Kenza eBookz

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 13

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 13

Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 13: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 13. *** Arƙam a nasa ɓangaren kamar ya yi hauka. Duka su ukun ya nema…

5,209 words

*** Arƙam a nasa ɓangaren kamar ya yi hauka. Duka su ukun ya nema shiru. Ko sun gaji zai so ganin a ƙalla ko da text ne layi ɗaya na cewa sun sauka lafiya. Baffa ya kira a ƙarshe bai nuna masa komai ba sai ya kasa tambayarsa game dasu. Da sassafe Baffa ya baro Maiduguri batare da ya nemi kowa cikin ƴaƴansa ba saboda zulumi. Duk yadda akayi wata maƙarkashiyar Alh. Audi ya shiryawa ƴarsa shi ya sa ya ɓullo musu ta wannan hanyar. Meye gaminsa da Tauhidat da zai aurawa ɗansa alhalin ya san matarsa ba ta haɗa son yarinyar da kowa? Da kuka sosai mai shiga rai Haj. Manga ta tare shi tana daga kwance akan gado. "Baffa ashe bayan Madam Zainaba zan sake kukan cin amana? A gabana Abayomi yake faɗawa Tauhida zai tsine mata a kaina? Me yasa duk wanda na nufa da alkhairi yake bina da sharri?" Ƙwalla dattijon mai kyakkyawar zuciya ya share, ya ɓoye damuwarsa da murmushin da bai kai zuci ba. "Idan duniya gabaɗaya za ta juya miki baya taci amanarki Hafsatu, ki tuna cewa babanki Umaru zai yi komai domin inganta rayuwarki. Har yau baki yi girman da zan dena zuwa gareki idan kina cikin damuwa ba. Abayomi kuma ki barni dashi." Kai ta girgiza a wahale, "Ka ƙyale shi kawai ya je inda yake ganin ya fiye masa. Dama Tauhida..." A hankali ya ce, "na sani kin damu da ƴarki ko ba don Arƙam ba. Zan je har inda Abayomi ɗin yake na tuntuɓe shi. Kin san ko bai faɗi gaskiya ba ni mai gano inda ya dosa ne." Sai lokacin ta ɗan ji sauƙi a ranta harda murmushi. Da zai fita bata iya ɓoyewa ba ta roƙi ya gano mata halin da Tauhida take ciki domin Mammalo ya faɗa musu tun jiya bata farka ba. "Tauhida ƴar Mangan Baffa. Ke ciwo ita ciwo. Wannan idan an aurawa Arƙam ɗin za ki barta ta tare kuwa?" Ya zolayeta. Kunya taji ita da Jamal suka dinga dariya har ya fita. Khul'i ya yanke shawarar yi wa Haj. Manga da Alh. Audi ya raba auren ko ta halin ƙaƙa, ko sa rabu da ƙwallon mangwaro su huta da ƙuda. Direbansa da ya kawo shi bai san gari ba sosai sai wanda aka bawa mukullin motar Haj. Manga ya nema don ya kaishi asibitin da Tauhidat take. Mammalo ne ya faɗa masa lambar ɗakin da suke. Suna fita yaron da Alh. Ari ya saka kai masa rahoton shige da ficen su a asibitin ya kira shi ya faɗa masa shi kuma ya sanar da Alh. Audi. Idanunsa akan wasu takardu ko ɗagowa bai yi ba ya ce, "ka tashi muje duba ta yanzu, sannan a saka min ido akan inda fitinannen tsohon zai je daga zuwansa. Shi ko hutawa baya son yi duk da ya yi ritaya. Ya zauna a gida ya raini tsufansa yaƙi." "Yana da kai a tsakiyar maƙoshi ina yaga ta zama? Ni ma ba don muna tare ba Alh. Audi ai da ina nan ina fama." Dariya suka saka harda tafawa sannan suka fice zuwa dubiya. *** "Tosin ki taimakeni ki buɗe idanunki na san kina jina. Kada ki mutu ki barni da dakon laifin da nayi muku bisa fin ƙarfi. Ki bar ta rayuwata, taki da ta yayanki da kuma ta Haj. Manga da ƴaƴanta duka amincewarki ce kadai za ta kuɓutar damu baki ɗaya." Ya faɗa da yarbanci. Maimakon ta buɗe ido sai hawaye ya gani suna zirarowa ta gefen idanunta. Tashi ya yi zai fita kira likita tunda ance masa tana tashi ya sanar yaji ta riƙe masa hannu. A lokacin kuma Baffa ya iso ƙofar ɗakin. Zai yi musu sallama yaji abinda take faɗa sai ya dakata. Kamar ta san yana wurin take maganar da hausa saboda sabo da yaren. "Papa akwai abinda Baba ya yi maka ne da yasa ka amince ka aurar dani a irin wannan yanayin da har abada Nanna kallon butulu za ta yi mana? Kullum abinda ka ke faɗa min kenan ko bayan ranka idan na butulce mata amana za ta ci ni amma yanzu da kanka kake cewa idan naje wurinta sai dai na sake uba. Tsine min za ka yi kenan?" Ta ƙarashe ta kuka. Nasa hawayen ya sharce da yatsun hannunsa ya riƙo ɗaya hannun nata yana sauke numfashi "kiyi min haƙuri ki zauna da Shamsu zuwa lokacin da zan samar mana mafita. Tosin babanki ba zama za yi ya zuba masa ido ba. Na san kina da hankali shi ya sa bani da niyyar ɓoye miki girman nauyin da yake kanki yanzu." Rungume shi ta yi sautin kukanta na ƙaruwa, "akwai wani abu da na sani akansa amma na kasa faɗawa kowa. Ko me zan yi maganar bata fita. Kuma abin zai taimaki su Nanna." Yana shafa kanta ya labarta mata yadda yake yawon police station akan abinda Alh. Audi ya faɗa masa da bakinsa shi ma ya kasa faɗa. Ga kuma barazanar da ya yi masa da Shaheed. Abin tausayi haka take kuka da sauti shi kuwa sai sharar hawaye. Baffa bai ji sauran maganar ba saboda da yarbanci suke yi amma ya fahimci akwai wata a ƙasa. Ƙofar ya tura tare da sallama. Da sauri Papa ya miƙe, haka ma Tauhidat ta soma kokarin tashi zaune. "Yi kwanciyarki Tauhida, kwanta ki huta." Kujera Papa Abayomi ya tura masa bayan ya zauna ya tambayi jikin Haj. Manga. "Da sauƙi sosai, sai dai ina mamakin yadda ka iya juya mata baya akan kuɗi." Kai ya sunkuyar ya rasa abin cewa. Baffa ya tsammaci dama da wuya ya iya faɗa kai tsaye indai akwai abinda yake tsoro. "Zan iya taimaka muku idan kun bani dama. Ba tun yau Audi yake neman ganin bayan ƴata ba saboda haka na karance shi ciki da bai. Ina so ka sani cewa duk abinda ya faɗa maka a matsayin dalilin son haɗa ɗansa da Tauhidat ƙaryane. Ka yi haƙuri da kalamaina amma ka sani kai da ƴaƴanka ba wani abu da zaku iya tare masa a rayuwa. Idan kuma akwai kawar daku daga doron ƙasa ba wahala zai yi masa ba. To idan haka ne me yake nema da ƴarka? Don ya cusgunawa Hafsatu ne? Ko ɗaya ban karba ba. Nafi tunanin dai ita din barazana ce ga wani abu nashi kuma bashi da damar rabata da rayuwarta shi ya sa ya ɓullo ta koma wace siga yazo gareka. Abayomi kai nake saurare, me ya haɗaka da Audi?" Ɗan sauran dauriyar da yake yi a gaban ƴarsa ya nema ya rasa. Bai ɓoye komai ba sai zahirin maganar wadda ba zai iya faɗa ba. Ya ƙara da bayanin da Tauhidat ta yi masa na ita ma tana da masaniya akan wani abu nasa. Baffa ya san za a rina. Alh. Audi yana amfani da sihiri da tsafi shi yasa suka kasa cewa komai. Idan ya bar yarinyar nan a hannunsa ba ƙaramar cuta bane garesu. Basu da wani gata sai Allah. Daga zuwa aiki a haɗa dasu a cikin faɗan da yafi ƙarfinsu. "Ka bar komai a hannuna in sha Allahu ba za ta tare da sunan matar Shamsu ba." "Yallabai me za ka yi?" Papa Abayomi ya tambaye shi cike da fargabar kada allura ta tono garma. Kwantar musu da hankali ya yi ganin sun tsorata, "kada ku damu zan bi komai ta hannun shari'a ne. Idan na raba auren kai da ita zaku bar ƙasar sannan yaronka ma dole ya baro inda ya tura shi." Yana gama magana ya tashi tsaye tare da yi musu sallama. Direban da ya kawo shi wanda kusan tare suka hawo saman inda ɗakunan kwanciya suke ya yi saurin matsawa daga jikin ƙofar kada a ganshi. A cikin wani banɗaki da babu kowa ya ɓuya har lokacin da Papa Abayomi da Baffa suka iso bakin benen. Yana jin muryar Baffa na cewa ya koma ya bar mara lafiya ita kaɗai. Musabaha suka yi Papa ya ƙara yi masa godiya sannan ya juya. Baffa na sauke ƙafa ɗaya a bakin benen shi kuma ya fito daga maɓuyarsa ya saka iya ƙarfinsa ya hanƙada shi. Baffa ya yi ta ƙoƙarin kama ƙarfen gefen benen Allah bai nufa ba. Haka ya yi ta gangarawa kansa na bugun ƙarfen benen da tudun steps ɗin har ƙasa. A take jini ya ɓalle daga kansa idanunsa suka juye. Direban komawa ya yi banɗakin ya sake laɓewa bayan aikin gama ya gama. Bai yi cikakken minti daya ba kuwa yaji ihu da hayaniya a wurin. Wata mai jinya ta sauko taci karo dashi a wurin. Babu bata lokaci aka ɗauke shi sai emergency. Wani nurse ya ciro wayarsa tunda basu ga alamar tare da wani yake ba aka fara neman layin wani nasa. Sunan Jamal suka gani a matsayin wanda suka yi wayar ƙarshe. Yana kira kuwa ya ɗauka. Tare suke da Nanna an rasa me daukar wayar Arqam ya masa bayanin halin da ake ciki. "Baffa kun taho ne?" Nurse ya ce "don Allah ka san me wayar nan?" Cikinsa ne ya ƙulle ya tashi a hankali zai fice Haj. Manga ta girgiza masa kai tare da ɗaure fuska. "Eh kakana ne." "To ku taho HS Clinic bashi da lafiya." Bai jira ya amsa ba ya katse kiran. Jamal hankali a tashe ya faɗawa Nanna. Da kanta ta cizge drip din hannunta ta tashi da sauri duk ta gigice. Mammalo na ganin yadda suka fito da gudu-gudu ya tado direban Baffa. Jamal ya karɓe mukullin saboda yi masa kwatance ma bata lokaci ne. Su huɗu suka ɗunguma zuwa asibitin. Suna fita layin Alh. Audi ya hangosu ya umarci direbansa da bin bayansu. Wani irin murmushin ƙeta Alh. Ari ya saki don ya tabbatar an cika umarninsa. A guje Haj. Manga take bin bayan likitan da ya tarbesu a reception. Yana ganinta ya ganeta. Bayani yake mata da sauri yana jagorantarsu zuwa hanyar dakin theatre da aka shiga da Baffa. A waje ya ce su tsaya yana zuwa. Hana kanta kuka ta yi ita kaɗai take faɗawa kanta cewa da ƙafafunsa zai fito. Baffanta jarumi ne a cikin maza, faɗowa daga bene ba zai masa komai ba. A ɗakinsu Tauhidat kuma ruwa ta nema Papa ya duba na fridge ɗin duka sunyi sanyi sosai. Saukowa ya yi ƙasa zai siyo a waje ya ga asibitin ya hargitse sai kai kawo jama'a suke yi. Daga kai ya yi sama ya hango Mammalo yana buɗe ƙofofin ɗakuna. Nemansu yake yi dama ya sanar dasu me yake faruwa. Ɗaga murya ya yi ya ƙwala masa kira. "Yauwa Fafa kai nake nema. Su Hajiya suna can an kwantar da Baffa." Zancen sai ya saukar masa bambarakwai, ya nufi hanyar da sauri. Shi kuma Mammalo zai sauko kamar ance ya kalli ɓangaren banɗakin sai ya hango fuskar direban nan ta madubin dake cikin banɗakin. Abin ya ɗaure masa kai sai dai muryar Tauhidat da yaji daga bayansa ta ɗauke masa hankali. Jiri ke ɗibarta tana dafa bango a sanyaye ta ce, "yauwa ni fa ince kamar muryarka nake ji." "Sauko muje Baffa ne ya hwado daga wannan hawan. Biyoni a sannu kema kada ki zame." Jiki a sanyaye ta isa gefen Haj. Manga wadda hankalinta ya kai ƙoluluwar tashi. Tsayuwa ce da babu mai ƙaunar yin irinta saboda tsananin fargaba da tararrabi. Suna wurin Alh. Audi da ɗan kanzaginsa suka iso. Ya yi mamaki ƙwarai da yaji abinda yake faruwa daga bakin maaikatan da suka yanyame shi kamar ƙudaje. Likitan da Haj. Manga ta fara gani ne ya fito yana saɓule safar hannunsa da ta ɓaci da jini. Ganin mutane da yawa ya saka shi jin nauyin maganar da dole sai ta fita. Kallon da take masa kaɗai ya ishe shi sanin sanarwar ba za ta zo da sauƙi ba amma ya ya iya. Alh. Audi ya nufa ganin shi namiji ne. "Alhaji ya ku ke da mutumin da..." A ƙagauce Haj. Manga ta ce,"babana ne, ni za ka yi wa bayani." Iska ya furzar daga bakinsa sannan ya ce, "sai dai kuyi haƙuri amma..." "Dakata" ta ce da sauri bakinta yana rawa, gabanta na matsananciyar faɗuwa, "kada ma ka ƙarasa. Dana babban likita ne bari na kira shi sai ka yi masa bayani. Idan aikin yafi karfinku shi ba zai gagare shi ba. Ah to kakansa ne dole ya yi duk yadda zai yi ya tayar min da uba." Wayarta ta ɗauko kowa na wurin jikinsa ya yi sanyi ciki kuwa harda Alh. Audi. Tauhidat da Jamal kuka suke yi sun riga sun san me mutumin zai ce daga yanayin fuskarsa. Arƙam na tuƙi wayarsa ta sanar masa Nanna ta kira shi. Earbud ɗinsa ya danna tare da ajiyar zuciya "Nanna me yake faruwa na kasa samunku tun jiya?" "Muna asibiti da Baffa ga likitan zai maka bayani sai ka faɗa musu abinda ya kamata suyi." Yana ji tana dakawa likitan tsawa saboda yaƙi karɓar wayar, "idan ba za ka karɓa ba ku fito min dashi mu tafi. Kuma a bani Nurse mai kula dashi kafin mu isa zan biya komai." Tausayi ta bashi sosai. Hawaye take yi ya jika gaban laffayarta batare da saninta ba. Gyaran murya ya yi anyi carko-carko ana kallonsa. "Patient ɗin ya fado daga bene ne ya samu TBI (traumatic brain injury)." "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. How severe is it?" Arƙam ya ce a lokacin da ya yi wani parking ɗin gaggawa a gefen titi. "Bruised and bleeding (ya ji rauni kuma yana zubar da jini a ƙwaƙwalwa) ina fata ka fahimceni." Ya ce a sanyaye sannan ya miƙa mata wayar. Haj. Manga na karɓa ta ce, "yauwa ka dai gane bayanin nasa ko? Ka yi mana booking ɗin komai a asibitinku idan babu jirgi yau gobe zamu taho." Runtse idanu ya yi wasu hawaye masu ɗumi suka wanke masa fuska, "Kiyi hakuri kinji Nanna, Baffa is no more (Baffa babu-ya rasu)." Sakin wayar ta yi ta nufi ɗakin gadan-gadan sai da Jamal ya riƙota da sauri. Tana ƙoƙaarin fizgewa cikin kuka take cewa "kana jin yayanka ko? Baffan nawa ne zai tafi ya barni? To waye kuma ya rage min? Ban san zafin maraici ba Jamal sai yanzu da girmana. Idan ya tafi waye gatana?" Ƙanƙameta ya yi ya toshe mata baki da hannunsa "kada kiyi saɓo Nanna, ki yi shiru." "Hala baka fahimceni ba? Baffana, Baffana babu. Hafsatu ta rasa bangon jingina." Kuka wurin harda Papa Abayomi. Tauhidat jikin bango ta samu ta durƙushe tana nata. An rasa mai rarrashin wani ya daure ya ce, "haƙurinki na yanzu shi ne ladanki." Wani irin kallo ta yi masa na tsana da ƙyama. A dalilinsa da ƴarsa Baffanta ya taho Abuja sannan zuwa wurinsu ya yi ajalinsa. Ita kuwa me za ta sake yi da waɗannan mutane? Alh. Audi da bata san ma yana wurin ba ya katse mata tunani da cewa tazo a kaita gida gobe sai a ɗauki gawar zuwa Maiduguri. Idanun nan nata kamar gauta ta ce "yanzu nake son tafiya dashi. A nema min jirgi don ba zai kwana a garin nan ba." Kwantar da murya ya yi saboda ganin idanun jama'a ya kalli agogonsa "kinga tara ta kusa dare ya riga ya yi." Wata irin tsawa ta daka masa wadda ta tsorata duk waɗanda suke wurin "kuɗin na ubanka ne da ba za ka fitar ka yi min shatar jirgi ba? Dukiya dai ta uban ƴaƴana ce to na ce a ɗauki ko nawa ne a nemi jirgin da zai kaini garinmu a yau ɗinnan." Kallon-kallo aka yi a wurin an kasa fahimtar inda maganarta ta dosa. Shi kuwa Alh. Audi zawo mai suna zawo ne ya tsirga a cikinsa sai da ya yi ta maza ya iya damƙe shi a mazaunansa bai bari ya feso ba. Idan ba dai mugun mafarki yake yi ba da sai ya ce da kunnuwansa ya ji tana zancen kuɗinsa nasu ne. Me yake shirin faruwa? Babu hannunsa a mutuwar Baffa to me zai sa asirinsa ya tashi tonuwa ko binne gawar ba ayi ba? Gumi na karyo masa ya ce, "Bari na fita nayi waya. Za a samu yanzu kuwa." Yana fita Papa Abayomi da Taihidat suka kalli juna. Dukkansu tunaninsu ɗaya wato sirrin ɓoye zai fito fili. Hannunta Haj. Manga ta kama har ta soma jin sanyi a ranta sai gani ta yi ta kaita gaban mahaifinta. Fuskar nan babu salama ta ce, "idan mu kaɗai muka rage a doron ƙasa Abayomi ka sani ba zan sake ko da kallon ƴarka ba bare nayi mata magana. Akanku yau na rasa babana. Saboda ya daidaita tsakaninmu ya zo asibitin nan ashe na turo shi ga ajalinsa ne. Ku zauna a ƙarƙashin inuwar wanda ya fini arziki har ranar sakayya ta gifta tsakaninmu." "Nanna" Tauhidat ta ce wani irin ƙunci mara misaltuwa na ratsa zuciya da duka sassan jikinta. Bata tanka mata ba suka fice ita da Jamal da ko waigenta bai sake yi ba. A wurin suka sake fashewa da kuka daga ita har mahaifinta. Ba don rasuwar Baffa ba kaɗai harda leƙowa da komawar farincikinsu na ganin Nanna ta soma tuna me yake faruwa. Mammalo yana nasa kukan ya hango direban da ya kawo Baffa asibitin a mota. Inda ya hango shi dazu ne ya fado masa ya tafi da niyar tambayarsa laɓen me yake a banɗaki sai ya ji muryar Alh. Audi yana magana ƙasa-ƙasa. Burki ya takawa ƙafarsa saboda maganar ta yi girma sosai. "Nayi maka rantsuwa babu hannuna a mutuwar mutumin nan me kuma ka ke so na ce?" Daga ɗaya ɓangaren Oga ya yi murmushin da ya tsaya iya fuska banda murya ya ce, "to dai gashi da bakinka ka faɗa min abinda ta ce a bainar jama'a. Yau sai na kwana aiki don shafe tasirin zancen daga ƙwaƙwalwasu." Tsawa ya yi masa "Ita kuma ya zan yi da ita? Dukiyar nan ko zan mutu ba zan bada ba. Ka san yadda zaka yi dani." Tsawar ce ta ƙara ɓata masa rai daga cikin abubuwan da yake yi masa ya ce, "Ina tsammanin ka manta waye a saman wani tsakanin ni da kai ko Audi? Idan ka tuna sai ka neme ni muyi shawarar yadda zamu ɓullo musu" "Tsinannun mutane. Idan zanyi tsafi da ƙasusuwan iyayena dake rami zan yi in ga har abada babu wanda ya sake tunawa da cewa dukiyar magada ce nake kai." Ya furta a zafafe. Yawu mai masifar ɗaci Mammalo ya haɗiye da sanda ya lallaɓa ya yi baya, zuciyarsa na luguɗe a ƙirjinsa. [2/23, 7:34 PM] Nasma: Daga cikin banɗakin falon karɓar bakinsa muryar Alh. Audi ke fitowa, "Ina jinka, me ka ke cewa a waya? Ɗan ƙaraso daga bakin ƙofar nan." Labarin da Alh. Ari ya kawo ba ƙaramin daɗi ya ji ba wurin samo shi. Tun a wurin da aka yi masa bayani ya kira Alh. Audi ya faɗa masa. Shi kuma sai ya buƙaci yazo gida ya same shi saboda ya soke komai yana hutawa sai an gama biki nan da kwana goma sha shida. Tashi ya yi kuwa yana sauri kamar wani zai riga shi zuwa kai labarin. Ƙofar a dan sakaye take ba ya iya hango cikin sosai. Sai da ya matso kusa ya ɗan tura bakinsa saitin ƙofar da kyau. "Ban sani ba ko ka tuna ranar da ka faɗawa Shamsu ka aura masa Tauhida a Maiduguri da furucin da ya yi." Zuciyar Alh. Audi tafarfasa take bayan ya gama cika bahon da ruwa ya daure ya ce, "wane furuci ya yi?" "Kana cewa ka aura masa ita ya ce ya saketa." "Au wannan? Kada ka damu ba matsala bace akwai sauran igiyoyi biyu." Haɗa hannuwa Alh. Ari ya yi, ya shirya sakin gurnetin tarwatsawa Alh. Audi shiri. "A'a fa Alhaji saurara kaji. Tun ranar maganar ta dameni shi ne na yi tattaki zuwa wurin wani malamin da na san baya kauce hanya." Yana daga bakin ƙofar ta ciki ya ce, "sai ya ce me?" "Babu sauran aure tsakaninsu kamar yadda ka ke zato. Tunda bata tare ba saki da kalma ɗaya daidai yake da datse duk wata igiyar aure a tsakaninsu. A yadda ya ce kuma na gamsu shi ne mace ba a mayar da ita sai tana cikin idda, ita kuma ka ga babu iddarsa a kanta ko?" Alh. Audi bude ƙofar ya yi suna fuskantar juna. Idanunsa sun ƙanƙance sosai saboda masifar da ke cinsa ya fizgo shi ciki da ƙarfi. Bai tsaya ko ina ba sai jikin bahon nan da ya cika da ruwa ya danna Alh. Ari har zuwa rabin ƙirjinsa. Kokawar ƙwacewa ya soma azabar rashin numfashi da ruwan da ya fara sha don dole ya addabe shi. Gwuiwa Alh. Audi yasa ya danne bayan shi, sannan ya haɗa hannuwansa biyu yana tura masa kai. Idan ya ga ya soma galabaita sai ya ɗago shi bayan sakanni kaɗan ya kuma mayar dashi. Alh. Ari ya ga izaya ganin ido don sai da karfin kwatar kai ya gagare shi. Sunyi haka sau shida sannan Alh. Audi ya yasar dashi a ƙasan banɗakin. Da yatsa ya nuna shi, cikin fuskarsa kamar bai taɓa sanin me ake nufi da murmushi ba "Wato Ari iya zamana da kai ban taɓa nuna maka Audi karen maguzawa ba ko?" Shiru ba amsa, sai tarin da yake yana fitar da ruwa ta baki da hanci. Tsorata ƙarshe dai ya yi don bai taba sanin zai masa haka ba. Gefen bahon Alh. Audi ya samu ya zauna, yana matse hannun rigarsa da ya jike. Magana ya cigaba tamkar komai lafiya ba wani abu da ya faru, "na kula ka sakawa jama'ar gidan nan ido fiye da ni maigidan. A abinda na kula ko tusa aka yi a cikin gidan nan kana sanin waye ya yi, da ƙarfe nawa ya yi da kuma tsayin lokacin da sautinta ya ɗauka yana fita." A wahale, idanu a waje sunyi jazur Alh. Ari ya ce, "me na yi?" "Da farko Haj. Manga ce mudubinka. Duk motsinta ka sani kana bibiya kamar kai ka aura min ita. Yanzu kuma abin ya koma kan furucina ko na tilon ɗana. Kada ka yaudari kanka waɗannan yaran na Fanna bani da tabbacin nawa ne duk da yanzu ta dena yawo. Na dai riƙe ne kawai don na kyautata maka. Idan na ce Shamsu mijin Tauhida ne to magana ta zauna a haka." Da sauri Alh. Ari ya dinga gyaɗa kai yana cewa, "to Alhaji." "Shamsu ba wani ilimin addini gare shi ba saboda haka ba zai taba sani ba. Kai dai ka kama bakinka. Kuma daga yau babu kai babu mutan gidana." Da taimakonsa Alh. Ari ya tashi a tsorace suka koma falo. Tafiya ma ya so yi saboda fargaba amma don rainin wayo sai Alh. Audi ya ce wai ya zauna su yi shawarar yadda zasu ɓullowa lamarin auren. "Alhaji ni me zan ce?" Cewar Alh. Ari baki na rawa. "Kuma fa da gaskiyarka. Ko ni aka yi wa wanka irin wannan zan kama bakina. Abinda za ayi shi ne zan sanar dashi cewa kada ya kuskura ko yatsanta ya taba. Malamin ya ce idan ya bari wani abu ya haɗasu to har abada ba zai warke ba kuma jama'ar gari zasu san lalurarsa." "Hakan ma ya yi. Ka ga idan anyi haka za ka tsare zuri'arka daga samuwar ƴaƴan zina." Murmushi ya yi, "ashe har ka yi wannan tunanin?" Matsawa baya ya yi ba shiri kada a sake damƙo shi, "manufata dama..." "Kada ka damu na gane. Abinda ya faru alheri ne a gareni. Yarinyar dama ba sonta nake ba musamman da za ta iya kawo min matsala a gaba. Gara ta zauna a haka ƙarƙashinmu tana tunanin da auren." Alh. Ari dai beben dole ya koma a wurin. Bayan Alh. Audi ya gama yanke shawarar abinda zai faɗawa Shamsu ya kira Fanna ta ɗaukowa mahaifinta kaya a cikin nasa, wai zamewa ya yi a banɗaki ya faɗa baho. *** Abin haushi da takaici a wurin Susu shi ne dawowarta daga gidan Maibindi babu ƴar tsaraba. Sanannen abu ne duk wanda yaje gidan boka yakan dawo da dan ƙullin magani ko guru ko laya. To ita haka taje siƙau ta dawo bai bata ba kuma bai karɓa ba. Maganganun da ya faɗa mata a matsayin matakan karkato da hankalin Shamsu cikin ƙanƙqlanin lokaci ta rainasu. Idan ma bata raina ba tabbas bata musu kallon hanya mai ɓullewa. Ƙwafa ta yi cike da bacin rai 'wato mutumin nan so ya yi ina zuwa a kamani ko a harbe' ta ce a zuci. Haƙuri ta ɗauko ta ɗorawa zuciyarta inda ta yi niytar rungumar ƙaddadarta ta auran Walid ta huta. Cikinsu lefenta aka fara kawowa wanda ya ɗan sanyaya mata zuciya. Akwatuna biyar da kit shakare da kaya na gani na faɗa harda dan setin gwal. Kuma abin burgewa Walid ya canja mota ya sayi jeep. Kanta ya yi gingirin ya ƙara girma ta shiga hura musu hanci. Da kanta ta farfaɗo da zumuncin nasu da ya suma tunda ta sami abinda take so. Sai dai kuma kamar haɗin baki cikin sati guda dangin Dr. Farouk da Abdulaziz mai auren Minasco suka aika nasu. Duka akwatuna seti biyu ne guda takwas. Kayan ciki suka janyo mata raina nata. Aisha ance a sababbin gidajen quarters ɗin malaman makarantarsu za ta zauna ita kuma Minasco gidajen maaikatan CBN na Abuja. Walid ma ya sami nasa gidan mai hawa biyu har dangin Susu sun je sun gani ana ta zuzuta kyaunsa. Tsautsayi da ba a sa masa rana, ana saura sati biyu bikin nasu aka sace masa mota harda kuɗaɗensa da suka haɗa da cikon kuɗin hayar da ya karɓo a banki zai bayar. Wannan mummunar ƙaddara ta taɓa tattalin arziƙisa ba kaɗan ba. Ya nemi da a soke dinner ɗin da ya shirya zai ɗauki nauyi sannan ya canja musu gida da ƙarami. Sai da ya gama komai ya faɗa mata. "Kafin Allah Yasa komai ya daidaita sai mu fara zama a wanda na kama yanzu. Ki sanar a gida sai a kaisu su gani." Tunda ya soma magana yatsun hannunta kawai take kallo taƙi ɗago kai. "Suwaida baki ce komai ba. Ki kwantar da hankalinki komai zai daidaita in sha Allahu. Ba ƙaramin taimakona Abdulaziz ya yi ba wurin samun gidan nan." Kai taɗago da sauri,"wane Abdulaziz ɗin?" "Na Minasco ɗinki mana. Gidansa ne inda ya zauna da ya gyara da nufin idan sun zo gari su dinga sauka. Ko kwandala bai karɓa ba ya ce mu zauna kafin ...." "Ahhhhhhhhh" Susu ta ƙwala ihu iyakar ƙarfinta. Walid ya tashi da sauri yana duddubawa ko wani abu ne ya sameta a wurin. Mama da Iyalle da yayunta biyu a guje suka fito suna ture juna. "Mene ne? Wani abu ya cije ki ne?" Walid yake tambayarta lokacin da suka fito hankalnsa a tashe. Kuka kamar ana yankar naman jikinta ta fashe dashi. Bata san yadda za ta kwatanta ɓacin rai da baƙincikin da take ciki ba. Kwalar Walid ta riƙo da ƙarfi tana masifa. Saboda kukan yaci ƙarfinta da ƙyar take iya haɗa kalmomi tana magana. "Ni zaka wulaƙanta ka ciwa mutumci a cikin ƙawayena? Yanzu Abdulaziz ɗinne ya baka gida ka karɓa saboda baka san darajar kanka ba? Yaushe ya yi kuɗin da har zan zauna a gidansa. Salon a dinga cewa alfarmar Minasco nake ci? Wallahi Walid ko ka nemi wani gidan ko na fasa auren..." Tana dire maganar hannun Mama na sauka a kumatunta. Ko gezau ta cigaba da zazzaga masa masifa. "Salihu zane min ƴar banzar yarinyar nan" Mama ta ce a fusace. Wannan baƙin hali na Suwaida na ci mata tuwo a ƙwarya. Dama a ciki yake da ita yayan nasu ya zare belt ya soma sauke mata a gadon baya. Iyalle na cewa ya ƙyalleta Walid ma yana ƙoƙarin janye shi amma bakinta yaƙi mutuwa. Sai da ya tabbatar ta daku sannan ya jata ciki Mama kuma ta bawa Walid haƙuri. Da Alh. Musa ya dawo aka faɗa masa shi ma ransa ya sosu. Faɗa ya yi mata sosai akan abinda ta yi. Iyalle kuwa ta kada baki ta ce, "Yarinya fa da gaskiyarta. Yanzu a ce Aminan da suka tashi tana taimakawa harda kwancen kaya ita ce wanda za ta aura zai basu gida kamar almajirai?" "Iyalle ba haka rayuwar duniyar take ba? Yau gareka gobe ga waninka. Meye aibu don ya basu gida. Na tabbata albarkacin kawancenta da Amina ya duba banda haka a ina zasu san juna." "Ana ƙasƙantar maka da ɗiya ka kasa gani? Ni dama Walid ɗin nan bai wani kwanta min ba." Iyalle ta ce tana tura baki. Ba don uwa uwa ba ce da Alh. Musa bai san maganar da zai faɗawa Iyalle ba. Walid ba ɗan masu kuɗi bane sai zafin nema. Shi yake ɗawainiya da iyayensa da ƴan uwa. Kafin Abdulaziz ya bashi gidan saboda sanin halin Susu na son burgewa zuwa ya yi ya nemi alfarmarsa da a ɗaga a ƙara masa wata biyu. Tausayin yaron yaji ya masa alƙawarin kama masa gida su ci su cinye a junansu babu mai ji. Ɗazu da rana ya kira ya faɗa masa yadda suka yi da Abdulaziz da ya kira ya yi masa jaje. To ina laifi don yana son kare martabarsa kada ya zamana baban amarya ne ya kama masa gida? Da kuka Susu ta kwana da ciwon kai saboda tunani. Idan ta bari aka yi auren nan haka girmanta ya gama zubewa. Ta gwammace ace wani ne ya bashi gidan da dai ace Abdulaziz ɗin Minasco. Ƙarfe takwas na safe babu wanda ya fito tsakar gidansu kowa na bacci ta lallaɓa ta yi waje. Daga ita sai kayan jikinta da dogon hijab har ƙasa sai kuɗin mota ta nufi tasha. Motar farko mai zuwa Abuja ta yi shahadar ƙuda ta shiga. Idan shawarar Maibindi ta ci ayi nasara. Idan bata ci ba kuma ta yi ƙaryar hauka. *** Daga tasha ta yi shatar mota ta ce ya kaita gidan Alh. Audi Karam. Kwanaki biyar suka rage a fara bikin Shamsu da Tauhidat a lokacin. Direban mota ya yanko kuɗi ta damƙa masa ya hau titi. Yanayin unguwar kaɗai ya tsinka mata zuciya, tunda ta fara cin karo da manya-manyan gidajen alfarma. Tana shawarar ta je ko ta koma sai ji ta yi ɗan tasi ya ce Hajiya mun iso. Wani hatsabibin sauti cikinta ya bada na tsoro da ta kalli tafkeken gate ɗin gidan. Baki na rawa ta ce, "kai maidani tashar da ka ɗaukoni." Juyawar da ya yi zai mata magana gate ɗin gidan ya fara buɗewa da kansa. Idanunta ƙyam suka sauka akan Tauhidat dake zaune a gaba da wani matashi a gefenta yana tuƙa motar. "Bi bayan waccan motar." Yana tada motar zai yi kwana wata motar ta sake fitowa daga gidan a guje. Gani ta yi kamar Shamsu amma babu tabbas tunda sau ɗaya ta taɓa ganinsa a jarida. "Waccan mai gudun za ka bi." Ta ce da sauri. "Ya haka ne? Ta farkon ko ta biyu ki zaɓi ɗaya." Hankalinta ya yi gaba saboda ya kusa ƙurewa ganinsu ta ce, "ta biyun, ka yi sauri." A guje ya fisgi motar yana ta sharara gudu kamar yadda Shamsu yake yi. Tafiya suke shiru bai tsaya ba har direban yana faɗa mata cewa duk abinda ya nema na kuɗi shi za ta biya. A ranta ta ce 'idan anyi nasara ba, idan ta kwabe in maka sharrin satoni ka yi.'

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull