Kenza eBookz

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 12

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 12

Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 12: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 12. Runtse idanunta ta yi ta gyaɗa kai. Arƙam ji ya yi kamar an yaye masa…

4,487 words

Runtse idanunta ta yi ta gyaɗa kai. Arƙam ji ya yi kamar an yaye masa wani duhu daga zuciyarsa. Inama zai samu a ɗaura masa aure da ita daga nan ya tafi da ita. Sun fi awa biyu a mall ɗin yana ta mata siyayya kamar bai san zafin nema ba. Warewa ya yi abinsa yana mata hirar soyayya ita kuma kunya duk ta hanata sakewa. Sai ƙarfe uku suka koma bayan ya matsa mata sun ci abinci. Jamal ya kira ya hau mata da kayan shi kuma ya ce ɗawafi zai je ya yi idan anyi la'asar ya dawo ya shirya. Tauhidat na jin haka ita ma taƙi sauka daga motar. Jamal ya shiga tsokanarsu don ya ga alamun komai sammakal an daidaita. Ɗaya daga cikin rigunan da ya saya mata ta saka da zasu tafi airport Jidda. Su Dada an sha kuka tana ta cewa ko da rabon ta sake ganinsa ko babu. Anti Nana ce kaɗai ta bisu da Uncle Kashim autan Baffa. Bayan tafiyarsa Haj. Manga ta shiga ɗaki taci kukanta ta more. Bata jin za ta taɓa yafewa Alh. Audi wannan halin da ya jefa mata iyali. Da don Arƙam ya sa ta alƙawarin ba za ta yi kuka ba idan zai tafi da Allah kaɗai Ya san irin kukan da Tauhidat za ta yi. Bare da ta ga ya gama checking-in zai wuce wurin boarding. Hawaye take gogewa wani na bin wani. Anti Nana kuwa ta ce kada ya yarda ya wuce sai ya tabbatar ta ga murmushin ƴar amanar Nanna. Mp3 player ya zaro daga jakar hannunsa suka koma gefe ya bata "saka a kunnenki." Ta saka earpiece ɗaya za ta saka na biyun ya yi saurin cewa, "wait!..." sannan da mafi dadin muryarsa ya kara da "I love you." Lumshi ido ta yi da murmushi ya ce, "is that all?" Ta sunkuyar da kai, "me too." Ya sake matsowa kusa da ita yana girgiza kai, "is that all?" Sai da ta kalli gefenta hagu da dama da sauri ta ce, "I love you Arqam." Kyakkyawan murmushi suka sakarwa juna ya ce "Missing you already" Sabuwar kwalla ce ta sake cika mata ido ta ce " Nanna ta ce zata zo dani." "Baffa zai yi Magana da Papa, Allah Yasa ya yarda a daura aurenmu kafin lokacin. Zan tura miki text kafin mu tashi, ki yi min reply da wuri kinji." Kai ta gyada ya nuna mp3 ɗin "ina fata wakar ta yi miki daɗi. Ke na yi wa sai na koma zan yi a studio. My last song possibly." Hawaye ta soma yi ya bar wurin ko juyawa bai sake ba saboda raunin da zuciyarsa ta yi. Haka suka rabu zuƙata na begen juna. Kafin jirginsu ya tashi ya kira Nanna ya faɗa mata ta fara shiri. Yadda ta nuna masa tamkar ta fishi murna ya ƙara kwantar masa da hankali. Text din da ya rubuta tun safe ya turawa Tauhidat kafin a fara sanarwar kasha waya wanda fassararsa take kamar haka. (Me kike so na fara yi miki idan na zo daukarku daga airport a matsayin mata ta?) Don ta san yana jiran amsa ne kuma ga yanayin rabuwar tasu amma da a fili ya yi tambayar sai dai ya nemi wani bakin ya bashi amsa. (Duk abinda ka ga ya dace da Cuddles.) Dama ya san za a rina, bai hakura ba ya sake tura wani (kina so duk wand kuke tare suce bani da kunya Kenan.) Kusan tuntube taci wurin kallon wayar a tsorace ta rubuta (me zaka yi?) (Abinda ya dace da Cuddles mana.) Ya tura yana murmushi ya kasha wayar. *** Kamar yadda suka zo a tafiya ma sai bayan awa biyu da tashin su Dada nasu jirgin ya tashi. Saɓanin yadda suka zo Tauhidat da Jamal na ta zuba surutu yau bata komai sai sauraron waƙar da Arƙam ya yi mata. Baitin da yafi kowanne tsaya mata take son haddacewa sai baya take da shi. Suna sauka su Baffa suka sake bin jirgi zuwa Maiduguri. Papa Abayomi suke sa ran gani yazo ɗaukarsu sai suka ga baƙuwar fuska. Tare da Mammalo suka zo yana ta murnar ganinsu. "Hajiya hannu da zuwa. Umara Tauhida da Umari Jamal duk hahhannunku." Babu wanda ya iya amsa masa saboda rashin ganin baban Tauhidat. Jamal ne ya tambaye shi bayan sun fara tafiya, "Ina Papa Abayomi?" "Iya gida sun fita da Alhaji ne. Da suka dawo ya ɗauko mukulli shi Alhajin sai ya ce ya huta" "Ka tabbata lafiya yake ko?" Inji Haj. Manga. "Sumul ƙalau Hajiya." Ya juyo baya yana murmushi "an fa kirani daga Daƙasoye. Yaya Uwani ta sauka an sami Muhammadu. Takwara ta yi min. Ina ta jira ki dawo he in tafi." Barka suka yi masa amma Haj. Manga jikinta duk wani iri yake yi mata. Da ta ga Tauhidat ta ɗan sake ne ma ta biye musu suna hira har suka isa gida. Suna zuwa Mammalo ya ce su wuce zai shigo da kayan falo sai masu aiki su hau musu dasu. Ƙananun jakankunansu Tauhidat ta ɗauko tana biye da Nanna har falon ƙasa. Mai gyaran ɓangaren Fanna ce ta tarbesu sannan ta faɗawa Haj. Manga cewa Alhaji yana kiranta a falonsa. "Jeki ki yi wanka kafin na hawo." Ta ce da Tauhidat. "Tare ya ce ku je babanta yana ciki hadda kai Jamal." Nan fa cikinsu duk su biyun ya tsirga da tsoro. Jikin mahaifinta ta tafi da sauri da suka shiga tana mai jin tsoron ko wani abu aka yi masa. Ganin ƙalau yake sai ta juya a kunyace ta gaishe da Alh. Audi da Alh. Ari. Alh. Ari ya washe baki kamar gonar auduga, "Haj. Manga barkanku da dawowa. Allah Yasa maƙabuliya ce." "Amin" ta ce fuska a gimtse tana neman wurin zama. Ya miƙa hannu, "Kafin ki zauna fara bani tukwicina." "Tukwici kuma? Me aka yi?" Gabanta yana tsananta faɗuwa. Alh. Audi ya kalli yadda jikinta ya yi sanyi ya sakar mata murmushi, "kinga Hafsatu ungo wannan" ya miƙa mata bandir din ƴan ɗari bibbiyu guda biyu. "Na meye?" "Sadakin ƴarki ne." Yawu mai ɗaci ne ya tokare mata wuya da ƙyar ta iya cewa, "wacce?" "Tauhidat mana hahah hahh" ya bata amsa yana dariya kamar ƙosasahen kwaɗo. "Da wa??" Haj. Manga ta tambaya baki na rawa. "Shamsu." Zabura Tauhidat ta yi daga jikin mahaifinta a gigice ta nufi Haj. Manga tana wani irin ƙuntataccen kuka da sautinsa yaƙi fitowa. Haj. Manga bata san lokacin da ta isa gabansa ta tsaya ba tana nuna shi da yatsa cikin ƙaraji ta ce, "baka isa ba Audi, kana jina? Idan ka isa ...." Kallon rashin damuwa ya bita dashi, "kada ki tsinewa kanki don aikin gama ya gama. Duk wani abin kirki da zan yi wa mutumin nan da iyalinsa sai kin nuna ɓacin rai. To wannan dai an gama!" Ɗaga hannu tayi kamar ta mare shi Jamal ya riƙeta yana nuna mata Tauhidat dake kokawa da numfashi a jikin Abayomi. A gigice ta taho ita ma Tauhidat ɗin ta tashi da ƙyar daga jikinsa ta nufeta da sauri. "Oluwatosin!" Abayomi ya daka mata tsawar da ta dakatar dasu su biyun, "idan ki ka ƙara taku ɗaya zuwa wajenta daga yau sai dai ki nemi wani uban bani ba." "Papa?" Ta ce zuciyarta na harbawa kamar ta ballo mata ƙirji. Haj. Manga da ta ware hannuwa ta rungumeta sai ta yi turus hannuwan suka sauka a jikinta. Tunda take a duniya bata taɓa ganin abinda ya kona mata rai na cin amana makamancin wannan ba. Kunnuwanta neman toshewa suke ga ƙafafunta sunyi mata mugun nauyi. Tana tsaye a wurin wasu zafafan hawaye suka shiga gudu a kumatunta. Idanun Tauhidat na sauka cikin nata kuwa Tauhidat ɗin ta sulale a wurin. Jamal cikin zafin nama ya fincikota daga jikin Papa Abayomi yana ihun kiran sunanta. Ƙirjinta ya mata nauyi tana jin kamar za ta fita hayyacinta amma a haka ta daka masa tsawa "Jamaluddeen! Sakar masa ƴarsa." Ya juyo shi ma kansa hawayen yake yi, "Nanna suma fa ta yi." "Na ce ka saketa." Ta juya a hankali cikin ƙunar rai tana tafiya. Bata fita daga falon ba ita ma ta yanke jiki ta faɗi. Jamal ya yi wa Tauhidat kallo ɗaya tana jikin babanta shi ma yana kuka ya isa wurin mahaifiyarsa da sauri. Juyawa ya yi neman taimako ya kula ashe babu kowa a falon sai su kaɗai. Cicciɓarta yake son yi amma ko shi ta fi shi tsayi bare kuma jiki. Jijjigata kawai yake yana kiran sunanta cike da tashin hankali.

Alhamdulillah Mu haɗu a kashi na biyu domin jin yadda za ta kaya. Taku BATUL MAMMAN.

[2/23, 7:34 PM] Nasma: 22 GA WATAN RAMADAN

Da sauri-sauri Alh. Audi ya kurbe ruwan giyar da ya zuba a kofi saboda tsoron kada wani ya shigo office ɗin ya kama shi. Giya dai rabin kofi ya tabbatar ba za ta karya masa azumi ba, amma sanin halin mutane na surutu yasa yake ɓoyewa. Kwalbar kacokan ya ɗaga da nufin shan karshe kafin ya tashi aiki aka banko ƙofar. Ba kowa bane illa Alh. Ari wanda ba shi da shamaki da ofishin. Duk abin Alh. Audi sai da ya ɗan ji tsoro kafin ya dake ya ɗauke kai. Fuska a haɗe ya ja dogon tsaki, "Ayi mutum bai san darajar sallama ba. Ji wannan buga ƙofa sai kace gidanka." Ko a jikinsa ya zauna, "wai kura ce za ta ce da kare maye. Duk abuna ina kai azumi ba kamar wasu ba da tsagerancinsu ya yi tsamarin da suke shan giyar da ko babu azumi haramun ce." "Kaga ni na tashi idan wani abin ne ya kawoka ka faɗa ba ka zauna kana neman ci min fuska ba." Gyara zama Alh. Ari ya yi ya zaro wani envelop daga gaban babbar rigarsa. Sai da Alh. Audi ya zauna shi ma sannan ya faɗa masa cewa abinda yake ciki ya shafi Haj. Manga. Nan da nan fuskarsa ta sauya zuwa mugun bacin rai, ya soma huci. "Ari nace ba, wai ko na sakar maka ita ne ka aura? Haba! ko ni da nake aurenta kuma na san manufofinta ba na bibiyarta kamar yadda kake yi. Don baƙar jaraba tana gaban ɗakin Allah ma bata tsira ba." Alh. Ari bai ce komai ba ya zazzage masa hotunan dake cikin envelop ɗin a gabansa. Tashin farko yaci karo da hoton Arƙam da Tauhidat akan hanyarsu ta masallaci. A ƙagauce ya dinga barbaza sauran akan teburin gilas ɗin gabansu. Hotuna ne birjik duka nasu Haj. Manga. Babu wani cikin tawagarsu da bai fito a hoton ba. Saboda tsaro na hotel ɗin ɗan aiken bai sami damar binsu ciki ba. Amma hatta shagunan da suke zuwa siyayya an ɗaukosu a wurin. Ɓacin ran da Alh. Audi ya shiga a wannan lokacin yana jin zai iya take mutum da mota amma bazai huce ba. Huci yake jikinsa na tsuma ba kunya ya kafa kai akan kwalbarsa ya tittile ta tas a rumbunsa. Yana magana kumfar yawu na watsowa har fuskar Alh. Ari don bala'i. "Sai na nunawa Manga cewa bakin rijiya ba wurin wasan yara bane. Wai ma to me ya kawota gidana tunda shegen yaron yana tare da ita?" Leɓensa ya shiga gurza da haƙori yana jin wani mugun takaici. Shi za ta ha'inta ta ƙala masa sharrin ɓoye mata ɗa saboda ta raina shi? Takaicinsa ɗaya takunkumin da Oga ya kafa masa. Da fari so ya yi ya koma a can inda ya kai Arƙam karatu ya tura shi yabi ubansa. Hakama Tauhidat ɗin da tuni ta bar numfashi. Amma Oga ya gargaɗe shi da cewa, duk ranar da ya sake kashe rai bayan wadanda ya yi a baya to ya tsumayi sakamako daga iyayen gidansu, wato aljanun da suke musu aiki musamman shugabar da suke kira Mai share musu hawaye. Shi ya sa fa ya dage da shige musu jiki ya ci su da dabara tunda an hana mai kankat. Tunda ya kunnu iyakar kunnuwa sai Alh. Ari ya soma nasa famfon, "Ina kyautata zaton fa maganar gadon nan bata binnu yadda muke tsammani bane. Talala matar nan take maka. Duk ranar..." "Kada ka yi min maganar banza. Abubuwa biyu masu mahimmanci na sadaukar domin kawar da hankalinta da na duk wani mahaluƙi akan dukiyar Ibrahim." Matsawa ya yi kusa da Alh. Ari ta yadda yake jin hucin numfashinsa ya nuna shi da yatsa, "Idan abinda na rasa basu isa su samar min da dawwamammen farinciki da rufuwar sirri ba, to ka sani bayan na tabbatar an tsinci gawar Oga a kwata taka ce za ta biyo baya." Alh. Ari ba ya tsoron barazanarsa ko kaɗan. Hasalima dai idan ya yi bai wuce ya ƙara masa ƙaimi wurin tsanarsa ba. Tunda ya nemi ya mallaka masa reshen dake kula da kwangilar titi na kamfaninsa ya ƙi yake jin haushi. "Ba ni na kar zomon ba kububuwa sai ka sauke fushinka a inda ya dace. Nan ka ce Oga ya faɗa maka lokacin zuwan direban nan da iyalinsa cewa ƴarsa tana daga cikin matsalolinka." Shiru ya yi na dan lokaci yana nazari, kafin daga baya ya kwashe wayoyi da tarkacensa ya yi waje. Ko da Alh. Ari ya isko shi a waje ya riga ya bada umarnin a ja motar su tafi. Da jerin rantsattsun motoci uku yake tafiya a ƙa'idarsa. Ta tsakiyar da yake ciki yau ƙaramar limousine ce mai ƙofa huɗu. Yadda yake neman kuɗi ta kowace siga, to fa haka yake rayuwa cikin nunawa duniya ya wuce sa a. Gidan gonarsa ya ce a wuce dashi saboda yana buƙatar lokacin yin nazari. Alh. Ari da ya ga ba hanyar gida suka nufa ba, sai ya umarci nasa direban da ya dena binsu. Ba zai bishi ba don ya tabbatar duk inda zai je to neman mafita zai yi. Shi kaɗai a cikin duhun ɗakin, dare ya raba yana kai gwauro yana kai mari. Tashinsa na huɗu kenan a duk lokacin da ya rufe idanunsa mafarkin Haj. Manga yake da ƴaƴanta da kuma Tauhidat suna cikin walwala shi kuma yana wulaƙantaccen yanayi. Akwai wanda ma ya ga Ibrahim yana murmushi, shi kuma yana ihu cikin wahala. Wannan abu ya tsaya masa a rai domin yana hango gagarumar barazana ga kyakkyawar rayuwar da ya ginawa kansa. Washegari ma haka ya wuni sai soke duk wasu abubuwansa masu mahimmanci aka yi. Fanna bata neme shi ba tunda mahaifinta ya fada mata cewa yana gidan gonarsa. A yini na biyu ya tara kwalaben giya kamar hauka a ɗakinsa sai ka ce ba musulmi a watan azumi ba. Sunan Shaheed ke masa yawo a kwanya, ya tuna musabbabin janyo yaron a jiki bai wuce domin yaji daɗin yin garkuwa dashi ba akan ƙanwarsa. Dariyar mugunta ya yi son rai sannan ya kimtsa ya nemi direbansa ya kaishi gida bayan ya kira Alh. Ari. Papa Abayomi da Mammalo suna wurin mota yana koya masa tuƙi yaji kira zuwa wurin shaƙatawar Alh. Audi a bayan gidan. Ba saba irin haka suka yi ba, shi ya sa hankalinsa ya tashi da saƙon ya riske shi. Shaheed ne ya faɗo masa a rai da kuma su Tauhidat. Da azama ya isa wurin daga ɗan nesa dasu ya kai gwuiwoyinsa ƙasa ya gaishe su. Faram-faram suka amsa masa sannan Alh. Audi ya soma jansa da hira. Wai a matsayinsu na magidanta ya kamata suna neman shawarar juna akan al'amuran yau da gobe na harkokin gida. Cikin faɗuwar gaba Papa Abayomi ya ce, "Alaji ni da na daɗe babu iyali ai bana cikin masu bada shawara akan komai. Yaran nawa ma kun riƙe min sai dai na yi ta bin ku da addu'a." Murmushi Alh. Audi ya yi sai ka zata da gaske maganar duka ta kirki ce, "zaman haka bashi da wata fa'ida Baban Shaheed. Ni ma fa matata ta farko rasuwa ta yi amma ka ga da nasan zaman haka yana ragewa mutum ƙima dole na auro wasu ba don na dena sonta ba." Hira sosai suka yi ta jansa da ita, ya nuna musu kamar ya saki jiki a zahiri. A zuci kuwa sai tararrabi yake saboda tun zuwansa yau ce rana ta farko da aka yi irin haka. Ya nisa a tunani ya ji muryar Alh. Ari a kusa dashi yana tambayar Alh. Audi game da hirarsu ta ɗazu. "Ina faɗa maka mutum mugun icce ne Ari, mutumin har ƙauye kaninsa yaje ya ɗauko shi ya jawo shi jikinsa sosai amma in taƙaice maka ƙanin yana mutuwa ya haye kan dukiyarsa ya yi kwanciyarsa a kai. Zancen da nake maka fa magadan ƙanin da duk wani mai ruwa da tsaki a lamarin ya rufe musu baki sun manta shaf da wani gado." Miƙewa Papa Abayomi ya yi, "Alaji bari na baku wuri." "Dawo Baban Shaheed ka tayani jin abin al'ajabi." Cewar Alh. Ari. Ɗan murmushi ya yi ya zura takalmansa zai tafi don hirar ba tasa bace Alh. Audi ya dakatar dashi. "Don Allah idan kai ne alƙali wane hukunci ka ke ganin ya dace da yayan mamacin?" Ba don yaso ba ya dan dakata daga gefe ya kuma durƙusawa, "gaskiya bai kyauta ba kuma barin irinsa a cikin mutane hatsari ne. Amma batun hukunci wannan sai alƙalai." Wani iri Alh. Audi ya yi da fuskarsa tamkar mai alhinin gaske kafin ya ce, "kuma fa ina tsammanin akwai hannunsa a mutuwar ƙanin nasa." Cike da jin haushin ko waye wannan mugun Papa Abayomi ya ce, "Innalillahi...Allah Ya bi misu haƙƙiinsu Ya saka musu. Shi kuma mai cin dukiyar haram Allah Ya tona asirinsa Ya hana shi samun kwanciyar hankalin da yake nema bayan zubar da jinin ƙaninsa. Alaji amana ta yi ƙaranci yanzu." Kashingiɗa Alh. Audi ya yi yana murmushin jindaɗi, ya ɗan kallo Papa Abayomi. Hankali kwance ya ce masa, "wai ka san kuwa labarin kaina na baka? Audi a ƙauye ya tashi wurin dangin mahaifiyarsa. Da Ibrahim ya girma mahaifiyarsa ta faɗa masa yana da yaya da suke uba ɗaya. A satin ya ɗaukoni daga ƙauye. Bayan shekara biyar na goge da sanin komai na kasuwancinsa." Ya gyara zama yana wata irin dariya ganin idanun Papa Abayomi na neman faɗowa don fargaba "wato kana ji ko, wasu abubuwa ne suka faru da suka kusa janyowa Ibrahim ya korani inda na fito sai kawai na ɗan haɗa masa tsautsayin da ya yi ajalinsa." Alh. Ari ya kwashe da dariya "dama an ce shege na ƙauye. Surukina kai fa abin tsoro ne." Shi ma dariyar yake yi cike da alfahari, "don ma ban faɗa maka cewa nasa an sace babban ɗan Ibrahim ba. Ya ma sunansa? Uhmm, wannan yaro mai kama da uwarsa sai tsayi kamar titin Zaria daga Kano...yauwa, yauwa Arƙam. Shi kuma ƙanin na mayar dashi ɗan ƙwaya." Ya ware hannuwa irin komai ya yi daidai. Zufa ta gama wanke Papa Abayomi sharkaf, amma bata hana shi rawar jiki ba. Ya rasa abinda zai ce saboda kaɗuwa ya zauna dabas a wurin saboda rashin ƙwarin jiki. Su kuwa ganin ya kai inda suke so Alh. Audi ya fito masa da cewa ya faɗa masa ne saboda yana son jan shi a jiki ya shiga cikinsu a dama dashi a arziƙin. Ɓacin rai muraran ya gani a fuskar direban matar tasa kuwa. A fusace ya tashi bai ji ko ɗar ba ya nuna shi da yatsa "Da ace a kan titi muka haɗu ka faɗa min wadannan maganganu tabbas da kafin na kaika wurin ƴan sanda sai na yi maka dukan da za ka kasa motsi. A yau duk wani girma da ƙimarku ya zube a idanuna. Wannan baiwar Allah banda kashe mata miji me yaranta suka yi maka da ba za ka barsu haka ba?" Tafi suke masa su biyun, suna neman manna masa hauka. Alh. Audi ya kwaɓe fuska kalar tausayi. "Sai da na gama faɗa maka sirrina zaka juya min baya? Na ji idan ba za ka shiga cikinmu ba babu matsala amma domin tabbatar da cewa sirrin nan ya zama tsakaninmu har abada ina buƙatar ka bani ƴarka Tauhida na aurawa Shamsu domin ta zame min garkuwa ko ba haka ba Ari?" Suka tafa kamar wasu yara. "Indai don wannan ne ka sa ranka a inuwa, domin har na mutu ba zan faɗawa kowa ba don na san kunfi ƙarfina. Allah Yana kallonku kuma lokaci Ya ara muku kafin ku koma gare Shi. Amma ƴata ko ta rasa miji Allah Ya tsareta da haɗa jini da mutum irinka." "Kana burgeni fa domin kana da riƙon gaskiya, to babu matsala. Kana iya tafiya." Jiki a sanyaye ya miƙe har ya soma tafiya ya ji ya soma cewa, "sati mai zuwa za a kama Shaheed da cocaine a kayansa. Ina jin Turkey ma hukuncin kisa suke yankewa masu safarar miyagun ƙwayoyi." Cak ya tsaya ya juyo yana kallon yadda Alh. Audi ke magana kamar ba mugun abu yake faɗa ba. Shi kuwa ko a jikinsa ya cigaba da cewa, "Jamal na dawowa zai sha ƙwayarsa ta yi masa karo ta yi ajalinsa. Shi kuma babban ko wane makirci zan ƙulla masa wa ya sani. Ohh ni Audi mutumcina ragagge ne." Ya kece da dariyar da ta ƙara mayar dashi baƙi a idon Papa Abayomi, "ka san uwarɗakin naka da son ƴaƴa haka baƙinciki zai yi ta nuƙurƙusarta har aji zuciyarta ta buga ita ma ta mutu bayan ƴan kwanaki. Wannan tashin hankalin kuma shi zai sa Tauhida tana tafiya a gefen hanya tirela ta markaɗeta batare da ta sani ba saboda damuwa." Idanu jazur babu tsoro bare fargaba Papa Abayomi ya ce, "Idan na fahimceka kana son ka faɗa min abinda zai faru ne saboda naƙi amincewa da haɗa hannu da kai?" "Wannan da ka yi boko ba ƙaramar ƙwaƙwalwa zaka yi ba. Haka yake nufi. Haj. Manga da ta rungumi ƴarka kamar ita ta haifeta tana gab da ta rasa rayuwarta da ta ƴaƴanta a dalilinka. Maganin wannan abu ba komai bane illa ka amince ka bawa Alhaji auren Tauhida ga Shamsu." "Ku kasheni tunda ni ku ka faɗawa ba su ba." "Idan ka mutu ma ɗaya bayan ɗaya su da danginka zasu biyoka." Ko gezau Papa Abayomi bai yi ba ya bar wurin. Sunyi mamaki ƙwarai don a tunaninsu zai firgita musamman akan ɗansa. Duk da haka basu damu ba ko kaɗan, domin kuwa bayan kwana uku kamar yadda suka shiryawa Shaheed gadar zare sai ga wayarsa ga mahaifinsa yana kuka sosai da roƙon a dawo dashi gida. An kaiwa abokansa mutum uku sumame kuma duk an same su da hodar ibilis. Abin tashin hankalin shi ne cikinsu babu mai ko shan taba a iya sanin Shaheed ɗin. Shi ma anyiwa ɗakinsa fata-fata ba a sami komai ba amma an saka ido a kansa. Abokan nasa kuwa da suke ƴan Nigeria su ma an kama su kuma an gama tabbatar masa da cewa babu abinda zai fito sai gawarsu. Wannan abu ya tada hankalin Papa Abayomi ƙarshe. Yara ne kamar ɗansa da iyayensu suka tura karatu. Biyu a ciki ma irin Shaheed tallafi ne suka samu ba ƴaƴan kowa bane. Da wannan Alh. Audi ya riƙe wuyansa ya rantse masa idan dai aka yi auren Tauhidat da Shamsu yaran nan zasu kubuta. Idan yaƙi yarda kuwa to har abada ya sani cewa akan taurin kansa iyalai uku zasu rasa ƴaƴansu. Darajar rayukan da babu ruwansu da kuma dahir da ya gani na cewa Alh. Audi da gaske yake yasa Papa Abayomi amincewa. Abinda basu sani ba shi da su Shaheed kuwa shi ne wasu zaune gari banza ƴan ƙasar aka biya suka firgitasu. Ba ƴan sanda bane kamar yadda suke zato. Tsorata dai sunyi ba kaɗan ba don suna fitowa biyu a ciki basu ƙara kwana a ƙasar ba ma. Bayan ya tabbatar da lafiyar ɗansa bai zame ko ina ba sai ofishin ƴan sanda mafi kusa. Sun zauna da wani Sergent ana jiran ya fara bayani domin a ɗauki statement ɗinsa ya sami kansa a irin mummunan yanayin da Tauhidat ta taɓa faɗawa. Ga dai bayani akan harshensa amma yaƙi fitowa. Ya yi-ya yi amma ina, indai wannan maganar ce sai yaji kamar an riƙe masa harshe. Ƙwalla ce ta cika masa idanu ya buƙaci a bashi biro da takarda. Nan ma sammakal inji Jamal, bai iya rubuta komai ba sai rawar hannu. Haka ya tashi ya fita jiki a saɓule. Bai daddara ba wani station ɗin yaje. Nan ma dai haka ta kasance har na uku da na huɗu. To fa a lokacin ya tabbatar cewa saduda ta zame masa wajibi a wannan gabar. Sauran barazanar basu daga masa hankali ba kamar wannan. Ace ka san abu kuma yana yawo a kanka amma ka kasa sanar da kowa. Da ƙafarsa ya kai kansa gare shi ya ce ya amince. Ya yarda cewa Alh. Audi ya musu fintinkau. Iyaka abinda zai iya yi wa Haj. Manga da nasa yaran bai wuce ya sadaukar da gudan jininsa ga maƙiyinsu ba. Ba kuma haka zai zauna ba, zai yi iya yinsa wurin ganin ya taimaka wurin fiddosu daga cikin wannan bala'i da ya tunkarosu. Bayan amincewar tasa ne aka ƙara masa da sharaɗin cewa ya raba Tauhidat da Haj. Manga ta yadda ko inuwa ɗaya ba za su ƙara zama ba. Saɓa hakan zai iya jawo abu mara dadi garesu. Ba musu ya amince. A yanzu kam ko me suke so zai karba don ya sakawa ransa cewa da izinin Allah akwai ranar da wannan azzalumin zai ciji yatsa idan ya fara girbe shukarsa. *** Da taimakon Fanna da ta sauko ƙasa, a lokacin Jamal ya kira Dr. Madaki aka kawo ambulance ɗaukar Haj. Manga. Papa Abayomi na jin taimako na zuwa gareta ya cicciɓi ƴarsa ya goya ya fita daga gidan. Duk wanda ya ganshi ya san ba lafiya amma bai iya tsayawa baiwa kowa amsar tambayoyinsu ba. Nauyinta bai dame shi ba haka ya shafe tafiyar tazarar dake tsakanin cikin gidan da bakin gate da sassarfa. Kafin ya ƙarasa Shamsu ya shigo a guje ya baɗesu da ƙura. Ya gan shi sarai da mutum a baya amma ƙurar da ta kwaso su ma bata ishe shi kallo ba. Direbobi biyu sun biyo shi da mota amma yaƙi shiga ga Mammalo yana biye dashi. Tasi ya tara ya faɗawa direban ya kaishi asibitin da zasu fara gani a hanya. Mammalo ya shiga gaban motar yana ta masa tambayoyi bai iya tanka masa ba. Hankalinsa ya tafi akan rashin kyakkyawan numfashi daga Tauhidat. Suna zuwa a emergency aka karɓeta bai ji wani bayani ba sama da cewa jininta ya yi mugun hawa. Ita ma Haj. Manga emergency ɗin aka wuce da ita a asibitin Dr. Madaki. Sunyi ta kiran Baffa tun kafin su sauka tunda Maiduguri suka wuce. Sai bayan awa uku lokacin anyi mata allurar bacci Jamal ya same shi. Haka ya masa bayani wayar Arƙam ta tara tana shigo masa. Bai san me zai ce da yayan nasa ba idan ya ɗauka. Ga mugun tausayinsa da na Tauhidat tare da Nannansu da ya mamaye masa zuciya. A ranar kam yaci kuka ya gode Allah.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull