Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 14
Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 14: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 14. *** Hanyar fita gari Shamsu ya ɗauka sai da ya yi nisa sosai ya tsayar…
6,005 words
*** Hanyar fita gari Shamsu ya ɗauka sai da ya yi nisa sosai ya tsayar da motar ya ɗora kai akan sitiyari yana hawaye. Ranar da ya wayi gari da labarin rasuwar Innarsa a ranar ya kamu da wannan muguwar lalura da taƙi jin magani. Rayuwa yake ba don daɗi ba a dalilinta. Babansa ya aura masa yarinyar da ko inuwarta ba ya ƙaunar gani amma har yanzu kusan wata uku shiru ka ke ji. Kuma wai a haka ya ce masa ko hannunta kada ya taɓa saboda idan ya haihu da ita komai zai ƙara lalacewa. Ina ake so ya sa ransa yaji daɗi ne? Sai yaushe ne zai samu waraka ya shiga cikin abokai kamar yadda matasa sa'aninsa suke yi? Ya zurfafa a tunani kamar daga sama yaji ana ƙwanƙwasa masa gilas ɗin mota. Ko da ya dago kai idanuwansa jiƙe suke da hawaye suka sauka cikin na Susu. Tsayin minti biyu tana tsaye a jikin motar tana kallonsa ta gama matso nata hawayen ƙaryar sannan ta taɓa gilas ɗin. Idanuwansu suka sarƙe da juna kowa da hawayensa. Shi ya fara katse shirun ya sauke gilas ɗin. Ya yi gyaran murya ya ce, "Lafiya ko?" Wasu sababbin hawayen ta goge sannan ta miƙa masa wani envelop ta koma gefe ta rakuɓe bata ce komai ba. Ya bude zai duba direban da ya kawota ya shiga danna horn da ƙarfi. Shamsu da bai ƙaunar hayaniya ya fita daga tasa motar cikin fushi. "Baka da hankali ne?" "Kuɗina za'a bani. Ta ce bata da su kaine mai biya. Dubu uku ne a bani na tafi." Kallon sannu da ƙarfin hali Shamsu ya yi mata, ta sunne kai da munafukan hawayenta. Ƴan ɗari bibbiyu ya zaro daga aljihunsa bai ƙirga ba ya watsawa mutumin. Yana haɗa kudin ya ja motarsa ya barsu a wurin. Titi ne na wajen gari duk motar da za ta zo wurin a guje take zuwa ta wuce. Bai kulata ba ya koma mota ya buɗe envelop ɗin. Pre-wedding pictures dinta da Walid ne kala biyar ya fara cin karo dasu. Yana kallonsu ya ƙara kallonta. Tana da kyau ya ce a zuci sannan ya buɗe wasiƙar da ta rubuta tun daren jiya. (Ni da kai bamu san juna ba amma wani abu da ya tsallake tunanina ya turoni gareka. Ban san da me zan kiraka ba. Ƙaddarata ko Kasadata. Kamar yadda ka ke gani a hoto saura sati biyu bikina. Kwatsam sai nake yawan mafarki da wani da ko mai kamaninsa ban taɓa gani ba a zahiri yana roƙona da na taimaka masa. Tun ina ɗaukar abin wasa ya zamana ko yaya na rufe ido shi nake gani. Halin da na shiga na firgita yasa babana kiran malami ayi min karatu. Shekaranjiya aka ce bayan anyi karatun anji na amsa da muryar da ba tawa ba. Ban taɓa sanin ina da aljanu ba sai ranar. Wadda ta yi magana ita ta turoni gareka. Ta ce ni da Shamsuddeen Audi Karam ƙaddararmu ɗaya ce. Kana tare da rashin lafiya tun kana ɗan shekara goma sha shida kuma aurenmu ne kaɗai zai magance maka ita. Ta daɗe da sanin makarin cutarka yana gareni amma bata bayyana ba saboda tana tunanin lokaci zai haɗamu. Yanzu ta zo ne saboda anyi maka aure da wadda idan bakayi sa a ba wannan cuta har tsufanka. Ba da sanin iyayena na taho ba. Tunda suka ji suka dage sai an aura min Walid ni kuma ka ƙi barina kullum ina ganinka. Don nace zan taho babana ya zane ni...) Kasa ƙarasawa ya yi saboda ƙwallar idonsa. A iya saninsa duk duniya daga shi sai babansa da Alh. Ari suka san lalurarsa. Mai neman kuka an jefe shi da kashin awaki. Yadda ya matsu ya warke babu abinda ba zai yi ba. Ji yarinya nutsatsiya mai cike da kamala da Allah Ya kawo masa. A bakin titin ya yaye mata hijabin sai ga shatin duka ɓaro-ɓaro inda Salihu ya zaneta. A wannan lokacin kuma Maibindi ya buga wani kasko da ƙasa. A take soyayyar Suwaida mai zafi ta sarƙi zuciyar Shamsu. Hannunta ya kamo ya matso da ita jikinsa suna shaƙar numfashin juna. A firgice take matuƙa tana jiran ya shaƙeta ko ya turata titi mota ta taketa. Hawayen gaske ta saki gabanta na faɗuwa sai ji ta yi yasa yatsansa yana share mata hawaye. A hankali ya ce, "Ya ya sunanki?" "Suwaida" ta ce da ƙaramar murya. "Suwaida zaki iya aurena? Zan biyaki ko nawa ne domin na warke daga lalurar da nake fama da ita." Daga hawayen tsoro sai na dadi suka maye gurbinsu inda ta dinga aikawa da Maibindi godiya a zuci. "Zan aureka Sham ko da iyayena da duka duniya zasu ƙi yarda." [2/23, 7:34 PM] Nasma: *Leda ya taka bai sani ba ƙarar fashewarta ta fargar da Alh. Audi cewa akwai mutum a kusa. Mammalo bai bari tsoro ya yi tasiri a zuciyarsa ba kada ya kaishi ya baro sai kawai ya fito daga maɓuyarsa da ƴar nokiyarsa 3310. Tuni ya ɗorata a kunne yana risgar kuka na fitar hankali. "Ina hwada miki Yaya Uwani daga saman bene aka ce ya dinga gangarowa har ƙar. Don baki ga yadda jini ya malale a wurin ba. Sai ya tuna min da Jarmai magini. Kin san hima an ce irin haka ce ta samai ko shurawa bai ba." Da Alh. Audi ya ji zancen yaƙi ƙarewa kuma ya fuskanci bai ji shi ba sai ya bar wurin zuwa inda yake hango Alh. Ari. Bayan wata mota Mammalo ya samu ya durƙusa yana mayar da numfashin tsira a lokaci guda ƙwaƙwalwarsa ta nausa birnin tunani. Shi kaɗai kamar zautacce yake magana a hankali. "Cabdijam, wato akwai abinda idanu basa gani a tattare da mijin Hajiya. In ba haka ba ba faɗa me ya kawo gaba? Idan bashi da masaniya me yasa yake cewa babu hannunsa a rasuwar babanta?" A hankali ya ɗago kansa ya hango Alh. Ari da Alh. Audi suna ta maganganun da baya iya ji daga inda yake. A take ya tuno tsawar da Haj. Manga ta yi masa a ciki tana cewa kuɗi na uban ƴaƴanta ne. Ɗora hannu ya yi a kansa yana juyayin wannan lamari da ya yi masa dabaibayi, "To ko wannan kuɗin da ta yi magana akai naji yana cewa ba zai taɓa badawa ba?" Sunansa da yaji ana kira ne ya tayar dashi a firgice. Direban Baffa ne ya sha nasa kukan. Shekaru sama da ashirin suna tare tun yana matashi. Sunyi jiran sama da awa biyu kafin Haj. Manga ta haƙura ta fito saboda ana ta bata baki akan ta jira sai da safe a tafi dashi. Dr. Samson Madaki ne ya iya shawo kanta. Ba ƙaramin bugunsa mutuwar ta yi ba. Kafin Baffa ya taho nan ɗin dazu sun jima suna tattaunawa akan lamuran gidan Alh. Audi. Ashe sallama suke yi bai sani ba. Shi Haj. Manga ta wakilta ya kira babban ɗan Baffa wato Ali ya sanar dashi rasuwar. Nan da nan zance ya bazu lungu da saƙo kuwa. Kafin wayewar gari duk wani wanda ya kamata ya san wannan mummunan labari ya same shi. Umma sumanta uku don ƙarshe ma ruwa aka saka mata tare da magungunan bacci. Dada ta haɗa kan ƴaƴanta baki ɗaya da Haji Lawalli wanda ya taho da matansa su biyu suka kama hanya da asubar fari. Kamar yadda ta buƙata hayar jirgi Alh. Audi ya ɗauka aka sako gawar a ciki. Sun isa Maiduguri takwas ta ɗan gota. Kai tsaye unguwarsu suka nufa layin Justice Umaru. Cincirindon mutane ba a cewa komai saboda tsabar yawansu. Da ƙyar motocinsu da ambulance din da aka turo daga wani asibitin gwamnati wadda ta ɗauko shi suka iya wucewa. Bawan Allah mai halin gaskiya da amana ko da rai ko babu yana cikin zuƙatan mutane. Koke-koke kawai ake ji yayin da ƴaƴansa da kansu suka ɗauki gawar mahaifinsu zuwa cikin gidan domin haɗa shi. Zuƙata sun raunana matuƙa a wannan rana. Umma da Haj. Manga sun zabge lokaci guda. Surukan gidan da jikoki ne ke iya taɓuka wani abu, suma ɗin a sanyaye. An shirya yin jana'izar ana idar da sallar azahar saboda ƴan uwa da abokan arziƙi na nesa da suka roƙi alfarma. Cikin waɗanda suke hanya tun safiyar ranar kuwa harda Papa Abayomi da Tauhidat. Shatar mota ya ɗaukar musu domin indai ba shi ma ya dena numfashi ba baya tunanin akwai abinda zai hanasu zuwa sai ikon Allah. Tafiyar tasu a wahale aka yi ta. Tsayuwarsu tafi shida Tauhidat tana amai. Gabaɗaya jikinta ya ƙarasa rikicewa tun bayan furucin Haj. Manga a gareta jiya. Shaɗaya suka isa unguwar amma a can bakin titi aka saukesu saboda rashin hanya. A haka Papa ya riƙota tana layi kamar za ta faɗi suka ratsa mutane zuwa ƙofar gidan. Wata mata da bai san ko wace ce ba ya roƙi alfarmar ta shigar da ita ciki wurinsu Umma ta yi musu ta'aziyya. Shi kuma ya koma inda ya hango su Mammalo da sauran ma'aikatan gidan a zaune. A hanyar babban falon gidan inda su Umma suke wata jikar Baffa da suke shiri sosai da Tauhidat ta gansu da matar nan. Da sauri ta ƙarasa ta riƙota suka shiga ciki tana mata sannu domin kana ganinta kaga mara lafiya. Wurin Haj. Manga ta kaita tunda basu san me yake faruwa ba. Haj. Lami wadda ita ma basu daɗe da isowa ba ita ta zaunar da ita. "Nanna jikin Tauhida ya yi zafi sosai ko dai asibiti za a kaita?" Ta tambayeta ganin kamar bata kula da zuwansu ba. Da yake abinda ke gabanta yanzu yafi ƙarfin fushinta kuma ga idon mutane sai ta miƙa hannu ta janyota jikinta. Allah Sarki kamar jira take, nan take ta fashe da wani matsanancin kuka ta ƙanƙame Nannanta. Hannun Umma dake rawa taji a cikin nata, cikin muryar da ta riga ta dashe ta ce, "Yi shiru Tauhida, ba a son yawaita kuka ga mamaci. Baffanku yau addu'a yafi buƙata daga duk wani masoyinsa." Wannan kalamai sun sake tsuma matan dake wurin aka cigaba da share ƙwalla, har zuwa lokacin da aka buƙaci iyalan Baffa Alƙali da suje suyi masa addu'a za a fitar dashi. Babu mai imanin da ba zai tausaya musu ba musamman Haj. Manga. Tunda ta kifa kai a jikinsa ba ita ta ɗaga ba sai da kowa ya fita. Hawaye ya kusa ƙafe mata tun tana kukan ana ganinsu har ta koma ajiyar zuciya kawai. Alh. Ari ba kunya ya shiga zugar ɗimbin jama'ar da suka zo domin kai Baffa gidansa na gaskiya. Daga nan yake son ɗora nasa aikin domin cimma burinsa na mallakawa jikokinsa kafatanin dukiyar da ta haramta ga ubansu. Gwamnoni uku ne suka sami halartar jana'izar ciki harda na Borno da kuma manya manyan alƙalai. Bayan isha gidan har lokacin a cikensa yake Jamal ya leƙo inda matan suke ya kira wata ƙanwarsa ƴar wajen daya daga cikin kawunnansa. "Kirawo min Tauhida." Murmushi ta ɗanyi na sha'awar dangantakarsa da Tauhidat. Hankali da nutsuwarta yasa cikinsu babu mai nuna mata ƙyama. To ko bata da hali basu isa su muzanta abar son Nanna ba. "Idan ta zo ka tilasta mata cin abinci. Tunda ta shigo ko ruwa bata sha ba a iya sanina." "Okay" Ya ce ba wai don bai damu ba. Damuwar ce ma baya son yi saboda bai manta halin da suka saka masa mahaifiya ba. Yanayin da ya ganta ya matuƙar tayar masa da hankali har yaso mantawa da gargaɗin Nanna. Ƙanwar tasa ta rame da gaske ba faɗawa da bahaushe kan faɗa ba. Haɗe rai ya yi da ta iso ya miƙa mata wayarsa. "Arƙam zai kira ki. Ki tabbata baki yi wani abu da zai sa ya gane halin da ake ciki ba. Idan komai ya lafa na rasuwar nan za a sanar dashi kinyi aure." Kifta ido ta yi hawaye mai ɗumi ya sauko mata. Ta manta da wani aure sai yanzu. Ciwon rabuwarta da Nanna ya shafe mata komai a kanta. Wani irin ruri na soyayyar Arƙam da bata taɓa sanin zuciya za ta ji ba ya damƙeta a lokacin. A sanyaye ta karɓi wayar da ta soma ƙara tana kallon fuskar Jamal. Wai yau ita ce ɗan uwanta rabin jiki wanda ko Shaheed bata shaƙu dashi kamar shi ba take ganin tsanarta a idanunsa. Harararta ya yi tabyi saurin ɗauke ido sannan ya ce, "ki ɗan kwantar masa da hankali don Nanna ta yi rantsuwar idan ya kuskura yazo sai ta saɓa masa. Tunda Dr. Madaki ya faɗa mata cewa impact (karfin buguwar) ɗin buguwar kan Baffa ya yi nuni da cewa turo shi aka yi da ƙarfi ba zamewa ya yi ba. Bamu sani ba ko surukinki ne yake harin rayuwarmu shi yasa ta ce ya zauna." Bata da wani kuzari sai gyaɗa kai da ta yi. Gefe ya matsa ya bata wuri ta zauna akan kafet da aka shimfiɗa a wajen ta takure jikinta. Sallamarta da yake ta jira ya ji a kunnuwansa. A take nutsuwa ta fara saukar masa ya zauna a kan kujerar falonsa. Cike da shauƙi da damuwar da ya rasa da wa zai raba domin ya ji sassauci ya ce, "Cuddles, I need you now more than ever (ina buƙatarki yanzu fiye da kowane lokaci). I miss you, Nanna ta hanani zuwa gida. Ki tayani roƙonta kinji. Tana buƙata ta a kusa amma taƙi amincewa nazo." Shiru ya ji sai shessheƙar kukanta da yake ƙara tayar masa da hankali. Hannunsa yasa ya rufe fuskarsa yana mai takaicin dalilin da yasa aka hana shi zuwa a lokacin da aka fi buƙatarsa kusa. "Cuddles." "Uhmmm" ta amsa da ƙyar saboda kukan da yake neman fin ƙarfinta. "Kiyi min magana. I am so lonely (kaɗaici ya yi min yawa)." Sai yanzu ta tuna ƙila fa maganarta ta ƙarshe kenan dashi. Kamar za a ƙwace wayar ta shiga cewa, "ba zan taɓa dena gode muku ba. Nanna, Jamal da kai..." ta numfasa hannunta ɗaya na share hawayen da suka ki dena zuba, "kun so ni kuma baku ƙyamaci matsayina a gareku ba." Mamakin kalamanta ya yi a wannan lokacin. Me ya kawo wannan maganar kuma? Ko dai saboda yadda mutuwar ta dokesu baki ɗaya ne take magana kamar bata cikin hayyacinta? "Na sani kuma zan so ki har numfashina na ƙarshe Tauhida." Idan ya barta haka me yiwuwa ta cigaba da shiga damuwa. Sai ya fara neman abinda zai haɗata dashi da zai zama kamar kawar da tunaninta daga damuwar da suke ciki. "Bari na baki aiki kafin muyi sallama. Na san dare ya yi kina buƙatar hutu." "Uhmhumm" kawai ta iya cewa. Duk fitar sautin muryarsa yana tafiya da wani ɓangare na zuciyarta ne. "Nanna tana buƙatarmu amma tunda bana kusa kece ni da ke a wurinta. Ki zama Arƙam ki zama Tauhida. Ki kular min da Jamal, yayan naki rago ne mai cika baki. Lastly, ki kular min da kanki. Kin san wani abu?" "A'a" Ya saki murmushi, "Haduwarmu ta gaba fa you will be Mrs Karam in sha Allah. Idan mun haifi namiji wane suna ki ke so?" "Sunan Baffa." Ta ce da ƙanƙanuwar murya. "Mace kuma Hafsa ko?" Ya faɗa yana ɗan murmushin tunanin yanayinta a lokacin. Ƙila tana nan tana rufe ido saboda kunya. Kuka ta fashe dashi mai sauti ta kasa bashi amsa. Rikicewa ya yi saboda yana yi ne kawai don ya rage mata tunani. Rarrashinta ya dinga yi har ta yi shiru. "Take care of our love Cuddles, bye." Kashe wayar ya yi da sauri saboda nasa hawayen zai fallasa raunin da zuciyarsa ta shiga. Me yasa Nanna za ta yi masa haka? A yanzu ne ya kamata ya kasance tare da ita yana bata kulawar da ta dace. Ya riga ya gama sanin cewa duk wani ƙarfin halinta saboda Baffanta yana tare da ita ne. A yau da babu shi yana tsoron kada maƙiyansu su gano cewa mace ce mai matuƙar rauni da buƙatar madogara. A gefe ɗaya kuma ga yarinyar da tunaninta yake tafiya da bugun zuciyarsa. A kullum yana godiya ga Allah da Ya haɗasu ta dalilin Nanna. Bai taba son wata mace kwatankwacin ƴar amanar Haj. Manga ba. *** Kamar wucewar iska haka kwanaki bakwai suka zo suka wuce aka share makoki. Da wuri su Fanna suka shirya bayan anyi addu'a. A gidansu na garin suka yi masauki har ma ta sauki wasu jama'ar Haj. Manga saboda cikar nasu gidan. Abinci aka jerawa su Alh. Audi a dinning table zasu ci su wuce. Kafin mahaifinta ya fito ta je ta same shi da ƙorafin rashin ganin Shamsu kamar bai san me yake faruwa ba. "To uwar kauɗi da kankanba ƴar baba na iya ina ruwanki?" Ta ji Alh. Ari yana cewa daga bayanta. Haɗe rai ta yi ita ma, "Daddy meye zai cinye shi idan ya zo ya yi gaisuwar rana daya? Surukin babansa ne fa kuma kakan Jamal. Ko don haƙƙin maƙotaka suna zama ga ɗaki ga ɗaki ai ya kamata..." "Sokuwa rufe min baki. Na kula matar nan ta daɗe da shanyeki kin koma hoto. Ina ruwanki da rashin zuwan Shamsu? Kinga fice ki haɗa kan yaranki ko zo ku tafi." Alh. Audi ta kalla, "banda kai a tafiyar?" "Ina jiran Shamsu ne zai zo ta'aziyyar surukinsa." Ɗan murmushi ta yi, "ka ga hakan ne daidai." Ta juya za ta tafi ta sake dawowa da sauri, "suruki ka ce fa, ko ba ta'aziyyar Baffa zai zo ba?" Alh. Ari kamar ya mangareta ya ce cikin faɗa, "idan da kara Marigayi ai kakan Tauhida matarsa ne." Su biyun ta dinga bi da kallon rashin fahimta. Alh. Audi ya murmusa, "na aurawa Shamsu ita idan na dawo kafin na tafi Kuwait sai mu yi maganar shirin biki. Ina son ayi komai a gama nan da wata biyu zuwa uku." A dimauce Fanna ta ce, "Shamsu na wajenka ka aurawa Tauhida ta wajen Haj. Manga?" "Eh kuma nace zaki jagoranci bikin ba." Daga murmushi sai ji suka yi ta kwashe da dariya. Abin dariya ta ɗauki zancen don ko da wasa bata tsammaci da gaske suke ba. Fita ma ta yi abinta ta ƙarasa shiri. Basu daɗe da barin gidan ba Shamsu ya iso yana ta cika da batsewa saboda tilasta masa zuwa da aka yi. Ba yadda bai yi ba akan baban nasa ya rabu dashi zai yi mata gaisuwa idan ta dawo amma yaƙi. Fuskarsa a gimtse kamar kullum ya gaishe da Alh. Ari sannan ya sami wuri ya zauna. "Naso ace cikin nutsuwa na sanar da kai abinda zan faɗa maka yanzu Shamsu. To amma ƙaddara ta riga fata. Wannan mutuwar da aka yi tasa za ka ji zancen babu ..." "Baba mene ne?" Ya katse shi cikin ƙosawa da zagayen da yake masa. "Na ɗaura auren maka aure da Tauhida." A zabure ya miƙe har yana kifar da dan ƙaramin tebur ɗin gabansa wanda aka ɗora kayan motsa baki. "Ni ka aurawa wannan yarinyar? To wallahi na saketa idan ma da gaske..." Tas Alh. Audi ya tsinke shi da marin da ya kusan ɗauke masa kumatu. Ransa a matuƙar ɓace yake Magana "kai ka fini ƙyamar ace na haɗa zuri'a da direban matata ne? Ba lafiya ka ke nema ba? Shekararmu nawa ina faɗi tashi akanka amma har yanzu shiru?" Hannunsa har lokacin a kumatu ya tambayeshi me yake nufi. "Wurin wani malami Ari ya kaini a Congo tun kafin zuwansu gidan. A lokacin ya faɗa min warakarka tana tafe idan tazo na haɗaku aure. Yadda ya kwatanta min yarinyar haka naga ƴar Abayomi sai dai ƙuruciya. Shi ne yasa fa ka ga na tura ɗan uwanta waje saboda daga martabarsu sannan nake janta a jikina. Yanzu ne daidai lokacin aurenku kafin ta fara jami'a idanunta su buɗe." Babu gamsuwa a irin kallon da Shamsu yake bin Alh. Audi dashi, sai dai kuma zai iya yin komai domin ganin ya sami lafiya kamar kowa. Zama suka yi suna ta ingiza shi akan ya amince da auren domin lafiyarsa ba don ita ba. "Aure dai kawai ake buƙata ko?" "Aure kawai, ta zama ƙarƙashinka shike nan. Idan kana so ma zan kaita wata ƙasar ta yi karatunta a can ba za ku dinga wani haɗuwa ba." Nan da nan ya sake ɗinke fuska, "ni banje wata ƙasar ba sai ita?" "To naji sai ta yi a Gwagwalada ita ma. Dama can suke nema basu san na sani ba." Amincewar da suke buƙata ya yi a ransa yana auna kalolin cin mutumcin da zai mata don yaji daɗin musgunawa Haj. Manga. Ɗaya daga ciki kuwa shi ne neman wani auren ya zamana lokaci guda ita da wadda ya samu zasu tare. Alh. Audi ne ya tuna masa da sakin da ya yi mata lokacin suna hanyar zuwa yin gaisuwa. "Igiya biyu ta rage muku. Idan ka kuskura ka ƙara sakinta zan nuna maka ɓacin raina." Ya dinga tunanin da ya sani ma kansa ya aurawa ba Shamsu ba. Ta haka zaifi jindaɗin saka ido a kanta yadda ya kamata ba wata fargaba. *** "Salamu alaikum wai Tajwidit tazo inji mijinta a waje." Cewar wani almajiri da ya leƙo falon da jama'ar gidan suke wanda yake da ƙofa a waje wurin ajiye motoci. Daga jin Tajwidit dai kowa ya gane wa ake nufi. Sai dai kuma cewar mijinta na kira sai ya sanya musu kokwanto. Dada hankali a tashe saboda Haj. Manga ta labarta mata yadda suka yi da Dr. Madaki da kuma umarnin da ta bawa Arƙam. Ko jiya da suka yi waya Dada ta sake jaddada masa cewa ya zauna to me ya kawo shi yau? Ita dasu Umma shi kaɗai suka sani a matsayin manemin Tauhidat. Shamsu da ya ƙosa ta fito saboda Alh. Audi ya ce ya koma Abuja da ita sai cika yake yana batsewa. Tsaki ya buga da ƙarfin da mazan wurin da ɗan dama sun ji ya tashi yabi hanyar da almajirin ya bi. A ciki ana ta neman ƙarin bayani sai ga ɗan halak ya faɗo musu ko sallama babu. Kallo ya koma kansa shi kuma yana ta rarraba idanu a tsakaninsu har ya hango Tauhidat a rakuɓe jikin bango ta kifa kai tana kuka. Wani dan gantsarewa ya yi shi ba tsayuwa ba shi ba durƙusu na gaisuwa ba ya ce "sannunku, Allah Ya jikan shi." Ya ɗaga hannu ya yafito ta saboda tana jin muryarsa ta ɗago kai a razane "ke taso mu tafi ina da abin yi." Haj. Lami ta kai maƙurar ɓacin rai ta ce "ba za ta tashi ba mara kunya fitsararre. A garinku wannan abin da ka yi tarbiya ce?" "Lami ki ƙyalesu su tafi matarsa ce." Haj. Manga ta sanar dasu. Hankula a tashe suke tambayar yaushe aka daura ta basu amsa da bata sani ba. An dai yi kafin su dawo ƙasar. Ko a jikinsa yana ji ana ta maganganu ya fice yana cewa ta fito ko ya tafi ya barta. A galabaice Tauhidat take zuciya da gangar jiki. Ta miƙe da ƙyar ta ɗauko jakar kayanta ta dawo ta durƙusa gaban su Umma ta sake musu gaisuwa sannan tabi sauran iyayen kowa ta yi musu sallama ta miƙe. Haj. Lami sai hawaye, "Manga kada kice min bari zakiyi a tauye marainiyar nan. Amanarta fa ki ka ɗauka." Kukan Tauhidat tamkar ruwan zafi yake ga Nannanta sai dai zuciyarta ta dake da bakincikin da take tunanin mahaifinta ya kunsa mata. Ga kuma rashin Baffa daga zuwa wurinsu har ana zargin turo shi akayi ba tsautsayi bane. To waye ya turo shi? Abin ya yi mata yawa ita kanta bata san wace igiyar za ta kama ba. "Da na ɗaukota ai tana da uba. Shi uban nata ya fini sonta kuma ya ga wannan rayuwar ce ta dace da ita saboda haka ni dai babu ruwana." Mamakinta ƴan uwanta suke yi. Babu wanda ya taɓa zaton haka daga gareta akan Tauhidat. Ita da akeyi dominta kuwa durƙusawa ta yi gabanta kuka ya hanata cewa komai ta miƙe a sanyaye ta fita. Ba ganin gabanta take yi da kyau ba saboda hawaye sai da ta ɗan jujjuya Allah Yasa ta hango Shamsu a jikin motar da yazo da ita. Tana tafiya ya ƙule da yadda take ɗaga ƙafafu da ƙyar. Ransa ya ɓaci ace wai ita yake jira ba ma ita ke jiransa ba. Cikin zafin nama ya tako da izza inda take ya saki ƙarfinsa ya make mata ƙeya. "Banza jaka, ɗaukarki ki ke so nayi da ba za ki ɗago ƙafa ba?" Taga-taga ta tafi saboda ƙarfin dukan ta yi karo da motar da tafi kusa da ita. Wani raɗaɗii mai azaba ya baƙunci goshinta kuwa. Akan idon Jamal, Mammalo da Papa Abayomi aka yi komai. Ran maza ya ɓaci Jamal bai san lokacin da gargaɗin Nanna yabi iska ba. Kukan kura ya yi ya faɗa kan Shamsu ya turmushe shi a ƙasa yana naushin duk inda ya samu a jikinsa. Papa Abayomi na ƙoƙarin rabasu amma dukkansu majiya ƙarfi ne. Dambe ne ya kaure tsakaninsu. Daga ciki su Haj. Manga suka ji hayaniya ta yi yawa. Suna fitowa suka tarar an raba su da ƙyar amma Jamal sai ƙoƙarin fizgewa yake daga hannun Kawunsa. Kallo ɗaya ta yiwa Tauhidat zuciyarta sai da ta nemi bugawa. Goshinta ya tashi ya kumbura ga idanu sun ƙanƙance kamar gauta. "Jamal zo ka wuce ɗakin Umma ka jirani" ta ce da ƙarfin hali. Huci kawai yake ya girgiza kai "kalli abinda ya yiwa ƙanwata. Kinga yadda ya ..." Yadda ta ɗaga murya wanda bai san me ake yi ba ma sai da hankalinsa ya dawo garesu. "Ita ta iya yiwa nata uban biyayya wato ni ce na haifi wanda bai san darajata ba ko?" Jikinsa ne ya yi sanyi ya dena kokawar ƙwacewa. Alh. Audi ya sami abinda yake so. Ai ba kowa da yake wurin bane ɗan uwansu. Munafukar fuskar da ya saba yi idan yana son nunawa duniya shi na ƙwarai ne ya yi. Muryarsa kamar ta muminai ya soma magana "ban san wannan haɗi zai zo mana da tashin hankali ba da ban fara ba." Wani abokin Baffa ya ce "me yake faruwa ne Alhaji?" Abayomi Alh. Ari ya nuna musu "wannan direbanta ne yazo gidan da marayun ƴaƴansa biyu, Haj. Manga tana ƙaunar yaran musamman macen nan Tauhidat. Shi ne don ya tayata kyautata musu ya ɗauki namijin yanzu haka bayan degree masters yake a Turkey. Ita kuma ya haɗata aure da ɗan cikinsa Shamsu a zatonsa za ta ji daɗi." Wani rausayar da kai ya yi "Allah Ya jiƙan Baffa amma rasuwarsa ce ta lafar da rigimar da take neman tadawa. Da ya bi ta shawarata tun ranar da ta nuna ɓacin ranta da an raba auren kowa ya huta." "Ba ayi haka ba Manga, irin wannan rigimar ma gabaɗaya ba abu bane da ya kamata ayi a bainar jama'a kinji ko. Aure kuma indai mu nan mun isa dake to babu ruwanki da neman a raba shi. Mutum kamar Alh. Audi ya haɗa zuri'a da direban matarsa ai abu ne na yabawa ba kushewa ba." 'Bukatarku ta biya sai ku zuba ruwa a ƙasa ku sha' ta ce a zuciyarta. A fili kuma murmushi ta yi ta matsa jikin Shamsu ta karkaɗe masa kayansa sannan ta buɗe gaban motar ta zaunar da Tauhidat. "Allah Ya baku zaman lafiya." Ta kalli ɓanngaren su Alh. Audi, "Alhaji ka yi haƙuri ajizanci ne. Zan kwaɓi Jamal in sha Allahu ba zai sake shiga hurumin da ba nashi ba." Daga nan ta juya ciki da yawa cikin ƴan uwanta ciki kuwa harda Haj. Lami sun shiga ruɗanin kasa gane me yake faruwa. Bata bari an sake kwana ba ta kira Arƙam da kanta ta faɗa masa halin da ake ciki. Shiru ya yi bai ce komai ba har ta gama bayaninta ya kashe wayar. Theatre ce dashi ya tashi ya shiga. Bayan ya fito kin komawa gidansa ya yi da aka tashi. Sam ba ya son yin wani tunani na Tauhida ta zama mallakin wani sannan mahaifiyarsa ta hana shi zuwa gida bare ya san abinda ya kamata ya yi. Zabi ɗaya ya rage masa shi ne komawa Arƙam ɗinsa na da. Mara walwala, mara shiga cikin mutane. Mai yawan aikin tamkar bai san me ake kira hutu ba. Da ƙuruciyarsa da komai hawan jini ya sarƙe shi saboda ƙuncin da yake ciki ya yi masa yawa. *** Kwanaki huɗu da dawowarsu Tauhidat Abuja. Taji sauƙi amma rayuwarta kamar mutum mutumi. Kayanta kaf Alh. Audi yasa masu aiki suka kwashe daga ɓangaren Haj. Manga aka mayar na masu aiki. A cewarsa ta koma can kafin a gama ginin da ya tasarma yiwa Shamsu a cikin gidan. Nata bai wuce to ba yanzu. Fanna da aka bawa kwangilar kula da lamuran biki ta rasa me yake mata daɗi. Wannan haɗi ba komai bane sai musgunawa ga Haj. Manga da Tauhidat ɗin. Ta dena jin zafinta a rai sai tausayawa. Sai da aka kwana ashirin da rasuwar Baffa sannan Haj. Manga ta dawo gida. Motoci uku manya ke biye da wadda take ciki an shaƙesu da kaya kai ka ce amarya aka kawo. Da yake da rana suka iso duk an ga shigowarsu. Matasa shida ne sanye da riguna masu tambarin wani kamfanin funiture da mata biyu Jamal ya jagoranta cikin gidan. Fanna da fara'a ta tarbesu ta sake mata ta'aziyya. Ita ma fuska a sake ta amsa mata. "Ina fata babu takura Fanna za a yi min aiki a wancan ɗakin." Ta nuna wani babban ɗakin baƙi da yake ƙasa wanda ba kowane irin baƙo Alh. Audi yake sauka a ɗakin ba sai matsayinka ya kai. "Babu komai Hajiya. Bari na tura a faɗawa Tauhida kin dawo. Tana can ɓangaren masu aiki Alhaji ya maidata." "Barta kawai sunfi kusa." Baki galala ta wuce ta bar Fanna. Mukullin ɗakin baƙin ta ɗauko ta buɗewa masu aikin ta umarcesu da fitar da komai da yake ciki. Baho dasu sink da komai na banɗakin ma sai da aka ɓamɓare mata shi. Aiki suke tuƙuru zuwa magariba an haɗa banɗaki da komai sabo sannan an soma haɗa kayan gado. Dakatar dasu ta yi zuwa gobe ta sallamesu. Kayan da aka fitar kuma tasa an kai wani empty ɗakin a ɓangaren ɗakunan baƙi an jibge masa. Lokacin da labari ya kaiwa su Tauhidat cewa Haj. Manga ta dawo ta so zuwa gaisheta mahaifinta ya hana. Da ya ga ta nuna rashin jindaɗi sai ya zauna a kusa da ita ya riƙe hannunta. "Tosin" ya kirata cike da kulawa. "Papa" ta amsa da ƴar ƙwallarta. "Banda Shaheed duk abinda muke yi jigonsa shi ne tseratar da rayuwar wadannan bayin Allah. Kada ki manta da gargaɗin da Alaji ya yi min akan rabaki da ita. Kada ki manta da nata furucin akanki sannan uwa uba duk da na san cewa bisa rashin sani take yi mana haka amma bana jindaɗi. Talaucina bai sa min zama maƙasƙancin da zai yi ta ɗauke kai ana cin zarafin ƴata ba. Tun ɗazu Shamsu yake yawo tsakanin ɓangarensu da cikin gidan. Na tabbata jira yake ki shiga ya wulaƙantaki a gabanta." Kwantawa ta yi a jikinsa a yanzu da ta sake fahimtar waye mahaifin nata. Ko ita da ya haifa tana ganin girma da ƙimarsa ba ta uba ba, ta mutum mai gaskiya wanda bai ɗauki duniya a bakin komai ba bare sonta ya ruɗe shi. Fatanta Allah Ya kawo ƙarshen wannan abu lafiya su koma yadda suke da mutanen da suka zame musu wani bigire mai mahimmanci a rayuwa. Sai wurin shabiyun dare Alh. Audi ya dawo. Yana shigowa wani maganaɗisun ƙamshin turarukan Haj. Manga suka fara ɗibarsa. Wulla idanu ya shiga yi ya kuwa yi sa'ar ganinta zaune ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Doguwar riga ce a jikinta irin ta Morocco da mayafi mai laushi ƙarami ta yane kanta dashi. Beni ba kya tsufa shi ne taken da ya dace da Hafsatu Manga. Ƙananun kitsonta na asalin barebari ya zubawa idanu da basu samu rufuwa ba. Rabon da ya ganta a yanayi na kwalliya irin wannan har ya manta. Zuciya uwar saƙe-saƙe har ta fara tesgunta masa ko neman shiri tazo yi. Ya yi dariya tare da ayyana yadda zai gurza mata aya a hannu kafin ya ɗorata a matsayin da ita kaɗai ta dace da riƙe shi na matar Audi abar tinƙaho a cikin gida da waje. Tasowa tayi tana rangaji, takunta daidai irin na matan da suka san kansu. "Alhaji ina son magana da kai ko zan sami aron minti goma ko kasa da haka?" Jikinsa har wani tsuma yake ya nuna mata hanyar bene, "muje ɗaki don a gajiye nake. Idan na yi wanka sai muyi maganar." Shu'umin murmushi ta yi na gano manufarsa "jeka kawai gobe sai muyi da wuri kafin ka fita." Ba arziƙi ya dawo don kada ya yi biyu babu. Gara ya saurareta ko ya samu hanyar juyata idan yaji buƙatunta. Hanyar dinning ta nufa yana jiran ganin ko ta haɗa masa irin abincin nan nata mai sa mutum a nannauyan sikelin santi sai ya ga wayam. Half-moon medicated glasses ɗinta ta ciro daga gidansu ta saka sannan ta ɗauko wasu manyan takardu ta waresu akan tebur ɗin. Zane ne na gini da aka fidda wanda a haka kaɗai ya gano wuri ne da zaici kuɗi kuma ya yi kyau idan ya sami ingantaccen aiki. Tana daga tsaye shi kuma ya zauna ta soma magana a nutse, "Wannan blue print ne na makarantar da za a gina min nursery da primary. Sunanta Sweet Memories Academy." Ga dama ta samu ya murmusa, "A ina za ki sami kuɗin aiki irin wannan?" Ita ma murmushin ta mayar masa sannan ta ja kujerar gefensa ta zauna. "Audi! Ina so ka saurareni da kyau domin maganar nan yau kaɗai zanyi ta da kai. Idan akasin abinda nake tsammani daga gareka ya biyo baya zan nuna maka Ibrahim bai bar raguwar mace ba, Baffana kuma bai bar marainiya ta tashi da rashin gata ba." "Me ya kawo waɗannan maganganun kuma?" Statement of account ɗinta ta miƙa masa,"ka gani da kyau ko? Hafsatu ta bawa miliyan ɗari baya. Wannan gadona ne da iyayena suka bar min sai kuma kyautatawa da iyalin Baffa suka ƙara min a gadonsu. Da waɗannan kudade zan gina makaranta kuma na kafa kasuwanci domin ƴaƴana." Kafe shi ta yi da idanu har sai da yaji a ransa sannan ta cigaba, "ko da wasa ko a mafarki kada kayi gangancin yi min abinda ka yi akan plaza ɗin Lagos. Babu abinda zanyi a bayan idonka don ba tsoronka nake ji ba. Tuntuɓe idan nayi akan aikin nan sai na shayar da kai mamaki fiye da zatonka. I could be dangerous when I want to." "Ni mijinki ki ke faɗawa irin waɗannan maganganu?" "Ban ma fara faɗa maka ba Audi. Ban dawo gidanka don nayi zaman aure ba. Zuciyata da ruhina sun haneni da barin gidan nan na rasa dalili. Abinda nafi yarda dashi shi ne ko yau ko gobe ko cikin shekaru masu zuwa mayafin da ya lulluɓeni ya min dabaibaiyi zai yaye na kalleka kallo na tonon asiri." A fusace ya miƙe tsaye jikinsa yana rawa da ɓacin rai, "ki kiyayeni fa Manga. Don kin sami waɗannan ƴan kudaɗen shi ne ki ke ganin wuyanki ya yi kaurin da zaki iya yin komai?" Taɓe baki tayi "ko ɗaya. Ina dai so ne mu shata layi daga yau saboda gudun ɓatawa juna rai. Na dawo ƙasa saman kana iya kara aure ka ajiyeta a ciki. Kayan ɗakin kuma suna ajiye ban taba maka ko tsinke ba." Takardunta ta tattara ta ɗan waigo "asirin maƙiyana ya fara tonuwa na ga Arƙam. Allah bai bari yarona ya wulaƙanta ba a inda yake. Jamal da ake son kassara min ta kowane hali shi ma da yardar Allah haka maƙiya zasu gansu shi da yayansa wata rana sun zama ababen kwatance da alkhairi." Ta zare gilashin idonta da murmushi "yauwa kuma tsakaninmu babu saki. Idan ma ka sakeni zan dawo kuma a matsayin matarka dai. So abu mafi dacewa shi ne ka barni muyi zaman ƴan haya kowa yaci gashin kansa. Mu kwana lafiya Alh. Audi." Ta ɗaga masa hannu ta wuce sabon ɗakinta.