayuwa tana jujjuyawa da ɗan Adam. Yau fari gobe tsumma haka maikuɗi da talaka suke tashi. Papa Abayomi yaje Hajji tare da wasu cikin ƴan uwansa da suka tashi a wannan shekarar. Ta garinsu ta biya masa dama saboda tafiya irin wannan tafi daɗi da idon sani. A cikin lokacin kamar yadda ta alƙawartawa Arƙam bayan wata biyu da ƴan kwanaki suka haɗu a England saboda kada Alh. Audi ya zargi komai. Hutu kawai ta ce masa za ta ya ce Allah Ya kiyaye hanya. Zaman nasu ya ƙara muni ya kuma dage akan ba zai saketa ba. Sai ta rabu dashi ta tattara hankalinta wurin aikin makarantar da za a soma gini. Tafiyar Dada umara domin haɗuwa da jikanta bata yi wu ba, saboda jikin tsufa tana ta rashin lafiya. Haƙura suka yi sai lokacin azumi sannan ta je. Amma yana yawan kiranta su gaisa. A haka Tauhidat ta kammala jarabawar SSCE suka sha murnarsu ita da Nanna. Alƙawarin umara ta yi mata batare da ta faɗa mata Arƙam zai je ba idan ta yi ƙoƙari. Shi ma kuma bata faɗa masa ba, saboda sanin halinsa zai dameta ne ya kuma hana Tauhidat sakat. Yanzun ma sai da ta karɓe wayarta da tana jarabawar. Sai ya ce kira ya yi ya mata fatan alkhairi amma sai an shafe minti goma ko sama da haka ana kus-kus. Nanna kanta rasa me suke cewa take yi. Jamal tara shi kawai yake wai ya musu farraƙu shi da ƙanwarsa. A can Kano aka sami guda cikin jikokin Dada ya je da dvd ɗin waƙar Arƙam gidansu. Mahaifiyarsa Anti Nana da ta kasance ita ce babba a cikin ƙannen Ibrahim tana ganin kwalin ta gane shi. Hankali a tashe ta kaiwa Dada tana zagin Haj. Manga. A dole ranar Dada ta feɗewa ƴaƴanta biri har wutsiya. Babu wanda baiyi Allah wadai da Alh. Audi ba. Suka taru wurin riƙe amanar ɗan uwansu. Biyu a ciki zasu bi Dada zuwa umarar da za ta je domin haɗuwa dashi. Gidan Baffa ma zasu je da Umma matarsa da duka ƴaƴsn nasu. Sun san halinsa, ya ja musu kunne sosai akan riƙon sirrin ƴar uwarsu. Hakama Dada, sun mata alƙawarin kame bakinsu tare da duƙufa wajen yin addu'ar kariya gareshi. Rana bata ƙarya ance sai dai uwar ɗiya taji kunya. Ranar da aka kai azumi takwas Arƙam ya tashi daga Baltimore zuwa ƙasa mai tsarki. Kwanansa ɗaya da sauka, saboda nisan tafiya a hanya ya kusa kai azumi na tara sannan su Haj. Manga suka taso a ranar da aka ɗauki na goma. Ita da Jamal da Tauhidat da iyalan Baffa sun tashi ta Abuja. Su Dada kuma daga Kano amma duka rana ɗaya. Alh. Audi yaso zuwa umara a shekarar, amma ƙyashin haɗuwa da zai dinga yi da Baffa Alƙali yasa shi fasawa. Fanna da ta ɗora rigimar son a barta taje da yaranta yasa babanta ya sille masa ita. Wai sun kula Haj. Manga ta wanke ta bata ta sha. To koma dai mene ne su kam abin ya tafi musu a daidai. Zasu tafi cikin kwanciyar hankali. Murna da ɗoki a wurin Tauhidat ba a cewa komai za ta ga dakin Allah. Ta sake zama ƴan mata kyawunta mai fisgar hankali ya kuma bayyana. Sirrukan gyaran jiki tun tana ƙwailarta Nanna take koyar da ita saboda Kanuri sun yarda da gyara sosai. Zaman awa biyu suka yi a airport ɗin Jidda har jirginsu Dada ya sauka sannan suka ɗunguma zuga guda zuwa Madinatul Munawwara. Madina garin Manzo SAW. Gabanin asuba suka isa Coral Al-Madina Hotel inda Arƙam ya yi masauki shi ma. Babu nisa sosai tsakaninsa da Harami (masallacin Annabi SAW). Babban hotel ne mai tsada yaci karo da mutanen da kuɗi ba matsalarsu bane. Kawu Safiyanu shi ne ɗan Dada na uku kuma tare aka zo dashi da Anti Nana. Bai yarda ya shiga aljihun Baffa ko Haj. Manga ba ya kama musu ɗakuna biyu. Ɗaya Dada da Anti Nana sai nasa. Baffa kuma ya kama biyar. Shi da Umma, Haj. Manga da Tauhidat, Jamal tare da baffaninsa a sauran ukun. Sallah suka fara yi sannan aka yi wanka tunda sunyi sahur a hanya. Maimakon bin lafiyar gado haƙarƙari ya huta sai suka ɗunguma zuwa ɗakin Baffa gabaɗayansu banda Tauhidat. Ita dai Nanna ta ce mata za ta je wurinsu Baffa ta yi kwanciyarta sai la'asar zasu je masallaci. Ko motsin kirki bata iyawa saboda gajiya ta kwanta bacci mai nauyi ya ɗauketa. Kowa na zaune Baffa ya kira Arƙam da lambar wayarsa da ya bashi tun ranar da ya iso. Bai daɗe da dawowa daga masallaci ba lokacin. Ya san ranar zasu iso amma bai san da sassafe ba, kuma bai san adadinsu ba. Yana ganin wayar gabansa ya faɗi, ya riga ya san ko waye. Jikinsa na rawa yau zai ga ƴan uwa ya fito daga ɗakin zuwa hawa biyu saman nasa inda Baffa ya faɗa masa ɗakinsa yake. A bude ya tarar da ƙofar suna tsatstsaye gabaɗayansu, sallamarsa ta ratsa kunnuwansu. Dada ya fara nema da ido ya yi sa'ar ganinta a kusa da Umman Baffa. Allah Ya sani zuciyarsa ta karye fiye da yadda zai iya jurewa. Hawayen tsufaffin nan ya ishi Alh. Audi haƙƙi. Haka suka sa Arƙam a tsakiya ana kukan farinciki. Anti Nana da kawunansa babu sunan wanda ya kuskure. Sun ƙara girma akan sanin da ya yi musu kafin ya tafi. Su ma suna mamakin tsayinsa. Ya cika ɗan Haj. Manga duk inda ya gilma ya fi kowa tsayi. Neman gajiya kowa ya yi ya rasa saboda farinciki. Ba su suka tashi ba sai da aka soma kiran azahar. Mazan suka ɗunguma zuwa Harami, matan suka yi sallolinsu a ɗakunansu. Suna dawowa Jamal ya gudu ɗakin Arƙam. Basu ɗauki lokaci ba kuwa sai bacci. Uku da kwata Tauhidat ta farka, ta faɗa wanka a gaggauce saboda sallar azahar da ta kufce mata. Tana idarwa suka fara shirin tafiya harami saboda samun la'asar. Don ɗoki ta hana Nanna sukuni. Ta dameta sai da ta shirya lokacin uku da arba'in. Ƙaramin akwatinta da ta saka hijabai da laffaya ta nema ta rasa ashe yana wurin Jamal, saboda shi ya ɗauko mata. Arƙam ta kira tunda ta san suna tare ya bashi ta faɗa masa ya ɗauko mata sannan su shirya su ma su wuce tare. Tauhidat da ta gaji da jiran ta ce ita za ta je ƙofar ɗakin da yake ta ƙwanƙwasa ya bata. Ita so take hatta kiran sallah ayi tana wurin. Haj. Manga bata hanata zuwa ba, tunda ta san kafin ta isa ɗakin ma ƙila ya ɗauko. Yadda take rawar jikin nan duk abinda zai hanasu fita da wuri zai iya sa ta kuka. Fuskarta babu wata kwalliya sama da hoda da ƙwalli amma ta yi fes da ita. Riga da skirt ne a jikinta na atampa da suka fiddo da yanayin jikinta. Ta ɗaura ɗankwalin sannan ta saka hijab mai hannu da ya zarta gwiwarta kaɗan ruwan ƙasa na wani irin yadi mai kyau mara nauyi. A sama take jin kanta yau gata a Madina. Ta fita ɗauke da murmushin nan nata Haj. Manga tana girgiza kai ita ma tana tayata. Arqam ne ya tafi dauko akwatin saboda Jamal lokacin yake shiryawa. Shirt mai gajeren hannu ce a jikinsa army green ya bar maballai biyun sama a bude ta yadda ake ganin ta ciki light green. Ya karbo akwatin yana bin lambobin sauran ɗakunan da kallo kada ya wuce na Nanna. Ita kuma Tauhidat ta karyo kwana daga bangaren dakin nasu za ta je inda a saninta nan Jamal yake. Duk tsirarun mutane masu wucewa ta wurin hankulansu gabadaya suna kan abinda ke gabansu. Kanta a kasa yake har lokacin da taji wani mayataccen kamshin turare mai dadi. Daurewa ta yi bata kalli mai fitar da ƙamshin ba lokacin da suka gilma juna. Arqam da bai da dabi'ar kallo sau daya ya kalleta ya dauke kansa. Sai dai yana dauke idanun ya dawo dasu da sauri ya bi bayanta zuciyarsa na wani irin bugu. Bata ankara ba ta ga mutum a gabanta. Dago dara-daran idanuwanta ta yi suka sauka a cikin nasa. A hankali, cikin nutsuwa, kamar yana tsoron yin kuskure ya ce, "Cuddles?" Yadda idanunta suka ƙara girma akan idonsa, da hannun da ta ɗora akan bakinta don kada ta yi ihun mamaki da murna ne suka tabbatar masa da cewa ita ɗin ce. "Kece da gaske? My God, I can't believe Nanna" Wannan karon da ƙwarin gwiwarsa ya faɗa. Fuskarsa na fitar da annurin farincikin da yake lulluɓe a zuciyarsa. Ita dai tunda ta ƙare masa kallo sau ɗaya, ta haɗiyi wani yawu bata san lokacin da ta juya da sauri ta bar wurin ba. Yanzu wannan mutumin ne Arƙam ɗin da take waya dashi? Rashin sanin yadda za ta kwatanta haibarsa da cikar zatti ya sa taji ƙafafunta sun gagara ɗaukarta. A wurin ya bar akwatin Nanna yabi bayanta da sauri yana kiranta. Kafin ya taddota ta buɗe ƙofar da gudu ta shige bayan Nanna dake zaune akan kujerar ɓangaren da yake kamar falo a ɗakin ta ɓuya. "Ke lafiyarki?" Ta tambayeta ganin tana faman cukwikuyeta. Ɗago kai ta yi ta kafaɗarta tana mayar da numfashi da sauri, "Nanna na ganshi?" "Shi wa?" Ta yi kamar bata gane ba. Daga bakin ƙofar ɗakin taji muryarsa, "Arƙam, kuma ta gudu." Sake ɓuyewa ta yi. Haj. Manga tana dariya za ta tashi taji ta riƙeta da kyau. "Yanzu banda abinki Tauhida meye abin gudu? Mutumin da ku ke cika mana kunne da surutunku a waya ki ke ɓoyewa?" Da ƙyar ta iya sauko da ƙafafunta kasa, amma taƙi dago kai ta kalle shi, "kunya naji ne wallahi." 'Kamar kin ga suruki? Ni ina akwatin ko babu wanda ya ɗauko cikinku?" Sai lokacin Arƙam ya sake yin magana. Sauraron muryar Tauhidat daga kurkusa haka kuma yana kallonta ya ɗauke masa hankali. "Shit" ya furta a hankali yana juyawa "Cud..." Kafin ya ƙarasa ta ɗago da sauri ta danna masa wata harara. Ko ita dashi a waya kunyar sunan take yi balle a gaban mahaifiyarsa. Murmushi ya yi mai sauti, "ba kya so Nanna ta ji? To taso muje ki tayani neman akwatin." Tafa hannuwa kawai Haj. Manga take yi tana cewa da alama dai sai sun rasa sallah. A ƙasan zuciyarta kuwa kamar sallar Idi. Fita suka yi hannuwan Tauhidat duka biyun ta rufe fuska dasu tana murmushi. "Ki cire na ganki don Allah." Hannu ɗaya ta cire ya zuba mata idanu an rasa mai magana a cikinsu suka ji muryar Jamal. Akwatin da suka fito nema ne a hannunsa ya rike haba da hannu ɗaya. "A watan azumi da rana tsaka me nake gani ni Jamalu?" Har lokacin idon Arƙam na kan ta ya ce masa, "ka gani kunyata take ji." "Ba dole ba, wannan kallo da ka tsareta dashi sai kace budurwarka." "Wai haka?" Wayam ya gani tuni ta karɓe akwatin ta gudu. Su huɗu suka tafi masallacin. Dada da Umma sun ce sai washegari. Anti Nana kuma dole ta zauna saboda taimakawa Dadan. Mazan ne dai sun jima da tafiya su ma sai taxi suka nema gudun lattin. Karatu suka zauna yi bayan an idar da sallah. Tun a nan Tauhidat take ta kwararawa mahaifiyarta, Papa da Nanna addu'o'i. Ba su suka bar masallacin ba sai da aka idar da sallar magrib suka sha ruwa a masallacin. Daga nan suka fito zuwa hotel ɗinsu domin su ci abinci su koma lokacin isha da taraweeh. Ita da Nanna ɗakinsu suka wuce jiran Arƙam da Jamal su karɓo musu abinci a wani restaurant da yake gefen hotel ɗin. Snacks da abinci da abin sha suka siyo. Komai an jera a tsakiyar falon suka zauna zagaye kowa yaja nasa abincin. Tauhidat ta takure ta kasa ci saboda Arƙam ba dai takura ba. Kai tsaya yake abubuwa abinsa. Ya raba kazarsa biyu ya ɗora mata a plate ɗinta, yazo ya tura mata samosa da doughnut. Gajiya ya yi da ganin yadda take tsakura kamar bata so yace, "Abincin babu daɗi ne? Na siyo miki wani?" "La'ilaha illahu! Ta ina za ta ci abincin har ta gane ko da daɗi ka dameta. Ni ku tashi ku koma ɗakinku. Ina dalili ku zo har makwancinta ku hanata sakewa." "Aahh Nanna ki ware mai laifi shi kaɗai banda jama'u." Cewar Jamal ya cika baki da shinkafa. Kan Arqam ne ya ɗaure don bai ga ta inda ya kuskure ba ya marairaice fuska, "me nayi? Cu..." "Ya isa zan ci, zan ci" Tauhidat ta cika cokali ta danna a bakinta. Haj. Manga da Jamal suka fara cewa sai an faɗa musu me ake ɓoyewa. Ita dai abinci take turawa babu bakin magana. Su uku suka tashi Haj. Manga ta ce su je ɗakinsu Dada yi musu barka da shan ruwa. Idan ta gama cin abincin ta same su can sai su koma masallaci. Jamal ya ce ta taho da jaka sai ta sako sauran snacks ɗin zai ci idan yaji yunwa kafin su dawo. A can suka samu Umma ita ma tare dasu tasha ruwa. Sun zauna ana taɓa hira Arƙam ya miƙe. "Dawo ka zauna" Haj. Manga ta ce fuska babu alamun wasa. Ta san inda zai je ko bai faɗa ba. Anti Nana ce ta bata amsa da cewa, "Ki ka san uzurinsa za ki hana shi fita kamar wani yaro. Babban likita tashi abinka ka ji." Ya miƙe kuwa kafin ma a kuma dawo da shi ya yi waje yana jiyo dariyar shaƙiyancin Jamal. A bakin ƙofar ɗakin ya tsaya, ta waje ya jingina bayansa da bango yana jiran fitowar Tauhidat. Ya kusa minti shabiyar kafin ya ji ta buɗe cikin nutsuwa ta fito. Ji ta yi kamar ta koma da suka haɗa ido ya rigata sake kulle ƙofar yana murza ɗan mukullin. "Meye haka ne Cuddles duk kin takura min?" "Ni ce ma na takura maka?" Ta ce tana dariyar hausarsa da kullum take a bauɗe. "Eh mana. Ko magana kin kasa yi min." Yadda ta juya bakinta ya shagaltar da shi, wajen kallo tana magana yana lumshe idanu. "Haka ne takura?" Tafiya suka soma gefe da gefe ya karɓe abin sallar da ta ɗebo musu ita da Nanna guda biyu. Ya rataya a hannunsa, "To me zan ce? Kin takura kanki saboda kin ganni kamar ba ki yi murna ba." Sai da ta shagwaɓe fuska ba tare da niyya ba ta bashi amsa da cewa, "Allah na yi." "Ban ga alama ba. Nafi son Cuddles ɗina ta waya. Wannan ina jin ƙanwar Jamal ce." [2/23, 7:34 PM] Nasma: Ta yi dariya, "Kaci sa'a ba ƙanwar Tarantula bace da ka gudu da kanka" "Amma me ya hanaki kula ni? Na ji haushi fa. Hmmm." Rasa kalmar da za ta kwatanta shi ta yi, sai kawai ta yi wannan murmushin nata bai bayyana siririyar wushiryarta. Dan tunani ya yi ya ce "How old are you?" "Ba na faɗa maka ranar birthday ɗina ba?" "Amma ki ka ɓoye shekarun ba." Ya dage gira yana kallonta ƴar ƙarama a gefensa. "18 zan yi fa." "What? Cuddles you are such a baby. I can't believe am this crazy for..." bai ƙarasa ba suka ji muryar Haj. Manga tana cewa shanyar tasu ta bushe. Ta ga alama ishar ma a gurguje suke son su isa masallaci. Dole hirar ta katse ba don suna so ba. Tare da Anti Nana suka tafi wannan karon. Kafin su isa masallaci Arƙam da Tauhidat sun sake ɗinkewa. Jamal ne ya dawo da baya ya shiga tsakaninsu. Arƙam sai ya dawo gefen Tauhidat shi kuma Jamal ya sake rabasu. Tana ta yi musu dariya ta hanzarta komawa gaba gefen Nanna ta barsu. Kwanakin da suka yi a Madina idan kowa zai manta dasu banda Arƙam, Tauhidat da Haj. Nanna. Duk wani motsinsu a kan idonta tana kallo tana jiran ranar da zasu fitowa da juna sirrin zukatansu. Arqam ba karamin so yake yiwa 'yar gaban goshin Nanna ba. Abin nasa ya hade da yanayin wurin da ya tashi sai ya zamana ba ya jin kunyar nuna mata kulawa a gaban iyayen nasu. A haka ma don Haj. Manga na taka masa burki ne da abin sai yafi haka. A ɓangaren Tauhidat yadda soyayyarsa ta mata shigar sauri haka sabo dashi ya yi mata. Tare suke tafiya masallaci kullum su dawo tare. Babu wata hirar soyayya a tsakaninsu amma sun san komai game da juna. Ranar da ta bashi labarin ƙwan da Susu ta turata yi a ƙasan gado ya jima rai a ɓace. Sai ta dawo bashi labarin Mammalo da mutan China. Da ƙyar ta kai ƙarshen labarin saboda dariyar da take yi. Motoci biyu suka yi bus zuwa Mikati domin ɗaukar haramar gabatar da Umra. Kowa ya fito cikin haraminsa suna ta talbiyya har suka isa Makka. Sun riga sun kama ɗakunan hotel ta yanar gizo saboda haka kaya kawai suka ajiye aka ɗunguma zuwa Masjidul Haram. Nan ma da addu'a suka shiga cikin wurin da yake ƙarshen ni'ima da haske a zuciyar mai imani. Tauhidat sai da ta zubar da ƙwalla saboda tsabar farinciki. A tare ƙungiyarsu take, saboda akwai cunkuso kada wani ya ɓata suka fara dawafi. Kowa yana kai kukansa wurin da za a share masa hawaye a ƙara masa da fiye da abinda ya roƙa. Bayan sun gama suka gabatar da nafila raka'a bibbiyu a bayan Mukam Ibrahim sannan aka wuce yin Sa'ayi (tafiya tsakanin Safa da Marwa). Cikin dare suka kammala kowa ya gaji aka koma masauki. Kafin su kwanta sai da aka cike ibadar da aski mazansu da matansu kowa ya yanke gwargwadon abinda shari'a ta lamunce masa. Washegari sai ga Arƙam da Jamal da huluna irin wadanda ake kira tashi ka fiye naci. Ƙwalƙwalin da Baffa ya ce lallai shi zasu yi ba saisaye ba suke rufewa. Sun fito tafiya masallaci Tauhidat ta gansu. Maganar da tayi ce tasa su rige-rigen cire hular. Inda ta ce da ace mata an halatta musu buɗe kai da ta nunawa duniya nata kan don kowa ya san cewa Allah Ya albarkaceta da yin umra. Baffa da Kawu Safiyanu suna wurin sai duka suka ji ta matuƙar burgesu. Azumi yana kwana ashirin da bakwai Arƙam ya gama tada hankalinsa akan yadda zai koma Baltimore shi kaɗai. Bashi da wata walwalar kirki sai ta zuwa masallaci. Tare yake tafiya da Tauhidat su wuni kowa na nasa bangaren yana ibada, sai lokacin tafiya su haɗu. Ita ma duk ta yi sukuku har tausayinsu Haj. Manga take ji. Sabo abu ne mai tsayuwa da cin rai. Daren jiya sai da ta yi kuka bayan ya fita daga ɗakinsu. Idanunsa jajur yake roƙon mahaifiyarsa akan ta barshi ya bisu sai ya zauna a Kano kafin hutunsa ya ƙare. "Arƙam kafi kowa sanin cewa ni ma ba don daɗi na barka kai kaɗai ba. Kana kallo na rasa da yadda zan yi na raba kaina da auren mutumin nan. Ga Jamal ko ɗazu ka ga irin turarrukan da ya saya masa wai shi mai uba. So kake yi kai da Allah Ya tseratar na ɗauka na damƙa masa?" Tashi Tauhidat ta yi za ta bar musu ɗakin saboda da farko hirar ba irin wannan bace. Yanzu kuwa ta fuskanci suna buƙatar ganawa cikin sirri. Ta kusa kaiwa bakin ƙofa ya daka mata tsawa, "koma ki zauna. Cuddles ba za ki iya tayani roƙonta ba shi ne zaki fita ko?" A gigice ta fashe da kuka saboda dama yanayinsa ya bata tausayi ga kuma tsawar da ta tayar mata da hankali. Ya kuwa taɓowa kansa don Haj. Manga bata masa da daɗi ba. Faɗa ta hau shi dashi akan me zai saka mata ƴa kuka. "Nanna ki dena masa faɗa ba don shi nake kukan ba. Kin gani na dena." Ta goge hawayen da sauri duk ta cabe gaban mayafin pashmina da ta yafa akan abayar jikinta. "Ji min sakarci. Ya saka ki kuka kuma kina kare masa." Shi ma da kukan nata ya ɗaga masa hankali sai ya koma bata haƙuri. "Zo na raka ki inda zaki je." "Na fasa" Ransa ƙara baci ya yi sai ka rantse kuka yake shirin yi ya ce, "Nanna kin ganta ko? Bata ma tunanin zamu daɗe bamu haɗu ba take min haka." Tausayinsu duka taji ta saki fuska, "Tashi kije ya saya miki ice cream kafin mu sauko. Ina son yin ɗawafi kafin a fara ƙiyamul laili da wuri zamu tafi yau. Kuma kada ki raga masa. Ki ɗauki duk abinda ki ke so." Fita suka yi aka rasa mai kula ɗan uwansa. Jamal ya haɗu dasu a wurin lift, ya soma tsokanarsu ya ga babu fuska sai ya wuce yana cewa faɗan masoya hutu ne. Wurin Haj. Manga yaje ta faɗa masa dalilin rigimar. "Ni fa idan ba Arƙam ba gaskiya ban ga wanda zan bawa ƙanwata ba. Tunda ni na amince ina ga kawai ayi komai a wuce wurin ni ma ki ji da ni." Pillow ta jefa masa tana cewa waye zai aure shi yaƙi maida hankali akan komai sai shiririta. Bacci taso yi kafin lokacin zuwansu masallaci amma ya addabeta da zance dole ta haƙura. Arƙam da Tauhidat na tsaye suna jiran a miƙo ice cream ɗin da ya saya mata na roba har lokacin sun ƙi kula juna. Godiyar da ta yi masa da ya miƙa mata ce ta kawo ƙarshen shirun. "Ɗazu kinyi magana da Papa?" "Eh" "Baki jin komai ace har za ki koma ko sau ɗaya bai taɓa sanin kina tare dani ba?" Zama suka yi a lobby ɗin hotel ɗinsu sannan ta soma magana tana share hawaye. Tunawa ta yi da abinda ta sani game da gadonsu wanda har yau koda takarda ta kasa rubutawa saboda bala'in asirin dake zagaye da rufuwar wannan sirrin. "Duk abinda Nanna take yi saboda ta kareka ne. Ni ma ba zan so mu koma wani abu ya sameka ba. Ka manta jiya ta ce next zuwa wurinka dani za ta zo?" Kwantar da kansa ya yi a jikin kujerar da yake zaune ya miƙe ƙafafunsa tare da ɗora hannu akan goshinsa. Sun kasa fahimtarsa. Ba wai saboda ya matsu da zuwa Nigeria bane. Damuwarsa yadda zai rasa ganin Tauhidat da ta mamaye ko ina a ruhinsa. Tana fara jami'a fa shikenan za ayi ta bashi uzurin tana makaranta aƙi zuwa da ita. Yanzu kuma kamar ta yi ƙanƙanta da aure. Kai anya kuwa? "Arƙam" ta ambaci sunansa karo na farko a cikin kunnuwansa. Da sauri ya buɗe ido ya gyara zamansa, hadda murmushin da ya yi masa ƙaura kwana biyu, "uhmm." "Me kake so Nanna ta yi sai na tayaka roƙonta." 'Ta bani ke', ya ce a zuci yana mai jin nauyin faɗa mata kalmar a zahiri, ba dan komai ba sai dan kada ya ɓata abinda ke tsakaninsu. Dole ya nema musu mafita kafin zuciyarsa da bata taɓa sanin soyayya ba ta buga akan ta. Washegari Jamal ya ƙara tunzura shi. Dama yaya lafiyar kura? Ya san damuwar yayan nasa da Tauhidat. Abinda ya fuskanta shi ne kamar Arƙam bai wani goge ta fannin wayewa da sanin soyayya ba. Abu na cin sa a rai amma ya kasa fitar dashi ya ji sauƙi. Ita kuma Tauhidat ya tabbatar ko zai sammata codein ba za ta taɓa fara cewa tana son Arƙam ba. Dawowarsu kenan gida zasu dan kwanta kafin su tafi masallaci ya taɓo ɗan uwan nasa. "Bana za a kwashi Jambitos. Fatana dai na makarantarmu su zama kyawawa. Ƴan Gwags kam zasu more da su Tauhidat." Babu wata kalma da Arƙam ya fahimta a zancen don jinsa yake kamar baƙon yare. "Meye Jambitos kuma?" Jamal ya ware idona kamar gaske, "kai fa baka san komai ba a ƙasarmu. Jambito na nufin fresh babes daga secondary school masu shiga level one." Ba shiri Arƙam ya tashi zaune, "matan kawai banda maza?" "Eh to hadda mazan amma ka san mu ƴan matan muke jira." "Kuyi musu me?" Arqam ya tambaya hankalinsa ya fara komawa kan Tauhidat. Yanayin fuskarsa sai da ya kusa sa Jamal dariya. Ya dai daure don ya fuskanci idan bai ɗora shi a hanya ba haka zai ta zama ciwon so na nuƙurƙusarsa. "Ka ga kamar ni da friends ɗina 'yan level one na shigowa muke sake ƴan mata. Ni dai iyakata na kashewa yarinya kuɗi amma irinsu Manniru kuwa ba a cewa komai." An taɓo maza, a fusace Arƙam ya ce, "indirectly you are trying to say wani zai yi Jambitos da Cuddles ko?" "Yes! Maganar gaskiya irinsu Tauhidat ne masu haɗa goslow ayi ta rigima tsakanin malamai da ɗalibai." "Allah Ya kiyaye. Ayi da wasu dai ba ita ba" ya tashi ya bar ɗakin a fusace. Jamal ya gyara kwanciyarsa yana cewa idan an haihu ayi masa takwara. *** Wajen shaɗaya na safe washegari Arƙam ya je ya gaishe da kakaninsa da iyaye. A ɗakin su Dada ya tarar da Haj. Manga ya tambayeta Tauhidat ta ce masa ta tafi masallaci yi wa mahaifiyarta ɗawafi. Tare suka saba tafiya sai yaji ya damu yana kokwonton kada taƙi soyayyarsa. Zama ya yi a ɗakin har Haj. Manga ta tashi komawa nata. Suna shiga ya ɗauko maganar da ko kusa bata yi mamaki ba. "Nanna don Allah ki bani Tauhida." Ya ce cikin yanayin tashin hankali da ban tausayi. Maganar Jamal ta jiya ko sahur bata barshi ya yi ba saboda damuwa. Zama tayi a kusa dashi ta riƙe hannunsa. "Arƙam Tauhida ba kaya bace, idan kana son ƴata ka nemi soyayyarta." "Idan taƙi amincewa fa?" "Sai ka haƙura." "I can't. To ki faɗa mata idan ta dawo." Ya soma yi mata magiya. "Kana nan da tsoron mata ashe. Ka yi ƙoƙari ka faɗa mata kafin mu bar ƙasar nan. In sha Allahu za ta amince." Yadda ya ga ta nuna masa farincikinta, ya ƙara masa ƙwarin gwuiwa sosai. Alƙawari ta yi masa cewa idan sun daidaita kansu tana komawa za ta turo masa takardunta ya nema mata admission a garin da yake. Su Baffa da kawunnansa na wurin uba zasu nema masa aurenta a wurin mahaifinta. Bai bar ɗakin ba suna ta shawarar yadda zasu gabatar da komai. Sharaɗi dai ta bashi cewa babu abinda za ta yi masa ba tare da amincewar Tauhida ba. Ranar da aka kai azumi ashirin da tara watan shawwal ya bayyana. Washegari ranar sallah ta zama babbar rana ga Haj. Manga da ƴaƴanta da duk mai ƙaunarsu. Sallah ce irin wadda suka daɗe rabonsu da ita. Yawo suka fice zaga wuraren tarihi a ƙasar har dare. Hotuna kuwa anyi ba iyaka. Sallah da kwana biyu Arƙam zai koma su kuma sai da kwana huɗu. Ana gobe zai tafi kusan babu wanda ya yi bacci. Suna tare family gabaɗaya ana ta hira. Tauhidat ce kawai ta fake da gajiya don ta basu damar kaɗaicewa. Bayan fitarta Baffa ya ce da Haj. Manga, "Hafsatu yarinyar nan kinyi mata kyakkyawar tarbiya. Wallahi ɗabi'unta suna burgeni sosai." "Baffa ɗorawa na yi, Allah Ya jiƙan mahaifiyarta ita ta ɗora ƴaƴanta akan kyakkyawar turba." Anti Nana ta murmusa "ina ta zuba ido ko za ayi ƴar gida da ƴar nan taki naji shiru. Shaƙuwarsu ta yi yawan da nake tausayin rabuwarsu." Umma ta karɓe da cewa yau kukan Tauhidat ya kai huɗu, saboda tsokanarsu da Jamal yake yi. Shikenan fa hira ta koma kan Arƙam da Tauhidat. Iyaye da suka shiga bashi ƙwarin gwuiwa akan kada ya bari gobe ta wuce bai nemi sun daidaita ba. Kunya ta sa shi barin ɗakin. Har mamaki suke yadda mawaƙi kamarsa mai mu'amala da mutane daban-daban ya gagara sanar da yarinyar da ko ba a faɗa ba an san tana son shi ita ma. Sai ƙarfe biyar zasu tafi raka shi Jidda washegari saboda jirgin dare zai bi. Tun da Tauhidat ta tashi fuskarta babu fara'a. Motsi kaɗan sai kuka har ya shigo ɗakin tare da Jamal. Ganin yana ta jan ta da tsokana taƙi biyewa yasa Jamal tambayar me yake damunta. Bata iya cewa komai ba sai wasu sababbin hawayen. Kan ta ta ɗora a cinyar Nanna tana kuka sosai. "Tauhida don Allah ki faɗa min abinda ke damunki. Ko baki da lafiya ne?" Haj. Manga ta tambayeta. "Zazzaɓi nake da ciwon kai" ta ce tana fashewa da wani kukan. Arƙam kallonta kawai yake yi yana jin kamar ya janyota jikinsa. "Ke da ki ke da likita a hannu har kya yi kukan ciwo? Dr. Arƙam Jambito is sick." Inji Jamal. Murmushin dole ya yi ba don yaso ba. Jamal ba ya rabo da neman tsokana. Sai da ya je bakin ƙofa sannan ya ce, "Cuddles zo." "Wannan suna wai ina ina aka raɗa shi?" Haj. Manga ta ce tana kallon bayan Arƙam. "Kashhh, Nanna shiru ake yi. Wannan suna baya buƙatar fassara." "Au to, ke Cuddles tashi kafin ya dawo don yau ko gyambo bai kai shi zafi ba." Ta ɗago mata kai daga cinyarta tana murmushi, "maza jeki ku yi sallama." A bakin ƙofar ɗakin suka haɗu ya yi gaba ta bishi suka shiga lift. Da suka sauko ƙasa taxi ya nema tana baya yana gaba. Sunyi tafiya mai ɗan nisa ya juyo, "me ki ke so na saya miki?" "Babu komai, kace ya juya mu koma." Ta share hawaye da bayan hannu. Zuciyarsa na kusa dama "Ya kike so nayi miki ne? Ba hadda ke ake supporting kada na biku Nigeria ba. Kukan na meye kuma?" Ta kwaɓe masa fuska kuwa tare da fashewa da kuka, "ba kaine ka ke min faɗa ba." Direban Taxi ɗin ya nunawa wani babban shopping mall a tsallaken titi ya ce ya saukesu a nan. Ɓangaren wurin wasu kujera ya kaita suka zauna. "Kina so na tayaki kukan ne?" Ta girgiza kai. "To ki dena kinji. Na dena faɗan. Ban san meye yake damuna ba. Gani nake kamar idan kun tafi ba zan sake ganinki ba." "Zan zo, Nanna ta ce za ta zo dani." Ta bashi amsa da sauri cike da kafin gwiwa. Gashi dai kuka take masa amma wani irin son ta yake ji yana ƙara yiwa zuciyarsa kyakkyawan kamu. Kallon cikin idanunta ya yi ya saki maganar da yake ta dako a ransa. "I love you so much Tauhidah. I don't even want to imagine life without you (bama na son yin tunanin rayuwa babu ke)." Sai ga ƙayataccen murmushi mai haɗe da tsantsar jin kunya ya mamaye fuskarta. Bai iya yin shiru ba tunda ya faɗi kalmar farkon ya cigaba da fallasa mata zuciyarsa. "Idan kin amince min muna komawa zan faɗawa Baffa." Kai ta cusa a tsakanin cinyoyinta yana ta magana tana jinsa taƙi ɗagowa. Sai da ya ce ko bata amince masa bane sannan ta ɗago a hankali. "Ni ka maidani wurin Nanna." "Is that a yes?" Ya kafeta da idanu.